Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 10
Mamman.., kallon ta baba lami tayi taji me za tace, ita kuwa yumna bama ta nuna ba taga yaron balle a saka ran za tayi magana wannan yarinya ba dai kafiya da taurin kai ba yawa kafurar farko haka baba lami ta ce a zuciyar'ta afili kuwa sai tace '' yumna ke fa ake kira..?, ajiye wayar ta tayi akan cinyar ta , tace '' baba ai ke zaki bashi amsa bani ba , yanzu ina magana ina saka kafana ina fita hmm labari zai sha bamban zaki kwashe min albarka ne kuce bani da kunya..., inna Hadiza tace '' ta Allah ya kyauta kai jeka kace tana zuwa.., tashi yumna tayi ta saka hijabinta ba wanda ta yiwa magana ta fara tafiya da sauri baba lami tace '' yumna ba zaki dauki daduma ba kullum baki da tunanin karrama bako ki saka mai abin da zai zauna sai ki bar shi a tsaye sai kace wani soja.., Jingina tayi da bango jikin ta duk yayi sanyi zuwa sati me zuwa tasan i yanzu tana gidan Mamman dan haka jikin'ta yayi wani irin sanyi amma zuciyar nan a tsaye take tana nan akan kudurinta tace '' nazeefa jeki, ki dauko min.., tashi nazeefa tayi cikin sauri karta dake ta , ta miko mata amsa tayi ta fita yana zaune akan wani dutsai shifiɗa dadumar tayi ta zauna tace '' gani..., da sauri ya ɗago ajiyar zuciya ya sauke yace '' wallahi ban ma san kin iso ba , ina ta tunani na zata ba zaki fito ba wai masoyiya me ya canza min ke lokaci guda na kasa gane kan ki bakya daukar waya ta ko zanyi kira ɗari ba zaki dauka ba dan girman Allah yumna ki tausayawa zuciya'ta dame zanji ke kiyi innar mu tayi wallahi ina cikin matsala.., kura mai ido tayi ta kasa kiftawa azuciya ta tace kai taga me sauƙi ce ƙasa yayi da kan'sa ya ci gaba da cewa ki tausaya min, ko yaya ta gurin ki na samu rangwami. ajiyar zuciya ta sauke ta dauke kan'ta daga kallon sa da take tace '' Mamman auren mu ina tunanin ba me dorewa bane tun yanzu ka fara korafi jarabawa nake ina son hutu amma kai baka fahimtar haka ko wanne bawa akwai irin tashi ƙaddarar ka dinfa saukaka kanka Ubangiji shi ne masanin gaibu.. da sauri ya ɗago yace '' to shikkenan wallahi yumna ko me kika yi daidai ne agurina bakya taba yin laifi zan jure komai nasan wata ran sai labari.., anya kuwa Mamman ba jinsin mayu bane kai akwai lauje cikin naɗi irin wannan naci haka turkashi ta raya wannan a cikin zuciyar ta , afili kuwa sai tace '' dare yana yi.., da sauri sauri yace '' to dame dame kika tsara ina so naki kudin da zaki yi duk abin da kike so inhar be fi karfina ba .., tashi tsaye tayi ta ninke dadumar ta , tace '' ah barshi wallahi kayi wani abin da bakai ba , bani da bukatar komai ba abin da na tsara, ba abin da zanyi.., saboda me ranar fa farin ciki ce..? limshe idanuwan'ta tayi ta saki sani murmushi wanda ake kira da yafi kuka ciwo tace '' Mamman kenan ni nace kayi abin da ya dace.., tashi tsaye yayi yana karkadai rigarsa yace '' karfa ya zamo abin Magana yumna ace ba kiyi komai ba.., au kenan dan riya zaka bani kudin, da ba dan haka ba ko karfanfana dattin aljihu ba zan gani ba ta faɗa tana tsare shi da manyan idanuwanta. ajiyar zuciya ya sauke yace '' wallahi Allah ko ɗaya kawai dai kinsan halin mutane musamman ma kawayen ki da suke yan duniya kar su dinga ganin kamar bakiyi sa'ar miji ba , bana so a dinga yi miki kallon kaskanci yumna idan ina da hali duniyar nan gaba ki ɗaya ace mallakina ce zan iya mallaka miki.., kallon sa take baki sake tace '' gwara da ka fito fili ka faɗa min abin da ke cikin ranka ka dena boyewa a zuciyar ka, kaga kawaye na ne ni da su kallon da kake mana kenan to ba komai bakomai Mamman akwai can za ayi hisabi wato shi ya saka yan gidan ku suke min wani irin kallo dana kasa fassara shi..., Haba yumna wai me ya saka duk hanyar da na kauce kar na biye miki sai ki ƙara fasa wata ni da baki na , na faɗa miki haka yumna ki dena abin da kike yi kar hakkina ya kama ki.. banza tayi mai ta shiga cikin gida tana kun kuni. Baba lami tace '' yumna lafiya kika shigo kamar an jewoki...?, saita kan'ta tayi domin kar su gane me yake faruwa tace '' tofa na shiga uku gani kika yi an cillo ni..?, kallon kallo suka shiga tsakanin inna Hadiza da baba lami ganin haka yumna ta shiga daki tana dariya tunawa da tayi ta bar wayar ta a tsakar gida da sauri ta fito ɗaukan ta tayi ta shiga dakin su zama tayi ta zuba ta gumi shamsiyya ce ta shigo zama tayi tace '' yauwa yumna me kika shirya lokaci fa yana kurewa ga katin can ma da Mamman ya bani jiya baki taɓa , ba ni nawa har na gama rabarwa kamar wacce bakya son auren nan yumna me yake faruwa..?, afusa ce tace '' uwar ki ce daman tun ɗazu naga bakin ki yana motsi ashe abin da zaki tambaye ni to ban sani ba idan ma wani ya turo ki kije ki faɗa mai duk abin kikai niya yau nake jin bakar jaraba ina cewa ni nakawo Mamman gidan nan ina son sa ....? sai kuma na dawo nace bana son sa saboda bani da hankali ban san me yake damuna ba to wallahi duk wanda ya ƙara tarata da wannan maganar nan sai na gurje mai baki, haba daman tun da na dawo kallon da ake min kenan to yasin zan wasa wuƙa ta wani ya kara tarata da wannan zancen zai ga me zai faru tun da ku baku san zuru ba.., sum sum shamsiyya ta tashi ta fita baba lami ta fito tace '' wai ke yumna me ya saka kin iya neman magana da tujara yanzu da ace tayi abin nan bata neme ki fa Allah ne yasan kadai me zaki yi mata wallahi ki gyara halayen ki gidan wani zaki duk wani datti ki zubar dashi a kofar gidan nan idan kika tafi dashi wallahi ba lallai su raga miki ba , kamar yadda mu muke raga miki ba..., baba lami muna ganin mutuncin ki tun kafin ranki ya ɓaci ki ɓace mana daga gani ko yanzu mu tarwatsa miki ƙwaƙwalwa.. da gudu baba lami ta fita har tana tun tuɓe yumna tana ganin ta fira, ta kwanta tana dariya har da riƙe ciki ta sani sarai idan ba haka tayi mata ba , ba zata rabu da ita ba zatai ta Magana ne ita bata san zuru ba , har sai malam ya shigo ya iske ta , daman ta lura haka take so ɗaga ƙafafuwan'ta sama tayi tace ''maganin biri ɗan katan uwa wace miki barno gabas ce wallahi kafin na bar gidan nan sai na saita muku zaman ku yan durin uwa haka kurum ku takura min da wani banzan zance aita magana ɗaya aure ne , na yarda zanyi to me kuma kuke bukata bayan wannan.., Bayan fitar baba lami dakin inna Hadiza ta tafi ta zauna tana zare ido sai leke take yawa wacce tayiwa sarki karya ganin haka inna Hadiza tace '' lami lafiya naga kina ta gumi..?, hmmm yaya yau ni naga tashin hankali daman ni nasan yarinyar nan wallahi ba ita kaɗai bace shi yasaka take iya shegen da ta ga dama malam be sani ba tsoro na ɗaya na fadawa malam abu ga ɓaci.. Kama haɓa inna Hadiza tayi tace '' me tace miki an shiga uku..?, hmmm ce min tayi zata fasa min ƙwaƙwalwa idan ban fita daga sabgar su ba ta faɗa ƙasa ƙasa domin tana gudu ta jiyo su lamari ya ɓaci.. wani yawu ya haɗiye me ɗaci tace '' mun shiga uku ni wallahi dama yau zata bar gidan nan , taje zan ta ƙarata sai barazana take mana da rayuwar mu daga wancan sai wannan kalli fa abin da tayi mana ƙwanaki Allah ne yayi da sauran kwanan mu a gaba.., Dari biyar ne ba yawa ki biyani hakkin rubutuna karki bari a sato ki karanta... 8141785374 amina Alhasan Muhammad opay Yan niger My nita 1000fcfah Ku turo sheda ta wannan number 08141785374 Dan Allah idan baki shirya ba kar kiyi min magana. Copy is not allowed Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku danna wannan link din sannan kuyi subscribe Dan Allah. https://youtu.be/cDE5bjYY2HY ___________________ https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c Episode 12 Baba lami tace '' wallahi kuwa gwara tatattara ta bar gidan nan ko masa mu sukuni haba wannan masifa haka dame tayi kama.., har karfe tara suna tattaunawa akan wannan matsala ta yumna washegari shamsiyya ta fita tana rabon katim yumna tun da ta fita yumna take Allah Allah ya dawo ta, taci uban'ta tun da ta faɗa mata bata ji ba to za tayi maganin ta. tamkar wacce tayiwa sarki karya haka ta ɗinga za gaye tana kaiwa tana komowa su inna Hadiza ido ne kawai nasu. domin lamarin yumna sai addu'a har wajen azahar tana wannan kaiwa tana komowa domin yau dole ta hukunta shamsiyya dan uwar baban ta. Assalamu alaikum da sauri ta fito jin sallamar shamsiyya sai dai wani abu da be mata dadi ba tare suke da malam dole tayi saranda ja da baya tayi malam yace '' yumna ashe baki da lafiya yanzu yar uwarki ke faɗa min me , me ya saka tun da wuri baki faɗamin ba.?, ƙasa tayi da kan'ta tace '' naji sauki ma bakamar lokacin da na tashi ba.., zama yayu cikin kulawa yace '' meke damin ki..?, yumna tace '' zazzaɓi da ciwon kai ne amma alhamdulilah yanzu naji sauki., to Allah ya ƙara sauki, amin ya Allah tace. tashi yayi yace '' shamsiyya jeki ki dauko min allo nayi mata rubutu.., shamsiyya da , daman tana tsaye tun da ta shigo ta kalli yumna tasan yan bala'in sun motsa. shiga dakin sa tayi ta dauko mai allo yumna ta shinfiɗa mai tabarma zama tayi a kusa da shi rubutu ya zauna yana yi jefi jefi yana tambayar ta ko tana da , damuwa. yana tausayin rayuwar ta sosai saboda bata da uwa shiɗin ba mazauni bane balle ya san me yake faruwa duk da yasan halin yar tasa ba kanwar lasa bace. yumna bata nuna mai akwai wata matsala ba da ya gama ya wanke ya bata , tasha amsa tayi tasha suka ɗan yaɓa hira ana kiran sallar magariba ya fita ita kuma, ta tashi tayi sallah, bayan ta idar ta kwanta a tsakar gida tana jij Radio da wayar ta zama kusa da ita shamsiyya tayi sarai ta ganta sai tai kamar bata ganta ba ta ci gaba da jin radio ta idon ta a rufe yaran gidan suka ta wasan jakai kwarai yumna tayi lafiya da , dane tun da ta fito tsakar gidan nan , ba wanda zai ƙara wani kwakkwaran motsi idan kuma mutum yayi taurin kai tofa jikin'sa zai faɗa mai. tana cikin jin radio shazali dan gidan baba lami ya faɗi mata aikuwa yaci ubansa domin duka tayi mai tas tare da han kaɗa shi, taja tsaki ta koma saki ta kwanta. baba lami tana jin ta amma batayi ƙoƙarin magana ba domin ba mutunci za tayi mata ba. washegari shamsiyya ta dinka musu kayan su da yake ta iya ɗinki yumna ce dai bata iya ba saboda ita bata ga me za tayi da sana'ar basir ba. bayan ta gama ta kai mata wajen kayanta ta ajiye. haka rayuwa taci gaba da wakana yau ana sauran kwana ɗaya daurin auren su kowa ya zo na arlit amma ban da ahlam da juraij hakan be wani bawa yumna mamaki ba tun da tasan shi dai ba mutunci ya cika ba , shi da matar sa biyu ce ta haɗu shi ba mutunci haka ma ita, juhud ma bata zo ba sai yusrah sai mommy da kakarta tawajen uwa sosai suka nuna mata gata domin ko dinki ɗaya bata saka ba akayan da Mamman ya kawo mata. zazzabi ne ya rufe ta fa'iza da nana suna tare da ita fa'iza ce tace '' wallahi yumna banga bin damuwa ba duk kinbi kin takura kanki ke wallahi ki godewa Allah ma zakije kici yancin kanki.., murmushin tayi, ta gyara kwanciyar ta zuciyar ta ba dad'i in banda tsabar rashin hankali wanne cin yan cin kai ce mata aka yi anan gidan, ba tacin yan cin kan'ta. ita wannan ciwon bawai na damuwa bane tana ganin bakwan watan ta dab yake da zuwa cikin ta ma ciwo yake , tashu tayi ta dafe kan'ta tace '' dan Allah cewa mommy bani da lafiya kaina ciwo yake da ciki na.., tashi fa'iza tayi ta fita ba jimawa gabaki ɗayan su , suka zo har da yusrah. mommy tace "subbanallahi tun yaushe ne baki ɗa lafiya amma kikai shiru da bakin ki...?," amai ne ya taso mata da sauri ta fito tsakar gida ta dinga kwara shi kowa sannu ya dinga yi mata bayan ta gama mommy ta wanke mata jiki kamata tayi suka shiga daki ta kwantar da kan'ta a cinyar kakarta tana sauke a jiyar zuciya daman haka period ke mata , bata mata , ta dad'i baka ramar wahala take sha ba. magani mommy ta bata , tasha bacci ya dauke ta kamu ba , ba ai yi da ita ba saboda ba lafiya sosai take jin jiki, washegari RANA bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya. sosai mutane suka taru daga gari daban daban domin malam na mutane ne ga kuma mahaifin Mamman alhaji Dauda me wuƙa sarkin fawa, masallaci ma kasa daukan mutanan yayi wasu suna waje daurin auren shamsiyya aka fara sannan na yumna lokacin da me shela ya sheɗa an daura auren ta ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba , tuni ta fara kwara a mai jikin ta ya zugage tas mommy ce ta gyara ta tare da bata magani bayan an gama MAMMAN da saurayin shamsiyya suka shigo domin gaisuwar surukai sai a lokacin ma ya ga bata da lafiya sosai ya tausaya mata . bayan ya fita ya koma gida mahaifiyar sa sai cika take tana batsaiwa. ko gaisuwar'sa bata amsa ba. wannan kenan da misalin karfe biyun suka tafi sukai mata jere dole sai da aka dawo da kaya da yawa saboda daki daya ne da ban daki sai kitchen shima ba wani babba ba yusrah tace '' kinga ko abin da nake faɗa miki yanzu ya za kiyi da wannan kaya..?, Mommy tace "'siyarwa zanyi na bata kudin sa mata wani amfanin taja jari..," shiru yusrah tayi bata ce komai ba Hajiya anni kakar mahaifiyar ta , tace '' aikuwa kin kyauta Allah yayi albarka..., amin tace da misalin karfe Biyar Na Yamma mommy ta shirya yumna cikin wani lece pink colour ba ƙaramin kyau yayi mata ba duk da saboda da cutar da tayi ta zabge ta rame lokaci ɗaya. nasiha tayi mata kuka kawai take yi share hawaye bayan ta gama yi mata faɗa ta haɗa su, su da shamsiyya ta kara yi musu sannan malam da su inna bayan sun gama daman masu daukan amarya suna jiran su yumna da ta fito sai da ta juyo ta kara kallon gidan su hawaye ne suka ƙara zubo mata , da kafar dama mommy tace ta shiga cikin motar. shiga tayi ta kifa kanta ta ci gaba da kuka. har suka isa nan ma da kafar dama mommy tace ta shiga batai musu ba ta shiga da ita kai tsaye gurin mahaifyat sa , suka nufa sallama su kayi kanwar sa hindatu ce ta amsa amma innar su Mamman ko nunawa ba tayi ba tasan da tsayuwar su. shigowa su kayi wasu suka tsaya a waje mommy tace '' barka da yamma ya taro..?, dakyar tace '' barka dai alhamdulilah.., sosai mommy take mamaki to ya akai bata san da wannan matsalar ba , da baza ta bari ayi auren nan ba , kar ta takurawa yumna danne abin tayi tace '' masha Allah to ga amana nan mun kawo miki duk.. ai bata karasa ba tace '' da kata ban amshi wannan amanar ba dan haka ku tattara ƙafafuwan'ku ku fitar min daga daki kafin ba gurza muku tashin mutunci. tashi su mayi yumna tamkar zata fadi saboda tashin hankali daman fa'iza ta dade tana faɗa mata innar su hindatu bata da kirki sai yau ita tashe da , da maganar fa'iza a gaban jama'a ta tozarta ta lallai jiya ba yau ba , ban da tayi sanyi yasin sai dai ta saka danta ya sake ta daman haka take bukata. dakin ta suka kaita sosai mommy take cikin ɓacin rai faɗa ta kara yi mata tai mata sallama su fa'iza ma ba jimawa suka tafi. zazzabi ne ya kara rufe ta da gudu ta fito tana kwara amai tamkar zata amayar da ya'yan hanjin ta innar su hindatu fitowa tayi ta kama kugu tace '' wallahi ba zata sabo ba daman da ciki kika shigo min cikin gidan ɗana.., ba karamin daga mata hankali wannan maganar tayi ba da sauri ta ɗago lokacin Mamman ya shugo yana baza babbar riga jin abin da mahaifiyar sa tace da sauri ya ƙara so cikin ɗaga murya da faɗa tace '' gata nan ta shigo maka da ciki cikin gidan ka dan haka wallahi sai ka saketa ba zan yarda ba ta zauna min da cikin shege a cikin gidan nan ji yadda ta ɗashe tayi fari anzo za'a cuci ɗana ayi laulayi a gidan sa dan kirufawa kanki asiri kawayen ki ba ƙananan karuwai bane dan haka kaji na rantsai maka idan baka saketa ba sai na tsine maka kuma saki uku nake so kayi mata domin wa'yannan mayu ne tsaf ubanta zai ƙara rubuce ka akan sai ka sake ta ga yarinyar nan yar mutunci na kawo maka amma kaki ka aura ka ɓuge da aurar ragowar titi.., ji yayi kan'sa ya sara mai shi ba mace bane balle ya iya tantance abin da innar sa take faɗi amma tabbas duk abin da ta faɗi gaskiya ne shima kan'sa kyan da yumna tayi ba ƙaramin mamaki yake bashi ba sai kawai ya barshi a gyaran jikin da aka yiwa amare ne shi ya mai data haka baya zargin yumna ya yarda da tarbiyar ta amma ya ya iya mahaifiya ba wasa ba. hawaye ne yake zubowa a idanuwan'ta tace '' be kamata ba dan bakya sona kiyi min wannan ƙazafin ba , ko da ace Mamman zai sake ni karka sakeni da wannan baƙin tabon da har abada ba zai taɓa gogewa ba a idanuwana da zuciyar'ta kina da ya'ya mata kin haifa be kamata ki jefeni da wannan kalmar ba. wata uwar buda ta saki tace '' au Allah maza saketa ina gani kuma ta taso na kaita har gidan su na shedawa kowa abin da , ta aikata.., Mamman dakyar ya iya haɗiyar yawu ganin yayi shiru innar sa ta saka kuka tare da kakorin tsine mai da sauri yumna ta girgiza kan'ta tace '' Mamman bakomai karka bari saboda dani ka ɓata lahirar ka , komai me wucewa ne wallahi.., a hankali ya furta na sake ki saki biyu.. share hawayen ta tayi ta tashi ta shiga daki mayafin'ta ta dauko ranar daurin auren ta an sake ta saki da ashe daman haka yake da ciwo ashe daman jin sa kawai take abaki amma wata zuciyar'ta ta murna take wata na bakin ciki saboda da bakin tabon da aka sake ta dashi. a daidai nan mahaifinsa ya zo hindatu ta kira shi saboda abin da yake faruwa. yana zuwa inna ta kora mai bayani tabbas ga amai nan amma yace '' ke kin tabbatar da wannan zargi tabawa kiji tsoran Allah Ubangijin fa baya yafe hakkin wani akan wani idan kinyi haka ne domin ki tozarta su wallahi Ubangiji zai jarabbe ki ta inda ba kiyi zato ba.., a dai-dai nan yumna ta fito tana saka mayafi mahaifinsa yace '' ya'ta koma ki kwanta gobe sai mu yi magana..., na rantse da Allah sai ta tafi ta zauna tayi me a cikin gidan nan..?, tashi yumna tayi ko gaban ta bata iya gani ta fita Mamman kuwa ya zama tamkar wani mutum mutumi, dakyar take iya tafiya ikon Allah ne ya kawo ta gida amma ba dan haka ba , da tuni wani zancen ake yi malam yana zaune asoro shida mommy suma magana ta shigo da yake akwai hasken fitila da sauri mommy ya zaro idon'ta tare da dafe kirjin ta da yake dukan uku uku malam kuwa daskarewa yayi dakyar ya iya cewa yumna me ya dawo dake..?, ɗurƙusawa tayi tana kuka tare da shashsheka ta kasa magana ganin haka mommy tace '' malam mu shiga daga cikin dakin nan na zaure har yanzu akwai mutane a cikin gidan nan wasu ma kwana za su yi. tashi yayi jikin sa duk a sanyaye ya buɗe dakin su hafizu shiga su kayi mommy ta ƙara mai maita mata tambayar dakyar yumna ta iya cewa sakina ta saka yayi saki biyu na fito ina amai tace cikine dani salati mommy ta saki shikkenan magana ta ƙare innalillahi wainna ilaihir raji'un haka suka shiga maimaitawa mommy tace '' Allah ya isa tsakanin mu da ita yarinyar da take al'ada wanne ciki insha'Allahu akan ya'yanta zata ga ciki alfarmar annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama sai dai ta gani akan nata badai akan kiba, ni daman tun da ta iya rufe ido ta ci mana mutunci nasan bata da imani bata da tsoron Allah yanzu maganar da muke yi da malam kenan a cikin daran nan a ranar da aka daura muku aure ta saka a yi miki wannan sakin hulakancin gaskiya matar nan bata da imani ko yan baki ba su soma watsewa ba insha'Allahu yumna sai kin zama wata makaranta kawai zaki koma da zarar takardun ki sun fito ta mai dake ƙaramar bazzawara., malam kasa cewa komai yayi ko da ya tashi binciken Mamman da man ance mahaifiyar sa tafi karfin mahaifinsa ashe kuwa haka abin yake da ya sani ƙeya da be haɗa wannan auren ba dama ya bar yarsa tun farko da ta nuna bata so bakomai haka Allah ya tsara daman auren su na wani lokaci ne , duk da ba'a shedar ɗan yau amma yasan halin kowa daga cikin ya'yansa ita dai yumna barta da daukan magana amma wallahi baya zarginta balle gashi nan ance ma al'ada take yi wannan mata ta cuce su bakomai Allah yana nan ma dakata. dakyar ya iya cewa yumna kiyi hakuri kiyi hakuri kiyi hakuri Allah yana tare da me gaskiya wata ran zatai nadamar abin da ta faɗa miki kafin su hafizu su zo ku tashi ku koma cikin gida.. da sauri mommy tace '' a'a duk da dare yayi kawai mu koma gidana ai haka kamar tozarta kai ne.., haka ne wallahi Allah ya rufamana asiri amin mommy tace ta tashi ta shiga yusra ta kwaso muku kayan su suka fito daman tun ɗazu kaka ta tafi buɗe Boot tayi ta zuba kayan sannan ta rufe. yusra ta shiga gidan gaba saboda ita zatai tukin daman ta matsu su tafi so take yi ta ganta a gidansu amma mommy tace ba yau ba sai gobe sub koma gidan yumna zuwa jibi su tafi. tamkar an warke ta daga Makanta taga mommy ta kamo hannun yumna ta buɗe baki za tayi magana mommy ta hade rai ta buɗe gidan baya ta shiga ganin haka itama ta tsuke bakin ta kwantar da kan'ta tayi a cinyar mommy tana kuka zazzaɓin jikin'ta ya ƙara tsanani ba irin abin da yumna bata saka aranta ba wayar ta da take makale da ita a cikin zaninta ta ciro tace '' mommy ajiye min.., cikin tausayawa mommy ta karɓar ta ajiye mata ba karamin tauyasin yumna take ji ba , dan ma yarinyar tana da karfin zuciya da wata ce faɗuwa za tayi idan ta ji wannan zance. sai karfe goma suka isa me gadi ya buɗe musu gate lokacin juraij ya dawo daga aiki shima turus yayi ganin

Chapter 7 of 10