Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 10
yumna ta fito abinka da babban gida ga wadatar hasken wutar lantarki tamkar rana jikin sa a sanyaye ya ƙara so yace '' mommy sannun ku da zuwa..?, Yauwa juraij yanzu ka dawo.. Eh wallahi yanzu na dawo nama biya ta gidan su ahlam jikin nata da sauki ba kamar jiya ba. Mommy tace '' to Allah ya kara sauki nama kirata ɗazu naji ya jikin ta wayar ta a kashe.., insha'Allahu zan faɗa mata kallon yumna yayi zai wuce mommy tace '' juraij ina son ganin ka.., gaban sane ya faɗi amma sai ya dake yace '' to mommy.., buɗe motar sa yayi ya ajiye kayan da ya dauko ya bi bayan su. lokacin mommy ta shiga daki yusra ta hau sama domin bacci take ji yumna ce a zaune a parlour be bi takanta ba ya nufi bedroom din mommy sallama yayi tana zaune ta rafka uban tagumi sai ya ya kara magana sannan taji shi. da sauri ta ɗago tace '' juriaj ashe ka shigo, zama yayi a ƙasa ya tankwashe ƙafafuwan'sa yace '' mommy me yake damin ki naga kin yi tagumi Allah ya saka lafiya wallahi na shiga tashin hankali sosai dana ganki a cikin wannan hali.., ajiyar zuciya ta sauke tace '' juraij wallahi ina cikin matsala kai kaɗai ne zaka iya fiddani a cikin wannan matsalar taufiq baya nan yana karatu da shi zanwa magana.., kallon ta yake cikin mamaki domin be san ina zancen ta ya dosa ba temako kuma yau mommy ce take neman temakon sa to duk yadda aka yi ba ƙaramin abu bane wannan dan haka yace '' mommy Dan Allah ki faɗa min me ke damu ba ki..?, ajiyar zuciya ta sauke ta share kwallar da take ƙoƙarin gangarowa a kurmin idon'ta tace '' yau an daurawa yumna aure a yau uwar mijinta, ta saka aka sake ta daman tun daga tarbar da tayi mana wallahi nasan ba mutuniyar kirki bace.., gumi ne ya shiga yanko mai ya shiga uku yasan yanzu haka shi momy zata ce , ya auri yumna ba zai iya adalci ba , ba zai iya haɗa ahlam da ko wacce mace ba , ba zai iya ba ji yayi ya shiga cikin wani irin hali wanda ya kasa fassara shi to wacce siga. tissue ta yago ta share hawayen ta tace '' kai nake da yaƙinin zaka iya riki min amana ko bayan raina ba zaka taɓa iya tozarta yumna ba , taufiq yana da wata dabi'a da wani hali ba ko wanne abu ya ke so ba , idan na tursasashi ba lallai yace min ba zai iya ba amma abin zai dinga ci mai rai ƙarshe ya haifar mai da wata lalurar kai nake da ya ƙinin za ka iya yi min wannan aikin kai zaka iya riƙe min wannan amanar duk da ba lallai ka amsa ba amma ka riƙe min ita ina so ka aure yumna tun da be ɗora mata idda ba habawa ji yayi tamkar an dauko ringimeman dotsai an ɗora mai akan zuciyar'sa ina bazai iya ba duk ba ba zai iya yiwa mahaifiyar sa musu ba amma ba zai iya yin adalci ba ƙasa magana yayi tun da ya sunkuyar da kan'sa ƙasa be dago ba har ta gama zancen ta bakin sa na rawa yace '' mommy auren ta zanyi...?, kai ta gyaɗa mai , baya son zubar hawayen mahaifansa baya son abin da zai saka tayi kuka yana da kuma maganin damuwar ta , ya saka yi mata bakin sa na rawa yace '' mommy ki gafarce ni bazan iya auren ta ba , saboda Muhsin yana son ta ba zan iya zama da abin da aminina yake so ba ina da yaƙinin Muhsin zai iya riƙe wannan amanar wallahi tun da ya ganta yake min maganar ta sai da na gaji na faɗa mai an mata miji duk da haka be hakura yanzu haka yau da nake ce mai yau ake ɗora mata aure wallahi yana kwance akan gadon asibiti idan aureta ban mai adalci ba hakika na cika bakin amini wata kila ma hakan ya kawo karshen alakarmu saboda so mugun abu ne zai iya haɗa mu duk irin amintar da take tsakanin mu dan Allah mommy karki ce ban bi umarnin ki ba amma me zai hana taci gaba da karatun ta yadda zata iya dogara da kan'ta zata tallafi rayuwar maraicinta har Allah yayi abin da ya tsara.., ya faɗa yana riko hannunta tare da goge mata hannunta. Mommy kasa magana tayi wannan ita ake kira da tsaka me wuya taso ace yumna ta auri Juraij daman tun farko shi taiwa sha'awar'ta sai kuma ya kawo mata ahlam ba yadda ta iya ta amince da auren ta tabbas ba za ta ita tauye mai hakkin sa ba duk abin da ya faɗi gaskiya ne zata bar zancen auren nan Allah ya zaɓa mata abin da ya fi alkairi dakyar tace '' bakomai wallahi Juraij Allah yayi maka albarka ya shige mana gaba daman nima cewa nayi ko a dakin mijinta ta ci gaba da karatu amma wannan abin har abada bazai bace mata a rai dan Allah ku jata a jiki ku hanata zaman kaɗaici duk abin da za tayi karku kyareta sai abu yayi mata yawa ku bita a hankali komai yana da lokaci komai zai wuce tamkar ba ayi shi ba..., insha'Allahu ya fada yana tashi ba karamin sanyi yayi ba lokacin da ya samu nutsuwa da amincewa da tayi da maganar sa.. Copy is not allowed Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku danna wannan link din sannan kuyi subscribe Dan Allah. https://youtu.be/cDE5bjYY2HY ___________________ https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c Episode 13 sai da safe yayi mata ya fita har zuwa lokacin yumna tana kwance akan kujera ta , takure guri ɗaya. wuce ta yayi ya fita tana ganin fitar sa ta miƙe ba karamin bacci take ji ba dai-dai lokacin mommy ta fito kama hannunta tayi ta kaita har dakin ta , wanda da aka sauketa a cikinsa kwanciya tayi akan gado tare da yin addu'a mommy ta ja mata kofa rufe idanuwan'ta tayi zuciyar ta na mata wani irin suya , bawai bakin ciki take da Mamman ya sake ta ba a'a daman abin da take nema kenan kuma sai ta samu, babban bakin Cikin da sharrin da mahaifiyar sa tayi mata , ba zato taji hawaye na bin kuncinta sharewa tayi ta gyara kwanciyar ta ranar yadda taga rana haka taga dare zazzaɓi ne ya ƙara rufe ta ko iya daga idanuwanta bata yi ga ciwo da kan'ta keyi tamkar zai fashe gida biyu. ji tayi anyi knocking kofar ta , ba damar tayi magana tayi shiru ko da aka turo kofar ko iya ɗaga kai bata yi ashe mommy ce ,, zama tayi a kusa da ita Alhaji yace '' yumna ya jikin naki..?, dakyar ta iya cewa Alhamdulilah da sauki.. sosai ya tausayawa yarinyar saukar sa kenan a ƙasar mommy take bashi labari shine ya shigo domin ya duba ta ,, kwalla mommy ta share tace'' Alhaji anya kuwa ba za'a kaita asibiti na , jikin nata yayi tsanani..?, Alhaji yace '' tun da ga taufiq nan ya dawo, ya duba ta da ace juraij be tafi wajen aiki ba da shi ya kamata ya duba ta tun da daman ɓangaren mata ya karanta. ajiyar zuciya ta sauke tace '' to bara na kirawo shi Allah ya saka be kwanta wannan shegen baccin nasa ba , yawa na mutuwa.., zauna ki kula da ita,zan kirawo shi to tace ta shafa kan yumna da yayi zafi raɗau tamkar garwashin wuta. cikin tausayawa tace '' yumna sannu me yake damun ki..?, kasa magana tayi sai bakin ta da yake rawa alamun tana so tayi magana ba halin yi hawaye mommy ta share mata , tace '' kiyi hakuri akwai Allah, komai yayi zafi maganin sa Allah.., kai kurum ta gyada da kyar, ta riƙo hannun mommy Assalamu alaikum.. da sauri mommy ta juyo jin muryar taufiq tace '' wa'alaikas'salam.., ƙarasa shiguwa yayi yana cire medical glasses din'sa yace '' wannan ce mara lafiyar..?, mommy ta kalle sa tace '' eh.., dan jim yayi sannan yace '' mommy ban tawo da komai ba ko , kayan sawata ban tawo da su ba , tun da na san ina dasu anan sai dan abinda zan yi amfani dashi, dashi na tawo , ko za aku kaita asibiti naga jikin nata yayi tsanani.., tashi mommy tayi tace '' dauko mota ka kai mu.., to yace ya fita Alhaji ya ci karo dashi yayi mai bayani yace to ba damuwa ya dauko ya kai su bayan ya gama dai-dai ta parking din'sa, ya dawo daukan ta yayi domin ba zata iya tafiya ba har cikin mota ya saka ta mommy ta shiga suka fati kai tsaye asibitin da yaza mo mallakin juraij wato J.M international hospital suka isa cikin gaggawa suka amshe ta saboda yanayin jikin nata kai tsaye emergency room suka shiga da ita. mommy jin gina tayi da bango taufiq yace '' mommy me ya haddasa mata wannan ciwon ne..? , zama tayi akan waiting chair tace'' taufiq labarin yana da yawa mudai samo kan'ta sai nai maka bayani.., jan bakin sa yayi ya tsuke ya zauna kusa da ita. Wannan kenan AGADEZ karfe goma malam ya shirya domin zuwa gidan su Mamman yaji ba'asin abin da ya faru har kawo i yanzu ba wanda yasan me yake faruwa da yaji nazeefa tana cewa zata gidan yumna hanata yayi yace shi baya son irin wannan daga yin auren har zata fara sintiri ko gidan shamsiyya be yarda ta je ba. yana gama fadar haka ya fice kai tsaye gidan su Mamman ya nufa bayan ya isa ya aika yaro ace yana sallama da mahaifin Muhammadu.., shiga yaron yayi ya fara rangaɗa wata uwar sallama yace '' wai inji malam NURA me sittin yana sallama da baban Muhammadu.., Innar su hindatu da take gaban wuta tana dumamen tuwo tace '' je ka , kace mai baya nan.., da sauri sarkin fawa ya fito yana cewa haba tabawa me ya saka kike haka ne tun da dai kin raba auren nan hankalin ki , ya kwanta ai sai ki ci wake ki sha ruwa kaf garin nan ana darajja malamin nan amma shi ne kika ce a faɗa mai haka..?, tamkar da dutsai yake magana bata dago Kai ta kalle sa ba girgiza kai yayi ya fita yana saɓa babbar riga a kafaɗa. samun malam yayi yana tsaye a kofar gidan nasa gaisawa sukai sannan yace '' bisimallah shigo zaure..., Malam yace '' a'a barshi nan ma ya isa.., Allah annabi yayi mai sannan ya shiga ba yadda ya iya daduma ya shinfida mai suka ƙara gaisawa sannan malam yace '' naji wani abu to domin na tabbatar shi ne na zo naji gaskiyar magana me ya faru yumna tace min Muhammadu ya sake ta..?, kunya ce ta rufe Sarkin fawa kan'sa yana ƙasa yace '' to, haka Allah ya nufa daman auren ba me dadewa bane, mahaifiyar sa , ce tace ya saketa wai saboda ta shigo mai gida da ciki Allah shi ne masani wallahi dole tai mai ya sake ta , ba yadda ya iya , wallahi nauyin ka ne ya hani zuwa na same ka mu tattauna amma insha'Allahu zan wa tubkar hanci da yardar Allah zata dawo dakinta saki biyu yayi mata , abin da nake zargi daman bata son ta shi ya saka tayi mata wannan sharrin.., kai kurum malam ya jinjina yace '' Allah ya saka hakane yafi alkairi bakomai Allah zai fitarwa da kowa hakkin sa alhamdulilah tun da kun gane ba haka bane ba damuwa ,ko za ku iya bani takardar ta.., dan Allah kayi hakuri nasan ba akyauta muku ba wallahi ba yadda zanyi cewar sarkin fawa. murmushi malam yayi har yanzu kamilar fuskar sa bata nuna damuwa ba ko ɓacin rai yace '' ba damuwa Allah ya yafe mana baki ɗaya.., godiya yayi mai ya ci gaba da cewa bara naje na saka shi ya rubuta takarda. to malam yace mai yana jiran sa be jima ba ya fito amsa yayi, yayi mai sallama ya ta fito yana tafiya tana zancen zuciya abin duniya duk ya ishe shi, maganar mutanen gari ma ta ishe shi, ace aure daga kwana ɗaya anyi saki to bakomai yasan Ubangiji jaraba shi yayi ya gwada imanin sa , Allah ya bashi ikon cinye wannan jarabawar har ya isa gida be dena tunani ba. koda ya isa a waje ya zauna yana karatu almajirai suka zauna yana karbar haddar kowa tare da ƙara musu wani sosai yaji zuciyar sa tayi sanyi tabbas Alkur'ani waraka ne , maganin damuwane al'ummar annabi mu dage da ibadar Allah. ko dan muga haske a cikin rayuwar mu. ##### Sai karfe 1:40 aka fito da ita an saka mata oxygen sannan an ɗaura mata drip a hannunta kai tsaye daki suka shiga da ita mommy za tabi bayan su taga Juraij ya fito ashe dashi aka shiga ba ƙaramin mamaki tayi ba da ganin sa da tayi saboda ɗazu bata ga an shiga da shiba tace '' juraij daman kana ciki..?, cire glove yayi matsawa yayi kusa da wani automatical dustbin tuni ga buɗe ya jefa su yace '' kirani su kayi akwai wata kofa a baya tanan na shigo.., nifa ince ya jikin nata..? juraij yace '' da sauki damuwa ce tayi mata yawa amma insha'Allahu zuwa anjima zata warware.., to Allah ya yarda mommy ta faɗa tana shiga world din da aka kai yumna tura kofa tayi taufiq ne zaune yana danna waya zama tayi a kujerar da take facing din sa tace '' bata farka ba ko..?, ɗagowa yayi ya kalli yumna da take kwance yace '' a'a ko motsi ba tayi ba , amma wani likita yace min sai nan da karfe biyar zata farka sun mata allura ne.., ajiyar zuciya ta sauke tace '' Allah ya kai mu darai da lafiya.., amin ya Allah ya faɗa yana tashi zura wayar sa a aljihunsa yayi yace '' mommy ni zan tafi zan turo miki yaran nan sa taya ki zama wallahi wani irin bacci nake ji duk na gaji.., Wallahi kuwa akwai gajiya yau ka sauka kuma kuma baka huta ba , Allah dai yayi albarka sai dai in yusrah juhud yanzu haka nasan ta , tafi gurin aiki, itama yusrah ko ta tafi makaranta Allah masani. Cikin kaunar mahaifiyar tasa yace '' amin ya Allah to zan dai duba na gani duk abin da ake ciki za kiga nayi miki waya ya jikin ahlam..?, mommy tace '' da sauki hice ko ka kirawo ta..?, shafa sumar kan'sa yayi yace '' eh na kirawo ta maman su ce ta ɗauka tace tana bacci amma zata faɗa mata.., To Allah ya ƙara sauki ciki ne me laulayi ga haɗo da rashin lafiya kullum ba lafiya wallahi tun ina ganin yarinyar nan lanjarewa take har kuma naga ashe ba lanjarewa take ba cutar ce Allah dai ya raba lafiya haka wani cikin yake sai ranar da aka sauke shi ake samun sauki amin ya Allah yace yana fita daga cikin dakin. AGADEZ kamar ance mai ya ɗaga idanuwan'sa ido hudu yayi da zaliha jikar hajiya rakiyar mahaifiyar marigayya da flask a kanta da wani a hannunta gaban sane ya faɗi bayan shi da Hajiya zainab ba wanda yasan da mutuwar auren yumna ba mamaki abinci tayiwa yumna za akai mata gidan ta , share zuba yayi be san ya zai yi ba , baya so mutuwar auren yumna ta fito yanzu duk da yasan koman daren dadewa dole abin ɓoye ya fito sarari. shiru yayi yana tunanin mafita duk hanyar da yabi sai yaga ba me bullewa bace baya so hajiya tasan da zancen nan kodan shekarunta sun ja zata iya shiga ko wanne hali. yana cikin wannan tunanin zaliha ta ƙaraso ba zato yaji tace '' malam ina wuni..?, wani irin dam kirjin'sa yayi dakyar ya iya dagowa ya kakalo fara'ar dole yace '' lafiya qalau ya jikin Hajiya..?, zaliha tace '' alhamdulilah wallahi da sauki ɗazu ma ta sha magani, abinci tace na kawo idan akwai wanda zai ke gidan aunty yumna sai mu tafi tare da shi.., Malam yace '' to masha Allah, Allah ya ƙara sauki a'a ba wanda zai je, amma kawo a ajiye idan akwai me tafiya sai na bashi ya kai mata kice ina godiya, ina yi mata kuma ya gajiya.., ajiyewa zaliha tayi tace '' to insha'Allahu zan faɗa mata.., kuɗi ya ciro a aljihunsa ya miƙa mata kin amsa tayi sai da yayi mata jan ido sannan ta amsa tana yi mai godiya ta bar gurin. ######### Misalin ƙarfe biyar dai-dai yumna ta farka buɗe idanuwan'ta tayi lokacin mommy da su juhud suna hira a hankali ta saka hannu ta cire oxygen din da aka saka mata da sauri mommy ta tashi tana cewa a'a yumna karki cire. tashi tayi dakyar tace '' mommy mu tafi gida naji sauki.., yumna ya jikin naki..? cewar taufiq da yake facing din ta da sauri ta ɗago jin wata murya da ba , taɓa jin ta ba kallo ɗaya tai mai tasan dan mommy saboda kamar da taga yana yi da ita a hankali tace '' da sauki.., TAUFIQ yace '' Allah ya ƙara sauki..., jingina tayi a bango tace amin.. mommy tace '' taufiq kirawo JURAIJ kace ta, tashi.., tashi yayi yace '' to.., fita yayi kai tsaye office din Juraij ya nufa sai da yayi knocking sannan ya bashi izinin shugowa shiga yayi ya zauna a kujera yace '' yaya yumna ta tashi yanzu tama cire oxygen din da kuka saka mata.., kwafa yayi yace '' yarinyar nan bata ji wallahi daman nasan zata iya aikata haka ..., yaya wai me ya faru da ita ne har ta shiga wannan hali..? cewar taufiq. Juraij yace '' nima ban sani ba ka tambayi mommy mana.., Copy is not allowed 🚫 Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku shiha wannan link din sannan ku danna min subscribe Dan Allah. https://youtu.be/cDE5bjYY2HY ___________________ https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c Episode ¹³ Hmm tace min sai ta gama warware wa zatai min bayani abin da yake faruwa. tashi juraij yayi yana cewa amma kazo kana tambaya ta , ashe ma tace zata baka labari har yanzu baka dena halinka ba nason jin zance ni wallahi dama karatun jarida su mommy suka tura ka ba karatun likitanci ba domin dashi ya dace dakai. dariya taufiq yayi yace '' wallahi kawai abin ne ya dame ni shiyasa nayi magana yarinyar ta shiga raina, musamman ma dana ji saboda damuwa ta shiga wannan hali ta ban tausayi da shekarunta kanana ta faɗa irin wannan hali.., hmm kawai juraij yace domin taufiq be san wace yumna ba amma Allah ya bata lafiya kwana ɗaya za tayi ya fahimci wace ita daukan folder yayi yace '' taufiq zaka zauna ne na je na dawo ko kuwa fita za muyi tare..?, tashi yayi yace '' a'a yanzu zan tafi sai kuma gobe insha'Allahu zan dawo naga ya jikin'ta yake.., okay kawai yace tare suka fita wata nurse ta bi bayan'sa yana shiga mommy na lallabata ta ci abinci takaici ne ya ishe shi ji yayi kamar ya buge ta sai wani shagwaɓa take yi mommy na biye mata Allah ne kaɗai yasan me tai wa mijinta ya sake ta shikkenan ta cuci kan'ta, ta zama ƙaramar bazzawara ƙara tamke fuskar'sa yayi domin baya son raini... jan kujera yayi ya zauna yace '' mommy barka da yamma.., cikin kulawa mommy tace '' barka dai ashe ya fada maka.., m Eh ya faɗa min ya faɗa yana buɗa folder din yumna batare da ya kalle ta ba yace '' ya jikin naki dame dame kike ji a jikin ki..?, dauke kai tayi tace '' na samu sauki ni ka sallame ni.., ji yayi kamar ya buge ta amma sai ya danne yace '' tambayar ki nayi me kike ji a jikin ki..?, ɗauke kai tayi ranta duk a ɓace tace '' nace maka na samu sauki fa.., ajiyar zuciya ya sauke yace '' okay.., ajiye folder din hannunsa yayi ya soma haɗa allura gaban tane ya faɗi ba abin da , ta tsana sama da allura har gwara magani tana iya sha idanuwanta ne suka fara kawo ruwa zuciyar ta , ta fara rawa tamkar zata faso kirjinta ta fito tace '' mommy ki yi mai magana nafa ce mai na samu sauki amma kinga yana haɗa allura.., mommy tace'' haba yumna ya zan shiga aikin sa, bakya so ki samu lafiya sosai kinga fa kwana biyu duk kin rame.., haɗe rai tayi zuciyar ta ba dadi wato itama mommy ta goyi da bayan sa ai kuwa ba allurar da zai mata kallon sa tayi tace '' ya Jawad cire min ƙarin ruwan nan zan shiga bayi.., be nuna ma yaji me take cewa ba , balle ta saka ran zai amsa mata ranta ne ya ɓaci tana wannan tunani sai ji tayi ƙarar shigar siriji a dantsan hannunta za bura za tayi tuni ya riƙe ta ya hanata ko da motsi sai da ya gama yi mata tas, sannan ya saka audiga a gurin yace '' ungo ki danne ta kar ta zame miki ciwo.., idan ta tanka shi to bango zai magana ganin haka ya saki murmushin mugunta karfin zuciyar ta yana bashi mamaki ta rasa da wa za ta dinga faɗa sai dashi yau zata gane kuranta, dannawa ɗaya yayi mata sai da kashin ta ya amsa cike da mugunta yake mulmula mata gurin , kuka ta saki amma be saurara mata ba har sa da yaga jikin'ta yayi laushi sannan ya barta. daukan folder yayi, yace '' mommy sai da safe.., Mommy tace '' yau da wuri haka zaka tashi..?, Eh wallahi ina so na biya gidan su ahlam na ƙara ganin jikin ta. to Allah ya ƙara sauki da sauri yusrah tace '' yaya zan bika daman yanzu nake shirin tafiya gida.., juraij yace '' to tashi mu tafi..., Juhud ta gallamata harara tace '' ni kuma ce miki aka yi ba tafiya zan yi ba , yusrah tace '' ai na zata da yaya taufiq za ku tafi ne shi ya saka ban yi zaton tare za mu tafi ba, baki tawo da motar ki bane..?, Mommy tace '' tuni taufiq ya tafi gida.., mommy ke kika bata amsa a gaban ta ya TAUFIQ yayi miki sallama yace amma shine take wannan maganar sai kace wacce ta sha kwaya juhud ta faɗa cikin zafin rai Dafa ta yusrah tayi tace '' Allah ya baki hakuri..., ganin zai tafi ba abin da kuma yace da sauri tace '' ya Juraij baka sallame ni ba, nace maka naji sauki..., wani kallo ya yi mata tuni ta hadeyi sauran zancen ta wannan kallo da yayi mata ba ƙaramin nutsar da ita yayi ba , kowa shakkar sa yake amma ita ce take ma iya musayar yawu da shi, saboda zafin sa bama ya shiga sabgar mutane musamman wanda yasan zai raina shi. bayan fitar su malam ya kirawo Hajiya da sauri ta ɗauka suka gaisa yace '' na karbo takardar ta saki biyu ne , ɗazu Hajiya ta kawo mata abinci to wallahi ban san yadda zan mata bayani ba kinga har yanzu na rasa nutsuwata bana so mutuwar auren yumna ta baza ko ina bana so a sani.., ajiyar zuciya ta sauke tace '' wallahi nima yau haka na yini cikin tunani ko wacce hanya nabi sai naga ba me bullewa bace ba , ga jikin hajiya bana so ta sani kar jikin'ta ya ƙara rikicewa azo a haifi da mara ido..., malam yace '' nima abin da nake jimami kenan wallahi.., mommy tace '' to Allah ya shige mana gaba wallahi matar nan Ubangiji ba zai taɓa barin ta ba da nayi ƙoƙarin daukan mataki sai kuma na gani idan na dauka tamkar na daɓawa kan mu wuƙa ne za a san me yake faruwa bayan so muku wannan sirrin ya rufu ba wanda zai ji shi nan kusa..., tabbas haka ne amma ba yadda muka iya wata ran dole a sani Allah dai ya shige mana gaba. amin ya Allah mommy tace kwanan yumna biyu ya sallame ta saboda jikin'ta yayi kyau taji sauki a lokacin ma ahlam ta dawo sosai suke takun saƙa da ahlam tambayar duniya ahlam tayiwa juraij wai fasa bikin akai ko kuma wani abu ne ya faru amma yayi mata banza baya ma tanka mata. hakan da yayi ba karamin fusata zuciyar ahlam yayi ba ji tayi ba wacce ta tsana a duniya sama da ita tsoran ta ɗaya kar juraij yace yana son ta tunda ta lura duk abin da ake so a jikin

Chapter 8 of 10