Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1


YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 39879



YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1

Reading Time: 3 Hours

Added On: 22, May 2025

Author: Oum Yasmeen ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08141785374

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 198.49 kb

File Type: txt

Views: 22+

Download: 2+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: YAN ZAMAN MAKKAH

Dan Allah naci albarkacin annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam kuyi min subscribe

https://youtube.com/@sajbeelnovel?si=Clh5GGzsqicvMZ8X


Zai fara zuwar muku asabuwar tashar ta in sha Allahu ku daure ku danna min subscribe
AGADEZ .....
Tsaya tsaya tsaya anan zan sauka tun dazu nake maka kwatancan inda zan sauka amma da yake kwakwalwar danƙo ce da kai , ka kasa fahimta kaf Niger wane besan malam Nura me sittin ba
me mashin ɗin ne ya tsaya yana yi mata wani irin kallo
saukowa tayi daga kan mashin ɗin tare da kuɗi ta ciro daga cikin jakarta ta miƙa mai
amsa yayi yana juyawa ya cillo mata yace '' ke wacce irin ɓarauniya ce tun dazu nake yawa da ke shine zaki dauko dari biyar ki bani..,
wani kallo tayi mai na tara saura kwata ta fisge kudinta tace
'' wallahi ka rasa wannan din da kake rainawa ni zaka kalla kace min ɓarauniya kai kuma sannu dan fashi kama godewa Allah dana dauko dari biyar na baka..,
lallai yarinyar nan ke yar akuya ce me mashin din ya faɗa yana saukowa daga kan mashin din sa
dariya yumna ta saki tace “sannu dan bunsuru wallahi yanzu sai nayi kasa kasa da kai saboda kaine sarkin ɓarayin duniya kake faɗamin haka..,
wannan maganar ita ta jawo hankalin malam da almajiran sa takaicine ya tukare malam
inda sabo yumna ta saba da jamai magana sai ta hau abin mutum ya gama zaga gari da ita ta ɗauki kuɗi kalilan ta da yawa na kanin uwar ta

hafizu almajirin malam ne ya tashi ya kalli me mashin yace '' lafiya bawan Allah naga kana naɗe hannun riga..,

ba dole na nade hannun riga ba na , naɗawa yarinyar nan duka tun dazu nake yawo da ita akasuwa shine zata ɗauki dari biyar ta bani
Kai ba ruwanka koma inda ka fito harni zai nunawa iskanci to wallahi ka gyara bakin ka ko yan zu na saka aci uwar ka
dauke ta zai yi da mari hafizu ya tare malam ne ya tashi yace '' bawan Allah kuɗin ka nawa ne..?,
Dubu ɗaya me mashin ya faɗa yana haɗe girar sama da ta ƙasa
da sauri yumna ta rufe bakin ta tace '' kut billahillazi karya yake malam kar ka bashi..,
wani kallo yayi mata tuni ta hadiye sauran zancen ta ja bakinta ta tsuke
ciro kudin malam yayi ya miƙa mai amsa me mashin yayi, ya hau mashin dinsa yayi gaba
kallonta malam yayi yace '' yumna ki nutsuwa..kiyi hankali ke ko , koyi da yan uwanki bakya yi..,
kai ta sosa tace '' insha'Allahu zanyi..,
komawa yayi mazaunin sa haka ma hafizu cikin gida ta nufa
Katon gida ne irin ginin nan na laka tana cewa Allah ya aikata munafukan mu ƙarshen duniya baba Hadiza da take wankin tukinya ta ɗago tace '' baki ma dai baya shiru yanzu yumna ki rasa da me zaki shigo sai da waka ...?,
kwafa tayi ta shige cikin daki ba tare da tace komai ba kamar na jefota ta fito da waya me madanne a kunnen ta tana cewa dan girman Allah ehyee chanchadi aikuwa nima billahillazi zan zo daman garin annabi ai dole a samu ni'ima yanzu saude gidan naku kika turo a buge shi kudin ma kenan a banza kuke samun sa ..?
saurarawa tayi domin taji me zata ce sai kuma ta ƙara kwashewa da , dariya tare da buga cinya tace “baba hadizuwa..,”
baba hadiza ɗagowa tayi tace “na'am yumna..”
kashe wayar ta tayi tare da zama ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tace '' baba Hadiza hmmm nima fa makka zan tafi neman arziki bazan zauna kuda ya bi bakina ba na tashi a talauci na girma a talauci dan girman Allah dubi Mamman da yake cewa yana sona ba wani abin arzkine da shi ba shikkenan rayuwar mu haka zata ƙare ba makoma me kyau ..,
salati baba Hadiza ta saki tace '' yanzu yumna takaru kike so ki zama yumna aure shine suturar ya'mace ki daure ki yiwa mahaifinki biyayya dan Allah ki bar zancen tafiya makkan nan wallahi idan yaji sai ranki ya ɓaci..,
bude baki tayi tana aikawa da baba Hadiza harara tana gama zancen ta ta miƙe tace '' alkur'an kamar naje na gama ne me makon kiyi min murna na tafi samo mana abin arziki kalli dan girman Allah na'ima ta aiko a rushe musu gida kalli inda nake kwana kamar ni yumna na dinga kwana a cikin laka ke ni acan ma zanyi aure yasin danni ba kalar wahala bace..,
Shamsiya ce ta shigo tace '' yumna kindawo kenan bara na faɗawa Mamman tun dazu yake zuwa..baya samin ki...,
ke da hallacan rufe min baki sai shegen surutu yawa kin hadiyi Radio yumna ta faɗa tana haɗe rai ina ita ina Mamman ita za zataiwa talauci bara zana zata tafi Makka nemo abin duniya
Shamsiya ce tace '' Allah ya wuci zuciyar ki..,
dan uwar ki ke kika saka min fetur da a shana a zuciyar tawa da zaki ce Allah ya wuci zuciya ta a'a taransufoma ce ƙarewar zafi wallahi shamsiya ki kiyaye ni bana son ciki da annami manci
sannu karya uwar faɗa ke dai idan kika fita daga gidan nan yaran gidan nan har wata sabuwar walwala ke zuwar musu kina dawowa shikkenan kin dinga tsangwamar su anya kuwa..? Yumna kina da cikakkiyar Lafiyar ƙwaƙwalwa baba lami ta faɗa tana fitowa daga dakin ta
Wani uban ihu yumna ta saki tare da jan ɗamara da mayafinta ta zube ta fara aljannun karya tana wallahi ba zamu yarda ba mu zata cewa mahaukata ke yau sai mun dora miki haukan shekara hamsin dan uwar baban ki tasalla me chukwi
wani yawu baba lami ta hadiye batayi zaton yumna na da aljanu ba abokin yar zamanta ta kalla tace '' yaya Hadiza daman yumna na da aljanu..,
dan kuttumar ubanki mu kikewa munafurci jiyama muna jinki ina faɗawa malam idan ba a tashi tsaye akan mu ba , muna neman mu fi karfin malam ma be faɗa mana muji
Dan girman Allah kuyi hakuri Ni da yumna nake
ihuuuu idan kina yi da yumna kamar da mu kike tun tana yarinya muke kula da ita shine ke gaki uwar iya wacce ta iya tarbiyya ko to Bara mu cire miki jijiya ɗaya muga inda tarbiyyar zata je basai kina da hankali ba zaki wa wani tarbiya..?,
YAN ZAMAN MAKKAH

Oumyasmeen

https://youtube.com/@sajbeelnovel?si=Clh5GGzsqicvMZ8X


Zai fara zuwar muku asabuwar tashar ta in sha Allahu ku daure ku danna min subscribe

______________

dafe kirji baba lami tayi tana zaro ido yawa an shake wuyan mage baba Hadiza tace '' ko a kirawo malam ni wallahi ba zan iya ba ba'a taɓa aljanu a gabana ba..bansan me ake musu ba..,
ƙara langwasa muya da hannaye yumna tayi tare da shaƙe murya tace '' wallahi kar wacce ta sake ta fita a cikin ku, idan kunne yaji, jiki ya tsira duk kuma wacce taki to wallahi tana ɗaga kafar ta zata ga ta cire..,
dafe bango shamsiya tayi, tana kuka har da fyece majina tun da take bata taɓa ganin tashin hankali irin na yau ba , baba hadiza da baba lami ido suƙa tsurawa yumna suna jiran kudirar Allah idan kuma yau Ubangiji zai kirawo su Allah ya saka su ciki da kalmar shahada baba lami tace '' yaya ..,
da sauri baba Hadiza ta saka hannu abakinta tana kibta mata ido gudun karta yi magana abu kuma yaci tura su yi laifi tamkar daga sama yumna taji sallamar malam da sauri ta tashi zaune tare da sakin wata uwar atishawa,
har gudu uku kwarara ajiyar zuciya su baba Hadiza suka saki kallon mamaki malam yake musu yace '' lafiya naga kunyi cirko cirko..?,
baba Hadiza ce tace '' lami faɗa mai..,
hade rai baba lami tayi tace '' ban gane na fada mai ba , baki, kika fini kome..?,
to ai gani nai ke kikai abin da har yumna
ai bata ƙarasa ba ta tari numfashin ta tace '' alkuran ba ruwana kinga nayi nan ..,
ta shige dakin ta
malam ne ya zauna yace '' lafiya ina tambayar ku, kuna sa'insa me ya faru..?,
wata dariya baba Hadiza tayi irin karya ɗauka da wani abu tace '' wallahi bakomai daman wani wasa muka shirya nida abokiyar zamana idan ka shigo muyi maka ta haka zamu gane ka kamu damu..,
ajiyar zuciya ya sauke yace '' ku dena irin haka idan wani abu ya faru da gaske zata zanyi wasa ne bazan dauka gaskiya bane ke yumna..,
turo baki tayi tana sosa kai tace '' na'am malam..,
ajiye carbinsa yayi yace '' wallahi yumna idan ba zaki nutsu ba zanyi maganin ki kaf cikin yan uwanki ba me kunya tani sama da ke kinsan ba zaki iya biyan mutum hakkinsa ba me zai saka ki dauke shi ya kawo ki har gida ki sauka mana abakin tito dole ne sai
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album