Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 10
tafi dake., kalar tausayi ta mai da fuskar'ta tace '' mommy., na'am yumna ta fadi haka cikin kulawa da nuna soyayya yar kwalla yumna ta ta share tace '' mommy bana son auren nan malam yace dole sai an yi ni wallahi bana son sa nafi so nayi karatu ina so naci gaba da karatuna., ba karamar damuwa mommy ta shiga ba tabbas ilimi me zurfi yana da kyau amma me ya malam zai tauye burin yarsa bayan yasan amfanin karatu duk wani mataki da ta taka ilimi ne ya ja mata ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta gama tunanin tace '' yumna bani da ikon dakatar da mahaifinki amma zan faɗa mai idan ya yarda shikkenan, amma ba auren bane illa inhar mijinki zai barki Alhamdulilah sai ki ci gaba ba wani abu bane mata nawa ne suke karatu suna gidan maza je su idan har ka saka kanka za kayi Allah zai dafa maka., kwalla ta kara sharewa ta kifa kanta a kan gwuiwar'ta tace '' shikkenan ni yanzu bani da gatan da za'a iya tsaya min na zama duk abin da nake son zama bana son sa wallahi idan na aure shi zan kashe shi ne na kashe kaina.., zaro ido mommy tayi da sauri ta tashi ta fita leƙawa waje tayi cikin Sa'a ta tarar da malam tare da juraij suna hira sallama tayi cikin sakin fuska malam yace '' a'a badai har zaku tafi ba , ba zaku bari a gama sanwar rana ba..?, zama tayi tace '' malam ba yanzu za mu tafi ba , yanzu ma tasowar da nayi wata babbar magana ce ta taso dani.., cikin mamami malam yace '' Allah ya saka lafiya, murmushi tayi tace '' lafiya ba lafiya ba malam akan maganar auren yumna ne., ganin yayi shiru yana sauraren ta, ta ci gaba da cewa tace min wallahi idan har aka aura mata shi saita kashe shi ta kashe kan'ta malam kai malami ne kasan illar yiwa yara auren dole zamanin da da yanzu ba ɗaya ba , yanzu idan muka matsa lamarin ya ɓaci azo ana dana sani..da tace min karatu take son yi da nace mata mace tana da aure tana karatu ba wani abu bane sai ta saka kuka tace ba zata iya zama dashi ba zata kashe kanta ta kashe shi ne. gyara zama yayi jikin sa yayi sanyi be san me yumna take son zama shi kuma irin tashi ƙaddarar kenan yace ''hajiya Rahama duk na fahimci abin da kike so na fahimta amma kinsan ba saboda haka tace ba zata auri yaron nan ba saboda ta tafi Makka aikatau ne , me take so duniya tace min na hana almajirina auren ya'ta lamarin yumna sai addu'a amma tun da haka ta zaɓa shikkenan magana ta ƙare zan bashi wata daga cikin ya'ya na ita kuma tai abin da taga dama tun da abin har yakai da za tayi kisan kai ina neman tsari bama iya zuri'a ta ba gaba ki ɗaya zuri'ar al'ummar musulmi., innalillahi wainna ilaihir raji'un aikatau Cikin takaici yace '' wallahi aikatau irin su yumna fa aurar dasu shi ne masalaha idan yaro kaga yana da alamun rashin ji yi addu'a Allah ya fito mai da miji yayi aure shine babban hutun mutum sai kuma ka bishi da addu'a shi yasa kika ga nace bazan janye ba amma tunda tayi wannan maganar shikkenan na hakura amma ta sani ba inda zata , shiru mommy tayi sannan tace '' wallahi na rasa abin da zan ce tabbas zancen ka gaskiya ne irin haka auren shi ne mafita ., cikin takaicin halin yumna malam yace ''yauwa yanzu wacce shawara kika yanke a fasa ko kuma ayi ina tsoron randa yumna zata zamar dani karamin mutum da wanne ido zan kalli mahaifan yaron nan nace yar ciki na kasa tankwara ta tabi abin da nake so, bayan da tana son shi bani na haɗa su ba tambayar ta nayi shin kina son sa tayi shiru tana jin kunya me to kinga kenan tana son sa banyi kasa a gwuiwa ba na saka yar uwarta nazeefa ta tambaye ta tace eh tana so to yanzu kuma ɗan ita ce uwar mu sai tace ta fasa wallahi wannan maganar kisa da kikai ba ƙaramin daga min hankali tayi ba amma bakomai zan faɗawa Allah, Ubangiji ya shige mana gaba‚‚ mommy tace '' to shikkenan malam duk hukuncin da ka zartar yayi dai-dai tabbas ba ita ta haifi kan'ta ba dan haka dole tabi abin da aka ga ba illa bane ba Allah ya daidaita lamarin. malam yace'' amin ya Allah.., duk wannan maganar da suke juraij yana zaune yana danna waya ko tari me ba kamar ma ba ya gurin, tashi mommy tayi tace '' malam ka huta lafiya zan shiga daga ciki.., to Hajiya Rahama cewar malam bayan tafiyar malam ya tashi yace '' juraij bara na saka a kawo mana ruwan alwala lokacin sallah yayi., ajiye wayar sa yayi ya duba agogo yace ''eh wallahi lokaci yayi., wani almajiri malam ya kirawo ya shiga cikin gida ya kawo musu ruwan alwala ba jimawa sai ga almajirin malam ya dawo da ruwa amsa sukai suka fara alwala bayan sun idar malam ya shiga Masallaci domin tada Sallah gaba ki ɗaya masallacin ya cika da al'ummar musulmi domin gabatar da sallar la'asar. wannan kenan. cikin gida kuwa tun da mommy ta dawo take wa yumna faɗa kamar gaske duk abin da take fadi tana binta da to ganin lokacin sallah yayi yumna da take haɗa salla tayi tace '' mommy an kira sallah.., mommy tace '' Allah yayi miki albarka yar gidan mommy., amin tace tana tashi ta fita bayan ta zuba musu ruwa a buta ta leko dakin tace '' mommy na zuba miki ruwa.., nan ma albarka ta saka mata ta taso tayi alwala baba Hadiza sakar baki tayi yau wacce rana yumna na sallah akan lokaci lallai aljanun yumna shu'umai ne. ta kuwa ɓangaren zuciyar yumna bawai ta amshi auren bane a'a akwai wata a ƙasa dole za ta hakura amma ko sati uku bata iya tunanin za tayi a gidan Mamman ba tare da ya bata takardar ta ba idan ta zama bazzawara tana da ikon yin komai ba me hanata bata hangowa kanta wata illar abin da zata aika ba ita kawai cikar burin ta take nema burinta ya cika a saka ta a matsayin na manyan mata masu amsa sunan su mata . dole ta cika burinta ta ko wacce hanya jin an dafa ta da sauri ta ɗago daga duniyar tunanin da ta lula tace '' mommy.., hannun mommy ta miƙo mata ba gardama ta miko mata ta riƙe ta suka shiga daki bayan sun idar da salla mommy tace '' yumna tunanin me kike ɗazu ki sakawa zuciyar ki hakuri komai sai kiga ya zama tarihi ki zama tamkar mahaifiyar ki ba ruwanta magana ma bata dame ta ba Allah ya kai rahama kabarin halima wallahi matace ta gari., kwalla yumna ta goge tace '' amin ya Allah insha'Allahu zanbi abin da kika ce., yauwa yar albarka ta faɗa tana buɗe jakar ta kudi ta dauko masu yawa ta bata noke ka faɗa tayi tace '' biki zanyi hutu fa muke yi.., to jeki ki faɗawa malam sannan kuma ki bashi hakuri. da sauri ta tashi ta fita akan igiya ta dauki mayafin'ta ta fita waye har yanzu yana kan tabarmar sa sallama tayi tamkar wata mumina malam da ya riga ya karan ce ta tsaf ya dauke kansa zama tayi tai shiru ta matsai kwallar karya tace '' malam dan Allah kai hakuri ka yafe min na dena wallahi zan zauna dashi yau ba mamman ba ko wani kace na aura zan aura mommy tai min wa'azi naji na ɗauka duniyar nan nawa take idan yau mune gobe ba mu bane dole sai muna sakawa zuciyar mu hakuri muna koyi da halin annabawa zan rungumi kaddarata. dan shiru malam yayi yana auna kalaman ta anya kuwa ba da wata a ƙasa ba yafi kowa sanin halin yumna ita din kaska ce sannan da musa ce bata ladabi a banza yace '' yumna anya kuwa.., hawaye ta matso dakyar ta share fuskarta tace '' wallahi malam da gaske nake karka kasa shakku akan komai Ubangiji ke shiryar da bawa a lokacin da ya gadama a kuma lokacin da ya so dan girman Allah ka yafe min shima zan bawa mamman hakuri komai ya wuce mu dawo kamar da., shiru yayi yana ƙara nazarin maganar ta anya kuwa ba wasan kwaikwayo za tai mai ba yumna fa yumna fa karfa ya sakan kance ta zame mai yar kunama yace '' to Allah ya yafe mana baki ɗaya .., amin ya Allah malam dan Allah ina so nabi mommy daman ai na ce maka idan akai hutu zan je kaga tun bikin da tayi ban ƙara zuwa ba , dan Allah malam karka ce min a'a ina son zuwa. Please subscribe. https://youtube.com/@nasreenminallah?si=fWc7Wzd4nPx_TifU EPISODE 5 Shiru malam yayi yana tunanin maganar ta ajiyar zuciya ya sauke yace '' yumna kunfa kusan komawa makaranta.., marairaice murya tayi tace '' dan Allah malam., to Allah ya tsare hanya ya faɗa yana dauke kai da ga kallon ta yafi kowa sanin wace yumna shi ya saka baya barin ta taje ko ina , shi da ta zamewa dole ya riƙe abar'sa ɗayan kan yumna yawa ne dashi riƙon mahaukaci sai sarki. ganin yayi shiru ta tashi tana washe baki ta fara tafiya a kofar zaure taci karo da mommy cikin jin dadi tace '' mommy ya barni.., momy tace '' kai Masha Allahu haka ake so jeki ki debo kayan ki., da gudu ta kara sa shiga cikin gidan ba wanda tayiwa magana baba lami da take raba abinci tace '' yumna zo ki dauki naki.., uhmm na koshi ta faɗa tana shiga daki tare da bude kwabar kayan ta tana sauko da su ƙasa. da sauri ta ɗago ta kalle ta tace '' kin koshi fa kika ce me kika ci..?, ɗagowa tayi tace '' ɗazu aka kawo min farfesun kaji.., zaro ido baba lami tayi ta kalli yaya Hadiza ta jin jina kai lallai lamarin aljanun yumna abin kullum gaba yake yi. ganin sun lula kogin tunani tace '' ko na saka a kawo muku, kuna so ne..?, da sauri inna hadiza tace '' a'a yumna mun gode.., bata ce ƙala ba ta ci gaba da shirinta zuciyar'ta fes bayan ta gama hada itana ina ta , ta fito tsakar gida tace '' to saduwar alkairi ni na tafi arlit.., cikin jin dadin tafiyar ta ya'yan su zasu sake su wahala baba lami tace '' Allah ya kiyaye hanya, amin yumna tace tana ci gaba da tafiya tana fita waje tararwa tayi har sun shiga mota ita suke jira da sauri ta kwankwasa musu bude kofar mommy tayi ta shigo tare da jakar kayan ta ɗora su tayi a kan cinya mommy ta rufe kofar suka fara tafiya kwantar da kanta tayi a kan kayan ta , tai shiru tana sake sake kala kala a zuciyar ta , sun fara daukan hanyar arlit mommy tace '' dan Allah yumna ki nutsu aure da kike gani ibada ne kinga wannan aikin da kike so ki tafi babban hatsari ne idan har baka hadu da na gari ba., shiri tayi tana sauraron zancen tamkar tana busa mata sarewa babban burin ta , sudai isa za nemo agent din na'ima tunda ai a arlit yake itama yayi mata visa bayan ta fito daga gidan Mamman ta , tafi makka dole ayi gwagwarmayar rayuwa da ita dan cimma burin ta ba abin da ake samu ta cikin sauki dan haka ta daura damarar yin komai tun da dai ba wata hanya mara kyau zata bi ba amma sun bi sun ɗaga hankalin su yawan wanda zata tafi yawan karuwanci tafiya ce ba fashi kamar tayi ta ta gama ne. anya kuwa ma sun san me duniya take ciki kai gaskiya basu sani ba da sun sani da sun mara mata baya. da wannan tunani bacci ya kwashe ta . Cikin ikon Allah suka isa *ARLIT* ungumar Cité COMINAK Horn yayi mai gadi ya bude masa tura hancin motar sa yayi ya shiga cikin hamshakin gida kallo ɗaya zakai mai kasan cewa gida ne masu hannu da shinu.. a parking space ya ajiye motar ya kashe tasowa yayi ya budewa mommy fito wa tayi tana cewa dan Allah juraij tasar min ita ka dauko mata kayan ta jikin ta ya saki yanzu ba zata iya daukan komai ba. takaici ne ya tukare shi bazai iya yi mata musu ba dan haka yace '' mata to.., zare kayan yayi ya buga mata ledar kayan ta akai da sauri ta zabura tare da danno wani uban ashar tace '' wane dan takazar uban ne ya dake ni akai.. Alkur'an ba zan yarda ba sai naci kaniyar mutum. bata ƙarasa faɗa ba juraij ya buge mata baki kuka ta saka tana kallon sa cikin tsare gida yace '' zaki dena kallo na ko sai na fasa miki fuska da wani idon ki me kama dana mujiya.., share hawaye tayi ta fito daga cikin motar tace '' ai a dangin ku ba maƙeri duk wanda ya raina tsayuwar wata ya nemo tsani ya hau ya gyara.., da sauri ya zare Écouteur (earphone) da yake ƙoƙarin sakawa yace '' me kika ce.., kai ta shiga girgizawa tana ja da baya jin tayi taci karo da mutum kafin ta gama tantance wa taci karo dashi taji an zabga mata mari da sauri ta dafe kuncinta ta kurawa wacce ta mare ta ido ko kifta wa ba tayi a cikin fusata ahlam tace '' chérie (honey) a ina ka samo wannan bagidajiyar wallahi ina upstairs na hango ku ban san ma na sauko ba , bana iya ganin gaba na., ahlam ta fadi haka cikin tsananin zafin kishi tare da tallafo habar juraij. hannun ta ya sauke ƙasa ya riƙe be yi magana ba ya fara tafiya kin binsa tayi tace '' magana fa nake maka kayi shiru badai da kaje sabon gari ba suka aura maka ita.., murmushi yayi yace '' aahhlam wallahi ina tsoran randa kishin ki zai illatar min dake, ko dan abin da ke tare da ke ya kamata ki rage damuwa zuwa tayi hutu.., ajiyar zuciya ta sauke tace '' wallahi juraij zan iya kisa akan ka duk randa wata tayi gigin shigowa rayuwar mu to sunan ta gawa na yarda na ƙarshe rayuwata a prison da ka auri wata.., bata ƙarasa ba taji saukar sanda a dokin huyan ta durkusa'wa tayi ta saki wani irin wahalallan ihu.. juraij da ya shiga wani hali a riki ce yace '' sweet me ya faru badai cikin bane na shiga uku ya Allah, duk tattalin da na ke yiwa wannan abu kar ace zu bewa zai yi.., da hannu tayi mai nuni domin bata da bakin magana ɗagowa yayi ido hudu sukai da yumna tana murguda baki tare da cin ɗamara da mayafin'ta tace '' ce miki akai jaka ce tayi yaye ni da zaki dake ni ku da tattabaru sarkin aure ko to wallahi duk wanda yayi min ba zan raga mai ba ai ba jaka aka kawo miki ba , Allah ya saka mazalkwaila ce uwar alawa kuma idan baki sani ba ki sani yau aka ɗaura mana aure sai ki mutu dan kishi.., sakar baki juraij yayi yarinyar ta soma ba shi tsoro yawa aljana kai anya kuwa kanta ɗaya dole ya koya mata hankali shu'umancin'ta yayi yawa dole ya tauna tsakuwa domin a'ya taji tsoro a fusa ce ya taso yayin da ahlam ta zun duba ihu ta danƙi huyan, yumna. duk karfin yumna kasa kwace wa tayi da ga rikon da ahlam tayi wa wuyan ta zaro ido ta din ga yi idon ahlam ya rufe babbar buƙatar taga ta kai yumna kasa , taga ko motsi ba tayi cikin ɗaga murya tace '' wallahi ina gamawa da ita kanka zan dawo daman ni naji a jiki na wannan yarinyar zaka auro ka kawo ta Cikin gida na to wallahi Allah ahlam daka kai har ita yau sai na koya muku *DARASI* wanda ko gaba aka ce ka ƙara gigin kawo min wata cikin gida na ba zaka ƙara ba..., Mommy da yusra suka fito cikin tashin hankali saboda me bawa shukoki ruwa ya je ya faɗa musu ahlam zatai kisa dakyar mommy ta karbi yumna a hannun ahlam yumna kuwa zubewa tayi a ƙasa tana farfari da idanuwanta zata tada aljanun karya ganin hankalin kowa yayo kanta ta maƙe murya tace '' wallahi ba zamu yarda ba , ni turkwa dan gidan Sarkin aljanu zata shaƙewa wuya to yasin sai na kwashe mata hanjin cikin ta tas..., ahlam tana jin wannan magana ta ɗora hannu akan ta , ta zunduma ihu gumi duk ya karyo mata ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba da jin wannan zance shikkenan unborn din su zai dena rayuwa itama tasan mutuwa za tayi ƙara shiga wani hali jin surutan da yumna ke yi. Mommy kuwa rasa me yake mata dadi tayi ta kalli juraij tace '' juraij dan Allah temaka ka dauke ta ka kaita parlour muyi mata addu'a ko a samu ta dawo dai-dai..., ƙara lankwasar da kai yumna tayi ta mai da hannayen ta baya tace '' yasin kana ɗaga kafar ka sai na cire maka jijiya ɗaya a wuyan ka ka dena motsi na tsawon shekaru goma sha biyar.., cikin fusata juraij yace '' ke zanci ubanki idan baki dawo dai-dai ba mu za kiyi wa Prétendre (pretending ) zan babɓallaki idan baki tashi ba., sandarewa tayi ta mimmiƙe tare da miƙe hannayen ta tace '' yau zaka ga me zai faru dole su aljani tsifur su tafi dakai.., mommy tace '' juraij bana son wauta karka sake ka ƙara cewa ƙala ka tafi gidan liman ka kirawo shi.., bece komai ba ya juya yumna najin haka ta dinga sakin atishawa zunbur ta tashi tace '' mommy jikina ciwo yake min.., mommy kamo yumna tayi ta rungume ta tace "sannu Allah ya baki lafiya.." ɗagowa tayi ta kalli mommy tace ''me ya faru..?ni lafiya ta qalau..., tausayin ta ne ya ƙara kama ta , mata tace '' bakomai tawo mu je ki ci abinci kiyi wanka..., washe baki yumna tayi ta juya ta dauki kayan ta , tace muje mommy.. mommy tace '' yusra kuje parlour ke da ita ina zuwa juraij tsaya.., to yusra tace ta riƙe hannun yumna suka shiga daga ciki kallon ahlam tayi da har yanzu ba ta dena kuka'ba tana shafa cikin'ta takaicin tane ya kama mommy tace '' ahlam sai kiyi shiru tunda komai ya lafa me ya faru.., ba kunya ta rungume juraij tana kuka tace '' wancan sandar ta dauko ta buga min a kafaɗata haka kurum kuma ashe juraij cin amanata yake wallahi ba zan yarda ba sai ya sake ta ko kuma na cire mata wuya.., cikin mamki mommy tace '' kanki ɗaya kuwa kinsan me kike fadi..? wa za ki cirewa kai ..?, dukan kirjin juraij ta fara tana wani gunjin kuka riƙe mata hannu yayi yace '' ahlam kanki ɗaya kuwa..? karya take fadi.., a fusace tace '' kai na dubu ba ɗaya ba daman kana da kunyar da zaka iya kallon idanuwana ka faɗa min haka...? to yasan ka jawa kowa na gidan nan sai na kona yarinyar nan.., mommy danne zuciyar ta tayi domin a ƙaramin takaicin halin ahlam take ba , ta mai da kan'ta yawa ' wata naga akan kishi bata ji bata gani tace '' juraij wai me yake faruwa ne ka tsaya ka zama gunki.., cikin takaici yace '' wannan yarinyar ce tace mata wai an daura mana aure Ita kuma batare da dogon bincike ba ta soma kuka shine fa ta shaƙe mata wuya.., wacce yarinyar mommy ta tambaya cikin tsare gida ban da rashin kirkin juraij sunan yumna ne ba sani ba kome. da sauri ahlam ta kalle ta tare da share hawayen ta tace '' mommy sannu da zuwa.., kai mommy ta dauke tace '' yauwa..,. tare da juyawa ta bar gurin. ahlam kallon sa tayi tace '' baby bazan iya zama ni kaɗai ba dan Allah karka fita kana dai ji abin da aljanunun nan suka ce ko dan girman Allah karka fita., kai ya girgiza yace '' ahlam kardai ki ce min kin manta abin da kikai min yanzu..?, turo baki tayi tace '' kai hakuri.., kama hannunta yayi be ce mata komai ba suka soma tafiya kai tsaye shashin su , suka nufa, zama juraij yayi yace '' ahlam yunwa nake ji me kika dafa.., zama tayi tana kauda kai tace '' ni ba abin da na dafa bana son jin kamshin abincin dan Allah idan kaga yusra tayi abinci nima sai ka samamamin na dan samu naci yunwa nake ji tun safe da kai mana breakfast ban ƙara cin komai ba., bece komai ba ya tashi yace '' ki haɗa min ruwan wanka., turo baki tayi tace '' beb nagaji wallahi yarinyar nan duk ta wahalar da rayuwa ta Please kai hakuri karka ce kana ta saka ni aiki ban yi ba nasan ba zaka ji dadi ba..., juyawa yayi ya shiga bedroom yana shiga ta kwanta ta ɗauki wayar ta , taci gaba da kallon ta a YouTube. Wannan kenan yumna tana shiga main parlour gidan ta nemi guri ta zauna tare da ɗora kafa ɗaya kan ɗaya a zuciyar ta cewa take ina ma wannan gidan nata ne , Allah dai ka kaita makkan nan ta kwashi arziki ta barshi a mazaunin sa. ga abincin naki yusra ta fadi tana ajiye mata tray a kan center table. da sauri ta sauko ta zauna tare da sauke tray din ƙasa tace '' Nagode.., ya tsuna fuska yusrah tayi ta dauki remote ta zauna ta chanza channel. taɓe baki yumna tayi tace '' halin ki ɗaya da wanki.., da sauri yusrah ta juyo tace '' ke magan kike.., shinkafa yumna ta watsa a bakin ta tace '' ah waka nake.., ke dan ubanki ni kike faɗawa haka kaga shegiyar kauye.., yusrah ta faɗa tana yowa kan yumna. juya idanuwan'ta yumna tayi tace '' ina matsowa sai na hanaki kashi na tsawon kwana takwas tare da ciwon ciki me tsanani.., Chak yusra ta , tsaya gaban ta ya fidi yace rass dafe kirji tayi ta bar gurin tane cewa juhud juhud juhud. juhud fitowa tayi tace '' lafiya yusrah kike kirana yawa wacce na ci miki wani abin..?, wallahi juhud mun shiga uku mommy ta kawo mana annoba cikin gidan nan. cire glasses din'ta tayi tace '' annoba kuma a ina ..?, zama tayi akan wasu kujeru da suke jere a gurin farare tas dasu gwanin sha'awa tace '' wallahi annoba yar gidan aunty halima..,. tunani juhud ta shiga yi domin ta dade ba'a kasar ba sannan koda can bata shiga sabgar mutane balle yanzu da ta taka wani matsayi me girma aiki take yi a babban Company wutar lantarki tace '' wace aunty halima ke ba'a raba ki da kwashe kwashe ke da mommy halin ku ɗaya wallahi.., sister din mommy fa dafa goshin ta tayi tace '' wallahi na manta ikon Allah ita tazo ..? da kike cewa annoba aka kawo mana akan ki zata zauna ne yusra ki deba abin da kike yi wallahi haka kurum ki dinga damun kanki da damuwar mutane.., Ya Allah ya juhud baki fa ki tsaya kin ji me zance ba kin hau faɗa., sarke hannuwanta tayi a kirji tayi '' oya faɗa min ina sauraren ki.., bata labari ta soma yi tun daga farko har karshe. dariya juhud tayi tace '' wallahi kun ban dariya da ilimin ku da komai ku tsaya ana raina muku hankali dama mom ta bar big bro yaci uban'ta gaba ko ce mata akai tayi wallahi ba za tai ba karya ne ba wani aljanu yanzu ke saboda ta faɗa miki haka shi ne kika tawo nan kafin ta hanaki kashi right..?,. cikin matsanancin tsoro yusra ta gyaɗa mata kai murmushi tayi tace '' jeki ki dauke shegiya da mari zata fahimci nan ba can bane.., cikin kwarin gwiwa yusra ta tashi juhud tace '' yauwa ta gida na idan da hali ki dauki tray din da kika kai mata abinci ki kwaɗawa shegiya ni wallahi bana son irin wannan rainin hankalin., to kawai yusra tace mata ta sauka ƙasa samin yumna tayi ta zauna sai zuba uwar loma take yi damarar ma da

Chapter 3 of 10