Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito,shima kanshi driver a tsorace yake daurewa kawai yake Adu'a shi ya samu C M a waya.
wata irin razananniyar ƙara Nainarh ta saki lokacin da su ka fara sakar ma motar harsashi,gaba ɗaya ta kifa under seat,shi ma kanshi driver bai san time ɗin daya saki wayar dake hannunshi ba,ƙarar da Nainarh ta saki ta tsoratar da shi.
kamar yaƙi haka su ka shiga sakar ma motar bullet,gashi anguwar ba kowa kamar anyi shara,sauƙin su ɗaya da motar ta kasance bulletproof ce.

*POLICE STATION HEADQUTER*

Gama dai daita parking motocin su suka yi a parking lot ɗin dake headquarter.
ɗaya bayan ɗaya su ka shiga fitowa daga cikin motocin,ɗaya daga cikin securitys ɗin ne su ka buɗe back seat ɗin motar dake tsakiyar su,ya Naeem ne ya fito ɗayan side ɗin A C M Usman ne ya fito,main entrance ɗin shiga P H ɗin su ka nufa, da sauri securitys ɗin su ka mara ma su baya amma sai ya Naeem ya dakatar da su hakan yasa su ka dakata,ciki su ka ƙarasa shida usman.
mai adaidaita ne yayi parking a bakin gate ɗin P H ɗin,wani dattijo ne ya fito wanda kallo ɗaya zaka mashi ka fahimci wahala ce ta mayar dashi tsoho sosai ba tare da shekarunshi sun kai ba.
ta ɗayan ɓangaren wata dattijuwa ce ta fito tareda wata yarinya da bazata gaza shekaru goma zuwa sha 12 ba a duniya wacce kallo ɗaya zaka mata ka fahimci babu isasshiyar lafiya a tattare da ita bayan halin na tsananin rayuwa da su ke ciki daga ita har iyayen nata wanda daga suturar jikinsu zaka tabbatar da haka.
gate ɗin shiga headquarter su ka nufa,da sauri securitys ɗin dake wurin su ka dakatar da su,ɗaya daga cikin securitys ɗin ya nufo su “kai tsoho! wai kai wane irin mai taurin kai ne,sau nawa muke faɗa maka ka daina zuwa nan,ka tafi can divisions dake anguwannin ku ka shigar da ƙararka,nan ba wurin kawo ƙananu ƙananun ƙorafi bane irin naka??” dattijon kamar zai fashe da ku ka yace “yallaɓai can ma sunƙi karɓar ƙorafin mu,wata matace tayi mana kwatancen nan tace nan ana karɓar ko wane irin ƙorafi,dan sanku da Manzon rahama ku tausaya ma yarinyar nan tana buƙatar a ɗaukar mata fansar abunda aka yi mata,an zalunceta, ku taimaka ku tsaya mata” ya faɗa yana haɗe hannayenshi wuri ɗaya alamar roƙo, girgiza kai security yayi “matar data turoka saboda ta san baka da hankali shiyasa ta turo ka nan”
“wallahi ba haka bane yallaɓai,tace in nemi inspector hussein”wani daga cikin police din ne yace
“kai dattijo babu wani ma'aikaci inspector hussein a nan,kaja jikar ka ku bar nan ko muyi maku korar kare”
fashewa da kuka matar shi tayi “don Allah yallaɓai ku taimake mu” ja in ja suka shiga yi da police ɗin, sun ƙi bari su shiga su kuma sun ƙi su tafi, sun kafe akan dole sai sunga inspector hussein
suna a haka su naeem suka fito, da sauri securitys ɗinshi suka nufi motocinsu,back seat suka buɗe masu,key su ka yima motocin su ka nufi get ɗin headquarter ta cikin mota ya Naeem ya hangi wannan dattijon sai fama security suke da shi akan ya tafi amma ya ƙi, dakatar da drever shi yayi,hakan yasa gaba ɗaya motocin securitys ɗin suka dakata,umarni ya ba drever da ya je yaji me ke faruwa,direban na fita wani daga cikin police din na fisgar hannun wannan dattijon ya hankaɗar da shi gaba daya tsohon ya nufi ƙasa ya fadi,fashewa da kuka matar shi da yar shi suka yi,da sauri driver nufi tsohon,kamashi yayi ya miƙar da shi ,kaf abunda ya faru akan idon ya Naeem, buɗe side ɗin da yake yayi ya fito hakan yasa securitys ɗin shi da ACM usman su ka fito,kama dattijon da dreve ke riƙe dashi ya Naeem yayi yana mashi sannu,masifa usman ya shiga yi mo polis ɗin suna bashi hakuri Hadi da faɗin “yallabai wannan dattijon da kake ganin shi ya cika taurin kai da
naci mun ce mashi banan zai shigar da ƙorafi ba,ya tafi division dake anguwannin su amma yaƙikullum sai ya zo nan”
“saboda baku san darajar manyanku ba shiyyasa za ku ture shi,idan kullum yana zuwa baza ku iya mashi uzuri ba,ko ba kuga shekarunshi sun ja ba?”
“ayi haƙuri yallaɓai in sha Allah hakan bazata sake faruwa ba” tsaki kawai yaja yana nufar ya Naeem da dattijon
“kayi haƙuri baba kamar yanda su ka faɗa maka ba nan zaka shigar da ƙorafi ba, division dake cikin yankin ku za kaje ka shigar da ƙorafinka”
“yaro can ma naje basu amshi ƙorfina ba sai ma kallon mahaukaci da su ke man,wata jami'a ce tace na zo nan na nemi inspector hussain zai taimaka man”
“duk da haka baba kayi haƙuri zanyi maka kwatancen inda ƙanina ke aiki in sha Allah nayi maka alƙawarin zai taimaka maka” sai a time ɗin ya Naeem yayi magana
“A'a Usman,baba wane ƙorafi ne ka ke son shigarwa” ya Naeem ya faɗa yana mai da duba shi ga dattijon,da sauri yayi ma matarshi da yarinyar alama da su zo,in da su ke suka ƙaraso, hannu yasa ya yaye hijab ɗin dake jikin yarinyar,da sauri ya Naeem da Usman su ka rintse ido suna ambatar innalillahi wa Innah ilaihi raji'un lokacin da idanunsu su ka sauka akan cikin yarinyar,da alama operation aka yi mata bata samu kulawar likita ba,wurin ya rure yayi jaga jaga ga wasu irin ruwa masu wari da yake fitarwa
“yaro kaga halin da yarinyar nan take ciki amma babu mai son ya taimaka mata,an cutar man da jikata” da ƙyar ya naeem ya buɗe idonshi amma ya kasa kallon yarinyar “baba mi yasa ku ka baro asibiti da ita,wannan babbar matsala ce!?”
ɗaya daga cikin police ɗin ne yayi carab wurin faɗin “abunda muke faɗa mashi kenan amma ya kasa fahimtar mu” cikin kwantar da murya ya Naeem yace “baba idan kuɗi ne matsalar ku taimako ya kamata ku nema,kuma ga asibitocin gomnati nan”
wasu irin hawaye ne su ka wanke fuskar dattijon “yaro da yawan mutane haka su ke faɗa,wa su ma gani su ke mungudu daga asibiti ne saboda kuɗi,amma ba haka bane yaro,daga tura yarinyar nan aikatau ta dawo mana a haka,ban san waye yayi mata hakan ba,shiya nake son shigar da ƙara ko hukuma zata ƙwatar mata ƴancinta,babu lalura ba bu komai su ka farke cikin jikkata,dan Allah yaro ka taimaka mana da abunda zaka iya dan ganin an ƙwatar mata haƙƙinta” dattijon ya faɗa hawaye na bin cheek ɗin shi,matarshi ma ku ka take tana roƙwan ya Naeem da kusan suman tsaye yayi tsabar shock ɗin daya shiga,babu wanda lamarin bai ɗaure ma kai ba,daga zuwa aiki ayima yarinya operation ba tare da sanin wani nata ba.
Ajiyar zuciya ya Naeem ya sauke “baba karka damu in sha Allah zanyi iya iyawata dan ganin na taimaka maku,amma yanzu tana buƙatar ganin likita barinta a haka haɗari ne,kunyi sakaci da baku kaita asibiti ba,yanzu abunda za'ayi zan fara kaita asibiti in sha Allah zata samu sauƙi kuma Allah zai toni asirin wanda su ka mata haka”
hawayen farin cikin jin za'a taimaki jikarshi ne su ka shiga zaryar a fuskarshi, godiya su ka shiga zuba ma ya Naeem kamar za su yi mayi sujjada
“karka damu baba” ya naeem ya faɗa.
a ɗaya daga cikin motocin security suka shiga,daga nan direct S I hospital su ka nufa, a parking lot securitys ɗin su ka tsaya ya Naeem da Usman ne su ka shiga ciki tare da su,kai tsaye office ɗin da fawar su ka nufa.
a zaune su ka sameshi kan chair ɗin shi yana duba wasu files na patient.
cikin girmamawa fawar ya tarebe su,yarinyar ya Naeem ya nuna mashi yace yana su su gano mike damunta sannan ayi mata treatment ɗin cikinta,kulawa ta musamman ya Naeem ya buƙaci da fawar ɗin yaba yarinyar sannan zata zauna a nan tare da iyayenta har lokacin da zata warke
“babu damuwa ya Naeem in sha Allah za ta samu kulawar mu fiye da zatonka”
“nagode sosai fawar,baba zaku zauna anan tare da ita har Allah ya bata lafiya,zata samu kulawar Dr in sha Allah zata samu sauƙi,duk wani abu da ku ke buƙata ga Dr nan kuyi mashi magana in sha Allah zai sanar dani” godiya su ka shiga yi mashi da Adu'ar gamawa da duniya lafiya
“karka damu baba,zuwa anjima zan dawo in sha Allah” ya faɗa yana kallon wayarshi da tun suna cikin mota take ƙara.
sallama su ka yima fawar su ka fice su ka bar dattijon da yarinyar.

*G J I hospital*

*V I P WARD*

Kainart a kwance take saman Electrical bed,hospital blue gown ce a jikinta, fuskarta tayi jazur ga idanunta da su ka kumbura,ƙarin jinine aka sa mata,daga yanayin yanda take fitar da numfashi zaka tabbatar da ba ƙaramin jin jiki take ba har wata muguwar rama tayi iya daren jiya kawai,ba'a da ɗe da fito da ita daga Emergency ward ba,mom na daga zaune gaban bed ɗin hannunta riƙe da hannun kainart ɗin da babu komai a jikinshi,da ka kalli fuskarta zaka fahimci ba ƙaramin ku ka tasha ba,
laatifa na daga kana sofa fuskar nan tayi jawur idanunta sun kumbura,time to time take sa hankey ta goge hawayen da tun jiya su ka gagara tsaya mata,wani irin mugun tausayin ƴar uwarta take ji,ba komai ta tunawa zuciyarta ke sake karya ba sai irin farin ciki data shiga ciki lokacin da fawar ya tabbatar mata tana da ciki,data tuna sai hawaye sun wanke fuskarta,dady da Abbah na daga tsaye gefen bed ɗin,dady ya goya hannayensa a baya yayinda Abba ke riƙe da sandarshi babu yanda ba suyi da shi ba akan ya zauna amma yace A'a,kowannan su kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar damuwar dake shimfiɗe a fuskarshi.
Zaabith na daga can bakin ƙofa ya rakuɓe kamar maraya kallon ɗaya zaka mashi shima ka hango tsantsar tashin hankali da ruɗun da yake ciki hatta rigar jallabiyar dake jikinshi a baibai take,har wata yar rama yayi dare ɗaya kawai,da ka kalli idonshi tsantsar nadamace kwance a cikin su,tunda ya shigo ɗakin ya toge a nan,wani mugun shakkar kowa yake da tsoron matakin da za su ɗauka akan shi.
ƙofar ward ɗin ce aka turo gaba ɗaya su ka kai dubansu ga ƙofar dan ganin waye zai shigo,wani faɗuwar gaba ne ya riske su a lokacin da su ka sauke idonsu akan waƴanda ke shigowa, zaabith zuciyarshi kusa tsayawa da aiki tayi,kallon juna Abbah da dady su kayi,da kalli fuskar su kasan suna cikin tsantsar tashin hankali,mom tayi tunani su yumnah ne su ka dawo,ba kowa bane face uncle mustafa,yana daga gaba mom Maryam da su Ammar na bayanshi,da gudu Ammar da Aman su ka nufo bakin bed ɗin suna kuka,mom Maryam ma ku ka take kamar ƙaramar yarinya,tashi mom tayi ta nufeta,kamo hannunta tayi tana lallashinta,bakin bed ɗin ya ƙarasa ba tare da ya kalli kowa dake cikin ɗakin ba,bazaka iya gane actuall halin da yake ciki ba fuskarshi ita ba a ɗaure ba ita ba a sake ba.
Inda mom ta tashi ya zo ya zauna,hannun kainart ɗin dake kan bed ya kamo cikin nashi ganin haka ne yasa zaabith lallaɓawa ya fice daga ɗakin a tunaninshi babu wanda ya ganshi, direct parking lot ɗin hospital ɗin ya nufa,motar shi dake wurin ya nufa,buɗe driver seat yayi da nufin zai shiga,ɗaga ƙafar da zaiyi yaji an toshe mashi baki ta baya,kokawa ya shiga yi da wanda rufe mashi baki,baiyi aune ba yaji an shaƙa mashi wani abu,baya yayi zai faɗi,da saurin wasu jibga jibgan ƙatti dake sanye da baƙaƙen kaya, fuskokinsu rufe da mask,sama su ka ɗagashi,booth motar dake kusa da tashi su ka buɗe su ka saka shi,babu wanda ya gansu kasancewar parking lot ɗin a ƙasan ginin hospital ɗin yake kuma haka nan ya fito ba tare da securitys ba,a tamanin su ka fice daga hospital ɗin gaba ɗaya.
su Aman na daga ɗayan side ɗin,kuka su ke suna kiran sunan mahaifiyar ta su wallahi dole su baka tausayi.
Adu'a ya shiga karantowa yana tofama Kainart ɗin
gaba ɗaya ɗakin zuba mashi ido su ka yi suna kallon shi har ya kammala yi mata Adu'a, kissing forehead ɗin ta da hannunta dake cikin nashi yayi kafin ya miƙe ya nufi ƙofar fita ya fice,babu wanda bai sha jinin jikinshi da wannan reaction ɗin na uncle mustafa ba,musamman dady da Abbah da ba su san waye ya sanar da shi ba.
wurin daya tashi mom Maryam ta nufa ta zauna, hawaye dake idonta ta goge,forehead ɗin kainart ɗin tayi kissing kafin ta ɗaga idonta ta kalli dady da Abbah gaishe da su tayi girmamawa tana tambayar su ya mai jiki da Alhmdllh su ka amsa mata,maida dubanta tayi akan fuskar kainart ɗin,dady ne ya kama hannun Ammar da Aman haɗa su yayi duka yayi hugging,ɗan bubbuga bayan su ya shiga yi yana lallashin su har su ka yi shiru.
ɗan gyaran murya Abbah yayi yana sauke ajiyar zuciya,bakin gadon ya matso,kallon seconds 10 yayi ma kainart ɗin kafin yayi mata Adu'a,kallon mom da mom Maryam yayi “ni zan koma gida, Allah ubangiji ya bata lafiya” da Ameen su ka amsa gaba ɗayan su, laatifa dake zaune kan sofa dady ya nufa,su Ammar yace su zauna kusa da ita “kukan ya isa haka laatifa in sha Allah zata samu sauƙi,ki lallashe su suma kinji”
“to dady” ta faɗa tana jansu zuwa jinkinta ta rungume su,a hankali take hitting bayan su,dady tare su ka fice da Abbah domin yayi mashi rakiya,a bakin ƙofar ward ɗin su ka samu securitys ɗin Abbah da drivern shi,cike da girmamawa suke tambaya ya mai jiki da Alhmdllh su ka amsa masu.
tun daga corridor da zai sada su da reception su ke jiyo hayaniya haɗe da koke koke,suna ƙarasowa reception ɗin uncle mutallab na shigowa ɗauke da Noor,Kamar bata numfashi bakinta sai fitar da kumfa yake,nureses na biye da shi da stretcher sun yi sun yi ya bari su ɗauki Noor ɗin yaƙi,mom Fatilah na bayan su sai ihu take kamar wacce uwarta ko ubanta su ka rasu gaba ɗaya ta cika reception ɗin da kuka,a hanzarce su ka ƙarasa cikin reception ɗin suna ambatar innalillahi wa Innah ilaihi raji'un...
Dr's biyu ne su ka nufo Uncle mutallab ɗin,babu wanda ya kalla a cikin su,Direct Emergency ward ya nufa da ita,mara mashi baya su ka yi harda wasu nurses,a bakin ƙofar dady da Abbah su ka tsaya hankalin su a tashe,ga kukan da mom fatilah ke yi duk wanda ya ganta sai yayi tunanin mutuwa aka mata.
lallashinta Abbah da dady su ke amma kamar ƙara tunzurata suke,abun nata kamar mai taɓin hankali.
a saman Electrical bed ɗin dake ɗakin ya kwantar da ita,da sauri ɗaya daga cikin nurses ɗin ta miƙa mashi surgical gown dake hannunta,Nurses ɗin da Dr's ɗin da su ka biyo shi suma gown ɗin su ka shiga zurawa a jikin su,ba komai yasa su ka kawo ido su ka zuba ma uncle mutallab ba sai he's being their colleague and bugu da ƙari hospital ɗin na su ne.
Emergency treatment su ka shiga ba ma Noor,sun shafe kusan two hours suna abu ɗaya da ƙyar su ka samu tafarfaɗo ta hanyar defibrillator,kwata kwata Bata cikin hayyacinta banda kiran sunan Irfan babu abunda take shima sai ka kai bakinka saitin kunnenta sosai tukun zaka iya ji.
allurar bacci uncle mutallab yayi mata saboda wannan motsa baki zai iya haifar mata da matsala,ba ƙaramin raunata tayi ba ta shiga halin rayuwa ko mutuwa,yayi mamakin ma yarda har take iya furta sunan irfan.
zama yayi gaban bed ɗin da take kwance,zuba mata ido yayi yana kallonta cike da tausayawa,yayi taikici da baƙin cikin halin data shiga saboda ta rasa abunda take so,wani irin tsanar kanshi yake ji na gaza yi mata abunda take so gashi har tana neman ɗaukar rayuwarta,wasu irin hawaye ne su ka taru a idonshi,wata irin wutar tausayinta ce ke ci a zuciyar shi,duk yanda yake daurewa sai da ya zubar mata da ƙwalla,ƙarasowa Dr's ɗin su ka yi inda yake,ganin yanda ya kama hannun Noor ɗin ya riƙe gashi da alama kuka yake yi, hakan yasa likitocin su ka shiga kwantar mashi da hankali in sha Allah zata samu sauƙin,jinjina masu kai kawai yayi,jinin Noor ɗin da su ka ɗiba ɗaya daga cikin nureses ɗin ta ɗauka ta nufi lab ɗin su,tana fita Abbah da dady su ka nufota suna tambayar lafiya haka ma mom fatilah
“Abbah ku kwantar da hankalin ku,in sha Allah zata samu sauƙi” ta faɗa tana nufar lab ɗin,ɗaya daga cikin Dr's ɗin ne ya fito,da sauri ya nufi su Abbah “Lelarh mike damunta ne?” dady ya faɗa
“she's poisoning her self” har haɗa baki su ke waurin furta innalillahi wa Innah ilaihi raji'un,wani sabon kuka mom fatilah ta sake fashewa da shi
“amma yanzu a wane hali take ciki?”
“to da sauƙi zamu ce,dan gaskiya she is on life support”
“innalillahi wa Innah ilaihi raji'un,amma wane irin poison ne tasha”
“abunda muke bincike kenan,poison ɗin ya mata illa gaskiya,ban san ya akayi ba har aka yi sakacen data aikata ma kanta haka ba” ya faɗa yana kallon mom fatilah dake ta aikin tsiyayar da hawaye
“zamu iya shiga ciki mu dubata?”
“She is in a critical condition gaskiya,ku yi haƙuri zuwa lokacin da zamu kammala binciken,in sha Allah zata samu sauƙi”
“to shikenan ba damuwa,ina mutallab ɗin yake?”
“yana ciki” ya basu amsa yana kallo mom fatilah da dole ta baka tausayi
“please ma'am ki daina wannan kukan, Adu'a ya kamata kiyi mata”
jinjina mashi kai tayi ba tare da ta daina hawayen ba gaba ɗaya gani take laifinta ne da ace ta amince da Aurenta da Irfan da duk hakan bata faru ba,wani irin mugun dana sanin abunda ta aikata take,tayi data sanin abunda taje tayi ma mom har gida,gashi yanzu ta dalili wani dalili nata mara tushe zata kashe ƴarta da kanta.
dady ma kwata kwata baiji dadi abun ya zo a haka ba,a ganin shi duk laifin mom ne da bata nuna ma Abbah bata son Auren da duk hakan bata faru da Noor ba.
“zan shiga lab ɗin naga halin da ake ciki kan binciken” Dr Lelarh ya faɗa “to shikenan dr” Abbah ya faɗa,anan tsaye ya barsu waiting chair dake kusa da su mom fatilah ta nufa ta zauna.
“Abbah ya kamata ka tafi gida ka huta tun asuba ka ke nan” dady ya faɗa yana kallon Abbah “Tahir da dai ka bari sun gama binciken sai na tafi”
“A'a Abbah gama binciken su ba yanzu ba,ka tafi kawai in sha Allah duk abunda ake ciki zan sanar da kai”
“to shikenan”Abbah ya faɗa,sauka su ka yi zuwa parking lot dake ƙasan ginin hospital ɗin,securitys ɗin shi da drivern shi na biye da su a baya,har gaban motar shi ya raka shi,da kanshi ya buɗema Abbah back seat ya shiga,shiga driver yayi securitys ɗin ma su ka shiga motocin su,key su ka yima motocin su ka nufi gate hospital ɗin,har sai da yaga ficewarsu daga hospital ɗin tukun ya juya da nufin komawa ciki idanunshi ne su ka sauka akan motar zaabith,
da mamaki yake kallon motar ganin driver seat a buɗe dama zaabith ɗin bai tafi ba kenan ya faɗa a zuciyarshi,nufar motar yayi,abun ya ɗan ɗaure mashi kai ganin motar a buɗe babu kowa a ciki,waige waige ya shiga yi amma bai ga kowa ba kasancewar parking lot a ƙasan ginin hospital ɗin yake ko compound ɗin asibitin ba'a gani,tunani ya fara ko tashin hankalin abunda ya faru ne yasa ya manta da ƙofar a buɗe,maida mashi marfin yayi ya rufe,yana shirin barin parking lot ɗin wata mota ta shigo, kallon motar yayi har su ka yi parking,buɗe door ɗin motar aka yi,mamy ce ta fito daga driver seat yayin da mom halima ta fito ta ɗayan side ɗin,back seat aka buɗe,hajiya zainab ce ta fito ƙanawar mom fatilah,cikin hospital ɗin su ka nufa kwata kwata ma ba su lura da dady dake tsaye ba, tsantsar tashin hankali ne kwance a saman fuskokin su,gaba ɗaya a kiɗime su ke,shima ciki ya nufa.
tun kafin su ƙarasa hajiya zainab ta fashe da ku ka ganin ƴar uwar ta ta ,mamy ma da mom Maryam ƙwalla su ke matsewa “garin yaya haka ta faru Aunty fatilah?” hajiya zainab ta faɗa cikin muryar kuka “zainab nima ban sani ba,mai aiki na ke sanar da ni wai taje ɗakin Noor ta sameta a kwance bakinta sai fitar da kumfa yake,lokacin da zan fito har mahaifinta ya fito da ita”
“amma waye zai bata guba,gida da ga ke sai mahaifinta?” mom halimatu ta faɗa “sai mai aikin su ba” a cewar mamy
“nima ban sani ba,amma ko waye ya cutar dani,bazan taɓa yafe mashi ba” mom fatilah ta faɗa tana goge hawayen dake zuba daga fuskarta.
dady ko da ya shigo bai dawo Emergency ward ɗin ba,VIP ward ya nufa in da aka kwantar da kainart,a bakin ƙofa ya tsaya yana ciro wayarshi daga cikin aljihu, Number uncle Mustafa yayi dialing dan gaba ɗaya hankalin shi bai kwanta da yanayin shi na ɗazu ba.
har kiran ya katse baiyi picking ba,nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke yana maida wayar cikin aljihun shi,tura ƙofar ward ɗin yayi ya shiga,kamar dai yanda ya barsu ɗazu a haka ya same su, Ammar da Aman tuni bacci ya ɗauke su a jikin Laatifa.
tunda ya shiga ya sauke idon shi akan mom dake zaune ɗayan side ɗin bed ɗin ta zabga uban tagumi,da wani irin kallon mai wuyar fassarawa ya ke binta,daga yanayin fuskarshi ta fahimci akwai matsala,dan damuwar data hango a fuskar shi ta wuce ta halin da kainart ke ciki, gaba ɗaya tasha jinin jikinta ganin irin kallon da yake jefa mata,kallon two to three minute yayi mata kafin ya sauke ajiyar zuciya,juyawa yayi ya nufi ƙofa ya fita,da mamaki take kallon shi har ya fice,tashi tayi tabi bayan shi a saman waiting chairs dake bakin ward ɗin ta same shi zaune,ƙarasawa tayi gaban shi tana faɗin “yallaɓai Lafiya?” ɗago da kanshi yayi, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai,zama tayi kusa da shi “yallaɓai magana nake,me ke damunka ne?” da buɗar bakin shi sai cewa yayi “mi yasa ki ka sauya Zulaihart,da ba haka ki ke ba?” da mamaki mom ke kallonshi “Janar nayi wani abu ne da yasa kace haka?” ɗan nisawa yayi kafin yace ”a da ke ɗin mai haƙuri ce, a da ke ɗin mai tausayi ce,a da ke ɗin mai tsoron cutar da bayin Allah ce, amma lokaci ɗaya kin sauya,baki ɗaya ɗabi'unki sun sauya” tunda dady ya fara magana mom ke bin shi da ido,idanunta sun kaɗa jawur,mijinta abun alfaharinta kullum ya buɗe baki Alkairinta yake faɗa yau an wayi gari da bakin shi yake faɗin ta sauya,tsintar kanta tayi a wani irin yanayi na karyewar zuciya “dan Allah yallaɓai kayi haƙuri ka faɗa man mi na aikata ka ke ganin na sauya,wa na cutar?”
murmushin takaici dady ya saki “a dalilin sauyin da ki ka yi kin cutar da yarinyar da ba taji ba ba ta gani ba Zulaihart” faɗuwa gaban mom yayi jin abun da dady yace,tuni hawayen da su ka taru idonta suka shiga zubowa “ka sani a duhu,dan Allah ka faɗa man mi na aikata?”
“saboda dalilinki mara tushe Noor tayi poisoning kanta, she's on life support!” wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi, da sauri ta dafe saitin zuciyarta kalmar life support ta shiga maimaitawa
“mi ye laifinta dan ta nuna tana son ɗanki,ai duk maso naka masoyinka ne” mom bata san lokacin data fashe da ku ka ba tana ambatar “innalillahi wa Innah ilaihi raji'un,wayyo Allah nah,Allah na tuba ka yafe man, wallahi ban yi haka da nufin cutar da kowa ba sai dan gudun halin da zan shiga Allah shi ne shaidata,dan Allah kayi haƙuri”
ƙalla dady bai ce mata ba sai ma kauda kai da yayi ya kalli gefe,yana jin kukanta amma ya zama dole ya nu na mata baiji daɗin abun da tayi ba
“magana nake kayi shiru, wallahi ba dan na cutar da ita naƙi amincewa ba,ban san har haka take son Irfan ba” still dady bai ce mata komaiba,hannuwanshi ta kamo “dan Allah ka yi haƙuri ka daina wannan fushin,in dai Aurensu ne na amince ko yanzu ku ke son ku ɗaura

Please Login or Register in order to submit comment