Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a haka rayuwarta zata ƙare.



idan tana tuna lokacin baya kafin suyi Aure sai taga kamar ba Zaabith ɗinta ba wanda kwata kwata baya son ganin ɓacin ranta,inda wani yace mata zai sauya mata bayan sunyi Aure bazata taɓa yarda ba saboda irin soyayyar da yake mata amma lokacin guda komai ya canza.



siraren hawayen da su ka zubo mata tasa hannu ta share,sauka tayi daga saman bed ɗin ta nufi toilet,alawa ta ɗauro ta zo ta kabbar sallah, nafilfilu ta shiga jerowa tana kai kukunta ga Ubangijin sammai,ta jima sosai tana Adu'a akan Allah ya shirya mata mijinta.



*UNITED STATE*


_*Las Vegas (Nevada)*_


*6:30 PM*


A kwance take saman leg press machine dake gym room ɗinta tana pressing leg ɗin ta up to down, active wears ne a jikinta vest da short Black color ta ɗaure sumar kanta da ribbon,kunnenta a manne yake da earphone tana sauraren sauti,sosai take press leg ɗinta ta haɗa uban gumi.


masu aikinta na zaune saman wasu benchs,hannun su riƙe da dumbbells,Gym room ɗin yana da girma sosai kamar gym center,babu kalar nau'in machine ɗin da babu a ciki gasu nan kala kala su exercise ball, punching bag, dumbbells,ellptical cross trainer, treadmill,bench press,step machine, trampoline, fitness cycle da dai sauran su.



Turo ƙofar Gym room ɗin a kayi,Aunty Sophia ce ta shigo cikin shigar shirt da dogon wando Black color ta ɗaure sumar kanta da ribbon black color, hannunta ɗauke jug Wanda ba komai bane a ciki sai tacaccen ruwan lemu na musamman wanda ta haɗa domin babynta, murmushi ta saki ganin yanda Nailarh ta dage bataji bata gani.


cikin Gym room ɗin ta ƙaraso,jug ɗin dake hannunta ta ajiye saman wani ɗan round table dake kusa da Nailar kafin ta nufi treadmill tahau,kunnawa tayi a hankali ta shiga running.


Nailar ta kai tsawan 30 minutes kafin ta dakata,dubanta ta kai ga Aunty Sophia, murmushi ta saki tana zame earphone ɗin dake kunnenta,alama jinjina tayi ma Aunty sophia, murmushi Aunty Sophia tayi tana maida mata martanin alamar da tayi mata.


Tashi tayi daga saman machine ɗin ɗaukar jug ɗin tayi ta nufi bench press,zama tayi,a hankali ta shiga shan lemun da Aunty Sophia ta haɗa mata, sai da tasha kusan rabin jug ɗin kafin ta ajiye,zufa har rige rigen fitowa take daga ƙofofin gashin jikinta,ɗaya daga cikin masu aikin ce ta nufo inda take da ɗan madaidaicin towel a hannunta.



goge mata gumin da tayi ta shiga yi,sai data tabbatar ta goge mata kafin ta koma mazauninsu,tashi Nailarh tayi ta nufi punching bag,boxing gloves dake ajiye saman wani table ta ɗauka ta zura a hannunta,a hankali ta fara kaima bag ɗin bugu kafin ta shiga kaimata duka da sauri sauri.



Wayarta dake hannun masu aiki ce ta fara ringing hakan ya dakatar mata da jin sautin da take da sauri mai aikin ta nufo ta,da katawa tayi, boxing gloves ɗin dake hannunta ta shiga zamewa,karɓar wayar tayi lokacin data gama zame hand glove ɗin, picking call ɗin tayi bayan ta duba sunan mai kiranta.


picking call ɗin tayi haɗi da kara wayar a kunne ba tare da tace ƙala ba,daga cikin wayar mahaifiyarta ce tace “hello baby”


shiru tayi tana turo baki kamar bada ita take magana ba, sake magana tayi tana faɗin
“baby fushi ki ke da momynki?”

still shiru tayi bata tanka mata ba, Aunty sophia dakatawa tayi da abunda take, in da nailarh take ta nufo, alama tayi mata da waye, turo baki nailarh tayi ba tare da ta bata amsar tambayar da tayi mata ba.


“please baby kiyi man magana mana, momynki ce fa?” mahaifiyar tata ta faɗa kamar zata sa mata kuka
“momy yaushe zaki dawo?” shine kawai abunda Nailarh tace mata,daga cikin wayar tana jiyo yanda mahaifiyar tata ta sauke ajiyar zuciya “kina so na dawo ne?”


“eh,gidan duk yayi baƙi saboda babuke a ciki, jina nake kamar ba ni ba saboda rashinki a kusa dani please momy ki dawo na gaji” ta faɗa kamar zata fashe mata da kuka, Aunty sophia na daga gefe tana kallonta, masu Aikin ma zuba mata ido sukai suna kallonta

“nima duk a daddafe nake saboda rashinki a tare da ni,amma ba sophia na nan ba?”
“tana nan mana, amma kin san matsayin kowa a cikinku daban a zuciyata, momy gaskiya ki dawo idan ba haka ba bazan sake zuwa Empire ba”
“baby kin cika rigima,nafa ce maki sai upper week zan dawo”


“ni dai na riga na faɗa maki bazan sake zuwa ko inaba muddin baki dawo ba”
“sorry zan dawo shikenan”
“yaushe?”ta jefa mata tambayar da son jin yaushe za tace
“yaushe ki ke son na dawo?”
“dis week”ta faɗa a shagwaɓe


“dis week yayi kusa Nailarh, ban kammala abunda nake ba fa”
“to zan biyoki”
“A'a ki bari zanyi ƙoƙarin squeezing schedules ɗina na dawo next week,hakan yayi maki?”
“Eh” ta bata amsa a shagwaɓe.


murmushi mahaifiyar ta saki tana faɗin “rigimammiyar yarinya kawai ina fatan baki manta da shipment ɗin mu ba?”
“ban manta ba”
“yawwa haka nake son ji, kiyi ƙoƙari ku isa port ɗin da wuri”
“please momy su Joseph suje port ɗin ni sai na same su a Orphanage ɗin”


“baby mi yasa ki ke son maida magana baya, na faɗa maki ke nake son kije,so nake ki koma ke ke kula da komai ba tare da wani ba”
“shikenan momy sai kin dawo”
“ok bye take care”
“bye” ta faɗa tana rejecting kiran, dubanta ta kai ga Aunty sophia data tsareta da idanu.

shafa fuskarta Nailarh tayi tana faɗin
“lafiya ki ke mana wannan kallon?”


girgiza mata kai tayi “ina za kije?”
“port” ta bata amsa tana nufar plyometric box ta zauna
“amma miza kiyi a can?”
“yau shipment ɗin mu zai ƙaraso”
“na sani, amma su Joseph ke zuwa ba ke ba,mi za kiyi a can??”


“su ke zuwa amma wannan time ɗin ni zanje” in da take Aunty sophia ta ƙaraso kamo hannunta tayi cikin nata “please Nailarh ki bari su suje,a kwai haɗari a irin wannan wurin kuma kinga dare ne”


“momy tace ni zanje, kuma Aunty sophi kin manta wacece ni,Nailarh ce fa, Queen, ni da nake kula da heart of vegas amsar kaya ne zai gagare ni”

“ba haka bane Nailarh, bana son wani abu ya sameki”
“ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ni”
“duk da haka Nailarh ko heart vegas da ki ke zuwa hankalina kullum a tashe yake, please ki bari suje da kansu” Aunty sophia ta faɗa da tsantsar damuwa tana matuƙar son Nailarh shiyyasa take tsoron wani abu ya sameta.



“nafa ce maki babu abunda zai same ni,ki kwantar da hankalin ki”
“shikenan” Aunty sophia ta faɗa ba dan ta so ba, murmushi Nailarh ta saki tana shafa gefen fuskarta

“na lura tunda ki ka ƙara tsufa tsoronki yayi yawa a kaina”
bige hannunta Aunty sophia tayi
“bana son shirme, kije kiyi wanka time ɗin dinner ɗinki yayi”


“ok muje yau kiyi man wanka da kanki” Nailarh ta faɗa tana miƙewa haɗi jan hannun Aunty sophia, saurin fisge hannunta tayi


“nailarh waike baki da kunya ne?” ɗaga mata gira tayi haɗi da faɗin
“eh” ta bata amsa a gadarance haɗi da kashe mata ido ɗaya, girgiza kai Aunty Sophia tayi

“idan ke baki da kunya ni inada ita”ta faɗa tana nufar ƙofar ficewa daga Gym room ɗin,bin bayanta Nailarh tayi tana sakin murmushi.


Part ɗin ta ta nufa,tana shiga direct toilet ta nufa anan ta samu Lara da Lolah da tun kafin ta shiga su ka san da zuwanta,babu ɓata lokaci su ka shiga abun da ya kawo su,ba su wani jimaba su ka kammala mata wankan ficewa tayi daga toilet ɗin ta nufi home of beauty ɗinta.



Aunty Sophia tana ficewa daga Gym room ɗin katafaren kitchen ɗin gidan ta nufa,tun daga waje ƙamshi abinci ya daki hancinta har sai da ta lumshe idonta,ciki ta ƙarasa,chafs ne maza da mata kowannan su ya duƙufa akan aikin haɗa dinner da su ke.


cikin girmamawa su ka shiga gaishe da ita,cike da kulawa take amsa masu tana nufar dinner table ɗin da su ka jera wermers,bubbuɗe wermers ɗin ta shiga yi tana ganin abunda su ka girka,jinjina kai ta shiga yi da alama ta yaba da aikin su.


“wannan girki haka sai kusa kunnen mutum ya tsinke tun kafin yaje bakin sa saboda daɗi,sannun ku da ƙoƙari”

washe mata baki su kayi suna faɗin “Thanks” jin jina kai tayi
“yanzu ba jimawa Nailarh zata sauko,ya kamata ku shirya dinning” da ok su ka amsa mata.


ficewa tayi daga kitchen ɗin,maza biyu daga cikin su suka shiga jidar wermers ɗin suna nufar ƙayataccen dinning room ɗin gidan,cikin ƙan ƙanin lokaci su ka kammala shirya dinning room ɗin.


Bedroom ɗin Nailarh ta nufa,direct home of beauty ɗinta ta nufa ta san bata wuce nan,tura ƙofar tayi ta shiga, a zaune ta hangota kan stool daga ita sai bathrobe Luna da Mary masu aikinta na gyara mata jiki.


cikin ɗakin Aunty Sophia ta ƙarasa,wuri ta samun saman ɗaya daga cikin chairs ɗin dake ɗakin ta zauna.

“baby an kammala haɗa dinner”
“thanks U Aunty sophi”ta faɗa tana miƙa mata hannunta,kama hannunta Aunty Sophia tayi.


har aka kammala mata gyaran jiki dana gashi hannunsu na a cikin na juna,a tare su ka fice daga ɗakin zuwa dinning room

Aunty sophia taso ta fara shiryawa amma ta nuna ba haka ba tafi son ta kammala dinner tukun.


A jere su ka isa katafaren dinning room ɗin,a zagaye yake da glass wall wanda ke waje zai iya hangen abunda ke ciki,daga sama ƙatuwar crystal Chandelier ce ta sauko ƙasa yayinda take bada wani irin haske mai ƙyatarwa, zungureren dinning table ne mai kyan gaske aƙalla yana ɗauje da 20 chairs,komai na cikin sa golding color ne
table ɗin a shaƙe yake da wasu irin warmers masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, kai tsaye zaka iya cewa da kumfar zinari aka yi su, sai ƙyalli su ke da ɗaukar ido.



chefs ne a tsaitsaye cikin dinning room ɗin, ciki su ka ƙarasa,cike da girmamawa chefs ɗin su ka shiga rissinawa suna gaishe da uwar ɗakin na su,ciki ta ƙarasa ba tare da ta amsa masu gaisuwar da su ke mata ba, cikin kulawa Aunty sophia tayi masu alamar jinjina,murmushi ne ya bayyana a fuskarsu.


kujerar dake gaban table wacce ke facing gaba ɗaya kujerun dinning ɗin Aunty sophia taja mata ta zauna,gaban table ɗin chefs ɗin su ka ƙaraso, ɗaya bayan ɗaya su ka shiga buɗe warmers, wani irin daddaɗan ƙamshi ne ya daki hancinta har sai dai ta lumshe ido.



madaidaicin plate ɗaya daga cikin chefs ɗin ya ɗauka haɗe da serving spoon, abunda ya girka ya ɗiba ya zuba a plete ɗin,a gabanta ya ajiye mata, jinjina kai tayi tana kama hannun Aunty sophia dake tsaye kamar sauran masu chefs.

“please ki zauna mana” ta faɗa fuska a marairaice, girgiza mata kai Aunty sophia tayi
“kiyi sauri kici time na tafiya” ƙwaɓe mata fuska tayi
“kin san bana iya cin abinci ni kaɗai” ta faɗa a shagwaɓe
“baby kina da rigima”
“ni dai naji, idan kuma baza ki bani ba na tashi”


“kema kin san bazan so ki zauna da yunwa, kwantar da hankalinki” Aunty sophia ta faɗa tana jan chair ɗin dake kusa da wacce take zaune ta zauna, spoon ɗin dake cikin abincin ta ɗauka, a hankali ta shiga ɗibar abincin tana bata,har wani lumshe ido take da alama ya mata daɗi, ba ƙaramin farin ciki chef ɗin yayi ba ganin yanda take lumshe ido.



spoon biyu zuwa uku ta amsa ta kauda kai, fahimtar abunda take nufi ne yasa wani chef ɗin saurin matsowa, shima ɗibar wanda ya girka yayi kamar na farkon ya miƙama Aunty sophia, amsa tayi tana ture wacan gefe, shima spoon biyu zuwa uku tayi ta kauda, ɗaya bayan ɗaya masu aikin su ka shiga zuba na su suna ba Aunty sophia,abun gwanin ban sha'awa chefs ɗin ke kallon su kamar uwa da ƴa,a ƙalla taci kusan kala shidda kafin ta buƙaci da Aunty sophia ta bata lemu.



ɗaya daga cikin chefs ɗin ne ya tsiyaya mata lemu a wani haɗaɗɗen cognac balloon glass ya miƙama Aunty sophia, amsa tayi tana nufar bakin Nailarh da cup ɗin,sai da tasha kusan rabi tukun ta janye bakinta,tashi tayi ta nufi ƙofar fita daga dinning room ɗin, ajiye cup ɗin Aunty sophia tayi tabi bayanta.


gyaran dinning room ɗin chefs ɗin su ka shigayi da kansu, su Luna na ganin ta nufi bedroom ɗinta su kayi saurin bin bayanta, dakatar da su Aunty sophia tayi, badan sun so ba su ka dakata, kwata kwata basa jin daɗin yanda Aunty sophia ke hanasu Aikin su wani lokacin, shiyyasa su ka fi son madam na gidan ita bata shiga hurumin Aikin su duk da kuwa itace mahaifiyar Nailarh.


A tsakiyar bedroom ɗinta ta sameta
“muje ko baby” Aunty Sophia ta faɗa tana kama hannunta cikin nata, dressing room ɗin ta su ka nufa
“yau ke zaki shirya ni ne?”
ɗaga mata kai Aunty Sophia tayi dai dai lokacin da take tura ƙofar dressing room ɗin.


faskeken mirror dake ɗakin Nailarh ta nufa zama tayi kan ɗaya daga cikin chairs ɗin Aunty Sophia kuma ciki ta ƙarasa.

ɓangaren haɗaɗɗun suit ɗinta Aunty Sophia ta nufa,bata wani tsaya ruwan ido ba ta ɗauki mata wasu Black color,wurin underwears ɗinta ta nufa plunge and high waist bikini ta ɗauko mata suma Black color.


mirror ta nufa hannunta ɗauke da kayan
“tashi kisa” Aunty Sophia ta faɗa tana miƙa mata kayan dake hannunta,kallon kayan tayi haɗi da kallon Aunty Sophia
“kin san bazan iya sa kayan nan ba”


ɗan hararar ta Aunty Sophia tayi “saboda baki da hannu ko mi?”
“amma ai kin san bani ke sawa da kaina ba,kuma ki ka hana masu saman shigowa,tunda har ki ka hana su shigowa dole ki saman da kanki”


cikin muryar lallashi Aunty Sophia tace “my baby mi yasa kullum ki ke son maida kanki baya ne,ya kamata ace yanzu da kanki ki ke wasu abubuwan ko dan saboda gaba,ko so ki ke kiyi Aure a haka komai sai anyi maki,ki sani ba kowane namiji bane zai lamunci wannan sangartar taki ba”


“wa yace maki ni zanyi Aure?” Nailarh ta faɗa tana tsare Aunty Sophia da idanu,yanayin fuskar Aunty Sophia ne ya canza ta rasa mike damun Brain ɗin Nailarh kwata kwata bata tunani irin na mutane.


“kina nufin haka zaki tabbata?”
“ƙwarai ma kuwa,ni Aure baya ɗaya daga cikin tsari na,a taƙaice ma na tsani maganar shi” ta faɗa tana wani ya mutse fuska.


girgiza kai Aunty Sophia tayi
“please ko dan saboda ni ki daure kina wasu abubuwan da kanki”
“bazan iya ba!” ta bata amsa a taƙaice, marairaice fuska Aunty Sophia tayi “please Nailarh Aunty Sophian ki fa?”


“sorry Aunty Sophi bazan iya ba ne”
“shikenan,yanzu karɓi ki sa”
“bazan iya ba” ta sake faɗa,lallashinta Aunty Sophia ta shigayi Dan ta samu ta sa kayan da kanta amma fir taƙi amincewa,dan dole Aunty Sophia ta shiryata da kanta.


sosai kayan su kayi mata kyau abunka da farar fata sai ta fito a ainihin baturiyar ta, high hills masu shegen tsini Aunty Sophia ta ɗauko mata tare da wristwatch haɗe da earrings,da kanta ta saka mata wristwatch da earrings ɗin bayan ta ajiye mata hills ɗin a ƙasa,zura ƙafarta tayi a takalmin.


“baby kin yi kyau sosai” Aunty Sophia ta faɗa, murmushi Nailarh ta saki “thanks” locker ta ta nufa,ƙofar fita Aunty Sophia ta nufa tana faɗin
“baby zan jiraki a parlor” Bata tsaya jin mi Nailarh za tace ba ta fice.


murmushi Nailarh ta saki ta rasa miye matsalar Aunty Sophi da gun kwata kwata bata son kallon locker ta bare akai da abunda ke cikin ta,buɗe locker tayi ta ɗauki pistol,a ƙugunta ta soke ta tukun ta rufe locker.


jerin shades ɗinta ta nufa,Black color ta ɗauka ta zura a idonta,ficewa tayi daga dressing room ɗin, wayarta dake ajiye saman makeken gadonta ta ɗauka.


a parlor ta samu Aunty Sophia na jiranta,tunda suka shigo main parlor gidan masu aiki ke bin Nailarh da kallo baƙaramin tafiya da su wankan nata yayi ba.


russunawa suka shiga yi suna gaishe da ita,hannun kawai ta ɗaga masu,a jere su ka samu motocin da zata fita da su a compound, jiki na rawa security guard ɗinta suka shiga gaishe da ita,suma hannu kawai su ka samu ta ɗaga masu,har gaban motar da zata shiga ƙirar ACURA RDX black color Aunty Sophia ta rakata,da kanta ta buɗe mata back seat ɗin motar ta shiga ta rufe,ɗaga mata hannu tayi tana juyawa ta koma ciki.



A jere motocin su ka fice daga gidan,babban titin da zai fitar da su gaba ɗaya street ɗin su ka hau,suna karya wata kwana motocin su Joseph suka kunno kai,haɗewa su kayi da nata motocin su ka ɗauki babbar hanyar da zata sada su da ƙaton PORT dake RENO.


Tafiya su kayi mai ɗan nisa tukun su ka iso PORT,ƙaton port ne iya ganinka,ga manya manyan truck dake kai kawo ɗauke da containers,a parking lot ɗin dake port ɗin su kayi parking.


kusan a tare su ka buɗe cars door ɗin su ka fito,motar Nailarh securitys ɗin su ka nufa tare da Joseph,car door su ka buɗe mata ta fito,ya mutse fuska tayi tana kallon port ɗin kafin ta kai dubanta ga Joseph.


“ina containers ɗin su ke ne?” ta faɗa ganin tarin containers dake wurin ga wanda trucks ke ɗawainiyar ɗauka.

“sai mun fara zuwa office ɗin C G tukun”
“ok mi kake jira”
“sorry boss” ya faɗa yana ɗan rissinar da kai haɗi da nufar office ɗin CG ɗin dake cikin port ɗin,tsaki taja tana komawa cikin motar ta zauna,bata rufe door ɗin ba ƙafarta ɗaya a ciki ɗaya a waje.



Bayan kamar 5 minutes Joseph ya dawo tare da wani mutumin dake sanye da uniform white color hannunshi ɗauke da wasu takardu, bayansu matasan samari ne har su shidda suna sanye da overall orange color.


har gaban motar su ka ƙaraso, ƙarasawa Joseph yayi bakin door ɗin motar
“boss ga CBP nan,shine in charge na cargos ɗin”

zame shade ɗin dake fuskarta tayi tana kallon mutumin da tunda Joseph yayi magana yake washe baki
“ƙarasa” Joseph ya faɗa yana nuna mashi bakin door ɗin motar,ƙarasawa mutumin yayi,fuskarshi ɗauke da fara'a ya gaishe da ita cikin girmamawa.


glass ɗinta dake hannunta ta ɗaga mashi alamar amsawa, murmushi ya saki yana jin jina kai, takardun dake hannunshi haɗe pen ya miƙa mata
“CG ya sa hannu sai naki kawai ya rage”
yamutse fuska tayi tana karɓar takardun da yake miƙo mata, sign ta shiga yi a takardun ba tare da ta ko karanta abun da su ka ƙunsa ba.


miƙa mashi tayi tana faɗin “what next?”
“za muje ne kiga kayan”
“ba sai naje ba kawai su ɗauko” ta faɗa
“please madam ganin yanada amfani,kuma zaki shaida adadin containers nawa ne su ka iso”


yamutse fuska tayi tana zuro ƙafarta da nufin fitowa ringing ɗin wayarta ne ya dakatar da ita,jawo wayar tayi tana duba sunan mai kiran nata Sweetheart shine sunan daya bayyana a screen ɗin.


picking call ɗin tayi haɗi da kara wayar a kunnenta,fitowa ta yi su ka nufi cikin inda containers su ke,cike da shagwaɓa take waya da mahaifiyar ta ta data kira dan taji ya abun yake tafiya.


a gaban wani ƙaton container ship dake bakin ruwa, trucks na jidar containers su ka tsaya, Nailarh na can bayan su tana waya,nuna ma Joseph containers ɗin su da trucks su ka ɗauka har guda biyar yayi.


jinjina kai Joseph ɗin yayi
“aikin ka yayi kyau,fatan kayi waya da Madam?”
“eh tun kafin ma ku ƙaraso ta kira ni”
“ok good,muje ko” Joseph ya faɗa yana nufar Nailarh harta kammala wayar.


Juyawa tayi ta koma inda su kayi parking,motar ta shiga security daya buɗe mata ya rufe door ɗin,sallama Joseph yayi ma in charge ɗin ya shige motar shi, a jere su ka fice daga port ɗin trucks ɗin containers ɗin su na biye da su...


A jere su ka fice daga port ɗin trucks ɗin containers ɗin su na biye da su, wata hanya su ka ɗauka daban, tafiya su kayi mai ɗan nisa kafin su ka iso wani ƙaton orphanage, daga yana yin ginin zaka san cewa bana ƙana nan mutane bane,yanada girma sosai.


horn su kayi a bakin gate ɗin, can cikin bacci masu gadin orphanage ɗin su ka ji ƙarar horn ɗin, ba suyi mamakin jin horn da tsohun dare nan ba saboda mamallakan orphanage ɗin sun saba yi masu shigar dare irin haka.


ɗaya daga cikin securitys ɗin ne ya leƙo ta ƴar ƙofar dake jikin gate ɗin,kallo ɗaya yayi ma motocin ya fahimci ko su waye, a hanzarce ya koma ciki, gate ɗin ne ya shiga zugewa zuwa gefe guda, da gudu motocin su ka danna kai zuwa cikin orphanage ɗin,da sauri securitys ɗin su ka shiga motocin dake bakin gate ɗin su ka bi bayan motocin.


wasu irin gine gine na zamani su ka shiga wucewa ba laifi Orphanage ɗin yanada girma sosai, a bakin wasu manya manyan store har guda biyar su ka yi parking,fitowa su ka shiga yi daga cikin motocin su, wani matashin saurayi ne ya fito daga motar Joseph tun ɗazu sai yanzu ya fito,black American ne, neck ɗin shi yasha zanen tattoo kallo ɗaya zaka mashi ka gane riƙaƙen ɗan duniya ne.



motar da Nailarh ke ciki Joseph ya nufo, back seat ya buɗe mata, fitowa tayi a dai dai lokacin da securitys ɗin ke ƙarasowa, da sauri su ka nufeta, gaishe da ita su ka shigayi cikin girmamawa, ko arziƙin kallo basu samu daga gareta ba, trucks ɗin ta nufa umarnin a buɗe su ta bada,fitowa drivers ɗin su ka shigayi,kowace truk mutum uku ne su ka fito daga cikinta, babu ɓata lokaci su ka shiga buɗe bayan truck ɗin, wasu irin tarin kwalaye ne a bayan truck ɗin, da hannu tayima Joseph alama da ya zo, da sauri ya nufo in da take, wayarta ta miƙa mashi,da sauri yasa hannu ya amsa,video ya shiga ɗaukar kayan.


truck ɗayace ba'a buɗe ba kallon drivers ɗin tayi “wannan fa?” ta tambaya tana nuna masu truck ɗin, Joseph ne yayi saurin faɗin
“ina tunanin itace wacce madam tace kar a shiga da ita”

cike da bada umarni ta furta “ku buɗeta” da sauri Joseph yace “ba kuji ana magana” a hanzarce su ka shiga buɗe truck ɗin, wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi a lokacin da tayi arba da abunda batayi tunanin gani ba, da tsantsar mamaki take kallon matasan ƴan mata da samari dake bayan truck ɗin an rufe masu bakunansu yayinda hannayen su ke a ɗaure.



da sauri Joseph ya sauke wayar ƙasa, da mugum mamaki tashiga kallon drivers ɗin kafinta sauke idanunta akan Joseph, cike da tuhuma ta furta“miye wannan?”babu wanda ya iya buɗe baki a cikin su ya bata amsa, suma sun shiga ruɗan, sunyi matuƙar mamakin ganin yaran, wata irin gigitacciyar tsawa ta daka masu kamar ba Nailarh ba.


“tambayar ku nake miye wannan, ina aka samu wannan yaran??”
ɗaya daga cikin drivers ɗin ne yayi ƙarfin halin bata amsa “mu ma bamu sani ba kawai dai mun samu truk ɗin a cikin jadawalin da miss m...“ kasa ƙarasawa yayi saboda tsawar data daka mashi, bashi da tayima tsawar ba hatta Joseph sai da ƴan hanjin cikinsa su ka kaɗa.


gaba ɗaya fuskarta ta rikiɗe da tsantsar ɓacin rai, a fusace ta buɗe baki da nufin magana amma sai ringing ɗin wayarta ya dakatar da ita, da saurin Joseph ya miƙa mata wayar, picking call ɗin tayi ba tare da ta ko duba sunan mai kiran nata ba.


muryar mahaifiyarta ce ta daki dodon kunnenta daga cikin wayar “hello baby har kun kammala” saurin maida kiran tayi zuwa video call, back camera ta kunna ta saita wayar dai dai inda truck ɗin take.


“momy wannan container ta waye?” ta faɗa ranta a matuƙar ɓace, a kwance take saman hammock chair a bakin beach daga Ita sai bra da wani matsiyacin pant mai igiya gefe da gefe kusan rabin mazaunanta a waje,ta rufe idonta da baƙin shade hannunta a riƙe da coconut drink tana sha.


cike da bariki irin bata fahimci mi Nailarh take nufi ba tace “wace container baby?”
“wacce idanunki su ka nuna maki” ta bata amsa dai dai da tambayarta dan ba ƙaramin ɓaci ranta yayi da ganin yaran ba.
“sorry baby na manta banyi maki bayani ba,marayu ne basu da gata, gashi suna fama da wata lalura na turo su nan ne saboda suna buƙatar emergency treatment”


maida front camera tayi tana jifar mahaifiyarta ta da wani kallon rainin wayao
“amma momy kwata kwata yaran

Please Login or Register in order to submit comment