Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiye saman table ɗin dake gaban sofa, a hankali take Operating ɗinta,Joseph na zaune saman sofa mai mazaunin mutum ɗaya, ya ɗau wankan black suit,rigar suit ɗin na ajiye saman hannun sofa da yake zaune, hannushi riƙe da fils.


daga gefe chief security ɗin gidan ne sai masu kula da C C TV sai drivers ɗin Nailarh da su Luna sai chefs,gaba ɗayan maids ɗin ne Aunty sophia ce kawai babu.


Aikin ko wane ta ke bincika dan sanin abun da ya faru bayan bata nan duk da suna sanar da ita abunda ke faruwa lokacin da bata nan, drivers ɗin Nailarh ta fara tsarewa da tambayar da bata nan ina da ina su ka kai Nailarh.


Alex ne ya shiga zayyana mata inda Nailarh taje bayan bata nan,shi ke driving motar Nailarh duk za su fita kuma shine shugaban drivers ɗin gidan baki ɗaya, jinjina kai ta shiga yi har ya kammala sanar da ita, maida hankalinta tayi kan su Luna suma dai magana ɗaya ce da Alex, sallamar su tayi su koma bakin aikin su.



Masu kula da C C TV gidan ne su ka fara kora mata bayanin kaf abunda ya faru,babban cikin su ne ya sanar da ita “ma'am still Sophia's CCTV doesn't work” jin jina kai tayi tana ɗan dakatawa da aikin da take
“duk gyaran da a ka yi?”
“yes ma'am” da kamar za tayi magana sai kuma ta fasa
“u can go” ta faɗa, gabanta ɗaya daga cikin su ya zo flash ya miƙa mata kafin ya fice.


tana cikin magana da Chefs Aunty sophia ta zo,kallo ɗaya za kayi mata ka hango tsantsar damuwar dake kwance a fuskarta,gaishe da miss Malika tayi da kulawa ta amsa mata “chefs sun ce baki lafiya,how do u feel now?”

“am feeling much better”
“I'm points hope quick recovery dear”
“thank U ma'am”


Nailarh ce ta fito daga bedroom ɗinta shirt da short ne a jikinta ta ɗaure gashin kanta da ribbon, ciki parlorn ta nufo, tunda ta fito su ka kafeta da ido musamman Joseph har wani ɗaga kai yake dan ya kalleta da kyau.


tana ƙarasowa tayi hugging ɗin Aunty sophia ta baya “good morning”
“morning baby, kin tashi lafiya”
“lafiya lau” Nailarh ta faɗa tana raba jikin su
“mi ya samu hannunki?” ta faɗa yayinda take riƙo hannun Aunty sophia

“yankewa nayi da glass”

“Ayyah, sorry chefs sun ce man baki da lafiya, mike damunki”
“it was a headache,but i got better now”
“is this tumor the cause you of the headache?” ta faɗa da tsantsar kulawa


girgiza mata kai Aunty sophia tayi “bashi bane”
“sorry” Nailarh ta faɗa kamar ƙaramar yarinya
jin jina mata kai Aunty sophia tayi.


mahaifiyarta dake zaune kan sofa ta nufa, ɗan rissinawa tayi ta sumbacin lips ɗinta, saurin rintse ido Aunty sophia tayi tana jin wani irin ɗaci a ranta.


“good morning” Nailarh ta faɗa
“morning beb” malika ta faɗa tana kashe mata ido ɗaya, kusa da ita ta zauna tana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.

“good morning boss” Joseph ne ya faɗa, amsa mashi tayi tana ɗaga mashi hannu, gaishe da ita chefs ɗin dake tsaye su ka shiga yi da kulawa take amsa masu.


sallamar chefs ɗin miss Malika tayi bayan sun gama bata amsoshin tambayar da tayi masu, sofa dake kusa da wacce Joseph ke zaune miss malika ta nuna ma Aunty sophia, zama tayi tana fuskantar ta.


Ta sowa Joseph yayi daga mazauninshi files ɗin dake hannunshi ya miƙama miss Malika, amsa tayi tana jinjina mashi kai “zaka iya tafiya,idan na kammala dubawa zan tura maka replys ta email”


“ok ma'am, have a nice day” rigar suit ɗinshi dake ajiye kan hannun sofa ya nufa,ɗaukar rigar yayi haɗe da briefcase ɗin shi dake gefe “bye” ya faɗa yana ɗaga masu hannu, jinjina mashi kai miss Malika tayi, ficewa yayi daga parlorn.


ɗaya daga cikin chefs ne ya shigo hannunshi ɗauke da madaidaicin tray wanda ya shirya masu coffee, Nailarh ya nufa ya fara miƙa mata ta ɗauka kafin miss Malika da Aunty sophia, barin parlorn yayi ya koma kitchen.


“Sophia!” miss Malika ta kira sunanta, ɗagowa Aunty sophia tayi ta fuskanceta da kyau

“William ya sanar dani har yanzu C C TV part ɗinki bata aiki, what is the problem?” ta faɗa tana kafeta da ido


“nothing, but naga is not good ace har a bedroom da bathroom an sa mana camera ba, a barshi a iya parlor kawai,bedroom and bathroom is our part of secret” tunda ta fara magana Malika ta kafeta da ido

“but if that offends u, am very sorry”
“saboda bai dace ba yasa ki ka lalata na part ɗinki?” cike da tuhuma miss Malika ta faɗa

“please momy Aunty sophia ce fa, mi kike son sani a game da rayuwarta da har sai kin sa mata C C TV, gaskiya i'm really not happy” Nailarh ta faɗa da alamar rashin jin daɗin abunda momy tata tayi


“shikenan nima ba dan komai yasa nake sawa ba sai dan na riƙa sanin halin da ku ke ciki,taking care of ur health is my responsibility”
“hakan yana da da kyau,we thank u for ur care for us” Aunty sophia ta faɗa, jin jina kai kawai Malika tayi, tashi Aunty sophia tayi ta nufi kitchen dan ta duba chefs, da kallo Malika ta bita har ta ɓacce ma ganinta.



“honestly momy baki kyauta ba, how many years Aunty sophia ke tare dake dan mi zaki sa mata C C TV a part,wannan old women ɗin mi kike tunanin zata iya aikatawa, ban da kula dani babu abunda take a gidan nan, that's why I love her,babu ruwanta”


wani kallon banza Malika tayi mata“u love her, ban gane ba?”

“yeah, ina jinta tamkar mahaifiyata wacce ta haife ni” harara Malika ta watsa mata
“ni fa?”
“u are special,ur position is different sweetheart” murmushi Malika ta saki.


❤💫❤💫❤💫❤💫❤💫❤


Tun da malika ta dawo Aunty sophia ta ƙauracema Nailarh ko part ɗin ta ta daina zuwa, iya karta ta duba masu aiki ta koma part ɗinta,duk wata hanya data san zata haɗata da malika tare da Nailarh tayi blocking ɗinta.

Yanzu ma tana kitchen ne tare da chefs tana sanar da su abubuwan da ya kamata su yi saboda celebration ɗin da za suyi bayan kammala wasan da Nailarh zata gabatar a yau, dama al'adarta ne duk ƙareshen shekara suna gabatar da wasa wanda ya fi kowane a N R T.


Duk wanda yake ji da kanshi a wasan doki zaka sameshi a ranar gasar, ƙwararrune daga yanki daban daban na ƙasar dama wasu ƙasashen ke halartar wasan, tsawan shekara biyar kenan suna gabatar da wasan har yau ba'a samu wani wanda yayi zarrar da zai zo na ɗaya a gasar wasan ko wane lokaci Nailarh dai.


A hankali ta lallaɓo masu aiki na kallonta amma ba halin suyi magana saboda gargaɗin da tayi masu,hannuwanta tasa tana rufe mata eyes ɗinta ta baya.


Murmushi Aunty sophia ta saki ta san babu wanda zaiyi mata hakan face ita, hannunta dake kan idanunta ta kama
“baby” ta kira sunanta, sakin idanunta Nailarh tayi tana ɓata fuska


“u are too quick to recognize ” ta faɗa tana turo baki, murmushi chefs ɗin suka saki
“banda abunki Nailarh waye zai yiman haka bayan ke,how was ur night,I hope u slept well?”
“fine,na biyoki har nan ne dan naji laifin me na maki ki ke avoiding ɗina tow days?”

gaishe da ita chefs ɗin su ka shiga yi,jinjina masu kai kawai tayi, shafa fuskarta Aunty sophia tayi

“baki man laifin komai ba, na barki ki samu enough time with ur momy” taɓe baki Nailarh tayi
“amma ai kin zo har ɗaki kiyi wishing ɗi na ko?”
“kema kin san zan zo, ina duba chefs ne”

“baby!” aka faɗa daga bayan su, saurin kai dubansu su ka yi ga Miss Malika dake tsaye, PJ ne a jikinta da alama daga bacci take.

Cike da girmamawa suka shiga gaishe da ita, da kulawa ta amsa masu tana nufar cikin kitchen ɗin , kama hannun Nailarh tayi “ashe kina nan ki ka bar ni sai wahalar nemanki nake”


“nazo wajen Aunty sophia ne”
“ok muje” jan hannunta tayi
“Aunty sophia sai kin zo” jinjina mata kai tayi, ficewa su kayi daga kitchen ɗin.



*ABUJA NIGERIA💫*


Shigowar su kenan daga school duk a gajiye su ke,Yumnah tun a parlor ta cire mayafin dake kanta, a saman bed ɗinta su ka yada zango.


“wallahi sis am very tired
har ƙosawa nayi a kammala lectures” Yumnah ta faɗa tana ya mutse fuska
“me too, yanzu bani da wani buri da wuce na watsa ruwa na kwanta na huta before magrib” Nainarh ta faɗa tana nufar dressing room.


kwanciya saman bed ɗin Yumnah tayi “ni gaskiya sai na tashi daga baccin tukun zan yi wanka”


Nainarh na shiga dressing room ɗin jakarta ta a jiye tukun ta cire kayan jikinta ta ɗaura towel, bedroom ɗin ta koma, Yumnah na nan kwance har bacci ya fara ɗaukarta.


toilet ta nufa ta watsa ruwa kafin ta fito, dressing room ta koma,gown ta saka mara nauyi kafin ta dawo bedroom ɗin kwanciya tayi kusa da Yumnah.


Duk yanda take jin bacci kafin ta kwanta, tana kwanciya taji kwata kwata baccin ya ƙaurace ma idonta,juyi ta shiga yi a bed ɗin Yumnah kuwa baccinta take hankali kwance.


shiru tayi tana ƙurama sailing ido, ba komai ya faɗo mata a rai ba sai photon da ta gani a part ɗin Abbah, bata san waye a photon ba amma haka nan ta kwaɗaitu da san sanin waye shi, kullum tana son tambayar Yumnah amma sai ta manta.


kallon fuskar Yumnah tayi kafin ta maida idonta akan teddy bears ɗinta dake ajiye saman head board ɗin bed ɗin.


ƙaramin tun bata da wayau mahaifiyarta ta bata shi, babban kuwa mahaifinta ya bata shi a matsayi kyautar ƙarin shekara lokacin data kai kimanin shekara goma.


Murmushi ta saki lokacin data tuna shirmenta na yarinta, haka zata tasa teddys ɗin a gaba tana faɗin ga momy ga dady,haka iyayenta za su tasata gaba suna dariya, duk tana tuna rayuwarta da iyayenta abun ba ƙaramin nishaɗi yake bata ba,amma lokaci ɗaya komai ya rushe, duk ta tuna kisan wulaƙantaki da aka yima mahaifinta da sharrin da aka da bai baye mahaifiyarta dashi sai taji wani ƙunci ya mamaye zuciyarta, ta rasa laifin mi su ka aikatama wanda yayi masu haka.



Adu'arta a kullum Allah ya toni asirin wanda yayi silar rushewar farin cikin su, shima Allah ya rusa nashi farin cikin, ya tozarta rayuwarshi kamar yanda ya tozarta ta su, sosai tayi nisa a duniyar tunani ringing ɗin wayar Yumnah ne ya dawo da ita hayyacinta, a jiyar zuciya ta sauke tana jawo jakar, wayar ta ciro, duba sunan mai kira tayi,ya Naeem ta gani.


da sauri ta ɗan bubbuga kafaɗar Yumnah “ki tashi ya Naeem na kira” juya kwanciya Yumnah tayi
“please ki ɗaga kice mashi bacci nake” picking call ɗin tayi tana kara wayar a kunenta


“Assalamu Alaikum” ta faɗa, on the other hand ya Naeem ya amsa mata sallamar
“ya Naeem ina wuni”
“lafiya lau Yumnah, kun dawo ne ko har yanzu kuna school?”
“ba ita bace, Nainarh ce” Nainarh ta bashi amsa
“yawwa Nainarh dama ke nake nema, kun dawo daga school ɗin?”


“eh” ta bashi amsa
“ok,meet me in the garden now” a sakale ta amsa mashi,mamaki ne ya cikata, neman mi yake mata

“right now” ya sake jaddada mata haɗi da rejecting ɗin call ɗin


“ni kuma, neman mi yake man” ta faɗa da tsantsar mamaki, ajiye wayar tayi ta nufi toilet, bata wani jimaba ta fito, dressing room ta nufa, hijab ta ɗauko,ficewa tayi daga ɗakin.


bata samu kowa a parlorn ba, tun daga nesa ta hango su saman chairs shi da ya Adnan a garden ɗin, waya ce kare a kunen ya Naeem ɗin da alama waya yake, tunda ta tunkaro su ya Adnan ya kafeta da ido yana kallota harta ƙaraso in da su ke, sallama tayi masu ya Adnan ne ya amsa mata ya Naeem kuwa hannu kawai ya ɗaga mata.


Cike da ladabi tana ɗan rissinawa ta gaishe da Ya Adnan ɗin, da kulawa ya amsa mata yana sakar mata murmushi ya nuna mata chair dake fuskantar wacce su ke zaune dan ta zauna, murmushi ta saki “nagode” ta faɗa tana zama.


“ya school,fatan kun dawo lafiya?”
“lafiya lau Alhmdllh” masha Allah ya faɗa, hankalin su ne ya koma kan ya Naeem dake waya


“it's a favor i'm asking for, please ka taimaka ranar birthday ɗinka ka zo,ya ɗauki ranar birthday ɗinka rana mai daraja da mahimmaci, ka daure a wannan karon ka tabbatar mashi da darajar ranar,the anger u have with him is enough, dan Allah ka kawo ƙarshen wannan guje mashin da ka ke”

ɗan dakatawa yayi da magana ya can ya cigaba

“kayi shiru ba kace komai ba, ka sa ni yanda ya ke sonka ko mu dake tare dashi baya mana son da yake maka, baka tare dashi amma duk wani abu daya shafeka baya wasa dashi,ka sani duk abunda zaiyi mana a rayuwa sai yayi maka,more than u think,wasu har gani suke kamar ya samu taɓin hankali a kan ka saboda wasu abun da yake hankali ma bazai ɗauka, please yaci albarkacin wannan ƙaunar da yake maka kayi haƙuri ka daina wannan fushin da shi” sosai ya Naeem ya kwantar da murya yana bashi haƙuri duk dan ya sauko.


zuba mashi ido Nainarh da ya Adnan su kayi, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai waye wannan ake haɗashi da Allah irin haka amma yaƙi yayi abunda ake so.


“shikenan kayi duk abunda ka ke ganin shine dai dai, amma ka sani haƙƙin baƙin cikin da kake cusa mashi bazai barka ba, he's ur father, ko wane irin laifi zaiyi maka aduniya he didn't not deserve to be anger with him” yana gama faɗar haka yayi rejecting call ɗin.


haka nan Nainarh ta tsinci kanta da rashin jin daɗin abun, bata san ko waye ba amma bai kyauta ba mahaifa ba abun wasa ba ne.


“in wuni ya Naeem”
“lafiya lau Nainarh, ya school”
da Alhmdllh ta amsa ma shi
“dama akwai wasu maganganu da nake son zamu tattauna game da abunda ya faru da dadynki”
tunda ya faɗi haka yanayin fuskarta ya canza, fahimtar hakan ne yasa shi cewa

“karki damu ba wani abu bane kawai ƴan tambayoyi ne zanyi maki,in dai ki ka bani haɗin kai in sha Allah za muyi nasarar gano wanda su ka kashe shi”

“in sha Allah zan baka haɗin kai, duk wani abu dana sani zanyi ƙoƙarin sanar da kai”

“yawwa haka nake son ji,
da na so muyi maganar yanzu,but bana da time, zuwa ranar Saturday za muyi magana ko kuje can gida keda Yumnah ku same ni”

“to shikenan, Allah ya kaimu”
“Ameen ya Allah, za ki iya tafiya kawai” to tace ta na tashi daga chair, sallama tayi masu ta koma cikin gidan, ranshi ya rigada ya gama ɓaci bayajin zai iya maganar da za suyi shiyyasa kawai ya sallameta.


tunda Nainarh ta fito daga gidan ta nufo garden yake tsaye bayan pillar da waya a hannunshi, da alama video yake ɗaukar su, baƙaƙen kaya ne a jikinshi ya rufe ko ina na jikinshi banda idanun shi babu wani abu da ake iya gani daga jikinshi.


Nainarh na tunkaro ƙofar shiga gidan yayi saurin ɓoyewa yana zura wayar Aljihun wandon jikinshi, kowaye da alama leƙen asiri yake masu.


ɗan dukan kafaɗar ya Adnan ya Naeem yayi ganin ya bi Nainarh da ido
“ya dai,lafiya ka kafe yar mutane da ido ka ke binta da wannan kallon ƙurillar?”

kauda kai gefe ya Adnan ɗin yayi yana sakin murmushi
“ba komai, kawai dai tana burgeni ne she's so innocent” murmushi ya Naeem yayi
“ka tsaya dai iya haka”

dariya ya Adnan ɗin yayi yana girgiza kai “ya ku ka yi da SAM ɗin ya amince kuwa?” ya Adnan ya faɗa yana kallon fuskar ya Naeem, tsaki ya Naeem yaja

“ka kyale SAM kawai Adnan,na rasa gane wane irin bauɗaɗɗan mutum ne shi, Allah ma muna mashi laifi ya yafe mana sai shi ne bazai yafe ba, na rasa a wajen ubanwa ya gaji wannan baƙar zuciyar da idan ya juyama abu baya ya juya mashi kenan?”

“uncle Mustafa shi ka manta tashi kalar zuciyar ne?”
“uhmmm Allah gara uncle Mustafa dashi, tsawan shekara nawa kenan ana fama dashi amma ya maida mutane shashashu, ka du ba fa ka ga irin haukan da dady keyi a kan shi wannan bai isa ba ace ya yi haƙuri,bawan Allah nan sau nawa yana taka ƙafa ya bishi amma haka zai ƙaraci zamanshi ya dawo bazai taɓa ganinshi ba haba” ya ƙare maganar cikin fushi


“Allah ya kyauta, amma SAM lamarin shi sai shi, ni kaina sai na kusa haɗa shekara banji muryarshi ba” ya Adnan ya faɗa
“wallahi zanyi mashi maganin abun da ke damunshi ne” murmushi ya Adnan ya saki
“ai da yake kunfi kusa, dama da kai yake uban ba da dady ba” tsaki kawai ya Naeem yaja.


*Queen Kainart💫*


tafe take kwata kwata bata lura da mutum dake tahowa ba duk da ƙofar ta glass ce,shima hankali shi baya gaban shi yana a kan wayarshi da yake latsawa.

saurin ja da baya tayi dalilin karon da su ka yi,wayar dake hannunshi ta faɗi ƙasa, dafe goshinta da ya bigi broad chest ɗin shi tayi,wani irin zafi ne ya ziyarci kwakwalwarta, a masifance ta ɗago tana kallonshi ido cikin ido

“dallah malam baka gani ne or are u blind da ka ke tafiya baka kallon gabanka??” ta faɗa tana wani zazzare mashi ido, wani irin haushin shi da tsanar shi take ji a ranta.


kasa magana yayi saboda mamaki daya rufe shi, ta bugeshi har ta yar mashi da waya ƙasa amma ta rufeshi da faɗa kamar wani sa'anta,mamakinshi ma a ina ta samu confidence ɗin yi mashi rashin kunya.

harara ta sake watsa mashi haɗi da jan tsaki,raɓawa tayi ta gefenshi zata wuce, rai a ɓace ya fisgo Arm ɗinta, gaba ɗaya ta tafi taga taga zata faɗin, riƙota yayi sosai, idan da abunda ya tsana a rayuwarshi tsaki, ya tsani tsaki musamman ace mace ce tayi mashi shi.

Raba idanu ta shiga yi a fuskarshi, ba ƙaramin tsorata tayi da yana yin shi ba,cike da mugunta ya sake matse hannunta,saurin rintse ido tayi saboda wani zafi daya shigeta.


Murya a kausashe yace “wa ki ke ma tsaki?” banza tayi da shi ƙoƙarin ƙwace kanta kawai take daga riƙon da yayi mata, tsawa ya daka mata “tambayarki nake wa ki ke ma tsaki??” ya faɗa yayin da yake murɗe hannunta

fashewa tayi da kukan azaba, murya na rawa tace “ai ba da kai nake ba”
“dawa ki ke” ya faɗa fuska a ɗaure
“dan Allah kayi haƙuri”
“tsaran wasanki ne ni?” girgiza mashi kai tayi hawaye na bin cheek.


“bani wayata” ya faɗa yana nuna mata wayarshi dake yashe a ƙasa
“ka sakar man hannu to” sakin hannunta yayi, duƙawa ƙasa tayi ta ɗauko mashi wayar
“gashi” ta faɗa tana turo mashi baki.


amsar wayar yayi yana sake riƙe hannunta “this should be the first and last time da za kiyi gigin yiman rashin kunya if not, sai na ɓaɓɓalaki a gidan nan useless”

“IRFAN” su ka ji an faɗa a bayan su.

saurin sakin hannunta yayi yana juyawa bayanshi,dady ne da uncle hashim,tun lokacin da su ka yi karo su ke tsaye suna kallon su.

hannunta da Irfan ɗin ya riƙe ta shiga murzawa saboda zafin da yake mata

“Irfan mi ya haɗaka da ita?” dady ya faɗa
“babu komai, ina wuni Uncle”
“lafiya lau” uncle hashim ya faɗa, saurin barin wajen Irfan yayi ya nufi garden wajen su ya Naeem.


“zo nan Nainarh”dady ya faɗa yana mata alama data zo, nufo su tayi har time ɗin hawaye na bin kumatunta, hannu dady yasa ya shiga share mata hawayen
“kukan ya isa haka, mi yasa ki ka yi mashi rashin kunya?”
“babu komai”
“he's ur elder brother, kar na sake gani,kina jina ko”
“eh dady in sha Allah bazan sake ba”


“haka nake son ji, ga Uncle ɗin ku nan ku gaisa” ya faɗa yana nuna mata Uncle hashim dake tsaye yana kallonsu
“in wuni Uncle”
“lafiya lau, ya ki ke, ya school??”
“lafiya lau Alhmdllh”
“masha Allah, Allah ya taimaka”
da Ameen ta amsa tana barin wurin ta nufi bedroom ɗin su.

tana shiga bedroom ɗin saurin zame hijab ɗin jikinta tayi tana kallon hannunta da Irfan ɗin ya riƙe wurin har yayi ja.


wasu hawaye ne su sake taruwa a idonta “mugu kawai” ta faɗa tana turo baki.



*Queen Kainart*💫


“muje ko” ya dady ya faɗa yana kallon Uncle hashim
“gida zan tafi”
“tafiya dai hashim, ai ka shiga ku gaisa da Zulaihart ko?”
“A'a yaya tafiya zanyi, idan na sake dawowa mun gaisa”
dady ya faɗi haka ne kawai amma dama ya san uncle hashim bazai tsaya ba in dai dan su gaisa da mom ne
“shikenan ka gaishe da mutanen gidan”
“za su ji, sai anjima” jin jina mashi kai dady yayi yana nufar sama zuwa part ɗin shi.


ficewa uncle hashim ɗin yayi amma instead of ya fice daga gidan baki ɗaya sai ya nufi part ɗin Mamy, bai samu kowa a falonta ba, masu aiki na part ɗin su Fa'iza na gidan shi wurin Balqis.


direct bedroom ɗinta ya nufa, bai sameta a ciki ba sai ƙarar ruwa da yaji a cikin toilet alamar tana ciki.


bed ɗinta ya nufa, zama yayi yana kwantar da kanshi jikin head board, wayarta dake ajiye kan nightstand ya ɗauka, babu password a wayar hakan ya bashi damar shiga contact da messages ɗinta.



turo ƙofar toilet ɗin tayi ta fito tana yarfe hannunta da alama alwala tayi, da mamaki take kallonshi bata san yaushe ya shigo ba, mamakin ganinshi a irin wannan lokacin ne ya hanata ƙarasawa gare shi.


wayarta dake hannunshi ya ajiye yana zuba mata mayatattun idanunshi “ƙaraso mana ki ka tsaya nan” ya faɗa ganin tayi tsaye kamar an dasata.


cikin ɗakin ta nufo kamar yanda ya umarta “yaushe ka shigo, baka tsoron wani ya ganka a irin wannan lokacin??” jin jina mata kai yayi alamar eh
“eh fa kace, baka gudun yayanka ya shigo gidan?”
“tare mu ka shigo da shi, yana part ɗin shi”
“amma shine ka shigo part ɗin, baka tsoron ya shigo part ɗina??”


“wait mabaruka kinyi farin cikin gani na ko na tashi na kama gabana?” ya faɗa yana ɗan tsuke fuska alamar rashin jin daɗin tambayoyinta
“kaima ka san am really happy to see u but kawai dai bana son abunda zai jawo mana matsala”


sauka yayi daga saman bed ɗin ya nufo inda take, kama hannunwanta yayi ciki nashi
“naga hankalinki bai kwanta da zuwana ba,lee me go” ya faɗa yana sakin hannunta, saurin kamo hannunshi tayi
“tunda har kai hankalinka a kwance yake bana da wata matsala”


“are u sure?”
“really sure, kai da kazo ma baka damu ba sai ni daka iske”
a jiyar zuciya ya sauke yana wani lumshe ido
“why did u not pick my call yesterday?”
“am with u brother, ka san jiya a wajena yake”


“mi yarinyar can take har yanzu bata bar gidan nan ba?”
tsaki taja “hmmm ka bari kawai u know ur brother yanda yake da matarshi komai tayi dai dai ne a wajansa, duk wata hanya na bi dan ganin ta bar gidan nan har mama Ameenah na sanar mawa tace za tayi mashi magana amma shiru, dama nayi mashi maganar sai shata man layi yayi akan yarinyar, wani mugun sonta yake ga yarinyar da ɗan banza kilibibi, duk wata hanya data san zata bi danta samu shiga a wurinshi sai da tayi”


“alright, amma dole yarinyar nan ta bar gidan nan kema kin san da haka?”
“i know, in sha Allah zanyi iya bakin ƙoƙari na ganin tabar gidan nan” jawota yayi zuwa jikinshi, cikin wata irin shu'umar murya yace
“alright, yaushe zaki bar ya Tahir ki dawo gare ni, na gaji da wannan raba dai dan da nake dashi” ya faɗa yana wani lumshe ido


“ko a yanzu a shirye nake, umarninka kawai nake jira” sake matso da ita yayi jikinshi, hannunshi ya zura bayanta, zip ɗin rigarta ya shiga zugewa, a hankali ya furta “har yanzu burinmu bai cika ba mabaruka”

“don't worry about that, nan da wani lokacin komai zai zo ƙarshe”
“are u sure?”
“am sure, Fa'iz da Fa'iza ne kawai nake ganin za suyi man cikas”


“karki damu da wannan sun riga da sun girma, kuma ko baki nan Zulaihart zata kula da su kamar yaranta, kuma da sunyi Aure ai shikenan”
“haka ne, amma maimunatu fa kasanfa bana son zama dakai tare da kowa?”


“maimunatu is not ur problem ni na san yanda zanyi da ita” ya faɗa yana wani kashe mata ido ɗaya, murmushi ta saki itama tana maida mashi martani.


saurin manne bakinshi yayi da nata, a zafafe ya shiga kissing ɗinta ba ƙaƙautawa,sun jima a haka har ƙafafunsu suka fara gajiya, ganin tsayuwar baza tayi masu bane yasa shi sakin bakinta,ida unzipping rigartar daya

Please Login or Register in order to submit comment