Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 8
komai, ina mai neman gafarar tarin laifin da na yi miki. Da ace ki na cikin hankalin ki a lokacin da na ke tare da ke a asibiti. Da kin tabbatar da cewa na tuba, na kuma fad'a cikin kaunar ki, son ki ya kama ni, a lokacin da zaman mu tare ya zo k'arshe. SAKI DAYA na yi miki ya ke ma'abociyar hakuri. Amma ki sani, a duk bagun numfashin da zuciya ta za ta yi a duniya, tare da bikon soyayyarki. Da ace zan sake samun wata dama ta auran ki, na yi rantsuwa da wanda ya halicce ni, zan nuna miki za6i na gari Abba yayi miki. A karshe ina addu'ar Allah ya raya mana Ameer, rayuwa mai kyau cikin addinin musulunci. Mai son kiNaseer Iliyas Balarabe! Bata gaskanta idon ta ba, balle ta yarda da abinda ta gani a rubuce. Ta sake maimaitawa. Ta tsaya kasake tana sauke Numfashi. Me ke cikin ranta wanda bata tantance shi ba? Kamar farin ciki ne ya kamata, to me yasa hawaye ke neman kubcewa? ----------------------------------------------------------------------------------------------- Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Gaba daya ta kidime. Ta sake duba takardar bisa sunan mai ita Naseer Iliyas Balarabe! Ta cicci6o Ameer ta rungume shi tana fadin,"Tare za mu koma gidan Babanka! Allah na yafe masa! Da kyar ta sami barcin kirki. Da safe ta tafi gaida Alhjn, tun daga fuskarta ya shaida tana cikin walwala, ba kamar dawowar ta jiya ba. Bayan sun gaisa, ya ce,"Kin ga sak'on? Ta amsa da kai, tana d'an murmushi. Ya dan dago habarta, ya ce,"To yaya? Ya fito bazawarin? Ta fado jikin sa ta kudundune fuska,"Kai Abba! Ya fasje da dariya,"Shi ke nan, na bari, to tashi ki ji." Ta mike ya ce,"Na san anjima zai zo, sai da ba shi da labarin komai, illa Ameer da zai dauka. Za'a ci kwalliya ko? Ta tashi da gudu, ta bar dakin. Ya kama dariya yana kwanciya bisa kujera,"Bebin Abba kenan 'yar albarka.," Karfe 9 da rabi Naseer ya iso gidan su, don gaida iyayen sa kamar yadda ya saba duk ranar asabar da lahadi. Yana shigowa. Malam Balarabe ya hau fada,"Kai menene dalilin kulle wayoyin ka. Alh.Basheer na ta neman ka tun jiya, bai same ka ba? Ya ce,"Uhm.............Ba su da caji ne. Ya ce,"Amma kai k'aryar ka ko hanyar masallaci bata sani ba Idan babu Nepa, ba akwai jenareto ba? Yayi shiru." Watau abin zai dawo ko? Da sauri ya ce,"A'a Abba! Ya ce,"To mike maza! Yana neman ka." Ya mike yana fadin,"Sai na dawo. "Umma ce kadai ta amsa mashi. Ya wuce babu kuzari. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sha daya yana ofis din Alhj ko zama bai yi ba, yace ya ke can gida ya dauke shi, an riga an gama kimtsa kayansa. Tafe yake kawai, amma ko alama baya son ganin Nusaiba, kar kwadayin dawo da ita ya taso masa. A haka ya iso. Yayi ta maza yayi sallama falon. Ummi ke zaune a falon ta yi masa sannu da zuwa, ya tsugunna ya gaishe ta. Ta kira Mariya, ta ce ta kira Nusaiba, ita kuma ta haye sama abin ta. Yayi zuru a zaune kirjinsa na duka. Mariya ta kawo masa tiran kayan motsa baki. Bai ta6a komai ba, wani lafiyayyen kamshi ya doki hancinsa. Ya ware ido saitin kofa. Zuwa can Nusaiba ta ratso rike da hannun. Ameer. Ya zura masa ido, ashe ma kadan ya gani, kyan Ameer a hoto. Jikin sa ya dauki rawa. Nusaiba ta daki zuciyar sa sosai. Bai daina kallon su ba har suka iso tsakar falon, tayi masa sannu da zuwa. Baki sake ya amsa. Ta zauna ta dubi Ameer ta ce,"Ga Abba." Ya kura mata ido ya ce,"Abba? Ta yi dan murmushi,"Babanka ne, je ka." Ta tura shi ya nufo Naseer. Mikewa yayi ya tarbe shi, ya rungume, "Oyoyo Abba na! Ya jima da shi a kirjin sa, kafin suka zauna, ya dora shi bisa cinyoyinsa, suka bi juna da kallo. Ya ce,"Ka sanni? Ya girgiza kai. Ya ce,"Baba ne. Ka ce Baba inji? Ya ce,"Baba." Ya sumbace shi a dukkan kuncin sa. Sannan ya dubi Nusaiba, suka hada ido, yayi dan murmushi, ya ce,"Kun dawo lafiya? Ta ce,"Lafiya lau, ya su Antina da su Umma? Ya ce,"Lafiyar su lau, sun ce a gaishe ki." Ta ce,"Ina amsawa." Suka yi shiru na dan lokaci, kafin suka sake kallon juna. Kowa yayi murmushi, ya dauke ido. Naseer ya kama yatsun Ameer ya hau kadawa, ya rasa abinda zai ce. Ameer ne ya katse shirun,"Baba, wai tare za mu tafi? Ya tallafo kuncin sa ya ce,"A'a za ka zauna tare da Mama tukuna ko? Ka na so? Ya kada kai,"Ni zan bi ka." Ya kwanto jikin sa ya lafe. Ya k'ara rungume shi, ya dubi Nuasaiba, murmushi kawai take yi kafin ta ce,"Yaro ya san gaskiya." Ya ce,"Wace gaskiya? Ai kyan sa ya zauna tare da ke in rink'a zuwa ina ganin sa." Ta ce,"A gidan wani? Ya 6ata fuska ya ce,"Anan gidan na ke nufi, idan son samu ne, mu kasance yana ganin mu tare kowane lokaci, shi zai taimaka ya san mu ne iyayen sa. Ta dan kada kai,"To ai kuma ba zama na zo yi ba gidan. Matsalar kenan." Ya sauke numfashi yayi shiru, ba don shi da abin fadi ba. Ta ci gaba da cewa,"Yanzu za ku tafi a fito da kayayyakin?? Ya dan kalle ta, kin kosa ne mu tafi? Ban ce ba, ayi hakuri." Haka hirar ta ci gaba su kamo nan, su kamo can, alamun babu natsuwa a tattare da Naseer. Sun sami awa 2 tare. Ya kwaso kayan Ameer ya taho da shi, hankalin sa tashe. A Zariya kowa na murnar ganin Ameer, shi ta shi ragaggiya ce, sbd zullumin sun kusa rabuwa da Nusaiba kwata-kwata sai wata k'addara za ta hado su Shi yasa kodayaushe yana Kaduna tare da Ameer wai yana kawo mata shi ne ta gan shi. Dariya take yi, ta ce ta gode." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sati 2 suka wuce Naseer na lilo tsakanin Kaduna da Zariya. A yau da la'asar ya isa bayan barin sa makaranta ya sa Ameer a mota suka zo. Suna tare da Nusaiba a waje suna shan iska. Alh.Basheer ya dawo, Naseer ya nufe shi suka gaisa daga nan Alhjn ya ce,"Yauwa tunda ga ka, shi kenan sai ka kai wa Malam Balarabe katin daurin auran Kanwar ta ka, wani satin." Naseer ya dask'are nan, har Alhj ya dauko jakar sa a mota ya buda, ya debo katuna." Ungo guda 10 ka ba shi. Haka kuma ga na ka nan, in za ka ba Friend din ka ne, in ba ka Twenty? Kamar ya ce,"A'a." Sai wata zuciya ta hana shi, ya ce,"Toh Alhj." Ya mika masa guda 30. Yasa hannu ya kar6a. Bayan sun yi sallama da Alhj, ya wuce ciki gida, ran sa 6ace, ya koma gun Nusaiba,"Me za ki 6oye min? Ashe Next week ne auran ki shine ko ki gaya min? Ni na isa in hana ne? Baki sake ta ce,"Shirin gaya maka na ke yi, sai Abba ya dawo ka tashi. Ayi hakuri. Ya suri Ameer,"Mu mun tafi. Allah ya bada zaman lafiya." Ya wuce ya bar ta zaune tana masa dariya. Yana zuwa, ya watsa katuna bayan mota, suka tafi. Iya wuya yake yau. Duk wanda ya ta6a shi, zai ji masifa, gida ya wuce da katunan bai kai wa Abba na shi ba. Yana zaune. Zarah da Ameer kadai ke hidimarsu cikin gidan Baya ko fahimce shi ba, suna kici ita da dan lelwn ta, suna girki. Yayi nisa a tunanin sa, kamar ya hadiye zuciya, don haushi. Me zai ci da katuna, banda ya banka wa 'yan iska wuta? Ya zabura a fusace ya fado kicin, babu magana ya hau bincike, ya 6aro mata da kayan cikin dirowar sama. Tayi tsaue tana fadi,"Yayana me ka ke nema? Ashana." Ta ga ya dauka, yai waje. Ta jefar da ludayi, ta biyo shi,"Yayana me za ka yi da ashana? Ya buda mota ya kwaso katuna, ya aje k'asa. Kafin ya kyasta ashanar ta kwashe su. Ya kama da karfin yana fadi,"Ki saki na ce ko? Ta dade bata yi auran ba, idan har sai mun je masu daurin aure! Ya fizzge iya rabon sa, ya watsar kasa, ya kyasta ashana. Ya cinna, yayin da Zarah ta buda ambulan, don ganin takardun da yake rawar jikin konawa? Kati ta gani ta zaro shi ta karanta. Dada masa duka ta yi a tsakar baya, yana duke yana cinna wuta, ta fadi da karfi,"Kai yaya na da kai ne! Duba ka gani,"Naseer Iliyas Balarabe aka sa! Ya mike ya fige katin a hannun ta, ya karanta. Gaba daya jikinsa yayi la'asar, ya zura mata ido, sannan ya dafe goshi, duk kunya ta kama shi. Ta ce,"Komai ba ka bincike, sai ka yanke hukunci." Ya rungumo ta, hayaki yayi sama, ta ce,"Ga dai sauran nan na cin wuta." Ya sake ta ya hau tsalle yana kashewa, tana masa dariya, duk da haka wasu sun k'one, wasu kuma sun yi dameji. Ya kwaso yana nuna mata,"Ni yanzu yaya zan yi? Katunan nan har da Abba? Ta yamutsa fuska, ta dubi Ameer dake tsaye gefenta, ta ce,"Mu ina ruwanmu ko sweetyna? Ya amsa da kai, yana dariya. Ta mik'a masa hannu,"Come on give me five! Ya bata hannu, suka kashe. Ta sure shi, ta ce,"Zo mu tafi abin mu, kar abincin mu ya kone. Baban ka ya zare! Ya kawo mata wawura, ta kwasa da gudu. T-shirt da wandon dake jikin ta ya bata damar gudu sosai. Ameer dariya yake yana murna. Kicin ya iske su suna ta yi masa dariya."Don Allah ki aje girkin nan, ki zo ki raka ni." Ta kama k'ugu, ta tambayi Ameer,,"Mu muka ce ya konawa Abba kati? Ya girgiza kai,"A'a, ta dube shi ta nuna shi da ludayi,"Ka ji ko? Saboda haka ba ruwan mu." Ya matso ya manne da jikinta,"Don Allah ki daina wasa, ki zo mu tafi."Ta k'are masa kallo kafin ta ce,"Jira ni ina zuwa." Ya sumbace ta, saboda Ameer yayi waje. Ta sauke numfashi, ta ce,"Allah na gode maka amarya za ta dawo." Ta sauke girki ta kashe (Cooker), ko dama sitiyu ce, ta rage mata. Daki ta je ta dora (After dress) akan kayan jikin ta, ta yafo mayanin ta fito, ta kulle gida. Ta same su a mota. Suka tafi Ameer na bisa cinyoyin ta. Shi kuwa waya ya dauko ya kira Sageer a Bauchi."Banza, ka na can za'a sha shagali! Shagalin me? Amaryar Zarah za ta dawo." Ah haba don Allah? Komai yayi dai-dai kenan." Ya ce,"Walllahi ni ban ma san Abban na ta ya hakura ba, kati kawai ya ba ni dazu." Cikin murna ya ce,"Congrats. Insha Allahu zan zo a daura da ni, wannan dole ne. Yaushe ne? Next week,"Ai kuwa zan zo da yardar Allah." Suka yi sallama ya aje waya. Ya dubi Zarah,"Ya ce, yana gaishe ki." Ina ansawa. Amma ba ka gaya masa ka zare ba, har ka kona katunan." Ya dunkule hannu ya dora bisa kuncinta. Allah zan kwashe miki hakora, ki kiyaye ni! ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Ya kuwa kama, ya danna masa cizo, ya janye da sauri yana dariya. Su ma suna yi masa. Ya shafa kan Ameer ya ce,"Ta koya ma mugunta ko? Ya lafe a kirjin ta, suka kwakume juna. Naseer ya sha mamaki da suka kai wa su Abba ragowar katin da suka rage masu kyau guda 15. Malam Balarabe ya ce idan ya na son k'ari ya zo ya ba shi. Kunshi 1 ya fito da su, wani samfu daban kuma bugun Malam Balarabe. Abin ya daure wa Nasrr kai, ya ce,"Ni fa ban gane ba? Umma ta ce,"Ai ba za ka gane ba, domin Abbanka da Alhj sun barka cikin duhu. Amma tun ranar da ka zo da Ameer gidan nan. Alhjn ya gaya wa Malam cewaR Nusaiba za ta dawo." Ya shagwa6e fuska,"Saboda Allah ya za'a min haka? Da na mutu fa kafin lokacin saboda damuwa? Zarah ta ce,"Sai a rufe ka mu ci sadaka. Ya harare ta. Umma na fadin, gaya masa dai Zarah. Take nan ta ba su labarin abinda yayi dazu. Me za su yi ba dariya ba. Koda ya je Kaduna dariya suka rinka yi masa, musamman Nusaiba. Shirye- shirye ya kankama. Da yawa mutane ba sun san Nusaiba bata gidan Naseer ba, sai da suka sake ganin kati, musamman jama'ar Alhj. Ranar juma'a da daddare Sageer ya iso, don haka da shi aka daura aure. Washe gari karfe 1 da rabi na rana. Antin Jordan ta dubi Naseer ta ce,"Lalai kai mai sa'a ne, ka yi wa Allah godiya, domin yayi maka baiwa." Ya sunkuyar da kai,"Na gode Anti." Ya wuce ta bi shi da kallo. Ibrahim ya fado mata, tausayin sa ya kamata. Ranar daya zo Injinya na masa bayanin hukuncin da Alhj ya yanke har ya bar wajen, fadi yake,"Ai dama na san Abba baya so na. Wannan karon ma har da Nusaiba, tunda ta iya barin k'asar nan, ba tare da sani na ba." Ta girgiza kai, ta ce a ranta,"Matar mutum kabarin sa." A ranar Nusaiba ta tare su Kausar suka rako ta. Suna shigowa Zarah ta kar6e ta, suka rungume juna, ta kamo ta zuwa sashinta. Kausar na ta fama da tsohin cikin ta, ta ya6e bakin gado. Naseer ya shigo, bayan sun gama cin abincin, suna shirin komawa. Ya ce,"To ga motar can sun shawo man sun dawo." Kausar ta ce,"Na ga ka na rawar jiki ne Jah-Jah, sai wani korarmu ka ke, ni fa ina nan an sai jibi zan koma." Ya ce,"Ga Jah-Jah nan a gaban ki, kin yi wani turus, in za ki kai jibin? Aka kwashe da dariya. Ta ce,"Anan gidan kuwa." Ya ce,"Ina, taso maza in lalla6a ki in sa a mota, kar ki caza min aiki. Ina angwancina, ace in taso asibiti zan kai ki." Ta ce,"Gaskiya ne, ba laifin ka ba ne, tana ji ta yi shiru, shi yasa ka ke kara fadi. Ta na shiru. Antin Jordan ta shigo. "Kausar cicci6o mana, sai da nace ki yi zaman ki gida, ki ka ki." Simi-simi Naseer ya fice. Kausar ta ce,"Ya ka tsere? Dawo mana mu ci gaba. Ka na Angwanci ko? Ya waigo a bakin kofa, ya amsa da kai, ya wuce yana dariya. Duk an watse. Kowa ya koma muhalinsa. Ba ango kadai ba, hatta Ameer yana murnar ganin Maman sa a cikin gidan, yayi ta tsalle-tsallensa ya bi can, ya bi nan. Amma yana cin abinci. Zarah ta yi masa wanka, gadon ta ya haye yayi barcin, bai nemi Maman sa ba. Tana zaune misalin 9, nazarin litattafanta take yi. Naseer ya shigo. Ta dube shi tana. Murmushi,"Ango kenan. Kamshin nan yayi Wallahi." Ya tsugunna ya dada mata duka a baya,"Ba kya ji ko? Ta ce,"Na kai ka rashin ji? Ya ciji kunnanta, ta shafi wajen, ta ce,"Amarya na jiran ka, tashi mu je in raka ka." Ta aje littafi ta kamo hannun sa, ya mike ya rungumo kafadar ta, suka fito zuwa sashin amrya. Ta turo kafar tare da sallama ta shiga. Amarya ta sha ado, sai wanda ya gani. Zarah ta ce,"Kai amarya, ai sai yayan mu ya mance sunansa." Ta sunkuyar da kai,"Antina kin dame ni tun dazu." Ta ce,"To babu ruwana, ga shi nan na kawo shi amana, gobe in an ga ya susuce, ke ce." Ta kama baki tana 'yar dariya. Ya kamo kunnanta,"Shi yasa nace ba kya jin, zo ki wuce." Yana rike da kunnan ya kai ta kofa, suna dariya. Ta tsaya ta ce,"Amarya ya kore ni, sai da safe kenan."Ita dai ta kasa magana, sai dariya. Zarah ta ja kofa." ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Ya tsaya ya k'are mata kallo, sannan ya sauke numfashi. Ya tako a hankali ya tsugunna gabanta, suka dubi juna, ta dan kauda kai, tana murmushi. A natse ya kwantar da kan sa bisa kafafuwanta, ya nisa yayi dan shiru. Haka ita ma take kallon sa idanuwanta suka kawo kwalla. Bata san lkcn da ta dora kan ta bisa bayan sa ba. Sun jima shiru haka kafin ya ce,"Na gode Allah, na sake gode masa daya nuna min wannan rana. Haka kuma na gode wa Abba daya sake mallaka min ke. Na yi kuskure gare ki Nusaiba wanda baya misaltuwa, ba na kuma son tuna su. Ki yafe min Nusaiba. Ta ce,"Tuntuni na yafe maka yayanmu. Ya wuce." Ya dago ya ce,"Na gode." Kin san wani abu? Ta kada kai. Ya lalibo aljihunsa ya dauko kudi, ya kamo hannun ta ya dora mata, ta ce "Na menene? Kudin ki ne, canjin ki dubu 15 da ki ka ba ni a asibiti. Ta saki baki tana kallon sa,"Kai yayanmu, shekara 2 da rabi? Ya sake kwantar da kan sa, ya ce,"Ba zan ta6a mancewa da su ba Nusaiba, domin daga ranar da ki ka miko min su. Allah ya manna min son ki a raina. A lkcn ba wai ba ni da su ba ne, amma ba su da amfani, tunda ban san yadda zan yi in ciro su ba. Alhalin ina matukar bukatar su. Da gaggawa. Kin min abinda ba zan ta6a mancewa da ke ba rayuwa, kin taimake ni a lkcn da na wulak'anta ki na.......... Ta rufe bakin sa."Na ce ya wuce yayan mu, ka daina tunawa." Ya dube ta ido cike da kwalla,"Kar ki yi kokwanto Nusaba, Ina son ki! Ina son ki!! Ina son ki Nusaiba!!! Ta ce ,"Na sani." To kice kina so na in ji, ko sau 1 ne." Ta yi dan murmushi ta ce, "Ina son ka yayan mu. Ga kuma kudin ka har canji na bar ma ka." Yahayo shimfidar sosai, ya ce,"Kin saye baki na ke nan? Ta yi 'yar dariya,"Na siya." To me ki ke sha'awar sha? Ta ce,"Uhm.......Cock, irin mai dan inabin nan. Ka gane ai? Ya tsura mata ido, tana masa dariya. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Zaman lafiya mai ban sha'awa ga kowa ya dore a gidan Naseer. Hankalinsa kwance, ba shi da matsala. Ya k'are Digirinsa. Shine gwarzon shekara, wanda ya fito da ajin farko a fanni da yake karanta, sannan ajin farko cikin jerin wadanda suka zo na farko a sauran kwasa- kwasai a wannan shekara. Don haka yana daya daga cikin masu rubuta jarabawar tantance masu tafiya Turai don karo ilimi tare da tallafin gwamnati. Kowa yayi masa murna. Shi kan sa ganin abin yake kamar a mafarki. Allah yayi gaskiya ya ce tashi in taimake ka. Tabbas hake ne, Naseer ya ga Zahiri. A Kaduna suka rubuta jarabawa 'yan makwanni tsakani sakamo ya fito. Naseer ya haye ya ci Nasarar tafita Ingila. Shirye-shirye ya kankama a lokacin cikin Nusaiba ya fara tsufa, domin kuwa ya shiga wata na 7. Ranar da zai tafi daren kasa barci yayi, saboda tunanin shekara 1 ba zai ga iyalansa ba, wad'anda ya riga ya aje su cikin ransa, baya son kasancewa da kowa sai su. A duk inda yake. Allah.Allah yake ya yi yadawo gida, saboda tsabar son da yake musu. Amma babu yadda zai yi, yana son ci gaba kuma a yanzu ya tauna dadin karatu ya dandana ya gane fa'idar sa. Kan dole ya dake zuciyar sa. Washe gari karfe 8 na dare jirgi ya cilla da su birnin Sarauniya. Sun kama karatu gadan-gadan, amma kodayaushe cikin waya suke da iyalansa. A haka watan haihuwar Nusaiba ya tsaya. Umma ta sa ido sosai a kan ta, babu ranar da bata zuwa Hanwa. Allah da ikonsa da safe ta fara nakuda, ga shi Zarah na da jarabawa kuma ta karshe ce, don kammala NCE din ta. Duk da haka ta hada kayan haihuwa ta wuce da Nusaiba asibiti. Sai da ta tabbtar an shiga da ita dakin haihuwa kafin ta kira Umma ta gaya mata asibitin da suke. Nan take Umma ta watsar da abinda take, ta biyo hanya. Tana isowa 8 dai-dai, sannan Zarah ta bar mata Ameer, ta wuce jarabawa, ta iske an shiga, sai da ta sha surutu, ta samu aka ba ta fefar. Da namiji Nusaiba ta sake Haifa, lafiya lau daga ita har Bebin. Umma da Ameer na murna. Nan da nan ta kira wayar Ummi, ta shaida mata ta sake sabon ango.... ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajinisa Yake3-06 Posted by ANaM Dorayi on 12:04 PM, 25-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ Suka yi farin ciki. Ta lallatsa ta nemo lambar Naseer. Suna gaisuwa, kudinta suka kare. Tir! Haushi ya kama ta, sai ga shi ya kira,"Menene Umma? Ta ce,"Ka yi Da. Nusaiba ta haihu yanzu." Farin ciki kamar yayi tsuntsu ya baro Ingila." Ina take Umma? Ta ce,"Ai tana ciki ba su riga sun fito da su ba, amma sun ce lafiya kalau suke ita da Bebin." Alhamdu-lillah! Allah ya amfana mana." Ta ce,"Amin. Haka ya kasance cikin doki, kamar yadda Zarah ke makaranta cikin zakuwa da son ta koma wajen Nusaiba. Kafin yamma gidan su ya cika da baki 'yan barka, angon karni kuwa ya ki barin mai jego sakat da waya, shi so yake ji kukan Bebi, "Bebi kuma ya ki yin kukan. Barcin sa kawai yake kwasa. Ranar suna, yaro ya ci sunan Alhj. Haka kuwa suke kiran sa(Alhaji) Ya ci gaba da girma tamkar Ameer, shi yasa idan Naseer ya rufe ido, baya ganin kowa illah 'ya'yan sa, tamakar 'yan 2. Watanni 3 bayan haihuwar ta. Alh.Basheer zai tafi harkokinsa Turai, ya wuce wa Naseer da hotunan dan sa, ya gan shi. Hankalinsa ya kwanta. Ya cire na Ameer daga firem ya zira wanda suke su 2. An ci gaba, renan Naseer Jah-Jah. Shi kansa yana mamakin kansa. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Kwanci tashi, shekara ta zagayo. Naseer ya dawo cikin iyalansa, kamar yadda yake so. Bayan ya huta sati 1. Alhj ya kira shi suka tafi bargar dawakansa. Abin ya ba shi mamaki, irin dawakan da ya gani suna harbin iska. Sake da baki ya dubi Alhj yace "Abba za'a fara wasa ne? Ya dafa shi ya ce,"Haka na ke zato, idan na sami amincewar Jah-Jah." Bakin sa har kunne ya ce,"Abba in dora sirdi in hau? Yayi murmushi ,"Why not." Ya kira mai kula da wajen, ya ce,"Je kawo sirdi." Nan da nan ya dora Naseer ya haye jikin sa na rawa ya zagaye bargar dawakan. Kamar kar ya sauka, dokin yayi masa dadi." Abba yaushe za'a fara? Ya ce,"Yau da yamma za'a fara a tisaye, sannan akwai club guda 3 da na ba takardar gayyata wasan sada zumunci. DABAI ta dawo sabuwa." Ya ce,"Insha- Allah kuma gagara gasar masu gasa." Ya kamo shi suka nufo mota yana fadin,"Akwai wani kokari da na ke maka, amma ba zan gaya maka ko menene ba, sai Allah ya tabbatar da abin, za ka ji. Ka ci gaba da addu'a. Allah za6a mafi alkhairi." Ya dan rankwafa ya ce,"To Abba, na gode. Allah ya saka da alkhairi." Wasa ya kankama. (DABAI RIDERS) ta dawo duniyar tseran Polo. Tutar Naseer Jah-Jah ta yi sama ta neman ta wuce yadda take da can baya. Watannin 9 yana ketawa cikin kungiyoyin Polo, yana ba su mamaki. Kwatsam! Abinda Alhj ke masa kokari ya samu. Ba wani abuba ne, illa samun shiga shaharrariyar kungiyar wasan Polo ta kasar Potugal. Naseer fa kamar yayi hauka, don murna. Haka Malam Balarabe, bai san abinda zai ce da Alh.Basheer ba. Kamar yadda aka bukace shi, daya iso 15 ga wata, haka yayi sallama da kowa suka tafi tare da Alhjn. Sun gwada shi, sun ga iya kwarewar sa a zahiri ko dama Alhj ya sha kai masu SD filet din wasaninsa na gida da waje. Kwarai sun gamsu da wasan Naseer, kuma da alamun za'a samu da shi. Can Alhj ya baro shi yana fafatawa cikin turawa. A lokacin ne ya k'ara tabbatar cewa komai in ka na da ilimi ya fi tafiya dai-dai, musamman a wannan zamani. An bashi gida da motar hawa. Naseer ya kasance ba shi da wata matsala sai ta kewar iyalan sa. Ita ma sun kusa magance ta. Cikin watanni 2 takardun zamansa dindin a Potugal suka kamala, ya sami izinin shigowa da iyalansa. Babu son kai. Zarah ce ta fara zuwa a matsayin ta, ta babba. Ameer yayi kukan son biyo ta, amma ina makaranta, ta hana. Wai! Wa ya gane min Zarah a Potugal? Ta shakata kwarai tsawon wata 1, ta koma Nusaiba ta damk'o hanya. Haka suka kasance suna yi wata guda-guda babu matsala balle tashin hankali. Kowacce ta zo Naseer yana jin dadin kasancewar tare da ita, bisa adalci da tsoron Allah. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Shekara 5 Naseer yayi karfi sosai a k'asar Potugal a fagen tseren Polo. Yayi farin jini kwarai da gaske, kowa na son shi. Sau da yawa wasu kungiyoyin na kawo masa cafka ta hanyar ninka masa abinda yake samu, amma ya kauda kai, saboda Alh.Basheer. Domin a halin yanzu arziki sai dai ya ba wani, bai ma san iya wadanda suke cin gajiyar sa ba a gida Najeriya. Duk shekara idan ya je hutu. Bayan dawowa ba tare daya buda wata cibiyar siye da siyarwa ya zuba matasa sun samun abinci ba. Hatta Naseer B dan hassada, ya saduda ya nemi gafara, ya dawo yana cin arzikin da Allah yayi wa Naseer. Yayi farin jini ba na wasa ba a Potugal, domin har tallace-tallace yake wa manyan kamafoni ta hanyar sana'arsa. Ba kananan dololi yake kamawa ba, kowacce talla yayi. A 'yan shekarun nan biyar. Nusaiba ta hada 'ya'yanta 4 a gidan Naseer, 2 maza, 2 mata. Hakika hankalin Naseer a kwance yake, kuma Alhj ya lura karfi sosai a club din sa, tseren dawaki sai dai ya ba 'yan baya tirenin. Saboda haka yayi iya yin sa wajen Injiniya Ahmad Kaita ta hannun sa ya samar masa a aikin yi ta 6angaran karatun da yayi, don kar ya tafi a banza. Allah mai ko! Takarda kawai aka ba Naseer ya je inta-biyu ofishin(Internet Globl Services) reshen Potugal, take nan suka yarda da takardunsa. Ya sami shiga aiki. Duk da haka bai bar Polo ba, amma ya zama na manya, wanda ake son tafiya da shi, musamman a gagarumin wasan duniya. A farkon wannan watan Zarah ce ke da zuwa Potugal, a filin jirgi ya je ya dauko ta. Suka shiga harkokin su kamar yadda

Chapter 7 of 8