Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
amma muna tare, ki kasa gaya min? Ba ki min adalci ba Nusaiba, domin da kin gaya min da tuni na yanke hukunci, sai dai ya nemi wani uban, ba ni ba! Kowa yayi tsuru-tsuru. Nusaiba kuwa tuni ta fara kuka. Ya matsa gadabn Ummi ya tsugunna." Hajiya ki yi wa girman Allah, ki yi hakuri. D'a ne ka haife shi ba ka haifi halin sa ba. Ko alama ban san halin da suke ciki da matar sa ba. Ga mahaifiyar sa nan a zaune, ko ita da ke zama tare da su munafikin Yaron nan bai ta6a barin ta gane wani abu ba, balle ni da ban zama cikin gida. Maganar tafiya da Nusaiba kuwa kun yi dai-dai, domin ko ni ne hakan zan yi. Saboda haka kowa yayi shaida. Ni Balarabe na tsame hannu na akan komai daya shafi Naseer, duk abinda ya ga dama yayi rayuwa ce................ Ya fashe da kuka, jikin kowa yayi sanyi, matan da ke wajen ma tuni suka soma taya shi, musamman Umma da ta ji abin kamar saukar aradu. Sageer ma waje yayi kirjin sa na bugawa, ga ranar da yake jin tsoron zuwanta, kullum yana gaya wa Naseer. Amma kunnuwansa iskar duniya ta dode masa su. M.Umar da Alhj suka riko M.Balarabe,"Ka yi shiru haka,"Malam Balarabe, kar zuciya ya kwashe ka, ka yi masa baki." Ya dube su ya ce,"Ni Naseer yayi wa tijara haka, Babu komai, rayuwa ce!Ya dubi Umma ya ce gaba,"Ke dauko masa D'ansa mu tafi, ki kai masa kayansa, idan ya ga dama ya jefa shi bola! Malam Umar ya ce,"A' ba'a yi haka bane, duk ku zauna a sasanta magana. Ai in rai ya 6aci, hankali ke nemo shi. Alhj ka yi hakuri, mu zauna da Naseer mu ji ta bakin sa, don girman Allah kar ku yanke hukunci kai tsaye haka." Alhj ya kada kai,"Ban k'i taka ba. Amma Naseer ya riga ya k'are magana, sai dai hukuncin daya yanke ne ban yarda da shi ba, d'a kan ba na mu bane, na shi ne. Don haka anan za'a bar shi. Iya magana kenan." Malam Balarabe ya ce,"Magana tayi dai- dai Alhj, ku bar masa shi, ya san uwar da za ta shayar masa D'an shi. Ki dauko shi mu tafi, na gaya miki, idan kuma ki na nan, ni na wuce! Yayi waje. Malam Umar ya bi shi. Umma ta dubi Ummi, ta ce,"Don girman Allah Hajiya kar ku yi wa Yaron nan haka, shi bai san komai ba, ku tausaya masa." Tayi shiru, ta rasa me za ta ce? Yadda Alhj ya fusato, babu mai sa shi dukan D'an nan. Haka Zarah ta rike Nusaiba,"Amarya kar ki ta fi, don Allah ki taimake ni. Idan ki ka tafi da wa zan zauna? Suka k'ara fashewa da kuka. Ita dai Fa'iza ba baki, sai ido. Bata fahimce komai ba, take ta faman kuka. Alhj ya fice ya bar su nan, suna ta faman magiya. Jim kadan ya dawo tare da Likita. Shi dai ya ga ana ta koke- koke, a zaton sa duk na murna ne, yayi abbuwan da zai yi, ya gama ya ba su sallama tare da takardar magunguna da za ta ci gaba da sha na tsawon kwana 7.Alhj da kansa ya rink'a dibar kaya yana kaiwa cikin mota, har ya kwashe su duka. Ya kamo hannun Nusaiba, ya wuce da ita. Ummi ta biyo bayan su, suka bar Umma da jariri bisa gado, yana ta faman barci. Ta k'ara fasa kuka. Inna ta kamota tana rarrashi. Haka Zarah ke durk'ushe, hannu 2 bisa kai.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Daga inda Naseer ke 6oye, yana hango su Alhj suka zo suka wuce a moTa. Yasa hannu ya goge hawayen da ke kuncinsa. Jimawa kadan ya hangi su Umma. Inna na dauke da Ameer, suka shiga motar da ta kawo su. Direba ya ja suka bar asibitin. Wasu hawayen suka sake zubo masa, yayi kamar ya hadiyi zuciya ya mutu. Ya nufi inda ya aje motar sa, ya shiga haka ya dawo gida, baya gani wuri sosai. Ya rasa inda zai je, sai yayi fakin kofar shago, ya shiga ya sallami su Abbas ya ce duk su tafi gida. Ya kulle kansa ciki, ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Cikin gidansu kuwa kamar anyi mutuwa, shiru ba ka jin motsin kowa. Jim kadan Zarah ta fito da jakar kayan ta, ta lallabo zuwa sasan su Umma. Ta leko a hankali, ta ga babu kowa, ta cire takalmanta ta wuce sadaf-sadaf kamar 6arauniya. Tayi waje kan ta tsaye tayi gidan su. Inna ta zura mata ido, kafin ta ce,"Ke kuma fa? Ta shige uwar daki da gudu. Inna ta biyota,"Na ce ke kuma fa? Kin shige da gudu. Menene na ce? Ta ce,"Allah Inna ni ma ba zan zauna ba. Haba ai wulakancin yayi yawa, ko alama yayana baya jin magana. Ta balbaleta da fada,"Laifin waye? Ai duk ku na sane, aka rasa wacce za ta gaya wa manya, don ayi maganin abin, sai yanzu da zance ya lalace, za ki ce Naseer ne baya jin magana? Maza dauko jakar nan, ki koma inda ki ka fito, tun kafin Babanki ya k'araso gidan nan, ya sameki." Ta 6arke da kuka, tana fadin,"Ba inda za ni Inna, idan har na koma gidan nan, to yayana ya dawo da Nusaiba. Kuma ku matsa min ku gani. Wallahi tafiya ta zan yi." Inna tasa mata ido tallafe da baki. "Ki ka ce me? Lallai wuyanki ya isa yanka, to zan ji idan kke ki ka haife mu." Ta yi zamanta bakin gado, har Inna ta gama babatun ta, ta fice." Na rantse da Allah ba zan koma ba, ya je ya ci kan sa a gidan, tunda shi ba'a gaya masa ya ji." Koda Malam Umar ya dawo, babu yadda ya iya yi da ita, ya gama fadansa da barazanarsa ko gezau zuciyar Zarah bata yi ba, kuma ta rantse ta maya, muddin suka bari ta bar nan, ba za su sake ganin ta ba. Shi yasa da ta dauko jaka ta fito. Inna ta dauko muciya ta kora ta daki, ta ce,"Koma daki marasa kunya, idan Naseer din ya zo ya dauke ki! Ta maida jaka ta yi zamanta cikin dacin rai da takaici tare da tausayin Nusaiba da karamin goyonta.
Sageer ma da ke zaune a dakinsa, babu abinda ya fi damun sa irin dan karamin yaron da aka aje. Alhalin bai san komai ba. Fa'iza ta ce,"Yakamata ku taimaka wa yaron nan a maida shi wajen Maman shi,"Wallahi shi ne abin tausayi, ba ka ji yadda na ke ji ba, kamar inyi tsuntsu kai shi wajen ta." Ya ce,"Shirun nan da ki ka ga nayi. Ameer kawai na ke tunani." Yayi hucin zafi, ya dauko waya daga aljihu ya nemo lambar Naseer. Ta dan jima tana bugawa kafin ya dauka, ya ce,"Ka na ina ne? Murya dishe ya amsa,"Shago." "To ina zuwa." Ya kashe waya, ya dubi Fa'iza,"Wai yana shago, bari in je in same shi." Ta ce,"To ba za ka dan ci komai ba? Ya kada kai, bari dai in je in dawo. Ya fice, tana fadin a dawo lafiya. Ya kwankwasa kofar shagon, ya zo ya bude, suka koma ciki tare. Daga kallon Naseer kawai. Sageer ya gane yayi nadama, gaba daya ya jeme ya fita hayya cin sa. Ya dube shi a sanyaye ya ce,"Ka ga irin abubuwan da na ke gaya maka ko? Yanzu ina ribar wannan abu? Kullum ina gaya maka yi wa iyaye biyayya ibada ce, duk kuma mai yin sa ba zai ta6a ganin 6acin rai ba. Amma Naseer na ka ji, ni ban san abinda ke damun ka ba. Dan yaro jariri an ajiye maka shi, ina amfanin sa? Iyayen ka na ta kuka saboda kai, wacce irin masifa ce wannan? Ka farka daga bacci Naseer, kai ba yaro ba ne."Ya dube shi kwalla suka zubo ya ce,"Ban san abinda zan ce ba Sageer, domin ni kaina na san mai laifi ne, saboda haka duk hukuncin da aka yanke min, yayi dai-dai. Sai dai babu wanda ya san cewa na dade da yin nadama, sannan in na ce ba son Nusaiba yanzu, na yiwa raina karya. Shi ya sa na dage ba dare ba rana wajen kula da ita tare da rokon Allah ya bata lafiya, don in samu in nemi gafarar ta, na kuma nuna mata iya so da kaunar da na ke mata yanzu. Allah da ikonsa sai ta sami sauki, hankalinta ya dawo jikin ta, a lokacin da iyayen ta ke wajen, sannan bata 6ata lokaci ba, ta zayyane masu komai. Ka yarda da ni Sageer? Ka taimake ni, domin ni yanzu ban san yadda zan yi ba." Sageer yayi shiru, yana kada kai
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Tabbas ya yarda da maganganun Naseer, saboda yana daya cikin masu mmkin yadda Naseer ya rinka kula tare da ririta Nusaiba, sai dai a lokacin ya dauka saboda halin da ta shiga ne, kuma bata son kowa ya kusance ta, sai shi. Ya nisa kafin ya ce,"Yanzu tinkarar Abban, tashin hankali ne ba karami ba, kuma dole ne aje a same shi, tunda shine jigon komai. Abin yi shine, ka taso mu je wajen sa, ayi ta ta kare ko kashe mu zai yi." Ya kada kai,"Gaskiya Sageer ba zan iya ba.ka je kai kadai tukuna, ni na fi kowa sanin halin Abba." Ya ce,"Shi ke nan. Za ka jira ni a anan din ne? Je ka dawo ina jira. Ungo key din mota don ka yi sauri. Ya kar6a ya fito a sukwane, ya fada mota, yayi gidan su Naseer. Yayi sallama falon Abba, a lokacin Umma tana goya Ameer ta fito ta siyo masa madarar jarirai, bayan ta nemi Zarah ta rasa a cikin gidan, don bar mata ajiyar yaron kafin ta dawo. Shi yasa zuciyan Abba ke kara tafarfasa, ya sani babu makawa ita ma tafiyar ta ta yi. Da kyar ya amsa sallamar Sageer. Ya shigo a darare, ya nemi gefe ya makure, ya ce,"Sannu Abba." Ya ce,"Me aka yi Sageer? Ya ce,"Abba Naseer ne................Ya dakatar da shi da hannun sa kafin ya ce,"Tashi ka tafi! Sannan idan ka je, ka gaya masa ita ma wacce yake son ta tafi abinta, saboda haka ya zo ya kwashe kayan sa, ta bar min gidana in huta." Ya tashi ya durk'usa Abba................Ya runtse idanuwansa,"Sageer ina ganin mutuncinka, don Allah, don son Annabi ka tashi ka tafi. In dai akan maganar abokinka ne, na riga na datse magana, na yi rantsuwa Naseer ba zai sake sani kaffara ba. Saboda haka ka je ka gaya masa, shi 'yantacce ne, kar ya dami kan sa. Tashi, kanzil ban ka kara fadi ba, idan har ni ina isa in gaya maka. Idan kuma ban isa ba, to kacigaba da zama. Sageer ya shiga 3, Abba ya daddaure shi, ga magana bakin sa babu damar fadi, yana ji, yana gani, ya tashi ya fice. Yayi tsaye jikin mota ya rasa tudun dafawa. Ga wata sabuwa, kuma ita ma Zarah ta yi gaba. Duk da dai yana ganin na ta mai sauke ni, amma ba dadi ace ita ma tana gidan su.Ya fi minti 5r a tsaye, sannan ya bude mota zai shiga. Ya hango Umma tafe. Ya tar6e yana mata sannu da Zuwa. Ta amsa za ta wuce cikin gida, ya ce,"Umma ku taimaki ni Naseer na cikin wani hali, komai za iya faruwa da shi. Ta ce,"Shine me? Sai aka ce karshen Umma ya zo? Ya ce,"Ba haka ba ne Umma. Wallahi Naseer yayi nadama, tun ranar da ta sami kan ta cikin wannan yanayin, kuma ba shi da wani buri daya wuce idan ta ji sauki, ya bata hkr akan abinda yayi mata. Sai kuma aka sami akasi, komai ya yamutse. Ta yi dan murmushin takaici ta ce,"Yaro man kaza. To yanzu da ka zo nan ka na ta dogon bayani, akwai Nusaiba a nan ne? Tana fa Kaduna, a gaban Ka Babanta ya dauke ta. Ba sai ya je can ba, ya roke ta. Menene abin zafi? Ya durk'usa bisa guiwa, ya ce,"Ku yi wa girman Allah Umma ku yafe masa, ke ma kin san duk abinda ki ka fadi, ba zai yuwa ba. Sai da goyon bayan ku." Yana sa aya Abba na tsayawa kofar zauran, bai ce wa Umma komai ba, ta wuce cikin gida. Shi ma ya bi bayan ta. Sageer ya sauke numfashi, ya tashi ya fito ya tafi.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Yana shiga shagon zama kawai yayi, ganin haka Naseer din ma yayi shiru, ya san babu nasara. Sun dau minti goma a haka, kafin Sageer ya ce,"Wai Zara ma ta tafi gidan su."Ya dube shi da sauri." Me na yimata ita kuma? Kashe ni suke so su yi ko? Shi kenan." Ya goge kwalla. Wayar sa ta hau bugawa, da kyar ya dauka. Yakubu ne ke kiran sa. Ya rasa ta yadda zai yi ya dauka. Ya dubi Sageer, ya ce,"Zo mu je gidan Yakubu." Ya tashi suka tafi. Ya maida masa bayanin komai. Yakubu yayi masa fada kamar zai ari baki, shi kansa ba karamar kunya ya ji ba lokacin da Alhj ya kira wayarsa, yana gaya masa Naseer ya ci amanarsa. Duk da haka yayi masa alkawarin shiga maganar, sai inda karfin sa ya kare. Shi kuwa Naseer B ana maganar, yana kallon kowa a dage, zuciyar sa gwanin haske, har yana addu'ar kada Allah yasa su shirya. Amma bisa fuskar sa, ya fi kowa nuna damuwa kamar yayi kuka. Daga gidan Yakubu, wajen Zarah suka iso, misalin karfe 1 na rana. Sun shigo gidan. Inna na kwashe abinci cikin kula. Ta daga ido ta dube su, tana amsa sallamar su. Gaban ta ya yanke ya fadi, ganin yadda Naseer yayi wanu duhu lokaci guda. Ta ce,"Dan Inna! An gaishe ka da aiki. Ku shiga gani nan zuwa." Ya wuce simi-simi. Sageer ya bi bayan sa, suna zaune. Inna ta gama abinda take yi a kicin, ta bi su dakin. Zarah ta leko daga bayi ta ga Inna, ta shige sai ta sadado ta aje buta, ta suri hijabin Inna dake shanye bisa igiya ta yi waje ta bar unguwar. "Sannu dan Inna, ka sha aiki Wallahi, ya gajiya? , Ya sunkuyar da kai Sageer ya ce,"Inna kuskure ne, kin kuma san ajizanci irin na Dan-adam. Amma a yau ya gane, har ya tuba........ Ta katse shi, tuban mazuru? Sau nawa Naseer ke cewa ya tuba a gidan na ma kawai, wanda na sani? Ai ba zan iya fadi ba. Yanzu wa gari ya waya? Babu abinda ba mu gaya maka ba D'an Inna, tun kafin ayi auran nan. Bayan anyi kuma, ba mu fasa ba, sai dai in kafar ka bata shigo da kai gidan nan ba, amma ba ka ji. A fuska lafiya lau ka ke, halin ne kawai ka kasa gyara shi, su yi dai-dai da fuskar ka. Me yasa? A yanzu wa ka ke ganin zai iya tunkar Alhj? Babu abinda za mu iya gaya masa, ya yarda, saboda ka riga ka rushe ginin tun ranar zane. Naseer ya ce,"To Inna shi kenan, haka za'a sa ido, auran ya kare kenan? Ta ce, "Eh mana, ta riga ta gayawa Babanta ba ka son ta, wa ka ke zaton zai je ya ce, karya ne? Ya ce,"Gaskiya Inna ban yarda ba, na san ana zuwa biko Inna. Sai dai in ba za ki je min ba ne kawai
Ta yi dan murmushin dole ta ce,"Dan Inna manya, ga laifi, ga saurin tuba. To shi kenan, ka bari Baban na ku ya dawo, za mu san yadda za'a yi." Ya numfasa ya ce,"Wai ita ma Zarah don ta kara min hawan jini shine ta bar gida ko? Ina take, sai ta ci dan banzan duka yau, in ni sa'an ta ne, za ta gaya min." Dariya suke da Inna da Sageer, kafin Inna ta ce,"Yanzu ta shiga bayi, za ta yi alwala ta yi sallah." "Ina nan ina jiran ta ta fito,." Inna ta mike,"Bari in kawo maku abinci Sageer. To Inna. Sageer ya amsa. Ta fice,"Sageer ya ce, "Na ciro maka wayar Rediyon can ne?, Me zan yi da ita? Dukan mana harka mance? Tsaki yayi ya dauke kai. Inna ta shigo da abinci ta ce,"Ka fa ci. Sageer ka matsa ma sa ya ci. Ya ce,"Ai zai ci Inna." Ta yi waje ta koma daki. Shiru- shiru Zarah ta ki fitowa daga bayi. Inna ta fito da wannan mamakin, tana tambayar kanta,"Ita wannan zaman me take yi a bayi?" Tana sa aya, ta aje ido bisa buta a gefe. Ta leko dakin ta ce,"An gama dukan?" To ai ban ji kuka ba, bata daku ba kenan." Suna dariya ya ce,"Ai bata shigo ba Inna.." Ta gintse fara'a ya ce,"Ban gane ba? Ga shi ta aje butar a waje. Ta juya ta fito tana kwala mata kira, yayin da dukkansu suka aje cokula suka fito. Kamar wasa, babu Zarah acikin gidan. Mamaki ya ishi Inna. Ta kama baki, tana kallon igiya babu hijabin da ta shanya. Sageer ya ce,"Wai ita Zarah da gaske take yi? Inna tayi shiru abin ya girmi shekarun ta. Naseer ya numfasa ya ce,"Inna ki gaya mata, idan ta ji ina asibiti kar ta sake ta zo guna. Zo mu je Sageer. Ya yi waje. Sageer ya ce,"Inna ki ce Allah ya bata hakuri. Sai anjima." Da kyar ta iya amsawa,"Allah ya ba mu alkhairi." Shi ma ya wuce. Inna ta ja kujera ta zauna, yau na ga zamani ni A'isha. Kiri- kiri yarinya ta ban kunya? Suna tafe a mota Sageer, ya ce,"Yanzu ina muka nufa? Ya ce,"Gidan za ni, duk ayi ta ta kare, idan ma yankana ni za su yi, su yanka. Ba shi kenan ba? Idan kowa yayi min, ai bai kamata Zarah ta yi min ba. Duk saboda wa na shiga wannan halin? Ba saboda sonta ba ne? Duk ba ta ga hakan ba." Ya furta. Sageer yayi shiru domin ya lura abokin sa ya zare gaba daya, kar ya tofa wani abu, ya kara masa zafi. Ya ci uban birki a kofar gidan, ya fito yayi cikib gida, bai ko saurari Sageer ba. Sai dai yana shigowa ciki ya tsinkayi Ameer na ta tsala kuka. Nan da nan ya yi turus, guiwa sa ta kwa6e, a salu6e yai sallama falon. Umma na kokarin goya Ameer a lkcn Abba kuwa na zaune gefe iya wuya yake. Kuma yana ji da kowa, duk wanda ya kuskura yi masa wata magana akan Naseer. Yana shigowa. Abba ya mike ya debi takalman sa ya bar gidan. Naseer ya bi shi da kallo, ya kasa cewa da shi komai, har Umma ta gama goyon, ta sa hannu ta dauke gwangwanin (Prisso-cream) din da ta siyo ta dora bisa firij, ta dauki fidar ta yi waje. Ita ma ya bi ta da kallo, sannan ya bi bayanta. Tana famfo tana wanke fidar da soso da omo. Ya bi ta, ya tsaya a gefen ta ya sanyaya murya,"Umma!Ji ta yi tamkar ya watsa mata wuta. Ranta ya ci gaba da k'una kamar ta rufe shi da dukan fitar hankali. Ya durk'usa ya mika hannayen sa gaba gare ta. Idanuwansa dauke da kwalla. "Umma, ki yi wa girman Allah ki amsa min. Umma ki dube ni ki saurari rokona. Na yi laifi Umma, amma tuni na gane kuskure na, ku ba ni dama ta karshe Umma. Da yardar Allah ba zan sake saba maku ba, Umma ki taimake ni." Ta gama dauraye fida, ta yarfe ruwan, ta juya ta koma daki tana daddaure su yadda suke. Naseer ya nemi wuri nan ya zanau dirshan! Sageer ya matso zai masa magana, yayi sauri ya riga shi." Je ka gidan abin ka Sageer. Na gode." Ya yi dan jim, yana kallon sa,"Ka ta fi na ce, babu komai, sai mun hadu." Ya numfasa ya ce,"Shi kenan, Allah shi kyauta." Ya juya ya fice, ba tare da Naseer ya sake cewa wani abu ba. Nan yayi ta zama har ya tuno, bai yi sallah ba. Yayi alwala a nan famfon, ya wucce sasan su, yayi Sallah a falo ya ci gaba da zama nan bisa sallaya. Babu abinda zuciyarsa bata saka masa ba. Zarah kuwa bata dowa ba, sai bayan sallar la'asar, ba shakkar komai. Ta yi sallama ta shigi ta wuce Inna a tsakar gida ta shigo daki. Inna ta tafa hannu ta ce,"Da izinin wa ki ka bar gidan nan? Ina kuma ki ka je? Kai tsaye ta amsa,"Inna ai na gaya maku ba zan koma ba. Kin zaci wasa na ke yi ko? Ta ce,"To ba kuwa zama a gidan nan ba, bari baban na ki ya shigo. Na lura so ki ke ki kawowa mutane raini. Ta juya ya bar dakin. Zarah ta matsa inda kulolin abinci ke aje, ta buda ta zuba ta hau ci. Karfe 5 M.Umar ya shigo gida, Inna ta feshe shi. Ya jinjina kai ya ce,"Wai Zarah da na sani ki ke fadi? Ta ce,"Ka na wasi-wasi kenan? Shiga tana nan a daki." Tunda ya baro dakinsa yake balbala masifa har cikin dakin."Ki hada kayan ki, ki koma inda ki ka fito! Ta ki motsi, M.Umar har da barazara duka, amma ko alama Zarah bata motsa ba, sai sharar kwalla take yi. M.Umar ya cika da al'ajabi, yana haki, ya koma dakin sa. Inna ta yi zuru tana kallon sabon salo. Fadi take cikin ranta,"Zarah ta kangare." Haka kowa ya kwana a wannan dare. Babu barcin kirki.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ ------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Washe gari bayan sallar asuba. Nusaiba ke zaune bisa gado, tunani bisa tunani. Tun jiya take cikin wannan yanayin. Musamman da ga Abbanta ba shi cikin sukuni kuma tun isowarsu gida, babu inda ya sake fita. Tashin hankalinta ya k'ara tsananta, tun daga lkcn da ta ga nononta ya cika, har ya fara tsiyayewa a banza. Bakin takaicin dake cinta kenan, a halin yanzu bisa gado, ta rasa inda za ta tsoma ran ta, ta ji sanyi sbd tunanin dan kyakkyawan dan ta. Ta tabbata yana can yana kukan neman nono, ga shi nan yana zubewa a iska. Farkewa ta yi da kuka, sbd tausayin rayuwar da Naseer ya je fasu ita fa dan ta,. Ji ta yi an riko ta. Muryar Umminta ke fadin,"Nusaiba! Daina kuka, ki yi hkr. Ta fado jikin Ummi ta rungume ta. Ummi ta shafa kanta ta ce,"Ki yi shiru na ce. Allah ne ya kaddaro miki wannan al'amari. Yanzu dago fuskar ki ki ji. Ta dago, Ummi ta sa hannu ta share mata hawaye, kafin ta ce,"Abinda na ke so da ke Nusaiba, ki yi hakuri mu je a dauko yaron nan.Bawan Allah ne shi, bai da laifin komai. Sannan shayar da shi da za ki yi, shine yake sanya shakuwar uwa da danta, soyayya tare da jin kai.Ki sani Nusaiba Ubangiji ne kadai ya san dubun ladan da uwa take samu tun daga daukan ciki, haihuwa, raino tare da bada tarbiya, ga 'ya'yan da Allah ya bata,kar ki bari wannan gara6asar ta wuce ki Nusaiba. Ki dauko dan ki ya shaku da ke, ya san cewa ke ce mahaifiyar sa.
Ta yadda zai ji kan ki, a cikin zuciyar sa, idan Allah ya raya shi. Na yiwa Abban ki magana, na rarrashe shi, na kuma yi nasara, ya amince, yanzu yardar ki na zo nema, domin ya ce shi ba zai matsa miki ba, duk abinda ki ka za6a shi za'ayi.
Shi kuma Naseer din muna nan muna jiran sa, ya kawo miki takardar ki.
Yanzu me ki ka ce?
Ta goge kwallan da suka dararo mata, ta ce,"Ki je ki dauko shi Ummi, babu komai."
Ta tallafo fuskarta ta ce,"Yayi kyau. Allah yayi miki albarka.
Amma ki tashi ki shirya Direba zai kai mu, don ki kintso kayan ku a natsa.
Tashi ki daina kuka, ba na son ki na damuwa, kin kuma san Abbanki hankalin sa ba zai kwanta ba.
Ta goge hawayenta sarai,. Umma ta kama ta ta riko, ta raka ta hanyar bayi, sannan ta fice ita ma, don shiryawa.
Abban ke kwance a falon sama bisa kujera, shi kadai yake kallon silin yana lissafon halayyar Dan- adam mai abin mamaki.
Nusaiba ta shigo cikin shirin tafiya.
Kamar mai ciwo yake kwance, bai motsa ba har ta zo gun sa, yana kallon ta.
Ta tsugunna ta kwanto kanta jikinsa, ta yi shiru.
Ya daka kanta ya ce,"Bebina, ki je ki dauko dan ki, ki shayar da shi.
Allah zai ba ki lada, kin ji?Ta amsa da kai. Ya ce,"Mike ku tafi, na ga Ummin ki ta gama shiryawa.
Allah ya kiyaye hanya." Ta ce,"Amin Abba na." Ta mike ta wuce ya bi ta da kalllo, ta kai kofa, ta waigo suka hada ido, yayi dan murmushi yana mata (bye-bye) da hannu.
Ita ma ta yi masa, sannan ta sauka, lkcn karfe 7:30am. Ummi ta matsa mata ta dan ci kayan karin safe.
Karfe 8 Direba ya dauko su, suka damk'i hanya.
Karfe 8 din dai-dai. Naseer ya shigo falon, Umma, don gaishe su ko ba za su amsa masa ba.
Umman kadai ke falon,
tana ta faman gyangyadi.
Da alama Ameer ya sami barci, domin cikin dare yana ta jin kukan sa.
Bata kalle shi ba, ya durk'usa gaban ta, ya ce,"Umma ina kwana?
Kamar za ta kyale shi, sai wata zuciya ta ce, amsa.
Bata kalle shi ba ta ce, lafiya.
Farin ciki ya lullube shi, ya ce,"Na gode Umma.."
Ta kyale shi.
Yayi dan jim yana kallonta, kafin ya ce,"Umma ina Abba?
A fusace ta dube shi, ta yi masa tsawa,"Ga shi nan a baya na a goye!
Tabatacce maras kunya.
Ka sake zuwa ka tambaye ni, ina Abba ya ke, sai na ci mutuncin ka!
Yasa hannu ya dafa guiwoyinta ya ce,"Yi hakuRi Ummana, ba zan sake ba.Dama Zarah ce ta ce ba za ta dawo ba, sai Nusaiba ta dawo, shine nace ko za ki sa baki ta yi hkr ta dawo kafin a shawo kan Alhj?
Kai tsaye ta dube shi, tsakar ido ta ce,"Ban zuwa." Kar mu yi haka dake Ummana. Wallahi na yi nadamar abinda ya faru, ku sa ke ba ni

Chapter 3 of 8