Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
/> Suka shige kowa, yayi na sa wuri, yana neman abinda yake so.
Nusaiba na jaye da Ameer cikin kwandon Shopping din ta saka shi, don kar ya rink'a bata wahala, yana gudu, tana kamo shi.
Bata ko lura da mutumin dake tsaye 6angarn kayan abincin yara ba, sai da ta ji yana fad'in,"Ameer!
Haka ka yi girma?
Ta waigo da sauri ta dube shi.
Ibrahim ne ke wasa da habar Ameer.
Bai kalle ta ba, ya ci gaba da cewa,"Ka ba Husna kewa, kullum maganar ka take."
Ameer washe baki yake yana dariya.
Ita kuwa Nusaiba jikinta rawa ya dauka, ta tsura masa ido.
A hankali ya dago, ya dube ta yayi dan murmushi ya ce,"Hajiya Nusaiba."
Ta yi yake, tana fadin a ranta, "Ibrahim ko maye ne?Kafin ta ce ,"Ya ku ke? Ina su Husna da Mamanta? Ya ce,"Lafiya lau suke.
Amma ba ki da kirki? Ta gyara fuska,"Da aka yi me?
Shekara 1 ki na garin nan, ki kasa kawo mana ziyara, ba ki yi alkawari ba.
Sakin ta ce min ta ba ki (Phone Number), amma ba ki kira ba." Lambar ce ta 6ace. Ka gaida min Husna."
Ta fadi tana tura keken (Shopping) tana ci gaba da kiran yara,"Sumayya ina ku ke? Ku zo mu tafi!
Ya dan sauke numfashi, ya biyo ta a hankali.
Suka hadu da yaran a wata kwana,"Anti ba mu gama ba,"Inji babbar cikin su Sumayyah.
Dai-dai Ibrahim na tsayuwa wajen.
Ta ce,"Gaskiya ba zan jira ku ba, gobe Direba ya sake kawo ku." Yayi fit yasa masu baki,"Haba Anti, bai kamata ba, ki kyale su su gama."
Duk suka bi shi da kallo.
Ya juya kan sa,"Ga Sumayyah ko? Ke fa? Ya nuna mai bi mata, ta ce,"Khadija."
Ke fa? Ta ce,"Mahadiyya." Ya duka ya kamo 'yar kamar ,"Ke fa? Ta ce,"Zainab." Ya runtse ido ya ce"Wash! Uwa da magani. Sannu Husna.
Mahadiyya ta cafe,"Ba husna sunanta ba ZEE AFLAN! Ta kai mata duka, suka kwashe mata da dariya. Takaici ya ishi Nusaiba, ta tura keke ta yi gaba.Ta bar shi yana rabon fada, wa ya radawa uwa ta ZEE AFLAM? Lalai ba zai sha (Ice-cream) ba yau."Mahadiyya ta ce,"Ba ni bace. Anti Sumayyah ce."
Ya kada kai,"Ba ki kyauta ba.
To ku tsaya in tambaye ku, yaushe Anti Nusaiba ta zo nan? Sumayya ta ce,"Ta dade, tun Ameer na jariri." Baban Ameer yana nan garin ne? Ta ce,"A'a yana Nijeriya." Wai ko ba za ku zo mu tafi ba ne?
Yau na ga yara.
Nusaiba ta leko tana kiran su.
Sumayya ta wuce da saurarinta. Khadija ta biyo bayanta. Ya kamo hannayen su. Zainab tana tambayar sa,"Kai ya sunan ka? Ya dube ta ya ce,"Suna na mai son Anti."
Suka kwashe da dariya,"Wannan suna, ban ta6a jin irin sa ba."
Inji Mahadiyya,"Ya ce,"Ga shi yau kin ji. Ko a gida aka tambaye ki, ki ce mai son Anti, sunana."
Ta ce,"To."
Ya debo kwalayen cakulet 2 da biskit 2, ya mika ma su. Suka yi godiya.
Wajen biyan kudi, suka same su, duk cin maganin Nusaiba sai da Ibrahim ya biya kudin.
Suka shiga mota, yana tsaye yana tunanin ta yaya zai binciko gaskiyar lamarin? Sun bada baya kadan, ya manta bai ma tambayi inda gidan su yake ba.
Ya zabura da sauri, ya fada motar shi, ya bi bayan su.
A haka a hankali yake bin su.
Nusaiba na jin Mahadiyya na tambayar su,"Kun san sunan mutumin nan? "Wai mai son Anti."
Gabanta ya fadi, ta zaro ido.
Sumayya ta ce,"Ah lallai ma wannan.
Antin Nusaiba, wai kin san shi ne? Ta ce,"Ina fa na shan shi, ku da ganin mutum kun tsaya ku na surutu da shi." Ta ce,"Anti ba ki san shi ba, shine ya san sunan ki da na Ameer? Ta ce,"To saura in ji maganar a bakin Anti, sai na murje bakin yarinya." Sumayayya ta kwa6e fuska, ta dubi 'yan uwanta, suka kama dariya,
suna toshe baki.A haka suka iso gida, yana biye da su. Yana kallo suka shiga get, yana kallo duk suka wuce cikin gida.
Farin cikin ya kama shi, domin ya san mai gidan.
Injiniya Ahmad Kaita.
Abokin ogan sa ne a ofis, kuma yana aiki da (Internet Global Services Jordan) ne."
Suna da manya rassa a Potugal, Iraq, Swedan,. Hedikwatarsu na birnin New-York. Hamdala yayi, sannan yayi ribas ya koma, farin cikin zuciyar sa ya dawo sabo ful!
Washe gari karfe 9, yana (Internet Globar Services). Ofishin Injinya Ahamd Kaita.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------ a
Bai sha wahalar ganin sa ba, saboda dama sun saba gaisawa idan ya zo wajen ogan sa.
Bayan sun gaisa, yayi masa bayanin abinda ke tafe da shi. Nan take dadi ya kama Injiniya, domin ya san Ibrahim mutumin kirki ne, ogansa ma na yabon sa.
Nan take yayi maraba da shi, ya kuma ba shi kati, ya ce idan ya zo ya kira wannan lambar.
Yayi godiya, ya fito.
Ofishinsu ya wuce yana mai murna da farin ciki, babu abinda yake hangowa, sai an daura auran sa da Nusaiba.
Wai! Yaya zai ji ranat? Yayi sauri ya dafe kirji, dadi zai kashe shi.
Injiniya na koma wa gidan kan sa ya kira Nusaiba, ya gaya mata anjima za ta yi bako, kuma yana rokon ta, don Allah ta ba shi hadin kai, domin mutumin kirki ne.
Ta amsa da to.
Ta koma dakin ta, ta yi iya tunanin ta, amma ta kasa gano mai neman dama mata lissafi. Su Sumayya da sun rantse sun maya ba su gayaea Ibrahim gidan su ba, balle ya san mai gidan.
To ko hadin Injiniya ne? Ta tambayi kan ta. Ta runtse ido takaicin duniya ya isheta.Dan ta karami, an dame ta da maganar aure.
Ita kuma ba shine a gaban ta ba, tana son isashen lokaci, don kula da dan ta.
Ta sallaci isha'i. Bayan cin abinci.
Wankan ma ta ki yi, balle ta gyara jikinta.
Yadda take tun safe, haka take zaune tana tana jiran ta ga dan rigimar dake neman auranta.
Bata gama tunanin ta ba.
Zainab ta zo da gudu ta gaya mata sako, inji Abbanta.
Ta kura wa Ameer ido dake barci, sannan ta wuce ta fito.
Zuwa karamin falo, inda aka ce bakon yake.
Kai,"Inna-lillahi"Wa-Inna-ilahir-raji'un!
Haka ta fada lkcn da ta yi ido 4 da Ibrahim.
Ya ce,"Dole ki yi salati, kin ga mayaeb zai cinye ki."
Ta ce,"Saboda Allah menene na bn diddigi? Ya girgiza kai,"Ba ki ma sani ba?
Lallai yau ne na gane cewa da hadin bakin ki Abba ya hana ni auran ki."
Ta dan yamutsa fuska,"Allah ne,Abba bai isa ya hana ka ba."
Kin di ni baki Nusaiba, kuma hakan yana k'ara min son ki.
Wannan karon da alamun nasara, ki dubi tsawon tazarar dake tsakanin Najeriya da Jordan, amma Allah ya ce je ki Nusaiba mijin ki na can." Ta yi dan murmushi, ta rasa me za ta ce da shi."
Ba karamin dadi murmushi ta yasa shi ba.
Ya dan langwabar da kai, ya sake fadin,"Kamar an fama min gyambo Nusaiba, tun ranar da na sake ganin ki tare da Sakina, kodayaushe sai mun yi hirar Ameer ni da Husna, shi yasa har yanzu bata mance da shi ba.
Da gangan ki ka batar da lambar da Sakina ta ba ki, saboda ba kya son in san komai game da ke?
Ta ce,"Tabbas haka ne, na kuma kar6i lambar ta ne kafin in san ko ita wace ce, da na zo na sani, sai na kiyayi kai na, saboda tunanin me zai je ya dawo?
Ya jinjina kai,"Kin yi gaskiya, amma da yake Ibrahim mai sa'a ne sai ga shi abinda ya je, ya dawo din.
Ko ba haka ba? Saura a ban dama, ayi ta ta kare"
Ta ce,"Yaro na karami ne, ban ko yaye shi ba, da dai............
Ya katse ta,"Ki na nufin Ameer? Je ki ji yadda yayi suna a gida na, balle kuma ki kawo min shi, gaba daya zai zama da na.Ta ce,"Ban tsara masa hakan ba."
Ko?
Ta ce,"Tabbas."
Yayi dan shiru, kafin ya ce,"Ba kya so na dai ke nan."
Ta ce,"Ban fad'a ba."
Ya ce,"Idan ba haka ba,"Ameer ne kawai zai hana ki k'i aure na? Ta nisa kafin ta ce,"Har da matarka, domin na lura Sakina na son ka da yawa, bai kamata in shiga tsakanin ku ba.
Mun yi hira sosai da ita a jirgi, amma ka na zuwa, ka nuna mata ka sanni, shi ke nan ta sauya min fuska.
Ka ji dalilin yaga lambar da ta bani, don ba na son tashin hankali."
Hankalinsa ya tashi kwarai, ya ce,"Ba ki fahimce ta ba ne Nusaiba.......
Ta ce,"Haka ne Wallahi, ai ka ga lokacin ba ta ma san halin da na ke ciki ba.
Ta ganni da Bebi, ba ita ba, kai kan ka ka yi zaton ina gidan mijina.
Quite O.K a lokacin ba mu rabu ba, sai daga baya.
To ina ga ace ga shi za ka aure ni?
"Babu abinda zai faru. Haka Sakina take, bata iya rufe kishin ta, amma bata da fada, idan ku ka fahime juna za ki gane tana da hakuri."
Ta ce,"Na ji."
In turo kenan?
"Ai na gaya maka ba yanzu na shirya yin aure ba."
Ya runtse ido, dafe da goshi ya ce,"Nusaiba ba kya so na.
Please!
Ki je ki yi shawara, abinda ki ke fadi ba hujja bace."
Ya bata tausayi kwarai, amma gaskiya ba za ta iya aure yanzu ba, shi yasa haka suka tashi hirar babu fahimtar juna, kowannan su ya koma cike da tunani.Musamman Ibrahim da yake ganin Nusaiba na son ta yi wasa da rayuwarsa, bayan ya lashi takobin wannan karon, sai ya ga abinda zai ture wa buzu nadi."
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Abubuwa da dama suke damun Nusaiba, ta kan ji kamar ta tsero ta bar k'asar, domin Injiniya da Antina sun tasa ta gaba, akan zancan Ibrahim, kamar yadda shi kan sa ya addabe ta da zuwa.
A hak'ik'anin gaskiya tana tunanin Istaharar ta, kuma tana aji a jikin ta akwai maganar da Naseer yake son gaya mata, dama ce kai bata ba shi ba.
A wannan gwagwarmayar suka shafe shekarar har ta yaye Ameer, yana neman wata 6 da yaye.
Ibrahim bai hakura ba, ita kuma bata sakar masa ba.
Anti kam har ta yi fushi ta daina yi mata magana, kamar yadda Injiniya ya sa ido, abinda ya sa a ransa shine wata kila Ibrahim din ne bata so.
Shi kuwa Ibrahim har su Husna ya kwaso ya kawo mata tabbacin cewa Sakina ta sani kenan.
Wannan bai dami Nusaiba ba, domin bata san irin bala in da ya sha a gida ba, akan hakan.
Ta fara riga ta ga duniya, babu wata yaudar da Da namiji zai nuna mata.
Idan gaskiya ne, ya ce zai kai ta gun Sakinar mana?
Bai ta6a gigi ba, sai dai ya kwaso mata su Husna.
Kwatsam! Sai ga Alh. Basheer a Jordan, ba zato ba tsammani. Kai murna a wajen Nusaiba, kamar ta zuba ruka k'asa ta sha.Tana kewar sa sosai, tunda ya zo take like da shi.
Shi kuwa Ameer ke zuciyar sa, ji yake kamar in zai koma ya wuce da shi, ya zauna gidan sa.
Yaron yayi saurin girma kamar ba dan shekara 2 da watanni ba.
Suna zaune dare ya fara yi ga Injiniya ga Antinta.
"Alhaji ya tambaya,"Wai 'yar gidan ta ku bata fidda wani ba? Jin haka yasa Nusaiba ta tashi ta bar falon.
Injiniya ya ce,"Ai mu Nusaiba ba mu san inda ta dosa ba."
Kamar yaya?
Ya ce,"Wani yaro ke son ta kamar zai yi hauka,
amma ba ka ga yadda take wahalar da shi ba.
Ni Wallahi tausayi yake ba ni.
Yana da mata da 'ya'ya'yen sa 3.
Ibrahim sunansa, yana aiki da (Nijeriyan Embasy) , yaro mai hankali, amma ta ki ba shi goyon baya."
Ya ce,"Ibrahim?
Ni kuwa kamar na san sunan nan?
Anya kuwa ba yaron nan ba ne daya so auran ta da?
Fatima ta ce,"Oho,"Nusaiba wani bayani za ta zauna ta yi.
Yarinya da ka fara magana, sai kuka.
Ni dai yara suke gaya min wai a (Super market) suka hadu, amma sun ga kamar dama can ya san ta.
Ya ce,"Lalai Ibrahim din da na ke magana ne.
Kuma da akwai alamun tana son sa, ni ne na cusa mata Zancen Naseer.
To me yasa yanzu ba za ta aure shi ba?
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

---------------------------------------------------------------------------------------------- Zaharaddeen shomar Whatsapp 08168575100 Ajinisa Yake3-05 Posted by ANaM Dorayi on 11:43 AM, 25-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ Ta ce,"Ba zai wuce wannan yaron da ta kwallafawa rai ba. Ta shaku da Ameer ko alama bata son a raba su. Ameer kuwa dole ya koma gidan ubansa, sanin kan ta ne ba zai kyale mata shi ba. Alh. Basheer yayi shiru, Injiniya ke fadin,"Nusaiba manya, abubuwanta dariya suke ban, na ga yadda za'ayi wannan al'amari." Alh. Ya ce,"Ku kyale ta, zan yi maganin abin."Suka saki wannan shafin, suka kama wani, dare yayi Alhj ya tafi masaukin sa. Yana tunani tare ba tare da yayi wa Nusaiba maganar Ibrham ba. Koda dama bisa hanya yake, harkokinsa ne, suka kawo shi, hanya ta ratso da shi nan. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Yana zaune cikin ofis a gida Nijeriya, misalin 11 rana. Naseer yayi sallama ya shigo. Ya amsa,"Lafiya lau. Ya jikin na Zarah? Ya ce,"An gode Allah. Wannan karon dai Likita ya ce dole ta huta daga wannan, saboda mahaifar ta ta yi rauni da yawa. Ya dan kada kai,"Ayya, gaskiya ya kamata ta huta, saboda lafiyar ta, ayi hakuri da abinda Allah ya kaddaro." Ya ce,"Haka ne. Dama tun jiya na zo in nuna maka Result. Ya fito na kammala Diploma." Ya washe baki,"Ah! Lallai abin ba wuya a wurin Allah." Yasa hannu ya kar6i takardu, ya duba,"Kai! First class! Gaskiya takardun sun yi kyau. Yana 'yar dariya ya shafi keya, ya ce,"Sun ba ni (Adimission ABU), Direct. Next month za'a fara Rigistireshon. Alhj ya miko masa hannu,"Congrat! Kai na ji dadi., Allah ya bada sa'a." Amin." Ya fadi bakin sa ya ki rufuwa, ganin yadda Alhj ke murna. Ya mike yana fadin,"Zan koma Abba, na gaishe ka." Ya ce,"To na gode. Zan tura ma da sako(Acconut) din ka, ba yawa, sai ayi Rijistireshon ko? Ya tsugunna yayi godiya.Alhjn ya jawo dirowa, ya dauko farar ambulan ya mika masa,"Wannan ma sakon ka ne." Cikin mamaki yasa hannu ya kar6a ya kara godiya ya fice. Yana shiga mota da rawar jiki, ya buda ambulan, don ganin me ke cikin su? Wasu zaradan hotunan Ameer, ya rinka zarowa daya bayan daya guda 24 kala-kala. Wasu tun yana dan wata 4 a zaune, wasu yana rarrafe, da yawa a tsaye yake. Ya zura wa hotuna ido, kamar ya sume, saboda doki da farin ciki. Ya sumbata, ya rungume ya ma rasa inda zai aje su. Take nan ya kira wayar Zarah,"Kin ga yadda Ameer dina yayi girma? Ta ce,"A ina ka gan shi? Hotunansa Abba ya zo min da shu, sai kin ga yaron Zarah, kamar dan larabawa." Ta ce,"Ka na ta sa min rai, yayana ka kawo min in gani mana." Ya ce,"Ki jira, yanzu zan baro Kaduna." Ta ce,"Allah ya tsare." Ya ce,"Amin. Ya kashe waya. Ya bi hoton hannun sa da kallo, can ya sauke numfashi, ya sake sumbatar sa, sannan yayi wa mota key, ya ya wuce. Yana isa Zariya. Su Umma ya fara kai wa hotuna suka gani. Umma ta dauki daya. Ya kai wa Inna ita ma ta za6i na ta. Daga nan ya cilla Shika ya kai wa Zarah. Wai ta ga hotuna kamar ta dauko Ameer yayi motsi a gaban su. Nan ya bar mata 2. Fitowar sa asibiti a hanya ya shiga shagon sai da (Gift) da (Frem) na sa Hotuna ya siyo kanana guda 24. Gaba daya hotunan sai da ya sa su cikin frem har da na wajen su Umma da Inna. Sageer an ba shi. Yakubu ma, ya samu har da dakin Hajiyar sa.Naseer B ma ya ce yana so a ba shi. Naseer kamar zai hauka ce, saboda son Ameer. Bayan kwana 2 daya koma Kaduna. Haka ya ga hoton bisa tebur din Alhj gaba dayan firem din mai kyan gaske. Ba k'aramin dadi ya ji ba. Shi yasa ya k'ara kaimi wajen addu'ar sa. Allah ya dai-daita auran sa da Nusaibansa. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sati 3 tsakani, cikin Zarah ya k'i zama, wannan karon ko wata 7 bai kai ba, watan sa 6. Dole aka bi shawarar Likitan nan take aka juya mata mahaifa, don ta huta da wahala, domin ba k'aramar wuya take ci ba kafin ta haihu, ban da jinin da take zubdawa. Yaya za ta yi? Haka Allah ya kaddaro. Ubangiji yasa kaffara ce. Bayan ta gagije, lafiya ta zauna mata sai Naseer ya neman mata F.C.E. Ta samu a saukake, shi ya gama mata komai ta fara karatu. English/Islamic. Asabar da lahadi ya fita da ita koyon mota, tun tana tsoro har ta kware. Cikin sati na 3, ita ke kai kan ta makaranta. Shi ke nan ya sakar mata (Honda Civic) din sa. Shi yana amfani da Jeep kawai. Kasancewar Sageer zai tafi sabis din sa bana, sai shagon dinkin sa yayi rauni. Ba sosai yake zama ba, su Abbas ne kula masa da shi. Idan ya taso makaranta yake zama ko ranakun da babu karatu. Kusan ace hankalin Naseer kwance yake, amma Allah kadai yasan abinda ke damunsa a dangane da son dawowa da Nusaiba gidan sa.Ba shi da bakin magana ne kawai, ko kuma mu ce babu wanda zai kai wa kukan sa balle a share masa hawaye. Shi yasa wani lokacin za ka gan shi a rame, wani lokacin kuma babu laifi. Bayan wata 2 da dawowar Alh. Basheer Jordan yana ta binciken halin da Nusaiba suke ciki da Ibrahim. Babu wani sauyi, kodayaushe nuna masa take ba za ta aure shi ba, shine dai ya k'i hak'ura. Jin haka yasa Alh.Basheer ya ce maza-maza ta dawo gida Nijeriya ta yi aure anan. Ta shiga shirin kaya, cikin bak'in ciki da 6acin rai har ta rink'a jin kamar ta cewa Ibrahim ya fito, don ta san tabbas Ibrahim na tsananin sonta. Amma da ta tuna abinda Sakina ta yi mata a filin jirgi, sai ta yi turus! A tunanin ta da kyar Sakina za ta bar ta sakewa gidan Ibrahim. Saboda haka ta watsar da maganar Ibrahim, ta ci gaba da shirinta ko gaya masa bata yi ba. Ana gobe za ta dawo. Alh. Basheer ya kira Naseer ya same shi a ofis. Yana zaune, yayi shiru yana jiran ya ji dalilin kiransa. Alhj ya dan gyara fuska ya ce,"Gobe Nusaiba za ta dawo maka da Ameer, saboda ta sami miji za ta yi aure. Shine nace zan gaya maka, idan sun iso, ka zo ka kar6i abin ka, ka sa shi makaranta, tunda da bakin sa. K'iris ya rage ba'a zare ran Naseer ba, daga inda yake zaune, domin ilahirin kwakwalwarsa sa ta daina aiki.Yayi zugudun, kai sunkuye, bai motsa ba, balle ya ce wani abu. Alh. Basheer ya zura masa ido, jim kafin ya sake fadin. "Ka na iya tafiya, dama shi kenan sak'on, da zarar sun iso, zan kira ka a waya." Ya dago ya dube shi, ido cike da kwalla, sun kada jajur, bakin sa dauke da magana, sai dai ya kasa furtawa, sai ya ce to kawai. Da kyar ya mike ya nufi kofa. Alhj ya bi shi da kallo. Goge hawaye yake da bayan hannu. Yasa kofa zai buda. Alhajin ya kira shi. Ya waigo a gigice, yana amsawa. Yayi jim kafin ya ce,"Don Allah ka gaida min Malama Balarabe da kyau." Ya hadiye miyau, ya ce,"Zai ji Insha-Allahu." Ya buda, kofa ya fice. Ya shigo gida karfe 7 na magariba. Kwanciya yayi a dakin sa ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Zarah ta yi tambayar duniya, ya kyale ta. Ta yi mita har ta gaji, bata samu wata amsa ba, duk ranta yayi mata k'unci. Cikin dare ta farka, ba shi cikin dakin." Ta fito ta biyo shi, yana falo zaune cikin duhu, sai da ta kunna fitila sannan ta gan shi. Ta matsa gaban sa ta ce,"Ikon Allah, watau yayana she akwai wani lokaci da zai zo, wanda ba dole ba ne in san me ke damunka? Gaskiya ne.............. Ya katse ta,"Zarah ba wata magana bace. Ameer ne za'a dawo min da shi. Nusaiba za ta yi aure." Ta numfasa ta koma dirshan ta zauna kafin ta ce,"Amma yaya ka na da abin mamaki. Nusaiba za ta yi aure, ba dole ta dawo maka da danka ba? Menene abin damuwa a nan? Yayi mata wani mugun kallon da bai ta6a yi mata irin sa ba, ya ce "Babu! Rok'ona gun ki shi ne ki koma ki sha barcin ki. Please and Please!Ta bi shi da kallo, bata ma san me ke bata mamaki ba. Ta buda baki za ta yi magana, ya kwarara mata tsawa,"Ki tashi na ce ko? Ban son jin komai nace! Idanuwanta suka cika da hawaye, ta tashi da gudu ta nufi. Sashin ta kuka kala-kala ta rink'a yi, kamar yadda tunanin ta yake kala-kala. Lallai son Nusaiba ya zauna masa, ko kuwa don yana ganin ita bata aje masa da ba ne, shi yasa ya fara yi mata kwakwazo? To ai daga Allah ne, kuma bata bakin cikin soyayyar sa da Nusaiba. Me yasa zai juya mata baya yau? Kafin safiya, idanuwanta sun kunbura. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Naseer na kallon ta, tana shirin tafiya makaranta. Ransa ya k'ara 6aci. Tana ta wanke- wanke a kicin ya biyo ta, bayan ta ya rungume, ya sumbace ta, ya rada mata,"I'm sorry. Jini na ne ya hau, kar ki yi fushi da ni sweet Zarah." Ta runtse ido, hawaye suka zubo, ya juyo ta ya share su." Ya isa haka, ai ya wuce ko? La66anta na rawa ta ce,"Yayana ba na bakin ciki. Ko ka fara son Nusaiba, kuma ina maku murna idan da za'a ce gidan nan za ta dawo. Amma menene na yi min ihu saboda na fadi gaskiya? Saboda ban aje maka da ba ko? Nan da nan idanuwan sa suka kada,"Kin san abinda ki ke fadi kuwa Zarah? Kin maida ni jahili kenan, ban san Allah ba? Ya juya mata baya, ban ta6a zaton wannan maganar ba daga gare ki Zarah."Take nan ta amsa laifinta, sai dai ka fin ta mik'a hannu, ta kamo na sa, yayi waje ya bar kicin din. Tana kokarin biyo shi, ta ji tashin motar sa. Tana fitowa wajen Mai gadi na rufe get, ya riga ya fice. Ta koma falo ta zauna, tana mai nadamar furucin ta. Daga ita har Naseer babu wanda ya fahimci karatun ranar. Shi kam Naseer caji 2 ke kan sa, shi yasa ya kashe wayayinsa, baya son magana da kowa. Bai dawo gida ba sai bayan issha, yana shigowa falo, ya ji ta a jikinsa, kiris ya rage ta kada shi. Mafarin daya rike ta sosai kenan. Ta ce,"Yayana na tuba. Allah na tuba ba zan sake ba." Yayi ajiyar zuciya mai karfi, ya kamo hannunta, suka zauna. Ya dube ta ya ce,"Magana makamanciyar wannan kar ki sake min ita, idan ki na son farin ciki na a duniya." Ta kama kunuwanta 2, ta ce,"Ba zan sake ba yayana." Ya jawo kafadar ta, ta kwanto masa,"Ya wuce, shi kenan." Ta ce,"To yaya su Nusaiba, sun iso? Ya ce,"Ni wayoyina ma kulle suke tun safe, ba na son ya kira ni, so ban san halin da suke ciki ba." Ta ce,"Hakuri za ka yi yayana, su gani suke har yanzu ba ka son ta ne." Yayi shiru ya rasa me zai ce? Ta dan dube shi. "Zo mu ci abinci ko? Ya ja hancin ta, ya ce,"Sure." Suka tashi suka nufi tebur don cin abinci."A dai- dai wannan lokaci Alh.Basheer da Nusaiba tare da Ameer suka shigo gida. Alhj ya dauko su daga filin jirgi. Ummi ta tar6e su, murna kamar su lashe juna. Duk da Ameer bai santa ba, ya saki jikinsa da ita sosai. Da yake shi ba mai bakunta ba ne. Bayan sun ci abinci, an yi masa wanka yai barci, ita ma ta kintsa, ta tafi kiran Abbanta, yana falonsa kwance labarai yake kallo. ------------------------------------------------------------------------------------------------ Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ------------------------------------------------------------------------------------------------ Tana shigowa ya tashi zaune yana fadin,"Zo nan 'yar albarka." Tana murmushi ta zo gun sa ta zauna. Ya ce,"Yauwa. Magana za mu yi. Kin tuna alkawarin da ki kai min a asibiti? Ta dube shi,"Wane alkawari Abba? Ya ce,"Lokacin da rigamar auran ki da Naseer ta taso. Ina ganin laifina ne, amma ki ka ce a'a, kuma ko nan gaba na sake za6a miki wani mijin, za ki aure shi. Kin tuna? Ta kada kai, ta ce,"Na tuna Abba." To za ki iya ciki min shi? Ta dan yi shiru, kafin ta ce,"Zan cika Abba na, umurnin ka kawai na ke jira." Ya rungumo kafadar ta ya ce,"Allah yayi miki albarka. Kafin nan na riga na gaya wa Naseer za ki dawo masa da Ameer. So kafin ya zo, ki tsaya ki duba wannan takardar, wasika ce daga mijin da na sami miki." Ina fatan za ki aje hankalin ki waje daya." Ya sa hannu kasan filon kujera ya dauko amblun, ya mika mata ta amsa jiki ba kwari. Tashi ki je ki karanta, ki yi nazari akai, kafin Allah ya kai mu gobe inji ta bakin ki." Ta mike ta wuce babu wani ishashen kuzari a jikinta. Ameer ta tsurawa ido, ta fashe da kuka. Shi ke nan za'a raba ta da shi. Rayuwa kenan, abinda ya kamata ita da Babansa su ba shi tarbiyar da ta tace Hakan ba zai samu ba ko? Ta tambayi kanta, gocewa ta sake yi da kuka. Can wata zuciya ta ce,"Ba ga Antin ki ba? Ai za ta iya rike miki shi tsakani da Allah. Ta goge hawaye, ta ce,"Haka ne. Na san Antina za ta iya." Ta ci gaba da share hawayen, tana ajiyar zuciya. Ta dauko ambulan din dake gefe ta jujjuya ta, sannan ta farke ta, ta warware ta fara karantawa, "Gaisuwa irin ta addinin Islama. Kafin na ce dake

Chapter 6 of 8