Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 8
can a waje, yana kuka."Ta ta6e baki ta ce,"Ban haihu ba, Antina ce ta mutu. Ya kamo ha6arta ya ce,"Dube ni, ki saurara da kyau, za ki ji kukan Bebi. A kawo shi ya sha? Tayi shiru, tana kallonsa. Ya sake kiran Zarah, ya ce ta kawo Bebi,. Ta zo da shi a shawul, ya kar6e shi, ta tsaya tana kallonta! Ya ce,"Yauwa, dube shi ki gani." Kyakkyawan kallo tai masa! Ya ce,"Yauwa, dube shi ki gani, kyakkyawa da shi." Ta leko ta dube shi,"Abba na wannan k'aton Yaron ai ya girme ni." Ya ce,"Ban son shirme, ba shi ki gani, idan bai sha ba, ki min duka." Ya dora mata shi bisa jikinta, ta 6allo wa Zarah harara, sannan ta dubi Naseer,"Abba na ka ce wa matar nan ta fita, ban son ganin ta. Munafuka kawai, duk sune suka kashe Antina." Hawaye suka kawo wa Zarah, ta juya ta fita. Ya ce,"To ta fita, ba shi ya sha. Ta ciro ta ba shi, ya kama sai tsotsa yake yi, bawan Allah ya sha kuka, shi yasa bai jima ba, barci ya kwashe shi. Naseeer yayi zuru, yana kallon su, tsabar tausayinta yake ji, kamar ya ce wayyo Allah. Ta ce,"Abba na ka daina kallo na mana." Ya ce, "Ah! Ai kowa dole in kalle ki, tunda ina son ki, kin zama abar kallona. Ko kuwa? Ta sadda kai, tana dan murmushi. Ya dan k'ara matso ta, ya ce,"Kin ga har yayi barci, to ke ma ya kamata ki kwanta ki yi barcin, ki huta ko?Ta yi hamma mai tsawo, yana rufe da bakinta, kafin ta ce, "Barci?" Kin ga ni ban son shirmen nan na ce. Kawo Bebin a kwantar da shi, ke ma ki kwanta ki gani." Ta ce,"Bar shi kawai, ya yi min dadin rikewa." Hirar su kawai suke yi, abin ya ba kowa mmk, har Alh.Basheer ya gama zirga-zirgar sa, ya dawo. Ummi ce ta mayar masa da yadda aka yi, ta yi shiru ta natsu. Ya shigo dakin a hankali Naseer ya mike yana masa sannu da zuwa, da ta fasa wata irin k'ara, gaba dayan su gigicewa suka yi. Naseer bai san lkcn daya koma gun ta ba,"Menene? Idanuwanta rufe tana fadin,"Ban son ganin sa! Ban son ganinsa!! Munafiki ne............. Ya rufe bakin ta, yayin da Alh.Basheer yayi waje da sauri. Naseer ya ce,"Ban son abinda ki ke yi Nusaiba, gaskiya ni ma zan tafi." Ta ce,"Na daina Abba." Ta ci gaba da surutu k'asa- k'asa,"Munafikin banza, munafikin wofi, ya wani shigo wa mutane ko kunya." Yayi shiru, ya kyaleta, kwalla suka zubo masa, ya share. Wannan al'amari da me yayi kama? Kuma fa duk shine sila ko? Ya tambayi kan sa. Wasu hawayen sharshar! Suka fito, ya sake gogewa. Alhj kuwa yana tare da su Ummi, shi ma sai da ya share kwalla, sannan ya mayar da yadda suka yi da Likita, kuma nan ba jimawa, za so zo su tafi da ita dakin hoto. Jama'a sun sha Zagi da tsinuwa lkcn da aka zo daukan ta, har da Naseer din da yake fada aji, ya zama munafiki, tunda yana gani zai kyale a tafi a kashe ta. Dole Likita yasa aka kawo masa wata allura, da kan sa ya zurkud'a mata. Take nan ta wuce luuuu....!!! Ba rai, ba dalilinsa. Sannan da masu daukan ta suka gara ta wajen hoto.Har aka dawo da ita, bata sani ba, nan suka bar ta tana ta barci. Hankalin kam ba a kwance yake ba. 'Yan dubiya na ta zuwa gaishe ta, amma tana barci, da yawa daga cikin su daga Kaduna suke zuwa. Haka Antin Jordan kodayaushe sai ta bugo ta tambayi jikinta. Bizar ta kawai take jira a gama, ta kamo hanya. Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Sakamakon duk gwaje-gwajen da aka yi mata suka fito. Likita ya kira Alhj ofishinsa, shi kuma ya kira Naseer, domin mijinta ne, hakkinsa ne ya san halin da matar sa ke ciki. Kowanne ya ja kujera ya zauna gaban Likita. Shi kuma ya firfito da sakamako, ya ci gaba da bayani."A gaba daya binciken da mu ka yi, babu wata matsala a tattare da ita. Kwakwalwarta lafiya lau, zuciya ma haka, k'oda lafiya lau, haka jirin ta lafiya yake. Saboda haka abin nan dana fara gaya maka Alhj, shi din dai za mu ci gaba da kula da ita akan shi." Alhj ya ce,"Yanzu ka na nufin tsabar damuwa ce ta jefa ta a wannan yanayin? Ya ce,"Kar ka yi mamaki, damuwa tana sanya hawan jini, kuma babu ga mai juna biyu. Saboda haka za mu ci gaba da bata taimakon daya dace, sannan daga wajen ku a matsayin ku na iyaye da mijin ta, rarrashi ne kawai. A ring'a lalla6ata, a kodayaushe, hanklinta ya zamana a kwance yake tare da samun isashshen barci. Insha Allah za ta warware, sai kun yi mamaki."Alhj ya munfusa, ya dubi Naseer,"Ka ji ko? Wannan aikin ka ne, ko dama kai kadai take son gani, mu duk mun zama munafukai. Don Allah ka yi hakuri da ita, sannan a rink'a had'a mata da addu'a. Idanuwansa cike da hawaye ya amsa,"Ya zama dole Abba, Allah ya taimake mu." Duk suka amsa da Amin." Tun lkcn aka bar wa Naseer ragamar komai ahanununsa, kowa ya koma gida, sai dai su zo akai-akai su duba ta, shi ma ta, taga, idan har idan ta 2, idan kuwa har ka ga wanin Naseer a kusa da ita, tabbaci hakika barci take yi. Zarah ma an sallame ta, ta koma gida, amma kodayaushe zuciyar na asibitin, shi yasa bata iya daurewa kullum ne sai ta zo, koda za ta wuni a waje tana lek'en taga tare da renon Ameer. Haka Likitocin ta ke iyakar kokarin su ba dare, ba rana akan ta. Magana ce ta kudi. Alh.Basheer kuwa ya saki komai ya dace ayi mata, komai tsadar magani. Shi kuwa d'an gogon, bai gajiya da yi mata hidima, shi ne cin ta, shine shan ta. Kullum yana like da ita, suna hiar shirme, domin kuwa shirme ce, yanzun nan za'ayi magana dai-dai, lkc guda sai ta ya6o shirmenta. Babu abinda ya dame ta.Idan dare yayi kuwa tana barci, zama yake bisa kujera ya zura mata ido, yana yi mata addu'o'i. Idan ya tuna da bayanin Likita kuwa, hawaye yake zubdawa sosai, domin ya tabbata shi ya tara maya damuwar sa ta jefa ta wannan mawuyacin halin.A haka so da k'aunar Nusaiba suka zauna kwarai da gaske cikin zuciyarsa, har yana mamakin kan sa." ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi Kwanan ta 11 yau, ya gama kintsa Ameer, ya kwantar da shi cikin (Net) din sa. Ya dube ta, tana ta lissafin zucci, ya ce,"Za ki sha Tin ne kafin ki kwanta? Ta ce,"Had'o Abba." Ya had'o mata dai-dai wanda ta saba sha. Ya zo da shi bakin gadon, ya zauna. Ya debo a cokali ya ce,"Ungo, sha 'yar gidan Abbanta." Ta dube shi, tayi murmushi," Miss you."Dariya ta ba shi, ya ce"Za ki fara ko? Ai ni fushi na ke da ke."Me na yi Abba na? Ya mika mata, ta kur6e ya ce,"Batan kin kori kowa, mutane na son ganin ki, amma kin hana, me yasa? Hmm... Abba na kullum ina raba ka, amma ba ka ji. Me za'ayi da munafukai? Ya ce,"Na fa hana ki ce musu munafukai. Haka dazu ki ka cewa Umma, sa'ar ki ce? Ta dan 6ata rai, tayi shiru, ya miko mata Tea ta ki kar6a. Ya aje cokali ya dago ha6arta."Fushi ki ka yi? Da ni ki ke fushi, shi kenan bari in zo in tafi." Ta ce,"Yanzu saboda Allah Abba duk wanda ya nuna baya so na, ba munafiki bane? Yanzu dubi yadda ka ke k'aunar Naseer, amma k'iri-k'iri ya nuna min, baya so na, yayi ta wulakanta ni. Saboda Allah Abba me zan kira shi ba munafiki ba, tunda ya munafunce ka." Tunda ta soma mgn, gabn sa ya yanke ya fad'i, yayi sukuiti duk jikin sa ya mutu, ya rasa me zai ce? Ta zura masa ido, ta ci ga,"Abba ai dai ka san na maka biyayya da ka ce min shi ka za6a min, ban maka musu ba ko, Amma ka san Allah, shi baya so na, wannan cikin na jiki na ma, ya ce da shi zan koma gidanmu, baya so. Na ce ai ban je da d'a gidan sa ba, ko fan fadi gaskiya ba? Hankalin Naseer fa ya yi mummunan tashi, ya tabbata wata rana a surutanta za ta iya fadi a gaban kowa. Idanunwan suka kad'a, ya aje Tea bisa dirowa ya rufe.Ya kamo kafadunta 2, suka yi wa juna zuru kafin ya ce,"Wannan maganar bata dace ki na fadar ta ba 'yar gidan Abbanta. Naseer masoyin ki ne, ni ya gaya min yana son ki kwarai da gaske." Ta girgiza kai,"Na rantse da girman Allah, karya yake maka Abba. Naseer munafiki ne, ina gaya maka maganar nan, ka yarda da ni Abba." Ya sake ta ya kama kai. Ta bi shi da kallo ta ce,"Mamaki ma ka ke yi? Kai har yanzu ba ka san mutane ba, ka na dai kallo aka kashe Antina, me za'ayi? Yayi hucin zafi ya ce,"Duk na ji, amma kin san abinda na ke son ki da shi ? Ki kyale maganar nan, kar ki gaya wa kowa, ni zan yi maganin abin. Kin yarda? "ka dai gaya masa, idan na haihu zan aje Yaron, shi zai maida shi cikin lemon gwangw........................ Ya like bakinta,"Nusaiba na ce ki bar maganar nan, zan fa tafi abi na." Ta ce,"Yi hakuri." To kin yarda ba za ki gaya wa kowa ba? Na yarda, amma ka san Allah, ka yi hankali da wad'annan mahaukatan da suke zuwa 6arayi ne." Yayi shiru yana kallonta, duk ta dagula masa lissafi." Ba ni Tin mana." Ya dauko ya ci gaba da bata, sai zuba masa surutu take, shi kuwa bakin sa ya mutu har ta yi barci. Yayi tagumi bisa kujera, ya rasa abinda ke masa dadi.Ta dai ce ta yarda ne kawai, ba za ta sake fadi ba, amma abin maras hankali, ai ba'a sirri da shi. Dan saukin ta ma, bata kula kowa sai shi. Daran nan bai runtsa ba saboda tunani. Safiyar yau kuma daga ya ce, bude baki ayi burosh, shi ke nan ta fasa kuka. Yayi rarrashin dunuya, ta k'i yin shiru, ta k'i kuma mgn, a haka ta shafe sama da mintu 30 ita da kan ta ta yi shiru. Ta gyara kwanciya, ya sanya mata ido, tana ta ajiyar zuciya, har barci ya sace ta. A lokacin shi kuma ya fara na shi hawayen da kyar ya iya tsaida su, saboda tsabar tausayinta. Ko me yasa ta kuka? Oho! Ya tambayi kan sa, ya ba kan sa amsa. Idanuwan sa suka kara ja, kamar garwashin wuta, dama ga rashin barcin da bai yi ba jiya. Yana nan zaune zuru, ya ji motsin Ameer, shi ma ya farka. Ya tashi ya zuba masa ruwan dimi a fida ya zuba glucose ya karkada, sannan ya dauko shi suka fito waje, ya zauna a kujera yana ba shi har ya shanye. Idon sa 2, amma baya kuka, yana ta 'yan wasannin sa. Naseer na taya shi. Muryar Alhj kawai ya ji yana masa sallama, ya dago da sauri yana amsawa. Tare suke da Ummi da Antin Jordan. Ya mike yana masu sannu da zuwa. AntIn Jordan ta kar6i Bebi tana fadin,"Sannu Naseer, don kai ne abin gaisarwa. Yaro duk ya rame." Yana murmushi ya tsugunna, ya gaishe su.Alhj ya ce,"Mutuniyar barci ta ke yi ne? Ya ce,"Eh. Ummi ta ce,"Yauwa mun yi sa'a, shigo Fatima ki gan ta."Suka dungoma cikin dakin, shiru suka yi suna kallon ta kawai, don kar su yi surutu ta farka. Sun kusa minti 10 a tsaye, sannan suka fito dan koridon. Naseer ya baza darduma, suka zazzauna. Ya koma gefe ya zauna, suka ci gaba da tambayar sa yanayin jikin na ta? Ya ce,"Da sauki, an gode Allah, amma ko dazu ta sha kuka, kuma ta k'i magana, abinda ma ya sa ta barci ke nan." Antin Jordan ta goge kwalla, ta dubi Alhj,"Gaskiya yaya idan babu wani ci gaba a fita da ita waje kawai." Ya ce,"Wannan maganar na rai na, akwai iiya kwanakin da na dibarwa Likitocin nan din ne, idan sungaza, zan dauke ta." Ta ce,"Wannan tashin hankali da yawa yake." Ya ce,"Jarabci ne, mun gode Allah, muna rok'onsa sauki. Kai Naseer ka yi ta hakuri, ka ji? Ya ce,"Hak'uri na mu ne duka Abba." Haka suka kasance tare, jama'a na ta zuwa kamar kullum. Koda ta farka. Naseer ne kawai ya shiga, ya kai mata Bebi. Allah da ikon sa babu kuka, sai hira kamar ma ba ita ta sharari kukan dazu ba. Yayi mata burosh, ya bata Tea, ta sha. Abin yana ta 6a Antin Jordan mmk har ta tambaya,"Yanzu ina shiga, sai ta fara Ihu?, Ummi ta ce,"Ko za ki gwada ne? "Don daukan alhaki? Na gan ta ta taga, ya isa. Allah ya yaye mata." Ta ce,"Amin. Kwananta 7 ta koma Jordan. Ranar da ta tafi, ranar Kausar ta iso da mijinta. Bata 6ata lokaci ba, ta fadawa dakin, kanta ta yi ta rungume ta sa kuka. Wani ihun da Nusaiba ta yi, dole ta sake ta, tana kallo, jiki na rawa. Ta runtse ido, tana zagi tana fadin. "Ban son ganin su. Ban son ganin su! Naseer ya rirrike ta. Mijin Kausar ya fito da ita, me za ta yi ba kuka ba. Haka ta fada jikin Ummi, tayi ma isar ta. Naseer kuwa da kyar ya shawo kan Nusaiba tayi shiru, ta daina zage-zage. Ba karamin Huashi Kausar ta bata ba, sbd ta6a tan da tayi.Yini guda masifar da ta rink'a yi kenan,"Wata munafuka ta zo ta cakume ni za ta kashe ni! Sai bayan la'asar tayi barci. Kausar ta je gun ta, tayi mata addu'o'i. Hawaye na zuba. Da yamma lilis suka koma Kaduna. Haka Kausar ta tafi da bak'in ciki, a duk lkcn da ta tuna hawaye, ke zubar mata. (Allah sarki Nusaiba Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 3-02 Posted by ANaM Dorayi on 08:53 PM, 20-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______

Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi
------------------------------------------------------------------------------------------------
To shi kenan ya wuce." Ya kamo ha6ar ta, yi dariya,"Yi dariya 'yar gidan Abba!
Ta fado kirjinsa, tana murmushi.
Ya rungume ta, ya runtse ido, wasu kwalla suka yi masa caa, fadi yake a ransa, "Son ki ya kama ni Nusaiba, ki yafe min don Allah.". (Hhhhhhh, Anzo gurin, ammafaaaa...uhm! Maji ma gani)

Bai ko san ta kici-kicin tashi ba, sai da ya ji tana kira,"Abba!
Ka shake ni!
Ya hanzarta sakin ta, yana goge kwallah. Ta bi shi da kallo,"Wash!
Ka wani matse ni Abba, ai sai in mutu."Ya tashi ya bata wuri, ya shige bayi ba tare da ya ce komai ba.
Jim kadan ya fito, ya wanke fuskarsa, kwance ya same ta, ya matsa gabanta ya ce,"Hirar ta isa haka, ki yi barci ki huta." Ta amsa da ka, ya duk'o ya sumbace ta, ya ja mata mayafi. Ya ja kujera ya zauna, ya sauke numfashi,"Allah ka ga iya kokarin da na ke yi. Allah ka taimake ni yarinyar nan ta sami lafiya.
Ta ce,"Ka kwanta mana Abba." Ya ce,"Zan kwanta, ke dai yi barcin ki." Ta rufe ido.
Tare da gyara kwanciya.
Da asuba ya fito bayi da alwalar sa, ya shimfida sallaya, yayi sallah. Ya jima yana addu'o'i kafin ya jiyo motsin ta.
Ya waigo yana kallon ta, ta tashi zaune, tayi mika tana salati. Ta kalli can, ta kalli nan, bai ce da ita k'ala ba.
Ta k'ura wa Bebin da ke barci cikin (Net) ido.
Ta dago kai ta dube shi, suka yi ido 4.
Yayi murmushi, ya ce,"Kin ta shi?
Fashewa tayi da kuka, ya taso da sauri ya zauna gefen ta."
Nusaiba, ke Nusaiba, za ki fara koke-koken nan ko?
Tayi shiru tana tunaniin Antin ta.
Hawaye na ta ambaliya.
Ya rik'o ta, ta kwace jikin ta, kuka take tana k'arawa.
Ya ce a ran sa,"Na shiga 3, yau kuma da kukan ta tashi." Ya matso, ta matsa. Ya ce,"Ni Nusaiba, ni ki ke gudu? Bata kalle shi ba, balle ta ce wani abu. Ya sake matsowa, ta matsa. Ya ce,"Shi kenan, bari in yi tafiya ta, in tafi ko? Ta amsa eh, da kai. Ya ce,"Tabd'i! Da magana yau,"Cikin ransa.Ya rasa yadda zai yi, dole ya sa mata ido, tayi ta kuka. Can kuma ta tashi ta fito koridon ta zauna, bisa kujera. Shi ma ya biyo ta nan ya zauna, yana gadin ta.
Jim kada ya ji kukan Ameer.
Ya mike ya ce da ita,"Ga Ameer can ya tashi, in kawo shi ya sha? Ta kyale, bai ma ishe ta kallo ba, ya shige ciki ya dauko shi, ya tsugunna gabanta,"Yauwa, 'yar gidan Abbanta kenan, dubi Bebin mu kuka yake yana jin yunwa, dan ba shi ya sha." Ta dauke kai, tamkar bada ita yake magana ba.
Abu fa ya gagara, dole ya dauko wa Ameer fida ya tura masa, yayi ta tsotson ruwa da glucose.
Kullum karfe 7 nan take masu. Alh.Basheer suna nan zaune kuwa, sai ga su.
Naseer ne ya fara hango su, ya mike ya nufo su.
Su ma tsayawa suka yi cak, ganin Nusaiba a zaune wajen.
"Yaya dai? Alh.Basheer ya tambaye shi, yayin da Ummi ta kar6i Ameer a hannun sa.
Ya ce,"Ai yau ko Ameer ta k'i ba shi nono.
Kuka kawai take yi,"Ya ce,"Likita ya zo?
Ya ce,"Ka tsaya nan, kai kuma koma gun ta, bari in nemo Likitan." Ya koma wajen ta.
Alhj ya zaga ya wuce, ita kuwa Ummi ta lafe.
Jimawa kadan suka dawo da Likita. Abin ya ba Naseer mamaki daya ga Lkita ya zo, ya tsaya gabanta bata zage shi ba.
Ya ce,"Nusaiba, tashi mu shiga ciki, mu yi wata magana." Kai tsaye ta mike ta wuce. Naseer ya saki baki, shi ma ya taso ya biyo su. Ta zauna bakin gado, ya jawo kujera ya zauna ya ce,"Kukan me ki ke yi?
Ta ce,"Antina ta mutu ko?Ya ce,"An gaya miki bata mutu ba, Antin ki na gida." Ta runtse ido wasu hawayen suka tsunke mata, ta sa hannu ta share. Ya ce,"An ce kin ki ba Bebin ki nono, saboda me? Haka za muyi da ke saboda Allah? Ta dube shi da kyau ta ce,"Doctor ka yi min wani taimako don Allah, lambar Abba na zan ba, ka kira min shi." Idanuwan Naseer suka k'ara yo waje, ya koma da baya da baya ya fito waje. Shi kuwa Likita k'ara tsura mata ido, ya ce,"Abban ki? Ta ce, eh. Ya ce,"Ina zuwa." Ya leka yayi kiran Alhj da hannu. Ya taso daga inda yake zaune ya zo. Likita ya kamo hannun sa, ya shigo da shi a hankali. Kan ta na duke ya ce,"Wannan Abban naki ki ke nema? Tana yo ido hudu da shi, ta mike hawayenta suka yawaita, ta ce,"Abba! Wani tsananin farin ciki ya kama Alhj, dole kwalla suka cika idon sa, ya ce,"Bebin Abba! Ta rugo da gudu ta rungume shi. Tuni Ummi ta fado dakin ta hade su ta rungume, kuka suke saboda murna. Haka Naseer ke sharar kwalla. Amma ya rasa abinda zuciyar sa ke sakawa game da wannan al'amari. Tabbas Nusaiba ta warke, to me zai biyo baya? Da alamun zai shiga magana, yanayin da ta nuna. Yayi ta maza ya shigo. Alhj Basheer ya rungume shi, suna wa juna barka. Likita ya fita, ya bar su cikin farin ciki da murna maras misaltuwa.Bayan sun natsa. Ummi ta dubeta, duk ta rame ta ce,"Sannu Nusaiba, Ubangiji Allah ya k'ara karewa." Ta ce,"Amin. Ta miko mata Bebi ta ce,"Kin ga Bebin da aka ciro miki? Ta dan dube shi, tayi murmushi , ta dauke ido,"Na gan shi Ummi ta. Kwalla suka taru fal a idonta, ta kasa shanye su, sai da suka zubo. Abban ya rungomu kafadunta, ya ce,"Yi hakuri daina kuka, komai ya wuce Insha-Allah." Ya ce,"Allah ya yarda Abba. Bari in yi sallah." Ta mike ta wuce bayi ta jima bisa sallaya, tana yi wa Allah godiya daya dawo mata da rayuwarta dai-dai. Ta dawo gefen gado ta zauna kusa da Abban ta. Ya jawo ta jikin sa, ta dan numfasa ta ce,"Abba lokaci yayi da zan gaya maka wata magana, ina fatan za ka gafarce ni." Naseer na jin haka, ya mike ya bar dakin. Abba ya ce,"Babu komai Bebina, gaya min, me ke da mun ki? Ummi ta sa masu ido tana kallo. Ta k'ara gyara zama ta ce,"Na san za ka yi mamaki, idan na gaya maka cewa tun aure na da Naseer, babu kwanciyar hankali tsakani na da shi. Ai kuwa Alh ya sha mamaki, ba shi da kadai ba har Ummi da take zaune. Ya kara dubanta, baki sake, ya tambaya, "Saboda me? Ta ce,"Abinda na fahinta,"Abba, shine ya kar6i aure na ne kawai don ka cika masa ido, ba zai iya ce maka a'a ba. Amma a hakakin gaskiya Naseer baya so na, kuma ya nuna min kiyayya, ba don Antyna na tsaye ba, ina ganin wuyar da zan sha, ba 'yar k'arama bace.
------------------------------------------------------------------------------------------------
Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi....
https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473
Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi

------------------------------------------------------------------------------------------------
Shi yasa na ke son ta, domin tayi min komai, kuma tayi iyakar kokarinta wajen jawo hankalinsa zuwa gare ni, sai dai haka bata samu ba, saboda babu sona a zuciyar sa." Ransa ya 6aci kwarai, ya ce,"Me yasa tuntuni ba ki gaya min ba? Ta ce,"Saboda kai ne Abba. Ba na son wani tashin hankali ya shiga tsakanin ku. Kuma ina ganin ai ya girmama ka ne, tunda ya kasa fitowa fili ya nuna maka baya so na. Shi yasa na yi ta kokarin zama da shi shekara daya da rabi, sai da Allah ya kawo rabon wannan Yaron, sannan ya shiga daki na. Daga baya na yi tunanin bai kamata mu zauna muna cutar da juna ba, shi yana jin haushi na, ni ma ina jin na shi. Sai na same shi a daran da wannan abin zai faru, na yi masa magana. Abba cewa yayi idan na k'ure shi, zai 6atacciya, dole in koma gidan mu, har d'an baya so, ya bar mana...................!!! Tana shiru. Ummi ta cafe,"Ina, inda kuma yayi karya kenan. Ai ba mu kai masa ke da Da ba." Alh.Basheer yayi shiru, zuciyar sa na tafasa, abin kamar a mafarki yake ganin sa, domin ko alama bai ta6a mafarkin Naseer zai ci amanar sa haka ba. Ya dubi Ummi ya ce,"Har hada mata kayan ta mu tafi." Ta mike tana fadin,"Ashe ga damuwar da ta kusan hallaka rayuwarki Nusaiba, kenan. Yayi wa kan sa. Kuma sai Allah yayi miki sakayya." Nusaiba ta kada kai,"Ba haka bane Ummi ta, ba laifin sa bane, kar ki manta soyayya, gamon jini ce, laifin sa 1, shine daya danki amanar da ba zai iya rikewa ba."Alhj ya ce,"Duk laifin iyayen sa............ Tayi saurin katse shi."A'a Abba, iyayen Naseer ba su da laifi kuma ina mai tabbatar maku yadda ya yaudare ku, haka ya yaudare su. Ba su san komai ba a game da zaman mu. Sun rike ni tamkar 'yar cikin su. Idan na ce ga abinda su kai min, na yi masu karya, sai Allah ya tambaye ni. Abba, rokon da zan maka daya ne, don Allah, don son Annabi kar ka k'ullaci kowa akan maganar nan, ni ce baya so, to ka dauki 'yar ka. Ai shikenan, an gama magana." Ya ce,"Haka ne Nusaiba, ki yi hkr, ni ma na gane kuskure na, ni na jawo miki duk abinda ya same ki." Ta ce,"Ban ta6a ba ka laifi ba Abba, ba kuma zan ta6a ba ka ba. Ai kai alheri ka k'ulla, sai dai ka san a wannan zamanin ba kowa yake son ayi masa za6in abinda ya kamace shi a ruywar sa ba. Ya fi son abinda ra'ayinsa ya ba shi. Ka ga kuskuren da aka samu. Ina alfari da kai Abba na, kuma ko a yanzu ka sake za6a min miji. Wallahi zan aure shi. Bai san lkcn da ya rungume ta, ya fara kwalla ba. Haka Ummi ke ta share hawaye, tana sawa Nusaiba albarka. Ta mike ta shiga hada kaya. Hayaniyar hama'a suka jiwo gaba daya jama'ar Naseer ne. Zarah ma kayan barci ne ajikin ta, ta dora zani ta sa hijabi. Suka doro cikin dakin. Zarah na fadin,"Amarya!Ta zaburo da gudu, "Antina! Suka rungume juna, sun sha kuka, sai da Umma ta raba su ita ma, ta rungume ta. Daga nan ta matsa ta gaida kowa. Su Malam Balarabe, Malam Umar. Ya gaisa da Sageer da amayar sa. Bayan an gama gaishe-gaishe. Malam Balarabe yasa aka yi addu'a, kowa ya shafa. Aanan suka lura babu Naseer tun shigowar su. Inna ta fara magana,"Jama'a wai ina dan Inna ne? Malam Umar ya ce,"Kai wai dama babu Naseer a wajen nan? Sageer ya amsa,"Ai kuwa baya wajen nan, tunda muka zo? Malam Balarabe ya ce,"Ah to ina ya je? Ya fadi, yana kallon Alh.Basheer. Ya ce,"Gaskiya ban san inda ya je ba. Kuma dama ina son ganin ka, idan ba za ka damu ba." Ya ce,"Bismillah Alhj, ba damuwa." Suka fito waje, yayin da Zarah da Nusaiba ke like da juna suna maida yadda abubuwa suka faru. Alh.Basheer ya kebe da M.Balarabe, ya kwashe bayanin da Nusaiba tayi masa kaf, ya gaya masa. Tun da ya soma magana, gaba daya jijiyoyin jikin Malam Balarane suka tsinke, jiri ya fara dibar sa. Allah yasa a zaune suke, da babu abinda zai hana shi faduwa. Tabbas ya san Naseer baya son auran nan, aka yi shi, amma ko alama bai ta6a sanin rashin mutunci da wulakancin da ya rinka aikatawa ba. Ya jima kafin ya ce,"Alhj wannan magana ta ban kunya, kuma Wallahi tallahi ban san komai a game da zancan ba. Nusaiba bata nuna mana ba, balle ta furta da bakin ta. Don girman Allah ka yi hakuri Alhj. Ya ce,"Ai magana ta k'are, tunda baya son ta, ni ina son abata kuma zan tafi da ita, ba tare da 6ata lkc ba. Amma D'a, ban sako mata shi cikin gara ba, sbd haka nan za ta aje shi ko ya kashe ko ya bar shi da rai, duk ya rage nasa. A karshe, ka gaya masa na gode. Allah ya saka da alkhairi. Kan M.Balarane yayi gingirinn! Kunya kamar ya nutse kasa. Idanuwan sa suka cika da kwalla, ya rasa me zai ce wa Alhj? Kawai sai ya juya ya dawo dakin, gaban kowa ya daga murya ya ce,"Nusaiba, don me za ki min haka???Akan me za ki zauna sama da shekaru 2 cikin wulakanci da bak'in ciki,

Chapter 2 of 8