Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 8
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Ajininsa yake 3-01 Posted by ANaM Dorayi on 06:55 PM, 19-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . .Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp zuwa bude blog, daga bisani sai nafahimci kamar da yawanmu vamufiyason shiga blog ba, Bansan dalilin hakanba, sakamakon yawan korafe korafe dake riskata yasanyani yin nazari wace hanyace ke da sauki bayan wannan, karshe dai natino face book, sakamakon haka muka yanke shawarar bude page a facebook din duk domin fadada hanyoyin sadarwarmu wadda ba dan komai mukeva sai dan jin dadinku,insha Allahu Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi Uku, :-Whatssap. 08139787515 :-Blog Anamdorayi.mywapblog.com Saikuma ... :-Face book.. https://mbasic.facebook.com/ HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7% 2CPAGE_ID10%2C7370123473 Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin kanku.. Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin mu sanya littafi na gaba.. Naku har kullum ANaM Dorayi --------------------------------------------------------;------------------ Ya koma rigingine ya kwanta, ya rasa dalilin da yasa Nusaiba ta tinkare shi da wadannan maganganun banzan. So take ta hada shi da iyayensa ko me? Idan kuma ta gaji ne, ai bai yi mata tirke ba. Iyakar ta Alh. Basheer ya ce ya aje masa komai na sa, sai me? Daran nan Nusaiba bata yi barci ba, gaban Ubangiji ta gurfana kamar yadda ta saba kai kukanta. Allah ya za6a mata alkhairi. Haka kuma tayi kukan bakin ciki yau ita da mijin auranta take cacar baki. Lallai rayuwa shirin Allah ce, amma ko a mafarki bata ta6a tunanin hakan ba a rayuwar ta. A kodayaushe zuciyar ta na shirya mata kyakkyawar rayuwa da jin dadi tare da gamsashshiyar soyayya ga duk mijin da ta aura. A kunnan ta aka yi kiran sallar farko, ciwon kai ya ce ga shi nan irin wanda bata ta6a jin irin sa ba. Da kyar ta sallaci asuba. Ta jawo filo ta jefa bisa sallayar ta kwanta. Dora kan ta, ke da wuya ta ji fitar Naseer kamar da gudu. Ta tashi zaune tana sauraron buga kofar falon sasn su Abba. Ta mike ta fito kofar falonsu a gwame. Tayi waje can sasan su Umma. Naseer ta ji yana fadin,"Zarah ba lfy, yanzu Inna tayo waya inje maza-maza. Kafun su Abba su gama salati, ya fice. Ta koma daki da saurin ta, ta dauko hijab ta suro jakar hannu.don ta tabbata haka Naseer ya fita babu ko sisi ajikinsa. Ta fito, ta iske su Umma ma tsaye suke a waje, ya tafi ya bar su. Makullin motar ta na cikin jakar ta bude ta dauko,"Umma zo mu bi shi a wannan motar." Ta ce,"Ba ni so ki na yawon nan Nusaiba, cikin ki ya tsufa." Abba ya ce,"Gari bai k'arasa waye ba ma, kun tafi ku 2 mata a mota? Gara ku bari gari ya waye sosai." Ta ce,"Ba komai Abba, Allah zai tsare. Umma zo mu je yanzun garin zai waye." Umma ta shiga suka rankaya. Malam Balarabe na tayi masu addu'a. Hajaran majaran! Suka iske Naseer da Inna, domin ance jaririryar ta mutu a ciki, sbd haka Likitar za ta yi iya kokarinta su fito da ita, idan kuma abin ya faskara, aiki za su yi mata. Nusaiba ta nemi waje ta zauna jinin ta ya k'ara hawa, kan ta kamar ya tsage, sbd tsabar ciwo. Bayan kusan minti 40. Likitan ta fito ta ce, maza-maza su je su biya kudin aiki. Ta mika wa Naseer takarda, hannunsa na rawa ya rike ya duba. Dubu 35 zai biya. Umma ta ce,"Ka fito da kudi ko ko? Ya girgiza kai,"Sai na koma gida, kuma ina jin kudin da ke gidan dubu 10 ne kawai, banki kuma ba su fito ba, ya za'ayi kenan? Ya tambaya hankalin sa tashe. Kafin Umma ta ce wani abu Nusaiba ta miko rafar kudi, ga wasu yi maza kaje ka biya. Ya bi tada kallo kafin yasa hannu ya kar6i kudi ya kwasa da gudu ya nufi wajen biya. (Allah sarki baiwar Allah, Allah yahadamu da mata masu tausayinmu da kaunarmu) Duba da yawan makaranta Hausa yasanyamu fadada hanyar sadarwar mu daga whatsapp zuwa bude blog, daga bisani sai nafahimci kamar da yawanmu vamufiyason shiga blog ba, Bansan dalilin hakanba, sakamakon yawan korafe korafe dake riskata yasanyani yin nazari wace hanyace ke da sauki bayan wannan, karshe dai natino face book, sakamakon haka muka yanke shawarar bude page a facebook din duk domin fadada hanyoyin sadarwarmu wadda ba dan komai mukeva sai dan jin dadinku,insha Allahu Labarinmu nagaba zai kasance ta hanyoyi Uku, :-Whatssap. 08139787515 :-Blog Anamdorayi.mywapblog.com Saikuma ... :-Face book.. https://mbasic.facebook.com/ HAUSA-Novels-389304544597988/?_e_pi_=7% 2CPAGE_ID10%2C7370123473 Hakan amma bazai tabbatuba sai da hadin kanku.. Dan haka inna bukatar 20,Like a group din kafin mu sanya littafi na gaba.. Naku har kullum ANaM Dorayi Nusaiba fa duk ta rude, ta k'ara rikicewa musamman yadda ta ga Nosis na shiga suna fita. Likitoci 2 ke kan ta, suna ta k'ara kokarin su, domin ba sa son ayi mata aikin. Allah da ikonsa kuwa Likitan da aka kira, yayi nasarar ciro matacciyar jaririyar, sai dai Zarah nan take numfashin ta ya dauke. Ba ta ba dalilinta, komai ya daina aiki a jikinta. Suka yi caa kanta, latsa nan, gwada can. Amma ba alamar motsi. Likita ya tura a dauko (Oxygen). Su Nusaiba na tsaye. Nos din ta fito da gudu, jim kadan ta dawo da shi da shige dakin. Zuciyar Nusaiba ta soma bugawa, ta nufin dakin tana fadin,"Shi kenan Antina! Su Umma suka rirriko ta, su ma kukan suke yi. Inna ta ce,"Zo ki zauna Nusaiba, kin ga ba ke kadai bace. Ki kwantar da hankalinki, ki yi mata addu'a. Tana shiru. Naseer na iso wajen, bai yarda da yanayin daya gansu ba. Ga Nusaiba na kuka tana ta fadin,"Shi kenan Antina." Ya ce,"Menene Umma? "Ba komai, ji ka ka gaya ma su ka biya kudin." Ya tsura wa Nusaiba ido, duk ta fita hayyacinta, ya ce,"Ki yi shiru mana." Ta ja hijabi ta rufe fuska, sannan ya wuce, ta biyo bayan sa. Yana isowa kofar. Likitin na fitowa. Ya mika masa takarda da siri,"Doctor an biya kudin,"Ya ce,"O.K, ka rike risit din za'a maida ma ku da kudin ku, an riga an ciro Bebin. Ita ma uwar sai dai ku yi hakuri.... Nusaiba ba ta gama jin bayayin ba, ta yanke jiki ta fadi, nan take ta hau fizga. Gaba daya suka yi caa kanta har da Likitan. Abin kamar bugun jinnu, duk gabobinta sun sandare, idanuwa sun kakkafe, baki kumfa. Likita ya ce, a kai ta ofishin sa. Naseer ya dauke cak! Ya kai ta ofishin, ya kwantar bisa dan gadon su. Su Umma ne biye da shi kamar za su yi hauka saboda tashin hankali. Shi kansa Naseer hawaye ne ke sauka bisa kuncinsa. Likita ya miko masa takarda,"Sa min hannu nan, dole a cire abinda ke cikin ta, don tsira da rayukansu." Bai jira Naseer ya gama sa hannun ba, ya fice da saurinsa. Jim kadan wasu Nosis suka shigo da gadon daukan maras lafiya, dukkan su da kayan dakin tiyata a jikin su. Irin kayan suka sanya wa Nusaiba, suka maida ta gadon da suka zo dashi, suka gara ta dakin tiyata. A tsakar wurin Naseer ya zube ya kame kan sa hannu 2, ya rasa duniyar da yake." Me zan gani yau? Inna-lillahi- wa"Inna-ilaihir-raji'un! Umma ce tayi karfin hali ta kar6i waya hannu Inna, ta kira Malam Balarabe,"Mallam ka yi maza ka zo, abubuwa sun rinca6e, daga Zarah har Nusaiba ba mu san halin da suke ciki ba. A zaton da mu ke yi ma dai Zarah babu ita. Nusaiba kuwa yanzu suka wuce tiyata da ita." Hankalin sa yayi mummunan tashi, salati yake yana k'arawa, har ya rufe gida, ya kama hanya. A mota ya kira Alh. Basheer ya labarta masa halin da suka wayi gari da shi. Subhanalillahi! Babu 6ata lkc suka baro Kaduna. Malam Balarabe na isa. Shi Malama Umar ya iso. Yadda suka same su zazzaune haka su ma suka nemi wuri suka zauna. Naseer na nan dunkule a kasa. Malam Umar bai ko shaida shi ba, sai da ya jima a wajen. Ya tashi ya matsa gun sa ya tsugunna ya dago kan sa,"Naseer! Tashi daga k'asan nan, zo nan ka zauna." Ya kamo shi ya taso da kyar, suka zauna bisa kujera, yana rungume da kafadar sa. M.Balarabe shi ma ya taso, ya tsugunna gabn su ya ce,"Sun bada gawar ne? Ya girgiza kai, hawaye suka kara kubce masa, ya ce,"Sun ce ba mutuwa tayi ba, doguwar suma ce, shine suka sa mata (Oxygen)Gaba dayan su suka sauke numfashi, suka yi hamdala ga Allah, tare da addu'ar Ubangiji ya ba su lafiya. Kamar wucewar minti goma da zuwan su Abba. Likita ya fito, duk suka mike suka nufi gun sa,"Yaya Likita? Yayi dan murmushi,"An yi nasara,"Bebi, na nan lafiya lau, shi da uwar sa. Za'a fito da su nan bada dadewa ba. Kowa sai hamdala. Umma da Inna suka rungume juna. Duk da haka hankalin Naseer bai kwanta ba, so yake ya gansu da idon sa, ya tabbatar da lafiya lau suke. An ba su izinin ganin Zarah na minti 5r. Haka suka yi tsaye gaban gadon suna mata kallon tausayi. Inna ta fara barin dakin ta dawo wajen ta zauna, tayi shiru hawaye na tsitaya, babu abinda za ta iya yi, komai Allah yayi, dai- dai ne. "Yan mintoci bayan fitowar su daga wajen Zarah, aka kawo ma su Bebin da aka ciro wa Nusaiba. Bebi ne katon gaske jajur da shi, sannan babu abinda ya bambata shi da Ameer. Illa girma daya fi shi. Kowa yasa masa albarka, suka mika wa Babansa. Ya zura masa ido kamar ya lashe shi so da kaunar Bebin suka kama zuciyar sa. Kwalla suka cika idanun sa,"Allah ka raya mi shi." Ya fadi a ransa.. A lokaci guda daran jiya ya fado masa, nan da nan ya mike ya ba Umma Bebi, ya fice da sauri ya sami wata kwana, ya hade kai da bango. Babu abinda ke yawo cikin ransa, sai maganganun daya cacca6awa Nusaiba, a idonsa yake ganin lokacin da ta miko masa rafar kudi, duk a tunanin take ganin halin da ta shiga. Wanda komai zai iya faruwa da ita. "Da mutuwa tayi da shi kenan, ta tafi ta bar ni da hakkinta a wuya na?" Ya fashe da kuka sosai, irin wanda bai ta6a yinsa a rayuwar sa ba. Ji yayi an kamo shi,"Malam Umar ne,"Haba Naseer, ka yi hkr mana, ka roki Allah ya ba su lafiya. Wannan koke-koken ai ba su da amfani. An san ka na cikin tashin hankali, amma jurewa za ka yi, ka zama namiji. Zo mu je, yanzu za mu tafi, don a samu a bizne jaririyar wajen Zarah. Yi hkr d'an gidan Inna." Ya goge masa fuska, ya riko hannun sa suka dawo. Yarinyar na lullube cikin zani, ya nuna wa Naseer ita, yayi jim, yana kallon ta, sannan ta dauke kai. Ya matsa kusa da Abba ya ce,"Ka zo da waya?" Ya ce,"Ga ta, ai na riga na gaya wa su Alhj, suna tafe." Ya ce,"To shi kenan, bari in kira Sageer." Ya kar6i waya, ya matsa gefe,ya kira duk wanda yake son kira, sannan ya maida wa Abba wayarsa, suka dauki shatan tasi ta maida su gida. Suna bada baya. Su Alh. Basheer na isowa. Abinka da asibitin Shika, sai suka rasa ina za su dosa, don haka ya kira wayar Naseer. Tana ta bugawa, amma da yake tana gida, babu mai dauka. Ya kira ta Abba, su kuma sun riga sun kusa gida, saboda haka Malam Umar yabasu lambar Inna, suka kira. Naseer ya fita ya nemo inda motar su tayi fakin. Yana isa wajen. Ummi ta fara kwalla. Yana neman tsugunnawa. Alhjn yayi sauri ya kamo shi,"Sannu Naseer ya fargaba? Ya ce,"Mun gode Allah." Ya ce,"Malam Balarabe ya ce ashe doguwar suma Zara tayi ko? Ya amsa da kai? Ya dan rungumo kafadar sa,"Ka yi hakuri kaji? Allah zai ba su lafiya." Ya gyada kai, ya dubi Ummi suka gaisa, sannan yayi masu jagora zuwa inda suke, suna tafe yana maida masu yadda abin ya faru. Bayan sun gaisa da su Umma. An jajanta wa juna, sai Alh.Basheer ya nemi ganin Likita. Abn ka ga mai kudi, nan da nan ya sami duk abubuwan daya bukata watau daki na musamman da likita shi ma na musamman. Kan ka ce kwabo, an hada Zarah da Nusaiba waje daya, an zuba masu komai na bukuta. Ummi na rike da Bebi, yana to son a zuba masa abinci a bakin sa. Da yake akwai kayayyakin Zarah, ruwan zafi kuma tana da zuma da dabino sbd tana yawan cin dabino, sai Inna ta kawo, duk Ummi ta ba shi, sannan ta dan kada zuma a ruwan dumi, ta cika masa ciki, nan da nan ya koma barci. Ganin hankali ya dan kwanta. Inna ta ce Naseer ya koma gida yayi wanka, daga nan ya kwaso wa Bevi kaya da ita Nusaiban. Yana fitowa su Sageer na shigowa shi da Fa'iza, dole ya sake komawa, suka gaida su Umma. Ya kawo masu Bebi suka gan shi. Wucewar 'yan mintoci 15 ya karbi mukullin motar Nusaiba, tunda ga Sageer zai tuka a maida ta gida. Sun yi fakin kofar gida, suka yi sallama suka tafi, ba tare da sun tsaya wani surutu ba, domin Naseer baya ma son yin magana. Yana shiga gida, ya tu6e kayan jikin sa, ya zaro sauran kudin da suka rage cikin rafar da Nusaiba ta ba shi. Ya zauna bakin gado ya zura masu ido, jim kadan ya sauke numfashi, ya aje su bisa filo. Ya wuce bayi ya sakarwa kan sa ruwa. Bayan yayi wanka, ya kimtsa ya kawo wayoyinsa da kudade ya zuba aljihu. Ya fito ya nufi dakin Nusaiba. Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi Gaban hoton ta ya tsaya ya k'are mata kalo ba tare da ya san me zuciyar sa ke sakawa ba. Wadirof ya bude, ya d'ebo riga da Zani kala 5r. Yayi tsaye yana tunanin a ina zai ga kayan Bebi, tunda bai ta6a siyowa ya ce mata ga shi ba? Abinda ya yanke shawara shine ya shiga kanti, ya siyo. Wata zuciya kuma ta ce masa "Kai dai dudduba." Yana gama tunanin sa, ya nufi akwatuna ya fara budewa, abn ya ba shi mamaki, domin setin nan kaf kayan Bebi ne ciki a mak'are. Yayi shiru duk al'ajabi ya ishe shi, ya nemo jaka ya debi kaya iya dibar sa, kayan shafe-shafe, su pampas da setin bahon wanka, wanda komai na bukatar wankan Bebi. Akwai shi a ciki. Ya loda kaya a but, ya sallami Abba ya koma asibiti. Yana shigowa da kaya niki-niki, ya iske Zarah ta farfado, sai faman kuka take yi, sbd jin abin daya faru da Nusaiba. Su Umma na ta bata hkr. Ganin Naseer ya shigo, dukkan su suka fita waje.Ya matsa wajen ta ya zauna gefen gadon, da sauri ta fado masa ta sake 6arkewa da kuka. Idanuwan sa suka cike da kwalla, ya kasa cewa uffan tsawon lokaci. Sannan ya dagota, ya share mata hawaye ya ce,"Ya isa haka. Ya jikin? "Yayi sauki. Ashe abinda ya faru kenan? Ya ce,"To yaya za'ayi? Allah ya ba ku lafiya." Kwalla suka sake zubo mata ta ce,"Amin.", Na ga Bebin mu kamar Ameer ne aka dawo mana da shi." Yayi dan murmushi,"Shi ne ma, domin shi ma sunan za'a maida masa." Ta ce,"Yayi dai-dai." Suka k'ura wa Nusaiba ido, a lkc guda kuma suka kalli juna ya ce,"Allah yasaa ita ma ta farfado. Lafiya, kamar yadda ki ka tashi." Ta ce,"Amin yayana." Ta wuce da kanta kirjin sa, tayi ajiyar zuciya, ya sumbaci tsakar kanta, sannan ya gaya mata su Sageer sun zo shi da Fa'iza. Suna gaishe su." Ta dago a hankali ya taimaka mata ta kwanta tana fadin,"Muna amsawa." Ta bi shi d kallo, ta ci gaba da cewa,"Na san ba ka ci komai ba yayana, ka hada Tea mana ka sha." Ya kada kai,"Ban jin yunwa Zarah." Ta ce,"Ai kai ba za ka ji ya ba, amma tana nan tana cin ka." Yayi dan murmushi ya ja ha6arta, ya ce,"Hankalina bai gama kwanciya bane Zarah, sai na ga farfadowar yarinyar nan." Ta dan lumshe ido, ta bude wani dadi ta ji ya ratsa, ta miko yatsun ta, ya rike ta.. Ta ce,"Insha Allahu lafiya lau za ta farfado. Kar ka ka zauna da yunwa yayanmu, za ta iya yi ma illa." Ya sumbaci, yatsun ya ce,"Shi kenan, zan sha yanzu." Umma tayi sallama, ya mike da sauri yana amsawa, ita ma maganar abincin tayi masa, sannan ta bude jakar kayan daya kawo, ta debo wa Yaro kaya, ta dauke shi suka fice. Anan ya hada Tea ya dawo bisa kujera gaban Zarah yana sha, suna hirar Nusaiba. Bayan sallar la'asar. Alh. Basheer ya ce shi zai koma. Ummi ma ta ce me za ta tsaya yi, tunda ga su Umma ga Inna? Haka suka wuce, duk ba su ga farfadowar Nusaiba ba, idan Allah ya kai rai gobe, za su dawo. Bebi kuwa na lkie da Zarah. Naseer ya tasa su yana ta fama kallon abin sa, son sa na k'ara kwarara jikin jinin sa da bargonsa suna kashe jijiyo har bisa fatar sa. Karfe 9n dare ya baro Shika. Zarah tare da Bebi ta kwana, ko ya motsa, ita ake mika wa ruwan dimi ta ba shi, duk da jikin ta babu kwari sosai. Shi kuwa Naseer kasa runtsawa yayi, saboda tsabar tunanin abubuwan daya aikata wa Nusaiba, wadanda a yau yake ganin suna so su zame masa da na sani. Lokacin sallar asubahi ya yi, ya tashi ya je yayi alwala, ya bada farali. Da kansa ya shiga kicin, ya shirya duk abubuwan da yake son tafiya da su asibiti. Yayi wanka, ya kimtsa. Karfe 7 saura kwata, ya dauki hanyar Shika. Karfe 8:30 Nusaiba ta farfado da surutai tare da sambatun da babu wanda yake fahintar me take fadi.Likita ya ce ba damuwa, za ta wartsake nan bada dadewa ba. Suna fa jin dadi, musamman Naseer da zuciyar sa ke cike da zullumi. Ko su Alh.Basheer da suka zo, sun yi farin ciki kwarai, anan suka iske su Malam Balarabe da Malam Umar. Shi yake gaya masu cewa Bebi sunan marigayi watau Iliyas ya ci. Wasa-wasa Nusaiba ta kai har dare bata gane kowa, sai sambatu. Likita dai sai kara basu hakuri yake yi, yana jadadda ma su za ta warware. Amma haka suka kwana da ita, ba barci. Surutai babu ma'ana. Abinda yafi basu tsoro, shine yadda harshen ta ya karye, tana magana kamar wacce ta sami matsalar shanyewar gefen jiki. Da safe kowa ya zo da kuzarin sa, turus! Yake yi, saboda abin akwai ban tausayi, ballatanta da idanuwan ta suka bud'e waras! Tana kallon kowa, amma bata sanin ko waye. Murna fa ta koma wa kowa ciki, domin al'amarin Nusaiba k'ara gaba yake yi, abin tamkar tabin hankali. Kwana 3 kenan. Da sassafe ta tashi da wani kuka mai tsuma zuciya da ban tausayi, babu abinda take kira, sai "Antina! Alhali ga Antin ta tana tallafe da ita. Ita ma kukan take yi, tana fadin,"Ga ni fa nan amarya, ba mutuwa na yi ba."Ta tsura mata ido zuru! Shi kan sa kallon mai ban tsoro ne, sbd idanuwan a juye suke, duk sun firfito waje. Zarah ta sake fadin,"Kin ganni? Ni ce amarya, ban mutu ba. Ki daina cewa za ki mike da gudu, kin ga (Operation) aka yi miki. Duba ki gani, kin ga Bebin mu? Ga Umma ga Inna. Yanzu yayan mu ma suna tafe. Ki na son ganin su ko? Ta girgiza kai, ta ce da karfi,"Antina ta mutu na ce! Wayyo Abba na, sun kashe Antina! Da gudu Zarah ta bar dakin, ta zube barandar waje, ta fasa kuka. Kwatsam! Sai ga su Ummi, tun daga nan suna jin ihun ta, tana kwala wa Abbanta kira. Ummi bata son lkcn da ta watsar da kayayyakin hannun ta ba, suka fada dakin. Su Umma na rirrike da ita. Alh.Basheer yayi azama ya rungumota,"Ga ni Nusaiba, ga ni, ki yi shiru." Amma kara fadi take,"Abba na ka zo sun kashe min Antina! Hankalin sa yayi mummunan tashi, ya dubi su Umma."Ina Doctor ne wai? Ta ce,"Sun zo har su 4. Nosis sun zuba magunguna cikin karin ruwar nan, sun mata allurai, har yanzu barci ya ki zuwa." Alh.Basheer yayi waje, ya nufi ofishin likitan daya dauka na musamman, cikin zafinsa ya shiga, a tsaye ya fara fadin. "Wai me ke faruwa ne Doctor? Ban gane condition din yarinya ta ba! Shi ma ya mike cikin sanyin murya ya ce,"Cool down Alhj, zauna." "No I can't sit Doctor! Kullum yarinya sai k'ara rikicewa take! Why? Wai ba anan ku ka yi mata tiyata ba ne? Ya ce,"Alhj babu wata maganar an ta6o mata wata jijiya. Infact, aikin ta bai shafi ko'ina a jikinta ba, sai inda Bebi yake. Ka zauna mu yi magana, Please! Da kyar ya zauna, shi ma Lkita ya zauna." Dama kai na ke jiran zuwan ka mu yi magana. Nusaiba ta fada cikin matsananciyar damuwa, wacce har ta sanya ta fizge-fizge, alhalin tana da ciki. Babbar matsalar ce ga mai ciki idan ta sami kan ta a irin wannan yanayin, domin ya kan kai a rasa su duka. Shine za ka ga mutan kauye da suka jahilci abin sai su ce bugun jinin ne, maimakon a hanzarta kawo ta asibiti, don daukan matakin gaggawa, sai a shiga hayaki da shafe-shafen turaren aljanu. Daga karshe ka ga an rasa uwa da Da. Abinda na ke so ka gane anan, damuwa babu abinda bata haifarwa, amma ina son ku natsu, za mu bicike da kyau, mu gano aininhin abinda ke damunta. A halin yanzun muna Expecting comma ta shiga, abinda muke magana kenan da sauran Doctor." Alhj fa bai yarda."Wannan ba comma bace, ta6in hankali ne, sbd haka idan ku yi bincike a kwakwalwarta, ko nawa ne zan kashe! Ya ce,"Wannan duk ba matsala, yanzu zan rubutu gwaje-gwaje da hotunan da za'ayi. Idan an rubuta kudaden, sai aje a biya." Rubuta min, in je a biya kudin." Yana zaune Likita ya rubuta duk binciken da za'ayo. Tare suka fito, ya hada shida Yaron da zai raka shi ofisoshin da za su rubuta kudaden. Al'amarin Nusaiba kuwa ta rikita kowa, kuka kawai suke yi. Shi kan sa Bebin kukan yake tsalawa, yana jin yunwa, amma ta hana su yi 'yan dabara a lika shi, ya sha nono. Naseer ya doso wajen, tun daga Nesa ya tsinkari muryar ta. Da gudun sa ya karaso, yana tambayar Zarah! "Me ya faru?, Murya na rawa ta ce,"Nusaiba ta rikice Kai tsaye ya shiga dakin, ya zube jakar da ke hannunsa, ya nufi gunta yana fadin,"Ya haka Umma? Duk suka dare, suka ba shi wuri, tana kyallo ido ta gan shi, ta zaburo tana mika masa hannu, "Abba na! Abba na, ina ta nemanka za su kashe ni? Bai san lkcn daya rungumota ba,"Menene? Iye? Ba ki san akwai ciwo a jikin ki ba? Allah da ikon sa, shiru tayi, tana ajiyar zuciya,"Kai na ke ta kira Abba na, ka ki zuwa, kai ma ba ka so na ne? Idanuwansa suka cika da kwalla. Kowa yayi waje yana share hawaye. Ya jima kafin ya ce,"Ai gani na zo, me aka yi? Wa ya sanya min ke kuka? Ta zura masa ido ta ce,"Antina suka kashe min, shine suka zo ni ma suka danne ni, za su kashe." An ce miki Antinki bata mutu ba, tsaya ki gan ta. Zarah! Ya kira ta. Ta shigo, ya jawo hannayensu ya hada,"Kin gan ta? Antinki ce. Ta fizge hannunta, ta saka ihu,"Ba ita bace! Allah ba ita bace,"Antina ta mutu Sabon shafinmu na face book zai fara aiki daga labarinmu na gaba,ku tallaffamana domin habakashi.... https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C7370123473 Akalla muna son Like daga mutum 20 kafin fara gudanar dashi Ya rufe bakinta ya ce,"Shi kenan na ce, shi kenan ba ita bace." Zarah ta yi sauri ta fice. Sannan tayi shiru. Ya dube ta ya ce,"Abinda ki ke yi, ba shi da kyau, ki na jin Bebin mu na kuka, kin ki bashi nono, me ki ke nufi? Ta ce,"Abba na ina naga Bebi kuma? Ga shi

Chapter 1 of 8