Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 8
ta miko min, ina bashi ya kama ya shiga tsotso yana ajiyar zuciya tanfar da ba'ayi ta fama dashi ya kama ya ki ba, Umma tana zaune tana sauraron abin da baba zai ce mata sai ya kalle ta ya ce dazu Junaidu ya yi min waya ya shaida min cewar Abdulhakam Alhajin tudu ya kira mish, ba Umma 93 ba hatta ni da ban san shi ba gabana faduwa yayi don ban yi zaton hakan ba sunan mahaifina mutumin da ban z0 duniya na sane shi ba sai dai tun daga ranar da aka bani labarinshi shi da mata rshi ban taba fashin yi musu addu'a ba. Umma ta daga ido ta kalli Baba ta ce ikon Allah, Abdul hakam ne? Sai kuma hawaye suka biyo bayan maganar tata suka yi ta gudu a fuskarta shar, shar,shar suka ki tsayuwa, Baba kuwa sai ya kawar da kanshi ya fita ya bar mu, ina gama bashi nono Umma ta ka rbe shi tasa a bayanta ta goya ta shiga hidimominta nima na gyara na kwanta wunin rannan kuwa babu abin da zuciyata ke yi in ban da tunanin mahaifana Abdulhakam da uwa kamar yanda su Umma suke kiranta. Satinmu biyu da haihuwa yaya Almu ya fara tasa Umma a gaba da maganar komawana dakina, ta ce ya dan kara hakuri muyi koda wata guda ne ya ce mata to, muna cika watan ya dawo ya ce mata Umma nazo ne kan alkawarinmu na komawar Rabi gida, Umma tayi murmushi ta ce ai kuma alkawari abin cikawa ne tayi maza ta mike ta nufi dakin Baba zuwa can sai gata ta dawo Tuskarta a daure, ta nemi wuri ta zauna ta kalli Yaya Almu ta ce mishi Alhaji ya ce bai hana ka 93 tafiya da matarka ba duk lokacin da ka shirya yin hakan, amma ya ce in gaya maka ita kadai zala dauka ban da Abdulhakam, gaba dayanmu daga ni bar yaya Almu tsura mata ido muka yi muna kallonta. Umma ta ci gaba da magana nayi kokarin ya yarda ku tafi in yayi wayo sai a dawo mishi dashi bai yarda ba, shiru yaya Almu yayi kamar ruwa ya cinye shi don haka maganar tafiyar dai ranar bata yiwu ba. Randa'muka cika wata biyu cif ranar ne kuma yaya Almu ya gama azumi sittin din da ya jera ranar kuwa a Legos yayi buda baki, ni na shirya mishi abin shan ruwa na kai mishi dakin da yake sauka bayan na tsala mishi kwalliyar da ko a ranar sunan ban yi irinta ba, sai da ya gama addu'o'in shi muka shafa kafin ya jefa dabinon da ya yi buda bakin dashi bakinshi duk abin da ya ci a lokacin dangin fruit ne sai da yaje yayi sallar Isha'i, ya dawo sannan ne ya soma cin abincin da na shirya mishi yana cin abincin ya daga ido yana kallona yanzu yaya zamu yi da maganar Baba Rabi? na ce kamar yaya? Ya ce to za ki yi ta zama a gida ne don renon yaro? Ai gara dai musan abin yi ko? Ni yanzu nazo mana da wata dabara zan rinka zuwa kawai ina yin kwana biyu anan in-je 94 gida in yi kwana biyu zan koma rabon kwana tsakaninki da Lailatu kin san ba zai yiwu inyi ta zaman zuba miki ido ba Rabi ba sai na tsaya yi miki dogon bayani ba tunda a yanzu babu maganar jan rai da wahalarwa a tsakaninmu. Na ce eh yaya Almu amma dai gaskiya irin wannan sarin ai zai yi wahala yau kana nan gobe kana can kuma a gabansu Umma da Baba suna kallonmu ma bai yi tsari ba, ka dai yi hakuri kawai ka dauka ni na zo wankan gida ne a gida kuma kana da matarka in ka samu lokaci kawai sai ka rinka zuwa duba mu. Ya sake kallona kafin ya ce min zan so mu fahimci juna ta yanda zamu taimaki kanmu mu duka ni da ke da yaron in kin yarda da hakan zan iya barinki har wata hudu nan gaba don ya samu yasha nono na tsawon watanni shida kafin in dauke ki mu tafi mu bar musu shi in kuwa baki yarda ba sai mu tafi yanzu mu barshi ai ba nono ke raya mutun ba, nayi maza na ce hu'un ba zan ya ba ya ce to shi kenan amma za ki kwana anan yau ko? Na ce ba zan iya ba hira kawai zan yi in tafi ya ce to jeki kawai ki bar hirar bana so na ce to na tashi nayi tafiyarta. Washe gari da safe na fito daga wanka kenan na gama shafa mai ina cikin sanya kayana sai 95 kawai Umma ta ce mun wai baba ya ce a tambaye ni in akwai abin da nake so ayi mun in fada don asahn nan zan koma dakina, na kalli Umma cikin natsuwa ace mata Umma da yaron? Ta yi mazata tsuke fuska ta ce mun babu yaro anan gidan za ki bar mishi shi tunda Lamido ya ce a bashi ke ku tafi naga kuma kema tun randa uwarki ta haife ki ta bar mishi ke shi ya rene ki ba nono ba, na yi maza na ce mata kiyi hakuri Umma saboda na gane ranta ya baci da maganar da nayi tana jin na bata hakurin kuma ta juya ta fita. Umma ce taja shirin komawar tawa har aka kai sati biyu saboda ta gane ina da damuwa game da barin yaron, duk da dai na 6oye don ba zai yiwuu Baba ko Umma su zartar da hukuncin da ba zan iya hakuri dashi ba ko da kuwa wane iri ne. Ana gobe zan koma Anti Rahma ta dawo daga Kaduna saboda ita ta jagoranci aikin gyaran wurina da aka yi ina jin ta tana baiwa Umman labarin irin yanda aka tsara wurin da yanda aka tsarawa yaro dakinshi Umma tayi murmushi ta ce shi Junaidun bai san ban da yaron ba ne a komawan har yake kashewa dakinshi kudi? Anti Rahma ta zaro ido tana kallon Umma sai dai ta kasa ce mata komai. 96 A haka na kona gida washe gari Umma karama ta maidani don da yaya Almu yazo daukarmu sai Ummana ta ce mishi ya tafi da Baba Talatu da Rabi'atu ni kuwa Umma karama ce zata dawo dani hakan kuwa aka yi tayi waya ta ce mata tazo ta maida ni dakina. Na koma gida na samu Lailatu cikin wani irin hali bata yi zaton dawowana ba watakila ta yiwa yaya Almu maganar raba mana gidane don ta fahimtar dashi cewar bata son zama dani, Lailatu bata dauki maganar dawowa na da sauki ba watakila tafi gwanmace wa da wata sabuwar kishiyar aka kawo mata kwana biyun farko da nayi a gidan nayi sune cikin halin zazzabi mai tsanani a dalilin ciwon nonon da ya rufan mun shi da kanshi yaya Almun duk zumudin shi na son in dawo da zalamar da ya nuna a sarari ya hakura ya saurara min saboda ganin halin da nake ciki ammna hakan bai sa Lailatu ta shigo dakina ta tambaye ni yaya jiki ba, gaba daya hidimar gidan kuma ta tsame hannunta wai ba girkinta ba ne, duk da hakan da tayi ban canza ba daga niyyar da na dawo da ita don kuwa Umma ta gaya min cewar ya zama dole in samarwa yaya Almu kwanciyar hankalin da yake bukata a cikin gidanshi na ce mata to ai wancan karon ma ba akan son raina aka 97 yi wancan zaman ba ta ce eh amma ai ke macece gidan ki kuma tazo kin san yanda zaki yi kdyi gyaran da ya dace, gaba daya laifin abin da ya farun a kaina Umma ta dora shi shima yaya Almu ta ce abin da ya yi duka ba wani laifi ba ne hakan da tayi ya sanya ni na yi ta yi mata kuka. kwana uku nayi ina fama da zazzabi na samu sauki don haka washe garin rana ta hudu ranar da zai sake dawowa dakina kenan sai na wastsake na fito nayi shirin karbar mijina a yau tun safe nake ta shirya irin nau'o'in abincin da zan shirya mishi gaba daya littatafan girkina na dauko ina ta dubawa don in ga abin da ya dace in shirya mishi. Ina zaune a tsakar gida ina jira a gama min gyaran kicin din mai aikin da Lailatu ta kawo ce mai yi min aikin Azumi don na riga na yanke shawarar yin mu'amalla da kowa, sai ga Rabi'atu ta nufo ni da gudu zata zo wurina cikin murna da dariyarta kan ta iso sai kawai naga Lailatu ta biyo ta da sauri ta cafe ta tana cewa ja'ira mara zuciya ni duk tsiyar mutum ba zai lashe min ke ina kallonshi ban ce mata komai ba, sai da na gama komai bayan cin abincin dare nayi kwalliya sosai wurin yaya Almu zan tafi sai na shiga dakin Lailatu nasa hannu na dauki Rabi'atu dake bacci na sabata a kafadata zan fita da ita ta kalle ni ta ce 98 ina kuma za ki kaita? Na ce zan je in lashe ta tawa ce ai tunda agabanki akan idonki Babanta ya bani ita daga yau na karbe ta na wuce naje na kwantar da ita a dakin da aka shirya don yaro wanda ba'a dawo dashi ba. Babu fitinar da Lailatu bata yi akan karbar yarinyar da nayi ba har yaji ta yi ta ce wai ba za ta dawo ba sai an mayar mata da 'yarta Ummana ma ta ce in mayar mata da 'yarta tunda ta dage kan hakan na ce mata sai dai in ba za ta dawo ba tayi ta zama da kuwa naga zata tilasta ni mayarwa Lailatu da ita nayi maza na gayawa Baba, shi kuwa ya ce ai ba kwace mata ita nayi ba shi bai taba ganin in da aka kwacewa uwa danta ba musamman ma da yake ba barin gidan akayi da ita ba don haka ta ishe mu dukanmu suka gaji da rike ta suka dawo da ita, aka zauna a haka, ni kuwa na dauki matakin duk in da zani da Rabi'a nake tafiya har Ummarar da muka tafi da Anti Rahma da ita na tafi ban barta a gida ba. Gaba daya al'amuran gidana na karbe su babu wani abin da nake sanyawa Lailatu ido akanshi in tana sha'aninta da mijin ta babu ruwana in kuma hidimar gidana ta ce ba zata yi ba sai kawai in sa ta yi ba tare da na saurareta ba, da kuwa na ji mijihta ya ce min ciki ne da ita sai kawai nasa aka 99 nemo mana mai girki na danka mata hidimar abincin gidan amma ban da na yaya Almu wannan ni da kaina nake yi mishi ban kuma damu da cewar ga girkina ba ga nata ana cikin haka nima na samu kaina cikin matsanancin halin zazzabi ga wasu kurarrajin bakin da nake fama da su nayi kamar 1n gayawa yaya Almu sai kuma kawai na ce bari dai in hakura tunda yana zumudin cikin da Lailatu ke dashi wacce har a tsakar gida take gayawa masu aiki cewar wannan karon namiji itama zata haifa ban tanka ba kallon su kawai nake yi musamman ma da yake ba ni take wa zancen ba. Rannan ina zaune a gida ina tare da yaya Almu abin karyawa nake shirya mishi sai ga yaya Junaidu yana sallama yayi maza ya mike ya karbe shi suka shigo tare nayi mishi sannu da zuwa na kuma zuba mishi nashi abin karyawar shima yana cikin karyawan ne ya kalle ni ya ce min Mustapha ya gaya miki cewar zan yi aure ko Adawiyyah? Da hannu biyu na dafe kirjina saboda tsananin kaduwar da nayi na ce aure yaya Junaidu? Me Anti Rahma tayi? Nagga kuma tana iyakacin kokarinta, ya y1 maza ya daure fuska ya ce kina nufin sai mace ta gajiya ne ake kara aure? Da aka ce mu auri mata bibiyu ko uku-uku ko hurhudu 100 kina nufin in matan sun gajiya ne zamu yi hakan? Ba haka ba ne in mun gamsu da adalcinmu ne aka bamu ikon yin hakan in kuma muka ga ba zamu iya ba sai aka ce to mu zauna da guda daya, nayi ajiyar zuciya mai karfi na ce haka ne to Allah ya. sanya alheri amma Anti Rahma fa? Ya ce na bari Umma zata je gidan tayi magana da ita ni kam zaman Jimami na koma na rasa me zanyi? Murna zanyi kawuna zai yi aure ko kuwa bakin ciki zanyi za'ayiwa Anti Rahma kishiya. Shi da kanshi yaya Junaidu ya gane jikina yayi sanyi da zancen auren nashi ya kalle ni ya yi murmushi ya ce Adawiyya kenan wato ku dai mata zumuncinku karfi ne dashi in ba haka ba ni da Rahma wanene ya fi kusa da ke? nayi murmushi na sunkuyar da kaina kasa ina yi mishi bayanin ba wai bana murna ba ne tashin hankali ne ba shi da dadi ya ce haka ne to ki kwantar da hankalinki babu wata wacce zata zo ta dagawa Rahma hankalinta in dai ba ita ce ta nemi ta daga wa wani ba, zan yi iyakar kokarina don in ga sun zauna lafiya, na ji dadin kalaman nashi na ce to Allah ya sanya alheri ya ce amin, na sake wani murmushin na ee lalle za muyi biki kenan ga bukin gidan ma ya zo yau bai fi saura kwana goma ba ga kuma wannan yaushe za ayı? Ya sake 101 kallona ya ce ai a gidan za'a bani auren baba ne zai kara min nayi maza na ce kawu a gida kuma? Ya ce eh mana Adawiyya ga kyawawan yanmata a gida yaushe zanje ina neman a waje? Na yi murmushi na ce ai fa anyi kyawawan yanmata a gidan ga kwalliya sai dai akwai wata da ta fisu kyau kawu iyaka dai bata isa auren bane kawai ya ce wacece? Na ce mishi takwarar Umma Amarya ya sake kallona ya ce yanzu nan Maryam bata isa aure ba? Na ce bata isa ba kawu sha shida ne shekarunta ya çe haka ne. Washe gari muka nufi Legos ni da yaya Almu wurin Anti Rahma naje don in dan tausata anyi sa'a bata dauki auren da wani tsanani ba tunda ya gaya mata cewar baba ne ya ce zai ba shi ba shi ne ya ce yana so ba, sabanin yanda ni kuma ya ce min shi ya ce yana so lokacin ne na tuna lokacin auren Lailatu nima cewa aka yi min ba yaya Almun ne yake so ba ba şhi kawai akayi. Daukar auren yaya Junaidu da sauki da Anti Rahma tayi sai yasa al'amura suka yi matukar yin dadi ta kowane 6angare mu'amalla mai dadi ake yi. Shirin biki sosai akayi gaba dayan mu rufe gidanmu muka yi a Kaduna muka nufi gida cikin shirin buki sosai. 102 Baba zai sake bukin wasu 'ya'yan buki na uku kenan tun bayan aurar damu da yayi sai dai tun daga wancan loka cin bai sake bukin yara masu yawa ba, kamar na wannan karon a yanzu zai yi auren 'yanmata bakwai ne samari kuma biyar in aka hada da yaya Junaidu mai yin kari shida zai ba da daya kuma a waje. Mun isa gida duk da ba wannan ne zuwan Lailatu gidan na farko ba nayi matukar kokarina wajen ganin na maida ita 'yar gida a gidan komai zanyi zan neme ta muyi tare ko da yake ita bata yarda ta zauna a inda nake wai ita 'yar dakin Umma karama ce don haka can take zuwa tana na mikawa, da daddare na dauki Rabi'atu naje falon Baba don in kai mishi ita sai na kira Lailatu muka tafi tare muka samu Umma amarya yaya Junaidu da kuma yaya Almu a ciki baba yana zaune a kasa yayin da Abdulhakam yake kan cinyarshi yayi matukar yin girma sai rigima yake yi mishi yana ta kokarin cire mishi madubin idonshi muka gaishe shi ni da Lailatu na kuma matsa kusa da shi na tura Rabi'atu na ce mata je ki ki gaida Baba ya mika mata hannu ya dauke ta yana cewa ke mai gashin doki wannan gashin dai ba naki ba ne kari uwarki tayi miki don kiyi barazana na ce a'a Baba nata ne ai gashi ne da ita don ma ina yankewa, 103 ban san Ummana ta shigo ba sai ji nayi tana cewa uh ka ji ashana sau daya nefa ta yanke matà gashin amma ka ji ta ce wai tana yankewa gaba daya aka kwashe da dariya. Umma ta dauki Abdulhakam ta gama ba shi kunnunshi ta ajiye a kasa ya ci gaba da wasanninshi yayin da baba yake tattanbayan Lailatu wasu abubuwa don dai ya nuna mata itama yarshi ce ni kuwa ina kusa da Umma amarya wata magana nake yi mata sai dai ba a ji muna cikın zancen sai naji baba yana cewa uwata ce dai ban san dalili ba kullum ka ganta a rame dubi yanda ta koma dakin gwanin kyau amma yau dube ta, wai maimakon Ummanta fadi wata magana ko kuma taja bakin ta tayi shiru sai kawai naji ta ce mishi Adawiyyah ai kishi ne da ita mai tsanani kishi kuwa hana mutum kyan gani yake yi sai kullum ayi ta rama in ba haka ba me ke damunta ba ga 'yar uwarta nan ba gwanin sha'awa da ita tayi mul-mul. Jawabin na Umma ya firgita ni a gaban kowa zata ce wai kishi ne yake hana ni yin kiba ban san lokacin da na sona yi mata kuka ba ina cewa babu bata kishi ba nc baba, yayi maza ya ce yi shiru uwata ba kishi ba ne amma menene damuwarki? Na ce mishi kurarrajin baki sun dame ni bana iya 104 cin abinci da yunwa nake wuni da na gaji da hakan nema na ce gara kawai in rinka yin niyya ina yin azumi har kafin su warke. Umma Amarya ta ce to an taba yin haka kullum ana azumi? Ba za a dauki matakin daya dace ba'? Yaya Almu ya ce ai Rabi taurin kai ne da ita umma gata da musu nayi mata magana tun farkon abin ta ce ba haka ba ne kurarraji ne kawa kuma Sun warke, ta ce amma ai kai lalurar da ta kawo kurarrajin aka yi ba ganewan da na yi tonawa kaina asiri kawai na yi a gaban kowa da kowa maimakon in kare kaina daga zargin kishi da Ummana ta yi min sai kawai na sulale na fita daga wurin na bar Baba yana yiwa yaya Almu fada har yana yi mishi barazanar sake rike ni har sai na haihu na yaye kafin ya bar ni in koma dakina tunda dai shi ba zai iya taimakona kan lalurata ba. Ni kam dakin Umma Amarya naje nayi kwanciyata saboda nasan wurin Ummana a cike yake da jama'a, Umma Amarya ta shigo ta same ni yanzu yau da kike yi Azumin da me kika yi buda baki? Na gaya mata ta kama yi min fada ke yarinya ce karama ba za ki taimaki kanki ba tunda kin san ga yanda kike in dai kowanc ciki sai anyi wadannan kurarrajin ai ya zama dole ke da 105 mijinki ku dauki matakin da ya dace, shiru nayi ban ce mata komai ba. Muna nan dakin muna hirarmu ni da Umma Amarya sai ga yaya Almu ya shigo, na daga ido na kalli agogo sha daya da rabi ne na dare, ya nemi wuri ya zauna cikin natsuwa ya kalli Umime ya ce mata in ranki ba zai baci ba Umma zan hakura da zama da Lailatu in yaso na natsa sai sai in kara wani auren don bana sha'awar zama da mace guda daya. A hankali Umman ta tambaye shi me tayi maka? Ya ce mata yanzun nan a daki, Junaidu ne ya banbare hannunta daga jikina yana bata hakuri, Umma ta ce a'a me yayi zafi haka? ya ce ta ce wai muna munafurtarta n1 da Rabi bamu gaya mata Rabin tana ciki ba sai anan a cikin mutane akaci mata fuska, na ce mata nima yanzu ne na tabbatar don a gida da na tambaye ta musu tayi min, amma bata yarda ba ta tada rigima wai sai na sake ta da na tashi zan fita kuma ta rike ni in ban da anan gidan nanne Umma ba zan yarda da hakan ba ta ce mishi to kayi hakuri amma ai babu wani abin bacin rai itama ba tuntuni ake cewa tana da nata Cikin ba wa yayi tashin hankali? Duk da kiran da Umma Amarya ta yiwa Lailatu tayi mata maganganu na kwantar da hankali ta kuma yiwa 106 yaya Almu fada a gabanta bai hanata barin gidan ba da sassafe ta tafi gidansu, don haka bata nan aka yi sakun lalle aka shiga hidimar bikin, ni kam ko wurin Ummana bana zuwa balle in ji ko ta san abin da ake ciki a sashin Umma Amarya nake zaune wacce duk da hidimar Jama'ar da take fama dasu bai hanata tarairayata ba sai wani ji dani take yi tana kuma nuna min cewar in yi iyakacin kokarina wajen ganin mijina ya zauna lafiya a gidanshi, gashi Allah ya baku haihuwar nan da aka dade ana nema. Ranar Asabar wajen karfe goma sha biyun rana aka soma hidimar daurin aure abin mamaki wai har da mai sunan Umma Amarya a cikin yanmatan da aka daura wa auren kuma wai ita aka baiwa yaya Junaidu. A wurin liyafar cin abincin dare da baba ya saba shiryawa 'yan uwa da abokan arziki a duk lokacin da yayi irin wannan hidimar ina zaune tare da yaya Almu yayin da Rabi'atu ke kan cinyata na waiwaya na kalli yaya Almun bayan na gama kallon yaya Junaidu da yar yarinyar da ya aura sai da nayi tsaki kafin na ce mishi gaskiya ban san yaya Junaidu budurwar zuciya ce dashi ba sai yau, don Allah dubi yar yarinyar da ya ce yana so kuma wai Baba ya bashi ita, ita kuma da 107 yake sokuwa ce dubi yanda take ta faman murmushi ko me yake gaya mata? Oho. Ita bata san tsobho ta aura ba. Yaya Almu yayi murmushi ya ce ba za ki gane abin da yayin ba komai ba ne sai nima na ce Baba ya bani wacce naga tana tasowa yanzu, nayi maza na galla mishi harara na ce ai sai kuyi tayi ku rinka auren sa'o'in 'ya'yan cikinku yayi daniya ya ce ba komai ba ne Rabi an riga an yardar mana yin hakan sai dai kuma kin san ko yar sila zan aura son da nake yi miki dabanne da wanda zan yiwa kowacce da haka na danji sanyi cikin zuciyata, To an tashi biki gaba daya amare da angwaye sun nufi gidajensu, don haka baki ma watsewa suke tayi, ina zaune tare da Baba a falonshi hira muke yi ni dashi da yaya Almu Abdulhakam yana bacci a gefenshi, hakan ya kara tabbatar min da maganar da Ummana ta gaya min cewar duk inda yake bai rabuwa dashi duk matar da take tare dashi kuma ita ce mai kula mishi dashi ko da kuwa wacece. Na kalli Baba cikin ladabi na ce mishi Baba ashe dama zaka iya ba da kari? Yayi murmushi ya ce zan bayar mana uwata ba hudu aka ce ayi ba? Na ce haka ne, yaya Almu ya kwashe abin da na 108 fada akan yaya junaidu da amaryarshi ya fada mishi baba yayi murmushi ya ce bai mata tsufa bba uwata, Junaidu ai yaro ne, yaya Almu ya ce ai1 nima nan gaba gida zan zo a kara min Baba cikin yankananan masu tasowa, nayi maza na ce a'a baba shi yaya Almu ai dama mata biyu ya ce min zai yi to ga riga kuma ya yi sai dai kawai ayi mana addu'ar zaman lafiya baba da yaya Almuu suka kyalkyale da dariya, baba ya kalli yaya Almu ya ce to ka ji Lamido uwata ta ce ya isheka haka. Mun koma gida bayan an kammala biki iyayen Lailatu kuma sun dawo da ita saboda ganewan da suka yi Yaya Amu dai bai shirya binta ba, sai dai ta dawo dinne kawai amma bata shirya a zauna lafiya da ita ba, tunda ta gane ciki ne dani ta tsire neman fitina mai tsanani bata zauna lafiya da mijinta ba balle kuma dani hatta su Baba Talatu da Azumi da ita da kanta ta kawo ta ta ce wai itama munafuka ce ta koma wurina. Kullum burinta tayi danbe dani ne ban san me take nufi ba watakila gani take tunda ina da lalura zata iya dukana, rannan na fito daga dakina zan shiga kicin ita kuma daga kicin din take zata nufi nata wurin, ban yi aune ba sai kawai naji ta bangaje ni, ni kuma sai nayi wuf na sharara mata 109 mari mai tsananin karti nan take ta juyo ta rarumame ni da karfi, abin da ya zama danbe mai tsanani a tsakaninmu daga Baba Talatu har Azumi baba abin da ba su yi ba don su raba mu Lailatu bata yarda ba kokarin ta kawai shi ne nata samu damar da ta buge ni a ciki ko kuma ta kai ni kasa, shi ne kuma abin da bata samu ikon yi ba saboda shigowan mutumin da ke kulawa yaya Almu da tsabtar gida abin da ya shafi share-share da gyaran furanni. Washe garin faruwar abin su Umma suka iso saboda kiran da Yaya Almu ya yi musu, Umma na ce tazo ita da Hajiya Hauwa sai Abdulhakam da tazo dashi. Gaba dayansu ni suka dorawa laifi a cewar wai da Lailatu ta bangaje ni sai in rabu da ita in yaso in yaya Almu ya dawo in gaya mishi tunda nasan bani kadai ba ce, Yaya Almu ya nuna musuu bacin rai mai yawa kan abin da nayin suma kumna suka taya shi jin haushina, Umma kuma ta sani na bashi hakuri, kafin ta kalle shi ta ce mishi to ko Adawiyyah zata je gida ne a'a Umma ba zai yiwu ace duk lokacin da take da ciki sai taje gida ba ta Zuana Hajiya Hauwa ta ce gaskiya ne Lamido to Allah ya raba su lafiya ya ce mata amin. 110 Bayan tafiyarsu na yi fama da rashin lafiya mai tsanani ga ciwon jiki ga kumburin da kafafuwana suka yi tayi amma ban gaya wa yaya Almu ba saboda duk da ba wani dadi muke yi ni dashi ba a dalilin fushin da yake yi dani dana lura da kyau kuma sai na gane rashin dadin da suke yi da Lailatu ya fi haka yawa don ya dage kan cewar kisan kai take so tayi mishi a gida in ban da haka me zai sa tayi danbe da mace mai ciki wata bakwai? Ko so kike itama tayi barinshi kamar yanda kika ce kinyi naki? don

Chapter 7 of 8