Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 8
gidan Yaya Almu na farko kenan, da sauri yaya Almun ya fito yana yi mishi sannu da zuwa bai tanka mishi ba, ya kalle ni ya ce min nan nace miki ki zauna umarnin da na baki kenan, ya juya ya fita ya tafi. Yaya A lmu ya shigo yana min sannu da zuwa tare da tambayata inda na tafi? Ban tanka mishi ba na dai gane kawai hankula sun tashi saboda daga shi har Lailatun sun shiga cikin hankalinsu, banga 57 su Tanbai ba ban kuma tambayi inda suke ba sai wata sabuwar mai aikin. Dare na yi yaya Almu ya shigo don dama yana ta nuna zumudi da farin cikinshi kan dawowana, na ce mishi ba na dawo zama ba ne balle ayi rabon kwana dani, nazo sauraron hukuncin da Baba zai zartar ne a tsakaninmu. Fafur na ki sauraron komai daga Yaya Almu balle kuma wata Lailatu na ma daina ganin Rabi'atu in sa hannu in dauke ta balle ayi min wulakanci girki kuwa in nayi ni da Baba Talatu nake zubawa in bar saura anan mai so ya diba. Sati guda cif da dawowana sai ga Umma Amarya tazo da sassafe ina zaune a kasa a gabanta bayan na gama shirya mata abin karyawa shima yaya Almu yazo ya gaishe ta ya kuma ki fita don ya san Baba ne ya turo ta, sai ta ce min Alhaji ne ya turo ni in zo kiyi min bayani kan abin da ke faruwa, bayani na dalla-dalla na yiwa Umma tun daga farkon zuwan Lailatu gidan har kawo ranar da na bar gidan ban rage komai ba tun daga girkin wata takwas da ya sani nayi babu sannu babu madalla har kawo marina da tayi a gabanshi da hukuncin da yayi na sanya Lailatu ta rama dukan da nayi mata kawo kan cewar da ya yi na yi asirin da na raba shi da ita don kar ta sake 58 haihuwa, babu abin da ban gaya mata ba har da maganganunshi na cewar bakin ciki zai kashe ni. Shiru tayi tamfar wacce ruwa ya cinyeta bata ce komai ba sai shi Yaya Almu ne da yaga shirun yayi yawa ya ce amma Umma.....tayı maza ta katse shi ta ce ba wurinka ya aiko ni ba ka bari sai ya ce yana so ya ji naka bayanin sai kayi wa wanda ya aiko maka tana fa [6/20, 9:22 PM] Hafsat C Sodangi: Yanda Baba ya tura sunan Abdulhakam katagun ya bar wa Baban tudu zabin sunan da za'a sanyawa jariri haka shima yaya Almu ya tura radin sunan katagun sai dai shi yaya Junaidu ya bar wa zabin sunan da za'a sanyawa jariran don haka ranar suna da sassafe bayan anyi kiran suna a can sai yayi waya ya fadi sunan yaran Jabir da Jibrin, muka yi sunan ma a Kaduna suma su Umma suka yi nasu sunan a gida anyi suna da 114 kwana biyar Umma karama tafi tana barin gidan kuwa na tsukewa yaya Almu fuska ya tasani a gaba yana son sanin dalili na ce mishi to dama muna magana da juna ne yaya Almu? Ai gaba kake yi dani ba sai muci gaba ba kawai ya ce amma bai wuce ba? Na ce da aka yi me ya wuce? Ina halin rashin lafiya baka ji tausayina ba kana fushi dani sai na samu lafiyar ka ce ya wuce? Ai muyi tayi kawai, ya kalle ni ya ce baki da hankali Rabi nayi maza na ce mishi da sannu ai zanyi. Muna cikin wannan zaman ni dashi sai kuma Lailatu ta fito da wata ka'ida wai bata yarda da shigowan da yake yi wurina ba tunda sbanci da girki zaman jego nake yi ya ce mata haka ake yi Lailatu ke da kika yi naki jegon haka tayi miki rikicin yayi tsanani a tsakaninsu har takai karar shi gidansu aka musu shari'a ban san me aka ce mishi ba ni dai naga ya shigo dakina yazo ya zauna ya ce min Rabi taimake ni ki karbi girkinki yau ban ce mishi don me ba? Ban kuma ce mishi ba zanyi ba don ba zai yiwu ace ta ko ina ba zai ji yanda yake so ba don haka sai kawai na ce mishi to, yayi matukar jin dadin hakan da nayi yayi min addu'a ya kuma tashi ya fita ya shiga wurin Lailatu. 115 Duk da sati uku ne kawai da haihuwata Baba Talatu tana gama abincin gidan dana sata tayi sai na fito ina sanye da kayan sanyi na suturta jikina na shiga kicin na shirya mishi abincin shi da lokacin kwanciya yayi kuwa shigowa yayi ya sallami Marka da Baba Talatu dake taya ni kwana da yaran ya ce musu su tafi wurinsu sai da safe shi zai taya ni duba yara suna cikin gadajensu muma muna namu, na kalli yaya Almu na ce mishi kai yaya Almu jego fa nake yi, ya ce nafi kowa sani tunda ga yantagwaye biyu can ina kallo wadanda Ubangiji ya azurtani dasu amma hakan ba zai hana ni in yi abin da naga zan iya ba, jego mai dadi nayi ran girkina ina manne jikin mijina a haka muke kwana in yara sun motsa kan in tashi ya riga ni zai yi musu komai sai dai ya miko min su ina daga kwance in ba su nono in sunsha sun koshi ya maida su wurin kwanciyar su, sannan ya dawo mu kwanta maimakon in takura sai kuma naga ni gata ma tayi min in bani ce da girki ba kuwa bana jiran sai yazo ganinsu ana gama musu wanka da gyara in na basu nono suka koshi sai in ce akai mishi su nima in kintsa in yi kwanciyata in yi ta baccina maid a di, kafin in yi wata guda daga ni har su munyi gwanin sha'awa. 116 Rannan na karbi girki, rannan kuwa kwanan mu talatin da bakwai ne, kwalliya sosai nayi wa mijina da zamu kwanta kuma na sanya wata shu'umar rigar barci da ban taba amfani da ita ba, ni ina ki ka samu irin rigunan baccinnan ne Rabi? Na dan kalle shi kadan kafin na maida hankalina kan yaron da nake baiwa nono don yaya Almu ya matsa in sa su suyi bacci na ce mishi tun rannan fa na gaya maka na ce maka set din akwati biyu Umma tayi min na rigunan bacci kawai, ya mika hannu yana wasa da igiyoyin rigar tare da fadin Tiga ce mai kyau Rabi na ce mishi eh. Kwalliya nayi don in burge yaya Almu in kuma faranta mishi rai amma ba don wani abu ba sai kuma ya ki yarda da tsayawa kan wasannin da muka saba yi, ya ce fafur shi yayi kokari kwanaki talatin da bakwai din da akayi ai tun ban fi sati biyu ba yake ganina ina sallah, to ina laifinshi? Da dai lura kin yarda na zai kawo bacin rai mai yawa sai kawai na sallama iyaka dai nayi tunanin matakin da zan dauka wanda zan taimaki kaina dashi. Randa muka yi arba'in ranar na tafi Legos ni dasu da Rabi'atu tare da baba Marka da Baba Talatu muka je na kaiwa Baba su ya gansu Baba yayi murna, murna kuwa mai1 tsanani ya kalleni 117 ya ce ikon Allah yau ga uwata da haihuwa har da ta yantagwaye, ni kam murmushi kawai nayi Umma karama co a wurinshi itama ina aka saka damu tayi, nayi kwana daya anan daya kuwa a gidan yaya junaidu zamanshi da matanshi gwanin sha'awa komai zasu yi tare suke yi shi kuma yana tsakaninsu, anti Rahma kuma ta yaba mun da adalcin yaya Junaidu, daga Legos gida muka wuce in da muka samu Ummana da Umma amarya muka fara bakunta mai dadi kwananmu uku da zwa sai ga Yaya Almu yazo wai zuwa yayi mu tafi ni kuwa na tubure na ce ai ba haka muka yi da shi ba, Umma cewa nayi zanyi kwana biyu a Legos in zo nan in yi bakwai in tafi katagun in yi biyar sai kuma kawai ko bakwai dinfarko ba ayi ba ya biyo mu ya ce bakuntar ta isa haka? Umma ta ce haka kuka yi Babangida? ya ce ch amma ai ta kwashe mutanen gidan ta tafi dasu don haka na fara bakuntar ta ishe ni haka tazo kawai mu tafi gida, Umma ta ce a'a ba zai yiwu ba sai taje katagun ta kaiwa su Alhajin tudu yara sun gansu don haka washegari muka nufi katagun har da yaya Aimu muka je mukayi kwana biyu muka wucc gida. Watana shida da haihuwa su sabir sunata zamansu har suna nema suy1 rarrafe sunyi 118 matukar yin girma gasu da lafiya gasu kullum kamanninsu sai karuwa yake yi yaya Almu sai ji dasu yake yi in suna wurinshi barin komai yake yi yayi hidimarsu, na shiga dakinshi na same shi tare dasu na ce mishi yaya ko zan je asibitin ne? Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce me kuma ya faru? Na ce mishi yauma al'ada nake yi kuma ba ka ga yanda take zuba ba kamar ba kwana bakwai ba ne kawai da daukewar wancan ya ce min to har na kama hannun Rabi'atu zamu tafi sai naji ya ce min tsaya Rabi, bari in zo mu tafi tare na gaji da wannan al'adar taki tunda muka fito daga asibitin yaya Almu bai ce min komai ba ga dukkan alamu dai ranshi a bace yake ban san mne Likitan ya gaya mishi ba don ya kira shi sun kebe can cikin Zuciyata cewa nake yi Allah dai yasa ba wani abu ya gaya mishi ba. Muna shiga gida naji ya kira Marka da Baba Talatu ya basu yara ya ce su kula dasu, shi kuwa ya biyo ni daki ya nemi wuri ya zauna ya daga ido ya kalle ni ya'ce min Rabi ai kin dade kina barin yin nesa dani ko? Ban iya amsa mishi tambayar ba saboda mamakin da ta bani kan in yi tunanin amsar da zan bashi sai naji ya ce za ki iya yin hakan a yanzu dama kina da gidan da kika sai wa kanki don hakan to ki koma ciki ki zauna ba zan 119 zo inda kike ba, na kalle shi na ce me ya faru? Ya ce babu komai ganinki ne kawai bana so na kuma baki minti talatin ne ki fita ki bani wuri, na ce ba ma sai an kai haka ba na mike na dauki jakata na fita na tsaya ina kiran Baba Talatu ta kawo min yara ya biyo ni da sauri ya ce bar su a inda ki ka same su. Tsananin mamaki da kaduwa ne ya same ni don haka ban je inda ya ce din ba gida na wuce kai tsaye don nasan Umma tana can na gama mayar mata da bayanin yanda aka yi duka mamaki ya kamata ta ce me kika yi mishi haka? Na ce nima ban sani ba sai tà ce to bari yazo muj tunda na kira shi, sai dare yaya Almu ya iso na kuma yi sa'a yazo da yaran har da Rabi'atu, yana shigowa ya ganni ya ce me ya kawo ki gaban Umma Rabi? Me yasa in wulakancin ki ya motsa ba kya barin abin ya tsaya tsakanina dake sai kinzo gabanta don kiyi sana din 6acin ranta? Ba gidanki na ce ki tafi ba? Umma ta ce haba nifa nasan haka kawai ba za ka yi irin wannan hukuncin ba, ina kuka yaya Almu ya kalle ni cikin takaicin ya ce ban san me zance miki ba Umma iyaka dai kin san mas'alar data samu Rabi ta yawan al'ada har tana ta zirga- zirgar asibiti Umma ta yi maza ta ce mishi eh, ya 120 ce to allurar da take yi ta hutun haihuwa da tsarin iyali ne ta jawo mata abinda Likita ya gaya min kenan. Umma tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta yana ganin haka ya mike zai fita wai zai je gaida Umma amarya Umma ta ce mishi debi su Jabir ka kai mata, ya ce to yana barin dakin Umma ta Soma zagıina wani irin zagin da bata taba yi min ba har tana kirana butulu, haihuwar da muka nema kamar yaya? Muka hadiyi bakin cikin da bai misaltuwa akanta ita ce a yau kika je neman tsari da ita saboda ke butulu ce maimakon ki zauna kiyi tayi wa Ubangiji godiya kan ni'imar da yayi mana, to ni ba su ishen ba jeki ki haifo su a jaka Adawiyyah ki kawo mun su, ba Lamido kike so kiyiwa tsiya ba, ni da dan 'uwana kike so kiyiwa don mune bamu da wata hanya ta yaduwar zuriyarmu sai ta dalilinki, Lamido ai in ya kara aure zai samu ya'ya a tare da matar, yanzu ma kuma kina tare da wata na kuma ji karama tana cewa ciki ne da ita, har yaya Almu ya dawo Umma bata hakura ta bar fadan da take yi min ba cikin sanyin jiki ya nemi wuri ya zauna ya shiga bata hakuri har yana ce mata wai ba butulci ne yasa nayi hakan ba wahalar kurarrajin bakin dake 121 hana min sukuni ne dalili amma nan gaba 71 dauki matakin da ya kamata. Da aka natsa yaya Almu ya ce in tashi mu tafi gida sai na ce mishi a'a ya barni kawai ya yi tafiyarshi ai tunda ya ce in fita in bar mishi gida ba zan sake komawa wannan gidan ba, ya soma yi min magana kiyi hakuri Rabi raina ne ya 6aci kema kin san.....Umma tayi maza ta katse shi ta ce kar ka baiwa Adawiyyah hakuri Babangida, kyaleta tayi abin da taga ya yi mata daidai ba dai burinta ta bata min rai ta sanya ni bakin ciki ba? To ta yi ta ji dadi ni kuma na yafe mata, na yafe miki Adawiyya na yafe miki kiyi min duk abin da kike so ba zan ji zafin ki ba, zanyi ta yafe miki tana maganar tana kuka, hankalin yaya Almu yayi matukar tashi ya shiga bata hakuri yana fadin laifinane Umma da na zartar da irin wannan hukuncin na dauka zata bi umarnin da na bata nata koma wurinta ban san zata kawo maganar gabanku ba amma kuyi hakuri, ke Rabi jeki ki dauko su Jibrin sai kizo mu tafi, Umma tayi maza ta ce a'a abar wa Maryam su bata da kowa a dakinta zasu yi mata dadi. Zubewa nayi a kasa ina kuka a gaban Umma bata kula ba, yaya Almu ya soma bata hakuri cikin sanyin jiki don shima bai son rabuwa da 122 yaran ta ce mishi kul ka ce zaka yi min wata magana ai na bar muku su sune ina jiran ku samu wani kar ayi ta barinku cikin kewa tunda kuwa basu dame ta ba to taje. Haka muka fito daga gidan daga ni sai yaya Almu itama Rabin Umma ta ce a barta a gidan ni kam nayi kuka har na gaji a gida kuwa ga kewar Rabi'a da yara ga ciwon nono gashi yaya Almu ya tasa ni a gaba duk wanda ya tambayi yana sai ya gaya mishi abin da nayi wanda yasa Umma ta kwace su duka wai har da yaya Junaidu ya gaywa shi kuma tunda ya gaya mishi ya daina maganna dani ko gaishe shi nake yi a dake yake amsawa wai bai taba ganin mai rashin hankali irina ba gaba daya na tsargu babu abin da nake so irin in sake jin Rurarrajin baki sun sake feso min shiru babu su babu dalilin su, hankalina yakai matuka wajen tashi kar dai na daina haihuwar kenan? Kullum tambayar da nake yiwa kaina kenan a duk lokacin da na tuna abin da nayin da irin wahalolin da muka sha a baya da bakin ciki da gorin haihuwar da akayi tayi sai inga to in ban da butulcin da Umma ta ce ina dashi me zai sa in je ieman hutun haihuwa? Ina yin irin wannan tunanin sai in yi maza inyi ta istigifari ina neman gafarar Ubangiji, yaya Almu kuwa kusan kullum 123 sai ya gaya min cewar shi fa ya riga ya saba da mu'amalla da yara tunda ni da Lailatu mun sake zama juyoyi to shi gaskiya zai nemi auren badurwa mai sha biyar ko sha shida wacce kafin ta gaji da haihuwar zata haifar mishi ko guda goma, in ce yana kyau haka din gara ka himmatu, ana cikin wannan halin rannan ina kwance kan gadona da rana na ji wani motsi da yayi min kamaa da motsin da a cikina zumbur nayi na mike zaune na kasa kunne ko zan sake jin wani motsin ban j1 ba, shiru ban sake jin komai ba na yi ta duba bakina ko zanga wurin da kurji ke shirin fitowa babu wata alama, har na hakura. Washegari dai da sassafe na nemi 1Zinin yaya Almü na zuwa asibiti ba tare da ya nemi sanin abin da zani inyi ba ya bar ni na tafi ina zaune a gaban Likita yana yi min dariyar yanda aka yi wai na haihu har da 'yan tagwayc amma na zauna da ciki yayi watanni ban gane ba, cikin zuciyata na ce Albamdulillahi na karbo magungunana na kama hanya na dawo gida ko Umma ban gaya wa abin da nake ciki ba, jan bakina nayi na yi shinu, gashi kuma nayi sa'a wannan cikin yasha banban da saura, cin abincina nake yi bani da wata mas'ala sai nayi kyau nayi kiba nayi mulmul gwanin sha'awa cikin kuma ya 6ace a jikina kamar babu shi, an dauki lokaci mai 124 tsa wo yaya Almu bai gane ba shima don anyi dace ne yayi motsina shi.kan ya ankara kuwa sai kawai yaga na haihu sai dai wannan karon ma da namiji aka samu sai aka sanya mishi Muhammad Bello wato sunan Baba kenan tun daga wannan lokacin ban sake wani tunani na neman hutun haihuwa ba tuni ma na daina sha'awarshi na kuma koma ganin wautar mata masu yi saboda irin illolin da ya haifarwa. Abdulhakam bai gama cika sheka ru takwas ba a duniya sai da na haifar mishi kanne biyar gaba dayansu kuma maza don haka a yanzu yaya Almu ya'ya bakwai ne cif dashi mace daya Rabi'atu sai maza shida dan karaminsu kuwa shi ne takwaran yaya Junaidu. A wannan lokacin tausayin Lailatu nake ji tun daga haihuwar Rabi'atu ko bari bata sake ba, tayi karyar cikin har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido ga Maryam mai auren kwanannan wai har ta haifi 'ya'ya uku a gidan yaya Junaidu. Anti Rahma shida amma ita shiru, duk da mun yi kwanaki sun kai hudu ni da ita ba wani kula juna muke yi ba saboda in suna 'yartsama da yaya Almu sai ta hada har dani da na ji tana yi mishi maganar zuwa asibiti bai kula ba wai shi ya gaji da biyan kudin wankin cikin da babu am fani, shiga daki nayi na 125 dauko kudi nazo na bata na ce mata jeki Asibitin, ta ce a'a tana dasu na ce karbi dai nawan ai ba ke ya kamata ki biya kudin asibiti ba, ta je ta dawo kuma na tambaye ta abin da suka ce, bata boye min ba don haka da kaina naje na samu Baba na gaya mishi mas'alar da Lailatu ke ciki, bayanin da nayi mishin yasa ya sanya yaya Junaidu ya shiryawa Lailatu tafiya kasar Cairo don ganin Likita. Bayan dawowan Lailatu Umma karama tazo gidan ban san me ta ce mata ba na dai ji ta kawai tana cewa a'a Umma ni na riga na gaji da wannan fitinannen zaman, a yanzu nafi bukatar zaman lafiya akan komai, musamman ma da yake duk mugun abin su da ake gaya min nima dai ita mun yiwa juna rashin kirki, tunda ita kam sha yanzu ne magani yanzu, to uwarta kam in na ce ta taba yi min wani abu ba alheri ba na yi mata karya, don haka a yanzu zan koma amfani da zahirin abin da idona ya gani maimakon jita-jita da tsofaffin labarai na abin da aka yi shekara da shekaru, ina jin umma karama ta kama salati nayi maza nayi wucewa ta, cikin zuciyata dai murna nayi da Lailatu ta gane fitintunun dasu Umma karama ke sanyata ba komai zasu haddasa mata ba illa rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali. 126 Tun daga wannan lokacin na dauki matakai masu yawa don ganin mun zauna lafiya da Lailatu, don haka in zan sai wa kaina abu sai itama in saya mata, in kuwa naji tana neman wani abu wurin yaya Almu bai yi mata ba sai in yi mata da kuma na lura tana kokarin gyara mu'amallarta da yara maimakon da da bata shiga harkarssu yanzu har tana sauraron maganarsu sai nima na rinka dorata kan al'amuransu, ko wani abu nasu ne ya taso sai in ce yaya Almu ya sata tayi, shima kuwa yayi matukar jin dadin hakan, nan da nan sai zaman mu ya dawo gwanin sha'awa rannan na shirya zan tafi makarantar islamiya ta asabar da Lahadi da nake zuwa sai na ce mata Lailatu ko zan karbo miki form ne mu rinka zuwa makaranta tare muna jin wa'azi? Kinga ba wani wahala ne da ita ba sau biyu ne kawai a sati? Yaya Almu yayi maza ya ce min a'a Lailatu ai tun tana 'yar karama taji wa'azinta wuce su nayi na tafi don nasan zolayarta yake so yayi da zan dawo sai nazo mata da form din ta cike muka soma zuwa tare. Nan daa nan ni da ita muka zama tanfar 'yan uwa komai zamu yi tare muke yi, in wani abin gida ne ya taso sai in shawarce ta mati yawanCin lokaci kuma na kan yi amfani da ra'ayinta ne in bar nawa a wannan lokacinne na fahimcI Lailatu mutunivar 127 kirki ce, mafi yawancin abubuwan da tayi ta yi a baya sata aka rinka yi ba halinta ba ne ita da kanta Lailatu taji dadin halinta da ta canza saboda yanda matsayinta ya karu wurin yaya Almu ni da kaina ban san yana yi mata irin son da yake yi mata ba sai a wannan lokacin da ta yarda da zaman lafiya, nasha jin shi yana cewa yana girmamata da ganin darajarta tare da jin tausayinta saboda ita ce uwar Rabi'atu 'yar da yake so kamar me? Sannan gashi bayan ita bata sake ba don haka a yanzu shagwaba take yi mishi irin yanda yanda taso nima kuma bana sanya ido kan abin da ya shafe ta da mijinta, tunda tana bani girmana ta kuma sa hannu biyu ta rungumi al'amarin yara. ** Shekaru goma bayan wannan lokacin na 1sa gida da yamma ni kadai amsa kiran da Umma tayi min nayi. Gidan cike yake da jama'a babu masaka tsinke, duk kuma wani wanda yake cikin gidan in ma dai da ne da baba ya rike ko kuma jika don haka taro ne na yan uwa, ma'ana babu wani bare a ciki. Sashin Umma Amarya na fara zuwa, Jibrin na fara gani ya fito da sauri zai karbi jakar dake hannuna, na kalle shi nayi murmushi na ce mishi 128 ga dukkan alamu aiki kuke yi saboda irin gumin da nake gani a tare da kai don haka jcka kayi aikinka ni zan iya kai jakata cikin daki tunda ai kaga makale take a hannuna ya taya ni murmushin da nake yi ya wuce ya tafi, na samu Umma a zaune a nemi wuri na zauna na gaishe ta na ce mata yaya jiki ta ce da sauki ai na ji sauki sosai na ce babu inda yake miki ciwo kenan? Ta kalle ni cikin natsuwa ta ce anya ana yin haka? Kayi irin wadannan shekarun da muka yi sannan ace an zauna babu abin da yake yin ciwo? An dai gode Allah tunda komai kana iyawa, na ce haka ne umma sai da muka danyi hira kafin na mike na nufi wurin Umma karama na gaishe ta sannan naje wurin Ummana, tana ganina ta daure fuska ke in banda na kira ki in ce ko da ba za ki zo ba ne? Na yi shiru ban ce mata komai ba ta kama yi min fada, Lailatu dake wurin ta kalle ta cikin murmushi ta ce mata da kuma tahowa don kanta tayi Umma da kinyi mata fada kince tayi rashin kunya gaba daya aka kwashe da dariya Umma ta yi murmushi ta ce to shi kenan na bar fadan tunda yar uwarki ta tare miki to amma ai wannan sha'ani ba biki bane hidima ce ta addini ai kya zo ayi ta dake, ni dai ban ce mata komai ba. Anti Rahma ta shigo wacce ita da Lailatu' ne a tsaye 129 kan hidimar tunda aka fara ta sunyi kusan sati guda a gida suna shirye-shiryen zuwan ranar sun sauka Umma yanzu an tafi dauko su nan ba da dadewa ba za su iso Umma ta kama murmushi tana share hawayen dake zuba a idonta tare da fadin babu Abdulhakam da uwa sai ni da Alhaji mune muke gunan musu, nan da nan aka shiga yi musu addu'a ita kuma ana bata hakuri. Wajcn karfe takwas da Rabi na dare suka iso kai tsaye babban falon karbar biki aka zarce an riga an shirya komai don haka ba'a dauki wani lokaci mai tsawo ba aka soma gabatar da al'amura bayan an gabatar da nau'o'in abinci iri-iri ga jama'a. A hankali na shigo wurin daga can baya na tsaya ina kallon duk abin da ake yi Abdulhakam wanda ake yin abin dominshi yana zaune tsakanin baba da yaya Junaidu tanfar wani babba alhalin shekaru goma sha bakwai ne kacal da shi, kullum kamanninshi da baba kara bayyana suke yi abin da kc sa wa mutane da yawa suke zaton wai ko karamin danshi ne kamar kullum yauma anko suka yi dai dai yau ankon nasu ya dan banbanta a dalilin shi Abdulhakam yana sanye da alkyabba da kuma rawanin da aka nada mishi 130 Baba na samu yana magana kamar bayar da labari yana kuma maganar ne cikin murmushi alamar dai a Cikin farin ciki yake. Ita kuwa ai hakurinta ba mai yawa ba ne uwarta ta fita hakuri, a zuciyata na ce a'a yau kuma me na yiwa baba yake kirana mara hakuri bayan na saba jin shi yane yabona akan hakurin? Da na kasa kunne da kyau sai na ji shi yana cewa, lokacin da ta rasa haihuwar nan ai nema tayi ta bijirewa Lamido na ce mata uwata aure daban haihuwa kuma daban ko babu haihuwa ana zaman aure ta ce a'a ita in bar ta kawai ta yi nesa da shi ya gara zama ya ce to a wancan lokacin nayi ta min addu'o'i da alkawura masu yawa saboda ina son auren nasu, na kuma san rashin-haihuwar ita ce babbar barazanar da auren yake fuskanta a cikin addu'o'i da alkawuran da na

Chapter 4 of 8