Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
yi har da wanda nayi yi dalilin taruwarmu anan yau na roki Allah ya baiwa uwata haihuwar da namiji da wasu mazan masu yawa bayanshi in ya bata da namijin to ni kuma ya bani rai da lafiyar da zan yi tarbiyar shi ta yanda zai zamo makarancin Alkur'ani wannan shi ne dalilin da ya sa da na ji tana da ciki sai na roketa da ta haihu mijinta ya nemi ta koma dakinta ba zai viwu in hanata ba sai nasa hannu na karbe jaririn duk da kankantarshi don nayi 131 alkawari akanshi, to gashi nan a yau kun shaida alkawarin ya cika, sannan ita uwata bayan shi ta haifi wasu mazan har guda b1yar ina ganin ma har yanzu bata da ya mace, ya dan juya da sauri yana sauraron abin da yaya Junaidu yake gaya mishi sannan ya juya cikin murmushi yana cewa au to, ashe kun ji wai daga bayan nan ta haifi Maryam cikin zuciyata na ce tafdijan wato ma Baba mancewa da ita yake yi, yanzu dai ga Junaidu nan zai gaya muku yanda tafiyar tamu ta kasance. Yaya Junaidu yana mikewa sai ya soma godiya ga Ubangiji ya yabe shi kan alhairorinsh ya gabatar da salati ga Manzon Rahma (S.A.W ya yi wa Alkur'ani kirari, ya fadi darajojinshi da daraicjin makarantunshi a ranar alkiyama da sakamakon wadanda suka tarbiyantar da yayansu akan karanta shı, da ya gama wannan sai ya shiga bayar da labarin gwagwarmayar da Abdulhakam ya yi a kokarinshi na yin haddar Alkur'ani mai girma da yand. suka tsaida shawarar shigar da shi cikin gasar karatun Alkur'ani don a kara zaburar dashi da ya zo karshe sai ya ce to tun a shekara bara mai alfarma sarkin Borno ya nada mishi rawanin zama goni a lokacin da ya lashe musabukar da ya shiga ta izifi sittin inda ya samu damar wakiltar kasa a musabukar duniya da za'ayi 132 a birnin riyard ta kasar Su'udiya, to gamu a yau mun dawo ina kuma farin cikin shaida muku cewar shi ne yazo na uku, gaba daya dakin ya dauki kabbara mai karfi da aka natsa sai ya ce to kamar yanda aka saba a dukkan gasar da muke zuwa akan tuho da kyaututtuka to a wannan ma haka ne, an bashi dama ta yin karatu a jami'ar Madina an bashi kudi da littatafai to 1littatafai dama kullum shi ke amfani dasu kudi kuwa akan raba su ne a tsakanın malamanshi to wannan ma hakan za'ayi don haka a yanzu sai mu kara natsuwa don mu saurari karatun Alkur'ani mai girma daga bakin goni Abdulhakam Mustapha. Abdulhakam ya mike cikin natsuwa dama kuma mai natsuwa ne bai da hayaniya gashi kama da kamun kai sai dai kuma fuskarshi bata rabuwa da fara'a cikin murya mai cike da natsuwa ga amo yana kuma karanto ayoyin kusa da karshe na cikin surarui Ma'ida, da ya gama sai ya koma ya zauna ya bar jama'a suna ta share hawaye, yaya Almu ya kalle ni a hankali ya ce min Allah ya yi mishi baiwa da murya ta karatun Alkur'ani, a hankali nima na ce mishi haka ne yaya, ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min gashi dai namu ne ni dake mu muka haife shi, to amma kin san ba renon mu ba ne bamu muka tarbiyantar dashi bai 133 ba mu muka karantar da shi ba, Baba da matansh guda uku ne suka yiwannan aikin mu namu ya'yan mun kwashe su duka mun kaisu karatun boko, na kalle shi cikin mumushi na ce mishi a bamu makara ba yaya ya yi maza ya ce to taimake ni rabina mu sake samun wani gonin kamarshi na ce mishi to. Da muka shirya ni da yaya Almu zamu tafi sai na kamo hannun Maryam dina falon baba muka shiga shi da Abdulhakam muka samu suna cin tuwo da hannu a kwano daya tsayar mishi da yarinyar nayi a gabanshi ni kuma na durkusa a gefe na ce mishi baba gata nan na kawo maka ka ganta da kyau, Umma Amarya ce don nan gaba kar ka sake mancewa da ita baba ya zuba mata ido yana kallonta cikin murmushi zuwa can sai ya ce min na ganta da kyau uwata ba zan sake mancewa da ita ba duk inda na ganta kuma zan shaideta tunda ma gashi ta yi sa'a irin idanuwan Abdulhakam dina ne a tare da ita, ni da yayaa Almu muka yi murmushi na fito naje na yi wa Umma amarya da Umma karama sallama sannan na nufi wurn Ummana da zamu yi bankwana da ita sai na ce mata Umma yi mun nasiha, ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min banı da wata nasiha da zanyi miki illa ta bin mijin ki rike shi gam da 134 [6/20, 9:22 PM] Hafsat C Sodangi: yayi yawa ya ce amma Umma.....tayı maza ta katse shi ta ce ba wurinka ya aiko ni ba ka bari sai ya ce yana so ya ji naka bayanin sai kayi wa wanda ya aiko maka tana fadin hakan kuma sai ta mike tayi tafiyarta. Da yamma na isa legos saboda Baba ya kira mu gidan a cike yake su yaya Zubairu su Yaya Kabiru dukan su suna nan sun zo gaba dayansu kowa fada yake yi min kan abin da nayi. A falon Baba kowa yana nan har da Ummana da Umma karama da Umma Amarya gasu yaya Zubairu duk an hallara, Baba ya ce kai Kabiru na kira ku ne anan dukanku don ku zo ku shaida abin da ke faruwa ko ya faru tsakanin Lamido da uwata cikin ku dukanku babu wanda ban yiwa shari'a tsakaninshi da iyalinshi ba, hakan bai damen ba saboda zo mu zauna zo mu saba, amma bayanin da Maryam tazo min dashi dazu ya banbanta da naku don haka na ce kuzo ku taya ni ji ke uwata kiji tsoron yin karya don ba za ta amfana miki komai ba, ki fadi gaskiya na ce mishi 59 to yanda na rattabawa Umma Amarya komai haka nan nayi bayan1 sai ma da na ga Umma karama a zaune na shaidawa Baba cewar duk sati biyu take zuwa gidan tunda Lailatu tazo bata kuma taba shiga dakina ta zauna ba wani lokaci ma fitanta kawai nake gani nan da nan jikin Umma ya dauki rawa ta kama kame-kame tana fadin wai ai ita Rabi'atu take zuwa gani, Baba bai kula ta ba wurin Yaya Almu ya juya ya tambaye shi anyi wadannan abubuwa ko ba ayi su ba? Yaya Almu ya sunkuyar da kai ya ce anyi su Baba, amma akwai dalilai, Baba ya yi maza ya ce to ko zaka gaya min dalilin dasa kasa uwata tayi wata takwas tana girki ita ka dai bayan ga abokiyar zamanta? Ya soma kame-kamen bayani ya sake tambayarshi da ta mare ta a gabanka ka hanta ramawa wane hukunci ka yi mata? Baba ya sake juyowa wurina ya ce min ke uwata don me ba ki taba gaya wa Zuwairah abubuwan dake faruwa ba? Na sunkuyar da kaina na ce mishi naje zan gaya mata ta ce min kar in koyi kai karar mijina in zama matar rufin asiri, Baba ya yi shiru dakin ma ya yi shiru, zuwa can sai ya ce daga yau na sanya Maryam da Junaidu su zama wakilai akan al'amarinki duk abin da ya dame ki ki gaya musu, na ce mishi to Baba. 60 Baba ya sake kallon su yaya Kabiru ya ce musu a yau na taraku ne anan don in shaida muku cewar randa duk aka wayi gari bana duniya to dukanku na bar wa amanar uwata ba wani mutum daya ba saboda ni da Baba ya yi gamsuwar da ya bar min amanaar Zuwaira ni kadai bayanshi rayuwa tasa na barta ta wahala balle Lamido da ya iya wahalar da uwata akan idona da na uwarshi, lokaci mai tsawo Baba ya dauka yana yin magana kafin ya ce, ke uwata laifin da kika yi na zartar wa kanki da hukunci da kike yi shi ne yasa ba zan yi komai kan duk wani abin da akayi miki ba, ina kuma so in kara jaddada miki cewar ko bayan raina ban yarda kisa kafa ki fita daga gidan Lamido ba don haka ki koma dakinki ki zauna na ce mishi to, ke kuma karama ba zan ce miki komai ba kije kiyi duk abin da kika ga yayi miki daidai. Mun fito zamu tafi yaya Junaidu ya kira ni nayi maza naje wurinshi sai ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min kar ki rudu da abin da Baba ya yiwa Mustapha a cikin mutane ki dauki hakan tamfar wata dama a wurinki da za ki rinka yi, mishi abin da ki ka ga dama ina fatan dai kina sane da cewar hakkukuwanshi da suke kanki basu sauya ba, sannan duk da bayanan da ki ka yi nina 61 yarda da cewar babu wani abin da Mustapha zai yi da nufin ya cuce ki don haka kiyi hankali da kanki ya wuce ya tafi ya bar ni a tsaye cikin tunani. Kalaman Yaya Junaidu sun kashe min jiki sai dai kuma inda mas'alar take shine a yanzu ba na son ganin Yaya Almu a kusa dani ko maganarshi naji sai in rinka jin gabana yana faduwa, babu lokacin da na kan samu natsuwa irin lokacin da na san ba ya gari bisa wannan dalili sai nafi sha'awar da a bar ni in koma wurina in yi zamana ni kadai in yaso su bar auren ace yana nan bai mutu ba don kuwa ni kaina ban taba sha'awar mutuwar auren namu ba don bana yiwa kaina sha'awar zawara. A wannan dawowar da muka yi babu abin da bai yi ba don mu daidiata mu zauna lafiya naki yarda bana shiga komai na hidimar gidan sabuwar 'yar aikin da suka kawo ba na sa ta ba na hana ta tsakanina da ita ina kwana ne kawai ina gajiya? Kayan da nayi amfani da su nawa nan take nake gyara su in adana na ma daina shiga kicin din da yake na hadakan a wanda yake cikin falona nake aiki na ba na kuma yin girkin tare da kowa, ina zaune cikin falona, Ice-Cream din da nayi nake sha, yaya Almu ya shigo ya zauna yana yi mun magana, Rabi'atu ta rarrafo ta shigo cikin falon tazo ta dafa jikina ta mike ta tsaya tana kallona da 62 sauraron inyi mata wasannin da muka saba, don kawai in bata mishi rai na kwalawa Baba Talatu kira ta shigo na ce mata dauke min wannan yarinyar ki bai wa wancan matar ita ta mika ta dakinsu, Baba Talatu tayi maz ata fice daga dakin tayi tafiyarta ba tare da tayi abin da na ce din ba, shima yayan ficewa yayi ya bar min dakin saboda yazo iya wuya da abin da nayin, sai bayan fitarshi ne nasa hannu na sureta muka shige can ciki, ko zuwa wurina yayi ranar girkina zai min wata magana sai in gaya mishi in raba ka da mai haihuwa zai mun wata magana sai in gaya mishi in raba ka da mai haihuwa don ka zauna tare dani da bana haihuwa to ai kai kuma sai kawai ka fita hanyata me zaka yi dani? Duk wani abin da na rinka yi mishi a wannan lokacin shanyewa ya rinka yi tanfar dai ba shi ne yaya Almun da na sani ba, illa iyaka dai gaba daya shima ya kame kanshi ya fita harkata. Ina kwance a dakina ranar Talata da safe bayan na gama wanke kurarrajin bakina da garin ararrabi da aka bani shawarar anfani dashi, ji nake tanfar in kurma ihu saboda tsananin zugin da bakina ke yi, Baba Talatu ta shigo ta same ni, yaya dai uwardakina? Na kalle ta cikin nutsuwa na ce mata bakina ya dame ni Baba ga kada 63 gwarzo yau ma ya sake fito min ko ruwa bata iya sha, ta kalle ni cikin kulawa da tausayawa sannu uwardakina ai kece kina fama da ciwo amma kin ki yarda ki gayawa maigidan an taba yin haka ace kana zaman mutum amma ba za ka gaya mishi damuwarka ba. Ina kwance anan wurin ina fama da kaina saboda matsanancin zazzabin da ya kama ni ina cikin tunanin abin yi sai ga Yaya Almu ya shigo cikin kwalliya sosai nan da nan kunshin turarenshi ya gauraye ko'ina ina shirin mu gama gaisawa in nemi izininshi don zuwa ganin Likita kan mas'alolin da suke damuna sai kawai naji ya ce min zan yi tafiya zuwa London da Lailatu zan akai ta ayi mata wankin ciki saboda yawan barin da take yi a dan tsakanin nan ina daga kwancen nace mishi to sai kun dawo, Allah ya kiyaye hanya, ya juya bayan ya ce amin, itama Lailatu ta shigo ta sha kwalliya ita da Rabi'atu sunyi matukar yin kyau suma kamshin suke yi mai dadi na mike muka y1 sallama nayi musu rakiya har zuwa jikin mota sai da suka tafi sannan na shigo gida, ina hawa kan gadona na soma kuka na fara gajiya da al'amuran yaya Almu, komai kankantar abin da yayi min a yanzu sai in ji kirjina yana ta 64 ciwo in ji kamar zan sa hannu in dauko zuciyata sbaoda tsananin zafin da take yi min, Lailatu da ta haihu watanni takwas da suka wuce ita ce wai an tafi da ita London don yi mata wankin ciki saboda tana yawan yin baci alhalin ni tun zuwan Lailatu gidan ya hanani zuwa ko'ina, hatta bikin da aka yi a Katagun bai bar ni naje ba duk da a gidanmu ne sai kawai ya tasa Lailatu a gaba suka yi tafiyarsu ya ce wai ta riga ni tambayarshi zuwa bikin kuma zata kai musu Rabi'atu su ganta, na ce haka ne ni kuma bani da abin kaiwa a gani sai kun dawo. Jikina yayi tsananin zafi saboda tsananin bacin rai ga kukan da nayi tayi don haka sai na kwana cikin matsanancin halin da sai da Baba Talatu ta taya ni kwana, gari na wayewa ta yiwa Baba wayya ta shaida mishi halin da nake ciki, ba a dauki wani lokaci mai tsawo da yawa ba sai ga Yaya Junaidu ya iso yana ganin halin da nake ciki ya tasa ni a gaba sai Legos kai tsaye gid aya kai ni gaban Baba, ya zuba min ido yana kallôna wane irin lalacewa kika yi haka uwata? Gaba daya kin tsangwami kanki kin hana kanki sakat kin ki ki saki ranki kiyi kyan gani, maganganun da Baba ya Soma yi min yasa na kama kuka ina rokon shi ya barni in zauna a gida na gaji da zama da yaya Almu yana nema ya haddasa min ciwon zuciya, 65 tsawon lokaci yana rarrashina kafin na hakura na daina kukan da nake yi. Washe ga rin zuwana Legos Ummana ta iso saboda kiran da Baba ya yi mata a dakinta ta same ni a kwance nayi kuka har idanuwana sun kumbura, Umma ta zuba min ido tana kallona cikin natsuwa da tausayawa me ke damunki haka Adawiyyah? na ce mata ban sani ba Umma illa iyaka dai kirjina yana min ciwo zuciyata ji nake yi tanfar in dauko ta saboda tsananinz afin da take yi min ga kada gwarzon dake damuna ta ce to tashi muje in kai ki asibiti ga Junaidu yazo zamu tafi tare nace mata to. Ina zaunc gaban Likita ina amsa tambayoyin da Likita ke yi min, sai Umma ta ka rbe tambayar ta hanyar cewa tana da mas'ala ne Dakta, gwaje- gwajen da aka yi mata a baya sun nuna tana da mas'alar kankantar mahaifa da yawa wanda suka ce ba zai bari ta haihu ba, Likita ya sake kallona kafin ya ce to amma a sakamakon wannan gwajin ai ya nuna ciki ne da ita, j1 na nayi tanfar ina yawo kan gajimare saboda rudewa, Umma kuwa cewa tayi a kira mata yaron da suka zo tare yana nan a waje, nan da nan yaya Junaidu ya shigo hankalinshi a tashe saboda yayi zaton wani abu ne mai tsanani ya faru. 66 Zauna ka taya ni jin wata magana Junaidu, ya yi maz aya zauna yana kallonta cikin sanyin jiki ya tambaye ta me ya faru Umma? Umma ta kalli Likita ta ce mishi Dakta me ka ce yana damun Adawiyyah? Likita yayi murmushi ya ce shekara nawa ne da auren nata ne Hajiya? Har ki ke so ki debe tsammani ta ce mishi bakwai har da wasu watanni, yaya Junaidu ya gyara zama ya ce mishi menene Dakta? Likita ya kara kallon takardun da aka kawo gabanshi ya ce, wannan normal abu ne yake gare ta, yaya Junaidu yayi wani motsi mai karfi kafin ya ce yi mata scarning Dakta don mu kara tabbatarwa yayi maza ya ce to shi kenan. Ina kwance kan gadon, Likita gaba daya hankalin Umma da yaya Junaidu har da nima yake kan allon computer da Likita ke dubawa, bayan ya shafa min wani ruwa mai dan sanyi yana kuma bin marata da dan wani mulmulallen abu yana goyawa nan da nan allon ya shiga baiyanar da abin da ake son gani gashi nan ai har ya zama mutum maganar Likita kenan yaya Junaidu ya ce tsarki ya tabbata ga Ubangiji, ya shiga yin tasbihr yayin da Umma ke ta faman kuka, ni kam a kwance nake zuciyata sai faman bugawa take yi jl nake tanfar a mafarki nake wai ciki ne dani abin da na riga na debe tsammani kowa ma ya hakura 67 cikin zuciyata na ce Allah na gode maka, Ubangiji kasa abin da nake ganin na motsin mutum a cikin cikina ya tabbata gaskiya ne ba mafarki nake ba, ciki ne gashi watanni kusan biyar ba ya motsi ne mai karfi a dalilin Rarancin kuzarin da ke gare shi bata cin abinci bata kula da kanta ta rasa abubuwa masu yawa, don haka shima ya rasa Rarfi ijikin Umma yana rawa ta ce yanzu meye abin yi Dr.? Ya ce zamu dan sa mata drip don ya rage mata yunwa kafin mu dauki matakin da ya dace. Ina kwance kan gadon Likita ana yi min karin ruwa a sabon dakin da aka kaini bayan tafiyar yaya Junaidu gida har lokacin Umma dake zaune a gefe na bata iya cewa komai ba in ban da kukan da take yi tsawon lokaci muna nan a haka har bacci mai karti ya dauke ni, farkawa kawai nayi daga baccin na samu Baba a tsaye a kaina tare da Likitan da ya duba nin, 1tama Umma tana tsaye a gefenshi, kin tashi uwata? Na ce eh Baba na yunkura don in tashi in gaishe shi yayı maza ya maida ni da hannunshi koma ki kwanta ki huta ki samu natsuwa, in Allah ya yarda Allah zai kawo mana karshen damuwarmu, ban yi magana ba saboda sai na ji ina jin nauyin amsawa, ya sake kallon Likitan ya ce mishi tunda ta farka a sake yin scarning din nan da nan Likita ya bi umarnin 68 da aka ba shi. Dr ya ce gashi nan yallabai, mutunne ka ganshi in kana son sanin mace ne ko namiji ma zamu iya dubawa, baba yayi maza ya ce a'a ba abin da nazo gani kenan ba mun gode Allah shine mafificin mai baiwa shine wanda ba a debe tsammani daga samun alherinshi, Umma ta yi ajiyar zuciya mai karfi ta ce haka ne, ya kara Juyawa wurinta ya ce iko sai Allah, wa yaga mun Zuwairah rike da dan da uwata ta haifar mata? Umma tayi murmushi a karo na farko tun bayan kukan da tayi, ta yi ta ce a'a menene da ban sauran ya'yan da nayi ta dauka fa? Yayi murmushi ya ce uh'uh dai Zuwairah, ya sake maida hankali wurin Likita ya ce mishi sallame ta su koma gida za a kula da ita kai kuma in ka tashi sai ka biyo ka ka r6i goron albishirinka, ya ce to ya yi ta godiya tun katin yasan me za'a ba shi. Mun dawo gida Likitan da ya ganni a asibiti kuma shi ne wanda ya ci gaba da zuwa gida yana duba ni saboda irin alherin da Baba yayi mishi, magunguna ya rnka bayar wa tare da shawarwari kan irin abincin da ya dace in rinka ci saboda kurarrajin dake damuna, nan da nan na samu karfi a jikina saboda na fara rabuwa da yunwa da nayi kan kace meye wannan kuma sai ga cikina ya kama motsi akai-akai, ba zan iya kwatanta farin 69 cikin Umma ba a wannan lokacin ba zan iya cewwa ga halin da take ciki ba. Duk da Umma karama tana gidan bata san me ke faruwa ba abin da ta sani dai kawai shine bani da lafiya, gashi kuma Umma tayi sa'a baba ya ce kowa ya kama bakinshi yayi shiru ba ya so ayi ta yawo da maganar sai dai kashedin da Baban yayi bai hana Umman yin waya ta shaidawa Umma Amarya abin da ake ciki ba. Sati biyu cif da tafiyar su Yaya Almu sai gasu sun dawo a gida suka sauka don isowar dare suka yi daga shi har Lailatu da Rabi'atun sun yi shar gwanin sha'awa da su kai ka ce ba asibiti suka je ba, daga butun amarci suka dawo, sai dai ganina da yaya Almu ya yi a gida. yayi matukar 6ata mishi rai, kasa boye bacin ranshi yayi don kuwa ko tafiya masaukinsu da aka basu shi da Lailatunshi bai je ba, ya zauna gaban Umma yana tambayarta abin da yasa ake keta mishi haddin gidanshi. Umma ta kalle shi cikin natsuwa ta ce mishi, to Babangida sai kayi hakuri nima kirana kawai Al haji yayi ya ce min in zo in kai Adawiyyah asibiti bata da lafiya. Cikin daren rannan muka hallara a gaban Baba saboda yaya Almu ya tubure ya ce bai yarda da 70 gatan da ake yi min bá wanda yake bani damar wulakantashi, don me' shi ba zan gaya mishi bani da lafiya ba sai bayan ya bar gida zan sa a fadaa a gida? In ba raini da wulakanci ba me zai sa in yi haka in ban da nasan ina da wadanda suka tsaya min? Yaya Junaidu shima ya shigo saboda kiran da aka yi mishi don yaya Almun ya ce yana da magana dashi. A fusace ya kalle shi ya ce mishi kái kake daurewa Rabi gindi kan duk wani abin da take yi min, kana shiga cikin harkokin iyalina da yawa, a wurinka ta samu kudaden da ta sai gida har ta samu tashi ta bar dakinta ta koma can da taimakonka tayi hakan tayi min rashin kunyar da yasa na hanata zuwa biki katagun sai da ka nuna min rashin jin dadinka kan hakan ka ce ban yi mata adalci ba, na hanata zuwa cikin dangi yanzu kuma ka shiga gidana ba izini kaje ka fito da ita ba tare da ka nemi 1zinina ba kuma baka samu lokacin da kayi waya ka gaya min abin da ake ciki ba to ya ishe ni haka nasan duk kokarinka bai wuce wai kai ka nuna min kai kawunta ba ne............ kan ya karasa maganar da zai fada yaya Junaidu ya katse maganar tashi ta hanyar ce mishi gyara maganar da kayi ta ce min wai kawu fusatar yaya Almu tayi yawa tanfar dai ya mance a gaban 71 Baba suke sai ya sake ce mishi an ce maka wai kawu, ni ina yi maka abin da kake yi min ne ko kai ba ka da mas'ala ne a gidanka? Yaya Junaidu ya ce mishi ina da ita, ya daga ido ya kalli Baba cikin natsuwa da girmamawa ya ce mishi Baba Mustapha ya yi min rashin kunya na ce min wai kawu da yayi baba ya ce rashin kunya mai girma kuwa don ya kamata ya fi kowa sanin cewa kai din ba wai ba ne tunda ya san uwarta ce tasha nono ta bar maka, don haka tunda ka nemi ya janye maganarshi ya ki to ni nasan kai ba wai ba ne a wurin uwata, shi yasa ma nake shugabantar da kai akan dukkan al'amuranta, nima kuma ba zan yarda ya maida kai wai ba, don ka wuce wai din, yaya Almu ya yi maza ya ce to kayi hakuri baba na janye maganar tawa raina ne ya baci da irin abin da Junaidu yake yi min, Baba ya ce eh ai nasan ranka ne ya baci shi yasa kayi mishi ràshin kunya a gabana ya kuma nemi ka janye rashin kunyar taka ka ki, saboda haka zan koya makaa yanda zaka rinka yin magana dashi nan gaba ko ranka ya baci saboda Junaidu surukinka ne, kai Junaidu yaya Junaidu ya yi maz aya ce na'am Baba, Baba ya ce mishi ka dauki uwata ka tafi da ita gidanka, kuje can ku sasanta randa Lamido ya 72 gane kai din kawunta ne da gaske ba kawun wai ba ne sai ka mayar mishi da ita gidanshi. Umma ta yi maza ta ce a'a Alhaji kar kayi irin wannan hukuncin a tsakaninsu shi Lamido ya ba Junaidu hakuri kawai ya dauki matanshi gobe su tafi gida. Baba ya ce ba zata bishi ba, ai har da laifinki a cikin rashin kunyar da ya yi wa Junaidu, a gabana ya kira shi wai? Junaidu wai ne? A haka Umma tana kuka Baba ya zartar da hukuncin in bi yaya Junaidu gidanshi, ni kam nayi matukar yin murna da hakan saboda na riga na gaji da yaya Almu da matarshi ko da dai a yanzu na daina jinz afin da nake ji a zuciyata, game da su, to amma kuma ina bukatar nima in 6oye musu cikin da nake dashi kamar yanda shima baba ya ce bai son a baza labarin cikin ya fi so kawai a bar shi ya fito da kanshi a gani. Ina zaune gidan Yaya Junaidu daga shi har Anti Rahma ji suke kamar zasu kashe ni saboda tarairaya ta da suke yi, ga kuma ya'yansu da suke matukar debe nmin kewa wadanda nayi matukar shakuwa dasu nake kuma son su kamar me, na yi matukar sakewa a gidan yaya Junaidu sau goma shima in ya shigo gidan sau goman kuma zai tambayi Anti Rahma ina Adawiyyah take? ta ci 73 abinci kuwa? tasha maganin ta? Nanj da nan na dawo cikin hayyacina na samu lafiya da kwanciyar hankali a dalilin na rabu da bacin rai gashi nan babu mai kuntata min. Yaya Almu kuwa yazo gidan nan ya kai sau goma don suyi maganata da Yaya Junaidu shi kuwa yaya Junaidun ya ki yarda suyi maganar sai suyi hirarsu su gama in ya kawo mishi zance na sai ya ce mishi mu bar wannan maganar tukuna sai ka gane ni din ba wai ba ne, yaya Almu ya ce haba Junaidu na ce kayi hakuri kan abin da ya faru ba zan sake ce maka kawun wai ba ka taimake

Chapter 5 of 8