Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
ni ka barni in tafi da matata Junaidu. Yaya Almu yayi shiru yana sauraron yaya Junaidu ya ce mishi to zan bishi mu tafi, sai kawai ya ji ya ce mishi to kaje sai na duba tukuna, abin yayi matukar bata mishi rai ya ce amma dai kasan babu gaskiya da adalci a cikin lamarin nan naka Junaidu, me nayi da zafi haka da zaka goyi bayan wannan abin da ake yi min? Me nayi wa Rabi wanda ba a taba yiwa wata ba? Ka fini adalcin aure ne? Yaya Junaidu ya ce to ka dai kama bakinka, yana fadin haka yaya Almu ya mike ya bar gidan. 74 Kwana biyar bayan nan sai ga aike daga gidan Baba wai maza-maza muje ana neman yaya Junaidu dani a lokacin nan kuwa kwanana arba'in ne cif a gidan Yaya Junaidu na yi mulmul, nayi gwanin sha'awa nayi kyau har ba a magana na maida jikina na murje nayi fes dani gashi nayi yar kiba mai ban sha'awa. Mun isa gida muka samu Baban tudu ashe shi ne yazo, yayi aiken muna shiga falo ya ganmu ya fara yin magana an ce maka kawun wai Junaidu, ni kuma na ce maka ka wun bahza kawun wofi, in ba kawun banza ba wa ke shiga gidan aure ya fito da 'yarshı? Wannan yarinyar ce mara lafiya? Ja'ira mara kunya mara jin magana, kina wani zazzare ido kamar an shake k, kin samu ana daure miki gindi kina yiwa Babangida rashin mutunci, a kanshi aka fara yin mata biyu? me yake yi miki? Har ya kara aure? Wannan dai shi ne laifin nashi in ban da shi kuma ban ga abin da yayi muku ba kai Junaidu ka fita daga idona ka fita daga goyon bayan Adawiyyah da kake yi tana yi wa mijinta rashin mutunci, wannan ai abin kunya ma kake yi don me za ka rike mishi matarshi? Maza-maza ka maida Adawiyyah dakinta, Yaya Junaidu ya amsa mishi ya kuma bashi hakuri, nima aka sallame ni na koma dakin Ummana akan zan shirya in bi 75 Yaya Almu mu tafi tare, saboda har yanzu Umman tana nan don Baba ya ce ba za ta koma gida ba zata zauna nan ta kula da lafiyata, sai na koma dakina tukuna, itama zata soma canje-canje da su amma a yanzu canjin yana tsakanin Umma Amarya ne da Umma karama, ina cikin zaman sauraron yaya Almun ban san yanda aka yi ba sai kawai naji an ce ya tafi ba tare da ya yi sallama da kowa ba. Tun daga nan ban sake komawa gidan yaya Junaidu ba ina zaune a gida daga Baba har Umma ji dani suke yi kamar zasu lashe ni, gashi kuma wannan karon Umma Amarya ma tazo tana nan kullum da sassafe take aiko min da abin karyawa wanda take shirya min da kanta, sai dai a yanzu duk da halin da nake ciki na kwanciyar hankali tunanina ya koma kan mijina na gaji da ganin abin da ake yi mishi kullum yazo gida sai ranshi ya 6aci so yake in koma dakina Baba ya hana nima a yanzu na fi son dakin nawa, yaya Almu mijina ne da muke .matukar son juna ni dashi, mafi yawancin abin da ya rinka shiga tsakanina dashi a baya daga mas'alar rashin haihuwa ne a yanzu bana tare da wannan mas'alar ciki ne dani har na tsawon watanni takwas har da wasu kwanaki, ba na jin haushin kowa ji nake tanfar ba zan sake 76 bacin rai ba a duniya, tunda babbar mas'alata an riga an yaye min ita, a yanzu babu abin da nake sha'awa irin ace na zauna kusa da yaya Almu na yaye mishi cikin dake tare dani wanda nake ta faman boyewa cikin manyan riguna ya gani, in ga irin nashi farin cikin da zai yi to babu hali, Baba ya ce bai yarda a gayawa kowa sai dai duk da haka yau kam nayi kewar yaya Almu, ji nake tanfar in ganni a gabanshi na tsunduma cikin tunanin hidimominshi da alhairorinshi iri-iri a gare ni tun daga kuruciyata can baya lokacin da nake ganin tanfar ni dashi din uba daya muke har kawo zamana dashi a matsayin miji da mata, zuwan Lailatu da kuma haihuwar Rabi'atu da tayi da abin da ya yi ta faruwa a tsakaninmu a wannan na tabbatarwa kaina da cewar yayi komai don yayi adalci abin da ya faru na kuskure kuwa wannan ajizanci ne irin na dan adam, don haka ba ma shi da yake mijina kuma dan uwana ba, hatta Lailatu dake kishiya wacce mafi yawancin sabaninmu dashi ya auku ne saboda ita na yafe mata duk wani abin da tayi in na ganshi kuma zan roke shi gafara kan irin 'yan rashin kunyar da na rinka yi mishi a dalilin kishi, ko da yake dai ni dama ba mai dabi'ar maidawa miji magana ba ne matukar dai ba wacce zai ji dadinta ba ne, balle 77 aje ana jero mishi fiye da abin da yake fada saboda Ummana ta riga ta tarbiyantar dani da cewar shi miji girmamashi kawai ake yi a kuma yi mishi biyaiya, na mika hannu na dauki wayata na soma danna lambobinshi da nufin kiranshi karo na farko da nayi hakan tun bayan dawowana gida, har ta fara alamar zata shiga sai nayi maza na katse ta saboda tunanin wata kila yana tare da matarshi musamman ganin lokacin farkon dare ne, sai dai ina katsetan kiranshi ya shigo tayi kara har ta katse ina kallon wayar ban dauka ba ya sake har sau uku ban motsa ba da dai naga ba zai daina kiran ba sai kawai na kashe wayar tawa gaba daya. Tsawon daren nan ban wani runtsa ba tunanin yaya Almu ya dawo cikin raina ban san dalili ba kishi ne yake damuna, na ni ina gida a zaune yaya Almu yana gidanshi tare da matarshi wajen wata hudu na bar mata shi ita kadai, Umma dake kwance can gefe da itama ta hakura da nata mijin ta bar wa Umma Amarya, saboda wai ba za ta rinka barina ina kwana ni kadai a daki da tsohon ciki ba saboda ba ta san abin da zai faru cikin dare ba, ta bude ido ta kalle ni ta ce min lafiya yau ki ka kasa bacci ko wani abu yana yi miki ciwo ne? Cikin natsuwa na ce mata lafiyata kalau Ummna, 78 yaya Almu ne kawai.....shiru nayi ban karasa ba saboda ganin yanda ta lumshe idonta a hankali ta kuma juya min baya alamar bata son jin maganar. Washe gari da sassafe sai ga Yaya Almu ya iso har cikin daki ya shigo ya same ni, don da nayi sallah komawa nayi na kwanta, yayi kwalliya sosai yayi matukar yin kyau sai wani annuri ke fitowa daga fuskarshi ga kanshinshi na kowane lokaci a tare dashi, a bakin gadon ya zauna ya zuba min ido yana kallona me ya faru Rabi? Jiya kinyi nufin kirana ki ka fasa na kira ki kuma ki ka ki dauka daga baya ma ki ka kashe wayar me ki ke son gaya min? Na ce ban kira ka ba, ya yi murmushi ya ce ban san ki da karya ba Rabina gaya min kawai in kinji kewata ne...na daure fuska na oe in yi kewarka saboda me tunda kai ba tawa kewar kake ji ba, ya ce uhun Rabi kenan, dama kin zo kin zauna a gida ne don kina tunanin zan rinka kewarki? Don ki samu ki yi ta azabtar dani ta haka, duk abin da ki ka rinka yi min muna tare bai ishe ki ba sai kin baro gidan kin dawo nan kin zauna saboda in yi ta azabtuwa da kewarki? Saboda in kuntata in kasa jin dadi, don kina ganin in ba kya nan a gidan ba zan samu natsuwar da nake bukatar samu ba, saboda ki nuna min ni din ba komai ba ne a wurinki, saboda ki nuna min 79 cewar za ki iya rayuwa mai dadi ko da kuwa babu ni a kusa da ke har ma kina ganin in kinyi nesa dani za ki fi samun kwanciyar hankali don haka ma ki ka tanadarwa kanki wurin zama, to in ke mace za ki iya nuna irin wannan jaruntakar to ni namiji fa? Ko fa ni kadai ne mijinki iyakar kuma gatan da su Umma da Baba zasu yi miki bai wuce dai wanda suke yi mikin yanzu ba, su yi ta tattalinki suna tarairayarki kina kiba irin ta rashin zuciya, ni kuwa fa? Ya zuba min ido yana kallona ban san dalili ba sai kawai naga na kama yi mishi kuka bai fasa ba ya ci gaba da maganarshi zaman gidan nan da kike yi dai kema kin san ba bis ayardana kike yi ba. Fin karfina aka yi aka rike min ke, don haka ke kin fi kowa sanin irin zaman da kike yi, naje na kai kara gun Baban tudu shima ban san me Baba ya ce mishi ba, ya ce wai in dan kara hakuri kadan, to zanyi tayin hakuri Rabi ba kadan ba ma zanyi mai yawa, to amma ki sanı daga yau ban yarda ki sake fita daga cikin gidan nan ba ko da kuwa gidan Junaidu ne balle in ji labarin kinje wani wuri ko da kuwa yiwa su Umma rakiya ne zuwa tafiyarsu, ki gaya musu na ce ban yarda da fitarki zuwa ko'ina ba kiyi ta zama a gida tunda gidan yana yi miki dadi. 80 Kukan da nake yi ya tsananta saboda na kasa hana kaina yin kukan a dalilin kalaman da yake ta jerowa wadanda ba masu dadin ji ba ne a wurina, don kuwa alama ne na yana cikin fushi mai yawa game da zaman nawa sai ya kara matsowa kusa dani yana cewa gaya wa Baba yau za ki koma dakinki Rabi sai muyi tafiyarmu ki koma dakinki kiyi zamanki ke kin san ina sonki fiye da komai a duniya, kin sani sarai kece mafi darajar abin da nake dashi a rayuwata, in kinyi abin da kika yin ne don ki horar dani ki nuna min matsayinki to na horu Rabi, na kuma kara jinjina al'amarinki tunda gashi ba barinki gidan nima na kasa zama a cikinshi, rabon da inyi kwana bakwai ina zaune a gid ahar na manta Rabi, yau ina nanne gobe ina can, kiyi hakuri ki yafe min abin da nayi miki wanda yasa kika yanke wa kanki hukuncin yin nesa dani ba tare da kinyi tunanin abin da hakan zai iya jawo min ba, ganin da nayi Yaya Almu yana shiin durkusawa da guiwowinshi biyu a kasa don ya roke ni yasa nayi zunbur na mike daga kwanciyar tawa, na zauna a tsakiyar gadon ina rokonshi kar kayi min haka yaya Almu ba sai ka durkusa min ba zan dawo dakina, da sauri ya ce min yaushe? Kan in ba shi amsa sai ya sake zuba min ido cikin natsuwa yana yi min wani irin 81 matsanancin kallon da ya yi dalilin da nayi maza na jawo abin ruhuwana na rufe kirjina da ya zubawa ido, ciki ne dake Rabi? Nayi maza.na ce mishi wane irin ciki? Cikin lafiya? Ni mai haihuwa ce? Ya ce to kirjinki da ya cika haka fa? Ban taba ganin nonuwanki sunyi irin cikan da suka yi ba yau mu gani? Na bata ido na ce kaga me? Nayi maza na mike na shige bandaki nayi wanka har na fito yana zaune a wurin zaman jiran fitowana yake yi, me ya canzaki ki ka zama haka Rabi? na ce zaman gaban iyaye na samu kwanciyar hankali da natsuwar da nake bukata, ban yarda ke ba Rabi dole akwai wani abin da ke tafiya wanda yasa Baban Tudu ya hakura ya huce fushin da ya zo da shi ya bar ki kike zaman gidan nan. Na ce to ko mna dai menene ai kuma ba ciki bane tunda yaushe? Yaushe rabon ma da ace an wani abinnan? Kaima yanzu ai ba za ka so ace maka ni ina da wani abu ba in dai ba nema kake wata babbar magana ta taso ba, wuce shi nayi cikin hanzari na nufi dakin Umma Amarya, a can na karya na kuma yi zamana tare da ita, rannan a gidan yaya Almu ya wuni. sai dai ni kam ban yarda mun sake zama dashi a wuri daya ba. 82 Kwana biyu bayan nan ya sake dawowa gaban Umma yana magana da ita can komawa gidanshi ya ce Umma in zama da Lailatu ne bata so sai in canza wa Lailatun wani gida in kai ta wani wuri don itama dama tana yi min magana akan in Rabi zata dawo to in kai ta wani wuri ita in bar ta anan gidan na ce mata a'a wannan gidan ai don Rabi aka gina shi sai dai in ma raba sun zanyi ita in kai ta wani gidan. Umma ta ce kul ka ce zaka raba su su zauna tare ai ya ishe su suyi hakuri da juna kawai, kai kuma kayi kokarin yin adalci a tsakaninsu, shi kenan.Yayi maza ya ce to Umma, to yaushe zata koma? Ta ce to bari in ga Alhaji anjima zan yi magana da shi ko zuwa gobe sai ka dawo ka ji yanda muka yi, ya ce a'a Umma ai wannan karon na riga na yankewa kaina hukuncin in yi ta zama a gidan nan in jira har zuwa lokacin da zaku yanke abin da ke tsakanina da Rabi, ku bani ita mu tafi ko kuma ku gaya min dalilin rike ta da kuka yi, ni ban taba ganin kun yiwa wani irin abin da kuka yi min ba Umma, ban kuma san dalilin da yasa ki ka yarda aka yi min hakan ba in wani laifi nayi miki ki yafe min, ya durkusa da guiwowinsa duka biyu a gabanta in har zaki juya min baya Umma to ai kenan na zama bani da kowa duniya ki yafe 83 min Umma, nan da nan Umma ta soma share hawaye a idonta tana fadin ba ka yi min komai ba Lamido baka yi laifin komai ba Babangida to me zaka yi min? Me zai faru da har zaka yi tunanin wani abu zai shiga tsakanina dakai Babangida? Ya sake dago ido a hankali ya kalle ta cikin natsuwa ya ce mata, to me yasa aka raba ni da matata kina kallo Umma? Ai kin fi kowa sanin ina sonta sabanin dake shiga tsakaninmu ai ba kiyayya ba ce yau da gobe ne kema kuma kin sha gaya min cewar zaman aure hakuri ne duk yanda aka kai da Son juna in ba ayi hakuri ba zaman ba zai yiwu ba, kiji tausayina mana Umma ba fa na iya zama a gida sosai, ba na jin dadi ji nake tanfar nayi laifi 1yayena sun kwace matar da suka bani saboda ban iya rike ta ba. Kafin Umman tasan abin da zata ce mishi sai ga Yaya Junaidu ya shigo da saurinshi kamar an aiko shi zo mana Mustapha dama Kaduna zan tafi don in ganka sai naji ance kana nan kazo, yaya Almu ya mike suka fita, suna barin dakin na kalli Umma cikin sanyin jiki na ce mata Umma yau kuma fitsari a zaune nake yi nayi-nay1 kuma in tsaida fitsarin na kasa, da sauri ta ce min fitsa Adawiyya ko dai haihuwa ce tazo? tashi mu gani, na yi kokarin nmotsawa in yunkura in tashi na kasa 84 janye kafata da na mike na sake kallonta cikin natsuwa na ce mata Umma masokiya ta rike min kafafuwana duka biyu ba zan iya tashi ba. Nan da nan jikin Umma ya kama bari tana fadin watakila dai haihuwa ce tazo miki Adawiyya, Allah dai ya raba ku lafiya tana fadin hakan ta kama kuka, kuka sosai Umma ta kama yi ta kuma kasa hassala komai kukan da take yi din ya bani tausayi don nasan abin da take tunawa wanda kuma shi take tsoro, na kalle ta cikin natsuwa na ce mata kiyi hakuri Umma. Umma Amarya ta shigo daidai lokacin da cikina yayi wani irin murdawa mai tsanan a firgice na kama salati ina ambaton sunayen Ubangiji da sauri Umma Amarya ta rike ni ta kaini wani daki dake kusa da na Ummana ta kwantar da ni kan wani gado wanda dama akanshi Nos din dake zuwa dubani take yi min awo, kiyi hakuri Adawiyyah kiyi hakuri yanzu Likita zai zo duba ki, don na ce a kira shi, tana maganar tana shafa ni bayana take shafawa tana kuma gaya min kalamai masu kwantar da hankali, zuwa can wani irin ciwo ya sake taso min mai tsananin rudarwa nayi matukar kidimcwa ina fadin waiyo Allah na waiyo Allah, ita kuwa Umma tanfar bata jin tausayin halin da nake ciki taki tabar ni in huta sai 85 fadi take yi, yi nishi Adawiyyah yi nishi mai karfi ga kan yaro nan ya iso yi nishi mai karfi sosai nayi matukar dagewa da iyakacin karfin nawa nayi nishin da take cewa in yi cikin yardar Ubangiji sai gashi a hannunta, yana ta faman kyara kuka ita kuwa bata kula ba sai tofa mishi addu'o'i take yi ta ko'ina, nan da nan kuma ta tauna dabino a bakinta ta diga mishi ruwan a nashi baki, sannan ta matso kaina tana nuna min shi kin ganshi Adawiyyah da namiji ne bari in mikawa Hajiya shi ta ganshi tana kai shi ta dawo kaina bata bar Nos ta taba ni ba sannu Adawiyyah sannu da kokari ke kam jarumar yarinya ce gaki kuma da hakuri har Umma ta gama abubuwan da zata yi min kalamai masu dadi na fatan alheri da addu'o'i iri-iri take yi min don haka har ta gama ban gundura da komai ba da kanta tayi min wanka ta riko ni ta dawo dani dakin Umma ta bani mai na shafa ta miko min doguwar riga mai laushi sabuwa na sanya bayan na sanya sabbin under wears ta bani tea nasha sannan ta ce wa Nos din to zo ki yi mata allura ta juya ta fita lokacin bata iya yin komai saboda tsananin tsorata da tayi. Umma Amarya tana fita sai ga Baba ya shigo da saurinshi iko sai Allah uwata ikon Allah yau uwata ta haifar min kani sannu uwata sannu da 86 kokari, kin ji wani abu yana yi miki ciwo ne? Na yi maza na ce mishi a'a Baba lafiyata kalau, ya mika wa Nos yaron ya ce mata gama kintsa shi sannan ya koma jikin Ummana ya zauna ya ce mata dubi nan ya nuna mata ni da dan yatsanshi ya ce mata uwata ta haihu lafiya ita da danta lafiyarsu kalau babu dalilin wannan kukan da kike yi ki kwantar da hankalinki babu abin da zai same ta wannan mafarki da kika yi ba komai ba ne dama na ce miki babu abin da zai same ta ita da cikinta sai alheri tsawon lokaci Baba yana rarrashinta na dago ido na kalle ta na ce mata Umma kiyi hakuri ki bar kuka ni lafiyata kalau taimake ni ki bani abin da zan ci don ji nake tanfar an sace min kayan cikina, da sauri Umma ta mike bari in sake hada miki tea, na yi maza na bata rai na ce tea kuma Umma tea me zai yi min? Ni tuwo za ki bani ko sakwara, ana cikin haka sai ga Yaya Almu ya shigo da saurinshi sallama yazo yi zai tafi gida, Umma tayi maza ta ce mishi to dan dakata min kadan Lamido ina zuwa, tayi maza ta dauki yaron ta danka mishi ta ce ungo wannan duba min shi tukuna kafin ka tafi, yana zubawa yaron ido ya nemi wuri ya zauna cikin sanyin jiki da natsuwa a hankali ya bude baki ya ce mata to da dai Rabi ta yarda da cewar da nayi 87 tana da ciki sannan haihuwa wani abu ne mai sauko to da sai in ce Rabi ce ta haifar min shi Umma, don kuwa kama dani da Baba ya yi kinga kuwa kama da gidan nan yake yi inda so kuwa shi ne namu ai da nine na dace da haihuwar dan da zai yi kama da mahaifina Umma ba wani ne zai haifa ba. Cikin natsuwa Umma ta ce mishi naka ne Lamido, Adawiyyarka ce ta haifar maka shi, tsawon lokaci yana zaune kanshi a sunkuye idanuwanshi akan yaroa ko kifta su ba ya yi yana kuma sauraron abin da Umma ke gaya mishi na cewar ba a kwance maka matarka ba Babangida, an dai rike maka ita ce don ta samu kwanciyar hankalihar ta haifar maka danka lafiya musamman da yake cikin nata mai lalura ne ko shi Yayan tudun da yazo kan maganarku rokon da Albaji yayi mishi kenan na abar mishi ita ta haihu a gabanshi. Shigowar da Umma Amarya tayi rike da foodflask mai wuri biyu a hannunta na dama ga kuma platc-plate a daya hannun nata yasa hankalina ya tashi daga sauraron zancen Umma da danta ya koma kan Umma Amarya da abincn da ta kawo min tuwon dawa ne miyar kukan da aka yi da naman kaji ga man shanu da yajin daddawa 88 ya ii, Umma hada min miyar da tuwon kawai a wuri daya, ta yi murmushi saboda tasan ba dabi'ata ba ce yin hakan, na gama cinye tuwon da ta zuba min din na kalle ta na ce mata na koshi bari in shiga toilet in wanke hannuna bana son wankewa a nan a zaune ta ce to bari in rike ki don ba karfi ne dake ba, yaya AImu yana jin haka yayi maza ya ce bari in kaita Umma, ta debi kwanukanta ta fita shi kuma ya rike ni ya kai ni na gama abin da zan yi ya dawo dani sai da ya gyara min kwanciyar da nayi sannan ya kalle ni cikin natsuwa ya ce tausayinki ya kama ni Rabi, kin yi ta wahala ke kadai ban ma sani ba sannan a yau din nan da kike fama da nakuda na sanyaki a gaba ina gaya miki bakaken maganganu ki yafe min duk wani abin da nayi miki na kan gaya miki magana ne don in dan ji sanyin bacin raina sbaoda gani nake tanfar kin ki zama da ni ne ki ka gudu kika barni amma na rantse miki Rabi ranar da ki ka bar gidan nan aka neme ki aka rasa a zaune na kwana akan kujera zuwa yau kuma da safe ban samu jin dadin da na saba ji ba a tare dani, amma a yanzu da naga wannan mutumin na gane duk abubuwan da ake yi min din suna da dalili har kuma ga kyautar da Ubangiji yayi mana, Rabi sai naji bani da sauran matsala a tare dani na godewa 89 da ya rufa min asiri ya yaye mana mas'alar Allah da ya bani haihuwa tare dake na gode mishi rayuwarmu na kuma gode mishi da ya azurta ni da dan da Ummana tayi ta zubar da hawaye don rashin samunshi, ya dago idanuwanshi a hankali ya kalle ni kafin ya ce min wannan dan na Umma ne Rabi nan gaba dai za ki haifar mana namu amma wannan nata ne ita da Baba da ma su suka yi renon cikin shi, nayi maza na ce mishi da Umma Amarya ma ya ce a'a Rabi Umma Amarya ai bata shiga lamarinmu tana jin kunya nayi murmushi na soma ba shi labarin abubuwa har dai daga karshe na ba shi labarin karbar haihuwar da tayi na kuma ce mishi to ko wannan kayan dake jikinmu ni dashi ai ita tazo dasu randa taje Umra, ya yi murmushin jin dadi ya ce to naji amma dai ba zan yarda kice su dukansu ukun ba sai dai kawai in kika kara haifo wani nan gaba sai ita Umma Amarya ta dauka, na ce mishi to shi kenan. Haihuwar da na yi lafiya ta saukar da wani irin farin ciki da annashuwa mai yawa cikin zukatan yan uwa da abokan arziki, tun ma kuma ba iyayenmu ba ko da yake dai Umma ta boye komai ba za ka ganta kaga wani canji a yanayinta ba, ta dauki haihuwar kamar kowacce da aka saba yi, to amma kuma kowa yasan ta boye abin da ke ranta 90 ne don kuwa dama ita mai barwa ranta al'amarinta ne na farin ciki ko bakin ciki ba ka safai takan baiyanar har kowa ya gane abin da take ciki ba. Yaya Almu kuwa tun washe garin ranar da aka yi haihuwar ya fara azumi saboda wai ya taba viwa Ubangiji alkawarin duk sanda ya bani ciki to zai yi mishi azumi talatin don godiya sannan ya sake yin wasu talatin din in na haihu lafiya. Sanin halin Ummana da nayi na kin dabi'ar 'yan zamani na nuna rashin kunya da rashin kara kan yayan da suke haifa na fari ya sa nayi matukar kamewa don dai in kara mata farin cikinta, tun washe ga rin haihuwar da yaya Almu yaje gida da zai dawo ya taho min da Baba Talatu da Rabi'atu, don haka Baba Talatu ke kula da al'amarin yaron yayin da Rabi'a kuwa take manne dani don bata manta ni ba, Lailatu kuwa da 'yan uwanta ba za a ce musu komai ba don ko barka ba su zo ba, itama Lailatun sai da taga abin zai zame mata bacin rai sannan ta biyo shi suka zo tare saboda sun ce wai dan ba na asali ba ne dashenshi akayi min don dai an matsu a ga na haihu. Gaba daya Baba ya hana shagalin suna mai yawa ya ce maimakon a maida hankali ga yin Shagalin suna gara ayi ta addu'a Ubangij1 ya rayaa abin da aka samun ya kuma sa ya zamo mai 91 albarka don haka gaba daya'sunan sai ya ce a tafi katagun ayi wannan dalilin yasa tun ana saura kwana biyu sunan yaya Junaidu da iyalinshi suka nufi katagun ya hada har da Rabi'atu wai ba za'ayi sunan Baba ita ba itama Umma amarya shiryawa ta yi ta yi tafiyarta wai zata kóma gida saboda masu zuwa gidan don Umma karama ma tana katagun din sai aka barni daga ni sai Ummana sai ko Baba don Baba Talato ti tafi. Ranat sunan da safe Baba ya shigo daidai Umma tana fama da yaron wanda ya tashi daa rikici sosai yasa hannu ya karbe shi daga gare ta yana kallon kukan da yake yi tare. da yi mishi magana tanfar dai yana jin abin da yake gaya mishi haba Mallam me yà same ka? Menene damuwarka? Kai kuwa ai bha kuri ya kámata kayi don kuwa wanda ka gaji sunanshi mai hakuri ne, Umma ta daga ido cikin natsuwa ta kalle ni ta ce sun fadí sunanne? Baba ya ika mata shi ya ce bata shi ta bashi nono tayi maža ta karbe shi

Chapter 6 of 8