Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
kanki in ce mishi haka ne in yi tafiyata. Rannan ina dakina da daddare addu'a nake yi bayan na idar da sallah hakuri da dangana nake rokon a kara min, sai na jiwo salatin Lailatu cikin 38 gurnanin kuka, da sauri na shafa fatihar na yiwo waje zan shiga dakin nata don naga kofar a bude sai kawai naji Y aya Almu yana rarrashinta wai ta bar shi yaje ya taso ni don bai kamata su tafi asibiti bai gaya min ba ina jin haka nayi sanaf- sanaf na koma dakina na hau gadona na kwanta tunda dai bata son in sani. Zuwa can ban san yanda aka yi ba sai gashi ya shigo dakina yana fadin ke Rabi tashi muje mu kai Lailatu asibiti ina ganin nakuda ce ta tashi mata kamar in ce mishi ba zani ba tunda bata da bukatar zuwan nawa sai kuma naga to don me zan yi hakan'? Na sanya hijabina na biyo bayanshi nasa hannu na kinkimi manyan akwatuna guda biyu da aka shake da kaya tanfar dai in anyi haihuwar can za'a zauna, shi kuma yaya Almu ya ciccibota ita da cikin nata zuwa cikin mota a haka muka isa asibiti, sai faman gurnani take y1 ina ta nanata sannun da nake yi mata, amma ban samu ta amsa guda daya ba. Gwajin farko da aka yi mata Nos din ta ce Hajiya da kin rike wannan nishin naki da kike faman yi sai bukatar nishin ya taso tukuna don in haihuwa tazo miki da sauri to sai kiyi ta nan da awa shida, na kalli agogo na ce zuwa takwas din safe kenan, yaya Almu ya bar mu a asibiti ya tafi 39 gida kan cewar zai je yayi sallah ya yi wanka ya dawo na ce mishi to, ina nan a wurin sai ga mutanen gidansu sun is0 in ban da na gaishe su da babu wanda ya ce min in ci kaina, muka zauna a haka suna sha'aninsu nima ina lazimina sai in sun jiwo mun hada ido su kwashe mun da dariya ina kallonsu. Wajen karfe bakwai yaya Almu ya dawo, na ce mishi to bari nima inje gida in dawo ya ce, a'a bana so ta haihu ba kya nan a wurin nan na ce mishi to na hakura, haihuwa bata zo ba sai wajen karfe daya da kwata muna wurin a tsaye, Nos ta fito tana tambayar ina wadanda suka kawo Lailatuu Mustapha muka yi maza muka mike ni dashi muka ce gamu suka ce to ta haihu an samu ya mace ni da Yaya muka kama murna yayin da fuskokin yan uwan Lailatu suka sauya alamar daa ba haka suka so ba. Muna shiga dakin na nufi Lailatu na rungume ta don murna turus din da ta yi mun ya dawo dan Cikin haiyacina na juya wurin yaya Almu dake rungume da yarinyar cikin matsanancin farın ciki yana ganin na kalle shi ya miko min ita, ungo ta. Rabi 'yarki ce ki rike ta taki ce ki rike ta da zuciya daya kiyi mata reno da gata irin wanda Umma tayi min ki kuma yarda da cewar haka kaddara ta 40 shiryo mana don kuwa kin san in da ina da iko akan al'amura to da ba haka ba, da na baki haihuwa kinyi ta-Rabi, kin yi ta har sai ta ishe ki kafin in baiwa sauran mutan da suke nema to bani da ikon komai don haka kiyi hakuri, na ce mishi babu komai Yayaa Ubangiji ya raya mana ita da imani yace mun amin. Juyawan da zamu yi sai kawai muka ga Lailatu tana ta faman kuka da sauri Yaya Almu ya tambaye ta ko menene? Sai ta ce mishi wai tun bata wastsake daga azabar nakudar da ta sha ba har yayi mata kyauta da yarta kuma a gabanta yana cewa dashi ke ba da haihuwa to da ba ita zai baiwa ba ni zai baiwa t ai abin na Allah ne in ma shi ba ya sonta Ubangijin da ya yi ta yana sonta ni da Yaya muka yi ta rarrashi muna yi mata bayani don fahimta r da ita abin da ake nufi. Bayan fitar Yaya Almu 'yan uwan Lailatu suka shigo suka karbi yarinya ina jinsu suna cewa wannan yarinya irin kamar da ta yi da Ubanta ina jin da namiji aka yi niyyar yi, surkullen da aka yi tayi ne yasa tazo a mace, surkullen da aka yi kuwa cikin da ya fiddo mace ai shine watarana zai fiddo namiji, naje yi dai ko in ce a juri zuwa rafi da tulu gaba daya suka kwashe da dariya. 41 Ni kam jin su kawai nake yi ina kuma sabgogina tanfar dai ban san dani suke yi ba. Tunda 'yan uwan Lailatu suka wastsake daga kaduwar ya macen da aka samu maimakon namijin da ake sa ran gani sai kuma suka koma hirar da suka saba na fadin darajar mace mai haihuwa yanda nan da nan take zama ta gaje gida ta zama ita ce uwar iyali ita da miji kuma sun zama daya sun zama ita yashi shi ya ita ta zama shi da dukiyarshi duka nata yanzu fa daga wannan haihuwar da Lailatu tayi komai na Lamido na tane, dayar ta ce na tane mana tunda ko mutuwa yayi 'yarta ce mai gadonshi, gabana ya yanke ya fadi saboda jin ana anbatowa Yaya Almu mutuwa don kawai an haifi 'ya guda daya tare dashi. A wannan lokacin na samu kaina cikin tsananin son Ummana da jin tausayinta saboda naa kara fahimtar ba karamin hakuri tayi ba a zaman da tayi gidan Baba ni dama nake zaune da Yaya Almu cikin gatan da babu wanda ya isa ya fito fili ya nuna min wata kiyaiya ko wulakanci saboda 1don Umma ya tsare al'amura masu yawan gaske kenan nake ganin haka akan rashin haihuwata to ita fa yaya taji da nata a lokacin da babu mai tsare mata? Ni kam a yau na sami ko Umma karama dake ta faman kai-kawo cikin al'amarin a boye 42 take yi sai dai ta cinma ayi amma bata fito fili ita da kanta tayi ba shi yasa ma ban taba buda baki na gayawa ita Umman ko baba irin zirga-zirgan da take yi a wurin Lailatu ba. Hakika na yarda na sakankance cewar matar dake da mas'alar rashin haihuwa suna ganin abin da suke gani na bakin ciki da kunan rai, musamman idan suka yi dace da irin mutanen nan da aiki da hadisin Manzon Rahama mai cewa Imanin dayanku ba zai cika ba har sai yaso wa dan uwanshi abin da yake so wa kanshi.' bai dame su ba. A wapnan lokacin ji nake yi tamfar ba don kaina nake son haihuwar ba ba kuma don Yaya Almu ba tunda shi kam ai ya riga ya samu son haihuwa nake yi don Umma na ta dai sa hannu ta dauki dan da na haifa dan da na san shi kadai ne zai zo duniya ya debe mata kishirwar haihuwa da bakin cikin rashinta da ta rayu a ciki, sannan ni ban damu ba ace mace ko namiji na samu in dai mutum ne mai amsa sunan bil'adam ai bani da zabi sai ko godiya, in na tuna halin da nake ciki da yanda Umma ta rasa kuzari da lafiya tun daga auren Yaya Almu zuwa yau duk da dai ta hadiye komai a cikinta babu mai sanin tana da wata damuwa. 43 Muna dawowa gida nay1 shiri na dauki yarinya na lullube ta na hau Jirgi na nufi Legos da ita na kaiwa Baba ya ganta, tana hannun Baba bayan ya gama yi mata addu'a yana kallona cikin tsananin farin ciki ya ce a'a uwata kun samu ya a gidanku, na yi murmushi na ce mishi wannan tawa ce Baba ni kadai in ta sake haifo wasu to suma sai su samu, Baba yayi dariya ya ce kiny1 gaskiya uwata. Kwana uku ca dawowarmu Baba ya aiko min da wata motar sabuwa dal wai tukuicin kai mishi yarinya da nayi, Lailatu da 'yan uwanta kuwa abin yayi matukar kona musu rai har suna fadin wai ai wannan shi ne wani da tusa wani da karbe riga, wannan in dai ba Jirgun sama Zai sai wa maijegon ba ai baa kulla gaskiya ba. Kwana hudu da haihuwar Ummana tazo ganin yarinya kai tsaye dakin Lailatu ta fara shiga ta dubata suka kuma gaisa da yan uwanta sannan tasa hannu ta dauki yarinya ta fito da ita ta shiga falon yaya Almu na same su a ciki tana kokarin hudawa yarinyar kunne wanda in ban da Yaya Almu yayi kashedin kar a huda da tuni iyayen Lailatu sunyi hakan na ce Umma shi ne sai yau ki ka zo buda mata kunnen bayan tasha iska ta gane zafin jikinta, Umma tayi dariya ta ce ita dai raguwa ce kawai mika ta a bata nono na ce to na 44 karbe ta na kai musu na dawo na zauna muka gaisa sai ta miko min wani dan akwatin da ta fiddo daga cikin Jakarta nasa hannu biyu na karba ina kallonta sai ta ce min kayan kwalliyar yarki ne a ciki na ce to Umma ai kuwa dai mun gode. Anyi shagalin suna irin wanda ba zai yiwu a tsaya bada labari ba, abu guda daya da zan fadi dai shine, 'yan uwa na birni da na kauye abokai na cikin kasa da waje sun halarci sunan, gaba daya cewa ake yi Lamido ya samu haihuwa, don haka ya zama dole a zo mishi suna Rabi'atu sunan da yaya ya sanya mata kenan, kyaututtuka kuwa inin wadanda Lailatu ta samu abin sai wanda ya ganı, amma bata gamsu ba saboda gaba daya kayan da ya fito daga gidanmu raba daidai akayi mana banbancin kawai shine kayan yara haka nan abokan yaya Almu suma kyautar raba daidai suka yi mana wannan dalili sai yasa ta kawar da kai daga kan abin da ta samu ta zubawa nawa ido tà mance cewar ita ce ta haifi 'yar, ta mance da cewar ni zan iya bayar da komai nawa don in samu 'yar kawai kar a hada mun ita da komai. Bayan yan suna sun watse muka dunguma cikin wai sabon zaman kuma zaman da nake matukar son ganin nayi mu'amalla mai kyau da yarinyar da muka samu yayin da ita kuma uwar 45 yar take iyakacin kokarinta wajen ganin ta shiga tsakanina da ita, nayi matukar kokarina wajen ganin al'amura sun daidaitu tsakanina da Lailatu musamman ma da yake ita ce wacce zata zama uwar 'ya'yan yaya Almu to me zai sa muyi ta fitina da ita? Na so ace Lailatu ta yarda mun zauna lafiya tayi ta haihuwar 'ya'yanta ni kuma ina renonsu to taki duk wani tayi na zaman lafiya da na kawo bata karba ba ta kabar dashi maimakon ta fahimci dalilin sassaucin da nake yi ta dan karyo don mu zauna lafiya, amma ina? Sai ta maida abin tsoro a bisa wannan dalili sai ya zama mun dole in kare kaina daga mummunan wulakancin da take fito min dashi babu abin da Lailatu ke yi min da yake matukar kona min rai irin sau goma in zan sa hannu in dauki Rabi'atu to sau goma kuma zata biyo ni tazo ta kwace ta ta tafi tana cewa zo muje kar a lashe miki kurwa kamar yanda aka lashewa ubanki. Rannan tayi hakan akan idon Yaya Almu ya ce haba Lailatu me yasa kike yin irin wanan abin ne Ta ce a'a a'a ta haifi nata, yi kokari ta haifi nata kawai amma kar asa min ido akan nawa bana son 1ya yi da neman wurin shiga irin nasu na gado. A fusace yasa hannu ya karbe yarinyar ya miko nmin ita ni kuwa sai nasa hannu na karbe ta 46 na rungume ina rarrashi saboda kukan da take yi a dalilin tsorata da tayi ita kuwa Lailatu sai cewa tayi tir da halin rashin zuciya irin taku ke kam ina jin sanda ake rabon zuciya ba kwanan a wurin ta juya ta nufi dakinta tana ganin Yaya Almu ya shiga wurinshi tayi maz ata fito tazo ta sure yarinyar ta shige daki ta kullo kofa ta barta tana ta ihu. A wannan lokacin dan Rankanin abu ne zai tashi Lailatu tayi mun gorin haihuwa ta ce mun n da da sai dai inga shirwa ta dauko dan tsako, ko kuma ta ce haihuwa ai ba abar banza ba ce gadonta ake yi in na zauna zanyi kukan bakin ciki sai Baba Talatu ta rufe ni da fada ta ce kukan butulci nake so in yi in ba haka ba menene ba ayi min ba na ni'imomin rayuwa? In ban da halinki na rashin zuciya me zai sa ba za ki fita hanyar yarta ba ba akanta take wulakanta ki ba? Na ce ba 'yarta ba ce Baba 'yar Yaya Almu ce don haka tawa ce, taja tsaki ta ce ai sai kiyi. Kalaman da Baba Talatu ke yi mun sun sanya Di na zamo mai yawan godiya a duk lokacin da damuwar rashin haihuwa ta bijiro min na kanyi maza in shiga kirgo ni'imomin da aka ni'imtani da su misali ni din marainiya ce bani da uwa bani da uba ban ma sansu ba, to amma sai na girma cikin 47 gatan da ya hana ni sanin ni din marainiya ce saboda samun Umma da Baba da nayi wadanda suka yi min gata suka maida ni yar lelensu har vau din nan kuma ban taba neman wani abu na rasa ba matukär abu ne wanda zasu iya yi min shi ba. Rannan ina cikin kicin ina aikin abincina don ni ke da girki ina shirya abincin rana duk da nasan Yaya Almu ba ci zai yi ba saboda yakan kwana ashirin bai ci abincina ba wai ban iya ba, abincin nawa babu dadi (taste) wato dandano, don haka in daina yi dashi na ce mishi to. Aikina nake yi ina rero baitocin Celine dion cikin wakarta mai taken Becouse u luv me. For all the standu stood for me, For all the truth dat u made me see For all the joy u brouth to my life, For all the wrong that u being right. Aikina nake yi ban kula zirga-zirgar da Lailatu ke yi tana fadin za'ayi kwaba ba har na iso inda take cewa. I was blessed b/cos was loved by y, sai kawai na ji Lailatu ta kwashe da dariya tana fadin da kenan amma yanzu ba ta taki ake ba kina dai zaman rashin zuciya ne kawai. Ajiye bayan Lailatu nasa hannu na cafke ta na bayan Lailatu nasa hannu na cafke ta na wanketa 48 da marI sau biyu, ta miko hannu zata rama na cafke shi na murde da karfi, ta kwallara ihu, Baba Talatu ta fito, kar kiyi fada da ita ga goyo a bayanta uwardakina, na cc mata to, na saki Lailatu na juya zan shiga kicin in ci gaba da aikina, sai kawai ta kama zagi tana ashar tana fadin wasu mugayen maganganu akan Ummana har tana tambayata wai menene bata sani ba namu? Ai komai an bata labarinshi da dai na ji rashin mutuncin nata ya ishen, sai kawai na fito na same ta nasa hannu na 6alla tawul din da tayi goyon dashi na kama yarinyar na ajiye ta a kasa, Tambai tayi maza ta dauke ta tana rarrashinta saboda kukan da take yi, Lailatu ta shiga fadin bar ta ta kashe ta dama duk abin da take mata munafurci ne taga anyi anci niba to anan babu wata ribar da zaki ci, na ce mata waye yayi ya ci riba? Tayi maza ta ce uwarki mana saboda itama a yanzu ta shiryawa danben musamman da yake taga ta ajiye teba, nayi maza na buge ta ga guiwar hannuna a baki abin da ya yi matukar kidimata duka na yiwa Lailatu ranar irin wanda bata taba zaton zan iya yi mata ba, sannan daga Baba Talatu zuwa su Larai da Tambai babu wanda ya yi kokarin rabawa sai cewa suke yi kuyi hakuri su dukansu suna daga nesa, ni da kaina ne na kyale 49 Lailatu saboda ganin da nayi duk wani kokarin ramawa da take yi ta daina nace mata gobe ma in wata magana ta tashi ki sake zagin uwata ki gani mara mutunci wacce 1yayenta ba su yi mata tarbiya ba na wuce na shiga wurina na bar ta tana fadin a zaga din sai dai bata sake ambaton Umma ba. Yaya Almu ya dawo ko leka inda yake banyi ba don kuwa dama ni dashi ganin nanne kawai ita ce dai tayi ta zirga-zirga zuwa can sai naji yana kwala min kira ban amsa ba na dai tashi kawai na tafi na ce mishi gani, a fusace yake magana me ya faru tsakaninki da Lailatu yau a gidan nan? Na ce babu komai ya kara fusata babu komai kamar yaya? Wannan ciwon da ki ka jijji mata fa kamar wata maiya? Me tayi miki ki ka buge ta? Kina nufin don takamar kina da karfi sai ki buge ta 'yarki ce? ke wake dukanki, to ba zan yarda ba don haka zaki yi mamakin matakin da zan dauka kan wannan abin da ki ka yi zaunar da ke zanyi ta rama dukan da ki ka yi mata a gabana, na daga ido na kalle shi nayi murmushi nace wannan shine tatsuniya, na tashi zan fita daidai ita kuma ta shigo saboda kiran da yayi mata naga bata da shirin kauce min a hanya nayi maza na hankada ta ta fadi a kasa don bata yi zaton zanyi mata hakan ba 50 a gabanshi na wuce na shiga falona, ya biyo ni yana fadin in baki yi hankali dani ba za ki raina kanki, da sauri Baba Talatu ta shigo ta shiga tsakanina dashi tana bashi hakuri, cikin kuka na ce mata bar shi ya buge ni Baba kar ki hana shi dukana bar shi ya ramawa Lailatu dukan da nayi mata ai uwar 'yarshi ce ni kuwa fa? Ina fadin haka Baba Talatu ta durkusa da guiwowinta biyu a Rasa tana kuka na wuce naje na shige bandaki na zauna nayi kuka sai da na gaji sannan nayi wanka tare da alwala na fito. Da daddare bayan yaya Almu ya tafi kai Lailatu da Rabi'atu asibiti saboda wai itama har da ita na daka naje na kira Baba Talatu a dakinsu ta biyo ni muka dawo wurina, na shaida mata abin da na shirya zan yi, cikin sanyin jiki ta kalle ni ta ce min amma da kararshi gida kika kai aka tsawatar mishi ina ganin da yafi, na ce ba zan iya ba ba zan je ina bata shi a gaban iyayenshi ba. Tunda akayi haka na kama kaina sosai girki gida dai gaba daya na daina yi sai dai in sa masu aiki suyi, kullum kuma bana wani cewa ga wata rana ta girkin Lailatu yaya Almu kuma ko kallon inda yake bana yi balle inje ina yi mishi wata magana in dai na ce mishi ina kwana ina gajiya to 51 shi kenan sai kuma gobe. Cikin raina dai nasan abin da nake shiryawa. Rannan bayan fitar Yaya Almu da rana sai nayi mishi waya na. ce mishi lalura ta same ni yanzu zan fita, ban jira naji amsar shi ba don nasan cewa zai yi bai yarda ba, nayi maza kuma na kashe wayar nayi ficewata daga gidan naje na gama abin da zan yi na dawo sai na same shi a tsakar gida a tsaye cikin huci ina kika je? Nayi maza na bude jakata na debo mishi magunguna na nuna mishi na ce kada gwarzo da kurarrajin baki sun dame ni, ya kawar da kai daga magungunan yana fadin tun-tun-tuni da kika fita kina wurin sayen maganin kada gwarzo da kurjin baki? Na ce eh na shige dakina ban sake sauraronshi ba. Wata guda bayan wannan loka cin ina kwance a dakina da daddare misalin sha biyu da rabi sai kawai naga yaya Almu ya shigo dakina alhalin girkin na Lailatu ne, na zuba mishi ido ina kallonshi cikin, mamaki gashi kuma babu alamar walwala a fuskarshi, na zuba ido ina kallonshi cikin sauraro sai kawai naji ya ce min wai me kike nufi ne da wannan abin da kike yi min? Wai ni haihuwar nan wani ne yake ba da ita Rabi da zaki je kina yi min surkullen da ban san dalilinshi ba? Cikin natsuwa na kalle shi na ce mishi, me nayi 52 maka? Ya ce kar ki ce min ba ki san komai ba don na riga an tabbatar da cewar ke kika yi kece kika yi abin da ki ka shiga tsakanina da Lailatu duk sanda zan kusance ta in rasa karfi saboda kina tsoron kar ta sake samun wani cikin, to akwai bakin ciki ne a tsakanina da ke? Na zuba wa Yaya Almu ido ina kallonshi cikin kaduwa da kyar na iya buda bakina na ce mishi darajar aure dake tsakaninmu da kuma na iyayen da suka haife mu na yafe maka duk abin da kake yi mn na juya na gyara kwanciyata tare da cewar amma daga yau ka gama. Washe gari da safe yana wurin Lailatu ina jinta tana kuka shi kuma yana ta bata hakuri tare da yi mata alkawarin daukar mataka kan abin da ke faruwa, nasa makulli na kulle wurinaa na kira Tanbai na bata kudi na ce su raba na kuma kira Baba Talatu muka fice daga gidan. Ina zamu uwardakina? Na ce mata ke dai zuba ido kawai ki gani Baba ta ce to. Titin Sultan na kaimu na yi tafiya ta cikin layin dake tsakanin bishiyoyi banyi wata tafiya mai yawa ba na saki babban titin na koma kan wanda ya nemi yamma gaban wata katuwar katanga naje na tsaya nayi bon maigadi yazo ya bude min kofa na shige ciki, sai da ya rufe kofar 53 ya biyo bayana muka gaisa sannan ya koma wurinshi nima na nufi cikin gidan sosai sai da naje muka gaisa da matar gidan dake zaune a bovvs kwatas wacce ta maigidan ce sannan na dawo nasa makulli na bude asalin gidan muka shiga ciki ni da Baba Talatu ajiye jakata kawai nayi na shige wani daki mai bandaki nayi alwala nayi sallah raka'a biyu nayi addu'o'ina na shafa sannan na fito na samu Baba Talatu ita kadai a falo, tana zaune sai kalle-kalle take yi. Na kalle ta nayi murmushi na ce gidan da na saya ne wannan Baba hannu biyu ta saka ta dafe kirjinta alamar kaduwa da mamaki na ce mata kishiya ce ta koro ki Baba sai ki ka zo kika yi renona a yau ke uwata ce duk inda zani tare dake zan tafi, tunda nima kishiyar ta koro ni yanzu sai kije ki debo mana 'yan jikokinki guda biyu ki kawo mana su taya mu zaman gidan nan. Baba Talatu ta zuba min ido cikin mamaki tana kallona, ke ki ka sayi gidan nan kika gyara shi haka uwardakina? Na ce mata eh Baba ko ba ki yarda ba ne? Ta yi maza ta ce a'a uwardakina ai ba ki da irin wannan wasan na dai kara jinjinawa al'amarinki ne nace mata tashi ma muje kiga wurin sosai na zaga da ita wurin na nuna mata 54 ko'ina ta yaba cikin murna da addu'o'i masu dadin 1i sai kuma naga ta fashe da kuka. Nayi maza na tambaye ta dalili sai ta ce min to Babangida fa? Na kalle ta cikin sanyin jik na ce mata to yaya zanyi dashi Baba? Ba zan iya wannan zaman ba ai gara kawai muyi nesa da juna sai wajen yamma nayi wa Umma text a dalilin na kasa boye mata kaina don nasan zata shiga tsananin damuwa ina tura mata text dn kuma nayi maza na sake rufe wayata. Ni da Baba Talatu muna zaune abinmu zamanmu gwanın dadi hankalinmu a kwance babu wata fitina girkinmu kawai muke yi muci1 sai muyi kallo in dare yayi mu kwanta da wuri saboda biyu da tabi nayi zamu farka ba kuma zamu sake kwanciya ba sai garı ya waye, bayan sallar asuba. Tun muna da kwana hudu a gidan Baba l'alatu ta sanya ni a gaba wai sai lalle na bude wayata da tata da na rufe don a san inda muke ai ko ba komai a yanzu tasan Yaya Almu ya gane kurenshi kan abubuwan da yake tayi min, nayi murmushi na ce Yaya Almu ai yanzu Lailatu da yarta ce damuwarshi ta ce wanc shi don dai kawai yana ganinki ne. Baba Talatu tayi matukar kaduwa da ganin gidan da na mallaka na kuma gyara sannan na 55 kawatashi da kayan alatu muna zaune da ita a bayan gidan cikin harabar dake baya shan iska muke yi ta kalle ni ta ce min, ni kuwa uwardakina yaya akayi ki ka samu ki ka mallaki wannan wuri haka? Nayi murmushi na ce komai nawa na sayar Baba har da sabuwar motar da Baba ya bani da duk kayan kwalliyata ko wannan sarkar dake jikina abin da yasa na barta don Umma ta ce min ta mahaifiyata ce na kuma hada da ajiyata ta tuntuni, Baba tayi murmushi addu'a kawai take yi ita kam ta gamsu ta yarda cewar wai ni din ja ruma ce don rago baya iya yiwa kanshi maganin abin takaicin da ya dame shi. Satinmu biyu cif a gidan rannan ina kwance a daki bayan na idar da sallar walaha sai kawai na mika hannu na dauko wayata dake ajiye kan mirrow nasa hannu na bude wayar nan da nan sai ga sakonni suna ta shigowa da sauri har wajen guda biyar, sakon da naga numbar Baba akai na fara budewa ga abin da na gani: Anya uwata kin kyauta min wannan abin da kika yi? Kafin in kai karshen sakon sai kawai ga wayar Yaya Junaidu ta shigo kasa bijire mata nayi don haka na daukc ta da sauri ya tambaye ni kina ina 56 ne Adawiyyah? Na gaya mishi na maida wayar na ajiye. Awowi biyu bayan sai kawai naji wayar yaya Junaidu yana shaida min 1sowarshi kofar gida, nayi maza na ce wa maigadi ya bude mishi, banyi zaton ganınshi tare da wani ba don haka nace ya shigo falon sai kawai na ganshi tare da Baba. A kidime na durkusa a kasa ina. yi mishi sannu da zuwa, bai amsa ba sai ya ce min wuce mu tafi ban yi magana ba nayi maza na bi bayanshi zuwa cikin motar da suka zo a ciki, shima yaya Junaidu ya gama kalle gidan ya taso Baba Talatu a gaba suka zo suka shiga ya fara tuki, har muka isa gidan Yaya Almu babu wanda ya ce komai in ban da ni da nake ta faman kuka saboda na gane maidani zai yi. Kai tsaye Baba ya tasa ni a gaba har cikin falona shi da Yaya Junaidu zuwan shi

Chapter 3 of 8