Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 8
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [6/20, 9:22 PM] Hafsat C Sodangi: WACECE NI? 4 Na Haj. Hafsat C. Sodangi (Mrs. Yunus Abdullahi Dabai) GODIYA Godiyata har kullum ga Allah take Madaukakin Sarki, gwani mai hikima cikin dukkan ayukanshi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugabanmu Annabin karshe, Muhammad (S.A.W) da Alayenshi da Sahabbanshi da wadanda suka bi tafarki na gaskiya har zuwa ranar Alkiyama, amin. Godiya mai dinbin yawa gare ku Makaranta littafin nan na kusa da na nesa na gode da irin kulawarku, Allah kuma ya kara zumuncin dake tsakaninmu ya kuma saka muku da mafificin sakamako amin summa amin. TUKUICIN LITTAFIN NAKI NE Yar uwa rabin jiki, Hajiya Khadija C. Sodangi (Mrs Nasir Kiru) SADAUKARWA Sadaukarwar littafin taku ne makaranta littattafaina, na nesa da na kusa na gode da irin kulawar da kuke nunawa rubutuna, na gode. JINJINA Jinjinar taku ce. Rabi'atu Abdul One Muhammad (Adawiyya) Rabi'atu Barau Potiskum (Amarya) Rahi'atu Ibrahim Gusau (Rabi) 3 Rabi'atu Bashir Sambo Rabi'atu Maikudi lafiya Rabi'atu Muhammad Aliyu GORO Goron littafin naki ne yar uwa, aminiya, Hajiya Lami Nasiru Goshi, na gode da kulawarki. JINJINAR LITTAFIN NAKA NE MIJINA Alhaji Yunusa Abdullahi Dabai, babansu Maryam, Aisha, Yunus da Abdulmajed, Ubangiji Allah ya saka maka da alhairinsa, amin. Hakkin Mallaka Hakkin mallakar littafin na Marubuciyar shi ne; HAJ. HAFSAT CHINDO SODANGI (Mrs Yunus Abdullahi Dabai) GORON NAKI NE Zuhuriyya Ibrahim Usman Zaria KINA RAINA Diyata Hafsat Abubakar Mamadawa GAISUWAR SADA ZUMUNCI GARE KI Halima Salihu Kwayakusur Maiduguri, Borno State. 4 YABO Yabon naki ne Aisha B. Dahiru (Mrs Shehu Tijjani) 5 Littattafan SODANGI: NAGA TA KAINA ABU NAKA HATTARA GARIN BANZA DAGA KIN GASKIYA DUK DAYA DA KAMAR WUYA YIWA WANI RABON KWAD0 WACECE NI? KIFI NA GANINKA... MAI UWA A GINDIN MURHU... 6 WACECE NI? 4 D uk da ban wani samu isasshen bacci a cikin daren ba, ga gajiyar wahalar biki ga rashin bacci da suka hadu suka haddasa min ciwon jiki mai nukurkusar kashi. Da gari ya waye na yi kokari na fito bayan na idar da sallah na shiga kicin na fara shirya abin karyawa saboda Ango da Amarya da kuma sauran Jama'ar dake gidan. Tunani sosai nayi don in shirya abin da zan gamsar da mutane, sai da na dama kunun gyada na shinkafa nayi alala sannan na shirya potato da corned Beef ga abubuwan da nayi amfani da su: (1) Dankalin Turawa manya takwas (2) Butter cokali takwas (3) Albasa guda biyu manya (4) Naman jajjagagge daidai kima. (5) Kayan kamshi dan madaidaici (6) Dessert Apple guda biyu manya Da yake abincin nawa bai wuce na mutum hudu ba, to ga yanda nayi na sarrafa komai, wanke dankalin nan nayi sosai ya wanku da kyau ba tare da na fere shi ba, na ajiye shi wuri mai tsabta sai da ya bushe sannan na goga mishi butter na dora shi kan bakin sheet na saka sh1 a oven ya gasu na kusan awa daya cikin madaidaiciyar wuta sai da naga ya gasu 7 Sannan na ciro su na kwakule cikinshi sai dai na kiyaye ban lagabar dashi ba ban kuma huda wani bari ba, na kawo jajjagagren naman nan na hada da wannan garin dankalin da na kwakwale na hada da maggi yankakken apple din nan da kayan kamshi na cakuda shi da albasar da na soya cikin butter tayi laushi sannan nayi ta cusawa cikin dankalin nan sai da na gama maida shi ciki gaba daya na sake sanyawa a oven ya yi ta gasuwa kafin na sake ciro shi na sanya shi cikin kwanon da na tanada mai tsabta. Ina cikin kokarin dora ruwan zafin da na tafasa cikin flask sai ga Baba Talatu ta shigo sannu da aiki uwar dakina, na cc yauwa Baba kin shigo? Ta ce mun ch, ta kuma kara marsowa kusa dani alamnar wata magana zata gaya min, don haka na kara bata hankalina. "Kinga idon wannan yarinyar kuwa? ani mirsisi da ita ni nace anya ma ihun nan da take tayi jiya na kama hannunne kuwa da gaske? Banga alamar ta kai budurcin nan ba." Na ce "Baba" Ta ce "Na'am." Na ce "Mu bar wannan magana." Ta ce "To." Ta shiga taya ni kintsa wurin zuwa can sai na sake jin ta ce min "in banga maigidan yayi wankin kayan shimfida ba irin na wancan karnon, anya budurcin nan..Nayi maza na katse ta na ce "Baba Talatu daina yi min wannan maganar, tana fadar min da gaba, don bana son jin ta wannan abin 8 da ya shafe su ne ita dashi bai shafe ni ba." Daga bayana na ji muryar Yaya Almu yana cewa, "menene bai shafe ki ba? Baba Talatu tayi maza ta fita ni kuwa na soma gaishe shi bai wan1 amsa ba ya kara matsowa gab da jikina, me zan samu Rabi? Na sunkuyar da kaina don bana son kallon fuskarshi, na ce duk abin da kake so akwai, ya ce 'to in dai haka dan fara bani bakinki in ji kwananshi, in ji laushin la6 6anki, nan da nan wani abu ya tokare ni a zuci har ban san lokacin 'da na bude baki na ce mishi, uh'uh in baka ji wadannan ba ai ka ji wasu..bai bari na karasa ba ya ce mun kul, kar ki rinka irin wannan maganar in ina tare dake ina tare dake in bana tare dake kar ki yarda zuciyarki ta raya miki komai ki dai yarda kawai a duk inda nake ina kewarki ina kuma son ganinki a gefena, na ce haka ne. Na kammala shirya komai kan tire na dauko na barwa Yaya Almu wanda zai taimake ni dashi juyowan da zanyi sai kawai naga Lailatu tana lekowa ta matsin kofarta tana kallon abin da ke faruwa tsakanina da Yaya Almu. Na yi kamar ban ga abin da take yi ba, na wuce naje na shirya komai a falon shi na sake dawowa na shiga dakin nata nace mata Amarya ina kwana? Ta ce min lafiya, amma dai sunana Lailatu, na yi kamar ban ji ta ba 9 na ce mata ki zo falo maigidan yana jiranmu, na juya na fita na barta. Mun zauna muna karyawa dukanmu muna kuma hira dukanmu saboda kokarin da Yayan ya yi wajen ganin ya tsoma kowa cikin maganar tashi, da aka natsu sai ya kalle ni ya ce mun Rabi ga Lailatu nan na sani kishiyarki ce, to amma zan so ki maida ita yar uwa ki yarda cewar taki ce zaki yi mu'amalla da ita bisa adalci ba don kowa ba sai don ni, tunda kin san ni na kawo ta na kuma san za kı 1ya y1 min adalcin maida duk wani abu nawa ya zama naki ko da kuwa ba akan son ranki yazo ba, saboda kin san duk wani abin da ya shigo gidan nan arzikinki yazo ci in kuma mallakarshi nayi to na ki ne." Cikin natsuwa ba tare da zuciyata ta raya komai ba, na ce mishi haka ne, sai kuma ya juya wajen Lailatu ya ce mata, ke Lailatu ga Rabi nan matata ce ko babu aure tsakanina da ita kuma 'yar uwata ce na kuma san duk yanda kishi yakai da zafi cikin zuciyar ta a ifin halinta da na sani da kuma irin tarbiyar da aka yi mata zata yi iya kokarinta wajen ganin tayi miki adalci, to ki bata hadin kai ki bata girman da ya dace da ita don ina bukatar ganin kun zauna lafiya kun samu fahimtar juna a tsakaninku. Wannan shi ne sha'awata da burina game da mata biyu, ke Rabi kinji abin da na ce? Na ce mishi ch, 10 naji Allah ya taya ka riko, ya yi maza ya ce min "amin, Lailatu dai bata ce komai ba har na fita. Zuwa can wajen karfee sha biyu da rabi bayan fitar Yaya Almu, ina falona ni da Baba Talatu ina kuma hango duk abin da tsakar gida ke ciki, yayin da Lailatu ke falonta tana kallo sai ga Umma Karama da Hajiya Hairan sun shigo gida da sauri na fito ina yi musu sannu da zuwa na kuma jagorance su don in kaisu dakina duk da dai nasan Umma Karama bata taba takowa tazo gidan saboda ni ba, to amma sanin da nayi cewar duk bakon da yazo gidanmu matukar ya fara ganin Umma to ko ba wajenta yazo ba to wurinta zata fara sauke shi ta bashi ruwa da abinci kafin tasa a kai shi wurin wanda yazo, to balle Umma Karama duk yanda takai da kina dolenta ni 'yarta ce, kan idonta aka haife ni ko babu wata alaka tsakanina da Baba ta dalilin Umma kawai ita uwata ce, balle kuma inta juya ta wurin Baba ni jikarta ce har yanzu kumna surukarta matar dan mijinta, amma bata şhiga dakin nawa ba sai ta ce min na rako Hairan ne tazo taga dakin Amarya, bari mu fito tukuna. Cikin murmushı na ce mata to, na shiga kicin na shirya abinci na bisu dashi zuwa dakin Lailatu na shiga na same ta tana cewa, in ana zancen aure ai babu maganar Zumunci a ciki dukanku daya ne dukanku daidai kuke in ta dauro ma kwanan nan sai ki kwace shi 11 tunda ke kam ai matar haihuwa ce kadan ya rage banyi 6ari ba, nayi maza na shanye bugun da zuciyata tayi nayi sallama suka amsa na shiga na kai musu abin da na shiryo musu na kuma gaishe su har na tsaya ina tambayar Umma, Umma daga Legos ku ke ne? Ta ce a'a a satin nan ne dai zan tafi na ce ai, na tashi na tafi nawa wurin da suka gama abin da zasu yi kuwa daga tsakar gida ta yi mun sallama wata kilama da ban ga fitowarsu ba da tafiyarsu kawai suka yi ba tare da sunyi min sallamar ba, Baba Talatu ta kalle ni ta ce tafdijam, wannan mata da rashin mutunci take in ban da Hajiya ta samu da ba a san irin tsiyar da ta yiwa mutane ba, na yi dariya kawai na tashi na nufi kicin don shirya abincin rana. Ina shiga kicin din sai ga Yaya AlImu ya dawo cikin kicin din ya biyo ni, na kalle shi cikin murmushi na yi mishi sannu da zuwa, ya kalle ni cikin wani murmushin mai gamsarwa ya ce min ran uwargida ya dade, na daga ido na kalle shi kamar in yi mishi wata magana in gaya mishi bana son sunan sai kuma na fasa na sunkuyar da kaina kawai da nufin in kama aikina, sai na ji ya matso kusa dani sosai yana fadin ke uwargida ce Rabi duk da mas'alar da muke da ita kuma zuciyata tana raya min cewar kcce uwar 1yalina, musamman ma da yake a yan kwanakin nan ina mafarkin kin haifar mun ya mace, na yi murmushi saboda jin dadin 12 kalaman nashi, na jawo kayayyakin da na hada zan soma aiki na sai ya ce mun me za ki shirya mana ne yanzu kuma? Na ce mishi stuffed chiken (2) in ba ka manta ba ka taba cin 1), din ya ce ch ban manta ba Rabi duk da dai na cishi ne tun ina saurayi, to gaya min me dame ki ka tanada? Na ce mishi gasu nan a gabanmu kana kalio sai dai hakan ba zai hana in gaya maka sunayensu ba (1) kaza, butter, shinkafa, kayan lambu, nama, curry, sai kuma maggi. Juyowan da nayi na hango Lailatu tana leko mu ta matsin kofarta yasa na ce wa yaya Almu jeka wurin amarya yaya in na gama zan zo in same ku bai yi musu ba ya juya ya tafi. Na kama aikin abincin san zuciyata a kun tace saboda ba wastsakewa nayi daga zafin kishin dakc cina ba, gashi kuma na ganc ita Lailatu bata shigo gidan da niyyar yarda da tayin zaman lafiyar da ni da Yaya Almu muke gabatar mata ba idonta da hankalinta gaba daya to kan mu a mallata da mijina take duk da cewar shekaran jiya ne kawai ta shigo gidan wannan in ta yi kwanaki yaya za'a kwashe da ita? Wannan ita ce tambayar da tazo cikin zuciyata, gani kawai nayi na gama girkin amma ban san yanda aka yi na hada komai ba, saboda tsananin tunanin da na samu kaina a ciki har na kammala na shirya komai kan tire na dauko na nufi falon Yaya Almu ban san da wani a ciki ba don haka ban wani 13 tsaya yin doguwar sallama ba na tura kaina cikin falon jikinshi na same ta tana yi mishi wasu abubuwan da nayi maza na kawar da kaina daga gare su, naje na ajiye musu abincin duk da ba yunwa nake ji ba na zauna muka ci tare don kar in basu damar da zasu gane na samu wata damuwa, sai da aka gama na tashi na tafi wurina. Da daddare ma na sake shirya tuwon Semovita miyar kuka da kuma farfesun bindin saniya, ina idar da sallar Isha'i nayi wanka na hau gado na na kwanta da nufin in yi wadataccen baccin da zan ji dadi in samu naatsuwa a jikina sai dai kuma kash! hakan bai yiwu ba ina rufe idona da nufin yin bacci sai inga Lailatu a jinshi tana tuhumarshi irin dai yanda na same ta tana yi mishi sai kuma in ji Zuciyata tana raya mun cewar yanzu haka ma abin da ke faruwa a tsakaninsu kenan, na yi kuka rannan har na gaji saboda ganin abin da ban taba ba kan na farko ken an da naga wata mace tana taba Yaya Almu a tsawon rayuwata tare dashi. Nayi matukar kokarina na shanye komai na hadiye duk wani abin da ya dame ni na yiwa Yaya Almu da Amaryarshi duk wani abin da ya dace in yi musu na kyautatawa a tsawon kwanaki bakwai din da yayi a dakin nata, duk da kasancewar kwanakin masu tsanani ne kwarai a gare ni. 14 A haka rannan ya dawo dakina bai jira naje nashi dalkin ba wurina yazo ya same ni sai dai duk Rokarin da nayi na in nuna mishi bani da wata mas'ala na kasa sakin jikina dashi sosai, ya zuba min ido yana kallona saboda ya gane abin da nake nufi a hankali cikin natsuwa da murya kuma irin ta rarrashi ya ce min auren da na yi fa bai canza komai ba tsakanina dake sai ma kara wa da ya yi saboda a yanzu babu abin da nake tausayi kamar ki ina ji ya ambaci tausayi sai na ji zuciyata tana raya min cewar saboda yasan ya cuce ni, nan take na kama yi mishi kuka, na yi kuka irin wanda ban taba yi ba, na yi kukan da tun yana rarrashina cikin tausayi har ya gaji ya ture ni ya fita daga dakin ba zan iya wannan zaman ba ba zan iya ba, abin da zuciyata take gaya mun kenan, na mika hannu na kira Umma da nufin in gaya mata cewar ta yafe mun tayi hakuri ta bar ni in yi abin da naga zai fiye min sai na ji muryar Yaya Junaidu yana cewa, Hello Adawiyya yi magana magana, menëne? Ashe lambobinshi na danna ban sani ba nayi maza na kashe wayar na maida ita na ajiye sai dai kuma kama ruri tayi shi ne ya sake bugowa cikin natsuwa nace mishi kayi hakuri Umma nayi nufin kira ya ce da wannan tsohon daren za ki katse mata baccinta? Na ce ar na fasa ya ce min to sai da safe, na ce to mu kwana lafiya na maida ita na ajIye sai dai kuma gari yana wayewa 15 da yaya Junaidu muka karya a gidan da sunan wai yazo ganin Amarya yayi wa yaya Almu fatan alheri ya kuma yiwa amarya kyauta sannan ya nemi 1zinin Yaya Almu ya biyo ni har cikin falona, nasiha mai yawa yayi min ya kuma nuna min muhimmancin in yi kokari ina boyewa Umma damuwata saboda ita din ta riga ta fara girma na ce mishi to ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min in kina da damuwa rinka gaya min zan taimake ki da shawarwarin da zasu taimake ki, na sake ce mishi to ya sake kallona ya sake tambayata yanzu menene damuwarki? Na ce mishi ina so in yi nesa da Yaya Almu ina so in daina ganinshi a kusa dani, ya sake zuba min ido cikin natsuwa ya ce min amma kin san mijinki ne wannan aure da yayi kuma ba laifi yayi ba halal dinshi ne, na ce eh, ya ce to kar ki yawaita tsananta al 'amarin a wajenki ki dauki komai da sauki zan kuma shirya miki tafiya Umra don ki je kiyi ziyara a Madina na ce mishi to. Sati guda bayan nan komai ya kammala na shirye-shiryen tafiyata saura tashi kawai, amma sai Yaya Almu ya ke kasa kasa ya ce babu in da zan1 saboda ba a nemi izininshi ta hanyar da ta dace ba, hanyar da aka bi wajen sheda mishin ya fi yi mishi kama da sanarwa maimakon neman izini. Ina zaune a dakina cikin bakin ciki da takaicin abin da ya yi na neman ya kuntata min tunda sau 16 nawa Yaya Junaidu yana shirya min irin wannan tafiyar bai tába cewa bai yarda ba sai a wannan lokacin, wannan neman kuntatawa ne kawai abin da zuciyata ta raya min kenan. Ya shigo dakina ya same ni don ranar ma girkina ne, na daga ido na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi me ka ke nufi da hana ni tafiyar da kayi? Ya cc abin da nakc nufi kenan ki gane zan iya nukurkusa ki in saki bakin ciki matukar ba ki janye daga matakan da kike dauka ba, na zuba mishi ido ina kallonshi, sai ya ce min kalle ni da kyau rabi don ki kara gane ko n wane iri ne na iya yin rarrashi in yi alheri in kuma saka mai kyau da mai kyau kamar yanda zan ya kuntatawa in saka munmuna da munmuna in halin hakan ya kama, ina yi miki wannan bayanin ne don in fahimtar dake ki gane cewar babu abin da zai fi zaman lafiya da bai wa juna hakki dadi a tsakanina dake, na rasa abin da zan ce mishi sai kawai na kama yi mishi kuka ina tambayarshi me nayi maka Yaya Almu? Me nayi maka ka tsane ni ka ke nema sai ka gana mun azaba? Me nayi maka da zaka tsare ni a cikin gidanka ka hana ni zuwa in da zan ji sanyi bayan ba sona kake yi ba, na gama kukana na mike na wuce shi zan shiga cikin dakina in kwanta yayi maza ya mika hannu ya kamo ni na fada jikinshi zo ki gaya min abin da nayi miki wanda yasa kika ce bana sonki ina kuntata miki? In ina sonki me kike 17 so in yi miki bayan wulakancin da kike yi mun yaushe rabonki da ki gyara mun shimfida? Rannan dai dole na na yarda muka shirya da Yaya Almu saboda yayi rantsuwar ba zai yarda da danne mishi hakkinshi da nake yi ba, ganin mun shirya yasa na sake rokonshi ya bar ni in je in yi Ummara ya ce ba yanzu ba zai shirya mun hakan a lokacin da yaga ya dace, amma yanzu ga Lailatu bakuwa bai kamata in fita daga gidana in bar mata shi ba da irin wadannan kalaman nashi ya kwantar min da hankali. Lailatu ba ta yi kama da amarya budurwa mai gane al'amuran gidan aure a hankali ba komai ake yi idonta yana kan duk da haka dai ina iyakacin kokarina wajen ganin na kawar don kaina, don in samu in cika umarnin da Umma ta bani na yi mata girgi tsawon watanni biyu wai taci amarci. Rannan da safe naje zan shiga dakin Yaya Almu sai na ji ta a ciki tana ce mishi ni fa na gaji da karbe mun kudin cefane da ake yi da sunan wai ana taya ni girki, daga yau a rinka bani kudina a hannuna ina yin lissafin cefanen in an kawo sai ta girka in har abin kirkin take son yi maka da gaske ba iya yi ba, ba na son kina fadin irin wadannan kalmomin akan Rabi Lailatun rannan na gaya miki bana so maganar kudin cefane kuwa ni ban saba bayarwa ba mafi yawancin lokaci ma ni bana sanin loka cin da ake 18 kawo abubuwan da ake amfani dasu a gidan nan, na koma da baya na koma wurina na basu wuri su gama maganganunsu sai da ya gama abin da zai yi ya fito yazo wurina zai yi min sallama ya miko min kudi ya ce ku raba ke da Lailatu wannan kuma ki bai wa Baba Talatu, nasa hannu biyu na karba nayi mishi godiya naje na bai wa Baba Talatu dubu goman da ya bata tayi ta godiya tana sa mishi albarka ita kuma Lailatu naje na ce mata amarya gashi in ji maigida dubu hamsin ne amma ko a jikinta na fito abina na dawo na same shi na ce mishi dukansu sunyi godiya muka gama maganar da za muyi da zai fita sai na ce mishi zan bai wa Amarya girkinta yau tunda kaga tayi wajen kwana arba'in a gidan nan gara muci irin nata girkin kuma muji irin dandanonshi bai yi wata magana ba alamar bai so in yi hakan, ni kuwa yana fita sai na kwala mata kira amarya, ta fito tazo ta ce mun gani, sai dai ni fa sunana ba amarya ba ne, ta yi maganar tana cune da baki na ce ni kuma sunan da nayi niyyar kiranki dashi kenan, Amarya ki shiga kicin yau ki yiwa mijinki abinci ya ci, na wuce ta naje dakina na yi wanka na tsala kwalliya na fito na zauna a inuwa a tsakar gid aina kallon mu'amallar ta da kicin din nata na kalli Baba Talatu dake gefena na ce mata ina jin anjima zan bukaci shan kunun 19 gyada ko za ki iya dama min? Ta ce yanzu kuwa uwar dakina ai ba ma sai anjima ba. Da daddare ranar ina dakina naji muryar yaya Almu yana kwala min kira nayi maza na amsa na tafi kwanukan abinci na samu a gaban shi ita kuma tana zaune a gefenshi tasha kwalliya ga baki yasha jan baki ita da kwanukan abincin nata sai sheki suke yi, ina ce mishi gani ya fara fada meye sunan wannan abincin da ki ka kwaba yau? Ban ce mishi komai ba sai ta yi maza ta ce mishi ai ni na yi bai yi dadi ba ne? To bari in sake shirya maka wani ta yi maza ta suri kwanukan ta fita dasu ta koma kicin nima na juya zan koma dakina sai ya yi maza ya kira ni me yasa kika bata girki ba da izinina ba? Na ce saboda na gaji na wuce na fita na koma dakina ban tsaya a falo ba don ganin ya biyo ni dame kika gaji? Da abincin da za ki girka min in ci? Me yasa kike nema ki koyi rashin kirki da can shekara nawa ki ka yi kina yin girkin ke kadai? Nayi shiru yayi ta maganganunshi sai da naga bai gane zurun da nayi mishi ba sai na ce mishi ai nayi kokari in ma kai baka gani ba ni na gani kwana arba'in ina yi muku girki sanda aka kawo maka ni ai shekaruna basu kai nata ba ni sha tara ce a lokacin ita kuwa an kawo maka ita da ashirin da uku, ni a wancan lokacın waya rinka yi mun girki, tunda ta iya gyara maka shimfida ai sai ta iya baka abincin da zaka rinka ci, 20 zuba mun ido yayi cikin takaici sannan yaya Wani mummunan tsaki ya fita. Tun daga wannan lokacin kullum ran girkin Lailatu ta rinka dibi-dibi kenan a kicin babu abin da zata girka ya gamsar gashi ita kuma fadin rai ya hanata ta rinka neman taimakona kamar yanda naji mijin

Chapter 1 of 8