Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
kan Ummana kenan ba zan iya barin Umma ta tozarta gaban makiyanta ba, don haka dole ne in bi umarnin da Hajiya Hauwa ta bani na komawa kan al'amuran gidana da kuma mijina. Washe gari da safe na tashi bisa tsarin da na saba, na kama hidimar gidana da sassafe ina cikin kicin wajen misalin tara na safe yaya Almu ya shigo kicin din sanye da doguwar jallabiya a jikinshi ga dukkan alamu murnar ganina a kicin din yake yi, me kike shirya mana ne? Ban kalle shi ba na ce mishi waina ce da miya ga kuma kunun gyada, ya ce to kin kyauta Rabi, kamar kin san cewar da yunwa na tashi da safen nan. Daga yaya Almu har Baba Talatu ji dani suka rinka yi suna ina aka saka dani saboda 119 ganin da suka yi na wastsake daga matakin da na dauka na kwana da kwanaki. Ina sallamar yaya Almu da ya shirya ya fita sai na yiwa yaya Junaidu waya na shaida mishi cewar ina bukatar ya turo min kudi don in fara sayayyar da Baba ya ce inyi, tsawon lokaci yana yi min nasiha da maganganu masu kwantar da hankali kafin ya tambaye ni abin đa zai bani, na ce mishi ba zan iya sani ba sai dai kawai yanda ya kama ina kuma so a bani Anti Rahma don ta taya ni, ya ce to babu laifi. Anti Rahma baro gidanta tayi a zo Kaduna ta zauna tsawon kwanaki hudu sai da muka gama hada komai na kayan kamu da na aure ta kuma jagoranci wadanda ta gayyató suka rakata suka je suka kai kayan sannan ta kama hanya ta koma gidanta. An kai kayan washe gari da sašsafe ina tare da yaya Almu a dakinshi baba ya bugo min waya albarka yake ta sanya min kan labarin da aka bashi na irin kayan da na hada na aike dasu yayi min addu'o'i masu dadi ya kuma roke ni in zamewa yaya Aimu kamar yanda Umniana ta zame mishi na ce to Baba. Shirin biki sosai na shiga don kuwa nasan biki za'ayi irin 'ya'yan gata yaya Almu ta 6angarenshi ba sai na tsaya ina wani dogon 120 bayani ba, to itama Lailatu ta bangarenta 'yar gata ce kwarai, mahaifiyarta ce uwargida a gidansu tana kuma yin yanda taso don kuwa amare dai-dai har bakwai akayi mata amma babu ko daya duk sun fita wadanda suka san sirrin gidan kuma sun ce Hajiya Hairan ce mai korar su don kuwa 'ya'yan da suke bari a gidan masu aikin gidan sun fi su 'yanci. Lailatu ce 'ya mace babba a wurin iyayenta a gabanta kuma akwai maza biyar, don haka ni da kaina nasan da gatanta to amma na hakura na yarda da zuwan nata na kuma shirya zama da ita zan kuma yi duk abin da zanyi don ganin bukatar wadanda suke shirin kawo ta bata biya ba, duk kuwa da na san Lailatu zata iya zuwa gidan ta haifi dan da ake bukatar samu in na tuna wannan shi ne abin da ya kan daki zuciyata har in kasa daurewa in hana idanuwana zubar da hawaye, to amma yaya zany1? In da don tani ne da tafiyata kawai zanyi in yi nesa dasu ta yanda zan kare kaina daga ganin bakin. ciki da bacin rai, to amma Umma tana son ci gaba da zamana a gidan ta jaddada min cewar tana son ganin Lailatu ta shigo ta same ni ta daukarwa Karama abin da take son dauka a gidan ina nan cikin shirin biki na sosai har ana saura kwana bakwai ayi bikin rannan da hantsi sai ga Ummana tare 121 da da Hajiya Hauwa sun iso gidan da hannu biyu na karbe su cikin murna da farin ciki sai dai abin da na gani a tare da Umma ne ya daga mun hankali ya kuma tayar mun da hankali cikin hawaye na kalle ta ina kuka na ce Umma ramewa kika yi? Maganar auren yaya Almu ne ya tayar miki da hankali haka? Umma ai zan haihu kar kiji tsoron komai babu wani wanda zai karbe miki danki daga gare ki zan kuma yi duk abin da zanyi wajen ganin na tsare.....ban karasa ba Umma ta katse ni wajen cewa kiyi bakin ciki don kinga ta samu rabu kowa yana rayuwa ne kan kaddarar da aka shirya mishi. Kwana biyu da tafiyarsu Umma ta aiko aka zo aka kwashe duk wani abin da yake cikin gidan aka maida sababbi daga sashina zuwa na yaya Almu babu abin da bata canza ba, Baba ma ya aiko mun da mota sabuwa dal, Umma amarya ma tayi min aike na wasu warawarai da zobuna wai inyi adon biki gashi dama duk sayaiyar da muka yiwa amarya bib1yu Anti Rahma ta sani nayi komai dai ina dashi kenan ga yaya Almu wanda ya tasa ni a gaba da tambaya duk da dai bani ke hidimar auren nan ba ai ya kamata ki gaya min me kike so in yi miki na fadan amarya? Na ce mishi babu komai ai su Baba sunyi ya kuma wadatar duk da haka sa da yayi 122 min kyautar wasu sarkoki guda biyu, abin dai gwanin sha'awa kamar ace bani da wata matsala amma ina? A duk lokacin da na kalli tarin dukiyar da aka tara min a dalilin auren sai inga ai ba abin da ake nema ba kenan da kamar kawo ta za'ayi don ta kamu wani abu wurin yaya Almu to da sai in ce ta makara don na rigata samu, to amma ba haka ba ne da ake nema a wurin ta babu mamaki kuma tana zuwa ta samu tunda Likitoci da yawa sun tabbatar min da cewar ni ke da matsalar da ta hana samun haihuwa tsakanina da mijina wannan shine abin da ya fi komai dukan zuciyata. Tun ana saura kwana biyu bikin gidan ya cika da mutane 'ya'yan kawayen Umma na kusa da na nesa babu wacce bata zo ba. Biki sosai Umma ta shirya ta kuma tsaya matsayinta ita ce uwar yaya Almu komai ita ke yi duk abin da ake nema ita ce mai bayarwa. Biki na kasaita akayi ta kowane bangare komai yaji nima anawa bangaren kawayen Umma ake waye dani suke 'ya'yansu ga matan abokan yaya Almu da muke ma'amalla mai dadi wadanda suka yi matukar nuna min kauna da kulawa ga yan uwa su Anti Basira da su Anti Kubra, Anti Aina'u, Anti Rahma kam babu abin da zan ce mata ko da yake ban yi mamaki ba 123 saboda irin tsayuwar yaya Junaidu kan al'amarina. Ranar daurin auren wuni yayi yana yi min waya yana tambayata babu dai matsala ko? In ce mishi a'a babu damuwa sai ya ce too kiyi hakuri ki kara akan wanda nasan kina dashi, in ce mishi to anyi daurin aure yaya Almu ya zama ango, anyi shagalin biki na halarci duk liyafofin da aka shirya na kuma yi duk abin da ya dace inyi wadanda basu san Lailatu ba sai a wannan lokacin sunyi ta gaya min cewar ai babu abin da zata nuna miki sai farar fata, bata kaiki kyau ba bata kaiki tsayuwa ba bata kaiki iya kwalliya ba, da kuma yin kyau da kwalliyar aike mai kyau ce Adawiyyah dolen miji ya soki ko don irin abin da aka kyautata miki halittar ki dashi, nayi murmush1 kawai na kalli Naja'atu yar Hajiya Hauwa da muke kai daya da ita na ce mata Naja, ba kyau yaya AImu yake nema ba wurin mace ko iya kwalliya haihuwa yake so ita yake nema in har ya same ta to bana zaton zai tsaya kallon wadannan abubuwa da kika lissafa tayi maza ta ce to ai kema zaki haihu lokaci ne kawai na ce mata abin da nake ta karfafa zuciyata dashi kenan to amma yau kam na karaya zuciyata kuma ta gama tsinkewa da al'amarin na kama yi mata kuka. 124 Da sauri ta dafa kafadata tana ta faman gaya min maganganu masu kwantar da hankali tana fadin ba fa Likita ke bada haihuwa ba Adawiyyah tsaya kawai kan yin addu'a a gida anyi wunin biki cikin shagali mai yawan gaske da gude-gude daga bangaren dangin amarya anawa bangaren ma ina cikin hayyacina da natsuwata kallon, komai nake yi don tun kafin a watse a barin da Lailatu na riga na gane lalle anyi mun ki shiya na kuma yarda cewar Umma Karama tana da dalilinta na jin sanadin auren yaya Almu da wannan yarinyar, duk abin da ke faruwa dai ban cewa kowa komai ba, jan bakina kawai nayi na tsuke ina kallon komai da idona, zuciyata kuma tana yi mishi irin fassarar da ta dace dashi, nayi kwalliya a bikin kwalliya kuwa irin ta burgewa irin wacce zata shaidawa Lailatu da duk wani nata duk abin da take takama dashi na gata to bata kama nawa kafar ba, don kuwa yanda na rinka canza zannuwa haka na rinka canza gold din da nake sanyawa, tsawon kwanakin bikin kuma ban fasa zuwa wurin mijina ba don kuwa abin da ya nemi inyi mishi kenan. Ranar budan kai da yamma iyayen amarya suka kawo ta falona da yamma kamar dai yanda al'ada take na kaiwa uwargida Amaryarta don 125 bada amana sai dai kuma su da suka zo cewa sukanyi to ga amarya nan min kawo ta gidan mijinta ta kuma zone don ta zauna ba wai ta leko ba ne zata koma. Hajiya Hauwa ta kalli kanwar uwartata mai wannan bayani tayi murmushi ta ce Hajiya joda kenan ai mu bamu za'a kawowa amarya ayiwa wannan jawabi ba, mu kam ai an sanmu da barin kishiya ta zauna matukar zata iya zuba ido tayi hakuri kin kuma san ance kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi, don haka in har kun kwabi 'yarku kunyi mata tarbiya to ni kuwa ina tabbatar miki da cewar zata zauna in har zata iya gani ta kyale, ana gama wannan bayani ta sake 6alla bakin jakarta sai da ta sake jefa wani cingam din a bakinta sannan ta zaro daurin naira dari biyar-biyar ta mika musu ta ce Adawiyya ta sayi bakin amarya suka tashi suka tafi. Yamma nayi yan uwa da abokan arziki suka Soma yin sallama suna tafiya gida da fahimtar juna in ce amin, ta bangaren amarya kuwa duk wacce zata tafi sai ta fito tsakar gida sai ta daga murya ta ce to mu zamu tafi kan badi kuma muna sauraron a kira mu suna don ba mun kawo ki ba ne kawai don ki rinka ci kina juyewa a masai mun kawo mishi ke ne don ki cika mishi gida da 'ya'ya tunda haihuwa kam ai kin gaje ta 126 sai kuma akwashe da dariya a tafa hannu kafin a rangada wata irin matsiyaciyar guda. Suma su Hajiya Hauwa da Hajiya Furera suka yi shirin tafiya kan su tafi kuwa sai da Hajiya Hauwa ta ta cafke kunnena ta rike tana fadin bari ni da kaina in kara jaddada miki cewar kwana bakwai ango yake yi a dakin amaryarshi budurwa don haka kar in ji kar in gani, nayi murmushi kawai na ce mata to Umma ku gaida gida, Allah ya kara girma suka ce amin Suka kuma fita da kwarin gwiwa saboda ganin irin sallamar da muka yi. Gaba daya an gama tafiya daga ni sai Baba Talatu da ta gama gyara min wajena muna zaune ne tana matsa min kafafuwana tare da jaddada min irin kokarin da take cewa wai nayi. na daga ido na kalle ta cikin natsuwa na ce mata shi kenan Baba yau burin yaya Almu ya cika ya maidani uwargida a gidanshi. Tayi maza ta ce babu komai dama abin da ya dace dake kenan, kiyi shugabanci ki jagoranci iyalin gidanshi baki ga kuma yanda hakan ya kera miki kwarjini fa kika ce Baba? Zubewar da nayi fa'? Ta ce ai bai baiyana kowa ya gane ba saboda ke dama jikinki mulmulallen jiki ne gashi kuma kin kame babu alamar wata damuwa a tare dake. Shigowar yaya Almu ta katse hirar 127 tamu, tayi mishi murnar tashin taron lafiya kamar yanda nima nayi mishi sannan ta tashi ta tafi wurinta. A natse yaya Almu ya kalle ni ya ce mun nasan agajiye kike to amma kuma yaya zanyi?2 Nayi maza na ce mishi me ya faru? Ya ce matsananciyar yunwa nake ji. Cikin hanzari na mike na shiga kicin don shirya mishi abin da zai ci mcat roll ga abubuwan da nayi amfani dasu. (1) Naman cinyar baya na yanka sa (2) albasa guda uku (3) mangyada ko butter, (4) murmushen biredi (5) kawai guda daya (6) tumatur manya guda hudu (7) maggi. (8) karas (9) Green beans, sai (10) kayan kamshi Na fara da yin amfani da wuka mai kaifi na rinka yiwa naman nan yankan faifai tanfar dai irin na masu tsire sai dai wannan yafi na mai tsire fadi tsayi da kuma kauri, sannan na dora pan a kan wuta na soya butter da albasar da na riga naa yanyanka kanana na kawo sauran kayaiyakin nan amma banda karas da green beans na zuba, sannan na koma murza naman nan akan rolling boad da kwalba har sai da na ga yayi fale-fale sai kuma na soma debo kayan cikin pan din nan wato su murmushen biredin nan da maggi da albasa chese da na hada da 128 butter ina shafe fallen naman na gaba da baya ina ajiyewa har sai da na gama da su duka sannan na koma na nade su kamar tabarma ina jefawa cikin ruwan buttern da na dora yayi zafi akan wuta na kuma zuba albasa har na gama soye shi tas sai da yayi jajajaja sannan na zuba tumatur da kavan kamshi a ciki na kuma zuba ruwa kadan na rufe tukunyar ya dahu sosai, sar na kawo plate masu kyau na shirya yankakken karas din nan da green beans a ciki sannan na tsamo roll din naman nan na jera su akai romon kuwa sai da yayi kauri tukuna shima sai na juye cikin plate din wato kan roll din naman. Sai kuma abin shan da na shirya mishi, ga abubuwan da nayi amfani da su. 1. Tanjarine guda takwas (8) 2. Sugar 3. garine captard cokali daya 4. Madarar gongoni guda daya 5. Madarar shanu rabin kofi.. Na kammala komai cikin natsuwa na dauko shi akan tire nazo da shi falona in da na bar yaya Almu na same shi kishingide har bacci ya soma daukarshi, saboda tsananin gajiya cikin natsuwa na tashe shi na ce mishi ga abincin an kawo ya mike zaune cikin yanayin gajiya da wahalar da yayi, ya kalli abincin cikin sha'awa da farin ciki 129 yayi min godiya tare da addu'o'i masu dadin ji har ya mika hannu zai fara ci sai na ce mishi a'a ango muje dai can sabon masaukin naka babu mamaki itama amaryar tana tare da yunwar yayi maza ya mike cikin jin dadin maganar da nayi yana fadin, gaskiya ne Rabi, lalle kuma na yarda uwargida ta sosai kike shirin zama. Na bi bayan Yaya Almu da tiren abincin a hannuna naje zan shiga dakin sai naji Lailatu tana magana cikin shisshikar kuka giurkina ne fa yau amma kaje ka mike a dakinta har kana yin bacci, gabana ya yanke ya fadi da jin ana yiwa yaya Almu togaciya da kashedin zaman shi a dakina, karo na farko kenan da aka taba yin hakan a rayuwarmu. Sallama sosai nayi kafin aka iya amsawa har nayi kamar in juya da tiren dake hannuna, sai kuma na fasa nayi ta jira dai har na samu aka bani izinin shiga ita kam fuskarta a daure babu alamar wasa shi ne dai yake ta kokarin murmushi da jawo hankula wuri daya don ya daidaita al'amura. Na kalle su nayi murmushi na ce amarya sauko daga nan don kiji dadin ci ban jira amsawarta ba na juya na koma dakina inda na samu Baba Talatu tana jirana, to ke kin kai musu abinci kin dawo kin hau gado kin kwanta 130 ke ba za ki ci komai ba ne? Na ce bana jin yunwa Baba cikina a cunkushe yake ban ci komai ba tun safe in ban da ruwan sanyi da nayi tasha amma kuma har yanzu ban ji kamar ina bukatar ci ba fatana dai kawai bai wuce in samu in yi bacci ba. Baba Talatu ta kara matsowa kusa dani tana yi min tausa tare da fadin uhun ai namiji da kike kallonshi kyale shi kawai ya kamata kiyi in har kika ce zaki biye mishi to sai yayi dalilin da zaki rinka tafiya kan hanya kina sanbatu, baki san lokacin da kika yi hakan ba mutanen gari kuma maimakon su tausaya miki sai suce dama aka hada su bada ke ba? Tunda in kishiya ce ai ba a kanki aka fara yinta ba, ai ni nan da kike kallona ni na san kishiya tunda dai ita ce tayi dalilin da na hakura da zaman aure tun a shekaruna na kuruciya ta raba ni da mijina, bayan kuma ina sonshi kamar inyi yaya? Cikin sauri na zubawa Baba Talatu ido ina mata kallo na ban mamaki da kaduwa na ce amma baki taba sanya wannan labarin cikin jerin labaran da kiká yi ta bani ba, taja wata irin ajiyar zuciya mai karfin gaske ta ce uhun to wannan labari in ba dalili yayi dalili ba me zai sa kayi ta bai wa yara shi? Kamar yau din nan dai da hali ya kama ai kinga zan gaya miki 131 komai, na kasa kunnuwwa na saki baki na zare ido ina sauraron labarin da Baba Talatu take shirin bani, sai kawai na jiwo ihun Lailatu daga tsakar gida tana kiran taimako, da iyakacin Rarfinta take fadin waiyo ta shiga uku waiyo za'a kashe ta, sanin da nayi na baro dakin tana kunkumin girkinta na yaya Almu yazo ya zauna a nawa dakin sai nayi nmaza na zabura zan kai mata taimako ga zatona maganar ce tayi tsanani har yaya Almu ya tunzura ya rufe ta da duka, sai naga Baba Talatu tayi wuf ta cafo ni ta maida ni kan gado ta danne da hannayenta duka biyu cikin haki saboda zafin naman da ta gwada wajen kamo nin, take tambayata, ina zaki haka da saurinki kamar kin ji ana neman ki, na kalı Baba cikin damuwa na ce yaya Almu zanje in bai wa hakuri ya kyale yarinyar nan kar ya ce zai biye mata. Baba Talatu ta zuba min ido cikin takaici tace, lalle ke kam da sauranki to ina ruwanki ina ganin ki da abin da suke yi? Ko kuwa wane karanbani ne zai kai ki ba da hakuri don kin ji ana kama hannun kishiyarki? Da sauri ciki wani irin mummunan faduwar gaban da ban taba jin irin shi ba na alli Baba Talatu a firgice na ce mata kama hannu? A hankali cikin natsuwa ta ce min eh nmana wannan ihu ai yai 132 kama da ihun shakiyanci da amare keyi yayin kama hannunsu, ban sake tankawa Baba Talatu zancen ta ba a hankali cikin karaya na maida kaina kan filo na kwantar yayin da wasu zafafan hawaye da suka fi kama da hawayen kishi suka yi ta zubowa daga idanuna cikin zuciyata kuwa sai fadi nake yi ka cuce ni yaya Almu, ka cuce ni.." Mu gamu a littafi na hudu don mu ji yanda za'a kwashe tsakanin Rabi'atul Adawiyyah da wannan kishiya tata. Littafin ya fito tare da na ukun, don haka a neme shi a karasa shan labarin. Na gode, Taku, Hafsat C, Sodangi. 133 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7