Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
Ke kadai ce ba ki da komai Rabi in ba ki sani ba in gaya miki, a hankali na ce mishi in mana sani amma yaya zanyi laifina ne? Na soma yi mishi kuka, yayi maza ya soma rarrashina ba laifin ki bane Rabi nima na sani yi hakuri kiyi hakuri kiyi shiru amma ina so ki fahimci cewar ba amarcine muhimman abu a wurinmu ba, muhimman abu shiine mu samu haihuwa kema kin san Umma da Baba suna Bukatar ganin' danmu kema kin sani sarai cewár babu wani da da zai debe musu kewar son ganin wanda zamu haifan musu don haka ina rokonki in akwai wani abin da kike yi ki daina don ina yawan jinki kina ambaton amarci nayi miki alkawarin daga ranar da kika tabbatar mini da abin da nake fatan gani a tare dake zan shigar dake cikin amarcin da baki taba sanin shi ba, a hankali cikin sanyin jiki na ce mishi bana yin komai yaya ya kara jawo ni jikinshi yana fadin na yarda Rabi na yarda ba za kiyi abin da zai cutar damu ba, don haka daga yau mu shiga yin addu'a kinji ko? Na ce mishi to. Tun daga wannan ranar yaya Almu ya dora min karanta suratul Maryam, kullum bayan kowace sallah ta asubahi, shi kuwa dama ma' abucin karatun Alkur'ani ne. Muna gaf da 81 cika wata tara cif da yin aurenmu sai kawai akayi waya aka ce wai Anti Aina'u ta haihu, an samu da namiji, tafdijam na kalli yaya Almu na ce mishi ba mu ma fa cika wata taran ba saura kwana goma, ya daure fuska ya ce to sai me Ance miki dole ne sai kowa ya kai wata tara daidai? Ko kuwa a lissafinki ne ba a cika wata tara ba awatan kalanda mu anamu lissafin an kai, naja bakina nayi shiru saboda ganin canzawar fuskarshi. Mun dawo daga sunan Anti Aina'u da kwana biyu, Anti Kubra ta haifi 'ya mace, kwana uku bayan nan sai ga waya daga Legos cewar Anti Rahma ma ta haihu kuma da namiji aka samu, cikin daren muka isa Legos saboda bamu iya hakurin bari sai gari yawaye ba. Hankalina bai tashi ba na samu kaina cikin tsananin damuwa sai da naga mun shiga wurin Umma don yi mata barka, maimakon tayi murnar ganinmu ni da yaya Almu kamar yanda ta saba yi wai sai kawai ta fashe da kuka, kuka kuma mai tsanani, jikina yana rawa na durkusa a gaban Umma na ce mata Umma don ban haihu ba ne kike kuka'? Umma ai zan haihu zan haifanwa yaya Almu da wanda za ki rike ki rene shi kiyi mishi riko irin wanda kika yi min, Umma me yasa zaki yi min haka? Ina fadin 82 hakan nima na soma yi mata kuka bama irin wanda take yi ba saboda zuciyata ta soma karaya. Yaya Almu yayi ta baiwa Umma hakuri wacce ganin kukan da nake yi yasa ta hakura da nata kukan tayi shiru, shi kuma yaya Almu sai ce mun yake yi ke kin yi magana mai dadi kin zo kuma kina kuka, yi hakuri kiyi shiru Rabi, nima zuciyata tana gaya min cewar za ki haihu, Rabi za ki haihu ya'ya masu yawa ma ba daya ko biyu ba. Hankalina bai kara tashi ba sai da na ga Anti Rahma da danta a gadon asibiti suna kwance abin gwanin sha'awa, danta gabjeje mai kyau dashi. Nasa hannu na karbi yaron na mikawa yaya Almu hannu biyu yasa ya karbe shi yayi ta karanto mishi addu'o'i yana tofa mishi cikin farin ciki da murna saboda yaya Junaidu baya nan yana waje sai kawai muka tsaya akayi sallama muka dauko Anti Rahma da danta muka kawo su gidan Baba don umarnin da Umma ta bayar kenan na a kawo mata ita tayi jego a nan. Daga nan na wuce sunan Anti Kubra da aka gama komai kuma na sake komawa Legos na Jira sunan Anti Rahma inda muka samu Aliyu wato sunan Baban Umma, bayan dawowarmu daga sunan Baban Umma kamar yanda na ji 83 kowa yana kiranshi ko sati biyu bamu yi ba muka nufi birnin Cairo don ganin wani Likita da Baba ya tura mu wurinshi, tun daga wannan lokaci muka tsunduma cikin maganar neman haihuwa yau muna nan gobe muna can shiru babu ciki babu dalilinshi ko batan wata ban taba ba balle akai gayin 6ari, ana nan a haka daga baya sai yaya Almu ya soma nokewa tafiye- tafiyen asibiti da na same shi nayi mish1 magana kan sabon halin nashi sai ya ce min mu nemi haihuwar kawai wurin mai ita Rabi na gaji da wadannan tafiye-tafiyen ni ban natsu na maida hankalina kan cikina ba ke ba ki zauna a dakinki kin huta ba, yanzu Junaidu da yake da 'ya'ya biyu a gidan shi asibitin ina yaje aka duba shi? Inda Likita na bada haihuwa ai da mun samu. Gashi dai gaskIya ya gaya min amma ban ji dadin gaskiyar ba, saboda zuciyata a yanzu babu abin da take so irin in ganni da da in ga dai na haifarwa yaya Almu da Umma da inga dai irin son da zasu nuna mishi a duniyar nan, tubburewar da yaya Almu yayi kan cewar shi kam ya gama zama a gaban Likita don rashin haihuwa ba wata lalura ta rashin lafiya ba ana mishi gwaje-gwajen da suka kamata dama wadanda basu kamata ba, na kawo wannan kawo wancan, yasa na nufi Legos Wurin Baba 84 don kai kara Umma na ce na samu a car ban kuma samu fadin abin da ya kai ni ba saboda rikicin da na samu anayi a gaban Baban, yaya Junaidu da Anti Rahma ne suka samu sabanin da yayi dalilin da yayi mata duka irin wanda ban taba tsammanin mutum mai hali irin nashi zai iya yin hakan ba. Ummana na samu a durkushe tana goye da Zuwairiya yar da Anti Rahma take goyo, tana kuka ga kuma yaya Junaidu can gefe a takure ya sunkuyar da kanshi kasa itama Rahman tana ciki kallo daya nayi mata na shiga taya Umma kukan da take yi saboda zaluntar ta da Yaya Junaidu yayi zagewa yayi da iyakacin karfinshi ya nada mata dukan tsiya, ban iya zama a wurinta ba saboda tausayinta na tashi na tafi wurin Umma na zauna ina jliran fitowarsu sai zuwa can sai ga Umma tana tashe da Anti Rahma sun shigo har lokacin Anti Rahma bata daina kuka ba itama Umma bata daina yi mata fada ba. Yau indaa haka kawai Junaidu yayi miki wannan zaluncin da kinyi mamakin abin da ya same shi, to amma akan me akan me zaki yi abin da kika yin? Rinka haihuwar su kina kawo mun su Rahma ni zan rike ba zan gaji da su ba, ai ni na rike ubansu Umma tana fadin ta soma kuka, a gigice na shiga tambayarta me ya faru ne Umma? Bata 85 tanka min ba ta tashi tana cewa tashi ki bishi ku tafi zan rike ta tare da dan uwanta in kin haifi na cikin kima zan karbe shi ki zauna kar ki wahala tana barin dakin na kalli Anti Rahma na ce wani cikin ne dake Anti Rahma? Ta gyada kai cikin takaici ni ke nan kullum ciki shi ne daga naje don a cire min munafukin Likita yayi waya ya tambaye shi shine yayi min wannan wulakancin, kuma zanga.....ban barta ta karasa ba nayi maza na mike ina kallonta, na ce mata kije ki cire Anti Rahma kije kiyi abin da kika ga dama, ni in yi kuka don ban samu ba ke kiyi kuka don kin samu sun ishe ki saboda butulci, saboda rashin adalci irin naki, kuma wai har kina kawo maganar gaban Umma na kin mance matsayin 'ya'yan yaya Junaidu a wurinta kin manta da cewar yaya Almu bai samu ya haifan mata ko guda daya ba, mun gode. Na yi maza na fice na bar mata dakin ban nemi kowa ba na bar gidan kawai na dawo gida cikin zuciyata ina mamakin butulci irin na mutane. A gida ban yiwa yaya Almu tadin ba musamman ma da yake na same shi yana fushin na fita gida ba tare da na nemi izininshi ba, don haka sai kawai muka ci gaba da zamanmu a haka sai dai kuma kwana daya ne kawai da dawowana sai ga yaya Junaidu ya biyo ni, ina 86 daki sai yaya Almu ya shigo fuskarshi a daure ki zo ga Junaidu yazo yana son ganinki, na ce to na tashi na dauki hijabina na sanya na nufi falon nashi nayi sallama yaya Almu ya amsa na shiga na nemi wuri na zauna a kasa, bayan na gabatar mishi da abinci da na sha ya gama amsa gaisuwar da nayi mishi sannan sai ya ce mun jiya sai kika taho ba kiyi sallama da kowa ba har da Baba me yasa kika yi haka? Na ce kayi hakuri kawu nayi kuskure hankalina ne ya tashi naje gida don in kai karar yaya Almu ya ki yarda muje asibiti kan mas'alar mu sai kuma naje na samu maganar ku shi yasa na hakura na dawo. Yaya Junaidu ya kalli yaya Almu ya ce yaya Mustapha akwai wani abu ne? Yaya Almu ya ce a'a ni dai ayuka sunyi min yawa ne kawai, ya ce to ko zaka ba da izini a shirya mata tafiyar ita taje? Ya ce eh to babu laifi amma a hada ta da wani, yaya Junaidu ya ce Umma Amarya zata ganin Likita ai sai su tafi tare ya ce ba laifi. Wannan tafiyar da muka yi da Umma amarya muka je asibiti ita ce ta baiyanar da asirin da yaya Almu ya dade yana boyewa, don kuwa a wannan tafiyar ne na samu damar da na karbi sakamakon Likita da hannuna. 87 Ina zaune gaban Ummana ni da ita kuka muke yi yaya Almu ya shigo ya same mu saboda kiran da Umman tayi mishi. Cikin natsuwa ya tambaye ta ko lafiya? Ta mika mishi takardun da nazo dasu ya gamna dubawa ya mayar a hankali ya ajiye ya ce ni ban yarda da wannan gwajin ba, Umma ban yarda da su ba in na samu sarari zan sake kaita ayi mana dukannmu, don haka ki kwantar da hankalinki kar ki samu damuwa, yayi ta rarrashin Umma har sai da ya kwantar mata da hankali sannan ya tasa ni a gaba muka dawo gida. Muna isowa ya balbale ni da fada ba tare da ya ji tausayin abin da nazo dashi ba, dama bukatar ki kenan kije asibiti ki zowa Umma da labarin da zai bakanta mata zuciya? Kina tsammanin tana da wani karfin da zata iya daukan wani bakin ciki daga gare ki? Abin da ta gani a rayuwar ta ya ishe ta kar ki sake binciko wani mummunan labari kije ki gaya mata, ki rike abinki a cikinki, kema ko ya zama jaruma kina rike damuwarki ba sai kin maida ita ta zama damuwar kowa ba. Mamakin tashin hankalin yaya Almu naji da ko in kula kan sakamakon LIkita dana zo dashi na cewar ba zan haihu ba amma sai na hadiye na daure na ce mishi amma yaya za'ayi in iya 88 hadiye wannan maganar ban gayawa Umma ba? Ya ce eh saboda ba kya tausayinta shi yasa ba za ki iya hadiye wa ba da kika dawo ai ni ya kamata ki fara gayawa ruwana ne 1n ce to mu gayawa su Umma da Baba ruwana ne kuma in ce to mu barwa cikinmu. Wannan test din naki ni ban shekara hudu da samunshi ba? Tun zuwa asibitin farko da muka yi aka gaya kin ga na gaya miki? Saboda kar in tayar miki da hankali, yana mikewa yaje ya kwaso takardun ya watsa min su ya ce kin ki yarda ne da baki je kika jiwo ba balle kije kina fada. Tattara takardun nayi na rungume su a kirjina ina wani irin matsanancin kuka ina fadin shi kenan shi kenan ni ba zan haifar maka dan da Umma zata dauke shi ba. Yaya Almu ya durkusa da gwiwowinshi biyu a gabana ya ce ban taba yarda da hakan ba Rabi, shi yasa na ce miki mu nemi haihuwar kawaai wurin mai bayarwa ban kuma fidda ran zai bamu ba kiyi hakurin fadan da nayi miki ki bar kukan da kike yi, amma ina so ne ki sani cewar ni dake ba zai yiwu mu zama sanadin bacin ran Umma ba don haka kar ki sake kai mata wani labari da zai tayar mata da hankali na ce mishi to. 89 An dauki lokaci mai tsawo yaya Almu yana rarrashina kafin na dawo cikin natsuwa ta hankalina ya dan kwanta saboda irin kalaman da yake yi min wai kenan ance miki dole sai an haihu ne ake farin ciki? Ba ki san wasu suna nadamar haihuwar da suka yi ba? Ai ita rayuwaa gamsuwa ne kawai Rabi in ka yarda ka gamsu da ni'imar da akayi maka kayi godiya kan hakan sai a baka kwanciyar hankalin da kake bukata, kina sona ina sonki hakan bai ishe mu godiya ba? Kullum irin kalamanshi kenan har dai na dan hakura, na tasa al'amarin mijina a gabana, na maida tattalinshi shine farin cikin rayuwata, kowane lokaci cikin shirya mishi nau'o'in abinci iri-iri nake a kowane lokaci kuma in dai yana gida to ina manne dashi in ma tafiya zai yi to mafi yawancin tafiye-tafiyen nashi tare muke yi. Mun bar hirar haihuwar da maganar nemanta sai dai kuma kullum a cikin yin addu'a muke ko na ce ni na gaji zan huta sai ya ce baki da hankali Rabi, kin taba ganin wanda ya gaji da rokon alheri wurin mai bayarwa? In ce a'a ya ce to kiyi ta addu'a ki kuma yawaita istigafari in ce mishi to. Abu daya dai da yafi damuna shine na rage zuwa wurin Umfa na sai dai na kanyi mata aike akai-akai, saboda na gane ganina yana tayar 90 Tmata da hankali mafi yawancin lokaci in ina tare da ita ba ma rabuwa sai tayi kuka ko ni kuwa cikin zuciyata mafi yawancin damuwata kan rashin haihuwar tawa saboda Umma ne in ga dai ta rike da a hannunta ace ni na haifan mata shi mana wannan shine abin da yafi muntsinina amma in don ta yaya almu ne ya hakura, ya shanye ya boye ya, ya barwa cikinshi in ma yana da damuwa to ban sani ba a zahirin abin da ya nuna min shi ne nice komai dinshi, nice farin cikinshi da kwanciyar hankalmshi ni kadai kuma na isa in cike mishi kowane irin gurbi na abin da ya rasa. Aurenmu ya cika shekaru biyar banyi niyyar tunawa yaya Almu da zagayowar ranar ba don hakan yana nufin tuna mishi da dadewar mu ne babu da, don haka naja bakina nayi shiru sai dai na shirya yi mishi abinci mai dadi don in kara mishi farin cikinshi Pasta mould na shirya mishi. ABUBUWAN BUKATA: 1. Shinkafa ne ko taliya, sai nayi amfani da shinkafa saboda sanin shi Yaya Almu ba ma'abucin cin taliya ba ne sosai. 2. Kayan kamshi 3. Mangyada 91 4. NikaRken nama 5. Tumatur 6. Alaiyaho 7. Maggi 8. Butter 9. Albasa Na tafasa shinkafa, ta dan fara dahuwa kadan sannan na juye ta na tsantsameta na barta tasha iska kafin na soyata a cikin Butter. Nasa a abin da zai iya zama a oven na ajiye a gefe. Na kawo rabin butter na soya da albasa na zuba naman, tumatur, kayan kamshi da magi, na hada na dafa sannan na dan dafa alaiyaho da magi kadan. Na hada alaiyaho da naman nan na wuta na gauraya na zuba akan shinkafar na rufe da foil paper nasa a oven na barshi cikin madaidaiciyar wuta, tsawon minti arba' in. Na kuma shirya mishi abin sha mai dadi, shima ga abubuwan da nayi amfani dasu. Kankana Lemo Sugar Citta Lemon tsami cokali (1) 92 A cire jan kankanan a bar bakon asa a bulanda a markada, a markada lemon zaki bayan an cire fari-farin abin da ke jikinshi, a matsa ruwan lemon tsami cokali daya akan ruwan kankana da lemon nan sai asa citta kadan da sugar daidai yanda ake bukata. Gaba daya na hada na juye na shirya mishi yana zaune yana kallon abincin sai ya kalle ni yace min hala dai an shirya min wannan abincin ne yau don a tuna min na sheka ra biyar yau da angwancewa? Na sunkuyar da kaina kasa cikin zuciyata na ce ashe shima yana sane da zagayowar ranar, na dago kaina a hankali na kalle shi na ce mishi eh yaya yau shekarunka biyar da angwancewa sai dai har yanzu....bai bari na karasa abin da nake shirin fadin ba, sai yasa hannu ya tallabe habata ya ce, har yanzu amarcinmu yana nan kullum kara son juna muke yi ni da ke babu abin da ya taba shiga tsakaninmu muna da fahimtar juna muna ganin darajar juna saboda akwai kauna mai yawa a tsakaninmu, don yi min alkawari a yau kamar yanda nasha yi miki a sauran shekaru hudu da suka wuce, na kalle shi cikin murmushi na ce alkawarin me zanyi maka yaya Almu? Ya zuba min ido yana kallona ya ce irin wanda 93 nake yi miki a rana irin ta yau, na ce ai ni bani da abin yi maka ko baka yayi maza ya ce kina da su da yawa Rabi, don haka zan roke ki kiyi min alkawarin har abada zaki yi tayi min abubuwa guda uku, na ce sune me? Ya ce zaki yi ta sona ko da kuwa a wane hali muka samu kanmu? Na yi murmushi na ce wannan ai rubutacce ne a zuciyata, ya ce to na gode yi min alkawari Rabi za ki bani hadin kai a duk lokacin da na nemi hadin kanki kan wani abin da ya taso min, na ce zan baka, ya ce to ina so ki zama mai taimakona a kowane lokaci na nemi taimakonki, na sake cewa zanyi hakan ya ce to na gode, yana fadin haka ya mike ya shiga dakinshi ya fito wata 'yar leda ya dauko da ya fito da wani dan akwati daga cikinta ya bude shi ya fiddo wasu warawarai masu asalin kyau ya kama hannuna ya zare wadanda nake sanye da su ya maida mun sabbin ya ce tukuci ne na kin shekara biyar kina hakuri da mijinki. Na kalle shi nayi murmushi na ce, na gode Yaya, abin da duk kake nema na alheri a rayuwa Allah ya baka shi, ya ce to amin. Da daddare ranar ina tare da yaya Almu bayan na tsala mishi kwalliyar da tayi dalilin al'amura masu yawan gaske, yana kwance can gefe kan faffadan gadon nashi cikin 94 matsananciyar gajiya, lumshe kuma da ido yana maida numfashinshi a hankali, zuwa can sai naji ya ce min "kinyi bacci ne Rabi? Na ce mishi a'a, ya ce to kar kiyi bari in zo muyi magana, na ce mishi to. Mikewa yayi ya shiga toilet yayi wanka ya fito nima ya bani umarnin yin hakan, naje nayi nazo nima nayi sallah raka'a hudu saboda abin da na samu yana yi kenan, ya gama addu'a ya shafa fatiha nima na shafa tawa sai ya juyo ya kalle ni cikin natsuwa babu alamar wasa a tare dashi, sai ya buda baki ya ce min, wannan maganar da na zaunar dake zan gaya miki a yau Rabi ta dade tana katse min dadin baccina saboda nauyinta a wurina yana da yawa, to amma babu yanda zanyi in yi ta boye miki ita musamman da yake abin kara matsowa yake yi, zuba mishi ido nayi ina kallonshi ina kuma sauraron bayanin nashi, sai ya ce min ni dake akwai fahimtar juna a tsakaninmu shine kuma muhimmin al'amari dama a tsakanin ma'aurata, ni na yarda dake na amince miki don nasan ba za ki taba yin wani abin da zai cutar dani na Kuma sani kema kin san in zan hango abin da zai cuce ki to zai gama dani ne kafin ya iso gare ki, ban taba zaton zanyi abin da nake shirin yin ba a wannan lokacin in ban da wasu al'amura masu tsanani da suka tasa ni a gaba. 95 Na ce mishi menene ya faru Yaya Almu? Menene ya taso mai tsanani da zai saka kayi abin da baka shirya ba? Ka gaya min kawai ba sai ka tsaya kana yi min dogon bayani ba, ya ce natsuwarki nake bukata so nake ki bani hadin kanki don hakanne kawai zai taimake mu ni da ke na ce na baka ka gaya min menene? Ya sassauta magana ya ce aure nake so in y1, ammna bani na nemi auren ba, bani yarinyar akayi na zuba mishi ido ina kallonshi cikin kaduwa ban taba tsammanin abin da zai gaya min ba kenan, na daga ido cikin natsuwa na kalle shi na ce don ni ba zan haihu ba kenan? Yayi maza ya ce a'a, a'a ba haka bane, kinsan shi aure zuwa yake yı, kuma don kisan ma babu wani abin da zai cutar dake Umma ta sani ita ce ma ta ce dole in karbi auren don da nace bana so nayi maza na ce Umma? Nan da nan ya canza zancen da cewar ba Umma nake nufi ba, amma ni dama can kin san ina gaya miki cewar sha'awar uwargidanci nake yi miki, na rinka yi miki hakanne don in fahimtar dake cewar ni din bani da burin zama da mace guda daya na ce haka ne, amma tun lokacin nima na gaya maka cewar bai bani sha'awa ba kuma zan taba yarda in yi shima har ma na taba gaya maka cewar kara auren mijina alama ne na shi din ya gaji dani, don haka yanzu 96 ma kan abin da zan tsaya kenan ka gaji dani ai ma kayi kokari ban haifar maka kowa ba bayan kana ganin duk wadanda muka yi aure tare 'ya'ya uku-uku suke shirin samu, gidan Yaya Junaidu kuwa tuni akayi ukun na hudu ake nema, lokacin ne na fara kuka sosai musamman da na kara tunawa cewa ni da kaina na karbo sakamakon Likita da ya tabbatar da cewar ba zan iya haihuwa ba ban da wanda yaya Almu ya dade yana boyewa. Hakan da nake yi ya kara sanyaya jikin Yaya Almu, ya matso kusa dani ya rungume ni "kiyi hakuri Rabi, ina tabbatar miki bana murnar wannan auren na san1 ban taba sha'awar zama mijin mace daya ba, amma lalurarki sai tasa ni jin tausayinki matsanancin tausayin da yasa na hakura na hakura da duk wadannan abubuwan, to amma a yanzu ya Zama mUn dole inyi Baba da Umma sun tasa ni a gaba ta kaima nayi watanni ban je in da suke ba amma basu hakura ba sai kuma kwatsam ga maganar wannan yarinyar ta taso. Umma kuma ta ce in karbi auren kin kuma san ba zai yiwu in ki bin umarninta ba. Ko da yake nasan yaya Almu kullum kan bin umarnin Umma yake amma sai na kalli wannan biyayyar tashi har da dama yana so, duk yanda 97 na kai da son kaina ya zama dole in yarda da cewar yaya Almu zai bukaci kara aure don samun haihuwa ko da kuwa kullum hadiye shi a ciki nake yi ina fito dashi, don tsananin kyautatawa, shi ne da guda daya da baba yake dashi ko kafin in mallaki hankalin kaina kuwa nasan babu wani abin da ke da daraja a gidanmu irin haihuwa, to yaya Almu bai samu ba an kuma ce nice mai matsalar, in baba ya sanya shi yayi aure bai yi laifi ba, don nasan yana son ganin danshi koma in ce 'ya'yanshi yanda duk ya kai da sona kuma ba zai bani mamaki ba in ya fifita wanda yake yi mishi akan nawa, to amma ita Umma fa, don me zata shiga zancen auren nashi? Tana nufin itama tafi sonshi a kaina? Wadannan sune tambayoyin da suka zo cikin zuciyata na kuma kudurawa raina ganin Umma don ta bani amsar su. Har gari ya waye ban sake daga ido na kalli Yaya Almu ba, balle in bashi amsar maganganun da yake ji, har yayi alwala ya fita sallar asuba nima na idar da sallah ban tsaya jan carbi ba don kar ya dawo ya same ni na yiwo waje mota na nema shata zuwa gida don nasan Umma bata Legos. Na iso gida wajen karfe goma, don haka kai tsaye sashin Ummana na nufa na kuma yi sa'a 98 sanyin da ake yi yasa Baba maigadi ne kawai a waje, ina shiga sashin Umma 'ya'yan yaya Junaidu na fara gani su uku, baban Umma, Zuwairiya da Halimatus-Sadiya cikin tafka- tafkan suwaitu suna wasan tseren kekuna, suna ganina suka nufo ni da gudu suna yi min oyoyo, nasa hannu na dauki Halima na karasa falon da ita Umma tana ciki tana zaune ita kadai na durkusa gabanta da nufin in gaisheta, sai dai ban iya cewa komai ba saboda hawayen da suka kama zuba daga idona, ban gama kukan ba sai ga yaya Almu ya shigo da alamar dama ya riga ni zuwa gidan, koma yana ganin shigowata ban fasa yin abin da ya kawo ni ba, na ce mata me nayi miki Umma da zaku hadu ke da Baba ku yanke min hukunci iri daya? In shi yafi sonshi dani kema za ki fi sonshi dani ne? Daga ido tayi cikin natsuwa ta kalle ni ta ce min kiyi hakuri Adawiyya, babu wani wanda yafi son Babangida a kanki tsakanin ni da Alhaji dukkan ku 'ya'ya ne, hukunci na adalci aka zartar a tsakaninku, ba zai yiwu babangida yayi ta zama dake ke kadai ba tare da lalurar dake gare ki, koda baki da wata lalura ma yana da yancin yin mata hudu don haka kiyi hakuri ki koma dakinki ki zauna mu rungumi kaddarar da ta same mu ta rashin haihuwa sai dai n....ban 99 san yanda akayi ba jina kawai nayi na katse Umma ina ta fadin maganganu, bani da wata kaddara da zan unguma Umma, in ku kun yarda da cewar ba zan haihu ba toni ban taba yarda ba, ba kuma zaku tilasta ni in yarda ba, ba kuma zai yiwu ku fake da hakan ku taimaki yaya Almu a kaina ya cuce ni ba, ba zan yarda ba ban yarda da cewar ni dashi daya ne a wurinki ba, kin fi sonshi dani na bar mishi ke, na barwa yaya Almu ke Umma, ki maida ni kawai in da kika je kika dauko uba...ban samu karasawa ba na jini kife a kasa, saboda wani irin wawan marin da aka kife ni dashi, tsawon lokaci ina kife kafin na dago kaina na kalle su Umma tana zaune ta sunkuyar da kanta kasa yan yatsun hannunta take kallo. Shi kuwa yaya Almu ni ya zubawa ido cikin matsanancin bacin rai, abin da ya tabbatar min da cewar shi ne yayi min wannan dukan na tare jinin dake ci gaba da zuba daga hancina ta tafin hannuna, na sake kallon shi na ce mishi, ko zaka kashe ni ba

Chapter 5 of 7