Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
kuma amfana kwarai da kawance na da ita don ita ta koya min kwalliya da gold maimakon yawan daura zani. Nayi kwalliya sosai na kuma yi kyau har ba'a magana ga hakorana biyu a lokacin nan da na sanyo sai daukar ido suke yi suna sheki suna 43 walwal saboda kasancewarsu jajaye wata mace tayi sallama ta shigo tana tashe da danta dake ta faman kuka yana shan majina, nayi mata sannu da zuwa na kuma shiga gaisheta tunda banga alamar zata karaso ba, sai dai bata wani amsa ba ta shiga ce min kece mamansu Junaidu? Na ce mata eh ta ce to kinga ki yiwa 'ya'yanki kashedi don bai zamo min komai ba in sanya a nada musu dukan tsiya sun tasa min yaro a gaba da duka na menene hakan? Na kalle ta a lalace na ce na menene za ki kisa ayi musu duka in baki yi haka ba baki haihu da kyau ba, a fusace ta ce ai abin da za ki gaya min kenan? Na ce na gaya miki ni sau nawa yaran unguwar nan suka fasawa 'ya'yana kai da duwatsu a garin jefe- jefensu kin taba ganin kafata na shiga wani gida don kai kara sai ke naki dan don an doke shi, to dan gwal ne da ba za a dake shi ba? Ta ce to shi kenan ta juya zata fita sai ga Alhaji ya fito daga falonshi ranshi a 6ace, ku zo nan mai yaro kiyi hakuri kiyi hakuri kin ji ko za'ayi musu fada yasa hannu a aljihu ya ciro kudi ya mikawa yaron ya ce gashi ko don Allah kuyi hakuri suka yi godiya suka fita, suna barin gidan ya rufe ni da fada kan me zanyi mata irin maganganun da nayi mata ina laifi da ta kawo min kara? Na ce tO amma ni gunwa nake kai kara? Ni sau nawa 44 ana yiwa yaran nan ciwo wa na taba gayawa? Yau inda da Junaidu kadai ake yi da da sauki, tunda shima ya iya dukan ya'yan Jama'a amma Babangida fadawa yake fada ga tabon dutse nan a kanshi har yanzu bai gama warkewa ba sai kuma ni ta shigo min gida zata yi min bakar magana? Haka ake yi? Ni ban taba ganin irin wannan rayuwar ba kai kasan darajar naka amma baka san na wani ba iyaye idonsu akan 'ya'ya babu kunya babu kawaici, yayi murmushi ya ce to ai banbancin zaman birni da na karkara kenan, yanzu mü a gida ka isa ma kace zaka yi magana akan abin da aka yiwa danka? Na ce ba a isa ba ya ce to ki rinka yin hakuri in an kawo kara ki bada hakuri in kuma an yiwa naki kiyi hakuri, na ce mishi to. Tafiya daya Alhaji ya yi bayan wannan lokacin ya dawo ya sauka a gidan su Karama bai zo gidanmu ya ganmu ba sai da ya kwana biyu abin da yayi matukar kona min rai, har na kasa boyewa. Ya shigo gidan nayi kamar ban san daga tafiya yake ba, ban da sannu da zuwan da rfayi mishi ban kara ba, ko ruwa kuma ban kawo mishi ba da dai ya lura ba wani tarbar arziki zanyi mishi ba sai kawai ya tashi yayi ficewarshi ya tafi, ban sake ganinshi ba ya gama saura kwana biyunshi na can gidan ina tunanin 45 yau dai ai dolenshi zai dawo nan din da ba ya so zan kuma gaya mishi na fara gajiya da hakurin da kullum nake yi, baya gani tunda bai gudun bacin raina sai nasu, ban taba ganin ranar da ya dawo ya wuni a gari bai je ya duba su ba sai ni da ya raina. Ina cikin jira yazo in jera mishi1 wadannan maganganun sai kawai ga dan aike an kawo min kudin cefane wai shi yayi tafiya na ce tafidijam, ban taba yin sha'awar yin yaji ba irin wannan ranar sai dai kuma inyi yaji inje ina? Haka na hakura na zauna raina a bace bai dawo ba kuwa sai da yayi sati uku ya sauka anan gidan. Rannan kuwa kwana nayi ina yi mishi kuka ya zuba min ido kawai yana kallona sai da nayi ya 1she ni nayi shiru sannan ya ce min, ai na dauka akwai wani sassauci a tsakanina dake ban taba dauka kina lura da wani abin da nake yi musu ba, na dauka tsakanina dake kawai kika sani, to amma tunda haka ne shikenan ba zan sake ba zan rinka kiyaye abin da nake yi musu in tabbatar nayi miki kamar yanda kema zan kiyaye wanda nake yi miki in rinka yi musu. Kunya ce ta kama ni da yayi min wannan maganar don nasan abin da yake nufi sai dai ban yarda ya gane naji kunyar ba ne eh ai gara ka rinka yin hakan, cikin raina dai na kudurawa 46 kaina cewar babu wani abin da zai sake yi min in bude baki in yi magana. A wannan shekarar ne Alhaji ya kaini kasarmu ta Senegal tare da yara na tafi tare da tsaraba mai yawan gaske, abin mamaki ashe wai har kanine dani wanda muke uwa daya uba daya, kuma wai tuni Alhaji ya dade da sani amma bai taba bani labari ba sai ran da muka isa. Bayan mun natsa sai ya kalle ni ya ce min, ina jin fa Muntakan nan shi ne kaninki da Baba ya bani labari da sauri na kalle shi na ce mishi kanina? Ya ce eh ita Inna ba wurin haihuwa ta rasu ba? Lokacin ne na tuna Babana ya sha gaya min Innata wurin haihuwar kanina ta rasu, na kalle shi na ce tafdijam, amma shine baka taba gaya min ba? Yayi murmushi ya ce, "to ai tayar miki da hankali kawai zanyi, na ce haka ne. A zaman bakuntar da nayi, nayi kokarin jan Muntaka a jikina muka yi sabo na kuma nuna mishi cewar ya bini muje yaga inda nake abin da kanin Babanmu wanda yake shine marikin shi yaso ya ki yarda nima kuwa na tasa Alhaji a gaba da kuka na ce mishi ai da ganin Muntaka ba dadinsuyake ji ba, ba gashi duk sunyiwa ya'yansu sa'o'inshi aure ba amma shi basu yi mishi ba, ya ce ai sun ce bara rashin lafiyar da yayi ne yasa ba ayi mishi bikin ba, na ce eh to 47 muje dai yaga wuri, ya yi murmushi ya ce to bari muji abin da Baban zai ce. A haka muka dawo da Muntaka gida akan zai ga wuri ya koma sai muyi zamanmu nan da nan ya wastsake daga duk wata wahala ya zama santalelen saurayi gashi tunda yazo ciwon cikin da suka ce yana dashi din bai sake tashi ba, gashi nan da nan Alhaji ya sanya shi cikin harkokin dukiya har ya shiga yin tafiye-tafiye dashi Alhaji ya kara nuna mishi gatan da ya tabbatar min da matsayina a wurinshi. Rannan ina zaune a falona bayan mun dawwo daga umrar da muka tafi ni da Hajiya Hauwa, hutawa nake yi cikin nishadi sai naga Muntaka ya shigo gida yana sanye da doguwar jallabiya fara sol a jikinshi da farar hula 'yar karama yayi matukar yin kyau yayi sallama a bakin kofa ya cire silifas din wanka dake kafarshi ya shigo ya zauna na zuba mishi ido ina kallonshi na ce, Muntaka baka je kasuwa ba ka kuma san Alhaji ba ya nan? Ya ce naje yanzu na dawo ina son yin magana dake ne sai 1n koma, na ce mishi to, na dan daga murya na kira Uwa na ce kawowa kawunku abinci, ta ce to taje ta kawo ta ajiye mishi ya ci kadan sai ya kalle ni ya ce so nake in yaya ya dawo ki rokar min shi ina so in koma kasarmu da sauri na ce mishi Senegal Mun 48 taka? Ya sunkuyar da kanshi kasa ya ce mun eh ai kinga ba na shekara biyu kenan har da watanni tunda muka zo da zamu taho kuwa cewa akayi zan zo in ga wuri in koma, na ce haka ne. Bayan fitar shi sai nayi ta kuka saboda ban son tafiyar tashi ina ganinshi a matsayin dangina gashi zai gudu ya barni, to ko dai wani laifi nayi mishi bai gaya min ba? Abin da ya tsaya min a zuciyata kenan, sai dai bance mishi komai ba sai da Alhajin ya dawo na bashi labari da ya gama sauraronä sai ya ce min ina ganin aure yake so ai ya girma bana shekarunshi ashirin da takwas kenan tunda ke kinyi talatin bana nace mishi hakane, ya ce to gaya mishi ya duba yarinyar da yake so sai a aura mishi, na ce to da na gayawa Muntaka sai ya ce min shi bai son auren don baiga wace yake so ba, Alhaji ya ce in gaya mishi yaje ya duba cikin 'ya'yan abokanshi ya sake cewa baya so. Rannan nayi kuka a gabanshi ina tambayar shi me yasa baka Sona Muntaka me yasa baka son zama dani? Kwana biyu bayan nan na kira Muntaka ina rarrashinshi don ya gaya min meye damuwarshi? Sai ya ce min tsoro nake kar in yi abin da ba a taba yi ba, nayi maza na tambaye shin me? Wane abu ne zaka yi wanda a duniya ba a riga ka yin shi ba? Ya sunkuyar da kanshi 49 kasa muryarshi tana rawa kamar yanda jikinshi ma ya dauki rawa ya ce da kin barni kawai na tafi na ce ba zan barka ba sai ka gaya min gaskiyarka, a hankali ya ce min nesa nake so in yi da Uwa tsoro nake ji kar in ce ina son....ya kasa karasawa, nan take kuma ya shiga shisshikar kuka saboda tsananin damuwar da ya shiga, da sauri nace mishi ai bani na haifi Uwa ba Muntaka, bani na haife ta ba, 'yar wan Alhaji ce ai kana da damar cewa kana sonta, na zauna na kwashe dukkan labarina tun daga kuruciyata a gaban Babanmu har kawo ranar da nake bashi labarin ban rage mishi komai ba. Shi kenan tun daga nan sai ya saki jiki ya koma al'amarinshi da Alhaji ya dawo kuma na bashi labari, yayi matukar jin dadi ya ce ai shi kenan sai kiyi tuwonki manki, na ce hakane. Ana yin haka na shiga shirin buki amma sai da naje Katagun na shaidawa yaya Balki in da ta nuna min bacin ranta kan hakan da nayi bisa cewar wai ba sai na gaya mata hukuncin da zan zartar a kanta ba. Ina dawowa na nemi izinin Alhaji na biyawa yaya Balki da Uwa kujera kamar yanda dama nasan Muntaka yana cikin mutanen da Alhaj1 ya ce zasu tafi. 50 An dawo babu dadewa aka yi bikinsu, biki na gata don babu abin da Alhaji bai yi musu ba na gata nima nayi gayya har daga Senegal yan uwa sun zo biki, taro ya tashi lafiya aka watse, kowa ya koma gidanshi aka bar ango da amarya dani kuma da na rinka ganin tamfar ni na fi kowa jin dadin zamani na hada aure tsakanin kanina uwa daya uba daya da 'yar da nake so yar da na rike 'yar da nake ganin 'ya ce. Auren Uwa da Muntaka ba karamin al'amari ba ne a wurina, don sai da na rinka ganin tamfar sune dangina gaba daya da nake ganin na rasa a baya, na rinka jin tamfa r duk wani bakin ciki da na gamu da shi a baya ya wuce, ya zama mun tarihi. Gidan su ya zame min wurin zuwa in naji zani unguwa sai in cewa Alhaji zani gidan su Uwa in dubo su wata rana ya ce min a gaishe su wata rana kuma ya ce bai yarda ba, wai na fitini yara da zirga-zirga a gida itama Uwa in taga kwana biyu bata ganni ba zata shirya tazo wuni in zata zo kuwa zata yiwo min girke-girke iri-iri tazo min dashi, Uwa da Muntaka suka maida ni 'yar gata sai ji dani suke yi nima ma ji dasu komai Alhaji ya shigo dashi gidan zan raba biyu in dorawa Babangida ko Junaidu in ce maza kai wa Uwa. 51 Ana nan a haka rannan muna hira da Alhaji sai ya ce min, ni Zuwaira in nace ki bani dava cikin 'ya'yanki in kaishi Turai yayi karatu wa za ki ba ni? Na zuba mishi ido cikin kaduwa ina kallonshi na ce ban fa wastsake daga kewar rabuwa da Uwa ba shine har ka fara tunanin sake raba ni da wani kuma? Ya ce to yaya zaki yi ai dukansu ma kwashe su zanyi in kaisu ka ratu ke dai mutum daya zan fitar daya zai yi ne a nan a gida amma ba zan bar miki gidan babu yara ba, zan kawo kanana in sa su suyi karatu manya kuma su taya ni harkokin kasuwanci na ce mishi to, na kuma yi mishi addu'a. Kwana biyu ya bani inyi tunani don haka da kwanakin biyu suka cika sai na gaya mishi akai Babangida Turai shi kuwa Junaidu a barshi yayi anan bai nemi sanin dalilina na fadin hakan ba nima ban tsaya yi mishi dogon bayani ba tunda naj ya ce to shi kenan sai nima nayi shiru. Tun daga nan bai sake ce min komai ba nima ban sake komawa kan maganar karatun nasu ba don ha Son tafiyar tasu nake yi ba rannan kawai sai Alhaji ya ce mun shirye-shiryen tafiyar yaran nan sai ta kammala ina ganin tatiyar ta matso, nayi maza na ce au a haka suna yan kanana ne za'a tafi dasu, ai na dauka sai sun girma tukuna? Gaskiya in dai yanzu ne na fasa a 52 bar mun su kawai sai sun kara hankali tukuna ya ce min to. Kwana hudu bayan nan daga fita sallar asuba $ai kawai naga yara shiru basu dawo ba sai da na gaji da jiran shigowarsu bayan na kammala abin karyawa na ce aje a kira mun su su zo mu karya sai kawai Alhaji yace mun ai an riga an tafi dasu za'a kai Junaidu wata makaranta a Akure shi kuwa Lamido za'a wuce dashi. Ihu na rinkayi da iyakacin karfina yana bani hakuri daga baya ma naga hakan ba zai mun ba na kama hanya na nufi katagan naje na bude dakin Baba da aka riga aka gyara tas na zauna a ciki zuwan Alhaji biyu naki binshi na ce ya barni anan kawai ai ya riga yasan ba zan iya zaman gidan babu yaran ba yarbani dasu ba tare da ya gaya min tafiyar tasu ba. Satina biyu a Katagun in ban da bacin rai babu abin da nake yi naja na tsaya kan lalle Alhaji ya dawo mun dasu kafin in dawo ko kuma ya bar nil in yi zamana anan. Rannan dai ya sake zuwa na ce a na riga na ce ba zan koma ba, ya ce ai na kawe wasu yaran nace to ina ruwana dasu? Ni nawa nake so in gani. Rannar dai yayan tudu yayi min fada irin wanda aka dade ba ayi min ba abin da ya tuna min da Baba nayi ta kuka a haka na biyo Alhaji 53 muka dawo gida na same shi cike da yara da ya kawo gaba daya ya'yan yan uwa ne da na sani nasan lokacin da aka haife su amma basu debe min kewar Junaidu da Babangida ba, basu hana ni kukan tafiyar su ba. Ban taba samun kaina cikin kuiyan yin girkjin gida ba sai a wannan lokacin duk abin da nayi niyyar girkawa in na tuna Junaidu da Babangida ba za su ci ba sai inga to wa zan girkawa akan dole Alhaji yasa Hajiya Hauwa ta nemo mishi mai girki inda ta kawo mishi wata daga baya kuma ta kawo mishi mai gyada don ita mai gyada tafi wancan tsabta da iya girki akan dole na bar wa mai gyada girkin gidan saboda na kasa, kasala ta kamani bani da wani aiki sai na tunanin yaran in kuwa rufe ido nayi da sunan barci in yi ta mafarkinsu a wannan lokacin kullum daga gidan Uwa ake kawo min abincin dare kowane kwana biyu kuma sai tazo gida wai tazo duba ni. Ana cikin haka ne na gane Uwa ciki ne da ita wai ban iya fadin farin cikina na hakura na kwantar da hankalina na koma kan lissafin cikin da Uwa ke dashi da kuma zumudin ganin abin da zata haifa, Uwa ta kanma zazzabin laulayi, kullum sai naje dubata in girka mata wannan in girka mata wancan sai dai bata iva ci saboda kurarrajin baki sun dame ta amma dai an samu 54 taji sauki sai dai kurarrajin kam sunki jin magani, dole aka hakura aka barta sai dai kullum zan dama mata kunun gyada na shinkafa da na tsamiya in hada da kindirmon dana sa mai nono tana kawo min in aike mata dashi shi ne ya zamo mata abinci. Duk da kurarrajin baki sun takurawa Uwa basu hanata murmurewa tayi kyau tayi fari sol ba duk da ita din ba fara sol ba ce, asalin kalar jikinta yana tsakanin fari da baki ne, wato a inda babu farare ita fara ce a inda kuwa suke da yawa to ita baka ce, tayi matukar yin kwarjini don kuwa dama doguwa ce sambal a mike take gata da idanuwa dara-dara wadanda a wannan lokacin suka kara fitowa suka kuma yi fari tas bakin kuma ya kara baza ba mijin uwa ba da yake matukar sonta yake ganin tanfar ita ce komai dinshi, don kuwa na taba zuwa gidan na gane Uwa tana kokarin boye min bacin ranta dana koma gida na neme shi na nuna mishi rashin jin dadi kan bata mata ran da yayi sai ya sunkuyar da kanshi kasa ya ce min ita ce mafi darajar abin da nake dashi, ita ce mafi soyuwar abin da nake so amma hakan ba zai hana in tayi kuskure in mata fada ba nace mishi haka ne amma maimakon fada rinka yi mata nasiha da abin da na raine ta bishi kenan zata bar duk wani 55 abin da baka so in ka gaya mata cikin natsuwa ya ce mun to, to ba mijinta dake yi mata irin wannan son ba ni da kaina bana gajiya da kallonta. A wannan lokacin duk wata hidima ta gidan Muntaka ya dauke mata ita sbaoda zuwan da nake yi in same shi yana aikace-aikacen gida yasa na daina yin sammakon zuw agidan sai na da' daici ya gama zai fita kasuwa ni kuma in dani mata hira. Muntaka da kanshi ya gano hikimar yi mata farfesun kanta yayi laushi sannan yayi amfani da turmin karfe mai tsabta ya dan daka shi don sauwake mata tauna ganewau da nayi cewar uwa da Muntaka so mai tsanani suke yiwa juna sai dadi ya kamani na kara sonsu wani irin son da ba zai yiwu in iya kwatantashi ba. Ana cikin wannan hali ne rannan Alhaji ya dawo dagga sallar Asuba naji shi yana kwalawa daya daga cikin yaran da suke gidan kira, yana fitowa bai ma saurari gaisuwar da yake yi mishi ba ya ce mishi maza tafi ka dubo min Muntaka me ya hana shi zuwa masallaci yau? Yaron ya fita da gudu ni kuma na fito ina ce mishi ko sun makarane? Ya ce to ban sani ba amma shi ba mai makara bane ni dashi mukanyi rige-rigen zuwan Masallacin ne watarana in riga shi wata 56 rana ya riga ni, muna tsaye a wurin har yaron ya dawo ya nemi wuri ya tsuguna ya shaidawva Alhaji bai jin dadi ne ciwon ciki na damunshi. Da sauri Alhaji ya fita ni kuma na tsaya ina fadin ikon Allah, yau kuma cikin nashi ya dan motsa kenan, ganin da nayi Alhaji bai dawo ba sai nayi zaton asibiti suka tafi gashi ya fita ban tambaye shi ba balle in je can gidan don haka Sia na tura maigyada na ce mata taje tazo min da Uwa. Isowarsu ne na gane Ciwon bana wasa ba ne saboda ganin yanda Uwa ta rude in ban da kuka babu abin da take yi na shiga rarrashinta ina fadin haba Uwa, in mijinki yana ciwo sai kiyi ta kuka haka? Tana kukan ta ce min ba kukan.ciwo nake yi ba mu..bata karasa ba saboda ganin da tayi na zuba mata ido ina kallonta kiyi hakuri Umma kiyi hakuri ta koma kuka tana bani hakuri, hankalina yayi matukar tashi na rasa inda zanyi na surn gyalena na yafa na tasa Uwa a gaba muka nufi asibitin don muga halin da suke ciki muna isa. Alhaji n2 maibindiga muka fara gani da sauri ya ce mun me ya fito dake? wa ya ce miki ki zo nan? Maza koma kiyi hakuri muna zuwa, muka dawo gida. Ba mu wani dade ba sai gasu sun dawo sai gashi ana ta shigowa gida ana diban butoci ina tsaye tsakar gida ina sauraron 57 Alhaji ya shigo ko wani wanda zai gaya min abin da ke faruwa ji nake tamfar inyi wajen in gananwa idona saboda tsananin bugun da zuciyata keyi, a cikin tsayuwar sai ga Hajiya Hauwa ta shigo kuka take yi sai ga Karama da Maryam sai ga matan abokan Alhaji da makwabta suna ta shigowa ashe wai Muntaka ya rasu ne, a wannan lokacin bata kaina nake yi ba saboda halin da Uwa take ciki suma take yi ana shafa mata ruwa inta yi kamar ta farfado sai kuma ta koma suman gata da ciki don haka akayi maza aka nufi asibiti da ita aka kwantar da ita ni kuma ina gida wai ina karbar gaisuwa daga baya naga zama ba nawa ba ne nasa aka je aka rokar min Alhaji ya barni inje asibiti wurin Uwa don tunda akayi mutuwar ya ki shigowa gida sai turowa yake yi wai a bani hakuri, bai hana ni zuwa asibitin ba don haka can na tafi naje wurin Uwa. Tsayuwa nayi na zama Jaruma nayi ta rarrashi ina bada hakuri ina kuma tuna mata da cewar mu din dukanmu zamanta muke yi sai dai in wa'adi bai cika ba, in nayi ta rarrashi sai kuma in koma kwadaitar da ita game da rayuwar da mai lmani ke sa ran samu bayan mutuwa, shi kuma imanin ba zai cika ba sai in zaka karbi.kaddara a yanda tazo maka, don haka kiyi hakuri saboda ki samu ladan musibar da ta 58 same ki da irin wannan ban bakin da irin wadannan kalaman na samu Uwa ta dawo cikin natsuwarta ta koma ambaton Ubangiji maimakon tsananin tashin hankali na neme sallama muka dawo gida. Ranar da aka cika uku ne nayi sammako tunda asuba na shiga wurin Alhaji tun bai fita sallah ba yana kan sallaya yana addu'a na jira shi ya shafa fatiha na gaishe shi nayi mishi ta'aziya na tashi na fito na dawo cikin gida. Alhaji ya karbi gaisuwa har tsawon kwana bakwai saboda Jama'ar da ke ta zuwa mishi ta'aziya. Bayan an gama karbar gaisuwa ne aka barni daga ni sai Uwa sai ko sauran mutanen gida. A wannan lokacin ne na samu kaina cikin wani irin tsanani ga dai zuciyata dake cike da dacin mutuwar dan uwana da na rasa wanda bani da kowa sai shi ban kuma same shi ba sai bayan da na dandani azabar zama ni kadai, to na same shi ina murna gashi kuma na rasa shi rasawa na farat daya a lokacin da ban taba tunanin hakan ba, da Muntaka ya danyi jinya nema watakila da ban dandani azaba mai yawan haka ba to gani kuma tashe da uwa mai ciki wacce bata taba daina kukan mutuwar mijinta ba, wacce ta kaurace wa cin abinci na zama bani 59 da aiki sai na rarrashi da ba da hakuri da nasiha tare da yin wa'azi in na dan samu ta dan sake ta dan soma zata yi magana yanzu ne zata soma hirar Muntaka daga haka kuma sai ta kama kuka, ni ba abin in ce zanyi mata yanda Alhaji yayi min ba, baya yarda maganar mutuwar tashi ta hada mu sai kawai ya mike ya fita a haka na zauna da Uwa wacce renonta yafi na dan jariri wahala, har cikinta ya kai wata takwas na shiga nuna don ganin sun kusa rabuwa itama ta huta watakila kuma in taga danta zata mai ya ce ta hakura dor ganin ga dan Muntaka a hannunta. A wannan lokacin tuni na gama shirin baihuwarta komai na tanade shi sai jiran zuwan haihuwar kawai nake yi itama ta danyi kuzari har na soma zuwa makarantarmu tare da ita. Rannan muna tsakar gida ni da ita zogale ta ce min tana sha'awa na aika aka sayo min danyenshi na gyara shi tsaf na dafa mata na tsiyaye ruwan a wani kofi na gyara ganyen na kwadanta mata shi yayi kyau yayi dadi na dauko na kawo mata na ce gashi nan ga kuma ruwanshi in kin kasa tauna ganyen sai ki kwankwade ruwan don dama yafi ganye amfani a jiki maigyada tana yi mana dariya tana fadin Hajiya kenan na ce eh to in banda dai sha'awa 60 mai sama da wadannan kurarraji yaushe zai iya cin ganye? Uwa ta tasa ganyen nan tana kallo nima ban tanka mata ba tunda dai ta yarda ta shanye ruwan sai ta kalle ni tayi murmushinta a hankali ta ce Umma ina son yi miki wata magana, ina tsoron nayi maza na ce haba Uwa tsoro ya hana ki gaya min magana, to wa za ki gayawa in ba ni ba? Ta dan saki wani lallausan murmushi ta ce kar hankalinki ya tashi ne nayi maza na ce mata gaya min kawai ba zai tashi ba ta ce idonane Umma bai gane kalan abu komai sai nake ganinshi baki gashi kuma sai in rinka ganin mutane suna rabuwa mun bibbiyu. Yanke jiki nayi na fadi a kasa saboda tsananin firgita da nayi da wannan bayani na Uwa, ciccibata akayi aka kaini daki nayi kuka rannan har na gaji ban daina ba, da Alhaji yazo dubani don anje an gaya mishi abin da ya faru na ce mishi aje a dauko ban boye mata komai ba ban ki gaya mata abin da nake tsoro ba don ta riga ta zama min 'yar uwa da na gama yi mata bayani sai kawai ta kalle ni cikin natsuwa ta ce to kina ganin kamar in muka hadu a nan da wani abin da zamu hana ne? Nayi maza nace mata bamu isa komai ba taya ni zaman gidan zaki yi, ta ce to shi kenan. Muka tasa Uwa a gaba ni 61 kam komai tayi idona yana kanta sai dai banga wata alama ba. Rannan muna kwance ni da ita a gado dama kuma tare muke kwanciya ita kuwa yaya Balki tana daya gadon sai naji tamfar Uwa tayi magana na ce mata me kike fadi? Sai da nayi mata tambayar sau biyu sai ta ce bada ke ba ne nace da waye? Ta ce da wannan ne

Chapter 3 of 7