Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
na sake jin wani faduwar gaban nayi maza na mike zaune na ce mata a ina kika ganshi Uwa? Kan ta ce min komai sai yaya Balki ta ce min ke kuwa me yasa kike irin wannan binciken ne Zuwaira? Me za ki iya yi ne? Kinga yanda kika maida kanki kuwa cikin 'yan kwanakin nan? Ashe shi mai imani ba da mika wuya aka sanshi ba? Kalaman yaya Balki ba su hanani kuka ba, cewar da uwa tayi da Muntaka take magana ya kara firgitani ina kuka na cewa Yaya Balki sai yaushe zan samu abin da nake so? Duk wanda naso rasa shi nake yi ta ce min da dai kin tuba kin yi ta istigafari kar ki sanya kanki cikin wata fitina, duk abin da kika so kika rasa din ai ba naki ba ne ajiyanshi aka baki ko sai mai shi ya fasa karba don kina so? Kwana biyu bayan nanne kawai Uwa ta haifi yarta mace bayan yar gajeriyar nakuda mai sauki bata kai awa guda bayan nan ba ta ce 62 garinku na kalle ta a kwance a shimfide na ce shi kenan Uwa shi kenan Rabi'atu kun tafi ke da mijinki kun bar min 'yarku shi kenan maimakon in yi kuka mikewa nayi naje na soma shirya ruwan da za'ayi mata wanka ni da kaina na wanketa da taimakon Maryam da Hauwa na sanya mata kayanta nayi mata addu'a aka zo aka fita da ita ina kallo nayi zaman karbar gaisuwa kwana uku da akayi bakwai kuma Alhaji ya ce sunanki Rabi'atu ya mayar miki da sunan Uwarki, na sa maigyada ta nemo min mai reno ta kawo min Talatu, da aka yi sati biyu sai na samu Alhaji na ce mishi so nake ya yardan min in je Katagun in dan zauna a dakin Baba in dan huta, ya ce min to in dan saurare shi tukuna na ce to. Rannan da ya shirya zai yi tafiya sai kawai ya ce min dauko yarki muje na ce mishi to, dani yayi wannan tafiyar da muka dawo kuma bai dawo dani gida ba sai ya ajiye ni a gidanshi na Legos, bai kuma sake sha'ani za'ayi sai bayan shekaru uku sai dai yaya Balki kanje Legos tayi min bakunta, tun bakuntar farko da taje mun kuwa na ce mata taje ta kwashe kayan dakina taje ta gyara nata wurin. Sai da aka gama ginin gidan nan na dawo muka sake haduwa dasu Karama saboda a lokacin kuma Alhaji yayi nufin sake hada 63 iyalinshi wuri, daya na, zo,na samu gida, çike da iyali ga yara maza da mata don sun riga ni dawowa. Nadaga ido na kalli Ummana cikin tausayawa bakin cikin da tayi na rasa wadanda taake, so nayi ajiyar zuciya sannanna, ge mata wato dai Umma ba ke kika, haife ni, ba mutanen da kike so ne suka haifan miki ni? Sai da ta zuba min ido kafin ta ce min kwarai kuwa, na kwantar da kaina jikinta na ce mata to sake gayawa kowa labarin nan Umma ki bar su kawai a kan ke kika haife ni tunda ma dai a nononki nasha na girma. Umma tayi murmushin farko tunda, ta fara ban labarin ta ce ban shayar dake nonona ba Adawiyya, Alhaji bai yarda nayi hakan ba na rene ki ne ta hanyar shayar dake da abincin jarirai, Babangida shine yaron da na, shayar dashi nonona, ina ganin biyu bisa ukun nonon da ya sha nawa ne saboda kullum a wurina yake kuma a wancan lokacin, Maryam kanyi yaji in Suka yi fada da Karama, ta barshi kan wannan dalilin sai ya zama nike shayar dashi.,Nan take naji kishin yaya Almu ya kama ni na ce wato yaya Almu ma danki ne? Ta yi maza tace nawa mana Adawiyya, Alhajj ne fa ya haife shi Babu kuma ya bani shi na kuma rene shi ta 64 hanyar shayar dashi nonona, shi kuma bai taba nuna min yasan yana da wata Uwa ba in ba ni ba ce Lamido ai na wane Adawiyyah nawa ne, ke kuwa Muntaka da uwana ne suka haifanmu ke, don haka bani da kamarku ke dashi sai ko Junaidu dukanku na wane hakan nema yasa na baiwa Alhaji sunan Junaidu lokacin da ya ce in taya shi zaben wanda zai barwa shugabancin kamfanoninshi. Na daga ido na kalli Umma zuciyata ta sake raya min wasu al'amura game da ita, ban sani ba ko ta gane tunani nake yi sai na ji ta ce min taimake ni kar ki ji wani canji a tare da ni don na ce miki bani ce mahaifiyarki ba, ke din kece komai nawa kece Muntaka, kece kuma Uwa, a duk lokacin da na daga ido na kalle ki na kan ganki ne da kamanni guda biyu, kina kama da Muntaka kamannin dake sawa mutane suna ganin kamanninki dani amma ni da aka haifi Uwa akan idona na kuma rene ta ta girma a gabana nasan abubuwanki da yawa nata ne mafi yawancin lokaci nakan biki da kallo ne saboda wasu abubuwa da kike yi wadanda nake ganin tamfar koyar dake su tayi sai dai kuma tunda nasan baki santa ba to na sanbà koyo ba ne gado ne. 65 Na matsa jikin Umma na kwantar da kaina a cinyarta cikin hawayen tausayi nace mata, kece komai dina Umma ba zan canza komai ba game da ke sai dai ma in kara sonki....kan Umma ta ce min komai sai naji muryar Baba a cikin falon Umma yana cewa me Zuwaira take yi ne a wurin nan ta barni ni kadai har yanzu? Kan tayi magana sai Baba ya shigo ya gammu tare, ashe baki baiwa Lamido matarshi ba shima ya samu ya huta kamar sauran 'yan uwanshi? Umma ta ce kayi hakuri gani nan zuwa, ya ce a'a kar ki zo alamar yayi fushi, ya juya ya tafi. Umma tayi maza ta dauki wayarta ta kira Umma amarya taimake ni kije gun Alhaji kar ki bari yayi fushi sai da safe zan shiga wurin naku ta maida wayar ta ajiye hakan da Umma tayi bani wani mamaki ba don nasha ganin tana baiwa Umma amarya kyautan girkinta. Gari na wayewa Hajiya Hauwa ta iso saboda wayar asuba da Umma tayi mata tana shigowa ta ce mata 'yarki zaki kai gidan mijin ta tun Alhaji bai fito ya ce ta tafi ita kadai ba ki ce don ni uwar miji ce yasa na bari yayi hakan Umma Hauwa ta ce eh mana me zai hana ni fada? Umma Karama kawai aka kai ni nayiwa sallama saboda Umma amarya bata fito daga wurin baba ba, a haka muka bar gidan daga ni 66 sai Umma Hauwa sai ko Baba Talatu da Ummma ta ce ta biyo ni don dama zamana take yi a pgidan muna tafiya ni da Umma abaya direba da Baba Talatu a gaba Umma Hauwa ta ce to ke Talatu ai gara ki hakura ki bar kuka haka tunda ga uwar dakinki kuna tare. Ni kam har muka kusa isa kaduna ina kuka, tausayin Ummana ne ya ke damuna ko damna can babu abin da nake so kamar Umma, amma ban taba sonta ba kwatankwacin son da nake yi mata a yau ba. Mun kusa shiga Kaduna direba yana kallon motar dake biye dashi ta cikin madubi saboda bata wurin da yayi ta wuce taki ya ce au Hajiya ai Lamido ne yake biye damu, Umma Hauwa tayi murnmushi ta ce, a to, uwarshi ta ce wai yayi gaba saboda yayi fushi da abin da Adawiyya tayi mishi ana fushi da Amarya ne? Yaya Almu ne ya wuce direba yabi bayanshi muka karasa gidan babu kowa a cikin gidan yaya Almu ne yasa makullai ya bude ko ina muka shiga ko'ina gwanin sha'awa sai kamshi da kamshi ke tashi komai tsaf komai a tsare a tsaftace gwanin sha'awa ga wani sanyi na ni'ima ai Alhaji yayi dabara daya ce kowace amarya tabi angonta kawai ba sai an kaita ba da yanzu duk wurin nan an lalatashi, tana wannan 67 maganar ni kuwa ina takure wuri daya cikin lullu6i ina ta karanto addu'o'i iri-iri da Baba Balki ta bani ta ce in karantasu a lokacin da na shiga gidan mijina sai a wannan lokacin ne ta fado min a rai wato haka ta ce ita ce mahaifiyar Uwata, wani tausayin ya sake kama ni da na tuna su san san uwa wato mahaifiyata nice ban san taba ban santa ba ban san Babana ba sai Umma da Baba na sani. Wasu sabbin hawayen suka soma zuba abin da ya fusata Umma Hauwa tayi tayi min fadi baba Talatu tana ta bata hakuri. Direban da ya kawo mu ya shigo rike da manyan iedoji ya ajiye ya koma ya sake debo wasu ya kawo, Umma ta ce kai sun isa haka bai ga mu uku ba ne? Da aka natsa Umma ta sanya ni na sake wanka na tsalla kwalliya cikin wani tsalelen leshi mai matukar laushi ya kuma karbe ni sosai don ya dace da kalan jikina gashi kuma dama Jikin nawa yayi shar a dalilin lallen da ta mulke ni dashi gaba daya. Tunda muka iso babu wanda ya sake jin motsin yaya Almu sai da muka yi sallar La'asar Umma ta ce a kira mata shi don zata tafi, lokacin ne ya shigo dakin cikin ladabi a kasa ya zauna kamar yanda nima dama aka san ya same ni sai Umma ce akan kujera. Sai da ta amsa 68 gaisuwar da yayi mata sannan ta ce mishi ni zan tafi Lamido ga matarka nan na kawo maka ba sai na ce maka komai ba, kafi kowa saninta, kayi tayin hakuri Allah ya saba halayenku ya kuma sa ta zame maka uwar iyali tana fadin hakan ta mike tayi waje tana goge fuskarta da gefen gyalenta yaya Almu ya mike cikin natsuwa ya bi bayanta don ganin tafiyarta. Baba Talatu kuma ta shigo tana ta bani hakuri tana cewa aike aure mai dadi kika yi uwardakina mijin da zai yi hakuri dake ai shi aka baki. Yaya Almu ya sake shigowa bayan tafiyar Umma Hauwa Baba Talatu tana ganin shi ta mike zata fita ya ce a'a kuyi zamanku Baba Talatu ya juya ya fita bai sake shigowa ba sai bayan sallar Isha'i, yaya dai Baba akwai damuwa ne? Tayi maza ta ce mishi babu babangida ya ce to kuna son wani abunci? Ta sake cewa a'a bamu da bukatar komai don akwai, yayi murmushi ya ce, to sai yaushe amaryar zata fara yin magana? Ta taya shi murmushin don jin ya shigar da raha cikin lamarin yace ina jin dai so take a sayi bakinta, ya juya zai fita yana cewa, ta yata kwana Baba, da sauri Baba Talatu ta ce mishi a'a ai ba za ayi haka dani ba, ba girmana ba ne yin hakan bai tsaya ba ya tafi. Da sauri na kalli Baba Talatu na 69 ce mata me yasa kika gaya mishi haka? Ta ce wane ni ai kawaici yayi mun so kike in jira shi sai ya ce in bashi wuri? Tana Cikin maganar wai kawai naji yaya Almu ya sake shigowa ta wata kofar daban san da ita ba Baba Talatu tana ganin haka tayi maza ta fice ta tafi wurinta shima yana karasowa ya maida kofar falon ya kulle ya dawo inda nake zaune cikin murmushi nazo sayen bakin amarya ne, yana maganar yana kallona ya miko hanmu a hankali ya tallabi habata ya karanto wasu addu'o'i ya tofa min a fuskata sanan ya mike ya sure ni zuwa daya daga cikin dakinan kwanan da suke wurin. Da Asuba na bi umarnin da ya bani na komawa daya dakin na kwanta bayan na idar da sallar Asuba kas ancewar tsawon daren ban samu na runtsa ba ga kunma gajiya da rashin bacci na kwana da kwanaki bacci mai nauyi Sosai nayi ban farka ba sai bayan shabiyu ko lokacin ma kuwa dana farkka dana lura sai na gane Baba Talatu ce ta taslhe ni saboda ganinta da nayi tana matsa min kafata, na kalle ta cikin natsuwa maimakon in gaya mata wata magana saboda kidimewa sai na ce mata bani da lafiya Baba tayi maza ta ce na sani uwardakina ko daga farin cikin maigidan da na gani na san abin da ake ciki balle tun safe ya wanke shinfidun da suka 70 lalace ya shanya su ga kuma alheri mai yawa da yayi min turaren atamfofi da turare gami da kudi ya bani Allah dai yayi muku albarka ya kuma sa ku zame mishi uwar iyalinshi. Ban tanka mata ba don ba abin da nake nufin gaya mata kenan ba na so ne kawai ta fahimci zazzabi ya kama ni. Mikewa nayi cikin karfin hali na shiga bandakin na dan hora kaina da ruwan zafin da na zubawa detol tunda na riga na girma ba sai na jira an gaya min abin da zan taimaki kaina dashi ba, na fito na samu abincin da ta kawo min na gama koma1 na sanya kayana bayan na gyara kaina nayi matukar yin kyau zani da riga na sanya na yadin material mai kyaun gaske, har na zauna da shirin ka ryawa sai na tambayi Baba Talatu yaya Almu ya fita ne? Ta ce a'a na ce to me aka kai mish1? Ta ce bai karbi komai ba na dai ce mishi akwai. tsallake abin karyawan nawa nayi na nufi kicin din don ganin abin da zan shirya mishi tunda na gane shima ba karya ba nan da nan na shirya mishi abubuwa masu sauki na hada da farfesun kajin da Baba Talatu tayi da na koda naje na har falonshi na kai mishi sai dai ban yarda na zauna mun karya tare ba kamar yanda ya nemi inyi fitowa nayi na dawo wajena na zuana ina karyawa da Baba Talatu tana yi min hira sai dai 71 gaba daya hirar tata yau kan budurcin ya mace ne ni kam ina jinta. Tun daga rannan na shiga kicin don girkin abincin da yaya Almu zai ci ban yarda amarci ya hanani yin hakan ba saboda irin kalaman da Umma na tayi mun kan muhimmancin aure da kuma kula da miji, sai dai kuma na kasa daurewa in barshi ya sake matsowa kusa dani saboda gani nake tanfar ya kware ni ko kuma in ce ya so kanshi da yawa a kaina don haka ina kai mishi abincin nake dawowa wurin in shiga in kulle ko'ina in yi kwanciyata. Rannan da safe ina kicin zan shirya mana abin karyawa rannan kuwa satina guda ne a gidan sai ya shigo kicin din yazo ya same ni ya ce amuna dai kin san tunda kika zo baki yi mun shinfida ba cikin ladabi na ce mishi bari in gama in zo in yi ya ce a'a bar wannan aikin kije kiyi mun wancan din tukuna, don ya fi muhimmanci a wurina na ce to na yi maza na wanke hannuna da sabulu na goge shi da tawul kafin na shiga dakina naje na dauko wani zanin gadon da zan canza mishi sai da na shiga can cikin dakin dakin wanda sai ranar na fara shiga naga komai a kintse a tsabtace ga kamshi mai dadi dake tashi a ciki, lokacinne na gane wayon da yaya Almu yayi mun saboda ganinshi da nayi a jikin 72 kofa r dana biyo ya tsare ko'ina ban ce mishi komai ba don na riga na gane abin da yake nufi. Abin da yaga dama yayi shi da kanshi kuma nasan yasan ya kware ni tunda duk wani abin da yayi na ya gamsar da kanshi ne kawai, na kwance a gefe ina kallonshi cikin hikima a zuciyata dai tunani nake yi ko kowa haka yake ko kuwa yaya Almu ne kawai mai irin wannan halin? Ban ankara ba da idona ya kai kan agogo sai naga wai sha biyu ta wuce na yunkura cikin karfin hali na fita na bar dakin yana kirana rabi, ban tanka mishi ba na koma dakina na zauna Baba ta biyo ni za'ayi miki wani abu ne? Na ce mata a'a in dai kin karya shi kenan ta ce to ta juya ta fita nima nayi abin da zanyi na kwanta. Tun daga rannan na yiwa yaya Almu ya ji ban sake yi mishi girki ba ban sake leka koda falonshi ba ne balle in kai ga shiga ko tsakar gida bana shigowa. Kwanana hudu da daukan wannan matakin ina kwance a dakina tun safe ban fito ba shima yaya Almu yana wurin shi sai kawai na ji sallamar da ta yi min kama da muryar Ummana da gudu na yiwo waje ashe kuwa ita ce sai dai har ta shiga wurin yaya Almu can na same su yana ta faman ina yaka saka da ita. Fadawa nayi Jikinta na kwanta ina tumurmusarta kamar wata 73 yar yarinya yaya Almu ne ya kawo mata abin sha ya koma gefe ya zauna cikin farin ciki yana cewa Umma ba ki ce mana zaki zo ba. Ta ce eh ai zuwan nawa ba na shiri ba ne Talatu ce tayi mun waya ta ce bata gane kan matar gidan ba da farko dai ta kar6i hidimar gidanta gwanin sha'awa amma yan kwanakin nan bata gane mata ba shi ne na ce to bari in zo in ji me ya faru? Na nemi wuri na zauna cikin natsuwa saboda jin maganar tata ban ga kuma alamar wasa a tare da ita ba, ta sake kallona ta ce me ya same ki Talatu ta ce kin saki hidimar mijinki? Ban yi magana ba na soma kuka saboda ganewan da nayi cewa dan kankanin laifi zanyi tayi min fada ganin ina kuka sai ta juya wurin yaya Almu ta tambaye shi nayi zaton ba zai yi magana ba sai kawai naji yace wai daga nasata ta shigo dakina ne Umma. Umma tayi shiru ba ta ce mishi komai ba, ta dai yi wasu yan maganganu ta mike zata tafi na ce baki shiga wurina ba fa Umma, ta ce sai randa na sake zuwa tunda ba kya jin magana ta fita waje Baba Talatu ta fito tana yi mata magana ta kawo kudi ta bata ta shiga mota ta tafi ta barni ina cizon yatsa saboda takaicin kin shiga wurina da tayi yan kwanaki kadan bayan wannan lokacin har nan kuma ban yarda mun 74 shirya da yaya Almu ba don nasan abin da shirin namu yake nufi sai kawai Umma ta bugo mun waya dana dauka sai ta ce min shiryawa zaki yi kiyi wa Lamido rakiya zuwa kasar Philipine kuje can kuyi amarcin daga nan kuma akwai aikin da zai yiwa Alhaji in kuma har ku ka dawo ba ki saki jiki dashi ba zan sa Talatu ta koma gida abar ku ku biyu a gidan ai kunyarta yake ji da bai yarda da wannan sakaran ba. To hakan kuwa akayi ba karamin morewa amarci yaya Almu yayi ba a wannan tafiya da muka yi tunda daki daya muke bayan haka kuma na kara yarda da maganar Umma ta cewar kunyar Baba Talatu yake ji. Cikin sati ukun da muka yi ya tilasta min sabawa da lalurarshi akan dole na hakura da hakan don babu dama yaga na bata rai sai ya ce min raguwa kawai, yara kanana ma ana aurensu su zauna kalau da mazansu balle ke bari muna komawa gida naga za ki sake kawo min wani sakarci sallamar Baba Talatu zanyi daga nan ta koma gida ta zauna tunda ba ki fahimci adalcina ba kina so ki fake bayan kunyar ta da nake ji ki takura min. Ban ce mishi komai ba har muka gama abin da zai yi muka dawo gida, a Legos muka sauka wurin Baba don yi mishi bayanin komai, Ummanane a wurinshi don bhaka ba karamin 75 sauka muka samu ba. Bayan mun gama cin abinci falon Baba ni da Umma muka dawo dakinta muna shiga ta ce mun kinga kyan da kika yi kuwa, ko kuwa dai kin tsallake wata ne? Na ce kai Umma kenan, na ki maganar ta ce cika na soma yi mata kukan shagwaba ina fadin, bana son abin da kike yi min Umma, ta ce to na daina, na daina Adawiyya. Ba mu dawo gida ba sai da muka je gidan yaya Junaidu wanda a yanzu na fahimci kawunane kanin mahaifiyata uwa daya uba daya, ita tasha nono ta bar mishi. Wata sabuwar mu'amalla muka yi tsakanina da Yaya Junaidu, girman darajarshi ya karu a idona shima ya kara kamewa sosai alamar dai ya na game matsayinshi a wurina, itama Anti Rahma kauna mai yawa ta nuna min da kulawa da zamu tafi kuma sai ta ce min ke 'ya ce a gidan nan kawunki ya riga yayi min bayanin komai don haka bai yiwuwa ki shigo gidan nan ki fita ba tare da kin ce ga abin da kike so ba, na yi murmushi na ce Anti Rahma Philipine muka fito kan hanyarmu ta dawowa kuma mun tsaya a Dubai. Ta ce ko a ina kika tsaya ai bai wuce in yi miki kyauta irin ta uwa ga 'yarta ba, na ce haka ne Anti, to hijabin dake iikinshi yayi min kyau 76 ina son shi, warddrop ta bude ta debo mun sabbi guda shida tana zuba min su cikin ledar shagon da aka saye su tana gaya min ai fitinar. kawunki yawa ne da ita wai har a cikin gida bai yarda in rinka yawo haka ba, saboda masu shigowa gidan nayi murmushi na ce yana da gaskiya Anti, mun fito falo inda su yaya Almu suke na zauna cikin ladabi ina yiwa Yaya Junaidu sallama sai ya ce min haka za ki fita ba ki dauki komai a gidan ba? Na ce na dauka na samu hijabai masu kyau wurin Anti Rahma, ya ce to madalla ku gaida gida. Mun dawo gida ni da yaya Almu abin gwanin sha'awa amarci sosai muke yi ni da shi, jin juna a rai muke yi yaya Almu ji yake tamfar ya lashe ni don dadi, ganin na saki jiki dashi na daina tsananta yi mishi rowar kaina sai dai in yi mishi shagwaba. Munyi matukar shakuwa tamfar dai auren namu ba sabo ba ne, ko da dai dama can akwai sabo da shakuwa mai yawa a tsakaninmu, to amma kuma ai shakuwar miji da mata daban ne tunda shakuwa ce ta aure. Muna isowa gida a dakin Yaya Almu muka tare abin da ya ce kenan hakan kuwa nayi mishi sai in wuni in kwana ban shi sa wurina ba in har ba bakuwa ce tazo ba ma dakinshi komai zanyi anan nake yi nasa hannu biyu na karbi hidimar 77 mijina da gidana, gaba daya kowane lokaci cikin shirya mishi nau'o'in abinci iri-iri nake yaya Almu mutum ne da ya san darajar mace ba mutum ba ne da ya damu da ya zauna komai sai anyi mishi in ma yaga zanyi dawainiya mai yawa zai taya ni zai kuma gaya min duk wannan abin da kike yi fa yi kike yi kawai don neman lada amma muhimmin aikinki anan gidan shine gyara mun shimfida. In ce mishi kai yaya Almu kar fa Baba Talatu ta ji ka, murmushi yake yi ya ce ba komai don ta ji ni tasan gaskiya nake fadi. Ina jin dadin zama da Baba Talatu ina kuma son zama da ita din a yau kuma ban dauke ta mai yi min hidima ba na dauke ta wani bangare nawa tanfar uwa musamman da na gane son da take yi mun na gaskiya ne, tunda taga zan bata wa mijina tayi maz ata shaidawa Ummana tazo tayi gyara ban da haka baba Talatu mai kamun kai ne mai rike girmanta ganewan da tayi yaya Almu ma'abocin shiga kicin ne in har ina ciki in ta ganni zan yi girki tasan yana gida kauda jikinta take yi ta shige wurin ta, da nayi mata magana sai ta ce min Lamido mai kunya ne bai, kamata in rinka nema in takura mishi ba, ganewar da nayi Baba Talatu tana sona tana 78 kuma son mijina sai na kara sonta da ganin girmanta. Rannan muna hira da Baba Talatu a tsakar gida saboda yaya Almu baya nan yana Abuja, don yana da case a babbar kotun Abuja, wato (Court of Apeal). Baba Talatu bani wani tsohon labari na wani abin da aka yi tun ina 'yar karama sai da na gama sauraronta naji tayi shiru sai na ce mata Baba za ki yi mana girki ne yau? Ta kalle ni ta ce saboda Lamido baya nan shi ne ba za ki yi mana ba ko? Na yi murmushi na ce a'a Baba bana jin dadi ne kawai yau kuiya nake ji shi yasa na ce bari in huta, ta yi murmushi ta ce sai in yi mana ai ma ina ganin kokarinki ke cikinki bai saki wani laulayi mai tsanani tanfar ba cikin fari ba. Nayi murmushi na ce tafdijan, wai ni me yasa ake yi min haka ne Baba? Babu dama in dan yi wani abu sai ace ciki Umma ta ce ciki yaya Almu ma haka gashi kema kin fara, ta ce eh ai kinyi kama da mai cikin ne kinga yanda kika dawo kuwa? Na ce to bani da komai sai na gama cin amarcina tukuna, tayi maza ta ce uh'uh kar dai kiyi wani abin da za ki kwari kanki ciki ba zai hana ki Cin amarci anan gidan ba sai dai ma ya kara miki ba sai na tsaya ina gaya miki darajar dan da za ki haifarwa Babangida ba, kin 79 kuma Sani sarai uwarki zata fi kowa murnar ganin hakan. Kwanaki kadan bayan nan na samu kaina cikin al'ada, yi alwala ki zo muyi sallah kinga ban samu jam'i ba a masallaci, yaya AImu ne ya ban wannan umarnin, sai na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi, ai da na je wanka dazu sai naga al'ada tazo min shi yasa ban yiwo alwala daga can ba, abin da kawai na gaya mishi kenan ya tsuke fuska tanfar wani mummunan labari na bashi. Cikin dare muna kwance na farka daga bacci na ganshi ido biyu, me ya faru yaya Almu kko kana da wata shari'ar ne gobe? Ya dan yi ajiyar zuciya kadan ya ce, al'adarki ce ta ishe ni, ni tana takura min a dalilin in tazo bata daukewa da wuri, gashi kuma dama na tsani ganin kina yinta, na ce ba ka son ganin ina yi fa ka ce? Yayi maza ya ce eh bana so shiga tsakanina dake take yi tsawon kwanaki bakwai ban da haka kuma na gaji da ganinki haka so nake in ganki da ciki Rabi, ya zuba min ido cikin natsuwa yana kallona, na dan matsa kusa dashi don in kwantar mishi da hankali sai na ce mishi ai amarci muke yi yanzu yaya, yayi maza ya ce bana son amarcin ya ishe ni haka tunda ke a wurinki in an samu ciki amarci ya kare ne, kina 80 nufin ki ce min sauran 'yan matan dukansu sun daina amarckine?

Chapter 4 of 7