Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
zaka hanani fadin gaskiya ba, in ban da taje ta dauko ubana yazo nan ya haife ni me zai hada ni da ku? In ban da ta...kan in fadi abin da zan fada din yayi wuf ya cukume ni yayi waje dani yana fadin tunda kinyi hauka Rabi muje gida kiyi a 100 can ba a gaban Umma zakiyi wannan rashin mutuncin ba. Mun fito yana kokarin tura ni cikin motarshi saboda tuburewar da nayi, ba zan bishi ba sai ga Umma amarya ta fito daga wurinta tana ganin mu tayi mishi tsawa, menene haka? Ya juyo yana kallonta kan yayi magana ta sake cewa menene haka? Wane irin rashin hankali ne wannan? Cikin ladabi ya ce mata gida zan kaita Umma wani abu ya sanme ta baki ji maganganun da take gayawa Umma ba, ta ce mishi sake ta, ya sake ni na tsuguna a kasa inä kuka, ta ce mun tashi ki shiga ciki, nabi umarnin da ta bani ina shiga ta biyo bayana bata bar ni na zauna ba ta ce inje inyi wanka na fito na gyara jikina na sanya wata doguwar riga da na samu ta ajiye mun, na fito na same ta a falo tana zaune abin ka ryawa ta fara bani nasha ruwan zafi don abin da kawai naji zan 1ya sha kenan. Ta zuba min ido tana kallona cikin natsuwa ta ce min, "Al haji ne yake son mijinki yayi aure laifin Hajiya guda daya ne da taja ta tsaya kan 1alle sai ya karbi wannan yarinyar da aka bashi, ni da naso ne ta fita cikin maganar ta barshi ya bijirewa wannan auren kamar yanda ya bijirewa saura da aka bashi ya ki karba, in yaso daga baya shi yaje ya nemarwa kanshi auren da 101 kanshi tunda ita wannan yarinyar ma da aka bashi ai munafurci ne yasa aka yi hakan ina dalilin da za ace Alhaji duniya abi sannu ne zai bashi aure? Tun yaushe ne mu'amalla taja baya tsakaninshi da Alhaji? Lokacin ne na san na dago kai na kalli Umma amarya na ce Umma 'yar gidan Hajiya Hairan kenan zai aura? Ta ce eh ita ce, nan da nan naji gumi yana feso min a jikina, saboda ganewar da nayi cewar da hannun Umma Karama cikin maganar auren don kuwa bata da wata Aminiyar da ta wuce Hajiya Hairan, haka nan saboda daukar zafi irin nata da taya Umma Karama kishi da take yi ko magana bata yi da Ummana, sai in Ummance ta gaishe ta, to wai ita ce zata baiwa yaya Almu aure, sannan ita Umma tana sane amma wai taja ta tsaya kan sai lalle yaya Almu ya karbi wannan auren cikin ladabi da natsuwa, na ce mata zan je mu tafi Umma kar yayi ta jirana, ta ce to kuje gida lafiya karki nemi wata magana ina amfanin wannan abin da yayi miki? Gashi ya kunbura miki gefen fuskarki babu kyan gani, ban ce mata komai ba nayi mata sallama na fito banga yaya Almu da motarshi ba, abin yayi min dadi nayi maza na kama hanyar fita gidan, ina fitowa sai gashi a bakin get yana zaune a bayan motar yana ganina ya diro yazo ya bude kofar 102 motar ya ce min zo ki shiga kawai, girma da arziki kin dai san nan kofar gida ne, kafin Umma amarya ta kawo miki agaji kin riga kin ji jiki, ban yi musun shiga ba saboda nasan gaskiya ya fada. Na shiga na zauna muka kama hanyar tafiya, na ce mishi dama 'yar gidan Hajiya Hairan zaka aura? Bai kallen ba ya ce eh menene? Na ce ban yarda da auren ba ne tunda kai ma kasan munafurci ne yasa aka baka ita, in ma kaga kana Son yin auren ne to na yarda kaje ka auri wata yarinyar amma ba ita ba, in dai har kana so in kayi a zauna lafiya. Sai da ya galla min dan banzan harara kafin yaja wani irin uban tsaki ya ce in anyi ki hana zama lafiya, sakarya mara hankali, mara kunya, mara mutunci, wacce gata ya maida ita shashasha, a gabana kika zagi Umma? har kina ce mata wai kin bar min ita? Kin taba jin ance miki takice? Sai da ya waiwayo ya kalle ni sannan ya ce min wai me kika dauki kanki ne ma tukuna? Ke kin dauka kin fini matsayi ne a wurinta? In ba ki sani ba in gaya miki, ni danta ne da ta shayar da nononta kinga kuwa tafi karfin in barwa wani ita na kuma fi karfin ace an bar min ita, dama tawa ce tare kika ganmu tare kuma zaki barmu, da cikin girma da arziki 103 ne kika ce min in bar wannan yarinyar in nemi wata da kinyi mamakin adalcin da nayi miki, amma tunda kika gayawa uwata maganar banza akan idona to sai nayi aurcn inga iyakar tsiyar da kika iya. Har muka isa gida ban daina kuka ba, ban kuma cewa yaya Almu komai ba saboda ban saba irin wadannan maganganun dashi ba, ban saba gayawa mijina bakar magana ba, gashi dai maganganu sai zuwa mun suke yi a zuciyata wadanda zan gaya mishi in rama abin da yake fada amma sanin da nayi in na fadi tawa magan ar ba kwashewa kalau zanyi ba, zunubi za a rubuta min tukuicin gayawa miji bakar magana sai naja bakina nayi shiru, in na ga abin yayi yawa dai na kan rama a zuci amma ba da baki ba, tunda sai na furta da baki ne za a rubuta min zunubin. Muna isa gida na samu Baba Talatu tana jiranmu don yaya Almu yayi mata bayani ina shiga dakina ta biyo ni' tana fadin hakuri kawai zaki yi uwardakina, ni tausayin Hajiya ne ma ya fi kama ni nayi maza na ce mata tausayin Umma? Jmma ai ita ce ta ce sai yaya Almu ya karbi auren cikin tausayawa ta ce waiyo to yaya za tayi? Zata hana shi aure ne? Wannan kishiya indai kina da hankali ai bake za'a yiwa ita ba. 104 Hajiya Karama ce fa sanadin auren, sannan kice dake ake yi? Dogon bayanin da Baba Talatu tayi min shi ne ya fahimtar dani cewar lalle kishiyar da ake nufin yi min din ba karamin al'amari take nufi ba, sanin da Umma Karama tayi cewar ni1 din ba zan haihu ba shi yasa tayi kutun-kutun din da Aminiyarta tasa mijinta ya fake da tsohon zumuncin dake tsakaninshi da Baba ya ce ya baiwa yaya Almu auren yarshi don ita tazo ta haihu don itama ta samu wata dama akan yaya Almu ta haka ne take ganin zata iya karbarwa Umma shi. Kishi mai tsanani ya kama ni da na tuna duk sanadin wannan abin rashin haihuwata ne, na tuna kalaman yaya Almu game da haihuwa na tuna kafin ya debe tsammani daga gare ni irin alkawuran da yake yi min daga ranar da kika yi min albishir da daukewar wannan fitinanniyar al'adar taki da duk wata sai tazo ta takura min Rabi ni kuma zanyi miki albishir da farin cikin da ba zai yanke miki ba, daya daga cikin kalamanshi na wancan lokacin kenan. Ashe ba ni ce zan yiwa yaya Almu wannan albishir din ba, na daga ido na kalli Baba Talatu na ce mata, zamana ne kawai yazo karshe ni da Yaya Almu, komai kuma yana da sanadinshi, ina fadin haka sai ta kama kuka tana rokona kar in yi haka, 105 dama abin da ake son gani kenan, na ce ba komai Baba gara mun hakan ba zan iya zama da yaya Almu ina gani wata mata tazo ta haifar mishi 'ya'ya ni bani da ko daya ba, yau in da ina da ko guda daya ne to da shi kenan sai in iya fuskantar kowace irin kishiya ce zata zo min, to amma bani da ko daya ba kuma zan haifa ba, yaya zanyi? Baba Talatu tayi kuka har ta gaji. Rannan ina zaune akan gadona cikin dare ina rungume da filo akan cinyata na makalkale shi a kirjina da hannayena duka biyu, tunani kawai nake y1 in saka wannan in kwance 1n saka wancan. Ina cikin wannan halin ne sai naga yaya Almu ya turo ko far da ta hada mu ya shigo yana sanye da doguwar jallabiya fara a jikinshi, matsowa yayi ya karbe filon yayi jifa dashi ya kuma sa hannu biyu ya sure ni ya nufi dakinshi dani kan gadonshi ya aJiye ni ya kuma zauna a gefena ya dora hannunshi kan cinyata yana magana cikin natsuwa, kwanakin nan duka bana bacci Rabi kar ki dauka ko ina jin dadin abubuwan da suke faruwa ne, bana ji ni dake bamu taba samun wani sabani ba a shekaru. biyar din da muka yi in ban da wannan karon ban gaya miki maganganun da na gava miki don komai ba sai don ba zan iya hakuri dake akan 6atawa Umma ba, don haka kiyi hakuri ki kuma 106 yafe min marin da nayi miki. A hankali cikin natsuwa na ce mishi na yafe ya ce to na gode, ya canzawa hannunshi wuri don bukatarshi ta ci gaba da sake taba ni, na ce mishi ka taba yi min alkawarin ba zaka taba son kanka a kaina ba, ya ce eh nayi ban manta ba, ba kuma zan saba ba, na ce to na roke ka yanda kake kokarin samun abin da kake so nima ka taimake ni in samu, ya ce me kike so in taimake ki akai? Na ce ka taimake ni kar ka sake taba ni ka kuma taimake ni ka nuna min zumunci ta hanyar kin marawa Umma da duk wani mutumin da zai nemi tilasta ni zama da kai baya tilasta n1 zaman zai zamo kuntatawa a gare ni na kuma san ba za ka so in kuntata ba, cikin sanyin jiki ya ce min me kenan kike nufi? Na ce abin da nake nufi kenan zan tsaya kan maganata, da dama na taba gaya maka in kuma aka nemı tilasta ni zaman to zan 1ya daukar kowane irin matakı, to maimakon ay1 haka kuma gara ayi komai cikin zumunci da mutuntawa juna rai. Bai sake ce min komai ba har gari ya waye, sai dai daga ni har shi babu wanda ya samu runtsawa. Washe gari wurin taran safe naga wayar yaya Junaidu wai baba yana son ganina, don haka duk abin da nake ciki in bari inzo ni da yaya Almu, na ce to naje nayi shirina nayi kwalliya 107 SOsai ta yanda zan boye duk wata damuwa dake tare dani, don nasan zan samu Umma Karama a can. Kwalliyar da na dade ban yi ba nayi, na daura wani tsalelen leshi na kuma kawata kwalliyar da adon gold na yane jikina da gyale mahadin takalmina loeshoe da jakar da nake rike da ita wadanda suka yi matukar kara wa kwalliyar tawa kwarjini. Ni da yaya Almu muka isa gidan kai tsaye falon Baba muka wuce inda muka same shi shi da Umma Karama da yaya Junaidu. Na sake kallon Baba cikin ladabi na sake gaishe shi sannan na ce mishi Baba ance kana son ganina, ya ce eh uwata mijinki ne yayi waya ya gaya min wata magana da yace wai a bakinki ta fito, kin kuma ce mishi za ki tabbatar da cewar kin tsaya akanta, shi ne nace bari in neme ki in ji kina da matsala ne game da auren nashi da har kike nema ki kawo mana wani sabani? Na kalli Baba cikin natsuwa kamar in gaya mishi abin da ke raina sai kuma na tuna ba a gaban Umma Karama zan yi hakan ba, don haka sai na ce bani da wata matsala Baba, Baba ya dar. ji dadin hakan da na fada ya ce to maganar da ya ce kin fada din fa? na ce baba wannan tsakanina dashi ne bai yi tsananin da zai kawo ta gabanka ba. 108 Baba yayi maza ya ce haka ne Uwata, na kuma yarda da cewar ke ba za ki so kiyi abin da zai tayar mana da hankali ni da Uwarki ba, don haka komai zaki yi kiyi shi cikin fahimta da sanin cewar babu wata mata da Lamido zai aura ta kaiki balle ta wuce ki a wurinshi, ke matarshi ce auren saurayi da budurwa, ke kanwarshi ce da ku ka girma daki daya, sannan shi din kanin mahaifiyarki ne, yanda kema ke da shi ku ka girma gaban Zuwaira haka shi da uwarki suka yi, bisa wadannan dalilai ne na kira ki in gaya miki cewar zanyi bakin ciki in har kika yi abin da Lamido ya cemin kina shirin yi ina kuma so in kara jaddada miki cewar girman Zuwaira a wurina yana da yawa, don kuwa babana bai bar min wasiya kan komai ba sai kan abu biyu, na farko in rike zumunci na biyu kuwa in rike mishi amanar Zuwaira, kar kiyi abin da zai kawo matsala tsakanina da ita tunda kin san tana sonki." Na sunkuyar da kaina kasa na ce Baba tana Son yaya Almu fiye dani....da sauri yaya Junaidu ya katse ni ta hanyar daka min tsawa, ke Adawi yya! dakata kai Junaidu, shima Baba ya dakatar dashi kyale uwata tayi min magana gaya min menene damuwa rki? Me Zuwaira tayi da ya nuna miki cewar tana yiwa wani irin son 109 da take yi miki? Kin san su wanene suka haife ki? Kin san matsayinsu a wurin Zuwairah? Kin san Uwa? Kin san yanda take a gaban Zuwaira? Kin san Abdulhakam? Ko kinsan Zuwaira bata taba mu'amalla da wani nata ba sai a kanshi? Ko kin san har yau din nan shekaru kusan ashirin da rasuwarshi ni da ita ban taba yarda hirarshi ta hada mu ba? Kina nufin amincewar da tayi na Lamido yayi aure fifitashi tayi a kanki? Adalci ne kawai irin nata da irin wannan adalcin nata ne kuma dama ta zarcewa sauran 1mata ita babu son zuciya a cikin al'amarinta yanda kike 'ya haka Lamido yake haka Junaidu dukanku ya'yanta ne dukanku kuna bukatar tayi muku adalci amma tunda har maganar tazo gabana to gaya min abin da kike so ni inyi, na daga ido cikin natsuwa nace mishi, bani da wata bukata baba bani da damuwa kan maganar auren nashi. Baba ya ji dadin zancen nawa, ya ce yauwa Uwata maza kiyi koyi da halin uwarki ki zama jaruma mai yiwa kishiya adalci, ba don ita ba sai don mijinki cewar da zuwaira tayi Lamizo ya karbi auren da aka bashi tayi hakan ne don ta- mutuntani ni uban 'ya'ya mata ne kin sani akan idonki nasha bayar da uarensu ba tare da na tuntubi wadanda zan baiwa din ba, in na zubawa mijinki ido kowacce aka bashi ya ce 110 baya so saboda gudun bacin ranki, uwata in nima akayi min haka na bada kannenki aka dawo mun da su aka ce ba a so ba za ki taya ni bakin ciki ba? Na ce zan tayaka baba, ya ce tunda kuwa haka ne ai muma bai dace muyi ta maida na wasu ba ko kuwa na ce haka ne. Tsawon lokaci Baba yana yi min kalamai na kwantar da hankali zuwa can sai ya ce min yanzu me zaki gaya min da zai kwantar min da hankali in san ba za ki yi abin da zai batawa Zuwaira ba, na kara sakin fuskata nace zan karbi auren yaya Almu da hannu bibbiyu baba zan kuma yiwa matar da zai aura irin abin da Umma tayi wa nata kishiyoyin. Da sauri Baba ya shiga sanya min albarka, ya kalli yaya Junaidu yace mishi kai Junaidu a gabanka nace na danka al'amarin auren Lamido a hannun uwata taje ta shirya duk wani abin da tasan ana yi tun daga kayan zane har na aure ta aike dashi sai ka shirya bata kudin hidimar da zata yi duk abin da ta nema a bata, yaya Junaidu ya ce to Baba, ya sake waiwayowa wurina ya ce min Iwata kije ki shirya duk wani abin da ya dace in zaki yi kuma kar ki kalli Lamido ni za ki duba. Na ce to Baba, ya sallame mu muka tashi muka fita na bar Umma Karama a zaune rai a bace, ga dukkan alamu ba abin da taso ji ba 111 kenan, ina fitowa wurin Umma na na shiga na nemi wuri na zauna ina kallon hotonmu dake dakin ni da ita ne tun ban fi shekaru goma ba, cikin zuciyata kuwa tunani nake yi ya dai tabbata kenan yaya Almu zai yi aure tunda har gashi baba da kanshi ya danka al'amarin bukin a hannuna, ina cikin haka sai ga Yaya Almu ya shigo, nan zamu kwana ne ko gida zamu tafi? Na kalle shi cikin natsuwa na ce wanne yafi1 maka daidai? ya ce duk inda kika zaba duk daya ne Rabi, illa iyaka dai ina so ki zabar mana inda za mu fi sakewa tunda ni ban saba irin wannan abin da kike yi min ba, ban saba kina yi min rowar jikinki ba ki daina kinji Rabi? Ki bar ni inyi yanda na saba yi dake aike tawa ce Rabi kin kuma sha gaya min cewar komai naki nawa ne ke din mallakina ne har abada kuma ni kadai ne zan mallake ki, na daga ido kawai na kalli yaya Almu wani sabon kishin ya sake mamaye zuciyata, sai dai ban ce mishi komai ba har na kammala duk wani abin da zanyi nazo na hau gadon Umma na kwanta da shirin yin bacci sai gashi shima ya shigo gadon nata yazo zai hau, nayi maza na kalle shi na ce mishi gadon Umman zaka hau? Ya ce menene? Gadon uwata ne tunda kika hau ai nima kin san zan hau tunda Kin san na gaya miki wurin da zamu sake zaki 112 kai mu, na sake kallonshi a natse nace mishi wai me kake nufi da sakewa ne? Ni fa ina nan akan maganata ba kuma zan canza ba, cikin kaduwa ya zuba min ido yana kallona, maganganun da kika yi a gaban Baba fa Rabi? Kina nufin yaudararshi kika yi? Kina nufin ba za kiyi mishi alfarmar da ya nema a wurinki ba na ki barshi ya zauna lafiya da matarshi? Na daga ido na kalli yaya Almu na ce mishi nike rike da aurensu? Kafin namu auren ai nasu ya shekara arba'in suna yinshi kar kuma ka sake kai karata gaban Baba in kuwa ka sake yin hakan to zan tabbatar da cewar baka sake ganina ba nayi shiru na juya nayi kwanciyata. A haka muka dawo gida ni da yaya Almu abin babu dadi sai dai kuma bai bari wani-ya gane hakan ba balle aje ga kanwa gaban Baba, ni dashi dai abin ya ki dadi babu irin rarrashin da banyi min ba naki in sauko to ki bari mana sai anyi auren kinga anyi miki ba daidai ba in yaso duk matakin da zaki dauka sai ki dauka maimakon kice daurin auren kawai yana nufin naki auren ya kare, ina alkawuran da muka tayiwa juna Rabi? Kina nufin don kana son matarka ta gida sai hakan ya hana ka karo wata? Shi nanmiji fa mijin mata hudu ne an halatta mishi yin hakan sai wanda yasan ba zai ya 113 adalci ba ne aka ce mishi ya zauna da guda daya, ni kuwa ai ba mara adalci ba ne balle ko kice kan haka ban cancanci zama da mata biyu ba, ban tanka mishi ba shiru kawai nayi yayi ya gama yaja bakinshi yayi shiru. Kwana biyu bayan wannan maganar ina zaune a falona wajen karfe goma na safe tunda gari ya waye ban leka wurin yaya Almu ba balle inyi tunanin abin da zan shirya mishi don karyawa, zuwan Baba Talatu biyu tana tambayata ko za'a dama kunun gyada ne tunda taga yana so na ce mata a'a kyale shi kawai yana azumi ta ce to ta juya ta tafi ta kama aikinta, ina nan wurin a zaune cikin kwalliya sai dai kuma kwalliyar ce kawai amma can cikin zuciyata abin babau dadi, ina cikin tunanin abin da zai faru tsakanina da yaya Almu matukar bai je ya ce ya janye daga wannan auren na gulma da munafurci da ake shirin kullawa ba, sai kawai naga Hajiya Hauwa ta shigo cikin gidan babu wata wadatacciyar sallama ta kuma sha kwalliya cikin wata tsaleliyar atamfa da ta yiwa kanta wani irin dauri mai kama da rawani ta kuma turo shi gaban goshinta. Cikin zuciyata na ce kai Allah kadai yasan irin kwalliyar da Hajiya tayi sanda take cikin kuruciyarta, kas din da naji ya fito daga bakin Hajiya ne yasa na gane cingam 114 take taunawa, nan da nan na shiga taitayina don kuwa na santa kamar yanda na san yunwar cikina, cikin sanyin jiki na ce mata sannu da 2uwa Umma, yaushe ki ka dawo? Ta zuba min ido tana kallona, ta ce ran Uwarki kinjini ko baki jini ba? Ungo nan, ta sake miko min dakuwa da hannayenta duka biyu tare da fadin ja'ira mara kunya marà hankali, mara wayo, sakarya wacce bata san ciwon kanta ba, haka kawai Zuwairah ta kyale ki kina shashanci tana kallonki tana nema ta barki sai kin ja mana abin kunya a gari, in baki bar gidan Mustapha ba yau to baki haifu da kyau ba, tana fadin haka naga ta yaye safcecen gyalenta ta ajiye ta cire dan kwalinta data bata lokaci wajen nadewa ta ajiye, gashin kanta ya bayyana wanda yasha gyara cikin tsabta duk da furfura ta ratsashi. Ina cikin kallon wannan abin mamaki da ya soma tsoratani sai kawai naga Umma ta kama rigarta zata tubbe ni kam nan take na fashe da kuka yayin da ita kuma baba Talatu ta shiga bata hakuri kiyi hakuri Hajiya, kiyi hakuri taja ta tsaya tana kallon Baba Talatu cikin huci barni kawai in tube Talatu a gaban yarinyar nan yau don ta nuna min tabon da kishiya tayi min a jikina, wanda take tsoron ita kar tazo tayi mata shi, Baba Talatu ta shiga bada hakuri da ban 115 baki kala-kala da kyar ta samu Umma ta hakura da tubewan ta maida rigarta har taja gyalenta ta rufo ko' ina a jikinta ta gyara zama ta kalle ni ta ce min tunda kika san Zuwairah a rayuwarta kin taba saninta ita kadai a wurin mijinta? Nayi maza na ce mata a'a, ta ce ni anawa gidan mu nawa ne? Na ce ku hudu, ta sake kallona a saninki guda nawa aka yi min? Na ce ban sani ba Umma, ta ce to goma sha uku goma sun tafi mna tare da uku kin taba zuwa gidan kin samu wals a zaune a kaina? Na ce mata a'a, ta ce to yan uwanki da akayi musu kishiyoyi kin taba jin snyi wata magana? Kin taba jin wata magar.a ta fito bakinsu? Na girgiza kaina cikin zuciyaia kuwa ina tuna gaba daya ya'yanta mata amare ne da su, na ce kin taba jin su suna irin sakarcin da kike yi? Na ce a'a kan in gama rufe bakina sai kawai tayi caraf ta rike min shi da iyakacio karfinta tana fadin sai naki bakin ne baya iya yin shiru saboda ba a farsa miki shi da kyau ba? Na shiga fadin uh'un cikin zafi da kokarin kwatar kaina daga hannunta sai dai na kasa sa'boda irin rikon da tayiwa bakin nawa B.ba Talatu ta sake shiga wani sabon ban bakin da ba da hakuri, ita kuwa Umma ko a jikinta sai fadi take yi bárni da ita kawai Talatu ai wannan laifin na Zuwaira ne data zuba mata 116 ido tana yin abin da taga dama bata sanar dani ba, ai da tuni nayi maganin rashin hankalinta, da kyar na samu ta sake ni a dalilin jinin da taga yana bin yan yatsunta ina ganin haka na kama kuka, ita kuwa ko a jikinta, sai fadi take yi Lailatu zaki barwa mijinki? Karama da Aininiyarta sunyi nasara kenan akan Zuwairah? Baba Talatu tayi maza ta ce ai fa kam nima abin da ya fi kona min rai kenan, Umma ta ce barta kawai ai mun gamu da ita jiya a wurin wani buki muka gaisa ta ce min ashe kuma Lamido biki yazo? Na ce mata ch, ai kinyi Rokari da kika yi hakan gara ke da Zuwairah ku sake haduwa a gidan Mustapha don wannan kishin naku na gidan Alhaji Bello ya tsufa gara ku sake sabunta shi. Nayi maza na katsc kukan da nake yi saboda umarnin da Umma ta bani na in hanzarta kawo mata abin karyawa sai dai Baba Talatu bata bari nayi hakan ba, ta karbe ni ta hanyar shiga kicin don ta shirya mata, tana baria dakin ta sake kallona ta ce min duk abin da kuke ciki ke da mijinki ya gaya min, ina so kici gaba da yin hakan ba zan ce miki ki daina ba, in kinga dama ki shirya kayan aure ki jagoranci hidimar da za'ayi don ki mutunta kanki kamar yanda Alhaji Bello ya mutunta ki ya danka lamarin a 117 sannunki in kuwa ba ki ga dama ba ki bari biki sai za'a yi shi don Zuwairah ta tabbatar mun da cewar zata tsaya wajen ganin Lamido yayi wannan auren don tana son ganin Karama tavi amfani da Lailatun wajen samun abin da take nema wurin Lamido ko ubanshi, ita kam Zuwairah ai bata da matsala, jaruma ce bata taba sai wa makiyi damar da yayi mata dariya ba, sai dai in ke kika ja mata hakan. Yaya Almu yayi sallama ya shigo ya nemi wuri ya zauna a kasa yana gaisheta cikin girmamawa, ita kuwa sai ta amsa mishi cikin natsuwa da sakin fuska da suka gama gaisawa sai ya sake rage murya ya ce mata Umma na kasa yin shiru ne kan abin da Rabi take yi min saboda bana son azo a same mu a haka, ta ce eh to in ta gane abin da ake nufi ta gyara ai shi kenan in kuwa bata gyara ba ba kowa ta wulakanta ba sai iyayenku, in kuwa bamu da mutunci a wurinta ai sai kawai ka zuba mata ko. Rannan da daddare yaya Almu yana dakina dan dole na sallama mishi komai nawa yayi yanda yaso dani, kasancewar kuma na janye wunina daga gare shi na tsawon lokaci hakan ya jawo al'amari mai tsanani a tsakaninmu ina kwance daga gefe ina kallon shi yayin da shi 118 kuma yake ta bacci saboda tsananin gajiya, kishi mai tsanani ya sake mamaye zuciyata yaya zanyi in yi hakurin mallakar yaya Almu tare da wata mace? Yaya zanyi in iya zuba mishi ido yana yi mata irin abubuwan da na san yana yi min in mun kebe? Lokaci mai tsawo ina cikin wannan tunanin kafin lokacin da zuciyatata tabbatar min da cewar dole ne in koyi jarumtakar kaina don ba zai yiwu in barwa Lailatu yaya Almu ba tunda hakan yana nufin Umma Karama tayi nasara

Chapter 6 of 7