Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
ya hana su aukuwa sai da aka daina ganinta, to balle Baba da na san bani da wani gata sai shi, shi ne komai dina shi kuma in na rasa shi a wane hali zan samu kaina? wace irin rayuwa zanyi cikin wadannan mutane?" Tsawon sati biyu komai yiwa Baba ake yi, a kwantar dashi a tayar dashi. Ana nan a haka sai kuma Allah da Ikonsa ya soma samun sauki kowa sai murna amma zan iya cewa babu wanda ya kaini daga samun saukin nashi kuma sai ya sallami kowa da kowa ya ce su tafi wurin gurin iyalansu ya baiwa Alhaji damar diban abinda yake da yake bukata. 24 kam ai ta wuce Zuwaira, sai dai mu ce Allah ya bamu ikon cikawa da Imani." Na yi ajiyar Zuciya na ce, amin. Baba ya riga ya rasa karfi mai yawa don haka ko kofar gida bai fita sai dai in yi mishi shimfida a gindin bishiyar dake kusa da dakin Baba Rabi ya fito ya zauna, saboda masu shigowa gaishe shi gaba daya hirarmu kuma sai ya maida ita yin nasiha. "Ki zama mai hakuri da juriya Zuwaira, sannan kiyi kokari ki rinka kawar da kai kan abin da idonki zai rinka gani, ba komai ki ka gani ne zaki bata rai ko kiyi magana a kanshi game da al'amarin mijinki kuma ki rike shi da al'amarin mijinki kuwa ki rike shi da al'amura guda biyu, hakuri da godiya in ya yi miki laifi kiyi hakuri, in yayi miki alheri ki gode mishi, kar ki yarda wani canjin rayuwa ya same ki kice mishi ya kai ki kasarku kiyi hakuri da duk abin da za ki gani watarana zaki bada labarinshi bayan ya wuce. A duk lokacin da Baba yake yi min wadannan maganganun, kuka nake yi saboda nasan duk abin da yake cewa in yin yana nufin 25 komai ba Zuwaira, addu'a kuwa kullum ina yi miki ita. Ubangiji ya wadata zuciyarki da hakuri ya kuma baki dauwamanmen rufin asiri in ce mishi amin. To a haka muka zauna babu ya rasa karfi nima na rasa kuzari zuciyata ta karaya na zama komai ma sa ni kuka yake yi. A haka Alhaji yazo ya same mu yayi kwana biyu ya tafi bisa cewar zai dawo sati mai zuwa tun daga nan ya koma zuwa duk Alhamis suyi sallar Juma'a tare sai ranar Asabar ya tafi. Rannan ina tare da Baba miyar kuka nayi mishi da naman kaza na kuma tuka mishi tuwon Alkama nasa mishi man shanu muna zaune ina yi mishi hira cikin natsuwa don dai in samu yaci tuwon da dan yawa sai ga yara sun shigo wurin nashi bayan dawowarsu daga Makarantar allo suna fadin "Umma yau kin manta ba ki bamu kudin Laraba ba, na ce eh ku kuma baku tuna min ba, Baba ya zuba musu ido yana kallonsu ni kuma na basu umarnin su bi Uwa taje ta sa musu abinci bayan tafiyarsu sai ya ce min yanzu da wadannan fararen kayan nasu kal- 26 kenan kike sanye da fararen kayan na suke kallon Baba cikin tsoro na ce mishi Baba nima ba furare kaya ne a jikina ba hankalinshi a kwance ya ce "au Haba? to ai shi kenan watakila idanuwan nawa sun gama aiki baba? Na kama kuka shi kuwa ko a jikinshi sai ma ya ce in kina yi mun haka ba zan rinka gaya miki magana ba, to menene don na fadi haka tsofaffi nawa ne hakan yake samunsu? Nayi shiru na bar kuka, don Baba kar yayi fushi wurin rannan wuni nayi ina tunanin in Baba ya daina gani irin abubuwan da zan rinka yi mishi don in rinka taimakonshi kan hakan. Har akayi sallar azahar kafin na tashi na koma wurinmu na gyaggyara ina shirin dora miya sai ga Babangida da gudu yana fadin wai in ji Baba wai kizo nayi maza na wanke hannuna na bi bayanshi naje na same shi a zaune a bakin gadonshi ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min, "alwala nake so kiyi min." Na yi maza na ce mishi "Ba ka da lafiya ne?" Ya ce min a'a kalau dina fitanne kawai bana so na ce to na daura mishi alwala ya sauka kan shimfidarshi ya zauna yayi sallarshi ban fita ba sai da naga ya idar sannan na ce mishi bari in je in dora miya zan turo maka su Junaidu su maka hira kafin in dawo, ya ce to na dawo wurin mu 27 na samu har Uwa ta ajiye mun sanwar miyar, mamaki ya kama ni don komai ta tsaida shi kamar yanda taga ina yi. Washe gari wajen azahar Alhaji ya iso tun daga nan ya karben yiwa Baba alwala ya ma. sani na kawo ruwa mai zafi yayi mishi wanka ya goge shi ya shafa mishi mai ya canza mishi kayanshi yayi tsaf sai kamshin turare yake yi da daddare na shigo dakin bayan sallar Isha'i na samu bai ci abincin da na kawo mishi ba, ya ce min cikin bai mishi dadi don haka sai ya lafa, Alhaji ya ce dan damo mishi kunu shi da yake ruwa ruwan na ce mishi to na damo na kawo na dawo dakina na gama abin da zanyi na hau gado na kwanta har bacci ya dauke ni, Alhaji bai shigo ba na farka ban ganshi ba gabana ya đan fadi saboda tunanin ko jikin Babanne babu dadi, na tashi na gyarawa yara kwanciya na dawo na zauna a bakin gadona cikin tunani iri-iri naga dai wannan ba zai min ba na fita nayi alwala na dawo nayi sallah raka'a hudu nayi addu'a na shafa na dawo kan gadona na kwanta sai dai kuma bacci bai sake daukana ba zuwa can sai gashi ya turo kofa a hankali ya shigo ina ganinshi nayi maza na tashi na zauna a bakin gadon nace yau kuma jikin Baba babu dadi ko? Bai wani yi magana sosai ba sai ya zauna a 28 gefena cikin natsuwa sai ya ce min Allah ya saka miki da alheri kan dawainiyar da kika yi da mahaifinmu, Ubangiji ya saka miki da mafificin sakarmako." Maganar tashi tayi min wani iri don ban taba jin yayi min irinta ba, don haka cikin rawar jiki da rawar murya sai na tambaye shi "babu shi ne Baban'?" A hankali ya buda baki ya ce min, "Babu shi Zuwaira, yau kam Baba ya barmu sai kiyi hakuri kar kice za ki tsananta yi mishi kuka, kiyi mishi abin da zai amfane shi shi ne addu'a." Tsawon daren nan ba zan iya tunawa da irin addu'o'in da na kwana ina yi mishi ba, illa iyaka dai nasan daga mutuwar Baba ban sake yin lattin sallah ba balle in je ina hada azahar da La'asar ko Magariba da Isha'i. Sai na rinka ganin tamkar lokacin sallolin nan lokacin ne kawai nake dashi, na mika addu'ata a gare shi bana hirar bakin cikin da nayi na rasa don ba zan iya kwatanta komai ba iyaka dai abin da na rike shi ne bayan rasuwar tashi ne nayi wata irin jinya mai tsanani irin wanda ban taba yi ba a rayuwata don sai da takai ma yayan tudu ya dauke ni daga sasanmu ni da yara ya maida mu sasanshi in da yaya Balki ke tafiyar mana da mafi yawancin al'amuran sai ko Uwa. A wannan lokacin komai ya sauya mun duniya tayi min fadi na kara tabbatarwa kaina 29 da cewar bani da kowa in ban da yan yarannan guda uku da suke manne dani har a halin rashin lafiyar da nake ciki basa rabuwa dani ta sani a gaba suke yi suyi ta kuka. Alhaji kam tun bayan zuwan da yayi akayi arba'in din Baba ya kwashi matanshi suka tafi ban sake sanya shi a idona ba. Har na soma jin sauki ina fitowa tsakar gida ina dan taimakon yaya Balki da 'yan ayuka tun tana hana ni har dai ta hakura ta barni. Rannan ina kwance a daki da 'yan yara guda uku da suke ta bacci yayin da ni kuma nake kwance idona biyu saboda tunanin rayuwa, . Baba nake tunawa da kalmominshi da yayi tayi min musamman na karshen rayuwarshi wani tunani yazo min cikin raina da wannan zaman kadaici da nake yi ga wulakanci daga wurin mutanen gida gore-gore da habaice-habaice wuni nake yi a cikinsu, ga Alhajin ma yanzu rabon da in sa shi a idona har na mance lissafi me zan hana kawai in yazo in ce mishi ya kaini wurin dangina sai kuma na tuna maganar Baba nayi kuka har na gaji daga karshe dai na yanke wa kaina hukuncin zama Jaruma da kuma bin dukkan shawarwarin da Baba yayi ta bani. Don haka washe gari da sassafe naje na gaida Yayan tudu na shaida mishi cewar tunda naji sauki ina 30 so zan koma wajena, ya ce kin ji sauki tunda kin mike daga kwanaya, amma ai ba ki warware ba kin ganki kuwa kinga irin karewar da kika yi? Na co ba komai ina so in koma can din ya ce to babu laifi. Ina gayawa yara zamu koma wurin mu suka yi ta murna nan da nan muka gyarashi muka koma ciki na kawar da kaina kan abin da ake yi a gida ko ina ji ana magana ta ban nuna nasan dani ake yi balle in tanka, na maida hankalina wajen saye da sayarwa wanda dama na fara tun Baba yana da rai, mutanen unguwa ma in zasu sayar sai su kawo min in suna bukata ma su zo wurina nema na maida dakin Baba da.dama ya bani wajen tara kayayyakin da nake sayarwa ina dan harkokina ga kuma 'yan dabbo bina da nake kiwatawa wadanda suma babanne ya kafa min tushensu sai dai kuma duk da hakan bana cikin jin dadi zuciya ta a kuntace take kewa da kadaici sun ishe ni. Ana cikin haka rannan sai muka wayi gari da safe Uwa ta dauki dusar shanu taje zata share musu wurin ta zuba musu sai gata ta dawo da gudu tana kuka tana fadin Umma zo ki gani, da sauri nabi bayanta sai kawai na hango bijimina babban a kwance an yanka shi daga nesa na kare mishi kallo tausayinshi ya kama ni na juyo 31 kawai na dawo nazo naci gaba da aikina, ita kuwa Uwa taje sashin yayan tudu ta fada, ya shigo yayi min jaje ya kuma tambaye ni saidawa za'ayi don a rage asara ko? Na ce mishi a'a a rabar dashi kawai sadaka, su kuwa sauran dabbobin a tasa su a gaba akai su kasuwa a sayar, ya ce eh to kin yi dabara ba zan ce ki barsu ba, don kar abin da ya samu sauran ma ya same su, in banda yaya Balki ba wanda yayi min jajen abin da ya faru, an dai basu sadakan nama sun cinye, sai da aka fitar da dabbobin nan daga wurin nan sai kuma na kara gane ashe suma suna debe kewa ashe ba karamin sabo dasu nayi ba a yanzu sai inga tamkar bani da aikin koma ga kuma yara kullum maganar su ba ta wuce Allah sarki shanunmu da yanzu suna nan da munyi kaza da kaza. Ba'a kwana talatin da faruwar wannan al'amarin ba, rannan sai na farka cikin darea firgice saboda ihun da nake jiwowa na gobara- gobara, da sauri na dauki Babangida na goya nna daure shi tamau a bayana, na dauki Junaidu na kankame sannan na kama hannun Uwa na rike don ban san ta inda wutar take ba, sai da muka fito ne naga ashe dakin Baba ne yake cin wuta, dakin da nake tara dukiyata. Muna tsaye muna kallo dakin yayi kurmus sai dai maimakon 32 wutar ta tsaya anan abinka da jinkan ciyawa sai da ta lamushe kusan rabin gidan, da kyar aka samu aka tsaida ita. Washe gari bayan an dan natsa yaya Balki tazo min hira tana kara jajanta min abin da ya farun, tana bani hakuri na ce mata ai ni tun bayan mutuwar Baba ban sake ganin wani abin da ya bata min rai ba, komai aka yi sai inga wasa ne, wannan bai kai ayi bakin ciki dominshi ba. Allah ya jikanshi ya saka mishi bisa rikon amanarshi tace min amin. Tun daga wannan lokacin na bar komai na bar kowace irin sana'a don kuwa na gane hakan zai iya jawo min kowane irin abu, shi kenan na zama bana komai in na gama 'yan ayukana sai in dauko 'yan littattafaina guda biyu da dama baba yake koyar dani na Kawa'idi da Ahlari, inyi ta karantawa in na kamo daga farko na kai karshe inyi ta maimaitawa daga baya ma na shiga koyawa yara. Wasa-wasa sai gashi mun sauke kawa'idin da su min shiga Ahlari. Muna nan a wurinmu rannan da daddarc sai kawai naji muryar yayan tudu yana tashina, jikina yana rawa na fito ya ce min taso yaran nan ku dawo nan ku rinka kwana, na ce to na kwaso yara nabi bayanshi zuwa dakin yaya Balki, can ya maida mu. Washe gari da safe kwaso 33 yayi min magana da cowar in yi hakuri in zauna a nan don hankalinshi ya kasa kwanciya da zaman nawa a can, na ce mish1 to. wannan lokaci na zama wata irin abin tausayi ban san menenc matsayina ba, babu Al haji babu dalinshi, matanshi ma Sun daina zuwa gida a shekara biyu da rasuwar baba ganin da nayi mishi tunda akayi arba'in bai fi sau uku ba, ga abubuwan da suke kewaye dani a gida 1rin mutanen da nake zaune dasu ga aiken da yake yi min ma ya daina ga abin hannuna babu ya kare don ma dai yayan tudu yana yi min kokari to shima kuma ba mar shi bane ga kumna iyali har mata uku da ya ya. Muna wannan zama rannan kwatsam sai ga Alhaji ya iso da yamma, cikin wata irin kwalliya ta ban mamaki da burgewa, ana tayi mishi oyoyo nn kuWa nayi maza na shige wani dan daki na buya in ban da Uwa ta biyo ni ta kira ni da ban san yanda za ayi in tito ba, na same shi a dakin da aka sauke shi saboda umurnin da yayan tudu yayi min 3a 1n e mu gaisa na Ce mishi to, na tali tare da yaran dukansu ya daga ido ya kallc ni ya rage fara'a ya ce yaya zaki zo min da yara kuma bayan su na riga na gansu Ban yi magana ba ya ce musu kuje gun yara kuyi wasa, suka ce to suka fita. Na sassauta 34 murya na gaishe shi cikin ladabi ya amsa na tambaye shi iyalinshi ban kara ba akan wannan naja bakina nayi shiru, ya ce min yaya akwai mas' ala ne haka naga gaba daya kin canza? Na hadiye bacin ran da tambayar ta sanya ni na ce mishi babu komai, ya ce to in babu komai ni gobe zan koma dama zuwa nayi in ganku na ce mishi to Allah ya kaimu na tashi na dawo daki na zauna ina tunanin irin canjin da na gani a tare da Alhaji, ya yi kyau yayi kwarjini bai bukatar cewa ya samu daula don jikinshi ma ya riga ya bayyana na kalli kaina naga yanda na zama na fige nayi muzai-muzai in ba wanda yayi min kyakkyawan sani ba sai yayi zaton shekaruna sun zarce yanda suke bai bukatar komai a tare dani bai sona ba ma zai lya nuna ni a yanzu ya ce nima matarshi ce ba, to me zai hana ya kaini wurin'yan uwana? Nayi kamar inyi mishi tuni kan ina da 'yan uwa me zai hana ya kai musu ni maimakon barina cikin nashi 'yan uwan da yake yi, sai kuma na tuna kalaman na tuno shi a hirarmu ta karshe yana cewa mahaifinki yana sane da danginshi ya bani amanarki, don haka ke din tawa ce kiyi hakurin zama a cikin 'yan uwanki in hali ya samu sai kije ki gano su, don sadar da zumunci. Hawaye suka zubo min a ido, 35 saboda tuna Baba da irin son da yake yi min da nayi. Uwa ta shigo dakin da sauri tana murma, "Umma wai kizo in ji Baba." Tamfar dai in ce mata ba zani ba, sai kuma naga ba zan 1ya ba na tashi na bi bayanta na sake shiga dakin da yake cikin na durkusa na ce mishi, gani ya zuba min ido yana kallona ya ce so nake in tambaye ki Zuwaira, kin daina sona ne? Lokaci mai tsawo baki ganni ba amma ki nuna min baki da wata bukata game dani, na kuma tambaye ki damuwa kin ce baki da ita, me kike nufi dani ko kuwa kin zuba min ido ne kina jiran ganin sakamakon da Baba ya ce miki zai same ni in har na zaluncee ki?" Na ce mishi a'a, bana neman sakamako a kanka ba ma kai ba da kake da matsayi mai girma a kaina, duk wani wanda ya danganci zuriyar baba bana neman sakamako a kanshi ko da kuwa me yayi min, na yafe mishi zan kuma ci gaba da yafe wa bayanin nawa yayi mishi dadi ya ce to amma in haka ne me yasa ba ki tambaye ni dalilin rashin zuwana ba? Na co nasan ba zaka yi hakan da gangan ba. Yayi murmushi ya ce na gode miki Zuwaira da ba ki kullace ni ba, kika kuma zama ma yafiya kan duk abin da ya same ki, bayan haka 36 ina so in tabbatar miki da cewar ban taba yin wani abu da nufin in zalunce ki ba, ina kuma son ki fiye da duk yanda kike zato ina son hakurinki, ina son dabi'arki ta girmama wanda yake gaba dake duk abin da kika ga nayi to na yi shi ne bisa hakan ya zama min dole in har akwai wani abin da yake bani tsoro a yanzu bai wuce zaluntarki ba, don kullum ina tuna kalaman Baba na įaddada min amanarki da zai bar min wannan dadewa da kike gani ina yi bana zuwa ba na kusa ne na tafi nema bana cikin kasa a yanzu kuwa na gama shirya miki wurinki ke da 'ya'yanki don haka nazo ne in tafi dake. Ban ce mishi komai ba har yayi zancen shi ya gama na tashi na tafi nayi, kwanciyata washe gari nazo zan gaishe sh1 sai na same su da yayan tudu bayan na gaishe su zan tafi sai Alhaji ya ce min ke Zuwaira! na ce mishi na'am, sai ya ce ga dukiyarki yaya ya kawo min kudin shanunki da ya sayar ya kuma juya miki su sun karu shi ne na ce maimakon in karba ko zan bar mishi ne ya ci gaba da juya miki ko? Na ce mishi to, na tashi na tafi. Washe gari ne kawai muka kamo hanya don ban tsaya kintsa komai ba, Alhaji ya ce ni da yara ne kawai zamu taho bai bukatar mu dauki 37 komai yaya Balki da wasu mata biyu cikin matan yayan Alhaji suka yi mana rakiya. Kai tsaye sabon gida Alhaji ya kaimu, tabkeken gida mai manya-manyan dakuna ciki da falo da akayi matukar kawatawa da kaya shi ne nawa ga wani dakin a kusa da nawan shi ne na Uwa can gefe wasu dakuna guda biyu daya wai na Junaidu da Babangida, dayan kuwa na yaran da zai debo mun, daya kuma wani wuri da aka kawata da kuma biyu da falo da bayan gida nan ne wai nashi, ni da kaina mamaki ne ya kama ni baile kuma wadanda suka yi min rakiya. Kwana uku 'yan rakiyata suka yi suka tafi, da za su tafi sai na ce wa yaya Balki in sun koma ta bude dakina ta kwashe duk kayan da suke ciki na bata tayi ta murna. Bayan tafiyarsu ina zaune a falo na tasa 'yan yara a gaba zuciyata cike da tunani iri-iri sai ga Alhaji ya shigo, Karama da Maryam suna biye dashi sunyi kitika-kitika sai wani juyi suke yi suna sheki na karbe su hannu bibiyu muka gaisa muka shiga hira sai dai da Maryam kawai don kuwa ita Karama bata iya hadiye bacin ranta ba nan take a gabana ta ce mishi dama ita kadaice zata zauna anan'? Ya ce mata eh, zata ai tayi shiru da zasu tafi na diban musu daddawa da 38 kukar da nazo da su daga gida, na basu tafiyarsu da kwana uku sai ga Maryam tazo min wuni, ta taya ni muka kara kintsa wuri, yayi kyau sOsai sai da na gama abincin dare taci sannan aka zo aka dauke ta ta tafi. Matan abokan Alhaji suka yi ta zuwa yi min sannu da zuwa saboda ya basu labarin uwargidanshi tazo a wannan lokacin ne muka so juna ni da Hajiya Hauwa, alhalin da can tana mu'amallah da su Karama, a wannan loka cin Karama tayi matukar tayar da hankalinta kan dawowa na da kuma ware ni da Alhaji yayi ni kadai ga kuma irin kawatuwan da yayi wa gidan da ya sanya min kan wannan abin har sau biyu tayi yaji ta tafi gida, zuwan farko yaje sai dai bai yarda da cewar da akayi ya hadamu wuri daya ba ya ce ai shi ba wannan lokacin ne ya fara raba mu ba tunda ya dade da debo su mu kuma ya bar mu a kauye me yasa tun wannan lokacin bata yi maganar ya hadamu a wancan lokacin ba sai yanzu? Karama bata gama wastsakewa daga wannan lamarin ba sai labari yaje mata cewar zan tafi aikin hajji ni da yayan tudu Alhaji ya biya mana in na tsaya cewa Alhaji ya jiyar dani dadi a wannan lokacin ya nuna min gata ya karrama ni to na bata bakina ne kawai don ba zai yiwu in fadi komai ba, abu daya dai da zan 39 gaya miki shine, nan da nan na goge nayi fes na zama matar birni nayi kyau irin wanda ban taba yi ba, gani dai dama mai tsabta ce kwarai to gani kuma na shiga daula na kuma yi dace na gamu da mata ma'abuta ado da iya kwalliya, irin su Hauwa. Kuruciyata ta dawo danya sharaf, fatata tayi matukar yin kyau har mutane da yawa ke zaton wai su Karama sun gime ni. Ina nan zaune da su Uwa da su gwanin sha'awa babu wanda yasan bani na haife su ba, saboda babu alamar da zata nuna hakan. Tunda aka fadi zan tafi aikin hajji Maryam tazo min murna, Karama kuwa sai da Alhaji ya taso ta a dalilin kawo su dukansu da yayi shine tazo. Nima bayan dawowana daga katagun na shirya naje musu wuni ni da yara na taf maimakon Karama ta sauke ni a dakinta a matsayinta na babba sai taki ta barni a tsakar gida sai Maryam ce ta matsa na shiga dakinta na dawo gida ina tunanin mahakurci dai shine mawadaci don kuwa daga kyan gida zuwa tsarin dakunan nafi su morewa gasu kuma su su biyu a can sun kuma kasa daidaita kansu su zauna lafiya. Rannan ina gida da yamma ni kadai saboda yaran gaba daya sun tafi Islamiya sai ga Alhaji 40 ya shigo ranshi a bace. Cikin natsuwa na tambaye shi abin da ya bata mishi rai, ya ce haba Zuwairah, ace mutanen unguwa suna ganin mutuncina amma kullum burinsu Maryam bai wuce su tozarta ni ba, kowane lokaci gidana yana cikin hayaniya wai yau har makwabta suna shigowa rabon fada? Nayi maza na ce assha, abu bai yi kyau ba sai kayi hakuri, ya ce a'a yau kam na gaji na bar musu gidan suje suci kansu, zasu dade basu sani a ido ba. Na sake sassauta murya na ce, "kayi hakuri kar ka yi abin da za'a zo maida magana ace kaima ga naka laifin, tsawon lokaci ina rarrashinshi kafin ya hakura ya tafi bayan ya ci abincin dare. Kwana biyu bayan naje gidan kai tsaye dakin Maryam na shiga bayan mun gaisa da Karama a tsakar gida na kalli Maryam na ce mata ba zan ci komai ba yau a dakinki dama kin tattara kin kwashe, ta ce haba-haba ai sai in yi fushi, na ce to kiyi fushin mana Maryam sai me, tunda ke kullum baki da aiki sai na batawa mijinki rai, ribar me kika ci a hakan da kike yi? Ta soma zata bani labarin Karama na ce mata kece za ki bani labarinta ko ni ce zan baki? Ta ce min to kiyi hakuri daga yau kuma ba zan sake kula ta ba ko me zata yi tunda dai nasan bata isa ta rufe 41 ni da duka ba, tund atasan ba kwashewa kalau zata yi ba in tayi hakan. Na ce to da yafi miki mutunci a wurin mijinki dama mutanen unguwa ga baki daya sai ki same shi ki bashi hakuri kar kuma ki yarda ya sake fushi dake saboda ita ta ce min to daga wannan lokaci Maryam ta daina fadan baki da Karama sai dai kuma zaman babu dadi. Yarda da shawarata da Maryam tayi sai naji dadi na dauke ta tamfar kanwa in naga tayi ba daidai ba ko in mijinsu ya gaya min laifinsu sai in gaya mata ta kiyaye yi mishi hakan duk abin da na hana ta kuma tana bari in kuma tana da damuwa zata zo ta gaya min in bata shawara haka kawai kuma zata shirya tazo min wuni don haka sai muka kulle sosai ni da ita tana bani girma nima ina mata adalci ko wani abu na gani ya bani sha'awa in zan saya tare nake saya mana in ma tayi min kukan wani abu zan kawo kudi in bata in ce taje tayi donni ban yarda na zauna bana sana'a ba babu abin da bana sayarwa in ban da tsiya na riki Maryam 'yar uwa sosai saboda dalilai guda biyu na farko ta yarda dani tana amfani da duk shawarar da na bata bayan haka kuma ita ce mahaifiyar Babangida tunda kuwa ina son Babangida babu dalilin da zai su in ki 42 Uwarshi ko da rashin kirki take min balle tana ganin girmana. Nayi sabo da mutane sosai saboda sana'ata gani kuma da yara wadanda abokansu na makaranta ke biyo su gida don wasa ni kuma duk yaron da ya shigo ban barin shi ya fita haka kawai sai na kawo dan abin tsarabar yara na bashi, nan da nan sai muka yi fice gidansu Junaidu, Junaidu da Babangida ne suka yi fice sosai saboda ita Uwa bata fita ko ina bata kuma dawasu kawaye kowane lokac1 muna tare a gida. Na dawo aikin hajji da dukiya mai yawa saboda dalilai biyu, na farko dai nayi aikin hajjin ne a shekarar da dala take matsayin kwabo tamanin da biyar wato sule takwas da sisi don haka kudaden da Alhaji ya ajiye min sai suka yi min auki sosai, gashi kuma ya hada ni da abokanshi guda biyu, Alhaji na maibindiga mijinsu Hauwa ga kuma Baba Wulle wadanda su kuma suka tafi da matansu a wannan lokacin ne muka kulle sosai da Hauwa na

Chapter 2 of 7