Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels WACECE NI? -3 Umma ta mike ta dauko rigar baccin dake ajiye can gefenta ta miko min. "Karbi ki suturta jikinki." Tayi maganar ba taree da ta kalle ni ba. Hannu biyu nasa na karbi rigar nayi yanda tace din, tana ganin nayi hakan ta nemi wuri ta zauna tana kallona cikin natsuwa ta ce "menene masalar da ta hanaki zama wurin mijinki ku more darenku na farko?" Nayi maza na sunkuyar da kaina kasa saboda jin nauyin maganar tata, gaba daya mukayi shiru na dan wani lokaci zuwa can sai na kawar da shirun namu ta hanyar yi mata tambayar taimake ni mana Umma yau kam ki gaya mun gaskiyar al'amarina taimake ni ki gaya mun don in san ni wacece?" Kallon da naga tayi min shi ne ya firgita ni, nan da nan naji cikina ya bada sautin kululululu.... cikin rawar jiki na tambaye ta "Da gaske ne Umma ni din shegiya ce?" Ta dan girgiza kai a hankali tare da fadin cewa "ko kadan ke ba shegiya ba ce Adawiyya." Na dan samu 'yar natsuwa kadan saboda jin abin da ta fadi, don haka sai na dan kara mats awa jikinta na ce, "Gaskiya Umma ke din ke kika haife ni?" Na zuba mata ido ina kallonta tare da sauraron 7 irin amsar da zata bani, sai na sake ganin ta motsa kanta. Da hannu biyu na bugi kirjina cikin tsananin kuka na ce mata "Na shiga uku Umma, tunda ba ke kika haife ni ba?" Na kama kuka mai tsananin yawa ina fadin "Shi kenan Umma ta rasa ku dukanku na rasa Baba kema kuma a yau na rasa ki bani da kowa kenan a duniya?" Umma ta jawo ni jikinta ta rungume itama taya ni kukan take yi tana fadin "Ba ki rasa kowa ba Adawiyya, ni da Alhaji mune iyayenki da kika sani mune kuma iyayenki na har abada ban taba tunanin hali zai yi da zan bayyana wannan sirrin ba in banda tsananin son da nake yiwa Babangida, da ban bari akayi aurenku ba, don nasan yin auren naku yana nufin bayyanar asirin da na dade ina boye miki. Na sake kallon Umma a kidime na ce mata "umma amma ai dake nake takama, gashi kuma a baya kin taba ce min kin haifi Rabi'atu kin kuma gaya min cewar Umma amarya tazo gidan nan da yaro a goye to ina ce shine yaya Almu?" Cikin natsuwa Umma ta kalle ni ta ce min, wancan yaro da na baki labari tuni dangin Ubanshi suka kar ba, duk da Alhaji yayi iyakar kokarinshi wajen ganin an bar mishi rikon shi amma basu yarda ba bisa uzurin da suka bayar 8 na cewar shi kadai ne dan uwan nasu ya rasu ya bari maganar haihuwar Rabi'atu kuwa biyo ni kawai kisha labari, a baya na tsaya ne a inda na gama baki labarin isowar Maryam gidan nan to yanzu ma daga nan zan tashi. "Isowar Maryam gidan ya saman min da saukin fitina ne, amma ba fita hanyata karama tayi ba, domin duk da amaryar da akayi mata kishinta yafi tsanani a kaina, don ita da bakinta sai da ta rinka gayawa mutane cewar da ta zauna dani a matsayin kishiyarta gara ta zauna da kishiyoyi guda uku duk da ita su zama hudu." Umma ta dan saki wani lallausan murmushi bayan fadin hakan da tayi. Sai kuma ta ci gaba da fadin "Baba abin da karama ta ki irin taga Alhaji a dakina koda kuwa nice dashi sai ta rasa kwanciyar hankali ta rasa inda zata tsoma ranta taji dadi muna cikin wannan zama ne mutancen gida suka gane ai Amarya ciki ne da ita, shi kenan ana gance hakan sai kuma kishin Karama ya kema can zaman lafiya ya gagara a tsakaninsu fadan safe daban na yamma daban bayan kafin ta gane Maryam na da juna biyu duk kokarinta bai wuce na ace su biyun sun hade mun kai ba, ita Maryam din ce bata yarda ba rikici tsakaninsu yayi tsanani 'yar magana ba 9 magana ba kumą sai ta rarumeta da danbe sai da Baba ya gaji da hakan yasa baki yayı kashedi akan danben shine aka dan samu sauki. Ni kam ina gefe kallonsu kawai nake yi ina kuma iya kokarina wajen boye halin na nake ciki saboda ban son a gane amma duk da yake sai da Alhaji da Baba suka gane ina zaune a kan tabarma a dakina rannam ina dama wa Alhaji furar da zai sha bayan dawowarshi daga kasuwa, sai ya kalle ni ya ce min "iko sai Allah, watakila kuma bana yan tagwaye zan samu a gidannan da kuma shekara da shekaru babu ko daya." Na yi kamar ban ji shi ba, na mika mishi furarshi ya kama sha. 'Yan kwanaki kadan bayan bayan nan kuwa ina tare da Baba muna hira sai ya ce min "to wai ni Zuwaira da kike ta faman wannan 6oye- boyen kin mance ne uwarki mai yi min lissafin cikinku yau bata nan? Na sunkuyar da kaina kasa cikin hawaye saboda na kasa daina kukan mutuwar Baba Rabi kullum cikin kewarta nake anyi wannan zancen babu wani dadewa sai kawai na haifi 'ya mace abin da ya baiwa Kowa mamaki har Alhaji da Baban da suka gane akwai cikin balle kuma wadanda basu gane ba a wannan lokacin yaya Balki ce ta tsaya akan hidimar jegona don gaba dayan matan gida sun 10 Ce babu hannunsu tunda dai na 6oye musu cikin don ina tsoron kar suyi amfani da maitarsu su Cinye abin da yake ciki to yanzu ma da ya fito ba za su taba shi ba don haka ita ce mai samun ruwa ta kwashe ta wanke yarinya ta gasa mata cibiya ita kuma Maryam tana yi mun wankin kayana da na yarinya dama duk wani aiki da ya dangance ni. Ranar suna Baba ya sanyawa yarinya suna Rabratu a wannan loka cin ba karamin karamci yaya Balki tayi min ba don kuwa har nayi arba'in 1ta ke sanya mun ruwan wanka ta kwashe tayiwa yarinya wanka safe da yamma bata yarda ta bari ba kamar yanda Alhaji ya ce ta huta da ji da hidimar yaran dake dakin ta wajen su bakwai ga guda biyu da ta haifa a kurkusa wadanda basa yarda su rabu da jikinta ko ina take suna manne da ita uwa da kuma Jumaindu. Ba zai yiwu in tsaya kwatanta miki irin son da Alhaji da Baba suke wa yarinyar nan ba illa dai kawai in ce miki ba al'adar mazan gidan ba ne daukar ya'yansu amma shi kam daukarta yake yi ya fita da ita ya kaita wurinta Baba suyi hira in kuwa ya ganta a bayana tana kuka ko ya ji ta zai ce min ban ita nan, ko da kuwa a cikin mutane ne nayi-nayi ya daina don ina jiye mishi kunyar hakan da yake yi,amma ya ki dainawa 11 sai ya ce "ke kyale ni kin hi shekara nawa nayi ban same ta ba?" Mun samun wajen watanni uku a lokacin nan tafi wani jaririn mai wata biyar girma da kuzari gata da idanuwa dara-dara gashi ba na jin kunyar gyarata kullum cikin tsabtace ta nake sai. kawai ta kamu da mura mai tsanani na wuni daya kawai sai kuma ta ce ga garinku nan. Baba ya yi ta kuka ina bashi hakuri shima Alhaji ya shiga cikin damuwa mai tsanani kowane loka ci sai yayi ta fadin "oh ashe yarinyar nan ba zama tazo yi ba?" In dan yi murmushi in ce mishi "I, ba mai zama ba ce sai kayi hakuri ya ce to yaya zanyi? Ni kaina boye damuwa kawai nayi amma zuciyata takai matukaa wajen zafi, don kuwa ina son da a wannan lokacin ban sani ba ko Baba ya gane hakanne sai ya ce min dakin nan naki zaiyi mikifili mai yawa na rasghin Rabi, koda take yar karama kin riga kin sa rai da ita. Don haka ki dauki Uwa itama wata Rabin ce sai ta rufa miki gurbin da ta bar miki." Nayi nurmushi na. ce "To Baba daga wannan ranar kuwa sai na kar6i rikon Uwa daga wurin Yaya Balki hakan kuma sai ya kara karfafa kauna mai yawa a tsakaninmu har muka zama tamfar 'yan uwa 12 Sati uku cif da rasuwar Rabi'atu sai Maryam ta haifi da namiji na kai wa Baba shi, bayan nayi mishi wanka ya kare mjshi kallo ya ce "kamarshi, daya da 'yar uwarshi da mace ne da sunanta na mayar mishi sai ki sa hannu biyu ki rike shi naki ne ki dauka shi da 'yar uwarshi da ta tafi duk daya ne tunda 'ya'yan Bello ne na ce "mishi to Baba na karbe shi na tafi na bar shi yana share hawaye da gefen rigarshi ni Baba ya tantaya in fadi sunan da nake so a sanyawa jariri na ce' yasa mishi sunaishi don haka ranar suna sar aka rada mishi Muhammadu Mustapha ni nake kiranshi Babangida shi kuwa Baba yake ce mishi Lamido. Hannu biyu na saka na karbi al'amarinshi tun yana dan jariri na kai kai shi gun Maryam ne kawai don yasha nono tunda Junaidu yaga jariri a dakina kullum zai zo ya zauna kusa dashi dama kuma ga Uwa ta dawo dakin don haka sai ya zama dare ne kawai ke raba shi da dakin daren ma kuma sai an bari yayi bacci nake kai shi ko kuma ita ta turo a dauke shi. Rannan ma dai da Alhaji ya gaji da ganın hakan sai ya ce min to wai ke me zai sa ba za ki bar yaron nan a dakin nan ba ne kawai ki hada su ki rike? Ina amfanin kullum sai an sako shi a dauke shi?" Na ce mishi to. 13 Shi kenan sai gani da 'ya'ya uku a daki ina kuma tafiyar da al'amarinmu gwanin sha'awa kowane lokaci muna cikin tsabta ko hira zani wurin Baba tasasu a gaba nake yi in tafi dasu, don nasan hakan yana faranta mishi rai. Kullum naje gabanshi tare da su kuwa sai ya gaya mun cewar wadannan yaran da kike gani naki ne sun kuma ishe ki kar ki yarda ki daga hankalinki don ganin wai baki haifa ya rayu ba kowa da kike ganin yana da irin jarrabawarshi in kuma kayi hakuri to da irin sakamakon da za'ayi maka in ce mishi to Baba. A wannan lokacin ne Alhaji ya soma yi min magana kan sha'awar da yake da ita ta fara yin kasuwanci zuwa wasu garuruwa yana min bayani kan muhimmancin neman halal, na ce haka ne ko kuwa ba kya son hakan?" Nayi maza na ce "A'a ai ni ba zan ce kar ka nemi arziki ba." Ya ce"eh na sani Zuwairah, shi yasa na gaya miki don ki taimake ni wurin Baba ya barni in fara don nayi mishi magana bai amince ba, kuma ya ki amincewar ne a dalilin wai ba ki da kowa sai ni sai ko shi in na fara tafiye-tafiyen wai zaki yi kewata da yawa gara sauran matan su suna da dangi anan kusa. Bayani mai tsawo yayi min cikin rarrashi da kamun kafar in sa baki Baba ya amince mishi da bukatar tashi har 14 yana yi min alkawarin wai ba zai rinka yin tafiyar yana dadewa ba, ban ce mishi komai ba har yay1 ya gama yayi shiru ban tanka ba saboda nima can Cikin zuciyata nasan zanyi kewarshi amma kuma duk da haka nayi mishi yanda yake so din wato in rokar mishi Baba cikin natsuwa na same shi nayi mishi bayanin ya daga ido ya kalle ni cikin kulawa ya ce "tausayinki nake ji Zuwaira, in har ya dandani dadin neman kudi a nesa da gida zai yi wuya ya dawo gidan ya zauna, amma tunda kin ce a barshi yaje shi kenan." Alhaji ya soma tafiya Fatauci daga gida zuwa garuruwa daban-daban na kurkusa, wani lokaci yayi kwana biyu ko uku ya dawo gida. Ana nan ana nan sai gashi in ya tafi sai ya kai har kwana ashirin bai dawo ba, in na zauna wurin Baba ina lissafin kwanakin tafiyar tashi sai ya ce, "a to, abin da na gudar miki kenan, ki ka ce a barshi ganewan da nayi shima Baba ba jin dadin dadewan nashi yake yi ba, sai na daina yi mishi zancen nayi kokarin kawar da damuwar kewarshi cikin raina, nayi matukar kokarina na maida hankalina kan al'amarin 'ya'yana wadanda suka riga suka fara girma suka yi wayo, nake matukar jin dadin mu'amalla dasu saboda tsananin son juna da muke yi suna sona 15 saboda suna daina buya in yi kukan kewar Alhaji saboda in har Uwa ta gane nayi kuka ta rinka kuka kenan saboda ita din tafi su wayo. Ina cikin wannan zaman da yaran ne rannan Alhaji ya dawo gida a dakina ya sauka. bayan al'amura masu yawa sun gudana a tsakaninmu, muna cikin hira sai ya sako mun wani zance da ya shafi harkokin kasuwancinshi irin alherin da yake samu da yanda kasuwa ta bude mishi, na taya shi murna har cikin zuciyata, sai kuma ya ci gaba da cewa "to kin san halina Zuwaira, babu wani al'amari nawa da yake 6oye a gare ki bana son zaman takura da kewa, don haka nace wannan karon in zan tafi tare dake zan táfi don na gaji da zaman kadaici." Maimakon in ji dadin wannan bayanin da yayi min tunda dama cikin kewarshi nake, sai na kasa yin farin ciki a dalilin ganin ya'ya uku dake kwance akan karamin gadona suna bacci, wadanda basu san kowa ba sai ni ko dawowa suka yi daga Makarantar allo basu ganni ba basa iya jirana in dawo sun rinka shiga sashi-sashi kenan suna nemana, ga kuma Baba wanda girma ya riga ya kama shi ni ce mai hidimarshi nice abokiyar hirarshi to tsallake su duka zanyi in tafi ko kuwa yaya zanyi?" 16 Da na kalli Alhaji sai kawai na kawar da fuskata gefe nace 'mishi "ba zani ba." Amsar da na bashin yayi matukar bashi mamaki, don ya saba yi ne ina ce mishi duk abin da ka gani. Cikin natsuwa ya mike ya zauna yana kallona da fuska mai dauke da alamar mamaki cikin muryar da ya tausasa ya ce min "kin zartar wa kanki da hukuncin rashin bina? Ban tanka mishi ba ban kuma bashi hakuri kan hakan da nayi ba sai dai nan take naji babu abin da nake son yi irin in yi kuka kukan kuwa nayi tayi yayi rarrashi har ya gaji ya ce min "haba Zuwaira me nayi miki da zafi haka? Ina ta baki hakuri kin ki ki hakura ko so kike sai yaran nan sun farka sun ganki kina kuka sun ji zafina tunda zasu ga na batawa uwarsu, bayan ni ba ma samun zama cikinsu nake yi ba?" Yana fadin haka nayi shiru na bar kukan, sai dai kuma har gari ya waye ban sake tankawa wata maganarshi ba, abin da bai taba faruwa a tsakaninmu ba. Don haka sai hankalinshi yayi matukar tashi da abin da nayin. Gari na wayewa na anmsa kiran Baba saboda ya kai maganar gabanshi. Ya gama baiyanawa Baba maganàr da ya ce ba a kara ba kan wannan baba sai kawai naga ta kama kuka bayanin da ta yiwa lajfi ban nuna bacin rai ba. 17 Baba ya gyara zama yace, "to yaya zaka nuna bacin rai bayan abin da kake so tayi maka? Ai dole Zuwaira tayi kuka tunda ta gane duk abin da kake nufi bai wuce son ka kwashe matanka ka tafi dasu ka barta ba, tunda su biyun dai babu wadda zata yarda ka dauki 'yar uwarta ka barta to kaje ka dauke su ka bar mu a nan. Hannu biyu Alhaji yasa ya dafe kanshi saboda tsananin tashin hankali bai taba zaton abin da Baba zai gaya mishi kenan ba, nima kuma nayi mamaki yanda akayi ya gane abin da ya darsu mun cikin zuciyata. Baba ya ci gaba da magana yana fadin "Zata tsallake ya'yanta ta tafi ne ko kuwa so kake ta kwashi 'ya'yan ku tafi ta bar ni? Ai tasan ko tuwo bana cin na wata a gidan nan in ba nata ba ne." Nan da nan Alhaji ya sunkuyar da kai kasa yayi ta bai wa Baba hakuri yana fadin "ya yi kuskure da bai yi wannan tunanin ba, amma tunda haka ne to a bar maganar tafiyar kawai na tashi na tafi na barsu saboda Baba ya sallame ni. Nayi matukar jin dadin yanda Baba yayi mishi wanda yasa nan da nan ya janye tafiyar da kowa saboda gudun bacin rai, amma kuma daga baya sai naga to ribar me naci in nayi hakan? Nasa an hana shi tafiya da matanshi alhalin ni ina da uzurin da ba zai yiwu in bishi ba, zanje ya 18 ci gaba da zama cikin kewa da kadaicin da yake cewa ya ishe shi, bayan ga matanshi guda uku a gida suna zaman jiranshi? Kwana biyu bayan nar sai na koma gaban Baba na ce mishi a bar shi ya tafi da duk wacce yake son tafiya, Baba ni na hakura na yafe mishi, Baba yayi tasa min albarka alamar ya ji dadin abin da nayin, sai dai kuma abin da Baban ya fada ne ya tabbata lokacin da Alhaji ya ce zai tafi da Maryam sai Karama ta ce bata yarda ba, don haka Baba ya ce ya tasasu a gaba dukansu ya tafi dasu. Hakan kuwa akayi. Shi kenan sai sashin namu ya zama ba kowa daga ni sai ya'yana muka sake muna ta sha'aninmu, in gari ya waye muna idar da sallah in na fito Uwa zata biyo ni ina abin karyawa tana wanke-wanke, kafin in yi dumame in dama kunu in toya kosai tuni har ta gama share wurin nan tas, har taje ta share turken dabbobi, ta kai musu dusarsu da ruwa tana dawowa sai mu kwashi abin karyawan mu ja kofar kara mu rufe wurin namu don kar kaji ko Akuyoyi su shiga suyi mana barnma, sai mu nufi wajen Baba can muke karyawa in mun gama in tura su Makaranta ni kuma in yi mishi abubuwan da zan yi mishi kamar su ruwan wanka da wanki da 19 share-share in rana tayi in dawo wajena don in yi mana abincin rana. Muna zamanmu a haka ko tunanin zuwan Alhaji ban fara ba saboda ganin dama can da yake shi kadai yana yin sati uku sati hudu balle kuma yanzu da ya tasa matanshi a gaba ya tafi dasu, don haka sha'anin gabana kawai nake yi. Kwatsam! Rannan sai naga Uwa tana tsalle tana murna cikin tsananin farin ciki ko magana bata iyawa a dalilin tsananin murnar da take yi, sai fadi takc "Babanmu yazo Umma, Babanmu yazo, Baba yana jin haka shima ya kama murna, ni kuwa nayi kamar ban damu ba. Wajen Baba ya fara shigowa tsarabar da yazo da ita ma a nan nasa aka jibge ta nan take na dibi ta yara na raba musu na kuma shiga kasa tsarabar gidan ina bayarwa Uwa tana kaiwa sassa-sassa tana dawowa na gama na juye naman saniya da yazo dashi na wanke na dora akan wuta sai naga wucewarshi zuwa daki nayi maza na shirya mishi abincin da ya samu nayi mana na kuma hada da danwaken da na jefa mishi don shi mai son danwake ne, na kawwo ruwa na ajiye mishi ina kallon shi yana cin danwaken sai ya dan kallen yace min dama kinyi zaton zanzo ne yau? Nayi maza na ce ko kadan, me ka gani? ya ce na same ku cikin 20 kwalliya dukanku har da Baba gashi kuma ke da Uwa lallenku sai sheki yake yi, na yi murmushi nace ai yau Juma'a ne amma ni kam ai ban ma soma sa rai da zuwanka a yanzu ba, na dauka sai nan da wata biyu ko uku tukuna amma ba yau ba sati biyu kacal da tafiyarka, daga ido yayi ya galla min harara saboda ya gane abin da maganar tawa take nufi. Karba sosai nayi mishi a wannan zuwan da yayi don kuwa maimakon kwana uku ko hudu da yayi niyyar yi bai tafi ba sai da ya kwana bakwai cif. Sati biyu kuma da tafiyarshi sai gashi ya sake dawowa, a haka sai ya ajiyewa kanshi yin sati biyu ko uku a can in ya dawo kuma sai yayi kwana biyar ko bakwai ya tafi. Nan da nan kuma sai maganganu suka soma yawo wai ya kwashi mata biyu ya kai birni ya ajiye ya dawo ya tare a wurina, ni kam ko a jikina jinsu kawai nake yi a wannan lokacin ne kuma kasuwa ta kara budewa. Alhaji duk wani abin da ya taba da nufin sayarwa sai ya ci riba a kanshi duk abin da ya kawo don sayarwa kuma sai ya zama tamfar warwarcnshi ake yi saboda saurin karewarshi, don haka in yazo gida zai tafi zai kawo kudi masu yawa ya bani ya rinka gaya min cewar komai zaku ci kuci mai kyau in ce mishi to yanda yake bani kudi haka yake baiwa 21 Baba shi kuma Baba in baya nan baya barina in sai komai ko da kuwa fura ne da nono komai saya mana yake yi don haka nan da nan sai ga kudi a hannuna na tara. Rannan ina hira da Baba sai ya tambaye ni. "Babu komai ne a hannunki? Ko mijinki bai baki komai ne?" Na ce mishi "Akwai Baba, yana bani in kawo maka su ne?" Ya ce min "eh to kawo." Naje na kawo mishi su dukansu, ya karba ya kirga su ya ce "eh lalle kina da kudi to bari yayanku na tudu yazo sai in tura shi yayi miki cinikin wata fadamar rake da akayi min tallanta na ce mishi to Baba." Da haka sai na mallaki fadamu guda biyu ga wacce Baba ya bani ga kuma wacce ya saya min da kudina. Cikin shekaru uku na samun kudin Alhaji da nayi ina tare da Baba a gida yayi min tattalin dukiya mai yawa bai bari na in sayi komai da kudina, gashi kuma ko fita yayi yaga wani abin sayarwa da za'aci riba zai dawo yace min "kawo kudin nan a dan gwada juya su ko za'a samu wani abu akai in ce mishi to, a wannan lokacin suma su Karama tuni suka goge suka zama matan birni sai dai dukansu a rame saboda- zaman lafiya ya gagara a tsakaninsu, fitinar safe daban ta yamma daban, gashi gidansu su biyu saboda Alhaji ya sai nashi gidan sun tashi daga 22 gidan hayan da suke zaune a duk lokacin da suka zo gida suka yi bakunta suka tafi in muna hira da Baba zai zolayen da maganarsu ya ce min yan uwanki sun zo suna kyalli sun baki sha'awa ko?" Ni kuwa sai in yi murmushi in ce "ai kyallin kawai na' gani Baba, amma naga kamar na fisu cika ido." Shi kuwa sai yayi dariya ya ce, "ai ba ki sha mamaki ba ma sai randa kika hadu dasu wuri daya kika ga suna neman rance a wurinki lokacin ne za ki kara gane kyallin ne kawai, su matan birni da kike gani ba duka ne suke da hikimar juya kudi ba, zama suke su mike kafa wai su nan ga masu jin dadi kin taba ganin jin dadi ga wanda bai da anini?" In yi murmushi in ce "A a, sai ya ce to kar ki yarda ki zauna ba kya sana'ar komai ko ba kiyi da kanki ba rinka baiwa wani amintacce yana juya miki, in ce mishi to Baba. 23 Alhaji ya kwaso matanshi suka dawo gida gaba daya, gida hankali ya tashi ganin halin da Baba yake ciki, ni kam nayi kuka har na gaji tunanin mutuwar Baba Rabi ya dawo min da halin da na tsinci kaina a ciki bayan mutuwar tata, ban taba samun ta kare min wasu abubuwa ba sai da bata nan na gane ashe ita din idonta ya tsare al'amura masu yawan gaske,

Chapter 1 of 7