Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
rokeni ta tare da danta mai shan nono wai watanninshi goma ne kawai bai son a raba ta da shi, ni kuam sai na ji ban son ya sha nonon nata tana gidan nan, don kar a haramta mishi auren ya'yanku, don ba a san abin da gobec za ta haifar ba." Na ce mishi, "To baba in ta zo din sai ka karbi yaron ka ba ni shi zan yaye mata shi." Baba ya yi ta murna yana sanya mini albarka. Ummana ta sake shafa hannuna ta kar jadada laushin jikina kafin ta ce mini, "To kin ji yanda aka yi na mallaki dukiya cikin gadon su Alhaji, baba ne ya yi mini kyauta." Na yi ajiyar zuciya mai karfi kafin na ce mata. "Umma." Ta ce, "Mene ne Adawiyyah?" Na ce, "Lallai Baba gadon alheri ya yi wurin mahaifinshi, tun da ni kar han taba jin labarin mutumin kirki irin shi ba." Umma ta ce, "Uhum! Me kika sani game da baba tun da ba zama da shi kika yi ba?" Na sake ce mata, "Umma." Ta ce mini, "Ina jinki Adawiyyah ke nake sauraro" Na ce,To shi wanna Amarya ta zo da shi shi ne ya zo ya zama yaya 119 Almu ko kuwa da ta zo nan gidan ma ta haifi.wani? Umma ta ce, "Wannan ne kuma ba zan iya amsa miki yanzu ba, don in na biye miki sai in kwana idona biyu." Na sake matsawa jikinta na kwantar da kaina a gadon bayanta sosai na cc mata, "Lallai kin yi gwagwarmaya da Umma Karama, Umma." Ta ce, "Ba kadan ba ai shi ya sa duk abin da take yi yanzu kallonta kawai nake yi na san ba zai yiwu ta maimaita abin da ta yi a baya ba." Na ce, "Haka ne gashi kuam kin yi sa'a baba yana matukar Sonki shi ya sa. ma da kiak tayata yi mishi laifi ya yi fushi da ke matsanancin fushi fiye da wanda ya yi da ita." Umma ta yi dariya ta ce, "Mu yi barci Adawiyya." Na ce to Umma, amma dai gaya mini yaushe ne kika haife ni? Ta ce, 'Ba yau ba." Na ce to gaya mini abu daya kin sake haihuwa bayan wancan haihuwar da kika yi? Ta yi maza ta ce na sake mana. Na ce to me kika haifa? Ta cc Rabi'atu. Na yi murmushi na kara nutsuwa cikin raina dadi ya kamani. Nan da nan barci mai dadi ya dauke ni. Washe gari kuwa farkawa na yi na ga haske vana kashe mini ido na tabbatar ba lokacin gari ya waye ba, na.yi maza na dauki agogona na duba karfe goma ne na safe. Da iya kacin karfina na shiga Cwalawa Umma kira, amma ba ta amsa ba, sai baba Talatu ce ta shigo tana murmushi. "Kin farka ne uwar dakina? Za a shirya miki 120 ruwan Wanka ne? Na ce mata, 'Eh." Na yi maza na yi waje, don ganin me Umma take yi. Tana zaune a falonta tare da su Anti Aina'u, lissatin kudi suke mata, ita kuma tanan tare da jakarta alamar tana shirin ba su. Na juya żan koma in da na fito ta kalieni ta ce mini, "Kin gaishe su ne?" Na ce, "Bari in wanke bakina tukunna." Na shiga wankana ban sake fitowa ba sai da na tabbatar sun fita. Sannan na fito cikin kwalliya mai matukar kyau na zo na zauna kusa da ita na fara gaishe ta. Ta kalleni a lalacc ta ce, 'Ai ba zan yi wata magana da ke ba yau, sai bayan kin je kin gaida su Aina'u, kin dawo." Sai kuwa kawai ta ja tsaki alamar dai ta ji takaicin kin gaishe su da na yi. Na fita waje don in je in gaida su Aina'u, dama duk wani wanda yake cikin gidan na san in ba hakan na yi ba ba shiryawa za mu yi da Umma ba. Ina fita na ga wani abin da ban san da shi ba. Mutanc suke ta shiga motoci ana ta fita da su, ga alama kuma tafiyar ba ta kusa. ba ce, don sai jefa jakunkunan ya'yansu suke yi a bayan motocin. SAnnan gaba dayansu janma'ar da na sani ne wato yan'uwa ko kuma abokan arziki na kusa. ina cikin kallon na su sai na ga Anti Rahma ta fito da saurinta ta sha kwalliya tana rungume da Jakarta, sai wani irin kamshi take yi. Na kalleta cikin 121 nutsuwa na ce, 'Anti wadannan fa ina za su?" Ta ce za Su jere. Na ce tun yau? Ta ce eh to a wurinki kam tun yau mana, amma ni kams da na san har Lagos za a tafi nawa jeren ai na san ba a yi sauri ba. Na sake kailonta na ce Lagos kuma za a kai ki? An yi wa Y aya Junaidu transfer ne? Ta saki wani lallausan murmushi ta ce 'Lah ashe baki da labarin ajiye aikin Junaidu ai shi baba ya zaba ya zama shugaban kamfanoninshi. Ai can Lagos za mu zauna a wannan sabon gidan na baba da ke unguwar My one.' Na ce, "Anti Rahma wane irin so baba yaké yi wa yaya Junaidu haka?" Ta kalleni ta kyalkyale da dariya ta ce, 'Ai fa kamn ni kin ga tafiyata." Ta wuce ta barni a tsayc ina bin ta da kallo a zuciyata kuwa cewa na yi, kai to ko dai ma yaya Junaidun ne dan baba na cikinshi, shugabancin kamfanoninshi da ya bashi ai yana nufin ya dauki duk dukiyarshi a hannun shi ne ga shi kuarn darna an co aure bai halarta ba tsakanina da shi, kuam shi yaya Almiu ya tabbata kenan shi ne wannan da da Umma Amarya ta zo da shi. Na wuce na gama gaida mutanen gida. Ina fitowa yaya Almu na fara gani ya yi adon karanan kaya, ya yi kyau har bai yiwuwa in yi ta,kwatantashi. Yana ganina ya yafuto ni na isa gare shi ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, "Ke kam kin yi sa'a, kunya ta anini baki da ita, gaba daya 'yanmata sun yi sammako sun bar gida, ke kuwa kian nan kina yawo cikin 122 mutanen da suka zo bikinki" Na ce, 'Aa ni kadai ce a gida da za a yi bikina kai fa?" Ya yi murmushi ya.cc, 'Ai ni ma yanz zan bar gidan in je yawon bankwana da samartaka in za ki zo mu tafi. Na ce, Aa ba inda za ni zan zauna wurin Umma mu yi hirarmu mai dadi. To shi kenan." Ya yi maza ya juya ya bar wurin, in duba abin da ya kore shi cikin sauri haka sai kawai na hango jerin motoci suna shigowa gidanmu Kawayen Umma ne ina jin sun shirya isowa tare ne don Kila sune masu tafiya jere na. Na yi maza na bi bayan yaya Almu na je na bude motar da na ganshi a ciki Ya yi maza ya juya kan motar, don barin gidan. Sai ga Hajiya Hauwa tana shigowa wai maimakon ta yi maza ta wuce tunda yaya Almu ya kauce mata, sai kawai na ga ta ja ta tsaya tana tambayarshi. "Kai Lamido ina za ka kai yarinyar nan? Da ita fa yau za ni gida, don ban riga na gama shirya maka ita ba." Yaya Almu ya yi magana a hankali, "Bari in fita in gaida Hajiya, don ga dukkan alamu ita ce Surukar tawa." Ya fito ya je ya gaisheta cikin girmamawa. Sannan na ji shi yana ce mata, 'A'a dauko baba kawai za mu." Ta yi dariya ta ce, 'Alhaji Bello zai hada iyayenshi aure ai.dole zama ya gagareshi, yana 123 Zumudin kwanannan zai fara ganin kanne." Ta yi wucewarta, muma muak sa kai muka fita muka hau hanya. Yaya Almu yana cewa, "Kina jin abin da ta ce?" Ban amsa ba ya yi ajiyar zuciya ya ce, Kowa sha'awar da yake yi mini kenan nima kuma ina yi wa kaina wannan sha'awar 'ya'ya nake so Rabi ke fa?" Na ce, 'Uhum ni ba.su damen ba." Nan da nan ya fusata yana fadin, "Ai ke ba ki da hankali ke kam sai dai a yi ta yi miki addu'a, mutum mai hankali ya ce wai haihuwa ba ta dame shi ba? Ko da yake ma ai ba ki da wani abin mamaki tun da kin yi mini abin da yafi wannan a gabana ina kallonki kina kallona kika ce za ki bukaci baba ya canza miki ni da Junaidu." Ya ja wani mummmunan tsakin da ya firgita ni, don kuwa na yi zaton kifa mini mari zai yi bayan ya gamna tsakin. Mun dauko su baba muna dawowa shi da Urmma Amarya suna bayan mota ni da yaya Almu a gaba, na ce, 'Ai kuwa baba babu wanda zai yi zaton zuwan ka a yau." Ya ce, eh uwata zumuncin aurenki ne ya dawo da ni gida, iyayena za su sake haduwa wuri daya zan sake zama dan gata daga ranar da zi daura aurenku ni din kuma ba maraya ba ne, ga ku wuri daya kun hadu sai kawai in yi ta fata da kuam sauraron isowar kannena, dan haka kuna hade wuri daya zan gaya muku ban yarda da tsarin iyali ba." 124 Kalaman Baba suka san ya ni jin kunya, nan take kuma suka sanyaya mini jiki, wato ba yaya Alimu kadai ne yake bukatar ganinan ina ta haihuwa ba, har da baba, tuni na san ra'ayin Umma ne wannan. Muna kawo su baba muka bar gidan, don ya riga ya cika da jama'a tamkar ba sai rana ita yau ne daurin auren ba. Wuni muka yi muna zaga wuraren shakatawa na ban sha'awa, mafi yawancin hirar yaya Almu a ranar magana ce kan muhimmancin haihuwa da darajar ya'ya a wurin iyaye. A duk lokacin da ya kalle ni kuwa sai ya jadada fadin, "Hakuri kawai za ki yi Rabi don 'ya'ya da yawa nake bukatar ki haifo mana, Ummanmu ta samu, Umma Karama ta samu, Umma Amarya ma." Haka na zuba mishi ido kawai na kallonshi ban iya cewa komai ba. Har dare ba mu dawo ba. Hajiya kuwa sau biyu tana yi mishi waya, "Kai Lamido kafa kawo mîi yarinyar nan haka." Ya ce mata, "To ga mu nan zuwa." Sai wajen karfe goman dare ya ajiye ni a kofar gidanta. Kwanaki shidan da na yi a gidan Hajlya auwa sune suka tsareni daga sanir abin da ya rinka faruwa a gidanmu, na dai san kawai ana sha'ani mai yawa, don ko ita ma can take wuni, sai dare take dawowa, in za ta tafi ne dai za ta fara mini jike- jikenta ta ce wai in yi maza in shanye su kafin ta 125 dawo. Tana isowa kuma za ta tasani a gaba da wasu kwayoyi ta yi ta sani ina hadiyesu, kamar zakara, tana kuma kara gaya mini kyan su har tana fadin Wai wadannan da kike gani kwanan nan za ki fara nemansu da kan ki in kika gane amfaninsu daga London na zo da su, saboda ke saura in kin je ya yi miki tabara ya ce sai kun ci amarci kafin ki fara haihuwa kull Kika yarda ai kina jegonki kina cin amarci, ina ganin kin dauki wani lokaci mai tsawo, ban ji wani bayani ba da kaina zan zo har Kadunan in same ki, kin san halina sari, don angwayen yanzu dabararsu kenan, wai a ce amarci kafin a fara haihuwa to ni ba yarda zan yiba in ma ita Hajiya Zuwairiya ta yi miku shiru ni ba kyaleku zan yi ba." Sai ana gobe daurin aure ne aka shirya dawo da ni gida. Ina jin Hajiya tana yi wa Ummana waya tana cewa, To uwar angwaye motoci muke so a turo su zo su dauke mu za mu kawo amarya wurin saka lalle. Umma tace bazan turo ba in motocin gidanku ba za su dauko ku ba, ki eike amaryar kar a saka mata lallen. Hajiya Hauwa ta kyalkyale da dariya ta ajiye wayarta lokacin ne na gane ita Umma ta tsaya matsayin uwar angwaye ne kenan, 1yayen amare suna da yawa, tunda nima Hajiya ce tawa uwar. Maganar da Umma ta yi bai hana abokan yaya Almu yin jeri gwanon motocin su a kofar gidan Hajiya Hauwa ba, dama kuma gidan nata a cike vake don mafiyawancin kawayen nasu nan suke taruwa 126 kafin su hadu su tafi gidanmu. Na sha kwalliya sosai, an yi mini gyaran jiki na ban mamaki, an kuma kawata jikin nawa da adon lalle mai kyan gani, ga wasu kaya na alfarma da Hajiya ta sanya mini. Sannan ta dauko mayafi ta lullube ni ta kuma wuce gaba tana rike da lullubin nawa ta yadda babu mai iya ganin komai nawa. Ta wuce muka shiga ni da ita mota, muna baya direba shi kadai a gaba ya ja muka bi.bayan sauran motocin da aka basu umarnin su fara tafiya. Sannan wasu suka biyo bayanmu. A haka har muka isa gida. Wajen karfe tara na dare aka saka mana lalle gaba dayanmu a wuri daya aka hadamu aka sanya mana. Muka kuma kwana wuri daya. Washe gari da safe ta ko'ina dirin mutane kake ji alamar dai gidan a cike kwarai yake. Gaba dayanmu mu shidan muna nan a dakin kowacce ta shiga cikin nutsuwar ta ni dai babu abin da ya tsaya mini a rai irin kewar rabuwarmu, shi kenan zaman tae ya kare, sai kuma zumunci abin da kullum Ummana take gaya mini kenan. Ina cikin wannan tunanin sai ga Hajiya ta shigo cikin wata irin kwalliya ta kasaita tasa katon mayfinta ta rufe ni ta yi waje.da ni. Sashin Ummana ta ki ni a wani daki da babu kowa a cikin shi muka shiga ta ce, "Shiga ki yi wanka ki fito ki shirya, don mu karbi Fatiha tare." Na fito daga wanka hajiya ta tasani a gaba tana shafa mini mai tana dariyar abin da 127 ke faruwa a falon Umma, inda wasu suke tambayar ina uwar Zubairu? Ta yi maza ta ce, "Gani nan." Suka gaya mata abin da suke nema, ta sa aka yi musu. Ba ta zauna ba sai ga wasu sun iso. "ewar Junaidu muke nema." Ta ce musu, "Ni ce." Nan suma suka kama bayani. Hajiya ta gyada kai a hankali ta ce, 'In kika gama wannan bikin mijinki ne zai ji jiki da ke, mu duk gudu za mu yi mu bar mishi ke." Kwalliyar amarci sosai Hajiya ta yi mini. Karfe goma sha daya daidai aka fara daurin auren ina kwance a jikinta ina sauraron abin da ke faruwa cikin zuciyata ina cewa, yau ne zan tabbatar tsakanin ni da yaya Almnu wake da baba a matsayin mahaifi? Gaba daya sai da aka yi daurin auren guda biyar gaba daya kuma mutane daban-daban ne suka bayar ko suka karba. Sannan sai na ji ana cewa, "Ina wakiyar Rabi'atu da wakilin Mustapha, mai bayarwa da mai karba kenan" Sai na ji ana cewa, To ya yi gasu nan sun zauna, Alhaji Bello Mustapha, uban 'yar gaba daya, uban angwaye da amaren duka shi ne da kanshi zai bayar da auren Rabi'atu yayin da aminishi Alhajin Malle żai karbarwa Mustapha auren." Ina jin haka na ce shi kenan na rasa baba a matsayin mahaifi na san babu yanda za a yi baba ya haifen. Sannan ya zauna ya bayar da aurena a gaban 128 'yan'uwanshi da abokashi bai wakilta wani ya ce ya yi mishi hakan ba. Hawayc suka zubo mini sharr! Ana shafa Fatiha Hajiya Hauwa ta kalleni ciki nutsuwa ta ce, "Yau din nan ranar farin cikin uwarki ne. Ban yarda ta ga hawayenki ba, ta kuma ga bakin ciki iri- iri, don haka taimaketa ta girbi alhcrin hakurinta, koma me ke cikinki watstsake mu yi shagalin bikin tare, hankalinmu kuma a kwance." Kalaman Hajiya suka kara fahimtar da ni cewa bai kamata in bari tUauna ta san halin da nake ciki ba a yanzu. Ana ta hidimar biki ta ko'ina sai tashin kida kake ji amare suna can a tsakar gida suna ta faman cashewa, angwaye da abokansu suna ta yi musu kari. Ni kam ina daki kwance a jikin Hajiya sai kukan sharbe nake yi, babu abin da ke kai kawo cikin zuciyata sai tambayar wane ne mahaifna? Shin yana raye a duniya ko ya mutu? Shin da gaske Umman ce ta haifen ko kuwa ma ni din 'yar tsintuwa ce, tun dama gashi wasu na yi mini łakabin shegiya. To in kuwa ni shegiya ce ai na tabbatar ba Ummana ce za ta yi wannan cikin shegen ba, na san darajarta ta. wuce hakan. Sau. biyu ana aikowa wai a fito da amarya ta yi rawa, sai kawayen Umma da ke falo su ce a'a a je a gaya musu .wannan amaryar ba mai rawa ba ce, ba ta iya ba. Da daddare misalin karfe takwas aka fara tafiya kasaitacciyar liyafar da baba ya shirya, don taya shi murnar auren 'ya'yanshi da ya yi. Ni kam ko 129 goggoron da amare ke sanyawa ban saka ba, katon gyale kawai Hajiya Hauwa ta miko mini na yi lullubi da shi, hakan nan da abokan yaya Almu suka nemi a ba su ni in tafi tare da ango kamar yanda aka yi wa sauran angwayen, hakuri hajiya Hauwa ta ba su ta ce musu su je za ta kawo musu ta su amaryar. Wurin liyafar ya kai ya kawo ko iyakacin abin da baba ya kashewa liyafar shi kadai ya kashe ya isa a ce ya kashe kudi. An yi matukar kawata wurin, abin ba a magana. Angwaye da amarensu suna kan high table ni kam ina zaune tsakanin kawayen Ummana Hajiya Hauwa da Hajiya Furera don su suka zo da ni daga inda muke zaune, ina kallon kowa ina hango Umma farin cikinta a bayyane yake, shi ma Baba haka. Na zuba mishi ido ina kallonshi cikin zuciyata na ce, wannan wane irin mutanne mai iya maida dan wani ya zama na shi? Ina cikin wannan tunanin aka fara bude taro da addu'a aka yi ta gabatar da abubuwa iri-iri kamar yanda aka tsara su. Zuwa can sai aka nemi mutum daya a cikin angwaye ya wakilce su ya yi jawabi. Yaya Junaidu ne ya yi hakan. Da ya gama. ya zauna sai aka,nemi wata daga cikin amare ma ta tashi ta yi magana a madadinsu. Ban 6ata lokaci ba na mike cikin lullubina har kasa hawaye suna zuba a idona na bude jawabin nawa da doguwar addu'ar da ta sanya gaba daya mutanen wurin suka shiga cikin nutsuwarsu. Na yi wa Annabin Rahama salati. Sannan na yi sallama ga 'yan'uwa Musulmi, wanda gaba daya 130 dakin ne suke amsa sallamar, saboda hankulansu sun riga sun dawo gareni. Na fara gabatar da godiya cikin harshen turanci amadadin da sauran amare duka ga 1yayenmu da daukacin jama'a maza da mata, wadanda suka taimaka wajen ganin komai ya tafi kamar yanda aka tsara shi. Sannan a karshe na ce, zan sake mika tawa godiyar ta musamman ga iyayena guda biyu da na sani a matsayin uwa da uba, wato Umma da baba. Na ce iyayen da suka rike ni, wani irin riko da ya shagaltar da ni daga tunanin 'WACE CE NI' sai a yau din nan na bayar da bayani na yarda na girma gabansu, ban taba tunanin iyaye ba, saboda tsananin gatan da suka yi mini. Na fadi yanda zuciyata ta yi ta kai kawo a iokacin da baba ya ce zai hadani aure da mutumin da nake ganin ni da shi duk daya, ma'ana dukkanmu ya'yanshi. A karshe dai na ture shi gefe na kuma yardarwa kaina cewar ni ce 'yar baba ta cikinshi, sai a yau din nan da gaskiya ta bayyana. Dakin ya rabu biyu wasu suna tausayin jawabin nawa, wasu kuwa dariya suke yi. Na kalli Wurin da baba yake zaune na ce mishi, "Godiya mai yawa gare ka ya kai babana, har abada ni a wurina kai na mahaifina. Na koma na zauna. ina zama sankiran da ke gabatar da abubuwa ya mike cikin ajiyar zuciya mai karfi ya ce, Wohoho! Ga wani jawabi mai ban tausayi jama'a kalubalane mu mutane nawa ne suke iya yi wa 131 ya'yan da ba na su ba ne irin rikon da yarinyar nan take bada labarin an yi mata? Ko ni in ban da ita da bakinta ta fada da tambayata aka yi in fidda mutum daya tsakanin ita a angon nata wane ne dan Alhaji Bello na cikinshi ita zan zaba." Yana gama maganar cikin raha gaba daya dakin aka kwashe da dariya, ya tsaya yana kallon kowa tamkar ba shi ne ya yi abin dariyar ba. Sai da ya ga an nutsu. Sannan ya sake cewa, To kalubalenmu mu iyaye. Yanzu kuma za mu sake neman wata daga cikin amare ta yi mana karatu Alkur'ani mai girma kafin mu rufe taron da addu'a." Ganin da na yi amaren ba su motsa ba, ya sa na sake mikewa na karanto ayoyi goman karshe na cikin suratul Bakara. Sannan na koma na' zauna. Ban san me, baba yake radawa Umma ba, na dai hange su ne yana gaya mata wani abu a kunne, ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa, sai murmushi take yi. Mun fito daga wurin liyafar bayan an rufe taron da addu'a Hajiyá Hauwa tana rike da ni za ta shigar da ni cikin motar da muka zo a ciki, don mu koma gida. Sai na ji yaya Almu yana ce mata. "Hajiya kin manta ai nine zan tafi da amarya." Ta yi maza ta ce, "Haka ne Mustapha omantawa na yi." Ta yi maza ta juya ta sakani çikin motar da yake tsaye a cikinta kan in ce komai har ya yi maza ya shige ciki ya zuge gilasan ta bakake ya rankwafo da 132 kanshi jikina ya ce,Y au iyaycn baba sun sake haudwa. " Yana fadin hakan ya saki wani kyakkyawan murmushi ya ce, Ai kin riga kin yi sallama da Umma, Baba y8 riga ya sallame mu ya ce kowanne ango yana da 'yancin tafiya da amäryarshi a yau. Junaidu yanzu yana hanyar airport ya nufa ya ce jirgin dare zai bi a gidanshi zai yi angwancinshi, nima ban samu jirgin ba ne mai zuwa Kaduna yanzu da daddare, amma duk da haka muna da daki." Ya dauko dan makullin ya nuna mini. Sai da na ji gabana ya fadi, ya sake kallona ya yi wani murmushin ya ce,Y anzu can za mu don ki gyara mini shimfida." Na ce, "Haba yaya Aimu auren da aka daura yau shi ne har za ka fara kira mishi irin wannan maganar?" Ya bata-rai ya ce, To bari in jira sai badi." Na ce, 'A'a ba haka nake nufi ba, amma dai ka san, ina da matsala da Umma, ina son ganinta don ta gaya mini wance ne mahaifina?" Ya ce, "Ni ba ni da matsala da ita a kan wannan tun da ni a sanuna mun riga mu warware. Na ce ni na bar miki baban, kuma ke ma dazu anan kin yi magana mai dadı' cewar shi ne mahaifinki na har abada, to ba shi kenan ba? Na ce, "A'a yaya Almu." Ya yi maza ya cc, 'A'a kar mu bata lokaci a 133 Kan wannan na vi miki alkawari nan da wata uku zan kawo ki ki ganta, in ya so lokacin sai ta yi miki wannan bayanin. Nan ce, 'To gaskiya ni ban yarda da zuwa wani wuri ba mu je gida kawai. Ya sake zuge gilas ya cewa direba shiga ka kai mu gida. Muna shiga dakin na su al'amura suka sauya, abin da ban taba tunani ba kwana daki aya da yaya Almu bai zame mini komai ba an yi hakan yati a kirga, ban taba ganin ranar da ya dora hannunshi a jikina ba. Na yi kokarin kwance kaina daga gare shi na kasa, na kalleshi cikin haki na ce mishi. Zan yi maka ihu ga su yaya Musa nan a dakin can su jika." Da ya dan saurara yana jn maganata yana jin abin da na fadi. Ya ci gaba da abin da yake yi yana cewa, "In ihun ya dame su sai su bar wurin, amma ni kam ai ba ni da matsala, don na dade da sanin cewar daren farko sau da yawa ba girma da arziki ake yin shi ba. " Ganin da na yi ya kusa yin galaba a kaina, don tuni ya riga ya gama zubar da kayan jikina ya sa na fara rokon shi. "Kar mu yi dambe da kai yaya Almu, kar ka ce za ka nuna mini karfi wanka kawai za ka bami in yi shi ne matsalata, don in ji dadin jikina." Yana jin haka ya yi maza yay tsallake ya nuii 134 ban daki don shirya mini ruwan wankan. Nima na yi maza na suri sabon tawul din da ya wurga akan kujera lokacin muka shigo na daura a kirjina na yi a hankali na bude kofa na yi waje da gudu. Wurin Ummana na nufa. Na yi sa'a wurin nata a bude yake daga nesa kana jiwo kamshin da ke fitowa daga cikin shi, ita kadai ce a ciki tana zaune gaban madubinta wai gyaran jikinta take yi. Tana ganina ta saki baki tana kallona cikin mamaki ta ce, "A daren nan Adawiyyah ga hadari me ya hana ki tsaya ki bai wa mijinki hakkinshi?" Ina jin wannan maganar tata na fashe mata da kuka na ce, "Umma!" Ta ce, 'Eh to mene ne Adawiyyah? Nima wurin mijina nake shirin zuwa me zai hana ke ma ki je wurin na ki mijin in ya so da safe mun hadu duk wata magana da kike son mu yi." Ina kukan na yi mata rantsuwa na oe, "Umma ba zan taba sauraran yaya AlImu ba. Ba zan taba bashi hadin kai ba. Ba zai samu abin da yake nema a wurina ba, har sai ranar da kika yarda kika gaya mini WACE CE NI? Umma ta zuba mini ido cikin nutsuwa, kallona take yi. Wani irin kallon da, ban san me yake nufi ba. Zuwa can ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ya zama dole in gaya miki ke wace ce? Tun da an riga an yi iska asiri kuma ya tonu." Mu tafi littafi na uku don jin wace ce Rabi'atun 135 tamu? Na gode. Ubangiji ya sake sada mu da alheri. Note: Kafin úwar Rabi'atu ta gaya mana ita din Wace Ce? Ke a naki tunanin WACE CE RABI'ATU? INA SAURARON AMSOSHINKU. 07035586299, 08025078968 Ta ku: Hafsat C, Sodangi. 136 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa

Chapter 8 of 9