Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
zuwan su ba, saboda dai ni din ni ce uwarta. To irin rayuwar da ni na yi irinta ita ma Adawiyyah za ta yi?" Yaya Junaidu ya kalleta cikin nutsuwa ya ce mata, 'Eh Umma za ta yi rayuwar gwagwarmaya da kwaramni'ya irin wacce kike cewa kina jiye mata tsoro, sai dai kar ki manta kin yi rayuwar gwagwarmayar ne a karkashin shugabancin mutum mai adalci, mutumin da ya san karamci da amana, wanda ya sadaukar da rayuwarshi don samarwa kasa da shi ingantacciyar rayuwa, ba kuma sai na gaya miki ba kin fi sanin cewar bai hada ki da kowa ba a zaman da kika yi da shi, balle ya fifita wani a kan ki. To ki yi wa Adawiyyah addu'a ita ma ta samu irin na kin, amma ba ki, rinka gudar mata ba. Na sha cin cewa Umma ina yi wa 'yanmata nasiha da cewar lallai ne su zamo masu godiya bisa alherin mazajensu." Umma ta yi shiru ta sunkuyar da kanta kasa lana sauraron shi da ya yi shiru, sai ta ce mishi, "Na 19 gode Junaidu." Suma suka yi mata sallama suka fita suka tafi na dan bi su da kallo. Sai da na ga sun bace. Sannan na matsa kusa da ita na ce mata; "Umma." Ta dago ta kalleni. Na ce mata, "Wai me ya kawo Wadannan abubuwan Umma?" Ta yi shiru tana kallona. Na ce,, "Kuma ga wasu maganganun ban mamaki da na ji Yaya Junaidu yana yi a gaban Baba da ban san me suke nufi ba. Anya Umma ba kya yi mini wani boye-boye kuwa ko wani kunu-kunu..." Kan in karasa sai kawai na ji ta kife ni da wani irin mari, sai da na dungura a kasa. Tsoro gami da mamaki suka taru suka lullubeni. Yau kawai sau biyu Umma ta maren, mari kuma ba na wasa ba. A tsawon zamana da ita kuma kafin yau hakan bai taba faruwa ba. Lamo na yi na kwanta a kasa ina sauraron abin da zai biyo baya, ko za ta rufc ni da duka ne? Shiru ban ji wanr motsi ba, don haka na lallaba nan ja jikina na shige cikin daki na hau gado na kwanta, na bar ta nan zaune a kan kujera kuka take ta yi a zuciyata na ce "Watakila dai da ma dan kadan kike jira." Yanda Umma ta kwana a zaune tana kuka haka nima na kwana a kwance idona biyu. Al'amurán wunin ranar na ke tunawa, tun daga ji dana yi baba yana anbaton hadani aure da Yaya Almu ko da yake dai ban samu wanda ya amsa cewar ya tayani jin 20 wannan zancen ba. 1o amma kuma al'amura musu yawa sun biyo bayan hakan, masu tsanani da kuma na ban mamaki. Gari na wayewa na y1 komai da na saba a dakin tun daga wanka,, da alwala da sallah. Na yi kwalliyata ta hanyar gyaran jikina na kuma shafe shi da turaren Humra. Sannan na sanya doguwar rigata na yane kaina na fito don in gaida Umma. A falo inda ta kwana a zaune kasa kallon fuskarta na yi, saboda kunburin idanuwanta. Ina gama gaishcta na shuri takalmana na fita ba ta kirani ba, watakila ta yi zaton za ni gaida mutanen gidan nc, ko kuma wurin Baba, tun da yana nan, ni kuam dakinsu Yaya Almu na nufa za ni wurin Yaya Junaidu, don na gane akwai wani abu muhimmis a tsakanina da shi. Sai da na ji ya amsa sallamar da na yi kafin na tura kofa na shiga dakin na su, yana kwance akan katifa yayin da Yaya Almu yake zaune kan kujera guda daya da ke dakin. Na durkusa na gaishe shi, yana amsawa cikin nutsuwa sosai watakila shi ma ya gane giFmamawar da nake yi mishi ya karu. Ya zuba mini ido cikin yanayin kulawa sosai kafin ya ce mini, "Me ya fito da ke yanzu a sanyin nan kuma da sassafe?" Na ce mishi, "Yaya Junaidu wurinka na zo, don na gane akwai wani abu mai girma a tsakanina da kai nan gane kana da wani muhimmanci mai karfi a 21 kaina, duk da ban san fa inda ya fito ba. A hankali ya ce mini, "Amma ina fata ba abin da kika zo tambaya kenan yanzu ko?" Na ce mishi, "Eh Yaya Junaidu zuwa na yi in tambayeka ka gaya mini gaskiya ka ji Baba ya ambaci sunana a wurin nan jiya?" A nutse ya ce mini, "Na ji ya ambaci sunanki Adawiyya mene ne?" So nake ka gaya mini dawa ka ji ya ce zai hada ni?" Cikin nutsuwa ya ce mini, "Da Mustapha ne." Na sake kallonshi na tambayc shi, 'Wane ne Mustaphan?" Kan Yaya Junaidu ya amsa mini sai na ji Yaya Almu ya ce mini, "Mustaphan wurin aikin ku, ko ba sunan yallabai din office din ku kenan ba? Ai kin san na gaya miki cewar bayan kin gama aikin nan zuwan yallabai din ku biyu ya zo wurin baba, saboda an ce mishi ba zai yiwu ya zo ya kiraki ba sai ya nemi izini. To shi ne daga baya ya turo iyaycnshi." Sanin da na yi an yi wadannan abubuwa da Yaya Almu ya fada duka ya sa na kidime nan da nan na shiga kokarin tunanin sunan yallabai na asali. Ina cikin haka Yaya Junaidu ya ce mini, "Saurare ni Adawiyyah." Na juya gare shi na maida hankalina wurin sauraron abin da zai gaya mini. Ya ce, Ki nutsu ki zama mai hankali, kin ji motsin wata yarinya a gidan 22 nan tun da aka yi maganar nan?" Na ce mishi, "A'a." T kina nufin su duk sun gamsu da abin da aka yi musu ne?" Ban amsa ba, sunkuyar da kaina kasa kawai na yi. Ya ce, To ina tabbatar miki biyayya kawai suka yi, don haka ki tafi ke ma ki nutsu ki zauna wurin daya ki kudurwa ranki yi wa Baba biyayyar da tafi ta su yawa." Na ce mishi, 'To." Na mike zan fita da ni, "Daga nan kar ki je ko'ina ki wuce wurin Umman ki kawai." "Zan je in gaida Baba tukunna." Na ce da shi. "Baba yana Lagos yanzu Adawiyya sai da muka ga tashin shi a filin jirgi ni da Mustapha. Sannan muka biyo hanya muka dawo muka yi sallar Asuba a gidan nan Ya dauki Umma Amarya sun tafi ya bar Umma Karama, duk da da ita ya kamata ya koma ta karasa kwanakinta da ba ta gama ba, saboda bai huce ba kan laifinta da ta yi mishi ita ma Umma ya tafi bai yi mata sallama ba, saboda ran shi ya baci da abin da. ta yi mishin, ko ni da Mustapha mun ji ana bude get din gida ne muka fita da sauri muka gan su za su tafi shi ne muka yi mishi rakiya, don haka ki nutsu ki shiga hankalinki kar ki bari shi ma ya yi fushi da ke." To yaya Junaidu." Na ce da shi. A falon Umma na same ta zaune kan sallayarta 23 na durkusa a gefenta duk da tsoron da nake ji na kar ta sake marina. Na ce mata, 'Umma baba ya taff" Ta gyada kai nuna alamar ta sani. Hawaye suka zubo shar! Daga idanuna loakcin da na buda baki na ce mata, 'Saboda ni ya yi fushi da ke?" Ta dan saki fuskarta ta shafa fatiha ta miko hannu tana share mini hawaye a hankali ta ce, "Ba saboda ke ba ne Adawiyya laifi na yi mishi." Na sake kallon Umma cikin nutsuwa a kumna tsoracc na ce mata, 'Umma." Ta zuba mini ido tana kallona cikin sauraro ni kuma ina tsoro fadin maganar, don ina tsoron marin da ta gane yi mini, ban sani ba ko ta gane haka ne sai ta miko mini hannunta alamar wai in kara matsawa jikinta, cikin sauri na yi hakan ta kwantar da kaina akan cinyarta ba tare da ta yi mini komai ba, nima kuma ban sake yin wata magana ba. Har baba Talatu ta shigo tana tambayar me za a shirya mata na abin karyawa? Wajcn karfc goma da rabi ne yaya Junaidu ya shigo ya gaida Umma, ya kuam shaida mata cewar za su bi bayan Baba za su je su bashi hakuri kan fushin da ya yi. Ta ce mishi yana da kyau hakan kai da wayc? Ya ce dukkan mu ni da Zubairu da Kabiru da Mustapha. Ta ce to ku gaishe shi. Bayan fitarshi su Yaya Kabiru duk suka shigo suka yi mata sallama, yaya Almu ne ya shigo a karshe yana ganina a zaune ya ce, Ya ya haka ba za ki shirya ba?" Na ce, 'Ai ban da ni." Ya ya maza ya ce, "Haba 24 Rabi shirya mana mu je ki yi mini rakiya." Na ce mishi to. Kasancewar wurin Baba za a je ya sa na yi kwalliyar atamfa fara super ce tana da dan adon furanni bakake jefi-jefi. Takalmin da na yi amfani da shi shi ma baki da fari ne hakan nan jakar hannuna sai na yafa farin gyaie na yi matukar yin kyau, sai daukan ido nake yi, ga kuma kamshina na kowanne lokaci. Na yi wa Umma sallama na fito na hangi yaya Almu yana fitowa daga wurin Umma karama lokacin ne na tuna yau ko gaisheta ban je na yi ba. Na same su a waje dukkansu sun shirya dukkansu kwalliyar ta zarce suka yi babu kuma wanda bai sanya hula ba a cikin su, sun yi matukar yin kyau, amma zan iya cewa yaya Almu daban yake kasancewar shi mai yawan amfani da fararen tufafi, saboda ganin shi a cikin su bai hanawa ka yi ta ganin kyan kwalliyar tashi ya yi kyau. Yaya Junaidu da yaya Zubairu ne a gaba, yaya Zubairu yana tuki, yaya Kabiru yana santar bayan direba sai yaya Almu a tsakiya ni kuma ina gefen shi ta jikin kofa. Ana tafiya suna hirarsu mafi yawancin magangarta su akan aure ne da halaiyar mata na tsananin kishi da rashin hakuri. Yaya Zubeairu yana ba Su labrin abin da Umma Karama ta. yi wa Baba da yanda ita da kanta ta nemi ya ba ta saki da kuma ya ce ya ba ta sakin ta rude tana ta faman kuka. To wannan wane irin abu ne naka? Yaya Kabiru ya ce, 25 Eh ai su haka suke suna son abu suke nuna wai ba su son shi a dole su ga masu jan aji. Su ka dan yi dariya cikin jinjina lamarin, shi kam Yaya Junaidu tsaki ya yi ya ce, "Ni fa ko dokin auren nan ba na yi saboda na san wani nauyi ne kawai zai hau kan mutum kuma ko daga kallon irin yadda al'amura suke tafiya ma ai kai ka san su baba hakuri kawai suke yi." Yaya Almu ya karkato ya sunkuyar da bakinshi ta wurin kunnena ya ce, "Ki ji mun Junaidu wai baya dokin aure, saboda sai an yi hakuri da mace ake iya zama da ita, shi ke nan yake jin haka ni kam dokin nake yi ina zumudis cikin raina a kowanne lokaci kuma kallon agogo nake yi ina ganin tafiyar lokaci, ina kirga sauran awowin da suka rage a kawo mini Uwale, kin san irin son da nake yi mata kuwa?" Na girgiza kai nuna alamar ban sani ba. Ya ce, "Uhm! To ko yau din nan sai da na ganta wajen sau hudu, amma har yanzu ban gaji da ganin nata ba, ji nake tamkar a bar mu mu biyu kawai a daki mu yi ta maganarmu mai dadi in kuma na ji ina ra'ayi in dan shafe ta in ji dadi." Na ce, "To ai kai da zamanka ka yi a gidansu kawai ba ka yiwo wannan tafiyar ba." Ya yi maza ya ce. 'Eh kuwa to sai dai kuma na riga ai na fito, amma dai bari kawai ba zan yarda a kwana ba yau din nan za mu dawo, don in je in ganta da daddare." Ya dago ido ya kalli Yaya Zubairu da ke ta faman tuki ya ce mishi, 26 "Kai Zubairu wannan irin tafiya da kake yi ni fa sauri nake yi, don ba kwana zan yi ba, zan dawo in tafi tadi." Yaya Kabiru ya ce, To mu sauke ka mana ka bi ta nan." Ya nuna mishi hanyar daji wai ya yi yanke. Gaba daya suka kwashe da dariya, suka ci gaba da zAncensu shi ma ya juyo wurina hannunshi ya miko- yana taba makalallen dankunnen kunnena na asalin azurfa, ya ce, "Rabi kenan ke kam kin iya kwalliya har dan kunnen nan ma fari ne da ratsin baki ga abin wuyan shi ma." Ya mika hannu zai ciro abin wuyan daga cikin gyalena wai ya kara gani, karo, na farko da na ji ba na son hakan na yi maza na hana shi. Cikin hanzari ya daga hannun nashi daga jikina yana cewa, "Uh! Gara in yi maza in koyi daina taba jikinki kar wata rana Uwa ta ganni, don na san kishi za ta yi, daga ganinta. To wannan fa na gamu da daidai da ni ni kishi-kishi ya ya kenan?" Ya zuba mini ido yana kallona cikin sauraro ban tanka mishi ba. Ke kin san kishin Uwa kuwa?" Ya sake tambayata, ,nima na sake yin kamar ba da ni yake maganar ba, ya dan yi murmushi ya ce, "To ko da yake dai babu komai tun da ina son ta kin san shi namiji kan matar da yake so kamar bawa yake." A Zuciyata na ce, kai ne dai hakan. "Ai ni babu abin da Uwa za ta yi mini in ce bana dokin aurenta, ko in rinka maganganu irin na Junaidu ji shi ji abin da yake fadi." Lokacin ne na 27 Jiwo hirar da Yaya Junaidu yake yi na wani abokin sh da wai saboda halaiyar matar shi, shi din ya daina Zuwa gidansu. Yaya Almu ya kalleni ya ce, "Ni doon irin su Junaidu sun daina zuwa gidana ni da Uwale ina ruwana? Ban da kawai mu rufe kofa mu yi ta sha'aninmu." Na kalle shi kawai cikin zuciyata na ce, 'Ai kai kam sai addu'a don ka riga ka tafi." Jirgin sha biyu da rabi muka hau, don haka a gida muka yi sallar Azahar. Bayan mun idar ne muak sami Baba a falo shi da Umma Amarya, ta sha kwalliya riga da siket wai Umma ta sanya tamkar wata 'yar yarinya. Baba yana cin abincin da Umma Amarya ta gama shirya mishi a gaban shi ya kalle mu ya ce, "Wannan wane irin zuwa kuka yi babu sanarwa, babu komai ko kuma kin zo ne don ku cinye mini abin dadin da Amaryata ta shirya mini?" Gaba daya aka dan yi murmushi, sai yaya Junaidu ya ce mishi, "Baba mun zo ne don mu baka hakuri kan laifin..... " Kan ya karasa baba ya katse shi. "Kar wanda ya ce zai yi mini wata magana ko ya ce zai ba ni hakuri, ba zan saurare shi ba tun da dai ita uwarku ta ga abin da ya dace ta rinka yi mini kenan, to mu je zubawa ni da ita." Gaba daya aka sake shiga wata nutsuwar ni kam kuka a kama yi. Yaya Zubairu ya kara rage murya ya ce, "Baba, Umma kuwa mai gudun Bacin. 28 ranka ce, ko wani ta hango zai bata ma hankalinta tashi yake yi." Ya ce, Eh, amma kuma tafi kowa yi mini abu cikin gadara ina abin da ya shigar da ita cikin maganata ni da matata, ita auro mini ita? Ko ba kwanan nan ne ta yi mini irin wannan abin ba na ce mata kar ta sake shi ne yanzu ma ta sake? Saboda ta raina ni, to hana ta tafiyar da kuka yi ni zan bar mata gidan na shekara guda ko daurin auren ku ba zani ba, su Yayan Tudu sa daura." Kukan da nake yi ya tsananta sosai, na ce, "Baba ka yi hakuri." Ya kalleni cikin bacin rai ya ce, Haba Uwata a ce har yanzu ni ban wuce Umman ku ta dauko hijabinta ta ce za ta bar mini gida ba, saboda wani abin bacin ran da na mata ba? Na ce, "Ka yi hakuri Baba ta san ta yi maka laifi, ta ce mini ta yi maka laifi." Ya zuba mini ido ya ce, Ta gaya miki?" Na yi maza na ce mishi, 'Eh Baba, ta ce mini ta yi maka laifi na kuma San ba ta ji dadin abin da ta yin ba." Ya ce, 'A'a ta ji dadin hakan da ta yi Uwata tana sane da abin da take in ba haka ba ai kwanan nan ne na ce mata kar ta sake yin hakan, ta ce ba za te sake ba." Yaya Almu ya dan gyara zama ya ce, Baba ba 1a kwanan nan ba ne tun Rabi tana da shekaru hudu ne abin ya faru." Baba ya ce, 'Af! To yaushe ne? Yaushe ne aka 29 naifi Uwata? Ba kwanan nan ba ne aka haifeta, anan gidan ne fa aka yi renonta. Aurena kuwa da ita uwar taku ai ba na shekaru arba'in ne daidai, amma saboda rikicin auren da ba a daura ba ta fito za ta tafi ana ba ta hakuri, babu kuma abin da yafi komai kona mini zuciya irin 'wuce ni da ta yi ina tsaye ai na fito ne don ta ganni ta koma, amma ta wuce ba ta fasa ba, wato bari ta nuna mini ni din me? Yaya Kabiru ya ce, Ka yi hakuri Baba, Umma ba za ta fadi haka ba ta dai yi maka ba daidai ba in mun je gida kuma za mu gaya mata duk da ta sani ta san ta yi maka laifi, kuma na san ta fi mu rashin jinn dadi." Baba ya dan yi shiru jimawa kadan ya ce, "Abin da take gadara da shi kenan ta san komai ta yi ba za ku bar ni in yi mata abin da ya dace da ita ba, ai ya dace ta shekara ba ta ganni ba, in Maryam ta gama kwanakinta ita Hajiya Karama ta zo ita kuwa ta yi ta zamanta anan." Yaya Junaidu ya sake gyara zama cikin nutsuwa ya kalle shi ya ce mishi, "Baba ka taba ce mana ba a biyewa mata." Baba ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya ne Junaidu ba a biye musu ku yi, ta hakuri da su, don kuwa su din manyansu da yaran su halinsu duk daya ne, yanzu ka duba ka gani irin gudun bacin ran yarinyar nan da nake yi, amma ko a jiknta, ita in tayi nishadi sai ta bata mini." 30 Jikina ya yi sanyi na yi zaton ko da ni baba yake maganar. Na yi maza na kalle shi na ce, Ni Baba?" Ya ce, "Uwar ki dai ke kam me za ki yi ki bata mini rai uwata?" Na dan sake kallon shi na ce, "Baba yanzu ka ce auren ku shekaru arba'in kuma kana ce mata yarinya? " Ya ce, Yarinya ce uwata na mafi ganin kuruciyar ta kan kowa, don kuwa an daura man aure ne tana da shekaru bakwai. Wani irin aure da mutunci da amana ya bani, amma wai kullum aka dan yi wani abu sai ta zaro gyale wai ita za ta bar ni a ce ba ta ci mutuncina ba?" Na ce, 'Gaskiya Baba ba ta kyauta ba ka yi hakuri." Ya ce, 'To ya ya zan yi? Ya wuce." Muka shiga hira sosai. Baba ya ce, "Za ku tafi ne ko kuwa kwana za ku yi?" Na yi maza na ce, "Ni dai kwana zan yi Baba." Yaya Zubairu ya ce, "Mu zamu koma don mun fito dukanmu ba mu bar kowa ba a gidan." Baba ya yi maza ya kalle shi ya ce, "Abin da nake yawan tunawa kenan, dukan ku za ku bar gidan ko da yake dai ga wasu samarin nan su Hamza, amma me kuke ganí?" Yaya Kabiru ya ce, "Za su iya yin komai baba a1 shi Hamza da Musa masu tsayawa ne kan al'amura za su daidaita komai." 31 Ana waunan maganar yaya Almu ya yi mini magana a hankali, "Ki dai san wannan zuwan na ki rakiya kika yi mini, don haka ba wani kwanan da za ki yi tafiya za mu yi, don ni ba zan kwana ba zan je gida in je tadi, zan kuma gayawa Baba." Na yi maza na ce, "A'a ina ruwana?" Baba ya kalleni ya ce, "Mene ne Uwata?" Na ce, "Baba Yaya Almu ne wai ba zan kwana ba." Ya ce, 'A'a a kan me? Shi ma ya kwana mana in yana so, mene ne na sai ya sa ki kin tafi? Ai ni ma ina son kwanan na ki sai mu yi hira ko? Na ce, "Eh Baba." Jin da na yi Baba ya co yana son kwanan ya sa na yi niyyar yi mishi girki, don ya kara jin dadi. Ana idar da sallar La'asar na shiga kicin na samu Umma Amarya a ciki na shiga tayata aikin da take shirin yi. Muna 'yar hira sai ga Yaya Almu ya iso kofar kicin din. "Rabi zo mana." Ban kalle shi ba, na ce, Girki zan yi wa Baba." Umma tana jin haka ta fice daga ciki, shi kuma ya shigo, "Ke yarinyar nan kina so ki raina ni fa kwanan nan in kinra ki ki ce ba za ki zo ba?" Na ce, 'A'a to mene ne in na fadi haka kai da kake murnar za ka samu matar da za ta raba ka da yan'uwa duka? Ai har da haka zai kara sawa in kwana, don in gayawa baba komai da komai, in yana 32 da abin yi tun wuri ya yi." Yaya Almu ya zuba mini ido ya ce, "Ke ki ce za ki zauna ne don ki kulla mini sharri, yaushe na gaya miki haka? ta uwa ma wannan salihar yarinyar yaushe za ta ce za ta raba ni da ku?" Na ce, Ai ba ita ce mai raba kan ba, ra'ayin ka ne hakan kana samun mata za ka rabu da 'yan'uwa." Yay ce, "Tabdijam! To ai gara da na biyo ki kicin din nan kin ga ai na ji irin kullalliyar da kike neman ki kulla mini." Na yi shiru na soma shirye-shiryen girkin da zan yi ina harhada kayayyakin da zan yi amfani da su ya matso kusa.da ni a hankali ya rada mini. "Da gaske aure nake so Rabi, kamar in yi ya ya? Yanzu na riga na girma son mace na ke kamar me? Da kuma ba ta damen ba, don ni ko 'yan mata a ban cika yi ba sai dai kawaye, amma a dan tsakanin nan ni ka ina a tsorace da kaina nake, shi ya sa kusan kullum ki ke ganina ina Azumi." Na ce, "Uh! Yana da kyau." Na ci gaba da aikina, shi kuma ya kara matsowa jikina. "In ban da sha'anin kima Rabi ai da na yi miki wata magana." Na ce, "Kamar wacce iri kenan?" Ya ce, "A'a na gane kamar kin tsorata sosai kan cewar da kika ce kin ji kamar baba ya yi na cewar Zai hadani da ke aure. 33 Na yi maza na kalleshi na ce, Zan tsorata manan hakan fa yana nufin tsakanin ni da kai akwai wanda ba baba ne ya haife shi ba." Hankalin Yaya Almu a kwance ya ce mini, "To sai me in an yi haka? Ni inda na san wannan kawai matsalarki ai da sai in ce miki ke ki rike baban kawai na ki ne, ke kadai tun da kin fi ni tabbacin zama yar shi ko ba komai ke Umma ce uwarki, yanzun nan ne kuma baba ya gama cewa tun tana da shekaru bakwai aka bashi ita, bayan haka ke kadai ce mai kama da ita a gidan nan. Ni kuwa muan da yawa ni ina kama da baba, Junaidu yana yi, Zubairu yana yi, Musa yana yi, kin ga da sai duk ki maida mu 'ya'yan dangi kawai, in ya so ni sai in zama surukin shi.' Na ce, 'A'a ai kai ma Umma Amarya ce ta haifeka." Ya ce, "Ai wannan ba komai ba ne tun da ita Umma Amarya ba budurwa ba ce, lokacin da baban ya aureta." Sai da plate din hannuna ya subuce kasa ya tamutse, jin maganar da Yaya Almu ya yi mini. Bai ku kara kaduwar da na yi ba sai kawai ya sunkuya ya tsine fasassun tangaran din ya zuba su cikin dosbin ya tawo ya tsaya kusa da ni, bayan ya wanke hannunshi. 'Ashe Umma ba ta taba gaya miki ba? Ai ita- Umma Amarya ta auri Baba ne bayan ta fita takabar mijints na farko kin ga kenan in dai dan'uwanshi ta 34 aura ta can na samo kamannina da shi, kamar dai su Junaidu kenan ko ya ya kika gani? Hakan bai yi ba?" Nan da nan zuciyata ta shiga kai kawo cikin tunani mai tsananin rudarwa a ce yaya Almu ba dan Baba ba ne na cikin shi? Kai zan ji tausayin shi in har hakan ya faru baki ne komai ba rabi nace kai yaya Almu ace zaune kaima badin Baba bane na cikin shi zanji tausayin shi in har hakan ya zai sance Baba yana bakarar da hanziri jarumi mutumin kirki kamar ka wanda zai yi alfahari dani wanda zai rinka daga ido yana kallonshi yana ganin shi a matsayin wani alheri da Ubangiji yayi yarda in kore shi in har zan iya yara in kore shi daga jikinshi ince kai din ba nashi bane don komai aurc ya halatta a tsakaninna da kai to na zamo mai son kaina da yawa in kuwa zane kaina akan Baba to banayiwa kaina adalci ba don haka muyi zamanmu kawai ni da kai dukkan mu ya'yan shi ne. Yaya Almu ya ce "Uhun Rabi ke nan ni a wurina da ace dukkanmu na shi ne gara a yi in wannan din, ke tashi ni surukinshi ai ya mallakmu dukanmu. Ke 'yarshi ta cikinsa wacce matar deb slke so ya ke girmamawa fiye da kowacce ta haifar rooshi, ga ki mai kyau, Rabi don kawai kin yi sa'a kin dauko kyau irin na Umma ke har ma kin so ki fita don kuwa ke kam ai ko namiji ya yi tsayinki ya more ina jin dai wurin Baba ki ka samo wannan tsayin naki, ga ki mai kirki da kuwa kin gaji kirki Rabi kin san yawa kirkin Umma da laherinta kuwa? Dubi irin shugabancin da 35 take yiwa Baba a gida yanzu ke a ganink ace ke matata ce, za ki zama mun uwargida a gidana ki y mun irin shugabancin da ki ka ga Umma ta na yi bai fi mun

Chapter 2 of 9