Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
daya ne? To me zai yi wa wata mace a duniya wanda bai yi miki shi ba?" Kullum baba ke rarrashina, hirarmu ta koma hirar bada hakuri. Gaba daya na zube na rasa girmana da hasken fatata, saboda tsananin bacin rai, abu daya dai dana rike shi ne ban yarda na daina kwalliya ba, kullum a cikinta nake. Rannan bayan fitar Alhaji daga dakina, sai na dauki buta na shiga wanka, saboda al'ada na gama ga zaton Karama wani abu muka, ba ta sani ba ni tun zuwanta babu wani abu tsakanina da shi, da yake ta zo gidan da girmanta, don ta kai shekaru sha biyar. Ashe dama ita ake ta son bashi, Baba Rabi ta hana su, kuma suka ki aurar da ita, shi nema dalilin da ya sa ta yi ta shige mini tana maida dakina wurin hirarta, don ta Tinka sa ido kan mu'amallata da mijina. Na fito daga bandaki sai na same ta tsaye kan hanya na yi kokarin kauce mata wurin wucewa, amma ina shige ta sai na ji tasa hannu ta jawo mini zanin da na ruhu da shi. "Ke ba kya ganin mutane ne kike ture su, saboda rashin hankali?" Tuni na riga na zo wuya da ita, saboda irin cin kashin da take kawo mini, don haka ina juyowa na dauke ta da mari. Ta yi maza ta 103 cakume ni da dambe, don dama abin da take so mu yi kenan, a ganinta tana da abin da za ta dauka a jikina, saboda ganin ta fini girma, ga ta kuam da masu mara mata baya sai sai dai sabanin hakan ne ya faru, don duka sosai na yi mata, kafin a kai ga raba mu ba a dauki lokaci mai tsawo bayan yin damben namu matan gida suka cika a dakinta aka ce wai ta yi bari a dalilin dukan da na yi mata, sai cewa suke yi, A'a dama da gangan ta yi ai dama ba ta yi karin komai ba illa cikin dama so take ta yi sanadin shi, ita ba ta haifa ba, kuma ba za ta bar mai haihuwa ta haifa ba." Aka yi ta wanko jini daga dakin Karama wai duk jinin barin nc. Haka Alhaji ya dawo saboda kiran da aka yi mishi, aka yi mishi bayanin abin da ya faru. Ban taba yin nadama ba irin na ranar na yi ta dana sanin kulata da na yi, ban san za ta yi bari ba da ban kulata ba, dana yi tafiyata kawai na bar mata zanin nawa da ta rike. Ina zaunc gaban Baba ina ta kuka, shi kuwa sai caccaka tokar kaskon shi yake yi da wani tsinke yana wasa da shi, bai kalleni ba. Zuwa can sai ya kallcni ya ce mini, "Kin dai san ya zame miki dole ki koyi zama da mutanen .nan tun da dai kin san zan barki a cikinsu." Rannan ko barci ban yi ba, saboda tunanin al'amurana. Baba Rbai ce ta rasu na shiga cikin wannan halin, to ran da aka ce babu baba fa? Wannan 104 shi ne abin da ya zo cikin raina tausayin kaina ya kamani ba ni da kowa sai Baba in na rasa shi ina zan tsoma raina? A wannan lokacin na shiga kunci mai tsanani gaba daya dangin Alhaji sun ce sarnun wurina ya yi yawa, ni ce bakuwa macce ma ba a san dangina ba, amma har na samu kwarin gwiwar dukan 'yarsu, in hukunci da aka yi mini bayana. Bayan a wannan lokacin Alhaji fushi yake yi da ni,, baya ko kallon inda nake bai kuma cin abincina. Karama ta sake sani a gaba fiye da kowanne lokaci na yi ta kakkauce mata musamman da yake an sake cewa tana da ciki, shi kuwa Alhaji sai faman kai kawo yake yi, ga matarshi tana da ciki za ta haifar mishi dan dana kasa haifar mishi. SAi da na kai ma ko girki na dora a kicin sai Karama. ta kwarawa muruhun ruwa, saboda neman magana sai dai in je sashin baba in yi girki, don ina tsoron kar in bar girkin a ce na bar mutanen gida da yunwa. Ina zaune a dakina cikin dare sai ga Alhaji ya shigo a fusace yana yi mini kashedi, ba zai lamunci abin da nake yi ba, dan an gaya mishi cewa ina neman in sake yin dambe da Karama, don na gane ciki nc da ita, wai har, yana cewa shi ya so bai so a fadi tana da cikin ba, don kar in sani. Na ce mishi haka ne. Ban sake wata magana ba na ja bakina na yi shiru, ina kallonshi yana ta maganganunshi bar ya yi ya gaji ya gama ya kwanta ya yi barcinshi. Gari na wayewa na je 105 na gama yi wa Baba aikinshi na shirya mishi abin karyawa na. kai mishi. Ina zaune a gcfc ina kallonshi har ya garna karyawarshi sai na kalleshi cikin cikin ladabi na ce mishi, 'Baba." Ya ce, 'Mene ne Zuwaira?" Na ce mishi, 'Lokacin da Babana ya ce mini zai kawo ni wurinka ya gaya mini cewar ka san komai gamc da shi, in na bukaci sanin inda dangina suke za ka gaya mini?" Ya daga ido ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, "Kina bukatar su ne a yanzu?" Na yi maza na ce mishi, 'Eh baba." Hawaye suka zubo mishi sharrr! Daga idanunshi ya ce, Baki bukaci saninsu a lokacin da zan iya kai ki ba, kin bukaci sanin su ne a lokacin da karfina ya kare, gaba daya bazan iya kai ki wurinsu ba, ba kuma ba zan wakilta wani don ya yi mini wannan aikin ba, amma ko ni na dade da gane kian bukatarsu don inda a cikinsu kike to da wadannan abubuwan ba su same ki ba, don kuwa dangine da ke masu yawan gaske." Fadin da Baba ya yi cewar dangi ne da ni masu yawa, amma gani nan ni kadai ban san kowa ba, kuma ba a tausayina kan hakar kullum sai an yi mini gorin dangi, ya sa na yi ta yi masa kuka. Cikin sanyin jiki ya ce mini, "Hakuri za ki yi Zuwaira ni din nan da kike ganina ni danginki ne nine kuma uwarki, nine ubanki 106 Zan kuma tsaya miki matsayin hakan a kowanne lokaci matsalar kawai ita ce zan iya barinki a kowanne lokaci." Yana fadin haka ya mike tsaye ya fita yana doddogara sandarshi, saboda rashin karfi ya je ya tura Kofar baba Rabi ya bude ya shigo yana gyara dakin. Na bi bayanshi na karbi tsintsiyar na ce mishi, "Bari in gyara maka Baba." Bai bari ba, tare muka yi aikin. Sai da muka gama ya ce mini,.'Dawo nan ki zauna kafin in ga abin da zan iya yi miki in Allah ya yarda ba zan tafi in barki cikin wannan halin ba, zan san abin da zan yi a kai." Na dawo dakin Baba Rabi na zauna kusa da Baba, ya kafa mini dokar kar ya sake ganina a wancan sashin kar in salke tambayar Alhaji komai, komai nake so in gaya mishi ko gaishe shi bai yarda in rinka yi ba, babu ruwana da shi. Na ce mishi to Baba. Girki ma namu mu biyu nake yi n kuma aka kawo mishi na seshin Albaji sai ya ce a bai wa almajirai shi ya riga ya koshi, in shiga wurinshi in yi hira in na ji barci in shiga dakin Baba Rabi in kwanta. A wannan lokacin babu abin da nake.yi irin tunaninta. Alhaji ya dawo daga tafiyar da ya yi ta kwana biyu ya same ni anan ya shiga wurin Baba ya tambaye shi wai ko ya yi wani laifi ne ya sa ya ce mini in dawo nan? Ya ce mishi, "Ba ka yi komai ba na nishadi ne kawai na karbeta tun da dama sanda na ba ka 1ta ai ba kar ka ce kana sonta ba, hasalima ko ganintä ba ka 107 taba yi ba na daura maka aure da ita, don haka in na karbeta ai ban yi laifi mai yawa ba ko? An yi wata biyu Alhaji yana ncman sañin laifinshi, baba yana cewa bai yi komai ba. Rannan ya ganshi ya zo zai shiga dakin da nake wai zai yi magana da ni don ya ga na ki kula shi. Baba ya yi maza ya dakatar da shi ya ce mishi, 'Kai Bello na haramta maka shiga dakin nan in kuwa ka yarda na ganka a ciki to ranka zai 6aci:" Zamana a wurin Baba sai na samu nutsuwa hankalina ya kwanta, na yi kiba, na yi kyau, na maida jikina. Kullum sai ya yi aike kasuwa an sayo mana nama na gasa mana in ya ga manshanu ko wani abu zai kare ya yi maza ya bada kudi a sayo mana. Komai Alhaji ya kawo mana sai ya ce, 'A'a kaiwa iyalinka kawai, ita wannan na sauke maka nauyinta ni kuam na yafe maka ba sai ka yi ta wahala da ni ba." Hankalin Alhaji ya yi mummunan tashi, ganin irin matakin da baba ya dauka a kan shi. Kowannc lokaci zai sa shi a gaba yana bashi hakuri, fare da tambayarshi. "Baba ita Zuwaira ta ce na yi mata wani abu ne?" Baba ya ce, 'A'a me ka yi mata? Ai ba ka yi mata komai ba, dan gata wanda yake cikin dangi ai shi ake yi wa laifi, amma ba irin ta ba." Tun Alhaji yana bai wa Baba hakuri yana rokonshi ya maidani, don gudun 6acin ra baban har 108 ya koma yi yake yi, don yana Son komawar nawa ya kuma matsa yana son ganina a dakinshi. Baba ya ce, ina ai an yi wannan zaman an gama in kuskure ya yi ya sa ya bashi ni, to yana neman gafara, Rannan na je gaishe shi da safe, sai ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, "Na yi niyya zan kai ki kasarku wurin danginki tun da na ji karfin jikina, amma ina so kafin mu tafi in sani in munje za ki biyo ni ne mu dawo tare bayan kin ga danginki ko kuwa za ki yi zanmanki ne a cikin su? Don in san irin shirin da zan yi miki." Na yi kamar in, cewa Baba zan yi zamana ne a cikin su sai na kasa gaya mishi hakan, don na san irin son da yake yi mini. Sai na rage murya cikin ladabi na ce mishi, "Baba ai ni taka ce ba zai yiwu in zartarwa kaina da wani hukunci ba, sai abin da ka zartar mini." Ya yi matukar jin dadin abin da na gaya mishi, ya ce mini, To ni in hukuncina ne ai ba zan rabaki da Bello ba Zuwaira, ai duk wannan abin da ke fruwa kuriciya ne da kuma halin zama na yau da gobe, saboda haka kai ki kawai zan yi ki gan su in dawo da ke." Jikina a sanyaye na ce mishi, "To Baba." Duk da dai ni kam da ba haka na so in ji ya ce ba. Ya yi ta shiri babu abin da bai shirya ba na dukiya da zai rike a hannunshi. Alhaji ya gane abin da Baba yake nufi ya tasa shi a gaba da roko da ban hakuri, gashi ya hana shi shiga dakin da nake, ni 109 kuwa ina ganinshi sai in kule ciki ba halin ya yi mini magana. Ana gobe za mu yi sammmako mu tafi, da yamma sai ga liman yana sallama da baba a waje. Kai tsaye baba ya ce mishi ya shigo. Ya shigo sashin shi. Na yi musu shimfida suka zauna na durkusa na gaishe shi. Sannan na koma daki. Liman ya kalli Baba ya ce mishi, "Haba malam Mustapha wane irin laifi ne yaron nan ya yi maka haka da aka rike mishi matarshi wata da watanni ka hana shi ita. Sannan yanzu wai kana shirin maida ita can wani wuri." Baba ya gyara zama ya kwashe labarina duka ya bashi, bai rage mishi komai ba. Sannan ya ce, To tun ina raye ma kenan ta shiga wannan hali, to in ba na nan fa ya ya za ta yi?" Liman ya jinjina al'amarin ya ce, "To babu komai al'amarin duka ba namu ba ne, ka yi hakuri ka bar mishi ita kar ka raba su ai fushin zuciya ba na ka ba nc, kai addu'a ce kawai ya' dace ka yi ta yi ita din yana da kyau ta san danginta, amma ba a irin wannan tafiyar ba, in ka maida ita dakinta aka zauna lafiya sai ka sa mijinta ya kai ta." Ina jin baba ya amsawa Liman ya janye tafiyar na yi ta kuka, shi kuwa Liman ya yi ta yi mishi godiya, ya mike zai tafi yana jaddada mishi, "Ka mayar mishi da matarshi yana." Yana cewa to. Da daddare Alhaji ya dawo yana murna, don 110 liman ya yi mishi bayanin yanda suka yi. Ya zo wurin Baba yana tambayar to yaushe zan dawo dakina? Ko kallon shi baab bai yi ba ya ce mishi, 'Sai ran da matarka ta haihu tukunna ba za ta koma a tsokane ta a yi dambe danginku su ce ta zubar da ciki ba, tun da ita na ta cikin a tafin hannu yake baya tashi kifewa sai an yi dambe da ita. To ku je in dai lissafin na ku irin nawa ne ai cikin ya yi wata bakwai, yanzu in ma bai fi ba, tun da ko zaman Zuwaira a nan wata hudu ne har da kwanaki." Maganar in koma dakina ya zama wani babban al'amari. Abin da Alhaji yake ganin ai zancen ya kare tun da har gashi an fasa maida ni, kuma an yarda za a maida ni dakina. Rannan dai ya gaji ya samu Baba a dakinshi muna tare, gasa mana naman rago nake yi a kan tire yana tayani jujjuyawa yana cewa saura nan din, nan bai gama gasuwa ba. In ce mishi to in juya. Alhaji ya shigo ya gaishe shi ya ci gaba da tsuguno, shi kuwa baba ya yi kamar bai ganshi ba. Sai da ya gaji ya ce, "Baba ina so ne in roke ka ka yi hakuri ka yafe mini laifin da na yi ka bar Zuwaira ta koma dakinta, kar ka ce sai Karama ta haihu, ni ban san ranar haihuwar ta ba, tun da jiya na tambaycta lissafin cikin kama-kame kawai take yi." Baba ya ce, 'Ai ya." Ya ci gaba da sauraron shi sai da ya ji ya gama duk bayanin da zai yi Sannan ya dauko mishi dogon tarihi tun farkon gamuwarshi da Babana, mu'amallar da ta hada su, da dadéwar da suka 111 yi ba su sadu ba; amma duk da haka ya yanke shawarar zabenshi a matsayin mutumin da ya dace ya bai wa amanar'yarshi da dalilin da ya sa shi kuma ya zabe shi ya bashi aurena, amma kuma akan idonshi ga abin da yake fruwa. Ya lissafawa Alhaji tas din abin da aka rinka yi mini wanda ni ban ma san ya sani ba, da ya gama sai ya ce mishi, "Wani ciki ne da ita? Matarka ba ta taba yin cikin ka gani ba, shi ne ba za ka lura ka gane ba, daga karya kawai?" Ni kaina ban taba zaton cikin karya Karama ke yi ba, sai a wannan lokacin. Alhaji ya ce, To ka yi hakuri baba ka barta ta dawo dakinta yau." Baba ya yi maza ya ce, 'A'a ba za ta shiga wannan kurar ba sai an samu okaci an gyara tukunna in na nutsa zan samu musu gyara mata in ba su su yi." A haka ya mike ya tafi. Kwana biyar bayan nan sai ya dawo ya samu Baba ya ce mishi, "Yaushe ne komawar tata?" Baba ya ce ai har yanzu bai samu gyara mini dakin ba. Alhaji ya ce mishi, "Na gyara Baba kullum cikin dare nake bude dakin in shiga in yi ta gyarawa sai Asuba ta ksua in fito, to jiya har kayanta na bayar a wanke saboda kura, nan dawo da su yanzu ka tura ka gani komai tsab yake cikin tsabtarshi" Baba ya yi murmushi ya ce, "Lallai kana so matarka ta dawo, to za ta dawo sai ka yi ta hakuri ka 112 hada su dukansu ku zauna lafiya." Bayan fitar shi ne baban ya kalleni ya ce mini, "To yaushe za ki koma dakin ki Zuwaira." Na cc sai karshen wata. Ya yi maza ya ce, 'A'a kul na ji kin yi wannan maganar yanzu dai yau ki kara lallenki ki tusashi ya yi sheki da safe sai ki je wurin Bilki ta yi miki kitso tun da dama ita ke yi miki da daddare kuwa sai in kirata in sata ta raka ki dakin ki, nima in ji dadi, don dama a kan dole na ke rike da ke tun da na san ba ni da 'yancin rike mishi matarshi. Ke matarshi ce yana kuam son ki fiye da komai, don haka ko bayan raina na yi miki umarnin ki yi hakuri da shi, ki kuma ragewa kan ki kishin da ke damunki." Na ce mishi to. Washe gari ko fita Alhaji bai yi ba ya makale a dakin baba watakila gani yake tamkar in ya fitan wani dalili zai sa baban ya fasa maida ni dakin nawa. Da daddare na yi wanka na yi kwalliyata cikin sabuwar atamfar da ya saya mini na ci abincina ni kadai, don dama ya fitar da ni cikin cin abincin taraiya. Yaya Bilki ta zo kamar yanda ya yi mata umami ta rakani dakina. Ranan na samu Alhaji cikin doki da zumudin samuna tamkar dai a ce ranar ne ya fara sanina. Zan iya cewa kusana wannan lokacin ne muka yi amarcinmu da Alhaji, don a farkon aurenmu shiriritar kuruciya ta hana ni in sakar mishi komai nawa ya morewa aurenshi. Rannan ina zaune wurin baba da hantsi muna 113 hira atishawa nake ta yi, sai ya kalleni ya ce mini, Wa ya sani ma ko wani rabo ne ya tunkaro ya sa Bello ya nacewa komawarki a lokacin nan Na yi murmushi na ce mishi, "Ba komai baba. Ya ce, To ki yi hakuri ko wata ta zo ta haihu sai ki tuna kin haifa kafin ita, kar kuna ki yarda ki dagawa mijinki hankali, kar kuma ki lura da abin da na yi mishi a kan ki ki ce z8 ki wulakanta shi, ki girmama shi, ki guji bacin ranshi, ki sani baki da wanda yafi shi. Ban kuma bashi ki ba sai da na san cewa shi ne wanda zai iya rike mini amanarka, ko bayana kin ji ko ba ki ji ba?" Na ce mishi na ji baba. Alhaji ya yi juyin duniya ya zauna da Karama lafiya abin ya gagara, saboda ba yanda take so ya yi mini yake yi ba. Gaba daya hankalinta ya tashi, ita da take sa ran za a maidani wurin dangina hakan bai yiwu bas, gashi kuma ba zato ba tsammani na dawoo dakina. Hankalin mijina kuma ya dawo gare ni, lokacin ne ta ganc a wancan lokacin ni ce na taimaketa ita da mukarrabanta, har suka samu suka sha gabana a wurinshi, yanzu kuwa na sa hannu biyu na karbe shi na kuma janye daga jin takaicin aurenshi, na yi niyya zan kyautata zamana da shi ne kawai, don na riga na kara sanin ba ni da kowa sai shi in kuma baya tare da ni to ba karamm tozarta zan yi ba wurn 'yan'uwanshi, masu son ganin iyakata. Babu yanda ba a yi ba a hadani da shi abin' ya gagara, kullum ya shigo dakina na san yanda zan yi in watstsakar da shi 114 daga duk wata damuwa da ya zo da ita, don haka in yana dakin kowanc lokaci cikin murmushi za ka ganshi. Ni da Karama kuwa ko kallon inda take ba na yi in gari ya waye na ce mata ina kwana? Sai kuma gobe in za ta Wuni tana zage-zagenta kuwa ba zan kulata ba. Rannan dai aka wayi gari a kan dole a ka ce Karama ta yi bari tun da ba a samu an yi dambe da ni ba, na ki yarda gashi kuma a lissafi ciki ya kai watanni tara. Jini ya yi ta gudu a tsakar gida ana kwara ruwa, ana wanke shi. Alhaji ya shigo gidan fuskarshi a daure alamar dai bai ji dadin 6arin da aka je aka ce mishi ta yi ba. Yana tsaye a tsakar gidan ya fara tambayar matar yaya babba wacce dama ita ce uwar dakinta. "Ina dan yake?" Ta yi maza ta soma yi mishi bayani. "Wane da ake maganar shi, wannan ciki da ya rididdige ya fadi a hankali ba a sani ba, ashe an dade da sa mata hannu a kan shi." Maganar tata ta kara fusata shiga sakin maganganu. Ina jin haka na yi maza na kulle kofata na tafi wurin baba na ba su wuri. Ban dawo ba sai da ya zo can din ya same' ni. Saanan muka dawo tare. Sati guda bayan nan aka zo aka tattara Karama aka tafi da ita bisa dalilin wai ansa mata hannu cikin ta ya lalace, amma ba a kula da ita ba, ba a kuma. dauki wani mataki ba na yin maganin hakan. Baba ya 115 ce ai ba ni ce na sa mata hannu ba, sh1 ne tun da ni kam wa nake dashi da zai yi mini wannan aikin? Sun yi zaton Allah zai yi ta zarya a kanta, su ma su ja mishi rai, kamar yanda suka ga baba ya yi mishi, shi kuwa sai ya yi banza da su. Rannan ina zaune wurin baba ina gyara mishi farce, sai ya ce mini, "Ni kuwa wata shawara nake so mu yi da ke duk da dai na san kishinki yawa ne da shi" Na yi murmushi na ce mishi, 'Gaya mini baba." Na yi zaton zai yi mini maganar dawowar Karama ne sai na ji ya ce, 'Shekaran jiya Liman ya zo wurina ya gaya mini cewar 'yarshi za ta fita taka ba gobc, shi ne nake tunanin ko zan gaya wa mijinki ya je ya ganta ne? Kin ga yarinya ce karama, bab ia fi Karama ba. Sannan tana goyon danta na fari, ga wadannan fitinannun mutanen da kike tare da su ba za su bar ku ku huta ba ke su tasaki a gaba da fitina, shi su tasa shi a gaba da karyar ciki. Na ce ko zai aurota ne? In ya yi sa'a sai ta haihu ke ma in kuka zama ukun za ki dan samu saukin abubuwa in ba ki shirya da wata ba, za ki shirya da wata." Ban yi musu ba na ce mishi to Baba. Kwana uku ne, kawai bayen nan sai aka yi daurin auren Alhaji da Maryam, don shi bai je ganinta ba, da Baba ya gaya mishi kawai sai ya ce ba sai ya je tadi ba, a sanar da liman kawai a ji abin da zai fadi. Ana gaya mishi kuwa ya ce gobe a dawo daurin 116 auren. Labarin auren Alhaji ya zamo kwaram a gidan nan gaba daya hankula suka tashi, saboda babu wanda ya yi zaton hakan, su suna jiran ya zo biko ne su gindaya mishi sharudda, wai har suna cewa ai nimna ba daga tafiyata ya kidime ba, sai da baba ya shiga ya fita. Sai kwaram suka suka ji zancen aure. Ranar kuma da yamma baba ya yi amfani da taron da aka yi na murmar auren da Alhaji ya kara ya tara gaba daya ya'yanshi maza da mata, ya kuma aika aka kira mishi aminanshi da sukai saura ciki har da liman. Gaba daya sai da aka taru. Sannan ya ce a dauko mishi abin rubutu, a rubuta. A ka je aka dauko abin rubutu ya mikawa Yayan Tudu ya ce, "Dukkan ku ku shaida don shi ne dalilin da ya sa na tarakun ku zamo shaidu kan cewar ko bayan raina wannan daki nawa da nake ciki da kuam fadamar rakena da ke kofar yamma basa cikin abin da magada za su gada na dukiya na bai wa Zuwaira su, daga yau su din mallakinta ne, na kuma bata šu ne tun ina raye, saboda na san ba ta daga cikin wadanda za su ci gadona, gashi kuam ita din 'yata ce da amana ya bani." Ya sake nuna wata saniya da danta tare da wani bijimi ya ce, "Hakan nan wadancan shanun nats ne, sanda mahaifinta ya kawo mini ita ya bani dukiyarta ya ce in rike in loakcin hidimar aurenta ya zo a yi mata da su, don haka babu komai nawa cikin 117 kudin kayan dakinta da kudinta na yi mata hidima, ni dai na dauki nauyin ciyar da jama'a ne kawai a lokacn tun a sannan kuwa na gaywa wasu daga cikin ku hakan. Bayan an gama bikin ne na gayawa Rabi cewar ga sauran kudinta da sukai saura sai dai babu yawa, ta ce mini a sayo mata tunkiya a daure mata. To da ta yadunc aka sayar da su aka sai mata karsana a kan idonku ne kuma ta haifi wannan ta yaye shi, ta kara wannan. Na roke ku kar ku zalunccta a bayana, ita ma yar uwarku ce don ba ta da kowa sai ku." Daga Karama har masu tsaya mata babu wanda ya furta wani abu kan wannan kyauta da baba ya yi mini, don sun riga sun ga abin da ya firgita su. In da da nc kuwa kafin auren Alhaji baba ya yi mini wannan kyautar da sun ce ya yi bambanci tsakanin matan danshi a wannan lokacin kokarinsu bai wuce Karama ta dawo katin tarewar amarya ba, wacce aka dibar mata kwana bakwai kacal. Shi kuma Alhaji ya ce ta yi zamanta tukunna sai amarya ta zo ya ga kamun ludayin zamana da ita kunna, don yana son gane waye mai fitina a tsakanina zaman. Baba ne ya ce a'a kar ya yi haka ya barta ta dawo dakinta shi dai kawai ya zama tsayayye kan lamarin gidanshi. Ya ce mishi to. Karama ta dawo da kwana biyu. Ita ma amarya ta iso ta kuwa iso cikin matsananciyar gata, ita ma dai kam mai dangin ce. Da yamma kafin zuwan nata baba ya kirani ya ce mini, "Wani alheri nake so ki yi mini." 118 Na ce mishi, To baba." Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, "Hakuri za ki yi ki dauki nauyin da yake kan ki duk da ke din kin yi wa hakan kuruciya, ita wannan amaryar liman ya

Chapter 7 of 9