Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 9
a dakinsu. Ina shiga na Tsugunna ina sauraron shi ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, Rabi kina sanin saura kwana nawa ne bakinmu kuwa?" Na zuba mishi 1do ina kallon shi, na ce, To 52 mene ne?" "Ban taba ji kin ce mini komai ba." Na kalle shi na ce mishi, "Ni yanzu ai ba biki ne a gabana ba, muhimmin abu a wurina shi ne in san asalina, in san waye mahaifina. Sannan ma ni yanzu auren naka baya gabaná, don na gane matsala zai zamo mini mai girma, saboda haka na ce zan ga baba in roke shi in ya zo daurin auren ni ya bai wa Yaya Junaidu kai ya ba ka Rahama ko kuma.." Da sauri Yaya Almu ya shiga cewa, "Ba ki da kai Rabi, ke ba ki da hankali, to in baki sani ba ma yau in gaya miki ke da Junaidu babu aure a tsakaninku." Na yi turus ina kallon Yaya Almu, yayin da shi kuma ya riga ya fusata da jin cewar zan bukaci a canza mini shi. Na ce mishi, "Yaya Almu... Bana so kar ki gaya mini komai, je ki ki bukaci baba ya eanza miki ni, ni ba na bukatar canji a kan ki ke nake so, ba kuma zan bukaci a canza mini ke ba. Ni tun kina 'yar jaririyar ki na ke son ki ban kuma taba dainawa ba. Je ki ki bukaci canji a kaina, in ba ki yi haka ba ai ba zan gane irin kiyayyar da kike yi mini ba." Na soma yi mishi kuka, saboda ganin irin fadan da yake ta yi mini. Na ce, Kana sona tun ina yar mitsitsiya, amma kake rerawa Aina'u wakoki a gabana? Ko ba ina nan a gidan nan ba kuke musayar Wasiku a tsakanin ku? Ko ban sha ganin wasikunta a 53 dakin nan ba? Ba ka sha jaddada mini irin son da kake yi mata ba? Don me ba zan nemi canji a kan ka ba? Shi na taba jin shi yana ambaton sunan wata budurwa ne? Kai ne kake son Aina'u kake son Uwale, na ga abin da Aina'u ta yi mini a kan sonka da take yi, ita ma 'yar uwata kenan saura Uwale, ita kunma ban san wanda za ta yi mini ba, in mun gamu. Cikin nutsuwa ya soma yi mini magana, "In kin ji ina yi wa wata maka Rabi tsokánarki kawai nake yi, don in lura da kishinki a kaina, ba zan yi mik musun kina ganin wasikunta anan ba, amma zan yi miki musu idan kika ce kin taba ganin wasikuna a dakin ku. Maganar Uwale kuwa ba ni da wata Uwalen da ta wuce ki Rabi, ni ke ce Uwalena in kin yarda da wannan bayani da na yi miki to ina so ki kwantar da hankalinki ki toshe kunnenki ki daina sauraron duk wani zance da wani zai gaya miki kina nufin in ni zan rude ki Umma ma za ta rude ki? Har Baba ma ya yi miki hakan? Na yi maza na ce mishi, 'A'a. "To ji ki ki shirya maza ki zo mu fita ki yi mini rakiya." Na yi shiru kawai na mike na fita. Na zo na samu Umma zaune a feionta na zauna rnima kusa da ita na kalleta na dan yi murmushi, don ta san a cikin kwanciyar hankali nake. Ta sake kallona cikin nutşuwa ta ce, 'Mene ne Adawiyya? Na ce, 'Ba komai Umma so dai kawai nake yi 54 in tambaye ki ni waye ma ya haifi Yaya Junaidu? Babu wata damuwa ta ce mini, "A'a yau kuma ba ki san uban Junaidu ba?" Na ce, "Eh Umma gani nake kamar ba hakan ba ne mantawa na yi." To Alhajin Tudu ne wan Alhaji, wanda suke uwa daya, uba daya amma akwai mace a tsakaninsu ita ce yaya Lami, mahaifiyar Aina'u. Wannan dogon bayanin da na jaddada miki ya gamsar da ke?" Na ce mata, "Eh Umma." Na dan sake kallonta na ce mata, "To nima Baban Tudun ne ya haife ni? Ta girgiza kai nuna alamar a'a. Ta sake kallona cikin murmushi tare da sansanyar ajiyar zuciya. Sannan ta sake kallona cikin nutsu wa ta ce, "In Alhajin Tudu ne ya haife ki da wani wanda ya isa ya ce ke ba 'ya ba ce a gidan nan?" Nan da nan na ga kuma ch haka ne. Na sake kallonta na ce, "To Umma gaya mini abu daya ni 'yar ki ce?" Ta yi maza ta ce mini, "Kwarai da gaske." Na sake cewa, "Ke kika haife ni?". Ta zuba mini ido cikin nutsuwa ta ce, "Kina tantamar hakan ne?" Na ce mata, 'A'a. To amma Umma...." Ta ce mini, "Ke nake sauraro." Na ce,"Nuna mini nankarwar ki." Ta yi maza ta ce, 'Yanzu kuwa." Ta sa hannu ta kwaye shimin da ke jikinta.. 55 Gasu nan rada-rada, kwance a kasan cikinta, har zuwa gefen cinyoyinta. Cikin zuciyata na ce tabbas wannan nankarwar da kan samu ne ta dalili haihuwar da ba ta halittar ba, Dadi ya kamani cikin zuciya na tabbata Ummana ita ce ta haifen. Na kalleta na yi murmushi na ce, Umma." Ta tayani murmushin ta ce, 'Mene ne Adawiyyah?" "Ni tun da dai ke kika haifen to magana ta kare komai mam zai biyo baya to ina ganin shi din mai sauki ne, zan iya hakuri in aka ce ba baba ne ya haifen ba, amma ba zan iya yin hakurin akan ki ba." Umma ta sa hannu ta jawo ni jikinta, na kwantar da kaina a gefen kafadarta cikin murya mai sanyi na ce mata, Ina jin mamakin abubuwa da suke fitowa kwanan nan a kaina Umma, na yi iyakacin tunanina na kasa gano dalili a ce wai aure ya haramta tsakanina da yaya Junaidu, ya kuma halarta tsakanina da yaya Almu. Wannan ba abin mamaki ba ne?" Ta yi maza ta bata rai ta ce, 'Eh abin mamaki ne sai ki je ki.yi ta bincike kina jiwo abin mamaki iri- iri." Na ce, Ba bincike ba ne Umma..." Ta ce, To wannan magana ta ishen haka." "To Umma." Na ja bakina na yi shiru. Shirin biki na sosai da sosai Umma ke yi. In tsaya kwatanta lamarin ma bata lokaci ne, a kowanne 56 lokaci cikin biki take, a kowane lokaci kuma a kan fita take, saboda al'amuran da ta ke gudanarwa ita da kawayenta guda biyu wadanda suke sune na hannun damarta, suka tafi Dubai, don sayayyar kayan dakin amare, wato Hajiya Hauwa da kuma Hajiya Furera. Ina kwance ni kadai a dakinta, saboda tafiyar tasu sai na ji kadaici ya dame ni na tashi na jawo suwaita na dora kan doguwar rigar da ke jikina na fito waje ina tafiya ni kadai nufina in isa wurin baba maigadi in zauna in taya shi hira, sai na hango yaya Junaidu yana tsaye jikin kofar motarshi da ke bude hankalinshi kuma ya tafi wajen kallon wani abin da ke zaune cikin motar. Da sauri na nufi wurin nashi, don ganin mene ne? Ina isa wurin na gaishe shi ya dago kai ya kalle ni cikin murmushi ya ce da ni, "Adawiyyah kin fito ne?" Na ce mishi, "Eh." To kun gaisa da Rahama ne?" Lokacin ne na lura ashe ita ce a cikin motar ita yake yi wa wannan karkacewar da na ganshi yana yi. Daga inda nake tsaye na ce mata, Sannu Anti Rahma." Ta amsa cikin wata irin muryar da ban taba sanin tana da ita ba. A zuciyata na ce a'a har yaya Junaidu da aka girma a gabanshi sai,an yi mai wannan kashe muryar? Na dan yi murmushi, Yaya Junaidu ya kalleni ya taya ni murmushin ya ce, 'Ai yan matan dukansu tuni suka watstsake suka shiga hidimar bakin su in da za ki leka dakin baki yanzu da za ki samu 57 Alna'u da Basira suma samarinsu sun zo. Kabiru da Rashida kuwa tun safe suka bar gidan nan, Mustapha ne shi kadai ga shi can a bayan motarshi yana zaune ko za ki je mishi hira ne?" Na yi kamar in ce mishi to, sai kuma na ji ina Son komawa wurin mu. Na ce mishi, 'A'a Yaya Junaidu." Na yi ma Anti Rahma sai da safe na juya na koma wurinmu. Ina shiga sashin Umma na ji jikina ya bani an shigo wurin. Na ja na tsaya ina kallon kofar falonta da ke rufe kamar yanda na bar shi. Shiga sashin Ummana ba komai ba ne, don wuri ne na mutane ko tana nan ko ba ta nan. To amma wannan karon sai na ji kamar ba irin shigar da aka saba yi ba ne. Ina cikin wannan tsayuwar na hangi inuwar wani ta bayan dakinta. Da gudu na fita ina ihun barawo! Barawo!! Da iyakacin karfina. Gaba daya samarin gidan manya da yara dama duk wani wanda yake cikin gidan aka firfito. Yaya Almu ya bai wa Baba maigadi umarnin rufe get kar a bar kowa ya shiga ko ya fita. "Barawo ki ka ce Adawiyya?" Yaya, Junaidu ya tambayan jikina yana bari na ce mishi, "Eh a sashin Umma na gan shi." Shi da Yaya Almu da yaya Harnza suka taso ni a gaba saura kuma suka ce su tsaya a nan, don kar wani ya ce zai zo ya fita, tun da katangar gidanmu dai babu mai iya tsallake ta. Muka isa sashin Umma na ja na tsaya daga nesa na nuna musu ta inda na hango 58 inuwar suka je suka duba suka dawo, suka ce babu kowa. "Anya ba tsorata kawai kika yi ba Adawiyyah?" Yaya Almu ay ce, "An shigo ga alamar kafa a nan," Gaba daya suka sake zubawa wurin ido. A hankali suka rinka bin takun suna dubc-dube zuwa can yaya Junaidu ya ce, Zo nan Mustapha ba a yi wani abu a wurin nan ba? Da sauri ni da yaya Hamza muka karasa wurin na su, yaya Almu ya kalli Hamza ya ce mishi, "Yi gudu ka kira mallam tare da baba maigadi, su Musa kuam su tsaya a get kar su bar kowa ya fita ko waye shi" Su baba maigadi da maiam suka iso. 'Malam ba a yi tono a wurin nan ba?" Yaya Almu ya tambaye shi. Ya ce, Eh to da alama dai kam an yi." Baba maigadi ya co, Eh to ai da akwai baki a gidan shekaran jiya kun tafi kai Hajiyá airport su kuma aka shigo da su." Yaya Junaidu ya kalle shi ya ce, 'Amma shi ne ka yi shiru ba ka fada ba'?" Ya kara rage murya ya ce, 'Ai na gane an saba kawo irin su, su gama, kwanakinsu su fita, ita kuam Hajiya nan ba mai yarda a rinka kawo mata irin wadannan laburan ba ne." Yaya Almu ya nemo shebur ya shiga kwashe kasar wurin. Tuno sosai aka yi aka tarar da wata 59 katuwar kwarya. Yana daga kwaryar sai ga dan kunkuru mai rai a kife. Gaba daya wuri ya dauki salati. Ni kam kuka na kama yi. Ya sa hannu ya dauko dan kunkurun wanda ni tsoro ya hanai kare mishi kallo, balle in ga abin da ake cewa an rataya mishi. Malam ya karbi dan kunkuru shi da baba maigadi suka tafi bayan sun jaddada muhimmancin a yi shiru kar a tada maganar. Yaya Junaidu ya kalleni ya ce, "Mu je can ki kwana a wurin mu. Ita ma baba Talatun da take tayaki kwana ta kwana a wurin su kawai a rufe nan din." Na ce mishi, "To." A dakin su Yaya Almu ina kan katifarsu su kuwa hirarsu suke yi a kan kujera. Farkawa kawai na yi cikin dare na ga ni kadai ce a dakin, amma ban tsorata ba don gaba daya wannan sashin nan samari ne. Ina kwance idona biyu ina tunanín abin da ya faru sashin Umma. "Yau me ake nufi da wannan abin da aka yi? A kashe ta ko a yi mata me? Aurena da yaya Almu ne kawai ya jawo hakan ko kuwa dama can ana yi sani ne kawai ban yi ba?" Hawaye suka suka yi ta zubowa a idona, saboda tausayinta da ya kamani, abin da na sani shi ne Umma zaune take zuciya daya da kowa, amma kuma ita ake zargi wai mai magani ce ta mallake baba, sai yanda ta yi da shi. Ina cikin haka na ji kamar ana magana a waje. Da sauri na.tashi na sanya suwaitar da 60 hular sanyina na fita. Wurin baba maigadi na nufa, don can na hango mutane a tsaye. Wasu mutane ne su uku sai zazzare 1do suke yi, alamar rashin gaskiya, shi kuwa baba maigadi yana zaune hankalinshi a kwance. "Ba zan bude gidan ba, sai gari ya waye yau ma," Umma Karama ta iso wurin tare da wani alamar kiranta ya je yi, ganina a tsaye ya sata ta yi wani iri alamar rashin jin dadi. "Maigadi ka ce ba za ka bude musu ba? Bayan ni na ce ka bude musu?" Ya ce, 'Ki yi hakuri Hajiya Lamido ne ya ce kar a bude sai gari ya waye tukunna. Ta daka mishi tsawa, 'Na ce ka bude musu da umanina da na Lamido wanne ne gaba?" Yaya Almu ya fito daga dakin baba maigadi, ashe dama yana ciki ya ce mata. "Ki yi hakuri Umma ba umarnina ba ne, umamin baba ne ya ce kar wanda ya shigo mishi gida bayan karfe goma, kar kuma a bar kowa ya fito bayan wannan lokacin. Yanzu karfe biyun dare ne an zo ana cewa a bude mishi gida kuam su wadannan mutane Idan gari ya waye zan hada su da hukuma nc, don su amsa tambayoyi kan abin da suka shigo mana gida babu izinin mu, suka keta mana haddin gidan. Bayan haka suna cikin gidan nan dazu aka yi ihun barayi, duk wani wanda yake cikin gidan nan ya fito, amma Su ban gan su ba, don haka ban yarda da su ba." 61 Umma ta soma fadin maganganu. Ya ce mata, "Ke uwata ce Umma, don haka na roke ki ki yi hakuri ba zan yi komai don cin mutuncinki ba, abin da kike tunani a kaina kuma ba haka ba ne, ni na kowane a gidan nan duk wanda yake ciki nawa ne, ba ni da wani bangare in kin ga ana yi miki wani abu wanda bai yi miki daidai ba gaya mini na yi alkawarin zan yi miki maganin abin ko waye mai yi mikin, kai ko baba ne ki gaya mini, don shi mai karbar nasihar na kasa da shi ne." Yaya Kabiru ya fito da moto ya zo ya tsaya. "Su shiga mu tafi." Da sauri ta ce, "Ina?" Yaya Almu ya ce, Police Station za'a kai su, don su yi bayani." Jikin Umma ya yi matukar yin sanyi ta kira yaya Almu yabi bayanta suka tafi. Nima na koma daki na kwanta, sai dai ba barci na yi ba, har gari ya karasa wayewa, idona biyu. Sai da gari ya waye na fito bayan na gama komai na kimtsa sashin Ummana na nufa don in ga abin da ake ciki. Yaya Almu na samu a wurin ko'ina a bude yake gaba daya kayan sashin Umma an. yi waje da shi. Cikin nutsuwa ya kalleni ya ce mini, "Kin karya ne?" Na ce mishi, "Eh." To ki koma can, nan ba ki ga ana aiki ba?" Na koma na je na gaida Umma Karama, na kuma tafi dakinsu Baba Talatu na hau gadon ta na 62 kwanta. Na kwanta muna hira da ita ta ce mini, "Au dama can haka ake zaune in ba a binne wannan ba yau gobe za a binne wancan. Na da bai yi komai ba, ai na yanzu ma ba zai yi ba." Na ce, 'Haka ne." Muka yi hirarmu. Ban fitò ba sai da yaya Almu ya aiko ya ce a kira ni. Na same shi a motarshi cikin kwalliya sosai, ga kamshin shi mai dadin ji. "Shigo mana unguwa,za ki raka ni." Na yi maza na shiga, saboda ina nson tambayarshi labarin mutnaen nan. Muna tafiya muna hira na ce mishi, "Yauwa yaya Almu." Ya ce, 'Na'am Uwale." Na yi maza na ce mishi, "Kai! Kai!! Yaya Almu gaskiya ba na son wannan sunan ko baba ma Uwata yake kirana ba Uwale ba." "To, to shi kenan Adawiyya." Na ce, "Yauwa. To mutanen nan nake son jin yanda ká yi da su." Bai kalleni ba, ya ce, "Ina ruwanki da maganarsu? Saura kuam ki ce za ki gayawa Umma abin da ya faru, don ke baki da wayo ba ki san abin da za ki rinka yi kina kwantar mata da hankali ba, kin dại san ba dabarar ki ba ce yasa kika ga wadannan nutanen za su iya yin abin su su gama babu wanda ya gansu, musamman da yake kin fito ne aka shiga, don ba a yi zaton komawarki a wannan lokacin ba, to 63 kuma da sun bari kin yi barci ma da za su shiga Su yi abin su, su gama babu mai ganinsu, amma saboda Umma ba ta da alhakinsu ita tana zaune da komai zuciya daya shi ya sa duk abin da ake yi babu wanda ya taba samunta. Ai kin ji Baba maigadi ya ce irin wadannan bakin sun saba zuwa ko? Na ce mishi, "Eh." To kar ki yi mata maganar na kuam san su Junaidu ba za su yi mata ba, yanzu dai za mu je ne ki zabar mata kayan da za su dace da wurin nata, don na sa an fitar da komai a mayar mata da sababbi." Na ce mishi, "To." Muna tafiya yana jaddada mini dole ne in zama mai hakuri kan al'amu masu yawa in gani in ki ji in ki gani, ko a gabana a ka yi abu in ba a ce in ganni ba sai in kawar da idona. "Da na ki da wanda ba naki ba, duk ki maida shi naki. Yanzu kamar Umma kina iya gane nata da wanda ba nata ba? Babu wani wanda bai da alaka mai karfi tsakaninshi da Umma Karama, saboda ita kanwar Baba ce, amma hakan ya hana su son Umma? Bai hanan su ba ko ba su sonta kuwa dole su hadiye su maida ita abokiyar mu'amallar su, saboda halinta, masu kin Umma na wajen gidan ne sune masu cewa wai abin da ya sa in ka zauna a gidan dole ka so ta, ko ka rinka jin maganarta wai asiri take yi a gishin miyar gidan ko?" Ya waiwayo ya dan kalleni cikin murmushi ya 64 ce, "Nima ki zo mini da irin wannan gishin Rabi. Na taya shi murmushin kawai a zuciyata na ce, ashe shi ma ana fada yana ji. Yana kallon hanya bai kalleni ba, ya ci gaba da magana. "Da kike ganina na fiki sanin Umma, na fiki sanin sirrinta, domin nine na santa tana ganiyar kuruciyarta, na san ta tun loakcin da kishi yake yi mata zafi, na santa a lokacin da ake yi mata abu ranta ya baci ta yi.fushi, ba yanzu ba da komai aka yi mata take kawar da ido akan shi, in da tana da dabi'a ta bin masu binne-binnen nan fo da nati kowa sanin hakan. Na kuam gayawa Umma Karama ban boye mnata ba cewar inda Umma tana yin irin abin da ake yi mata, to da an yi nasara a kan ta. To amma ba ta yi, don haka babu abin da zai faru da ita, sai alheri; don shi ta sani take kuma yi." Cikin kwanaki biyu kacal aka yi wa sashin Umma gyara na ban sha'awa, harabar wurinta gaba daya tiles ne masu tsadar gaske, sun yi matukar kawata wurin babu sauran a y1 mata biso a wurinta. Gaba daya furannin wurin babu Su, sai yan kadan da aka kawata wurin da su ta hanyar aj1yewa kawai, amma ba shuka ba. Hatta labulayenta sabbbi ne farare Sol, marasa nauyi. Sai kuma aka bi, bayan su da masu ruwan sararin sama. Kayan fafon gaba daya irin kalarshi kenan, bai yiwu ma in tsaya kkwatanta kyan da wurn Ummana ya yi. Sai da aka gama gyara komai. Sannan yaya Almu ya rufe shi. Ni kuwa na 65 koma da kwana a dakinmu tare da su Aina'u ko ba komai dai na lura da gani har su mun ji jiki a damben da aka yi, don kuwa a yanzu ba sa yi mini irin kama- karyar da suka saba yi mini. Na kuma lura na gane Aina'u ba karamin son yaya Almu take yi ba, duk da zirga-zirgar saurayinta a wurinta ta kasa kawar da kai daga al'amarinshi, ko wayata ce ta yi motsi sai ta kasa kunne ta ji dawa nake magana? Ni kuwa dana ganetaa in tana wuri ya yi mini magana sai in sake mu yi ta hirarmu mai dadi, ina kyalkyalewa da dariya, sabanin in a gaban shi na ke sakin baki da nake yi in yi ta gaya mishi maganganu masu dadin ji, in kashe murya in yi ta gaya mishi irin son shi da nake yi da darajojin da yake da su wadanda suka bambanta shi da sauran maza. Ya sa babu dama ya yi minti talatin bai yi mini waya ba, sai dai in wani aiki yake yi, bai sani ba ni don in kular da Anti Aina'u mai nuna kishi a fili nake yin hakan. Rannan Ummana za ta dawo tun safe yaya Almu ya bude wurinta. Baba Talatu ta shiga ta gama gyara komai nima ina tayata, muka gama na faffesa turararruka kala daban-daban. Sannan ya sake rufewa Nima na je na yi wanka, muka yi shiri ni da shi muka tafi dauko su a airport cikin motar da ake dauko baba. Umma tana zaune a falonta bayan sun gama cin abinci, sun huta an maida kawayenta gida ta kuam gama gaisawa da jama'a ta kalle ni cikin murmushin dake kara bayyanar da farin cikinta ta ce mini, 66 Wannan dai aikin Babangida ne?" Na ce mata, "Eh Umm." Kamar in gaya mata abin da ya faru wanda ya yi dalilin da aka yi mata aikin. Sai kuma na tuna kashedin da ya ba ni na cewar ba wai zai 6oye maganar ba ne, don yana son a cutar da ita, shi mai yin komai ne wajen ganin ya kareta daga kowacce irin cuta, sanin darajar Umma wurin yaya Almu ya sa nima na kame bakina, na yi shiru, na bar ta ta yi ta farin cikinta. Rannan muna kwance a kan gadon Umma da daddare, ko wurin yaya Almu ban yarda na je ba, saboda dokin dawowar Ummana, hira mai dadi muke yi. Maganganun da suka shafe mu muke yi cikin hirar ta mu ce Umma ta yi mirii maganar da ta sanya ni yi mata tambaya. Bayan ta kai karshen zancen nata, cikin nutsuwa na ce mata, "Umma!" A hankali ta ce mini, "Mene ne ya faru Adawiyya?" Na ce mata, "Kin taba gaya .mini cewar ke din baki hada komai ba da baba a mu'amalla ta zumunci, amma kuma gashi a yau kina ba ni labarin gadon da kika ci a gidan su Baba." Ta miko hannu tana shafa hannuna, dana shagala kan wuyanta ta ce, "Kai Adawiyyah wane irin taushi jikinki ya yi haka?" Na ce mata, Yaya Almu ne ya canza mini 67 kayan shafa." Ta yi murmushi ta ce, "Bari yau in dan baki labari na dan kadan tun da kin girma kin yi hankall. kwanaki kadan ne kuanm suka rage mana za ki tafi gidan mijinki bai kamata a ce ba ki san komai a kan al'amarinki ba, ko da yake dai mijin da za ki aura ya san komai a kana, babu wanda ya san sirrina irin shi, shi ya sa nake kara son aurenku don kuwa mutumin da ,nake so fiye da kowane Alhaji zai bai wa ke wannan alheri da Alhaji ya yi mini ya kara bayyanar mini da muhimmancina a wurin shi. Na ce, "Haka ne Umma, to ba ni labarin na ki in ji?" Ta ce, 'Yanzu kuwa." Tana yin gyaran murya ta ce mini to. Ni dai ko ban gaya miki bab kin san sunana Zuwairiya, hakan nan na sha gaya miki cewar ni din ban taba sanin mahaifiyata ba, ina dai kawai na san ina matukar kama da ita, abin da babana ya gaya mini kenan mahaifiyata mai hakuri ce kwarai. Na sha jin shi yana jaddada hakurin nata a lokuta daban-daban. Babana ya yi abota ne da mahaifinsu Alhaji suka yi mu'amalla a kan harkar dukiya na dan lokaci kadan, sai suka rabu, saboda dama abotar ta su a kan harkar sana'a ce garin su ba daya ba ne. An yi hakan ne kumna shekaru masu yawa katin a haife ni, amma har na yi wayo baba yana bani labarin amana irin ta mallam Mai Hadisi, samun irinta wurin mutanen 68 wannan zamani da wuya Bayan rasuwar mahaifiyata baba bai sake aure ba, na sha jin aminanshi suna ce mishi mallam Aliyu ina amfanin wannan zaman nan ka a haka? Shi kuwa ya kan yi murmushi ya ce inda sauran auren sai wani dalili ya sa yi. Mafi yawancin sanin da na yi wa baba na yi mishi ne a kwanakin da lafiya ta yi mishi karanci, watakila saboda yawan shekaru, watakila kuma saboda kusantowar wa'adi. A irin hirarrakin da ya kan yi mini ne a wancan lokacin ya sanar da ni nufin shi na kaini wurin malam Mai Hadisi ya bayar da amanata a gare shi, sąboda ya san shi din zai rike ni kamar 'yar cikin shi, koma fiye da hakan; don bai taba ganin mai amana irin ta shi ba. A irin soyayyar da na san Babana yana yi mini nan kuma ji shi yana cewa zai bada rikona a wani wuri sai na tsorata na yi ta kuka ina rokon shi ya bar ni in zauna tare da shi: Ya kalleni cikin tausayawa ya ce "Ki yi hakuri kamar yanda nima na yi, ina jin tsoron kar in mutu in bar ki a nan ba ni da wasu 'yan'uwa a kusa tun da ni ba mutumin nan kusa ba ne. Sannan ba zan 1ya bada,amanar ki wurin kowa ba in ba shi ba, don ko na yi hakan hankalina ba kwanciya zai yi ba. Mai Hadisi shi ne kadai mutumin da na bai wa ajiyar dukiyata a lokacin da zan tafi kasarzmu na je na dawo na same ta ko kwanceta bai yi ba, balle ya taba bayan na je na yi shekaru uku maimakon watsa shidan da na ce mishi zan yi, sauran wadanda na bai 69 wa ajiyar duk sun cinye, wasu ma cewa su y1 ban ba su komai ba. A yanzu na riga na tsorata da rashin lafiyar nan don na san halin ciwon da ke

Chapter 4 of 9