Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
Alhaji mai kyau ne, gashi dama na riga na saba da aiki na kuam iya girkin ko da yake baba Rabi tana cewa wai bai war girkin ne da ni, don komai na yi mai dadi ne. Kullum zan gama girkina da wuri in na gama in kai wa kowa na shi, na su Alhaji a dauka a kai sashin yaya babba, don a can suke haduwa su ci. Nima in je mu ci da matan gida bayan na kai wa su baba na su. Muna gama cin abincin, zan dawo in zo in juye ruwan wankana in yi, in yi kwalliya saboda Alhaji ya hanani zama hira a cikinsu, In ji shi wai duk sun haife ni bai yarda in rinka wani hira da su ba, tun da dai sun ce mu ci abinci tare, to muna gamawa in kwashe kwanuka in tashi. Hakan nan kullum na gama girki in yi wanka don bai son warin hayaki, na ce mishi to. Wadannan abubuwa. biyu sai suka kara tsananta bakin jini na a wurinsu, wai ba na zama a cikinsu na dauki kaina daban, gani nake tamkar na fi su, bayan ni din ba komai ba ce in ban da daure mini gindi da baba ya yi, ya fifitani akan kowa, ya sa nake raina mutanc. Kuma wai'ni na cika son miji fitina ce da ni, ba na barin shi ya huta kullum ina makale da shi, don fitina ma wai kullum sai na yi wanka da daddare. Kan wadannan maganganun na su sai na rinka kin yin wankan dare, nan abin ya rinka hadani rikici da Alhaji har rannan ya kai ni kara wurin baba. Na je wurin baban hira kamar yanda na saba yi 87 kullum, don ban taba fasa zuwa mishi hira ba. Kullum zani mu yi hirar mu ni da shi da Baba Rabi, shi ma Alhaji yana yin tashi hirar wurin yayanshi sai dai bai dadewa in ya dawo ya dade yana jirana ban dawo ba, in na shiga ya yi ta mita yana fadin zai dauki matakin hanani barci a duk ranar da na je na dade wurin hirar tun da ban san ya kamata ba. Ina zaune muna hira da baba ita kuwa Baba Rabi tana sude kwanon romon kaji da na kawo musu, ta lashe hannunta ta mutstsuke su tare tana cewa, To Alhamdulillahi Allah ka yi wa Bello albarka ka yalwata mishi arzikinshi ka bashi ikon ciyar da jama'a." Baba ya yi murmushi ya ce, 'Ita kuma mai girkawar fa?" Baba Rabi ta ce, 'In Bello ya yi albarka ai ta yi" Ya yi maza ya ce, 'A'a ban yarda ba, rinka yi mata tata addu'ar daban." Ta yi dariya ta ce, 'To Allah ya wadata ta da hakuri ta zame mishi uwar iyali." Ya ce, To amin." Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, "Mijinki ya kawo mini maganarki ko da yake bai gaya mini laifin da kika yi mjshin ba, nima kuma ban tambaye shi ba, amma ya ce mini ba. kya jin maganar shi kin fi jin tsoron matan gida akan gudun bacin ranshi, haka ne?" Na soma yin kuka. Baba Rabi ta ce, "Tana 88 nema ne ta zama sakarya tana nema ta biye waa kazantarsu, kwanannan ba ka ga ba ta wanka ba? Saboda suna cewa son miji ne yake sata wnakan dare." Baba ya ce, 'Ashsha! To ina ruwanki da su Zuwaira? Mijinki kuwa ai shi kika sani abin da ya ke so kuma shi ne abin yin ki, ki kuma guji bacin ranshi, tun da shi ma yana kiyaye kan shi, ya kode a jikinki kar kuam in sake jin ya ce mini ba kya jin maganarshi, yanzun nan ma ki tashi ki je ki yi wanka, kar kuma ki dawo mini hirar sai gobe da safe, don nima kwanciya zan yi in ban da sakaran namiji wa zai yarda da mace tana dankon kazanta? Me mijinki ya rage miki da ba za ki yi mishi yanda yake so ba? Na dawo dakina na yi yanda Baba ya ce mini. Na gama shafa ina kokarin sanya sabbin kayan da na fito da su, sai ga Alhaji ya shigo cikin murmushi ya ce, To sa kayan me kuam za ki yi yanzu da daddaren nan?" Ban kula shi ba, zan ci gaba da sanya rigata ya yi maza ya kulle kofa ya iso gare ni. A wannan lokacin ne na samu kaina cikin wan yanayi na rashin jin dadi, kowanne lokaci ina kwance ba ni da kuzari ga barci komai ban iya har salla ma. Kowanne loakci Alhajis a cikin nata yake. 'Wai ke me ya same ki ne? Kullum tambayar shi kenan In ce mishi ban sani ba, ba na dai jin dadi kawai. Ya kalleni cikins nutsuwa ya ce, To ko dai kina yawan tunawa da Baba 89 ne tun da dai ni ban ga alamar rashin lafiya a tare da ke ba, kin ga yanda kika kara kyau kike wani sheki kuwa?" Na ce mishi ba na zaton tuanwa da Baba ne tun da dai ai ban taba ma mantawa da shi ba, kullum ina yi mishi addu'a. Ya ce, To bari nan da kwana biyuu in bai daina yi miki ba zan san abin da zan yi a kai, ni in banda tsoron su Baba ma ai da asibiti na kai ki. To sai su ce mene ne dalilin zuwa asibitin?" Na ce haka ne. Sati biyu bayan wannan lokacin ya dawo gida ya zo ya same ni na yi kuka har idanuwana sun kumbura ko abincin dare rannan ban fito na dora ba. "Lafiya dai na same ki a haka?" Ina kuka na ce mishi, "Wani abu ne yake yi mini motsi a ciki." "A ciki?" Da sauri ya yi tambayar na ce mishi, Eh." Ya nemi wuri ya zauna ya dora hannu a cikin nawa yana kokarin jin motsin da na gaya mishin, sai kuwa ya ji. Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, "Anya kuwa ba ciki ne da ke ba kuwa Zuwaira? Kin ga fa tun da kika yi al'adar nan sau daya ba ki sake ba. Sannan gashi yanzu cikinki yana motsi ina ji mutum ne don in ciwo ne ai ba zai yiwu ki yi kiba haka ba." Na zuba masa ido ina kallon shi, ya ce, "Ko kuam bari in je in gayawa Baba in ji abin da za ta ce." Na yi maza na ce mishi, "A'a kar ka gaya mata bari in je in dora girkina, murhu biyu zan yi yanzu zan gama." Ya ce mini, To yi sauri don akwai wani 90 labarin da nake son baki, amma sai kin yi wanka kin shafa jan bakinki tukunna." Kwana uku ne kawai bayan nan na gane ashe dama su Baba da Baba Rabi sun san ciki ne da ni, shiru dai kawai suka yi suna kallona. Wanki na zo karba wurin Baba Rabi, kamar yanda na saba yi in zan yi nawa in hada da nata. Sai ta ce mini wai a'a ita ta yafe wankin nan, yanzu in ji da kaina kawai za ta rinka yin kayanta, in ya so in Allah ya sauke ni lafiya na gama jego na yi mata. Daga ni har Alhaji kunya ce ta kama mu shi kam mikewa ya yi ya bar dakin, ya bar ni ina mutsu- mutsu. Baba kuwa ya yi ta yi mata fada, yana fadin. Wannan wane irin girma ne, ba dama ki ce mata kin hutar da ita wankin kawai sai kin tsaya yi musu bayanin dalilinki." Ban san lissafin ciki ba, gani dai kawai na yi baba ya tara lodin itace a bayan kicin, har sai da ya kere tsawon kicin din. Rannan ina hira ni da Baba da Baba Rabi, Alhaji ya shigo ya tsugunna ya gaishe su. Dabarar da. ya gano kenan wai in ganshi zai wuce daki, baba ya kalleshi ya ce mishi, "In watan nan ya kare Zuwaira za ta dawo dakin uwarta don kar haihųwa ta zo mata cikin dare ba ta sani ba." Alhaji ya sunkuyar da kai kasa ya yi shiru ya ki amsawa. Ya sake tambayar shi, "To ko za a bar maka ita ne tukunna?" 91 A nutse ya amsa mishi, 'Eh." Baba ya ce, "To me za ta yi maka?" Baba Rabi tana dariya ta ce, "Ka ji mini malamn shi da matarshi ka tambayeshi me za ta yi mishi?" Ya ce, To kar in ji na gaya maka kar ka yarda ka matsa mata. A haka muka yi zamanmu ni da Alhaji, komai a nutse yake aiwatar da shi, nima kuam na riga na fahimci mijina bai samun wata matsala a tare da ni, don haka hankalinshi a kwance yake, gashi bai ganin girman cikin nawa don gaba daya yaki fitowa. Wannan dalili ya sa ko na nemi bijire mishi, bai daukan atakure nake, sai ya dauki matakin yin rarrashi da bada hakuri. Rannan cikin dare tun yunkurin da na yi na baro mishi shinniidar shi in dawo tawa in kwanta. Bayana ya amsa gaba daya wani irin kidimammen ciwo ya kamani hankalin Alhaji ya yi mummunan tashi, don gani yake tamkar shi ya jawo mini ciwon ya yi yunkurin zuwa kiran Baba Rabi, ya kasa saboda tsoron kar su gane an yi wani abu ne ya sa ciwon ya tashi. Nima a tsoracen nake don haka na ce mishi ya barta kawai, na yi ta fama in mirgina nan, in mirigina can. Shi kuwa sai faman kamo ni yake yi, .yana ta kuak tare da yi mini alkawarin daga yau ba zai sake kula ni ba. Zuwa can dare ya yi nisa sosai, na rude, na kidime na yi zaton mutuwa zan yi. Na kalleshi cikin 92 rawar jiki da rawar murya na ce mishi, 'Wani abu zai fasa jikina ya fito." Da sauri ya sake ni ya yi waje da gudu kiran Baba Rabi. Ya tafi kafin su dawo har abin da ke son fitowa ya fito. Na yunkuro ina kokawa don in ga ko mene ne saboda ban yi zaton haihuwa na yi ba, sai ga su sun shigo daidai yaron yana atishawa. Nan dan ya kyanyara kuka. Baba tana salati tana fadin, 'Ai haihu ta yi ga yaro nan, ga yaro. " Ta sa hannu ta dauke shi. Nan da na aka taso matan gida aka fito da ni daga dakina aka'kái hi dakin Baba. Bayan an hura wuta a dakin na hau gado na kwanta, gani nake tamkar ba haihuwar na yi ba, sai zazzaro ido na ke yi ina kallon mutane. Ina jin matan yayan Alhaji suna cewa ai da an bar ni a dakina kawai, don su ba su ga amfanin daukonin ba. Wata ma har tana cewa kin ga yaron kuwa kafin a wanke shi ai duk jikinshi kazanta ne, ba su rabu da juna ba har ta haihu. Ni dai na yi lamo na rufe idona kamar ina barci, nan kuwa ba barcin nake yi ba. Cikin zuciyata dai tsoro nake ji kar ita ma baba Rabi ta gane hakan ta yi muni fada. Farin ciki wurin Baba bai misaltuwa, sai kawai da kawowa yake yi, sau goma ya shigo gidan nan sau goma zai tambaya Zuwaira kalau ko? A ce mishi kalau dinta. Ya ce to shi wannan mutumin su? A ce mishi shi ma kalau din shi. Ni kam ko kałon yaron ban yi ma saboda kunya, sai dai na ji baba Rabi tana 93 yawan cewa wannan da da karanbani yake wai shi kuma da malam yake kama. Wannan al'amari ya yi mata dadi, don duk wanda ya zo barka in ta mika mishi yaron sai ta gaya mishi gashi nan karambana ya tsallake iyayen shi kaf bai dauko su ba sai ya dauko mini mijina gata daya, sai a yi dariya a ce to baba ai shi ne mijin na asali. Ta ce a'a, a'a mijin kazanta dai ko. Alhaji ya kan yi kokarin shigowa wurina a dakin Baba Rabi da Asuba lokacin da takan zauna gaban wuta wai kar ta rika mutuwa, sai turoni dan ya tafasa tukunna. A duk lokacin ya shigo zubawa yaron indo yake yi yana kallonshi. "Dan miko mini shi nan." In ce mishi, 'A'a idan baba Rabi ta shigo ta same ka fa?" Sai ya dan yi waiwaye ko zai ganta tana zuwa in bai hangota ba sai ya yi maza ya dauke shi ya dan jujjuyashi ya maida shi ya kwantar, sai ya kallen ya ce mini, "A gadona zan rinka kwanciya da shi mu bar ki a na ki gadon, don kar ki zo ki danne shi garin wannan wawan kwanciyar na ki." In ce mishi, 'Ai ma kafin in dawo ya girma Baba Rabi ta kar6e shi." Ya zaro ido yana kallona. "Wai nan wankan bangali kike yi ne?" In ce, 'Eh mana. Ya ce, Kai ba yarda zan yi ba, na san abin da 94 Zan yi ai lokacin da zan bukaci dawowarki ya yi." Ranar suna Baba ya radawa yaro suna Aliyu, takwaran Babana kenan. Ni kaina cikin zuciyata na yi murna. Tun da aka yi suna kullum aka yi mishi wanka aka sanya mishi kayan shi wurin baba ake kai shi ya yi ta barci, har sai ya farka Sannan a dawo da shi a ce in ba shi nono. Satinmu uku rannan aka tashi baya kama nono ya sha, cikin shi ya kumbura, har ya haura kan kirjinshi sai nishi yake yi daidai, alamar dai baya cikin hayyacinshi. Hankalin su Baba ya yi matukar tashi su jika wannan su bashi, su jika wancan su ba shi. Ni kam ina kwance har ma barci ya daukeni. Tashina aka yi daga barci na ji Baba Rabi tana fadin magana cikin kuka. "Dama zuwa ka yi mu ganka ka koma?" Na shiga dube-dube don jin maganar tata da kuma hakurin da ako ta ba ta. Lokacin ne na hango yaron shimfide a tsakar daki a Rasa an nade shi cikin zaninta, baba ya zo ya tsaya a bakin kofa ya ce mata, "Miko mini shi nan." Ta mika mishi shi suka tafi, ita kuma ta kara tsananta kukan da take yi Shi kan shi Alhaji kasa hadiye damuwar shi ya yi kan rasuwar yaron, har na ji baba yana ce mishi, "Sai ka yi hakuri wannan sai an je can za'a more shi, haihuwa kuma ai soma ta kuka yi." Ni kam na hadiye babu wanda ya gane damuwata, sai dai kuam na shiga wahala ga ciwon 95 nono, gashi a yanzu ruwan zafin da ake kwara mini safe da yamma kona ni yake yi, ba na son wankan ba abin da nake so irin a ce an gama wankan nan, gashi kuam sai na jiwo magana cewar wai ai arba'in biyu zan yi, hankalina ya yi mummunan tashi da jin hakan. Rannan Alhaji ya dawo daga kasuwa da yamma ya shigo wurina ya zuba mii ido yana kallona cikin tausayi. "Daga gobe dai za ki huta da wahalar wankan nan tun da gobe ne arba'in din." Na kalle shi cikin nutsuwa na ce mishi, "Ai arba'in biyu, aka ce zan yi." Ya sake kallona ya ce, Har da babu yaron ma Zuwaira ba za a tausaya mniki ba? Kin fa rame." Ban tanka mishi ba ya juya ya fita. Ban san me ya faru ba, ko kuma me ya yi? Illa dai kawai na ji baba yana cewa Baba Rabi, "Ke Rabi. ki baiwa yaron nan matarshi ki bar wankan nan haka, watakila wani rabon ne mai tsanani ya kori wancan kin ga ya gama zagaye-zagayen shi ban kulashi ba, to jiya ya fito fili ya yi mini magana ya ce a yi hakuri a bar wankan haka." Baba Rabi ta ce, "To ai ba bta gasu ba." Ya ce, "Eh maida mishi da ita in ta sake wata haihuwar kya hada gaba daya ki. gasata da kyau, anma yanzu yana ganin babu dan ai ba zai iya hakuri ba." Kememe baba Rabi ta yi ta ce ba za ta maida ni ban gama wanka ba, ai in na zo wata haihuwar sai 96 in rinka kumburi, jikina ya danyace. Ya ce, "To babu laifi Rabi rike ta ku zauna." Alhaji ya maida dakin Baba Rabi ya zama nan ne wurin zaman shi yana fitowa daga sallar Asuba na zai zo ya zauna in an ce in fito a yi mini wanka ya ringa tsaki kénan yana cewa, "Ke ba za ki rinka yi mata kuka a wurin wankan nan ba, don ta san wahala kike sha?" In yi kamar ban ji shi ba. Da daddare ma in ya fito daga wurin yawonshi nan zai zo ya zauna suna hira shi da ita, tun tana amsa hirar har ta koma gyangyadi sai jifa-jifa ne za ta rinka amsa abin da yake gaya mata, ni kuwa in yi ta barcina. Rannan ina jin baba yana cewa mata, Ai maganinki kenan duk inda kika dan zauna ki kama gyangyadi, saboda ba kya samun barci ga tashin Asuba, wannan dogon hirar da Bello yake yi miki ai ke ma ma kin san abin da take nufi da matarshi take dakinshi kina ganin shi ne a dakinki da daddare?". A hakan sai da ta yi mini wankan wata biyu safe da yamma. Sannan ta sa aka gyara mini dakina fes aka wanke mini kwanukana da tasoshina aka sake jere daki ya yi ras. Da Alhaji ya shigo mata hira da daddare ranar ta ce mishi "Ba ni wuri barci zan yi gobe war haka in ka dawo za ka samu matarka a dakinka." To haka aka yi na dawo dakina ina tare da mijina muna zaune lafiya, babu wanda ya taba sjin tsakanin mu akan wani sabani. Yana matukar sona, 97 yana matukar kyautata mini kowane lokaci idon shia kaina yake, ga iyayenmu da ke matukar sona suke kaf-kaf da al'amurana. Sai dai shiru babu ciki, babu alamar shi. A wannan lokakcin ko atishawa mai karfi na yi sai Baba Rabi ta ce ai ina jin juna biyu ne da ita, saboda tsananin matsuwarta da son ta ganni da ciki. Nan da nan sai ga ta ta shiga yi mini jike-iiken sauwowi, wai maganin haihuwa. Shi kuwa Baba sai ya ce mata, "Da kin yi hakuri ita haihuwar nan inta tashi zuwa ai za ta zo da can saiwa aka ba ta? Alhaji da kan shi ya soma matsuwa da son ganin na haihu, dan kankani abu ne zai faru sai ka ji yana cewa da yanzu yana nan da an yaye shi, ga shi har yanzu shiru me ya faru ne? In yi shiru kawai in sunkuyar da kaina ina sauraron shi, sai kuam ya ce, na ganin har da raba shimiida da kike sawa muna yi daga yanzu ba zan sake yarda ba." Yayin da Alhaj! yake wadannan maganganun a daki su kuma matan tsakar gida cewa suke yi ai ita mace in ta cika mannewa miji ma haihuwa gagararta take yi. Da na gaji da irin fitinarshi sai na ce mishi da ka dan rinka barina ina hutwa, saboda ga abin da su yaya suke lada. Ya ce, 'Rabu da su ba su san komai ba, kar ki rinka zama a wurin hirarsu." In ce mishi to. A wannan lokacin ne Alhaji ya zama saurayi sosai, ya kuma hada karfinshi wuri daya ya murje ya yi kumari, kwarjininshi ya soma bayyana sosa1, kyan Sar ya kara fitowa, gashi ya Soma samun barka sosai, 98 kasuwa ta bude mishi ta ko'ina, duk abin da ya taba sai ka ga alheri ne ke ta faman shigowa fiyc da yanda aka yi zato. Ni kaina yanzu ne ya dacc a ce na zama budurwa shekaruna goma sha bakwai ne, na yi kyau har ba a magana, na riga na san dadin mijina yanzu ne na kara fahimtar auren sosai, in muka shiga daki ni da Alhaji mu kadai mu ka san abin da ke faruwa, shi kuwa Alhaji dama zani ce ta tadda mujemu don haka da rana ma barin kasuwa yake yi ya taho gida duk lokacin da zai shigo kuwa ba zai shigo haka ba, sai ya riko wani abu ya ce "Raba ki kaiwa su Baba da mutanen gida ke ma ki dauki naki." A wannan lokacin dakin Baba da Baba Rabi bai rabuwa da naman kaji soyayyu a ajiye hakan ai hanawa kullum ya zo da wadanda za a yi musu farfesu, ga zuma a ajiye, ga yaji da manshanu. Kullum Baba Rabi ta gama cin abincinta in tana lashe yatsa za ta ce, "Ubangiji ka yalwatawa Bello arzikinshi don ay ciyar da jama'a." Muna cikin wannan hali ne kawai baba Rabi ta kamu da zazzabi ko a jikina ban damu ba, don ta saba yin rashin lafiya irin wannan tana warkewa, don haka na dauki matakin kulawa da ita kawai, kamar yanda na saba. Na kai mata ruwan wankanta na riketa na ka ta ta yi na rikota na dawo da ita dakinta. Bayan ta yiwo alwala muka dawo daki ta kwanta, na gyara mata ruhuwa na je na kawo mata gaurwáshin wuta na Zauna 1na dama mata furarta ina shirin ba ta sai na ji ta 99 kama shakuwa mai karfi, da sauri na dago ta ganin halin da take ciki ya sa na yi maza na maida ita na je kira Baba muka shigo tare na sake dagota na rumgumeta ya zuba mata ido yana kallonta hawaye suka zubo sharrr! Daga idanuwanshi. A hankali ya ce, "Ashe haka za mu yi da ke ke ma Rabi? To Ubangiji ya baki sa'ar tafiya, sai na zo." Yana fadin haka ya soma shafa mata ruwa, yana salati yana nanatawa, har ita ma ta kama yi. Zuwa can sai ta yi shiru. Baba ya yi ajiyar zuciya mai karfi, ya yi kalmomin godiya ga Ubangiji da nemar mata rahama ya kalleni ya ce mini, "Shi kenan Zuwaira Rabi ma tabi bayan yan'uwanta su duka ukun sun tafi sun bar ni. " Rasuwar Baba Rabi a gidan nan ba karamin al'amari ba ne a gidan nan. A wurina dai rasuwarta ita ce ta sankar da ni yanda dacin mutuwar mahaifiya take. Ko kwana arba'in da matuwarta ba a yi ba aka ware ni a gidan, ba ma shiga harkata, babu mai magana da ni. Maganganu iri-iris suke yi ta fitowa ciki har da haihuwar da na yi ni kadai a daki ban kira su ba. A ka'ida kuma wai uwar gidan yaya babba ake kira in ana nakuda sai kuma ta kira sauran matan da ta zaba su zo su kewaye mai nakudar, ita Baba Rabi a kan je ne kawai a gaya mata an yi haihuwar amma ni da mijina ba mu yi haka ba. Wasu suka ce to in dai ma namiji ne ai alkawarinshi ragagge ne muna nan da ku 100 zai yi mata kishiya sai kuam mu ga tsiya, tun da tana zauni ita kadai ba ta kama mu ba, ai kishiya ba za ta zo ta cc mana ta san da mu mu yarda ba. A wannan lokacin ne na gane Baba Rabi ta tare mini abubuwa da yawa a gidan nan. Ni kam ina jin su ba na kuam ta tasu, na maida hankalina wurin baba, wanda ya rasa lafiya tun bayan mutuwar matarshi kowanne lokaci ina tare da shi, ina yi mishi hidimominshi ko in taya shi hira ko shi Alhaji a wannan lokacin nan wurin nashi yake hira. Koda baba ya watstsake nan wurin shi muka mayar da hira da safe da daddare, nima na maida kicin din baba Rabi wurin aikina, saboda yafi kusa da wurinshi ina aikina muna hirarmu, don fito mishi da shimfida nake yi a inuwar bishiyar da ke nan sashin, sai na zama in ba Alhaji ne ya dawo ba ba na zuwa sashin da nake, saboda ba na wani jituwa da wadanda muke taren. Kullum dai baba ya kan gaya mini, "Kar ki yarda ki tanka musu duk abin da za su yi miki nan in da kike ganinsu babu wacce ba ta haifcki ba, in ban da Bilki." In ce mishi to Baba. Ana cikin haka ne aka wayi gari daurin aure da safe a gida, ashe wai kanin Baba mai binshi ne ya bai wa Alhaji auren yarshi bisa hujjar wai ni din ba mai haihuwa ba ce. Ran Baba ya yi matukar baci da jan maganar tasu ya ce da ba shi auren kawai aka yi aka yi shiru da ban ji takaici ba, amma a ce Zuwaira ba ta haihuwa? Ai ta haifu ba a bar mata ba ne. Yana 101 maganar cikin hawaye ya kalleni ya ce mini, "Kar in ji kar in ganni, kar ki yarda in ji kin yi wa miinki wata magana, wannan auren da kike gani an dade ana son bashi Rabi ta yi uwa ta yi makarbiya ta ki yarda, don haka ki yi hakuri ki daure ki bai wa mara da kunya." Na ce mishi to baba. Umarnin da baba ya bani na in zuba ido shi na bi na yi matukar kokarina wajen cire auren daga raina, duk da tsananin kishin da ke damuna babu halin in ga ya shiga dakinta sai in rinka ganin tamkar shi kenan abin da yake yi mini ita ma shi yake yi mata, bisa wannan dalili sai zafin kishi ya ringaye ni, na shiga yi mishi rowar kaina, na bijirewa duk wani rarrashi nashi, gashi kuma dama mutancn gida gaba daya suna tarc da amarya ne, ita yar dangi ce ko ba haka ba ma dama sun riga sun kosa su ga an yi mini ita. Sai na zama ba ni da wani abokin mu'amalla mai dadi sai baba. Bisa wannan al'amari sai Karama ta yi amfani da abin da ta gani na juyawar Alhaji wurinta de goyon bayanta da takc da shi wurin dangi duk ta ki yarda ta marawa kokarina na ganin mu zauna lafiya. Ana cikin haka sai aka ce wai tana da ciki, gaba daya gida ya dauka matar Bello juna biyu ne da ita, ko bako ne ya zo sai an gaya mishi, in aka gani a wurin ma an fi tsananta bayanin. Rannan ina zaunc gaban Baba kuka nake yi, Kuka kuwa ba na wasa ba, saboda na fara gajiya da ganin abin da nake gani. Rarrarshina yake yi yana ba 102 ni hakuri. Da ya ga na yi shiru sai ya kalleni ya ce mini, "Ashe ba ki da hakuri ban sani ba? Ai ita rayuwa babu abin da ya dace da ita irin hakuri. Ashe ba za ki iya zuba ido ki kalli Bello da mutanen nan ba ko da na shekara

Chapter 6 of 9