Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
alamun damuwa karara a fuskarsa, meyiyuwa su basu lura da hakan ba domin kawunansu a sunkuye suke. "Biyo ni mu shiga ciki in nuna maka wani abu". Dakta sulaiman ya dubeta cikin mamaki, daidai lokacinne wani katon kuda kore ya yiyo hijira daga kan bawon ayabar da yara suka jefar ya nufo kunnen Dakta sulaiman yanayi masa Bu! Bu!! Dakta sulaiman yakai duka ya mari fuskarsa a banza. "Banjiki sosai ba kina nufin mu shiga ciki"? Dan abu zan nuna maka yanzun nan zamu fito ko minti daya ba zamu yiba". Tana gama fadin haka saita juya ta fara tafiya ta nufi zauren gidan. Sulaiman yayi kamar kada ya shiga gidan domin baisan abinda take nufi ba gashi kuma uwa uba babu alamun dake karfafa masa gwiwa. To amma sa'ar da yaga gadan-gadan shigewa zatayi, sai sulaiman ya bita a baya cikin sauri har da sassarfa, kadan ya rage ya taka wuyan wata farar kaza. Badawiyya ta rage sauri sa'ar dataga yana biye da ita. Tana tafiya tana tunani. Acan wani bangare na zuciyarta gani take yi abinda tayi daidai ne domin ahalin da ake ciki a yanzu itace hanya mafi sauki da zata kirkira domin ta rabu da wannan sabuwar masifar da ta kunno mata kai. Ta sani cewa duk tsayin lokacin nan zuru kawai akayi mata saboda tausayin halinda take ciki, amma da tuni an fara tunanin araba aurenta da Nuri tunda dai babu ranar warkewarsa. A gareta duk wani abu da zai rabata da Nuri dinta masifa ne. Tauraron da sa'ar Badawiyya ya haskaka sa'ar da suka shiga tsaka gidan domin mahaifiyar Nuraddin ta zagaya bandaki. Dan haka cikin sauri sai Badawiyya ta wuce da sulaiman kai tsaye zuwa inda Nuraddin yake kwance. Badawiyya ta dago ta dubi sulaiman da niyar nuna masa Nuraddin, amma alamun kaduwar data gani karara akan fuskarsa. Sun isa ta san yaga Nuraddin. Tsawon lokaci likitan na tsaye ya kurawa Nuraddin idanu, can sai yayi ajiyar zuciya ya dubi Badawiyya yace. "wannan shine abinda kike son nuna min din"? Badawiyya ta gyada kai sannan tace. "zo mu koma waje". Dakta sulaiman ya bita a baya zugum-zugum kamar rakumi da akala, duk ilahirin jikinsa rawa yake kamar mazari. Suna fita kofar gidan sai dakta sulaiman yayi sauri ya jingina da jikin motarsa, domin ji yake yi kamar kafarsa bazata iya daukarsa ba. A tsahon lokacin da yayi yana aikin likita ya sha ganin munanan abubuwa, kamar irin su gawar hadarin mota da sauransu, amma sa'ar da yaga Nuraddin, sai da hanjin cikinsa ya yamutse, gashi a kanannade babu kyan gani amma wai da rai. Badawiyya ta dubi fuskar Dakta Sulaiman taga ta hada gumin sharkaf. "Ina fatan ka kare masa kallo"? Dakta sulaiman ya gyada kai lokaci guda kuma yayi ajiyar zuciya yace bakinsa na rawa. "Menene dalilin nuna min shi"? Badawiyya ta dubeshi ido da ido tace. "Wadanda suka kwatanta maka kazo nan ka sameni basu baka labarin abinda ya mayar dashi haka ba"? Dakta sulaiman ya girgiza kai, yawun bakinsa ya bushe. Tsawon lokaci suna duban juna, can sai tace dashi. "wannan mutumin da na nuna maka mijina ne, kwana daya da daura mana aure aka mayar dashi haka". Dakta sulaiman ya dubeta a rude. "mijinki fa kika ce"? Badawiyya ta gyada kai. "Kwarai kuwa, da lafiyarsa kalau, kamarka yake a dalilin wai saiya rabu dani yaki wata aljana ta mayar dashi haka. Me yiyuwa bazaka yarda da wannan labarin ba, amma haka dai abin yake". Ta danyi shiru kana saita dubeshi. "shiyasa na nuna maka shi domin na sanar dakai cewa duk da haka din da yake, a duniyar nan babu wanda nake kaunar gani kamarsa. Akan sai ya rabu dani aljana ta mayar dashi haka, don haka nake son ka fahimta aljana ma tayi kokarin raba mu bata samu nasara ba, ballantana kai mutum mai 'yar kankanuwar soyayya, babu mai rabani da Nuri darling sai mutuwa". Tana gama fadin haka sai ta juya da sauri ta koma cikin gida. Wata sassanyar iska ta fara busa fuskar Dakta Sulaima. Abin yayi matukar kadashi bai taba jin labari kamar wannan ba. Da sassafe misalin karfe shida saura 'yan mintuna, Badawiyya ta tashi zaune akan gadonta, domin lokacin yin wankanta yayi, sai taji kanta ya fara sarawa. Dama tunda asuba kan nata ya fara alamun zaiyi ciwo. Badawiyya ta janyo matashin kan dake kusa da ita ta tura shi a bayanta kana ta jingina da bango, lokaci guda ta zura hannunta da dauko hoton Nuraddin dake kan wani teburi dafda gadonta ta dora hoton akan kirjinta sannan ta zura masa idananu. Abdullahi Yusuf Maitama. ALJANI YA TAKA WUTA {p.37} Ba'a fi ko dakiku ashirin ba da fara kallon hoton sai hawaye ya fara sartu akan kyawawan kumatunta shar-shar. Wannan sabuwar al'ada da Badawiyya ta tarka ba karamin konawa mahaifiyarta rai take ba. Tun tsawon watanni shidan nan, haka Badawiyya kanyi aduk safiyar duniya. Ga al'adarta kullum karfe shida take tashi na safe, ta dauki hoton Nuraddin ta kura masa idanu tayita kuka. Haka nan zatayi ta fama har zuwa bakwai, wani sa'in har sai idan mahaifiyarta ta shigo ta lallasheta, sannan zata bar kukan ta wuce zuwa bandaki tayi wanka. Dan haka wannan safiyar sai taji hawayen da yake zuba yafi na kowacce rana domin in har ciwon kan yaci gaba da takura mata zaiyi wuya in har zata iya zuwa gurin Nuraddin dinta, wannan kuwa yafi komai kona rai a gareta. Aka kwankwasa kofar a tausashe. Badawiyya ta dubi kofar cikin gaggawa, haka nan lokaci guda ta ajiye hoton dake kan kirjinta akan katifar gadon. Kofar dakin ta bude ahankali mahaifiyarta ta leko, sanye take da doguwar riga baka kanta daure da dan kwali na zani. Koda Badawiyya ta dubeta sai taga alamun damuwa karara akan fuskarta wannan shine yasa ta mikewa zaunen sosai ta dubi mahaifiyarta, har yanzu akwai sauran hawaye akan fuskarta. "kukan dai kike Badawiyya"? Mahaifiyarta ta tambaya. Adaidai lokacin data zauna a bakin gadon ta fuskanci 'yarta Badawiyya. "Ina ganin lokaci yayi daya kamata ki sallamawa ubangiji dukkan abinda ke damunki kada ki bata rayuwarki a banza". Badawiyya taji gabanta ya fadi, domin bata taba tsammanin haka daga bakin mahaifiyarta ba. "yanzu ace mutum Badawiyya bashi da aiki kullum kwanan duniya sai koke-koke da kuncin zuciya, wannan ai sai hawan jini ya kamaki. Ina ganin ya kamata ki rage zuwa gun Nuraddin haka nan domin ganinsa shike jefa ki cikin damuwa". Badawiyya taji kamar an watsa mata wuta a fuska, ta dafe kirji cikin razana, rashin ganin Nuraddin yafi kowacce irin masifa azaba a gurinta, sai gashi kuma yanzu mahaifiyarta da kanta tana cewa wai ta rage zuwa gurin Nuraddin dinta. Nan da nan taji hawaye ya fara yi mata sartu akan kumatu sar sar kamar ruwa. "Ba kuka zakiyi ba, hankalinki yaki bani nan na fahimtar dake abinda nake nufi". Ta danyi shiru na wani lokaci, kana taci gaba. "Ba wai ina nufin ki daina zuwa gurinsa bane kwata-kwata, amma ya kamata ki rage . Ina laifin kina zuwa gurinsa sau daya a sati. Amma ki tafi can ki tare kullum sai kinje, watanni shida kenan fa. Kuma banda wannan ma kina nufin zaki yi ta zama da shi ahaka kenan har abada bazaki sake aure ba"? Numfashinta ya dauke akaro na farko ta dago kai ta dubi mahaifiyarta tace cikin rarraunar muya tana kuka. "shi kuma fa.. Yaya zanyi dashi? Shi ba mijina bane"? Ganin halin da Badawiyya ta shiga shiyasa mahaifiyarta ta matso kusa da ita sannan ta dafata tace. "Nasan mijinkine Badawiyya, kuma har yanzu da aure a tsakaninku amma yayi muguwar nakasa, nakasar da bashi da wani amfani agareki. Yanzu ke kya iya zama da mutum a kanannade haka har abda? Sai dai ki bashi abinci kiyi masa wanka ki kwantar ki tayar, haka zata yiyu kuwa Badawiyya". Badawiyya taji zuciyarta na neman tsagewa, irin wandannan maganganu na mahaifiyarta sun fara isarta domin basu da wata ma'ana agareta. "mama saboda nifa Nuraddin ya shiga halinda yake ciki ayanzu, da yabi umarninta ya gujeni da yanzu yana nan lafiya klau kamar mu. Nikam bazan iya rabuwa da shiba domin koda na rabu da shi din ma zuciya da duk wani bangare na ruhina suna tare dashi". Ta sake fashewa da kuka. "ke har yanzu yarinya ce ana rabaki da kiwon akuya kina kwalla ta haihu abin da baki gane ba shine kada ki kasancd mai yawan son kanki ke kadai ki tunafa ni mahaifiyarki be, kuma kina da mahaifi, ki sani kuma babban burinmu a duniya shine mu sami jikoki muyi alfahari dasu kamar kowanne kaka aduniya, to yanzu Badawiyya ta yaya wannan buri namu zai cika idan kuna tare da wannan yaro wanda a yanzu mutuwarsa tafi rayuwarsa"? Tadan saurara tana nazarin fuskarta. "ki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki kuma fahimci abinda nake kokarin yi miki. Kinga yanzu akwai yaro dake masifar kaunarki kyakykyawa dashi, shi baima san kinada aureba sai daga baya tunda kullum a gida yake ganinki, kamata yayi a raba aurenku da Nuraddin sai a hadaki dashi". Badawiyya ta zabura ta dago a tsorace ta dubi mahaifiyarta cikin kuka. "Bana fatan Allah ya nunamin wannan rana... Arabani da Nuri"? Mahaifiyarta ta harareta. "shashar banza, kinsan dawa nake nufin za'a hadaki? Wannan likitanne fa daya dubaki alokacin da kika suma, dakta sulaiman. Kuma in kin aureshin dinma wayace kin rabu da Nuraddin har abada, sai insa mijin naki duk sati yana kaiki kina dubo shi". Badawiyya ta zuro kafafunta kasan gadon kana ta sunkuyar da kai tana shasshekar kuka tace. "Bani da wani mijin da ya wuce Nuri, bazan iya rabuwa dashi ba, tunda ya shiga masifa saboda ni nayi alkawarin babu mai rabani da shi sai mutuwa. "zakwa ki ci ubanki 'yar banza sokuwa inkayi wasa wallahi saina hana ki fita koda nan da tsakar gidane". JANI YA TAKA WUTA {P.38} Awannan ranar saboda abinda ya faru tsakaninta da mahaifiyarta bata sami damar dawowa daga gurin Nuri dinta ba sai baya karfe goma sha daya da rabi na dare. Lokacin data dawo gida maigadi ya gaisheta, sannan ya janyo kofar gidan ya rufe. Tsahon watanni shida kenan kullum itace karshe shigowa gidan saita shigo za'a rufe. Maigadin yan matukar tausaya mata domin laraba mai dafa abinci a gidan ta taba yi masa gulmar duk abubuwan dake faruwa akan Badawiyya. Cikin sauri Badawiyya ta nufi dakinta. Ta riga tasan kullum da anyi sallar isha'i mahaifiyarta take yin barci koda yake dai koda tsakar darene sai mahaifyarta ta leko dakin ta tabbatar ta dawo sannan zata koma ta kwanta. Badawiyya ta tura kofar dakin ahankali sai taji gabanta ya fadi ras, domin tana budewa sai wani haske ya kashe mata idanu. Kusan dakiku biyar tana tsaye kafin idanunta su saba da hasken dake dakin. A lokacinne to Badawiyya taji gabanta ya fadi. Hasken daga kan gadonta yake bullowa. A zaune a bakin gadonta tasha kwalliya da kayan kawa na gaske, fuskarta na kyalkyali kamar madubi acikim rana Amal ce 'yar sarkin Aljanu. Tun wani lokaci daya shude Amal ta daina baiwa Badawiyya tsoro, dan haka a wannan irin yanayi da ita kanta Badawiyya ke neman abokin mutuwa sai taji ko kankani Amal ta daina razanata. "Me zaki yimin kike jirana? Ko zuwa kika yi nima ki nannade ni? Idan wannan ce niyyarki to bismillah domin wallahi bani da kaico don kin nannadeni tunda dai kin mayar da Nuri na haka macuciya"! Amal ta dubeta tana murmushi. "Bakaken maganganunki na iya sawa kiyi nadama". "Babu wata nadama da zanyi, domin a yanzu bana tsoron komai, tun daga ranar da kika nakastamin abin begena, naji na daina tsoronki bana tsoron kowa a duniya inba Allah ba. Na riga na kuna bana tsoron kauri dan haka a yanzu ina umartarki dan Allah ki mayar dani kamar Nuraddin dan uban da ya haifeki makira"! Amal ta dubi Badawiyya cikin mamaki dan bata taba tsammanin irin wannan taurin kai daga gareta ba. "Abin bai kai da zagi ba Badawiyya sasin kanki ne idan inaso yanzun nan ina iya marayar dake KARAS ko kuma TUNKIYA, amma ni ba wannan ce ta kawoni ba, abinda ya kawo ni shine zuwa nayi na baki dama ta karshe, domin ina tausaya miki a matsayinki na 'yar uwata mace". Badawiyya ta dubeta cikin rashin aminci, dumbin tsana karara akan fuskarta. "Wacce dama kuma zaki iya bani, tunda kin nannade abin kaunata"? Amal ta mike tsaye daga kan gadonta ta nufo inda Badawiyya take tsaye, a tsakar dakin. Badawiyya tayi tsaye kikam ko gezau bata yiba, duk kuwa da cewa ta lura da farin takalmin dake kafafun Amal na farar azurfa ne. Badawiyya tayi mamakin abinda ke cikin takalmin shin tafin kafa ne ko kuwa kofato". "kin cika taurin kai Badawiyya kamar Nuraddin". Amal tace da ita tana dubanta. "Wannan shiya tabbatar da cewa irin jininmu daya da mijina Nuri". Badawiyya ta bata amsa. Mijina din data ce shi yafi komai konawa Amal 'yar sarkin Aljanu zuciya fiye da komai. "zabin da zan baki shine na karshe, in kin yarda kin tserar da shi, idan kuwa kinki to haka Nuraddin zaiyi ta zama har abada ni kuwa baza ki kara gani na ba". "Allah ya fiki makira, kuma ko yaushe naga damar ganinki saina ganki shin ko kin manta ne da zoben dake hannuna"? Badawiyya ta daga danyatsanta sama. Amal ta dubi zoben da ta baiwa Nuraddin cikin takaici, tasan duk cika bakin da take na banza ne, do muddin Badawiyya na tare da zoben nan, ko babanta mai hancin karas bai isa ya tabata ba ballantana Amal. "kinga Badawiyya irin halinda Nuraddin dinki ke ciki, kashi da fitsari duk a kwance, amma idan naga dama yanzun nan saina mayar dashi kamar yadda yake ada in har zaki yimin alkawarin abu daya". Badawiyya ta dubeta cikin rashin yarda. "wane alkawari"? Amal ta dubeta tace "ina so kiyi min alkawarin indai na warkar dashi zaki bar min shi na aura. Ke kuma ki sai ki auri wannan sulaiman din da ke son ki yaya kika gani"? Badawiyya ta harari Amal tace. "Amal idan zaki yarda da kaddarar mahalicci, to ki yarda kawai ki warkar da Nuraddin amma zancen na bar miki shi baima taso ba' domin babu mai rabani da Nuri darling sai muuwa. Amal 'yar sarkin aljanu ta fashe da dariya tace. "kada ki cuceshi ki cuci kanki, na baki daga yau zuwa gobe kiyi tunani, in dai har dagaske ne kina kaunarsa, ki bari mana na warkar dashi na aureshi domin zamansa lafiya baya tare dake yafi zamansa a nannade tare dake, ko kuwa me kika gani"? Ta danyi shiru sannan taci gaba. "Gobe zan dawo da daddare kiyi tunani da kyau Badawiyya kawata". Kafin kiftawa da bismillah Amal ta bace. Dakin yayi shiru dif! Kamar makabarta. Badawiyya jiki na rawa ta jingina da bangon dakin sannan ta lumshe idanunta tace a fili. "ALLAH kayi min maganin wannan masifa". ALJANI YA TAKA WUTA part39 Washe gari tun karfe tara saura kwata na safe Badawiyya ta isa gidansu Nuraddin. A daren jiya batayi barci ba, zuciyarta cike da abinda ya wakana tsakaninta da Amal 'yar sarkin aljanu. Badawiyya ta yarda cewa abinda Amal ta fada gaskiya ne, tabbas da ace Nuraddin yaci gaba da zama a haka gara Amal ta warkar dashi ta aure shi. Amma tambayar da Badawiyya ta kasa kawo amsarta shine, shin anyan kuwa zata iya zama a duniya ba tare da Nuri Darling dinta ba? Ta kuma riga ta san tsabar taurin kan Nuri ba dole bane ma idan Amal din ta warkar shi ya yarda ya aureta ba. Wadannan abubuwan su suka cunkushe kwakwalwarta. Daga karshe dai ta yanke a zuciyarta cewa koma dai menene gara ta amince da sharudan Amal in har zata warkar da Nuri, dadai yayi ta zama a haka a nannade har iya rayuwarsa gara ta bari Amal din ta warkar dashi ta aura din. Akalla dai, badawiyya tace cikin zuciyarta, koda mutuwa nayi, nabar abin tarihi mutane na baya masu zuwa idan sunji labarin zasu san cewa ban zalunci Nuri ba, kuma na mutu a kokarin ceto shi daga mummunan kangin rayuwa. Da wannan hukunci a zuciyarta ta isa gidansu Nuri. Tana zuwa suka gaisa da mahaifiyarsa sannan ta wuce kai tsaye zuwa inda Nuri ke kwance kamar kwarangwal, an lullube shi da farin kyalle kamar gawa babu komai a jikinsa sai diras. Badawiyya tasa hannu ta yaye kyallan zuwa iya fuskarsa lokaci guda kuma ta ajiye jakar dake hannunta ta zauna kusa dashi ta kura masa idanu. "sannu Nuri... Allah ya sauwakema kaji"? Tace dashi. Wani zazzafao hawayen bakin ciki yayi sartu akan kuncinta, Badawiyya tayi saurin dauke kanta gefe guda ta goge hawayen saboda tasan duk da yakedai Nuri baya iya koda motsi, idan yaga hawayen sai zuciyarsa ta soye dan bakin ciki. Badawiyya ta dubi agogon dake hannunta, karfe tara daidai, lokaci baiwa Nuri abinci yayi tace cikin zuciyarta. Dan haka ciki gaggawa ta dauko kwanon farar tasar dake kusa dashi wanda a cikinsa kulum take juya madar kafin ta bashi, domin baya iya sha kai tsaye daga kwalbar. Badawiyya ta zaro kwalbar madarar mai sanyi daga cikin jakar da tazo da ita, ta juye madarar cikin kwanon. Badawiyya na kokarin bashi madarar kenan sai taga kamar madarar tayi kauri da yawa, sai ta dan kara ruwa ciki, sannan tasa dan yatsanta guda daya wanda ke sanye da zobe ta fara gauraya madarar, bayan ta gama sai ta tsotse dan yatsan da tasa cikin madarar a bakinta, sannan sai ta lura da cewa duk madarar ta bata zoben dan haka shima zoben saita sashi a bakinta ta tsotse shi cikin jindadi domin tasan zoben ya taba zama a hannun Nuri. Ahankali cikin tausayawa ta tallafi kan Nuri ta dora akan cinyarta, sannan ta dauko kwanon tasar da madarar ke ciki ta dungura a bakin Nuri da niyar ya sha. "Kada ki bashi! Kada ki kuskura ki bashi! Idan kika bashi mutuwa zaiyi". Wata fikakkiyar murya ce take fadin maganar cikin karaji, akwai alamar razana karara a muryar. Badawiyya ta juya a tsorace bata ga kowa ba. "kada ki bashi! Zai mutu idan yasha"! Cikin firgici. Badawiyya ta dubi idanun Nuri abinda ta gani sun bata al'ajabi, fuskarsa ta fara motsi tana kokarin nuna mata wani abu, tabbas idanunsa nuni suke da cewa abashi madarar yasha. Badawiyya bata bata lokaci ba sai ta durawa Nuri abaki. Nuri ya hadiyi madarar kut!. "wayyo Allah na shiga uku na lalace wallahi Badawiyya kin cuceni" muryar ce ke ihu tana kuka. Ga mamakin Badawiyya sai taji kamar jikin Nuri ya fara nauyi akan ciyarta, da farko bata gane abinda ke shirin faruwaba, saida ta kura masa idanu sannan taga jikinsa ya fara rikidewa yana dada kumbura, kifin kiftawa da bismillah jikin Nuraddin ya warware ya koma kamar yadda yake abin kamar a mafarki. "Alhamdulillah" nuri yace ya tashi zaune. Badawiyya ta mike tsaye zumbur a kidime, ta rungume Nuraddin cikin Kuka. "NURADDIN... Wayyo Allah Nuraddin ya akayi ka warke"? Nuri ya mike tsaye, Badawiyya ta dubeshi sai taga ya warke garau babu sauran wata nakasa a jikinsa kamar ma wani abu bai taba samunsa ba. Nuri ya kama dan yatsan Badawiyya sannan ya rike zoben daya bata yace. "Har kullum kwanan duniya nakan gwada miki da idanuna cewa ki jikamin zoben nan ki bani nasha, amma kin kasa ganewa sai yau Allah yasa kika gauraya madarar da danyatsanki mai zoben". Yadan yi shiru yana duban jikinsa kana yaci gaba. Wallahi daga yau dinnan makircinta ya kare agaremu har abada domin duk wanda yasha wani abu da ya taba zobennan bazata taba iya cutar dashi ba, shi ya sa kikaga tunda farko ta kasa tabaki, duk karyar banza take fada miki da ace tanada iko da tuni ta nannade ki kamar ni". ALJANI YA TAKA WUTA KARSHEN LABARI. "Nuri darlin! Wayyo Allah nurina"! Badawiyya ta dada rungumeshi. Gaba daya nema take ta zama mahaukaciya. Mahaifiyar Nuraddin tana daki sai ta jiyo hayaniyarsu a waje. Gabanta ya fadi sa'ar da taji wata murya kamar ta danta Nuraddin. Wannan shiyasa ta fitowa waje cikin gaggawa sai suka yi ido biyu da Nuraddin. Atake a gurin ta fadi summamiya. "Nuri darling na godewa Alla daya warkar dakai, don Allah zo mutafi gidanmu yanzun nan mama ta ganka". Nuraddin yayi murmushi "Amal ta fadamin labarin komai, wai da wani mijin za'a aura miki ko"? Gaban Badawiyya ya fadi ta dubeshi cikin damuwa tace. "yaushe ta fada ma? Nuraddin yace. Jiya da tsakar dare, kinsan kullum saita kawomin labarin da zai konamin zuciya. Yayi shiru gami da murmushi, sannan sai ya kama hannun Badawiyya yace. "zo mu tafi gidan naku mu bata mamaki me yiyuwa ita ma idan ta ganni sai an zuba mata ruwa saboda kaduwa". Cikin farin ciki marar misaltuwa, Badawiyya ta kama hannunsa suka nufi zaure. Koda suka zo daf da kofar gidan zasu fita sai Badawiyya ta rkeshi suka tsaya sannan sai ta dubeshi ta kyalkyale da dariya tace. "Nuri darling Duk mun rude dubi fa a yadda jikinka yake har zamu fita waje. Ka koma gida ka sako wandonka da riga sannan ka yayyafawa mamanmu ruwa". Badawiyya ta sake fashewa da dariya. Nuraddin ya dubi jikinsa cikin mamaki domin ganin abinda take yiwa dariya. Sannanne to ya lura ashe tik yake tsirara daga shi sai DIRAS!. KARSHEN LABARI. ALHAMDULILLAH. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6