Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels LABARIN ALJANI YA TAKA WUTA Part 1. Duk wannan kadan ne daga cikin cikin kaunar da yarinyar take nuna masa yau kusan shekaru shida kenan tun suna firamire, kullum aikin t kenan taso shi ta kuma yi masa wahala, kuma duk sanda zai koma makaranta ita ke zuwa da motar gidansu ta mayar dashi, bayan yan kananan siye- siye da take yi masa har kudi take bashi. Amma kuma abinda bata saniba shine mafi yawa daga cikin kudin da take bashi a shaye shaye da yawace-yawacen banza suke tafiya,domin in har kana neman shaidani a duk fadin makarantarsu, idan ka sami Nuraddin ka kare."Badawiyya kenan". Nuraddin yace gami da dan tattausan murmushi."Nuri 'darling' kenan". Badawiyya tace.Ga mamakinsa sai ya ga ta dauko tsohuwar jakar da take cewa bazata dauka ba, ta rataya kafada."Zo mu tafi dan Allah Nuri so kake muyi rana?Nuraddin na gaba dauke da jakankunan ledar biyu, ita kuma na biye dashi a baya dauke da mushenzakaran jakar Nuraddin. Duk inda ta wuce, sai tabar iskar gurin da madaukakin kamshin turaren dake jikinta, tana tafiya iska na kada siraran gashin kanta wadanda ke kokarin fitowa ta ciki farin gyalenta mai raga-raga dake lullube da kanta.Hajara ta fito daga daki a dai- dai lokacin da yaran biyun suka ratso tsakar gidan. Badawiyya tayi sauri ta durkusa."mama ina kwana?""Lafiya lau Badawiyya", Mahaifiyar Nuraddin ta amsa, sannan kuma ta dubi Badawiyya. "oh 'yar nan bakya rabuwa da wahala, ko yaushe dai sai kinyi masa wahala, 'Badawiyya ta sunkuyar da kai cikin girmamawada alkunya tace a hankali."ba.... Babu komai mama"."An gode to, Allah ya saka miki Badawiyya." mahaifiyar Nuraddin tace da ita sannan ta juyo ga Nuraddin."Ga wannan ka tafi da ita, malam ne yace a baka, maganin tsautsayi ce, yace duk inda zaka, ka rinka tafiya da ita," Ta mika masa wata 'yar kankanuwar laya wacce aka rufeta da jara fata.Nuraddin ya karba, ya dubi Badawiyya suka yiwa juna murmushi, sannan sai yara biyun suka juya suka tafi."Allah ya kiyaye Nura." mahaifiyarsatace dasu."To mama saina dawo.Koda yaran suka fice daga gidan saibabar Nuraddin ta dubesu sannan ta Dubi Badawiyya ta girgiza kai sannan tace cikin zuciyarta "kai wannan soyayya ta yaran nan da ban mamaki take, yanzu ace yarinyakamar wannan ta makalewa wannan yaro wanda shi ba komai ba, to, meyiyuwa dai shima farin jinin malam zai biyo." sai kuma abinda bata sani ba shine farin jini ma yanzu ya fara, domin kuwa bada dadewa ba farin jinin zai sake hada shi da wata sabuwar budurwar mai ban mamaki.*** *** ***Nuraddin ya mika, sannan yayi wanikwakwaran fito ya dirgo daga kan gado, ya dubi sauran gadajen dake dakin babu kowa akansu sai gado daya wanda Auwalu surajo ke kwance a kai yana karatu. Karfe tarada rabi na dare, duk sauran daliban dake daikin sun tafi ajujuwan karatunsu domin bitar abinda aka koya musu.Nuraddin ya durkusa karka shin gadonsa ya janyo akwatinsa, sannan ya bude ciki. A lafe a kasan akwatin, kudin kusan Naira dubu biyar duk Badawiyya ce ta bashi kudin. Nuraddin ya zaro dari daga cikin kudin ya tura ciki aljihun gaban rigarsa. Sannan ne yaji motsia bayansa, yayi firgigit cikin sauri yarufe jakarsa don gudun kada wanda ke shigowa yaga kudin da yake ciki. Duk yake dai Nuraddin yasan babu wani shege a cewarsa, daya isa ya taba kayansa koda wasa ballanta nada sunan sata, amma yasan in an tambaye shi dole shima ya bayar, tunda ana bashi, wannan shiyasa baya son asan yanada kudi da yawa."Mene ne na boyewa ai mu dama ganin falleliyar babynnan ta kawokacikin arniyar motar nan munsan da karfinka ka dira.Nuraddin ya juyo domin ganin mai maganar, duk da dai kafin ya juya ma yasan duk daniyar ba mai muryar nan sai wazirinsa Nafi'u {BOSS}."shegen duniya daga ina haka, dakin karatu ko makaranta?" Nuraddin yace sannan ya mika masa hannu suka tafa tas! Kamar an mari jaki da faranti."wace irin makaranta kuma banda wannan da muke ciki?" Nafi'u boss ya tambaya lokaci guda kuma ya zauna bakin gadon Nuraddin."Ku dubu allonku daya nake nufi".Oh shet! Men, ai abin da ya kawo ni kenan, ance kuwa fim din yau wani arnen Indiya ne, ana fadamin labarin sai ka fado min a rai, to ni sam-sam ban dauka ka bayyana ba to shine hamza siyasiya ya ce min ai dazu yaga bayyanarka kuma wai wata ba kyau din beby ce ta kawoka,nan da nan na garzayo, domin yau duk aljihun ka zamu shiga sinimar nan dan bai yiyuwa fim din nan ya wuce mu". Nafi'u boss yace ya dan tsagaita yana mayar da numfashi."to uban shegen surutu ka gama tsarani din?""Ah! Haba Nuri namu, kai kasan ai mu da kai haka muke". Ya hada tafikan hannunsa biyu guri guda."wai ina su Basiru logarizim ne?" Nuraddin ya tamba.Duk suna can bayan 'central hall' kai muke jira kawai yau duk aljihunka zamu shiga sinima kai harsigari ma yau ba mai siya da kudinsa...... Aljani Ya Taka Wuta!..2 ; ; sunyi sanadiyar faduwar dalibai da dama jarabawa, haka nan tun da suka shigo makarantar basu da aiki sai shiririta, yau kusan shekaransu shida kenan, wannan itace shekaransu ta karshe a sakandiren. Da yawa daga cikin su suna zuwa makarantar ne kawai don ace sun gama, amma badan su sami sa kamako mai kyauba. Ba kowanne mutum bane, ba kuma ko wanne mai karfin zuciya bane zai baƙin kungurumin dajin dake tsakanin makarantar zuwa cikin gari ba, domin tafiyar kusan kilo mita biyar ne zuwa cikin garin, an kuma ce zai hanyar cike take da aljanu da kwumakwumai, amma hakan bai tsorata su ba musamman Nuruddin, domin shi ko babu mai zuwa zai gwab kama hanya abinsa shi kaɗai, dole ne sai yaje. Anyi musu nasiha sunkiji an horesu da bulala duk banza kai har wa'azi na anyi musu. Malam mahmud bashir malamin arabiyyane a makarantarsu Nuruddin ya taɓa cewa dasu watarana suna ɗaukar darasi " kuyi a hankali yara, mun sami labarin akwai wasu takadarai acikin ku waɗanda kullum kwanan duniya sai sun shiga gari sunyi kallo a sinima, to ina shawartarku ku da ku bari, ba don komai ba kuma sai don lafiyar ku, kunsha da jin haɗarin dake tattare da wannan dajin na irin kwankwamai dake ciki, amma don taurin kai ku nace sai kun fita cikin dare. To wallahi kuyi a hankali inba so kuke watarana wani ya farka a cikinku da siririn hannu shanyayye kamar lagwanin risho ba " yaran suka fashe da dariya to amma nasihar malam mahmud bashir tamkar zuga ce ga takadaran yaran biyar. "kai rabu dashi ajawo, muzai yiwa wa'azi da wani dogon gemunsa kamar buroshin wanke kwalabe ". Nuruddin yace da yaran su kuma suka bushe da dariya. Watanni biyar kenan da faruwan hakan. **** Cikin sinimar ya dauki hayaniya lokacin da bangwaleliyar kalmar *{ THE END }* ta yiwa kanta gurin zama a kan farin allon sinimar. Ba a dade ba su Nuraddin suka fito, suka kamo hanyar dawowa makarantar karfe daya da rabi na dare, domin ranar fim biyu akayi a sinimar.Yaran biyar suka keto cikin bakin daji, bakajin komai sai hayaniyar yaran wadanda ke tafiya sunata hayaniya gami da tada kura kamar shanu. Babu alamar farin wata a cikin dajin, babu kuma wani kwakkwaran sauti sai jefi-jefin kukan gyare dana tsuntsaye nan da can."Kai ku tsayani na taka kaya." basiru logarizim yace dasu."Gafara can malam waye zai tsayaka, ka kwana ma a nan mana waya damu da kai". Nuraddin yace dashi."To kada ku tsaya din mana wata tsiyar ce". Sauran yaran suka busheda dariya sannan sukayi gaba suka barshi gurin tsugunne yana ko ƙarincire kayar.Basu dade da barinsa ba, sai basiru yaji motsi a bayansa yana juyawa sai sukayi ido biyu da wata katuwar kyanwa baƙa ƙirin da ita kamar kwanta. Idanunta jajaye suna sheki kamar kwalba a cikin rana. Basiru ya dubi magen itama ta dubeshi , iska taci gaba da karkada ganyayyakin bishiyoyin dake zagaye sannan ya rarumi wani bushashen itacen bishiya dake kusa da shi ya nufo magen, amma sai taki guduwa."Ah! Kaga marar kunya! Basiru ya fada cikin karaji sannan sai ya ɗaga itacen yakai mata duka. Tun kafin itacen yakai ga kan magen yaji hannunsa ya yi sakh yayi lararraf dashi kamar tsumma, babu nauyi, ga mamakinsa sai yaga hannun yana motsewa a hankali a hankali har ya koma kamar kaurin kyandir, sannan sai yaji hannun nasa ya fado jikinsa tamkar dama ba a jikinsa yake ba."wayyo Allah na shiga uku! Ah! Ah! Ah! Nura! Dan Allah kuzo na shiga uku.....Na lalace".Sannan sai wata kakkausar murya ta kece da dariya, muryar babu dadin ji kamar muryar jaki.Ihun da suka ji a bayansu, shiyasa su juyowa lokaci guda tamkar sojoji yayin faretin ban girma a gaban shugaban kasa."Kunji wannan shegen kamar sunana yake kira, ihun menen...Sauran maganar ta makale a fatar bakin nuraddin lokacin da sukaji an sake ihun, a wannan karon har da kuka. Yara hudun suka dubi juna sannan suka dubi ciki duhun dajin inda suka baro Basiru. Kuzo mu ko mu gano shi. Nuraddin yace da sauran ko wannensu tsumayake, sun gama tsorata don haka sai sukayi sororo kamar gumaka suna kallon Nuraddin."ko bakwaji nane? ¤¤¤¤ A dai dai lokacin ne suka hangi basiru ya ratso cikin duhun dajin yana tafiya yana hada hanya kamar dan giya hannunsa na hagu a dafe ahannunsa na dama yana kuka, sannan sai kakkausar muryar mai kama data jaki ta sake kecewa da dariya. Yaran suka fara waige waigecikin firgici a tsorace sai dai kuma basu ga mai dariyar ba, duk abin nan da akeyi, shi Nuraddin ko ajikinsa, domin idan akwai wani abuda ake kira tsoro a duniya shi baima sanshi ba."yau ga shegantakar banza inba tsoro ba a fito fili mana!" Nuraddin yace cikin karaji. Dajin ya amsa kuwwar abin da yace.Cikin firgici, Nafi'u Boss ya matso kusa daf da Nura ya dakeshi a baya."Me...Menene kuma haka nura, so kake a halaka mu a banza?" Yace bakinsa na rawa.Nuraddin ya buge hannunsa gefe guda sannan yayi sauri ya tari Basiru wanda ke tafe yana tangadi kamar dan giya. Nuraddin na taba shi sai basiru ya zube kasa yana kuka. Aljani ya Taka Wuta!.....3 - - - yana tangadi kamar dan giya. Nuraddin na taba shi sai basiru ya zube kasa yana kuka, yamu sashshen shanyayyen hannunsa ya fadi gefe guda sharaf kamar mushen maciji.Wata sassanyar iska ta fara busawatsakanin yara biyar gashi dai ba lokacin sanyi bane amma iskar tafi iskar sanyi sanyaya kashi da bargo. Nuraddin yaji gashin jikinsa duk sun mimmike. Ko kusa ko alama, dafarko Nuraddin bai tsorata da ihun da yaji ba, to amma ba karamar girgiza yayi ba lokacin dayaga hannun basiru ya tsotse ya yamushe tamkar lawashin albasa a cikin rana. Ba karamin bala'i bane ace 'yan mintoci kadan kuna tare damutum kowa da hannayensa biyu, amma kuma tsakanin wani dan lokaci ace hannunsa dayan ya shanye ya zamama daya da rabi.Nuraddin ya tallafi Basiru ya tashe shi tsaye sannan yace da sauran kuzo mu tafi.Samarin suka bishi a baya sumu-sumu ba magana. Fara tafiyar ke da wuya sai karfin iskar yafara karuwa, saida takai ta kawo samarin na tafiya da kyar sbd karfin iska. Wannan al'amari shi yasa samari biyar din suka dada rikicewa, tuni sun fara tunanin anya kuwa zasu koma da hannunsu bibiyu? Kamar hadin baki lokaci guda sai kowanne daga cikin yaran banda Nuraddin goggoya hannayensu a bayansu wai a tunaninsu yin hakan na iya kare hannayensu daga shanyewa irin na Basiru. Abinda yafi basu tsoro shineduk irin mahaukaciyar iskar dake karkadasu tana wasa dasu kamar shanya hakan baisa koda ganye daya daga cikin ganyayen bishiyoyin dake wajen motsi ba. Hakan shaya tabbatar musu cewa iskar sukadai take kadawa a cikin dajin domin inhar basu kadai take karkadawa ba yaya to ganyen bishiya baya motsi?Adai dai lokacin samarin dake ratsawa ta cikin iskar domin tsira daransu, sai kwatsam wani abu ya bayyana a gabansu. Babu zato babutsammani wani mai kamar bakin labule ya ziraro gabansu. Saboda tsananin duhun dake gurin idan suka juya baya basa hango bayansu. Adai-dai lokacin ne kakkausar muryar ta sake kecewa da dariya mai hargitsa hanjin cikin mutum, awannan karon dariyar harda kyakyatawa. Su Nuraddin sukayi tsumu suna dube-dube ga iskar na kadawa amma gumi kamar ruwa ake zuba musu a jiki, da zaka tsaga wani acikinsu dazaiyi wuya ka sami jini ajikinsu saboda firgici."kudaina waige-waige! Domin kuwaduk wani waige-waigenku bazai iya hango muku ni gaba dayana, sai daikuna iya ganin tsakiyar kaina duhunda kuke gani a gabanku ba duhu bane nice na tsare hanyar tsakiyar kaina kuke gani haka bakin kirin".Kaukausar muryar tayi shiru ga barin magana mummuna sannan sai taci gaba da cewa. "daga yau saiyau, kada na kara ganinku akan hanyar nan cikin dare, domin nan hanyar mahaifina ce ba taku bace, in banda rashin kunyarku ta bil'adama ina ku ina bin hanyar sarkin sarakunan aljanun duniya. Zan baku hanya ku wuce' sai dai kuma duk wanda ya sake tunanin karan banin b tanan gurin to na tabbatar masa cewa saina nannadeshi kamar alkaki.Kamar budin ido kakkausar muryar nayin shir duhu ya yaye iskar ta tsaya cak, sannan sai dajin ya dawokamar yadda yake. Yaran suka dubi juna jikinsu na diga kamar an narkasu sbd gumi. In banda shanyayyen hannun Basiru da sai ka rantse da Allah babu abinda ya faru.Yara ukun suka dubi Nuraddin wanda ke rungume da basiru, sannan kamar daman sun shawarcijuna sai suka ruga da gudu suka nufi hanyar makaranta.Basiru ya dubi yace yanzu kaima guduwa zakayi ka barni?"Haba Basiru ah ko nawa hannun zata shanye bazan gudu na barka ba. Bakomai Basiru ka barni da ita zamu sake haduwane"."Tayaya zaku hadu? Basiru ya tambaya har yanzu a jingine yake ajikin Nuraddin."Bata ce kada musake biyo hanyar nan ba, to wallahi ni banga uban da ya isa ya hanani bita hanyar nan ba tunda ba hanyar ubanta bace......Kafinya rufe bakinsa, sai yaji muryar nan na cewa kayi a hankali marar kunya idan baso kake na nanna deka ba! Dajin.........Nuraddin ya dubi basiru wanda tuni ya sume a jikinsa saboda tsoro. Don haka sai ya sungumeshi kamardamin itace ya dorashi a kafada ya kama hanyar makaranta dashi. Yana tafiya shanyayyen hannun basiru na dukan gadon bayansa. Fara tafiyar keda wuya sai yaji mummunar muryar ta sake kecewa da dariya. Daga nan kuma ba'a sakecewa dashi komai ba."zaki yi dariya"! Nuraddin yace a fusace. - **** **** **** Tun acikin daren da al'amarin ya faru labarin ya iske duk kusan rabin makarantar, sannan kafin tara na safiya ranar, labarin ya gama mamaye cikin gari kamar wutar daji.Mutane sukai ta bada labari iri-iri nagaskiya dana karya. A cewar wani mai gadin makarantar wanda ke bada labari a cikin gari, yace duk kusan yara biyar din shanyayyen hannu suka shigo makarantar, kuma wai kowannensu da ido daya yadawo, sannan kuma ya dada da cewar wai duk agabansa aka wuce da yara biyar din duk kuwa da cewarrabonsa da gadin dare tun wancan satin da ya wuce.A safiyar ranar aka tara daliban makarantar gaba dayansu a gurin taron dalibai, sannan malam mahmud malamin arabiya ya sake yin nasiha gami da dada jan kunnen dalibai. ALJANI YA TAKA WUTA 4. Nuraddin ya yi mika, sanna ya yi wani kwakkwaran fito ya dirgo daga kan gado, ya dubi sauran gadajen da ke dakin babu kowa akansu sai gado daya wanda Auwalu Surajo ke kwance a kai yana karatu. Karfe tara da rabi na dare, duk sauran daliban da ke dakin sun tafi ajujuwan karatunsu domin bitar abinda aka koya musu. Nuraddin ya durkusa karkashin gadonsa ya janyo akwatinsa, sannan ya bude ciki. A lafe a kasan akwatin, kudi ne kusan naira dubu biyar duk Badawiyya ce ta bashi kudin. Nuraddin ya zaro naira dari daga cikin kudin ya tura cikin aljihun gaban rigarsa. Sannan ne to ya ji motsi a bayansa, ya yi firgigit cikin sauri ya rufe jakarsa don gudun kada wanda ke shigowa dakin ya ga kudin da ke ciki. Duk da yake dai Nuraddin ya san babu wani shege a cewarsa, da ya isa ya ta6a kayansa ko da wasa ballantana da sunan sata, amma ya san in an tambayeshi dole ne shima ya bayar, tunda ana bashi, wannan shi ya sa ba ya son a san yana a kudi da yawa. "Mene ne na 6oyewa, ai mu dama ganin wannan falleliyar Bebinnan ta kawo ka cikin arniyar motar nan mun san da karfinka ka dira. Nuraddin ya juyo domin ganin mai maganar, duk da dai kafin ya juya ma ya san duk duniya babu mai muryar nan sai wazirinsa Nafiu (Boss). "Shegen duniya daga ina haka, dakin karatu ko makaranta?" Nuraddin ya ce, sannan ya mika masa hannu suka tafa tas! Kamar an mari jaki da faranti. "Wacce irin makaranta kuma ban da wannan da muke ciki?" Nafiu Boss ya tambaya lokaci guda kuma ya zauna bakin gadon Nuraddin. "Ku dubu allonku daya nake nufi". "Oh Shet! Men, ai abin da ya kawo ni ke nan, an ce kuwa Fim din yau wani arnen Indiya ne, ana fadamin labarin sai ka fado min a rai, to ni sam-sam ban dauka ka bayyana ba, to shi ne Hamza Siyasiya ya ce min ai dazu ya ga bayyanarka kuma wai wata ba kyau din Bebe ce ta kawoka, nan da nan na garzayo, domin duk a aljihunka zamu shiga sinimar nan, dan bai yiwuwa Fim din nan ya wuce mu". Nafiu Boss ya dan tsagaita yana mayar da numfashi. "To uban shegen surutu ka gama tsarani din?" "Ah! Haba Nuri namu, kai ka san ai mu da kai haka muke." Ya hada tafikan hannunsa biyu guri guda. "Wai ina su Basiru Logarizim ne?" Nuraddin ya tambaya. "Duk suna can bayan 'Central Hall' kai kawai muke jira, yau kowa a aljihunka zai shiga kallon fim, kai har sigari ma yau babu me saya da kudinsa." Cikin murmushi sai Nuraddin ya kama hannun Nafiu Boss suka yi waje. Ko da suka nufi kofar Hostel din, sai Nuraddin ya dubi Nafiu ya ce. "Ah, yau zaka shigo da mutuniyar taka ne?q "Wa kenan?" Nafiu ya tambaya yana kallonsa. "Ladi dala-dala mana." "Oh shege Nuri, ashe baka manta ba, kai ma kasan ai dole ne na shigo da ita tunda ka shigo gari." Mintina biyar da yin hakan, sai samarin biyar suka dunguma suka fice daga makarantar zuwa cikin gari. Wadannan samari biyar shedanun mutane ne, domin Allah ne kawai Ya san iya yawan daliban da suka dora akan hanyar banza. Sunyi sanadiyar faduwar dalibai da dama jarabawa, haka nan tun da suka shigo makarantar ba su da aiki sai shiririta, yau kusan shekararsu ta karshe a sakandiren. Da yawa daga cikinsu suna zuwa makarantar ne don kawaia ce sun gama, amma ba dan su sami sakamako mai kyau ba. Ba kowanne mutum ba ne, ba kuma kowanne mai karfin zuciya bane zai iya ratsa bakin kungurmin dajin da ke tsakanin makarantar zuwa cikin gari ba, domin tafiyar kusan kilomita biyar ne zuwa cikin gari, an kuma ce wai hanyar cike take da aljanu da kwankwamai, amma hakan bai ta6a tsorata yaran ba, musamman Nuraddin, domin shi ko da babu mai zuwa zai iya kama hanya abinsa shi kadai, dole ne sai ya je. An yi musu nasiha sun ki ji, an horesu da bulala duk a banza, kai har wa'azai ma an yi musu. Malam Mahmus Bashir malamin Arabiyya ne a makarantar su Nuraddin ya ta6a cewa da su wata rana suna daukar darasi. "Ku yi a hankali,mun samu labarin akwai wasu takadirai a cikinku wadanda kullum kwanan diuniya sai sun shiga gari sun yi kallo a sinima, to ina shawartarku da ku bari, ba don komai ba kuma sai don lafiyarku, kun sha fa jin labarin hadarin da ke tattare da wannan dajin da irin kwankwamai da ke ciki, amma don taurin kai ku nace sai kun fita cikin dare. To wallahi ku yi a hankali in ba so ku ke wata raba wani ya farka a cikinku ya tsinci kansa da siririn hannu shanyayye kamar lagwanin risho ba" Yaran suka fashe da dariya. To amma nasihar malam Mahmud Bashir tamkar zuga ce ga takadiran yaran nan biyar. "Kai rabu da shi ajawo, mu zai yiwa wa'azi da wani dogon gemunsa kamar burushin wanke kwalabe" Nuraddin ya ce da yaran, su kuma suka bushe da dariya. Watanni biyar ke nan da faruwar hakan. BY NAZIR ADAM SALIH. .............ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {5}....... Nuraddin ya dubi basiru wanda tuni ya sume a jikinsa saboda tsoro. Don haka sai ya sungumeshi kamar damin itace ya dorashi a kafada ya kama hanyar makaranta dashi. Yana tafiya shanyayyen hannun basiru na dukan gadon bayansa. Fara tafiyar keda wuya sai yaji mummunar muryar ta sake kecewa da dariya. Daga nan kuma ba'a sake cewa dashi komai ba. "zaki yi dariya"! Nuraddin yace a fusace. * * * Tun acikin daren da al'amarin ya faru labarin ya iske duk kusan rabin makarantar, sannan kafin tara na safiya ranar, labarin ya gama mamaye cikin gari kamar wutar daji. Mutane sukai ta bada labari iri-iri na gaskiya dana karya. A cewar wani mai gadin makarantar wanda ke bada labari a cikin gari, yace duk kusan yara biyar din shanyayyen hannu suka shigo makarantar, kuma wai kowannensu da ido daya yadawo, sannan kuma ya dada da cewar wai duk agabansa aka wuce da yara biyar din duk kuwa da cewar rabonsa da gadin dare tun wancan satin da ya wuce. A safiyar ranar aka tara daliban makarantar gaba dayansu a gurin taron dalibai, sannan malam mahmud malamin arabiya ya sake yin nasiha gami da dada jan kunnen dalibai akan fita daga cikin makarantar. "ku guji fita yawace-yawacen banza marasa amfani cikin dare, kuyi zamanku a makaranta ku karanta littattafan ku yafi muku. Na tabbata indai dalibi ba fita yayi ba to Allah subhanahu wata'ala bazai baiwa kowanne aljani ikon cutar daku ba, "wasu daga cikin dalibai sukayi kabbara. Lokacin da malam mahamud yazo karshen jawabinsa. Daga karshe aka yiwa su Nuraddin horo mai tsanani, sannan aka basu gargadi na karshe wanda daga shi idan suka sake laifi to korarsu za'ayi. "kai! Rabu dasu, wa zasu yiwa wa'azi"! Nuraddin yace da Nafi'u (BOSS) lokacin da suke kan hanyar ajujuwan karatunsu bayan an sallamesu daga gurin asambili. "Ni dai nasan wannan mai muryar jakin bata isa ta hanani fita kallon film din yau ba don wallahi canis za,a yi da 'American film' ballen kuma wa'azin wani mai dogon gemu, 'yar bulalarshi ashirin! Sufa sun dauka wai duka zai hanamu abinda mukeyi ko? Nuraddin ya tambaya yana duban abokinsa Nafi'u. Nafi'u yayi masa irin kallon dazaka yiwa kyankyason daya fada a cikin furaraka yace. "kanka daya kuwa Nura"? "to in ba daya bane ina na baro dayan ko kai da kai biyu kake ganina? Nuradadin yace yana jijjiga littafin dake hannunsa a dai-dai lokacin da suka karaso kusa da ofishin shugaban makarantar. "To inba haka ba mezai sa da hankalinka da komai ka kai kanka ga halaka, aini wallahi ko karatu dare na daina fita, haka kawai naje nima hannuna ya yamushe tab! Ai idan ka ganni a lahira to kaini akai bada kafata naje ba. Nuraddin ya dubeshi ya fashe da dariya. "wallahi bansan kai mugun matsoraci bane sai yau, yanzu kai da haka kake da tsoro har ake kiranka da Boss, to in dai hakane daga yau bani ba kai domin bana abota da matsoraci". "Wallahi tafi nono fari". Nafi'u yace. "Domin idan mutum ya biye ta kai sai ya tsinci kansa a kushewa kwanansa bai kareba. "Ai me rabon ganin badi sai ya gani ko ana ruwan kibiya daga sama da kasa. Nafi'u ya girgiza kai kana ya dubi nuraddin dai dai lokacin da suka kawo kofar ajin. "Kana nufin yauma fita zakayi kenan"? "Ai idan kaji fita daya kenan ma, kai dai tsaya nan kana shirme, haka kawai ka bari wasu kananan kwankwamai da muryar jaki su mayar dakai laushi, ka jirani na dawo na baka labari". Nuraddin ya juya abinsa zai yi gaba. Nafi'u ya sa hannu ya rike rigarsa ta baya. "Nura kaga fa wallahi........" Bai karasa ba Nuraddin ya tankwabe hannunsa yana zazzare idanu. "Kada ka bata bakinka Nafi'u domin banga dalilin dazaisa ta shanyewa dan uwanmu hannu ba mu kyaleta tunda tace kada mu sake bi ta hanyar, to ni yau saina bi na tambayeta dalilin shanewa dan uwanmu hannu." yayi shiru sannan batare da ya dubi Nafi'u ba wai kai Nafi'u (BOSS), to in gaskiya ne yau ka biyoni muga iyakacin taurin kanka". Nuraddin ya wuce cikin ajinsu ya bar Nafi'u nan tsaye yana kirga takun sawunsa. "Mahaukaci ne, tabbas mahauka cine. Babu mamaki abinda ya faru jiya ya tabashi". Nafi'u yace da kansa. Nuraddain ya shiga ajin Nafi'u na

Chapter 1 of 6