Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
da gine ginen alfarma iri-iri. Adai dai lokacin ne muka kawo ga wata katuwar kofa tsayinta ya kusan tokare. Sararin samaniya. Amal ta dubeshi tace. "kada kaji tsoro, nan gidanku ne babu abinda za'ayi maka". Kofar garin tayi kara mai kamar rugugin aradu, sannan sai ta bude a hankali wata shintimemiyar halitta ta fito harshen halittar guda biyu ne manya manyan kamar tabarma. Fitowarsa keda wuya sai aljanin ya zuro harsunansa waje ya shimfidasu gaban Nuraddin da Amal. Nuraddin yayi baya cikin razana. "kada kaji tsoro Nuraddin, hau daya harshen nima na hau daya, akansa za'a kaimu zuwa fadar mahaifina". A dai dai lokacin ne to wata katuwar murya tayi ihu mai tsanani sannan tace. "Allah ya kiyaye wani dan Adam ya aureki bani ba"!! Kafin kiftawa da bisimillah sai wani farin hayaki ya fara mamaye ko wanne sashe dake katuwar kofar. "Amal!!" Nuraddin ya kwala mata kira a gigice domin baya iya ganinta saboda hayakin. A dai-dai lokacin da duk wannan ke faruwa, Badawiyya na can kwance male-male akan gadonta tana barcin. Acikin barcin nata ne tayi mafarkin wai suna cikin tafiya ita da Nuraddin aciki wani kungurmin bakin daji, sai suka hango wata mage ta nufosu da gudu tana zuwa gabansu saita rikida da ta zama wata jibgegiyar mata, mai zako-zakon hakora kamar kibiya, jikinta duk gashi kamar na tunkiya. A lokacin ta zaro tafka-tafkan hannayenta ta kama wuyan Nuraddin zata yi sama dashi. Badawiyya ta kwala ihu a rude sa'ar da taga abin dake shirin faruwa. A hakan hajiya habiba mahaifiyarta ta sameta ta kankame matashin kai tana ihu. "ke menene"? Badawiyya ta yi firgigit ta tashi zaune, sukayi ido biyu da mahaifiyar ta. "momi, wallahi wani mummunan mafarki nake". "kuma dan kina mafarki sai kiyi ta ihu, bazaki ambaci sunan Allah ba? Duk abinda ya sameki na masifa sai kice innalillahi wa inna'ilaihirraji'un". Badawiyya ta sunkuyar da kanta tana tunanin mummunar matar dake kokarin dauke mata Nuraddin. "kada na sake ganin kina ihu a mafarki, addu'a akeyi ba ihu ba". Mahaifiyarta ta kuma fadi sannan ta fice daga dakin ta koma dakinta. Karfe uku na dare abin ya faru, to amma har gari ya waye Badawiyya bata sake komawa baccin ba. Washe gari da yamma misalin karfe shida Badawiyya na zaune a dakinta. Sai tunani Nuri 'DARLING' dinta ya fado mata. Ta mike tsaye a hankali ta fara suntiri a cikin. Oh! Nuri 'DARLING' yanzu yana can makaranta ko me yake yi yanzu? Ta tambayi kanta. Sannan ne to idanunta ya kawo ga ZOBEN da Nuraddin ya bata. Asannan nima lokaci yayi. Sai gobe da safe.. ALJANI YA TAKA WUTA!_14 ' ' Ko da Amal ta dubi idanunta saitaga kamanninta sun fara sauyawa daga na firgita zuwa na wani yanayi da ban. "Badawiyya". Amal ta kira sunanta. "inaso ki fahimci cewa koda ada can Nuraddin masoyinki ne, to ki yarda cewa yanzu ya miki nisa, domin na fiki sonsa, na kuma fiki daukaka, iko da karfin mulki ballanta kuma uwa uba kyawu. Wannan itace maganar data raboni da Nuraddin nazo gareki na sanar dake cewa daga yau babu ke babu shi"! - Badawiyya taji kamar Amal ta watsa mata wuta a fuska. *NA RABU DA NURADDIN? Tab! Ai kuwa sai dai mutuwa, kai ba 'yar gidan aljanu ba, ko 'yar gidan balbalin bala'i ce bata isa ba. "kada ki bata bakinki"! Badawiyya tace cikin fushi tana dubanta acikin madubin. "Bazan rabu da Nuri ba, babu kuma wanda ya isa ya rabani dashi sai Allah". Ta danyi shiru tana duban Amal, wacce ke tsaye acikin madubin cikin kaduwar ganin wacce keyi mata magiya tana rokonta kuma yanzu ta birkice take fada mata bakaken maganganu. "kuma naji abin da kika fada 'yar gidan sarkin aljanu, kince kin fini mulki, da iko da dukiya, da kuma kyawu to duk naji na yarda, domin duk Allah ne ke bada su ba mutum ba ko aljani. Amma kin san dai cewa duk halittar ubangiji babu wacce tafi mutum daraja, kuma kyawun da kike takama dashi ai na karyane domin a siffarmu ta 'yan adam kika fito min, in gaskiyane ki koma kirarku mana ta aljanu sai muyi takarar kyawun...." "Ke! Marar kunya kisan abinda yake fita daga bakinki in kuma ba hakaba wallahi zakiyi nadama". Amal tace a fusace. "Rashin kunya ba gadonta akeyi ba Amal agurinki na koya, wahala kuma ko nadama indai akan Nuri Darling ne to hutuce agareni. Bazan barshi ba kuma barin na maimaita miki babu abin da ya isa rabani da Nuri sai ko mutuwa. Haba Amal tunfa ina 'yar kankanuwa Allah ya dasa harsashin kaunarsa a raina, ina girma itama kaunar na girma cikin zuciyata, tare muka girma shine jini, tsoka, kashi, bargo, ke shine rabin ruhin raina. Shi bakiji sunansa ba ne Nuri? Ma'ana hasken raina. Koma garinku Amal ki auri dan uwanki aljani mai kan karfe, NURI kam nawane". Amal 'yar sarkin aljanu tayi sororo cikin tsananin takaici da kaduwa tana duban Badawiyya. Dakiku ashirin suka shude Amal na tsaye ta kasa cewa komai. Can sata nisa tace. "Nagode Badawiyya, daman kunce jiki magayi to jikinki zai gaya miki, kada ki tsorata domin bake zan taba ba, Nuri naki zan nannade na mayar dashi kamar abinciku alkaki, fitsari da kashi sai a kwance inyaso ki aureshi haka ki nuna min kin fini kaunarsa ko"? "Na daina tsoronki Amal kuma kada ki sake cewa ina tsoronki, abinda ya dazuma nake baki hakuri na dauka wani abune dabam ya kawoki, amma indai zancen ki rabani da Nuri ne to bani ba tsoronki har abada, nasan dai bai wuce kice zaki nakasa shiba, ko ki kasheni, to bari kiji Amal indai in rabu da Nurine, saidai kiyi duk abinda kikayi niyya, domin rabuwa dashi sunfi mutuwa ko nakasa zafi a gareni". Badawiyya ta mike tsaye tana duban Amal, tawul din wankan dake daure a jikinta rike a hannunta na hagun. "shikenan Badawiyya ma jiyi ma gani, a ga wanda zai gaza". Amal tace. Sannan tayi shiru tana duban zobenta da ta bawa Nuraddin a hannun Badawiyya cikin takaici. Amal taji zuciyarta kamar ta fashe da kuka. Mahaifinta yasha bata tarihin zobunan guda uku, biyun da suke hannunta da kuma wanda ke hannun Badawiyya a yanzu. Mahaifinta yasha cewa da ita. "Wannan zoben yafi shekara dubu biyar a gurina tun zamani annabi sulaiman {A.S} yake, zoben alkawarine, dan haka ki rikeshi da kyau kuma kada ki sake ki cutar da duk bil'adaman dake sanye da daya daga cikin zobunan guda uku, idan kuwa kika aitata sabanin haka, to ki kuka da kanki domin nannadewa zakiyi ki zama gurguwa baiwa wulakantacciya a cikin jinsin aljanu, kiyi ta yawo a kwararo da lungu-lungun duniya cikin kazanta". Tunanin wannan dogon jawabi na mahaifinta, da kuma fargabar abinda zai biyo baya, shiya hana Amal ta nannadewa Badawiyya kafafu da hannu. Kai in ba don zoben dake hannunta ba, da saita kakkaryata ta shanye bargonta. "sai gani na biyu Badawiyya huduwar da ina tabbatar miki da cewa bazata zamo alkhairi agareki ba, kuma aure ni da Nuraddin kamar anyi ne, kinga yanzu haka ma muna tare dashi a kofar gidanmu zamu shiga su gaisa da mahaifina sai kawai naji kinyi kirana". Badawiyya ta dubi Amal cikin rashin fahimta tace. "kamar yaya nayi kiranki, kufa Aljanu bakwa rabuwa da karya da yawan son wasa, yanzu ke ko kunyar fada bakya yi wai kuna tare dashi? To Allah yasaa ma baya garinnan, yana makaranta. Kuma da zaki ce nayi kiranki yaushe na kiraki"? Amal ta dubi zoben dake hannun Badawiyya ta girgiza kai. Zakisan yadda akayi kikayi kirana, amma sai nan gaba, kuma sai kinyi nadama marar kunya. ALJANI YA TAKA WUTA!__15 - - - ...Wani bakin hayaki ya turnuke dakin sannan lokaci guda sai ya washe. Badawiyya taja da baya cikin kaduwa, sa'ar da bakin hayakin ya washe, sai ta sake duban madubin. Babu alamar kyakykyawar surar Amal sama ko kasa ta bace. Adaidai lokacinne kofar dakin ta bude, "keda wa naji kina magana yanzunnan"? Badawiyya ta nufi mahaifiyarta da gudu ta rungumeta sannan ta fashe da kuka wiwi. **** "Amal! Nuraddin ya sake kwalawa Amal kira karo na biyu daidai lokacin da farin hayakin yaci gaba da tunuke gurin. Tuni Nuraddin ya fara zargin kansa da wautar da yayi, wai soyayya da aljana, kuma dan karin sabon haukama wai har ya amince ya biyota garinsu, togashi nan yanzu ta kawo shi gaban mai dogo harshe mai muryar jaki suna kokarin hallaka shi. Nuraddin yaji kamar akan iska yake ninkaya domin kafafunsa basa taba kasa, amma duk ba wannan bace tafi bashi tsoroba, sai muryar nan da yaji mai amon kukan jaki tana cewa dashi wai ya rabu da Amal ba mai aurenta sai ni. Yanzu inba dan rigima ma irin tawa ba ina ni ina takarar budurwar aljanu, kuma aljanun ma masu muryar jaki? Nuraddin ya tambayi fuskars. Adai dai lokacinne ba zato ba tsammani sai farin hayakin ya washe tamkar ma ba'ayi shiba Nuraddin ya dubi inda yake fuskanta cikin mamaki domin har yanzu dai yana nan tsaye gindin katangar nan, hakannan kuma dankareren aljanin nan mai dogon harshe na tsaye yana zalo- zalo da harshensa kamar tabarma. "Kada kaji tsoro". Wata muryar tace da Nuraddin wacce daga baya ya fihimci ashe muryar aljanin nance mai dogon harshe. "kai bakonmu ne, bazamu cutar dakaiba. Muryar daka ji tana yi maka tsawa ta wani shaidanin dan sarkin ce daga cikin kananan sarakunan aljanu. Ya dade yana son ya auri Amal amma taki amince masa, bata kaunarsa koda kwayar zarra. Ya cika nacin tsiya, munsha yi masa kashedin ya rabu da ita kuma kada ya sake zuwa gidan nan amma yaki, to yau munyi maganinsa, domin a yanzu haka yana can cikin karkashin kasa mun daure shi, saboda tsawar da yayi maka a matsayinka na babban bakon sarkinmu. Don haka a madadin sauran aljanu ni babban maigadin gidan sarkin aljanu inayi maka barka da zuwa mijin gimbiya". Koda aljanin ya gama dogon jawabinsa, sai Nuraddin ya bude baki da niyyar ya tambayeshi inda Amal ta tafi ta barshi. Kafin ya tambayane to Amal ta sake bayyana a gabansa cikin sauri kamar an jehota daga sama. "kayi hakuri Nuraddin," Amal tace "Wallahi kiran gaggawa akayi min shine na tafi, amma daman nasan babu abinda zai sameka, shiyasa na bar maigadinmu ya kula da kai kada nacaccen nan ya tabamin kai". "Ina kika je"? Amal ta dubi Nuraddin sannan ta sunkuyar dakai Bazata iya fada masa cewa daga wurin Badawiyya take ba ballantaoa kuma azo ga zancen alkawarin da tayiwa Badawiyya na nannade shi. Don haka ba tare da ta iya hada idanu dashi ba tace. "Al'adar gidanmu ce duk lokacin dakazo da bako mai mahimmanci kamarka, sai anyi kiranka kayi bayanin cewa kun karaso, sannan sai a shigo da bakon. Nuraddin ya dubeta cikin rashin gamsuwa, ko shakka babu yasan karya take. Amal ta sake matsowa kusa dashi taci gaba da cewa ina fatan ka gamsu"? Nuraddin ya gyada kai baiyi magana ba. "To ai sai mu tafi ko"? Tace dashi. Kafin kiftawa da bismillah, katon aljanin nan maigadi ya shimfida dogon harshensa mai kamar tabarma. Suka hau sannan yayi sama dasu ya tsallake katangar gidan. Har sa'ar da aka ajiye Nuraddi agaban sarkin aljanu bai daina zargin kansa da wauta ba, haka nan yayi wa kansa alkawarin inhar ta mayar dashi makaranta bazai sake binta ko ina ba. A wani bangaren na zuciyarsa ma saida ya fara tunanin anya kuwa zai iya ci gaba da soyayya da ita? Nuraddin ya dago kansa a hankali cikin fargaba, yana kallon aljanun da sukayi sahu- sahu a fadar sarkin aljanu. Tun da yake, bai taba ganin halitta mai ban tsoro da muni irin tasu ba. Fadar cike take makil da jinsin aljanu iri-iri, kuma tun daga kan bakake da fararen aljanu zuwa kan masu faka fakan kunnuwa kamar faranti, kai wasu babu kunnuwan gaba daya, haka wasu zako-zakon hakora da manyan kunnuwa, wasu kuma manyan kawuna kamar goran kamun kifi, wasu kuwa 'yan kawunansu gwanin ban dariya, domin 'yan kananane kamar dunkulen fura, sai katon uban jiki kamar giwaye. Nuraddin ya dubi surukinsa sarkin sarakuna mai mulkin Aljanu wato mahaifin Amal, sai yaga kansa kamar an taka gwanda da tayar mota, kunnensa daya ido daya haka nan hancinsa dogone kamar karas. "ka rike alkawari Nuraddin," sarkin Aljanu ya fara jawabi, yayin da sauran aljanu sukayi tsit suna da faman fifita da faka-fakan kunnuwansu. "Muna farin ciki dakai, kuma in dai zaka rike alkawari, to zan baka 'yata Amal ka aura domin tace duk duniya babu wanda take kauna sai kai, bisa wannan dalili dole ne nin na kaunace ka, domin duk abin da take kauna nima ina kaunarsa. Yaya kake gani, zaka iya rike alkawari zaka kuma aureta?? Aljani YaTaka Wuta!....16 - - ...abin da take kauna nima ina kaunarsa. Yaya kake gani, zaka iya rike alkawari zaka kuma aureta?? "Kuyi hakuri ansamu typin errors a wannan page na littafin " - Tun fara hangenta daga nesa Nuraddin ya fadawa kansa cewa lallai ba lafiya ba, domin fuskarta murtuk! Take a hade, kuma abinda ya kara sashi kaduwa ma shine harya kusa isa gurinta Badawiyya bata saki fuskarta ba ballantama tayi masa murmushin nan na alkawari data saba yi masa maimakon haka ma sai harara. Nuraddin ya matsa kusa da Badawiyya a hankali wacce hannunta ke dafe da saman motar kirar Toyota da aka kawota a ciki, fuskarta na duban kasa, akwai wani yanayi dake kan fuskarta wanda yasa 'yar autar hantar cikin Nuri kadawa. "sannu da zuwa". Nuraddin yace da ita sa'ar da ya dada matsawa kusa da ita. "sannunka dai". Badawiyya ta fada a yatsine. Tayi shiru bata sake cewa kala ba. "Badawiyya meke faruwane ina fatan dai lafiya"? Nuri ya tambayeta cikin damuwa. "Lafiyar kenan". Badawiyya tace sannan tayi ajiyar zuciya ta sunkuyar da kanta kasa tana duban inuwarta ajin mota. Nuraddin ya sake dubanta cikin tsananin damuwa sannan ya dan dauke kansa gefe guda ya dubi can cikin farfajiyar makarantar inda dalibai ke ta harkokin gabansu. "Badawiyya kada ki boyemin komai in wani abune ki sanar dani mana kin barni cikin zulumi da damuwa, ni kuma nasan ba wani abu na miki ba tunda shekaran jiya-jiyan nan fa kika zo da farin ciki da sanyi rai muka rabu dake amma gashi yanzu kinzo ranki a hade ni...ni dai na kasa gane wannan abu"? "nace dakai babu komai, in kuma zuwa gurin naka danayi baka so to sai nayi tafiya". Badawiyya tace fuskarta a murtuke. Cikin damuwa, Nuraddin ya lalubi aljihunsa ya zaro kyalle daga goshinsa. "kada kiyi min haka Badawiyya, alkawarin dake tsakanina dake baice haka ba, ki tuna fa tun muna yara muke son juna, wani sabani makamancin wannan bai taba shiga tsakaninmu ba, in kuwa hakane mezai sa yanzu ki rufe idonki a kaina"? Ya danyi shiru yana mayar da numfashi. "idan kuma laifi nayi miki batare dana sani ba ki fada mana saina baki hakuri tunda dai Allah ya halicci kaunarki cikin zuciyata". Jin haka shiya sa Badawiyya ajiyar zuciya sannan ta dago kai ta dubeshi da dara-daran idanunta tace. "Nuri meye hadinka da aljana"? Numfashin Nuraddin ya dauke. Daman ni nasa a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Ya fada cikin ransa. "Ban fahimce ki ba". Ya fada a fili. Lokaci guda kuma ya fara kokarin sa alamun rashin fahimtarta akan fuskarsa duk kuwa da cewa zuciyarsa ta dade da zargin abinda ya faru. "Nace inda alkawarin kamar yadda ka gama fada meye hadinka da aljana? Badawiyya ta sake maimaitawa. Wani sassanyan gumi ya fara sartu wuyansa ya gangaro har zuwa ramin tsakar bayansa. "Badawiyya waye inba mahaukaci ba zaiyi soyayya da aljana," Nuraddin yace cikin karfin hali yana girgiza kai. "Gaskiya nin Badawiyya duk kin rudani...ni yau na kasa fahimtar inda kika sa gaba". Badawiyya ta dube shi tana kokarin karantar fuskarsa sannan tace. Mu shiga daga cikin motar in fahimtar dakai, labarin nada yawa". Tana fadin haka sai ta bude gidan baya na motar ta zauna. Nuraddi jiki ba kwari, ya shiga ya zauna a kusa da ita yanata sakar zuci. Badawiyya tadanyi shiru na lokaci tana hangen direban daya kawota wanda ke can gefe guda kusa da wata tsohuwar rijiya da dalibai kan dauki ruwa idan ana wahalar ruwa a makarantar. "Nuri" ta kira sunan a sanyaye, sannan taci gaba da cewa. "wata aljana ce ta bayyana kanta agareni tace duk duniyar nan ba wanda take so ta aura sai kai". Kusan tsawon mintuna arba'in kenan Nuraddin na zaune yana sauraron abin al'ajabi daga bakin masoyiyarsa Badawiyya. Ko shakka baya yi duk abinda tace sunyi da Amal 'yar sarkin aljanu gaskiya ne, domin ganau ne ba jiyau ba. A daidai lokacin da Nuraddin ya fara jin kamar kansa zai rabe gida biyu saboda firgicin labarin, sai Badawiyya tayi ajiyar zuciya, ta kare zancenta da cewa. " shin to kai Nuri, a ina kuka hadu da ita? Nuraddin yayi murmushin yake yace. "Nima tambayar dana kewa kaina". Badawiyya ta dubeshi cikin rashin fahimta "kamar yaya kenan kake nufi"? Ta sake tambayarsa karo na biyu. "saboda ni ban san wata aljana wai ita Amal ba ballantana ma harna iya soyayya da ita". Nuraddin yace batareda ya iya hada idanu da itaba. Badawiyya ta dubeshi a rude amma babu alamar zargi a fuskarta, hakan ya karwa Nuraddin karfin gwiwar lallai zai iya jirkitar da zanceta, ya mayar mata da duk abinda sukayi jiya itada Amal ya zam kamar mafarki. "To.... Kana nufin kace duk surutun da mukayi da ita a daren jiya ba gaskiya bane"? Nuraddin yayi ajiyar zuciya, sannan ya dubeta da murmushi yace. "wallahi yau kin sani cikin damuwa a banza, ni da na dauka ma wani laifi nayi miki? Yanzu keda wannan dan abin duk shiya rikitaki haka"? Nuraddin ya danyi shiru gami da dubanta ido da ido. "Bari na fada miki wani abu da baki sani ba, aljanu ne kawai suke son wasa da hankalinki saboda ganin irin tsabar kaunar da muke wa junanmu. - Nuraddin ya kara cewa, kinga nima kaina a 'yan kwanakinnan haka nake ta fama da 'yan mafarke mafarken ban tsoro, fada mikine kawai bana yi dan kada hankalinki ya tashi, amma ni basu taba zuwa min a zahiri ba, kema dan macece, shiyasa amma kada ki damu, ki kwantar da hankalinki in kinje gida kisa a miki rokon Allah kada suci gaba da zuwa miki a zahiri". Badawiyya ta dube shi gami da ajiyar zuciya tace "Nuri darlin wallahi ni har na gama tsora na dauka da gaske soyayya ka fara da aljana. Nuraddin ya girgiza kai da dan murmushi. "karya ce kawai da iya shegen aljanu kin sansu da son wasa kamar daren sallah. Allah ne kawai zai iya rabani da ke Badawiyyata". Acan gefe guda, kimanin taku ashirin Daga inda suke zaune, Amal ce 'yar sarkin aljanu ita da fadawanta tana kallon duk abin dake faruwa tsakanin masoyan biyu. "shegiya nacacciya kya yi kya barshi saina munana fuskarki"! Amal ta ce ciki zuciyarta a fusace. Saura kwanaki uku kacal su Nuraddin su fara jarabawarsu ta karshe, wato ta kammala karatun su a makarantar. Karfe hudu da 'yan mintuna na yammacin ranar ne Nuraddin ya shiga makarantar dauke da farar leda ahamnunsa. Daga cikin gari yake jakar dake hannusa kayan marmari ne da ire- iren nau'in abincin gwangwani wanda a yanzu sun abin shansa da cinsa. Wannan ba abin mamaki bane domin duk sa'ar da yaso ya kashe kudi hannunsa kawai zai tura cikin aljihunsa sai yaji dumus, ya zaro iya adadin da yake bukata ya kashe abinsa. Yau kusan kwana arbain kenan rabonsa da Badawiyya Amal kuwa tun sa'ar da ta dawo da shi daga garinsu bai kara ganinta ba ido biyu ba, amma takan zo masa a mafarki cikin dare suyi hira abinsu. A ire- iren hirarrakin da suke yine ma a daren jiya tace dashi yayi jiranta yau zata zo gurinsa da yamma domin su tattauna akan maganar fara jarabawar sannan kuma tace da shi da zarar ya kammala karatu zata kawo masa kudin da zai sai motar hawa shima ya samin abin yawo a gari. Wannan ita tasa Nuraddin shigowa makarantar cikin sauri har yana sassarfa. Amma fa duk wannan hira da ake sha tsakaninsa da Amal 'yar sarkin aljanu, har yanzu hankalin Nuraddin a tashe yake zuciyarsa ta kasa tsayawa guri guda. A gaskia so kam ya fi kaunar gimbiyarsa ta ainihi wato Badawiyya. Tasha wahala akansa kuma a kullum idan ya kwanta barci yakan ce da kansa da Badawiyya ce keda arzikin Amal, to da ko raine tana iya saya masa idan tana da iko, Amma Amal fa? Cewa tayi tana kaunarsa saboda shi jarumi ne. Gaskiya ba kwanta min ba soyayyarta bata da inganci. Yace da kansa. Aljanun nan basu da tabbas, yanzu idan wata rana ya aureta ta kuskure ta sauya kamanni irin na mahaifinta mummuna mai dogon hanci kamar karas yaya zaiyi? Tab!! Falcao! Kenan yace a ransa sa'ar da ya tuna wani aljani da ya gani mai manyan kunnuwa kamar takalmi. Tambaya daya da Nuraddi yake wa kansa ita ce. Idan Amal bata kwanta masa a rai ba meyasa ya dau alkawarin aurenta? Arzikin da tace zata baka. Wata zuciyar ta bashi amsar tambayarra. Tabbas yana bukatar kudi. Wani babban sirri dake boye a zuciyar Nuraddin shine, tun farkon fara haduwarsu da Amal Nuraddin ya amince mata ne duk saboda Badawiyya. Ya sha fada ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba cewa, wahalar da Badawiyya keyi masa ta isa haka, domin abin yayi yawa, tun suna firamare take wahala dashi, sau da yawa ma ita ke zuwa musu da abincin ma da suke ci idan sun fito tara, hakanan kuma ita ke bashi kudin kashewa. A lokacin Nuraddin ma kazami ne bai fiye son wanka ba, ansha fito dashi filin taron dalibai ayi masa bulala a matsayin dalibin da yafi kowa rashin tsafta. Amma duk wannan bata sa daidai da kwayar zarra Badawiyya ta kyamace shi ba. Wasu lokutan ma idan aka dake shi ya fara kuka, ita takan zo tayi ta lallashinsa har sai ya huce. A haka har suka zo sakandire, nan ma taci gaba da wahala akansa, kudin makaranta, na kashewarsa, littafansa da kayan amfaninsa na yau da kullum. To irin wannan dawainiya ita tasa tun nuraddin baya damuwa har abin ya fara damunsa, ya fara tunanin a duniya fa babu zaman wacce yake inba Badawiyya ba, kullum burinsa a duniya shine Allah ya azurta shi ya nunawa Badawiyya cewa tofa shima dane. Don haka haduwarsu da Amal keda wuya sai yaga cewa damarsa tazo na ya saka mata na sama da abinda ta masa. Abinka da takadiri irin Nuraddi, ko kusa ko alama zuciyarsa bata taba tsoratar dashi irin hadarin da yake kokarin jefa kansa aciki ba. Tunaninsa kawai Badawiyya, tuni ya fara tunanin idan Amal tazo bashi kudin sayan motar da tayi masa alkawari zaiyi kokarin ya karbin kudin mota biyu datasa da ta Badawiyya. Wadannan tunane-tunane suke ta kai kawo cikin zuciyar Nuraddin har sa'ar da ya kawo cikin makarantar. Lokacin da ya karasa bangarensu na Seniors {manyan dalibai} gurin babu ko dalibi daya duk sun tafi daukar karatu, saboda kusantowar jarabawar da zazu fara nan da kwana uku, da yawa daga cikinsu basa dawowa dakin sai waje asuba Nuraddin ya nufi dakinsu cikin sauri sai yayi turus da....- Aljani Ya taka wuta!....18 - - - Nuraddin ya fara tafiya a hankali baki bude cikin mamaki. A iya sanin Nuraddin daliban da suke cikin dakin basu taba tafiya sun barshi a bude ba, haka basa barin wutar lantarki a kunne tun bayan wata gobara da aka yi suna aji daya, amma yanzu da Nuraddin yaci gaba da nufo dakin sai yaga dakin a bude, haske ko ina duk kuwa da cewa har yanzu da sauraran hasken ran, kuma abin mamaki hasken har waje kamar kwaya- kwayan wutar lantarki dake dakin sunkai dari. Gaban Nuraddin na faduwa amma ba wai don tsoro ba sai don mamakin da kuma dokin ya shiga yaga abin dake faruwa. A haka Nuraddin ya shiga dakin. Shigarsa keda wuya sai sukayi ido biyu da ita zaune akan gadonsa tana haskake masa idanu da fararen idaninta. "Sannu da zuwa". Amal tace dashi cikin annushuwa. "Haba ni fa nasan wani aikin sai ke". Nuraddin yace shima cikin murmushi, lokaci guda kuma yana kallon sauran zobunan guda biyu da suka rage a 'yan yatsunta. Nuraddin ya karasa cikin dakin yana fara'a ya zauna kusa da ita. Duk kamshinki ya mamaye mana daki" Nuraddi yace yana dubanta. "Naji dadin hakan". Amal tace cikin fara'a da jin dadi, duk mai hankali idan ya dubi irin kallon da take yi masa zai san cewa lallai tarko nan mai magani daya ya mamayi zuciyarta ya cafketa wato S0!. "Na bata miki lokaci ko? Cikin gari wallahi naje siyan 'yan kayayyaki, dan ma nayi sauri da bazan karaso yanzu ba". "Haba Nuraddin ba komai wallahi, nima dai azarbabina ne ya kowo tun wuri, kuma gashi DUNDUMA baya kusa na aike shi karas SIN ballantana ma ya sanar dani inda ka tafi, naso ma na biyo ta cikin gari na daukoka muzo tare". Nuraddin ya dubeta cikin rashin fahimta yace "wanene kuma DUNDUMA"? "Bawa na mai kula dakai". Nuraddin ya dubeta kirjinsa na bugawa cikin fargaba. Ashe 'yar masu dogon hancin nan han dan leken asiri ta makalkalamin. Nuraddin ya fada a ransa. Wani sansanyan gumi ya fara kwararowa a tsajiyar gadon bayansa. Yanzu da magulmacin ya dauki duk maganganun da sukayi da Badawiyya ya fada mata yaya kenan? Maganar Amal ta katse tunaninsa. "Tunanin me kake yine? Dan kaji nace DUNDUMA? Ai tsaron lafiyarka yakeyi, yaushe zan bari tsautsayi ya samar min kai Nuraddin? Ai bazai yiyu ba, kai dai na san abin da kake tunani, to ba leken asirinka yake yiba". Nuraddim yai ajiyar zuciya gami da murmushin yake kana ya dubeta yace "ke kuwa kin cika zargi, to ni tunanin da nake ma bai shafi wannan ba". "to Me kake tunani? Nuraddin ya jefeta da tattausan murmushin yaudara. "Ranar aurenmu nake tunani". Amal ta washe baki cikin farin ciki, sannan ta dan matso kusa dashi. "wallahi nima kullum tunanina kenan. Nuraddin yaushe zaku fara jarabawar ne nina matsu ku fara ko kwa gama a fara zancen aurenmu". "Ai ranar litinin dinnan mai zuwa zamu fara. Yau saura kwana uku". Amal ta dubeshi tace "kada ka damu kanka, saurara da kyau, idan ranar litinin tazo zan shigo cikin ajin daza kuyi jarabawar, zan buda maka tafin hannua, zakaga duk amsoshin a jiki". Nuraddi bai gaskata, kunnuwansa ba ya dubeta cikin kaduwa. "kada ka damu, duk ajin babu wanda ya isa ya ganni sai masoyina". Ranar litinin, rana ta faduwar gaba ga kusan dukkan daliban da zasu fara zan jarabawarsu ta karshe a makarantar. Wasu daga cikinsu suna fargabar ranar ne saboda basu yarda da kansu ba, domin sun tabbata dan abinda suka karanta bai isa sukai labari ba. Yayin da wasu kuma suke fargaba kawai saboda basu taba zaman jarabawa ma mahimmanci wannan ba a rayuwarsu. Haka kuma basu san wadanne irin tambayoyi za'a kawo ba a wannan shekarar. Koma dai menene shi Nuraddin ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa. Tun karfe tara saura na safiyar ranar suka fara jarabawar. Basu dade da shiga ba malaman suka shi rarraba musu takardun jarabawa tare da bakaken 'yan sanda guda hudu dake binsu a baya suna muzurai kamar zasu hidiye mutum danye da ransa. "kai gyara zamanka"! Wani daga cikinsu ya bugawa Nuraddin tsawa sa'ar kafar Nuraddin ta hagu ke kan teburin rubutunsa. Sai da akayi kusan mintuna arba'in da fara jarabawar Nuraddi bai zana alif ba. Yana zaune yana tsammanin warabbuka wai malam yaki yin Noma don zakka. Adai dai lokacin Nuraddin ya fara zazzare idanu yana tunanin ko bazata zoba, sai kawai ya kamar daga sama yaji ance. "Kada ka damu masoyina, ina nan kusa da kai. Da yardar Allah yanzu zaka gama". Sannan sai Amal ta bayyana kusa dashi tana murmushi. Nuraddin ya daga kansa ya dubi sauran daliban da kuma malaman dake tsaronsu, ko kusa ko alama babu wanda hankalinsa ya kawo gareshi, ballantana ma su nuna alamar sunji abinda tace. "Dubi tafin hannuna," Amal tace dashi a tausashe, lokaci guda ta daga tafin hannunta sama, kamar wasa sai ga rubutu a jiki "fara kwafa wannan ce amsar tambayarka ta farko". Nuraddin jiki na rawa ya fara kallon tafin hannunta yana rubuta abinda ya gani ba magana don gudun kada a jishi a cikin aji. "Idan kaso muna iya yin hirar mu ma kana aikinka. Domin babu mai jinmu ballanta ganina. Aljani

Chapter 3 of 6