Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
ta wannan hatta numfashi idan akayi a bayana, indai kece sai na gane domin ba idanuna bane kawai suke ganinki ba Badawiyya, hakika duk wani shashe na jikina ganinki yakeyi musamman ma zuciyata". Wannan tunani shiya dada sa Badawiyya ta sakankance cewa Nuraddin baya dakin. Wata zuciya tace da ita fita ki nemi mijinki a waje. Badawiyya, domin dakin da take tsaye shi kadai ne bashi da kwan wuta. Dama ba wata tsiya bace a cikin dakin, kilishine kawai shimfide da kujeru kanana guda biyu, tuni daman Badawiya ta sanar da mahaifinta cewa gidan fa ya musu girma ita da mijinta Nuri, domin dakuna sunyi yawa aciki. Badawiyya na nan dai tsaye tana son ta juya, amma tsigar jikinta sai wani yar-yar take yi. "NURADDIN". Ta sake kiran sunan cikin wata rarraunar murya, shi ta dada gaishe da kunnenta. Wani sassanyan gumi ya fara sartu a gefen fuskarta. Badawiyya tayi sauri tasa bayan hannunta ta share, babu abinda ta tsana irin ace tayi kwalliya, amma gumi ya fara kokarin bata mata kwalliyar musamman ma wannan rana data shafe sama da sa'o'i biyu gaban madubi tana shafe-shafe da goge goge, duk dan mijinta Nuri. Idanun Badawiyya sun fara sun fara sabawa da duhun dakin, hakan ita tasa ta fara hangen duhu-duhun wani abu kamar kullin kayan wanki acan kuryar dakin. Abu na farko data fara tunani shine inda makunnin lantarkin dakin yake, duk da dai a iya saninta, har lokacin da suka zo duba gidn ita da Nuraddin yana daya daga cikin dakunan da basu da kwan lantarki, amma tasan tun shekaranjiya mahaifinta ya turo ma'aikata domin susa duk wani abu da babu shi a gidan. Wannan shiyasa Badawiyya ta dada matsawa kadan jikin bango ta fara laluben makunnar lantarkin dakin. Adaidai lokacin da hannunta ya tabo makunnar wutar lantarkin ne to taji kafarta ta zunguri wani abu. Gabanta ya fadi ras! Abinda ta zungura yaso yayi mata kama da jikin mutuma. Badawiyya tayi tsaye nan sororo hannunta akan makunnin wutar. Tsahon dakiku tana nan tsaye zuciyarta na harbawa, daga inda take tsaye tana jiyo haniyar samari da 'yan mata dake shagali da sowa a farfajiya gidan. Ba zato ba tsammani sai taji abinda ta shura da kafarta ya dan motsa. Badawiyya taji kamar ta saki fitsar a wando saboda kaduwa, kwatsam kuma sai taji an fara wani gurnani marar dadin ji, gurnanin yaso yayi kama dana namun daji, hantar cikinta ta kada. maryam Ellelah ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {P.29} "Na shiga uku" Badawiyya tace gami da rike numfashi. Cikin gaggawa tayi niyyar ja da baya domin ficewa daga dakin, rabon sai tayi mummunar gani, sai dan yatsanta ya janyo makunnar kwan lantarki batare da ta sani ba nan dan dakin ya gauraye da haske. Da farko Badawiyya bataga komai ba har sai bayan dakiku uku lokacin da idanunta suka saba da hasken sannan ta lura da dan sauran abin da ya rage daga jikin masoyinta Nuri. Dan tsurut acikin babbar rigar kafar a shanye hannu a shanye kyakykyawar fuskar da ganinta kan jefa Badawiyya cikin nishadi da farin ciki duk ta yakune kamar matsatstsen lemon tsami, hakoransa sun fito sarari gayau! Dasu babu kyan gani sunyi reras dasu acikin bakinsa dasu babu kyan gani sunyi reras dasu acikin bakinsa kamar gonar kasusuwa, kan yayi kato tim kamar dan tulu, idanun sun zazzaro waje gwara-gwara kamar idon kwado. In banda agogon dake daure a shanyayyen hannunsa wanda ya nuna mata a daren jiya yace dashi zaije wajen shagalin bikinsu, da har abada Badawiyya bazata taba imani wannan shanyayyiyar halitta mai kamar aljani a matsayin Nuri dinta ba. Da farko tsabar kaduwa da girgiza tasa Badawiyya ta kasa motsi da zurawa mutum mutumin Nuraddin idanu tayi can kuma sai ta dora hannu aka ta kwala ihu. "Wayyo Allah! Nuraddin na shiga uku"! Ta dada kwala ihu. Dakunan gidan da basu sami isassun kaya ba suka amsa kuwar ihun kukan Badawiyya. Tun kafin amsa kuwwar ta dusashe Badawiyya ta fadi gefen Nuraddin sumammiya. A can kuryar gidan daga bangaren gabas, wasu motoci ne a jere marsandi fara, honda shudiya da kuma dankwaleliyar jeep launin rawaya. Wadannan motoci guda uku kyautace ta musamman daga mahaifin Badawiyya. Tun ana sauran kwana uku a daura auren yasa aka kawo musu. Da yawa daga cikin bakin da aka gayyata babu wanda zai iya kallon motocin ba tare da ya sake kallonta ba, domin sababbine fii-fil hakan ce tasa wasu daga ciki masu karancin wayewa har hannu suke sawa su dan shafi jikin motocin suji yadda suke kome suke ji a jikin motar? Allah masa. Dayake tsakanin inda motocin suke zuwa inda ake shagalin bikin da 'yar tazara, sa'ar da aka sami damar gyara wutar sai duk baki suka bar inda motacin suke suka nufi can cikin gidan. To amma fa banda wasu samari biyu wadanda ke boye a bayan motar suna shawagi, lokaci guda kuma suna mahawara. "kaga Yusuf, tunda dai kanada Aysha a hannu kamata yayi ka barmin bakuwar nan". Saurayin dake magana sunansa Abbati, dan gajerene baki kakkaura, fuskarsa tana da kyawun gani, sai dai kuma kansa yafi uban jikinsa girma, wannan shiyasa da yawa daga cikin abokanansa suke kiransa da Abba kwandal. "zance banza kenan", yusuf yace dashi yana harararsa. "Me kake nufi da inada Aysha a hannu? Aysha da kullum saita gasamin aya a hannu ita ce har kake kokari kafamin hujja da ita? Kaga Abba kwandal nifa *bebe* din nan babu mai rabani da ita sai Allah". Abbati kwandal ya fashe da dariya. "yaufa ake zukin mazallako wai da daga ciki yana rokon uba kwabo. Yusuf meye kuma na wani fusata? Babe din da ko sunanta ma bamu sani ba". Yusuf ya girgiza kai yace. "kaine dai ba san sunanta ba, amma ni na sani". Abbatai kwandal ya dafa motar da suke boye a bayanta da hunnunsa na hagun. "To menene sunanta idan ka sani"? Yusuf da wasa yake yiwa Abbati, domin shima kamar sauran duk mazajen dake gurin yau ya fara ganin kyakykyawar budurwar ballantanama har yasan sunanta, dan haka sa'ar da Abbati ya tambayeshi sunan sai ya daga kai sama kamar wanda yake kokarin tuno sunan. "sunana Amal". Wata sassanyar murya busasshiya mai tayar da tsigar jiki, maral alkibla tace dasu daga baya. Samarin biyu suka juyo firgigit cikin mamaki- mamaki tsoro-tsoro, domin basu taba jin irin sautin muryar ba. Koda suka juya sai sukaga wayam ba kowa abayansu. Yusuf ya dubi Abbati, sannan Abbati ya dubi yusuf a rude. "ma...magana naji anyi a bayanmu ne? Yusuf ya tambaya bakinsa na rawa. Abbati ya gyada kai a tsorace. "Magana ce... Magana ce akayi wallahi". Samarin biyu sukayi mutuwar tsohuwa a gurin jikinsu na bari kamar mazari, gashi dai inda suke tsaye suna iya hangen samari da 'yan matan a can wani bangare na gidan ta ciki gilashi motar da suke tsaye a bayanta, amma tsoro ya hana su motsawa daga gurin, ko shakka basayi maganar mace sukaji gashi basuga mai maganar ba. Abba kwandal ya mirgina katon kansa mai kamar masaki gefe guda kana ya karkata kunnuwa yayi fakare kamar zakara yana kokarin ya sake jin daga inda muryar ta fito. Yusuf na nan tsaye kusa dashi bayan rigarsa ya jike sharkaf da gumi, a zuciyarsa yanata zargin kansa da wautar rabo kansu daga cikin jama'a. Shi daman tun farkon shigowarsu gidan sai daya ayyana a ransa cewa yanzu haka acike yake da kwankwamai domin girmansa yayi yawa. "mu bar gurin nan". Abbati yace da yusuf cikin rada yana magana da gefen baki. A daidai wannan lokacinne fa suka ji daga can cikin gidan an kwalla ihu da karfin gaske. Time up. ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {PART 31} Dakta sulaiman yayi fakin da motarsa kirar honda a farfajiyar asibitin, sai ya bude kofar motar cikin gaggawa ya nufi cikin asibitin. Akwai alamun farin ciki da nishadi karara a fuskarsa, wannan ce matasa aranar da duk leburan da yayi masa barka da zuwa sai ya juya ya jefe shi da murmushi. Wani sa'in ma har tsayawa yakan danyi ya danyi musu wasa da barkwanci kana yaci gaba da tafiya. Wannan sabuwar dabi'a da Dakta sulaiman ya shigo da ita asibitin aranar ta baiwa kowa mamaki, musamman ma kananan leburori wadanda su dama Dakta sulaiman bai daukesu komai ba, baya da dillalan kashi. Dakta sulaiman Bafillatanine dan kimanin shekaru talatin a duniya, dogo fari sosai, yanada fashin goshi, amma bai fito sosai ba. Yana da farin jini mai tarin yawa a gurin mata duk kuwa da cewa sun tsani tsabar girman kansa. Dakta sulaiman ma'abocin sa farin tabarau ne, tunda ya fara aiki a asibitin, ba'a taba ganinsa ba tabarau ba. Wani makaryacin ma ya rawaito cewa wai Dakta sulaima da gilashin yake bacci. Da yawa yawan mata abinda ke burgesu ga surar daktan shine fararen kwayar idananunsa da kan fito rangadadau ta cikin farin tabaran. Abinda basu sani ba shine, duk kyawun idanun farinsu da girmansu gululun banza ne domin baya gani sosai sai da taimakon farin gilashin nan. Wannan ya samo asali ne saboda tsabar karatu da hana idanu barci gami da kallon farar takarda acikin hasken rana zamanin da yake karatun aikin likitansa a jami'a. "Barka da zuwa wani yankunannan tsOho dake faman goge tayil da tsumma yace dashi. "yauwa baba tanimu, har yanzu baka tafi gidaba? Karfe tara saura na dare fa". Tsananin mamaki da kaduwa ya hana tsohon kara cewa uffan, sai kawai ya bi dakta sulaiman da kallo. Tunda tsohon yake aiki a asibitin sama da shekaru ashirin da doriya baitaba ganin likita mai tsabar girman kai kamar iblis irin sulaiman. Ai a tunaninsa ya gaishe da Daktan sama da dari uku amma bai taba amsa masa ba. Duk wannan bata hana tsohon cigaba da gaishe da litkitan ba, domin ko banza lokaci lokaci idan Dakta Sulaiman ya bushi iska, yakan mika masa naira dari zuwa dari biyu ba tare da yayi masa magana ba. Dakta sulaiman yaci gaba da tafiya cikin sauri yana duban agogo tara saura kwata. Ai nayi sauri ma. Yace cikin zuciyarsa kana ya yiwa kansa murmushi. Duk da yake dai ba dadin rai ne ya kawo shi asibitin ba, amma cike yake da farin ciki. A cikin shekaru uku da yayi yana kula da al'amuran lafiya na iyalan Alhaji Danbaba kullum addu'arsa itace Allah ya kawo dalilin dazai sa ya sami damar da zai duba wannan kyakykyawar budurwa. Amma bata taba ko ciwon kai ba ballantana ya sami damar ganawa da ita, sai gashi yau a banza sa'arsa ta haska, mahaifinta da kansa yayi masa waya yace wai yayi sauri yaje asibitin ya duba Badawiyya. Sulaiman ya yi tsaye jikin farar kofar na 'yan dakiku yana nazarinta, kana daga karshe sai ya tura kofar a hankali ya shiga dakin zuciyarsa na harbawa das! Das! Dakin da dakta sulaiman ya shiga yana daya daga cikin dakuna na musamman da aka tanada a asibitin don kwantar da masu hannu da shuni. Dakin bashi da girma sosai, gado daya ne jal a cikinsa sai wata kujerar roca guda daya. Lokacin da Dakta Sulaiman ya shiga cikin dakin bai damu da yayi sallama ba, haka nan kuma bai damu da ya kalli matan dake ciki dakin ba, domin gaba dayan hankalinsa yana kan gadon da Badawiyya take kwance. Dakta sulaiman ya mayar da kofar ya rufe. Ya matso da a hankali kusa da Badawiyya ya rankwafa hannayensa akan bakin gadon ya kurawa Badawiyya idanu baya ko kiftawa. Kai wannan yarinya da kyawun sa dauke numfashi take. Sulaiman yace a cikin zuciyarsa. Tsahon lokaci yana rankwafe yana ta nazarin duk wani bangare na jikin Badawiyya sai hadiyar yawu yake kamar tsohon maye. "Ta farka kuwa"? Sulaiman ya tambayi jerin matan dake cikin dakin a karo na farko. Inda a lokacin za'a tambayeshi bai san mata nawa ne a cikin dakin ba. A gaskiyar Al'amari mata biyar ne cikin dakin akwai mahaifiyar Badawiyya, sai kakarta ta wajen uba hakan nan kuma akwai kanwar babanta. Sauran matan biyu dangin uwartane, wannan iya wadanda ke ciki kenan amma farfajiyar asibitin akwai 'yan uwa da abokan Arziki sama da guda ashirin. Sa'ar da Dakta sulaiman yayi tambayar bai sami amsa da gaggawa ba domin matan babu abinda suke yi sai sharbar kuka. Tsohuwar nan kakar Badawiyya ita tayi karfin hali ta dago kai tace dashi. "Ta farka harma ta bude idanunta... Sai dai kuma shi... Tsohuwar ta sake fashe wa da kuka sauran matan suka rufe mata Baya............................... Dafatan kunajin dadin labarin matasa maza da mata??????? ALJANI YA TAKA WUTA CIGABBN LABARI {PART 33} "Kaine likita sulaiman"? Yawun bakinsa ya kafe, dan haka sai kawai ya gyada mata kai kamar kadangare. 'yar budurwar ta dada bude kofar sosai, sannan ta matsa gefe guda. "zo muje na rakaka, yana ciki yana jiranka". "To nagode". Dakta sulaiman ya fadi a karo na farko. Budurwar ta wuce gaba tana rausaya kamar dawisu, shiko dakta na binta a baya, a zuciyarsa yana tasbihi ga sarki mai komai mahaliccin kyawawa. Budurwar ta tsaya dab da wata kofa launi kasa- kasa mai sheki kana ta juyo ta dubeshi da murmushi tace. "kana iya shiga.. Yana ciki kai yake jira". Dakta sulaiman yaji dadin murmushin dan haka shima ya haskaketa da fararen hakoransa. "kefa baza ki shiga ba"? Budurwar ta girgiza kai. "maganarku ce kai dashi". Suka danyi shiru na 'yan dakiku suna tsaye suna duban juna. Daktanne ya fara magana. "kinso ki yimin kama da wata kawata A'isha da mukayi jami'a tare. Budurwar ta gyara tsayuwa tana murmushi tace. "Allah ko"? Sulaiman ya gyada kai. "To, ni dai ba Aisha nake ba". Sulaiman yaji zuciyarsa ta harba shin wannan dama ce agare shi ta ya tambayi sunanta"? "Me kike to"? Budurwa tayi dariya har da tafa haNnu. "Au! Kaima wato irin maganata kake kwaiKwayo ko? To sunana Badawiyya". Ta danyi shiru kana sai ta dada da cewa. "Ko kuma kana iya kirana ma da Badawiyya Nuri". Dakta sulaiman yaji kamar ta watsa masa wuta a doron zuciya. Yayi sauri ya boye kishin dake ruruwa a zuciyarsa ya dubeta cikin mamaki yace. "Badawiyya Nuri"? Ta gyada kai. "Kwarai kuwa shine mijin da zan aura insha Allahu". Tun daga wannan lokaci har zuwa yanzun nan da Dakta sulaiman ke tsaye akan Badawiyya bai daina Addu'ar Allah yasa wata dama ta sake hadasu ba, saboda tun bayan wannan al'amarin bai sake samun damar tsayawa da ita daidai na minti guda ba, sai dai gaisu a tsaitsaye. Dakta sulaiman yayi firgigit, tunaninsa ya katse a daidai lokacin da yaji tsohuwar nan kakar Badawiyya tana cewa. "Badawiyya... Badawiyya bude idanunki". Dakta sulaiman ya lura da cewa ashe Badawiyya ta farka. "ku kyaleta sannu a hankali zata wartsake". Yace dasu a sanyaye lokaci guda kuma ya mike tsaye yana duban matan guda biyar wadanda motsin Badawiyya du yasa sun mike. "kuyi hakuri ku dan jirani a waje zan dubata". Cikin biyayya ba musu, matan suka nufi kofar fita, kakar Badawiyya ce agaba sauran matan biye da ita. Mahaifiyar Badawiyya itace ta karshen fita sa'ar datazo fita saita dubi sulaiman tace bakinta na rawa. "Don Allah likita.... Ka dubamin ita da kyau... Bana son ta mutu..." zuciyarta ta karye sai ta fashe da kuka. Dakta sulaiman ya matsa dab da ita, ya tausasa murya gareta, wani abu da bai taba yiwa wani ba yace. "kada ki damu kaduwace kawai ta sata sumewa". A haka ya lallabata ta fice daga dakin. Fitarta ke da wuya sai idanun Badawiyya suka bude. Sulaiman ya kurawa kyakykyawar fuskar idanu baya ko kiftawa. Tsawon lokaci suna nan a haka. Ga shi dai idanunta wayam a bude, amma basa kiftawa. Sulaiman ya fara tunanin tabbas har yanzu tana cikin tsabar kaduwa ne. Ya matsa kusa da gadon sannan ya daga dan yatsansa na dama da niyyar taba gashin idanunta. "Kada ka tabani ina ganinka". Rarraunar muryar Badawiyya ta katse masa hanzari. Hannunsa makale a sararin subhanahu, a wannan karon shine cikin kaduwa. "Badawiyya... Sannu yaya jikin naki"? Ya sami kansa yana mai fadi. Shiru bata amsa masa ba. Can kuma ba zato ba tsammani sai ta mike zaune zumbur ta dafe kirji tace ciki karaji. "Na shiga uku! Ina Nuri... Nuri... Nuri"! Ta sake kwalla kara. Cikin gaggawa sulaiman yayi waje ya dagawa wasu daga cikin matan da suka fita hannu, suka shigo cikin gaggawa. "ku rikemin ita". Likitan ya basu umarni. "wayyo Nuraddin! Dan Allah ku kyaleni na nemo shi wallahi kashe shizata yi bata da imani. Dan Allah ku kyaleni wallahi bata isa ta rabani dashi ba, wayyo"! Ihunta ya kashe sa'ar da taji tsinin allura ya soketa. Ba'a kara minti guda ba barci ya saceta. Dakta sulaiman yaja baya ya tsaya yana haki cikin kaduwa. Bawai ihu, ko abubuwan da Badawiyya keyi bane ya sashi kaduwa ba, wannan yasha jinsu a baya amma maganganun datake yi su suka jefashi cikin tunani. Nuri? Mijin da zata aura kenan, shin wacece ke son rabasu? Dakta sulaiman ya tambayi kansa. *** *** *** wani katon zakara mai jar cera yabi wata 'yar karamar kaza aguje suka fara tsere a tsakar gidan. Kai! Amma dai anyi girman banza. Nuraddin yace cikin zuciyarsa sa'ar da yabi kajin da kallo sun nufi zauren gidan aguje. Kallo, numfashi da cin abinci mai ruwa-ruwa sune kadai abinda Nuraddin zai iyayi tun bayanda masifar ta sameshi. Sannu a hankali kusan watanni shida kenan da faruwar al,amarin. Acikin watanni shidan nan abubuwa da yawa sun faru wadanda mafi yawa daga cikinsu na bakin ciki ne. Alal misali tun sa'ar da aka kawo Nuraddin gida mahaifiyarsa bata kara samun lafiya ba, yau cuta gobe cuta, kullum ta dubi Nuraddin a kwance akan katifa a tsakar gida nannade kamar igiya sai ta sashi gaba tayi ta kuka. ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {part34} Dakyar da ban baki da rokon Allah 'yan uwa suka shawo kanta ta fara cin abinci kadan- kadan. Abangaren abin da ya shafi magani kuwa ya zuwa yanzu an sami bokaye kusan talatin, malaman tsibbu arba'in da sauran 'yan bani na iya sama da goma sha uku amma duk a banza. Duk wanda yazo ya dubi Nuraddin sai ya girgiza kai yace. Wannan sai dai abinda Allah yayi. Duk wannan dawainiyar kashe- kashen kudi da ake ta faman yi ba wani ke yinta ba sai mahaifin Badawiyya. Ganin kullum sai kashe kudi akeyi a banza babu alamun sauki shiyasa mahaifin Nuraddin wata rana yaje har gida ya sami mahaifin Badawiyya yace dashi. "ya kamata ka daina kashe kudinka haka nan, abinda kayi Allah saka maka da alherinsa, Allah yaga niyyarka kayi kayi iya yinka Allah ne dai baiyi zai samu sauki ba". Alhaji Danbaba ya dubi Dattijon mahaifin Nuraddin ya girgiza kai cikin tausayi kana yace. "A'a malama ina fa zai yiyu a kyale yaro acikin irin wannan hali babu magani ai bashi yiyuwa". Mahaifin Nuraddin ya danyi shiru na wani lokaci kana sai ya dago kai yace. "Abinda nake son ka fahimta shine wadannan bokaye babu abinda zasu iya yiwa yaron nan, shiyasa nake ganin kawai mu mika komai ga Allah a sami malamai suci gaba da yi masa addu'a kullum". Tun daga ranar sai suka ajje zancen bokaye a gefe, Alhaji Danbaba ya sami wasu amintattun malamai wadanda duk kwana ukun duniya sai sun karantawa Nuraddin Al-qur'ani mai girma su kuma yi masa addu'ar Allah ya bashi sauki. Tunda Badawiyya ta sami sauki sai ta tare a gidansu Nuraddin, anan take kwana sai dai akawo mata suturunta da abincinta nan. Ita ke taimakawa mahaifiyarsa suyiwa Nuraddin dinta wanka, ita ke bashi ruwan zuma ko madara, da sauran dangin abinci masu ruwa-ruwa. Haka Badawiyya ta kasance acikin wannan hali na tsawon lokaci, kullum haka zatasa masoyinta agaba tana cewa cikin kuka. Nuri darling nida kai alkawari ne babu mai rabani da kai sai mutuwa. Wani sa'in da zarar ta fadi haka, saita tallabo kwandalelen kan Nuraddin ta dora akan cinyarta tana kuka kuma tana cewa... "sannu Nuri kaji... Kayi hakuri Allah ne ya dora mana, idan yaso yau ma saiya yaye mana". Aikin kenan ba dare ba rana. Wani sa'in idan Mahaifiyar Nuraddin ta jiyo Badawiyya tana fadin irin maganganun sai tayi sauri tabar guri saboda tausayi, ta koma can cikin dakinta tayi ta kuka a boye. Wata rana a cikin ranakun da suka biyo baya, Badawiyya na zaune tana durawa Nurin ta ruwan madara, sai mahaifiyarsa tace da ita cikin sanyin murya. "Badawiyya ina ganin da komawa kika yi gida da kwana, kinga kwana anan bana irin naki bane.. Makwancin bashi da kyau kuma muddin kina ganinsa a kullum hankalinki bazai taba kwanciya ba". Badawiyya ta sunkuyar da kai gami da murmushin yake lokaci guda kuma ta fara yiwa Nuri fifita. "Baba... Idan na daina kwana ma anan ba daina tunaninsa zanyi ba, gara dai ina kusa dashi idan mutuwa ma zaiyi gara mu mutu tare". "mema ya kawo zancen mutuwa, abinda nake so dake shine ki koma kwana a gidanku inya so in ma zuwan zakiyi kya ke zuwa da safe, amma yanzu kullum kina nan, gashi babu ranar warkewa ki barwa Allah Badawiya nasan yadda kike ji a zuciyarki to amma sai hakuri". Tun daga wannan rana ne Badawiyya ta koma gida da kwana, yau wata hudu kenan daidai amma duk da haka kullum karfe takwas na safe take baro gida tazo gurin Nurin ta bazata koma gida ba sai goma na dare. Adaidai lokacin da katon zakaran mai cara yabi kazar da gudu ne Badawiyya ta shigo zauren gidan hannayenta dauke da jakankunan leda guda biyu wadanda ke cike da kayan shaye-shaye iri-iri. "salamu alaikum". Badawiyya tai sallama. Mahaifiyar Nuraddin wacce ke shara a tsakar gida ta amsa sallamar gami da mikewa tsaye. "Badawiya har kin iso"? Badawiyya ta gyada kai. Sannan idanunta suka nufi inda kuturturan Nuraddin yake. "ina su Hajiya da Alhaji ina fatan dai suna lafiya"? "Lafiyarsu kalau". Badawiyya ta amsa, kana ta nufi inda Nuri yake ahankali tana nazarin yanayin jikinsa. Akwai tsammanin dake damun zuciyarta, akullum idan tabar Nuri tunani take yi kamar gobe idan ta dawo zata same shi ya warware. Amma sabanin tunaninta duk sa'ar data zo saita tarar dashi jiya ya yau. Suturar dake jikin Badawiyya ba wata ta kuzo ku gani bace doguwar riga ce baka kafarta kuwa takallamine silifa, tun ranar da Nuri ya nannade ta daina kwalliya. Badawiyya ta matsa dafda katitafar da yake kwance ta ajje jakankunan ledar a gefe guda, sannan ta fara yin abubuwan data saba yi masa na al'ada tun tsawon watannin shida da suka shude. "Nuraddin ina kwana". Tace a tausashe tana duban fuskarsa, tasan bazai amsa mata ba domin babu bakinsa an rufe, amma duk da haka akwai alamun da take ganin a fuskarsa ta gamsu da cewa lallai ya amsa gaisuwarta. "ya jikin naka"? Idanuwansa suka motsa wannan shi ya tabbatar mata da cewa ya amsa. Tun a mako na farko da faruwar al'amarin Badawiyya ta fahimci cewa duk abinda aka ce da Nuraddin yana fahimta mayarwa ne dai bazai iya ba. ======ALJANI YA TAKA WUTA CI GABAN LABARI {P.35}======= Wannan tunani na Badawiyya gaskiya ne, domin tun ranar da aljana Amal ta shanye shi, duk abinda ake cewa yana ji, sai dai bashi da ikon magana. Bakin cikin dake kunshe a zuciyar Nuraddin yafi bakin cikin bayan tukunyar dahuwar shayin bakin kasuwa. Yaya za'a ce kullum sai Badawiyyarsa tayi masa magana amma shi baida ikon maganar. In banda tunanin da sa ran akullum zai iya warkewa, su sake ganawa sosai da masoyiyarsa Badawiyya da tuni ya hadiyi zuciya ya mutu. Akwai lokuta da dama da Amal kan bayyana gabansa tayi ta kyakyata masa dariyar mugunta. Zuciyar Nuraddin takan tafasa ta kone saboda bakin ciki. Badawiyya ta dada matsowa kusa da Nuri ta tallafi kansa ta dorashi bisa cinyarta, kana ta bude daya daga cikin jakankunan ledar da tazo dasu ta dauko wata doguwar kwalba mai dauke da tacacciyar madara sannan a hankali ta bude ta fara baiwa Nuraddin a baki. *Bani da kamarki Badawiyya, Allah ya bani sauki na rama miki abinda kike yimin*. Nuraddin ne ke fadin haka cikin zuciyarsa. Duk abinda Badawiyya ke masa yana gani kuma yana ji. Tsahon lokaci suna nan a wannan hali, Badawiyya na bashi madarar shiko yana shan rabi, rabin na kwararewa ta gefen Bakinsa. "Bari inzo in gogge masa jikin". Mahaifiyarsa ce ke cewa da Badawiyya hakan. Badawiyxa ta girgiza kai cikin ladabi. "ki bari zan goge masa". Mahaifiyar Nuraddin tayi tsaye tana dubansu ta tuna da cewa kwana daya kawai da daura aurensu, masifar ta sameshi amma dubi yadda take fama dashi kamar daman sunyi shekaru masu yawa amatsayin ma'aurata. Hawaye ya kwace mata. Cikin gaggawa ta juya ta nufi dakin girke-girke domin bata son ta tashi hankalin Badawiyya. Wani yaro ya shigo tsakar gidan a guje, kaji da tattabaru suka yi tsalle gefe guda. Kwakwazon kajin shiyasa mahaifiyar Nuraddin dake dakin girke-girke fitowa cikin sauri tana share hawaye ta tari yaron. "lafiya ka shigo a guje? Kufa bakwa rabuwa da kiriniyar banza". Yaron yaci gaba da tsalle-tsalle agabanta. "wallahi wai...wai ana kiran Badawiyya.. Badawiyya taji abinda yaron yace cikin mamaki ta dago kai ta dubi mahaifiyar Nuraddin . "wai ke ake kira". Mahaifiyar Nuraddin tace tana duban Badawiyya. Akwai alamun mamaki karara a muryarta. Badawiyya ta ajiye tsumman data gama goge jikin Nuraddin, kana ta dada gyara masa kwanciya ta dubi yaron. "wanene ke kirana"? Kwakwalwarta ta fara tunanin gaggawa, a iya saninta ko a gidansu babu wani mutum in ba kawayenta ba da yake zuwa nemanta, sai gashi yanzu wani na kiranta a waje. "ko kuwa dai macece"? Ta kuma tambayar yaron. "Wani ne... Wani mutum ne a mota yazo". Sukayi jim na dan lokaci, mahaifiyar Nuraddin ce ta fara magana. "Ai sai kije ki gano, Allah sa dai lafiya". Badawiyya ta mike a hankali, ta dubi Nuraddin tace. "Ina zuwa Nuri yanzu zan dawo minti daya kawai". Ta daga danyatsa akan fuskarsa kana ta jefe shi da murmushin karfin hali idanun Nuraddin suka kifta alamun ya fahinta. Cikin gaggawa ta nufi kofar gidan don kawai biyayya ga mahaifiyar Nuraddin bawai don taso ba. Badawiyya na fita tayi turus kamar ta fada cikin fasassun tukwane. A tsaye a jikin wata shudiyar marsandi sanye da jaket da wando shudaye, kafarsa sanye cikin takalmi baki mai walwalin dauke idanu. Idanunsa boye a bayan farin tabarau, wani dogon saurayi ne fari mai dan siririn fashin goshi. Saurayin yayi mata murmushi yace "ki gafarceni Badawiyya ina fatan kin ganeni"? Badawiyya ta zura masa idanu kamar biri da kararrawa tana kallonsa ko kiftawa batayi tsawon lokaci bata dauke idanunta ba ita ko bace dashi kala ba. "Badawiyya ko baki ganeni bane"? Saurayin ya kuma tambaya. Badawiyya tayi firgigit kamar wacce ta nutse a kogin tunani sannan saita sunkuyar dakai tace. "Na ganeka mana ba kaine Dakta Sulaiman"? Dakta Sulaiman ya laltbi kwibin aljihun rigarsa na dama ya zaro wani rawayan kyalle na siliki sannan ya fara goge fuskarsa. Tabbas gumi yake yi. Akwai wani yanayi na ko in kula da lumbu- lumbu dake kan fuskar Badawiyya, wannan shiya sashi rauni, kana yaji gumi ya fara sartu akan goshinsa. "Yaya gidan lafiya"? Ya sami kansa yana fadi. "lafiya Badawiyya ta amsa a takaice kana sai ta dan juya masa baya tace. "Sai kayi sauri ka fadi abinda kake son ka fada domin minti daya na nemo izni. Dakta Sulaiman yaji duk gwiwowinsa sunyi sanyi. Ya dada share gumi yace muryarsa na rawa. "maganganuna da nazo dasu suna da yawa Badawiyya, domin sama da shekaru uku kenan ina fatan Allah ya kawo mu wannan rana dazan Amayar miki abinda ke boye a zuciyata". Badawiyya ta juya a yatsine sannan ta gyara tsayuwa tace. "Ina jinka amayar". Dakta sulaiman ya gyara Tsayuwa ya jingina bayansa jikin motar kana ya fara. "Tun sa'ar dana fara dora idanuna akanki nake kaunarki Badawiyya kuma nauyin mahaifinki da nake ji su suka hanani na furta miki manufata tun farko". Yayi shiru kana ya gyara farin tabaran dak idanunsa yaci gaba. Abdullahi Yusuf Maitama. ====ALJANI YA TAKA WUTA CIGABAN LABARI {P.36}==== "Badawiyya ayau ciwon dake cikin zuciyata ya tsananta, tun ina boyewa gashi har ya fito fili. Badawiyya ina sonki sani cewa ayau bana ganin komai sai ke haka banajin komai sai muryarki, sai abinda kika yi dani". Dakta sulaiman yayi shiru akwai alamun taraddadi ta karaya karara akan fuskarsa domin bai san irin amsar da zata fito daga bakinta ba. "kagama"? Badawiyya ta tambayeshi a yatsine. Jikinsa na rawa sulaiman ya dubeta kamar ya fashe da kuka ya daga hannayensa biyu ya dora akan cinyarsa yace. "Babu zance gamawa Badawiyya sai da ace wannan shine mafi mahimmancin abinda ke tafe dani". Tsahon lokaci matasan biyu na tsaye suna duban juna, akwai

Chapter 5 of 6