Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
iya kirkire2 ba ma anan kasar ba har da kasar yaje yayi bama anan kasar kadi aka ji da shi ba har kasar da yake yayi karatun sa (Germany) sunyi alfahari da shi a matsayin dalibinsu da yake shiga cikin masu jajayen kunnuwa yana kirkire2, su dama nasara irin mutanen da suke so kenan masu baiwa shi yasa tym din suka fifita shi, suke ji da shi, da ya gama karatu suka nemi rike shi a wani kamfaninsu na kere2 jirage, da gida da albashi mai tsoka za su ba shi amma yace ba zai iya zama can ba gara ya dawo kasarsa cikin addininsa da ala'adarsa da en uwansa. Hajiya tace, Aneesa naji kinyi shiru, bana son in tauye miki hakkinki meye ra'ayinki. Ta sadda kai kasa saboda yanzun har ta fara kunyar Hajiya tace, na amince Hajiya, wlh ko yaya Ishaq ba na gari bane zan iya miki biyayya in aure shi balle halayyarsa da dabi'unsa zuwa mu'amularsa babu abin kushewa, amma hajiya shima ya amince? Naga fa yana son Aunty safeena sosai. Hajiya tayi murmushi, ya amince sannan don yana sonta shine ba zai kara aure ba? Ai duk wadda kika ga mijinta ya kara aure ba wai baya sonta ne, wani ra'ayinsa ne wani kuma koyi da Manzon Rahma (saw) ne, kalilan ne karawa don matansu ba su kyautata musu, duk irin son da yake mata zai iya yi miki fiye da nata, in dai kina kyautata masa don babu abin da Namiji ke son irin kyautatawa, kamar yin masa ladabi da biyayya da gudun bacin ransa don son abinda yake so in dai bai sabawa shari'a ba, da son en uwansa, idan kika rike wadannan to zaki kama namiji a hannunki. 94) A wannan rana magabatn Ishaq suka je gidansu Aneesam dama Hajiya ta fara sanar da Abbansu Aneesa. Su ka ba da kudin gaisuwa aka yanka musu sadaki dubu talatin amma baban sasa yace ko ranar daura aure ne suna iya kawowa. A cikin gidansu Aneesa tsegumi ne ya dinga tashi daga bangaren Hanne ta dinga yada habaici a tsakar gida. Oh! Allah mai iko wannan auren huce haushi kenan ko auren me? Allah ya raka taki gona bamu kwashi ragowa ba, ita ta kwasarwa danta, an cuce shi. Sai diyarta Haula tace, mama kika sani ko shima ragowarsa ce tunda dai dubi irin hidimar da yake mata ba dangin iya ba na baba, ga gidanshi da take zuwa wai hutu, kika san me suke yi a can Allah sarki matarsa duk anje an gane mata sirri ga shi za'a daure mata miji. Uwar tace, au dama me ne gaya muku kwanaki, daman ace daga hutu sai kunji wani abu ya bullo kinga kuwa ashe zancen aure ne zai biyo baya. Haka suka yi ta wannan tsegumin da sharrin don halima ta tanka musu, bata tanka ba, sai dai ta bari 'ya'yan Hanne sun fita sai ta same ta a kicin tace, wlh maman haula ki bar kushe da hassada saboda taki ne ga mai rabo, kin kushe Aneesa kinyi mata sharri sai ga shi Allah ya bata miji wanda ya fi kaninki shine kuma ke da 'ya'yanki kuke hassada, har uwar yarinyar nan ta bar duniya ba taba tanka wa sharrin da kike mata ba, ita da diyarta, hakan bai sa ki nadama ba yanzu ma bayan ranta bi ta da kulli yana cigaba, to yanzun kina hadawa da dan manya dan masu galihu ina tsoron ranar da wannan sharrin naki zaije kunnen uwar yaron nan in kina ganin Aneesa bata da gata shi dan gata ne, kuma shi wani ne, zasu iya daukar mataki akan irin wadannan sharri naki, ki tsaya kan Aneesa ko ki gyara bakinki kiyi masa linzami don Aneesa yanzun matar manya ce, idan kika ci gaba da mata bita da kulli mijinta zai dauki mataki akanki ke da 'ya'yanki, idan kunne yaji to gangan jiki ya tsira, Hanne ta tafa hannu tace, to kinibabbiya, kina iya zuwa ki gayawa Hajiya nayi wa danta sharri sai a daureni har igiya tayi rara ke kuma sai ki zuba ruwa kasa ki sha, munafuka ai fa ke yanzun nan zaki tare 'yarku zatayi aure gidan masu kudi, lallai kam! Muna nan muna sa ido zamu ga yin auren, auren cin amana. Ita dai Halima tunda ta riga ta gama gaya masa gaskiyya daki ta shige ta barta tana babatu wanda ta san idan ta ci gaba da kulata yau haka za su wani sun musanyar yawu. Aneesa kam! Kasa sukuni tayi tunda wannan lamari ya zamo haka, gidan Hajiya ma da take wuni a can kullum yanzun sai ta soma ragewa, saboda nauyin Hajiyan take ji yanzu, har sai da Hajiyan ta sa aka kirata tayi mata fada sosai akan wannan matakinda ta daukarwa kanta, sannan ne fa ta saki jikinta, wanda Inshaq yace zauyi wa waya kawo mata waya ya zo ya kawo mata ta zabi Nokia mai tsada har da kayi da kudi ya sa mata, sau daya Ishaq ya kirata shima gaisawa sukayi. *************** *************** ************95) Ishaq tunda ya bar zariya a mita yake ta sake saken wannan al'amarin yadda ya kasance. Da ya koma gida kasa sukuni yayi sai da ya zauna yayi shiru yana tunanin hanyar da zai sanar da Safeena zancen wanna auren bai san yaya zai yi mata bayani ta fahimta ba, saboda ita baudaddiya ce, duk yadda ka so ka fahimtar da ita abu bata yarda tafi aminta da abinda zuciyarta ta kitsa mata, balle yanzu. Da ta zama ma'akaciya dabi'unta gaba daya ta canza su, sau da yawa su kan sami sabanin ra'ayi a zamantakewarsu shi ya rasa dalili, to balle yanzu idan yake mata da wannan mafi munin zancen a gurinta. Da dare yayi lokacin kwanciyarsu yayi taje ta aki yaranta dakinsu ta janyo musu kofa ta nufi dakinsa, a bakin gadon ta same shi zaune ya tallabi kuncinsa da hannu 2, ta zo ta dan taba shi sannan ya dubeta yace, kin kwantar da su Yasmin ne? Tace, eh duk sunyi barci, na jika shiru ne a daki lfy dai kake kwana biyun nan ko? Yace lfy lau me kika gani? Lfy ta kalau, ta girgiza kai tace, ba lfy kake ba tunda ba haka na saba ganinka ba, inkuwa lfy jikinka yake to ba lfy zuciyarka take ba, akwai wata mummunar damuwa a tare da kai..... 96) Ya fuskance ta sosai, yace zauna muyi maganar tabbas, zuciyata akwai abinda ke damunta, na rasa ta yadda zan gaya miki ne ki fahimta shi yasa abinke damuna a zuciya yana mini ciwo, kin yarda in gaya miki ba za ki bani matsala ba? Tunda taji haka sai jikinta yayi sanyi ta san cewa akwai wani abu da zai faru da ita na bakin ciki, kuma kila daga zaria abin ya samo tushe, sai dai ba ta fatan abinda zuciyarta ke ayyana mata ya kasance gaskiyya. Ta zauna suka fuskanci juna sosai sannan tace, bana fatan abin da zaka gaya mini ya kawo matsala a tsakaninmu sai dai in dama lamarin mai matsala ne to kaga ba daga gareni bane. Ya janyo hannuwanta ya makale su cikin nata ya soma murza su a hankali ta sauke ajiyar zuciya, ta tsura masa idanu tana sauraronsa. Yace, safeena kiyi hkr nasan abin da zan gaya miki zaiyi miki ciwo, aure aka bani a zaria, kuma babu yadda zanyi in kaucewa auren dole na amsa. Hannuwanta ta fizge cikin nasa tamkar wadda ta rike rushin wuta, ta mike tana huci ta nuna shi da dan yatsanta sannan tace, daman na san za'a rina, wannan sintiri da kakeyi a zaria ai yayi yawa, tuni zuciyata ta soma ayyana mini wannan mugun lamarin ina yakice shi, ashe zai tabbata akaina ne da gaske. Yanzu kai kamar ka da Iliminka da kudinka da wayewarka, za'a baka aure baka so ka amsa, sai dai in dama can kana so ne amma ba zan yarda baka akayi ba, gara ka fito barao2 kace min ka nemo aure a zaria har an baka zan fi yarda. Yace, ni wlh ba ni na nema ba, bani akayi, kuma duk kudina da ilimi na da wayewata ban isa in ki bin umarnin na gaba da ni ba, har duniya ta nade su ne sama dani dole inyi musu biyayya, nafi son farin cikin su da nawa, nafi gudun bacin ransu akan nawa, shi yasa da suka bani auren na amsa tare da godiya don nasan ba dan su cutar da ni ne suka bani auren nan ba, alheri ne suka kulla. 97) Dama ai ba za su cutar da kai ba tunda abin alheri suka kulla maka, nice dai suka cuta zasu kulla min abinda ba alheri ba. Kaiko a family dinku waye ya baka wannan auren ka amsa? Yace ba wata bace sai wadda ta isa dani, wato hajiyata. Auren kuma da Aneesa ne za'ayi. Ta ware idanu tace, Hajiya ta baka auren Aneesa!!! Yanzu kai a wayewarka me zaka yi da wannan yarinyar? Yace shi yasa nima nake ganin idan kika kwantar da hankalinki zaki juya yarinyar nan duk yadda kika so, tunda ita ba mai hayaniya bace, ba zaki sami matsalat zama da ita ba. Ta dakatar da shi tace, Ya isa! Ya isa!! Tun yanzu har ka zo gaba na kana yabonta, tun bata zo gidan nan ba, to bari kaji in gaya maka aure ko kaje kayi Allah ya bada sa'a, amma tsakanin ni da kai babu sauran zaman lfy, balle ita kanta idan ta zo gidan zata gwammace gara agidan yari da gidan nan ban,don ba za taji dadi da ma'aurata keji a gidan aure ba, ai duk macen da tace zata auri mijin wata to (MIJIN ARO) zai zame mata, saboda haka ina nan ina jiran zuwanta. Ta dauki saman rigar baccinta da ta cire ta aje bisa gadonsa ta fice daga dakin, yana kiranta ko sauraronsa bata yi ba ta nufi dakinta, ta murza key ta rufe kofarta, don ma kada ya shigo ya dameta. Kwana tayi kuka da sake2 abinyi, amma har gari ya waye bata samo wa kanta mafita ba, na yadda zata wargaza auren. Da sassafe ko sauraronsa bata yi ba, ta tuta masa sako ta wayarsa, cewa zata fita anguwa, bata jira mai zaice ba ta fice, su Yusra gida ta barsu gurin mai kula da su. Gidan aminiyarta ta nufa, guri daya suke aiki, ta girmeta da shekaru akalla biyar. Haj. Nuratu manyan mata kenan masu juya naira saboda ba aikin kadai takeyi ba, tana safara zuwa Dubai, sannan shi ma mijinta juya shi takeyi tamkar karamin yaro duk da yake babban mutum ne amma macece ke jan ragamarsa. Tana ganin safeena ido kode ya jeme da kuka, ta riko ta suka shiga dakin barcinta, tana tsokanarta. Ho! 'Yar lelel Captain me kuma ya faru ne? Na dai san ba Captain bane tunda shi baya laifi kullum cikin faranta miki yakeyi, kece ma in 'yan tsiyarki ya tashi kike gara shi, bawan Allah inji ki, ni kam namiji ban dauke shi abin tausayi ba, sai da kawai ya bauta mini ni kuma in juya shi yadda raina ke so. 98) Safeena ta zauna tana sauke ajiyar zuciya tace, yau Captain ya tabo ni na daina yabonsa har abada in dai baya janye Alkaba'in da ya dauko mini ba. Haj. Nuratu ta kyalkyale da dariya tace, hala aure zaiyi, don nasan tatsuniyar maza bata wuce aure in dai sunji su lafiyyayu, ba sa son bin matar waje to yanzu za suce aure don ba su cika son cin tuwo daya kullum ba. Murmushin takaici Safeena tayi tace, wlh kamar kin sani aure zaiyi wai Hajiyarsa ce ta ba shi yarinyar a can zaria, kinma san yarinyar wadda zaki ga hajiyan nan- nan da ita tamkar wata autarta, wata fara sirirya, shegiya sai nono da duwawu ( Hahahaha kunji fah, ita ina nata) kilama shi Captain din ya gani suka tsole masa idanu, dan na san halin kayana. Haj. Nuratu ta saka dariya tace, ai tuni nake gaya miki namiji ba abin yarda bane, tun kafin ya saki kuka gara kiyi maganinsa ta yadda kina ganin sai yadda kikayi da shi, to ai ga irinta nan ya dauko auren er garinsu, en zariya masu shegen asiri, su kansu iyayen ba haka suke barin 'ya'yansu ba, yanzu ai kinga zama bai gammu ba, sai ki tashi mu san abinyi. Safeena ta tashi daga kishingidan da tayi tace, to hajiyarmu yanzun meye abinyi? Tace tashi zaki yi mu kama hanya dole mu hana auren, wani kauye zamuje nan kusa da birnin gwari, zaki ga aiki da cikwa. Sun hau motar Haj. Nuratu ne sukai ta sharara gudu awa daya da rabi sannan suka isa kauyen. Haj. Nuratu ta zayyanewa bokan abinda ke tafe su, yayi dariya yace, ku sha kuruminku daga auren har zarian ba zai kara yin maganarsu ba, ku tashi ku tafi. Suka aje masa kudi masu yawa suka baro kurgurmin dajin 99) Tun daga ranar Ishaq bai sakeyi wa safeena maganar aurensu ba, ta sa idanu taga ko zaije zaria nan ma shiru, tun daga tym din ta soma murna a ranta, asirinta ya kamshi, tunda har ta raba shi da auren da ya rakito ta nisanta shi da mahaifarsa. Hajiya kuma taji shiru ba zuwa ba waya, abin ya bata mamaki, abinda Ishaq bai taba yi ba don ba ya sati biyu bai zo ba mahaifarsa ba, in kuwa bai zo ba to baya kasar ne, to zai ta yiwa Hajiya waya yana bata hkr tare da jin lfiyarta, sai ga shi yanzu har yayi wata guda cur! Rabosa da zaria kuma ko yi mata waya, sai ita ne wani tym ta kan kira shi, amma ba ko yaushe take samunsa ba sai tayi sa'a, sau biyu idan ta kita safeena na dauka tace wai baya garin wayarce ke gida. Tun daga tym din Hajiya ta sha jinin jikinta, ta tashi tsaye da rokon Allah akansa sam, bata bacci dama ita, kauwama ce ( mai yawan tsayuwar dare) Kuma sauwama ce ( mai yawan azumin nafila ce). Har malamai nagartattu masu sani tasa suka dinga taya da rokon Allah. Gabatowar bikinsu da aksa ya zo ne tare da samun nasarar rokon Allah din da akayi masa, don kwatsam! Ranar juma'a Ishaq yace wa safeena zai taho zaria, abin ya bata mamaki ba ta gama dawowa daga duniyar mamakin da ta lula ba, kawai sai taji tashin motarsa ya bar gidan, ita ma mota ta sura ta nufi gidan Haj. Nuratu suka fantsama kuayen Birnin gwari, bokan nan ya tabbatar musu, tabbas za'ayi aure nan don kuwa yaga rabon haihuwa a tsakaninsu. Safeena ta dafe kirji tace, rabon haihuwa? Na shiga 3 gashi ai a haihuwar su Yusra nasa an juya mini mahaifata ba tare da ya sani ba, ba zan sake haihuwa ba, don Allah boka kasan yadda zakayi ka hana auren nan don ba zaiyi wu ina ji ina gani wata ta zo ta dinga haihuwa ba alhalin ni na daina, ga shi 'yan mazan da nake da takama da su Allah ya amshi daya saura daya, shima bani da tabbacin rayuwarsa... 100) Yayi en surkullensa ya gama sannan ya dubeta yace, zan iya hana auren amma ba zan iya hana samuwar rabonda ke tsakaninsu ba, ki yarda yayi zina da ita su haifi rabon da ke tsakaninsu ba tare da auren ba? Tayi saurin gyada kai tace, wlh na yarda in dai ba za suyi aure ba ko meye suje suyi ko 'ya'ya gima za'a haifa masa a waje na yarda in dai ba zai auro mace ya kawo mini gida ta zama kishiyata.***** *********** Wa 'iya zubillah! Kuskuren da mata keyi kenan da akawo musu kishiyar cikin gida ta saunna gara a aje kishiyar titi, ayi ta masha'a in da rabo ma har a haifar masa 'ya'ay'ye a titi babu ruwanta tunda ba 'ya'yan cikin gida na sunna bane! Anya munyi wa mijinmu da yaran da zai haifa a waje da ita matar da yake so ya auro kika hana adalci? Shin meye makomar ki idan kika yi irin wannan sanadin ranar gobe kiyama? *************** ********** Boka yace, an gama yau zan zuba ma yarinyar rabonsa a mahaifarta, tun da naga rabon da ke tsakaninsu mai gaggawa ne, in yaso hakan sai ya zamo sanadin fasawar auren, don idan ta sami cikin akwai abinda zamuyi masa yayi musun, cikin ba nasa bane, idan tace shi yayi mata kinga zumuncin da ke tsakaninsu ma duk zai rushe, sai suyi uwar watsi kowa tasa ta fisheshi. Safeena da Haj. Nuratu suka tafa duniya tayi musu dadi. Naura dubu dari suka direwa boka saboda suna son aikin cikin gaggawa kafin ya dawo Abuja mai aukuwa ta auku, tunda yace gamuwa daya zasuyi ya yada mata rabonsa, to gara ayi gamuwar da gaggwa ko hanaklinsu ya huta. Kwatsam! Hajiya taji ladidi na murna tare da hamdala. Bata zaci Ishaq bane, ta dauka wani abin ne ya faru take murna, tana fitowa sai taga Ishaq, murmushi tayi masa tace, maraba da dan gidan Hajiya. Ya isa gabanta ya kama hannunwanta yace, Hajiya bakiyi fushi da ni ba ko? Na rasa yadda akayi har sati 4 banzo gida ba, yau kawai naji ke da en uwana nake son gani, kiyi min afuwa, ki gafarta mini hajiyata. 101) Ta bugi kafadarsa tace, babu komai muna tare da Allah sai zai shige mana gaba ni banyi fushi da kai ba. Aneesa na zaune tana jinsu karaf! Idanunsa ya sarke da nata yayi mata murmushi yace, a'a kanwata kina kallona ashe baki zo yi min oyoyo ba, ga ladidi da Hajiyata sai murna sukeyi. Ta taso tana murmushi tace, sannu da zuwa kazo lfy? Ya su suhail? Ya ji dadi aransa yadda komia zatayi sai tambayi yaransa, shi kam, ko don haka ma zai iya aurenta a matsayin tana mai kauna yaransa. Yace duk suna lfy, sunce na gaida Auntyn zariya, sukayi dariya ita da su Hajiya. Da yamma bayan ya tashi daga bacci da yayi tun zuwansa, yayi wanka ya sallaci la'asar ya sake wata kaftani ta shadda ya murza hula ya fesa turare ya iske Hajiya a dakinta, tana ganinsa tace, a'a sai ina kuma? Ina fatan Anguwan juma zaka je don suna kewarka? Yace zan shiga gaida surukaina ne, ina ita matar tawa naga sai dari2 take da ni. Hajiya tace, ta tafi gida amma yanzu zata dawo daga can ka biya gidan yayyinka, maman su sadiq tasha ciwo. Yace ba dai ciwonta ne ya tashi ba? Tace shine wannan karon ta sha wuya, yace idan nutsu zan fita da ita kasar waje dob akwai wani shahararren likitan zuciya da ita kasar da naga sanarwa aikinsa ta internet, can zan kaita a dubata. Hajiya tace Allah ya taimaka ya baka iko. Daga gidansu Aneesa yaje Unguwar juma daga nan gidan yayyinsa yabi dukkansu ukun da sauran gidajen en uwansa. Sannan ya dawo gida. Washegari tunda yaga Aneesa tana hada masa abin karya a kicin din Hajiya yaji wani abu na masa yawo a kwanya game da ita, zuciyarsa na kitsa masa wani mummunan lamari wanda ba yanzu bane hakan ya kamata ya bijiro masa a zuciya ba, amma yaji shedan na ta rinjayarsa. Wata irin matsananciyar sha'awar Aneesa yake ji wanda bai taba jin sha'awar diya mace ya bijiro masa irin haka ba. 102) Yayi kokarinsa ya danne abin amma ya gagare shi, saboda duk gilmawar da tayi sai yaji abu na masa yawo a tsokar jikinsa, surorinta ne kawai ke masa gizo, a daddafe yayi sallar magriba ya shigo yana ganinta abin ya dawo masa sabo. Ya dubeta yace, kinyi sallar magriba? Tace nayi, yanzun na idar gama abincinka can. Yace bar abincin nan ina Hajiya? Tace, tana daki ina jin ta idar da sallah yanzu. Ya sami Hajiya a daki a zauna gefenta bisa carpet yace, zan fita anguwa ne, amma zaki bani aron 'yarki ta rakani, ko nayi ba daidai ba? Tace, Gaskiyya ba zai yiwu ka fita da ita ba, tunda ba matarka bace, mai zatayi maka idan ta rakaka? Yace Hajiya kin manta dazun nan su baba Ali suka zo gidansu suka kawo sadakinta iyayenta sun amsa sunce sun bani. Amma wannan ba hujja bace da zai sa I fita da ita ba. Zata dai rakani ne nan GRA gidan abokina Captain yawale zamu duba wasu kayan sawa na mata ne da matarsa ta kawo daga china, ko a gidan zan iya hado lefen tunda babu abinda bata sayarwa har akwatuna. Haka ya kashe Hajiya da dadin baki ya dauko Aneesa a motarsa suka nufo GRA. Aneesa tunda ta shiga motarsa sanyin Ac da kamshin turarensa ya kashe mata jiki tayi lakwas, shi kam sai kallonta yake yadda tayi masa kyau shi kansa ya san idan ya aureta zai more sosai saboda yarinyar tana da abubuwan da yake so ajikin mace. Tun kafin su iso inda zasuje, taji kirjinta na bugawa, bata san dalili ba, har suka is wani dandasheshen gida a cikin GRA. Mai gadi ya zo ya bude musu gate suka shiga ciki, ita dai tunda ta zauna a falon gidan bata ji motsin masu gidan ba, illah kukan tsuntsaye bataji tsoron komai ba, don ta tabbata Ishaq ba zai halakar da ita ba. Can ya fito da lemu mai sanyi ya mika mata, ta amsa ta ajiye ya zo ya matsa mata wai ta sha kafin masu gidan su fito, can sai ya fito yace ta shigo ciki ta gaida Hajiyan sai ta duba kayayyakin. Wani dakin barrci taga sun shiga, yace ta zauna bari ya fito, ita dai dama jiri ta soma ji shiya sa ta kosa ta zauna, tana zama sai ta soma ganin taurari taurari suna gilmawa daga nan sai taga dindin, jikinta duk ya mace sama2 take ganin abinda ke faruwa, Ishaq ya kwantar da ita flat a gadon nan ya rabata da rigar jikinta, tayi kokarin ta hana shi amma ta kasa, jikinta ba kwari, shi kanshi jinsa yake tamkar ana azalzala shi ya aikata abinda zuciyarsa ke raya masa, bai san kuma takamaiman dalilinsa na aikata wannan cin amanar ba. KARSHEN BOOK 1 Ebook din nan yazo maku ne daga shafin http://hausaebooks.cf Namba daya a fadin Africa . Ga mai bukatar wasu hausa ebooks din sai yayi maza maza ya ziyarci shafinmu na yanar gizo gizo akan adireshi http://hausaebooks.cf . Wanda yake son a mayar mai da littafinsa ya koma ebook sai yayi sauri ya samemu a shafinmu na facebook ta hanyar bin wannan adireshi http://fb.com/hausaebooks Sai yayi like da mu sannan ya sanar da mu dukkan abun da yake bukata . An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7