Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
baiwa ne ta bangaren karatunsa, a aviation har zuwa fita kasar turai da yayi karatu, zuwa aikinsa a Nnamdi Azikwe international airport a abuja. Tayi sallama ta shigo, ya amsa sallamarta sannan ya nuna mata kujerar da ke fuskantarshi yace ta zauna, kafin ta zauna sai ta tambayeshi Hajiya yace, yanxun ta shiga daki je ki gaisheta ki dawo. Taje ta gaida Hajiya sannan ta dawo gurinsa ta zauna ta gaishe shi tace, ina su suhail da mamansu? Yace yanzu drive ya kaita gidansu wata kawarta da sukayi karatu tare a jami'ar abuja, za su dameni na tarkata mata su ya hada mata da su da mai rainon su Yusra. Sun danyi shiru ya soma mata dangane da karatuna ta gaya masa komai, yace to akwai kudi zan dinga turowa ta account din Hajiya na hidamarku ke da kanneki, don bana son in kuna cikin matsa ko yaya take, duk sati hajiya zata dinga baku kudin da za kuyi anfani da su, larurar shc kuma komai ya taso kije ki gaya mata, bana son zurfin ciki irin naki, sannan wayar mama da take hannunki ki ba Abbanku, bana so ki rike waya, saboda ina son ki fito da sakamon sch ma kyau ta yadda ko da kinsa mi mijin mun aurar da ke zaki cigaba da karatun jami'a a gidansa, Hajiya ta taba gaya min akwai yaron da ke son auranki dan gida ne, ina fatan kina sonsa ko? Ta sinne fuskarta hakan ya bashi tabbacin tana son yaron. 67) To tunda kina sonsa sai ki tsaida shi banda jajibe2 kinsan yawancin samarin yanzun mayaudara ne, kada ki biye dadin bakin wasunsu basu da kirki, kina jina? Ta gyada kai. Ya saka hannu a aljihu ya dauko kudi dubu biyar ya mika mata yace, ga wannan ki rike a hannunki ko da wani abu zai taso muku, mu yau zamu wuce insha Allahu, amma nxt wk idan na sami tym zanzo, ki ci gaba da hkr, ki kula da kannenki sosai kisa ido a karatunsu kada ki bari suna fashi sai da kwakwaran dalili kinji? Tace Insha Allahu zan kula, mun gode Allah ya kaiku gida lfy, yace ameen. Tana gidan har su safeena suka dawo da yake basu dade ba, suna dawowa sukayi shirin wucewa, su sultan suka rike Aneesa wai saai an tafi da ita. Ishaq yace tana yin jarabawa ku bari idan ta gama sai ta zo can ta sameku, suka ce to su zasu zauna gurin Hajiya su jirata ta gama jarabawar, yace to ku kuma naku karatun wa zaiyi muku? Da kyar dai aka lallaba su suka tafi. Bayan tafiyarsu ta dawo cikin gida tare da Hajiya, haka kurum taji Hajiya taji tana dada jin tsananin tausayin Aneesa fiye da sauran yaran. Saboda tafi shakuwa da maman sannan yanzun duk wani nauyin kula da yaran zai koma kanta, da ma can ita ce ta jibanci yawancin al'amuransu. Hajiya ma haka ta tasa Aneesa gaba da nasihohi da en shawarwari akan yadda zaman gidan su, da ita kanta yadda zata kame mutuncinta tunda yanzun babu mai kulawa da tarbiyarsu a gidan sai wanda Allah ya so...... 68) *************** *************** ************** A halin yaanzu Aneesa ta shiga ajinta na karshe kenan na secondary, Iyayen sagir sun zo sunyi maganar neman masa aurenta, saboda yanzun har ya sami ya so mayi. Shi ya sa ya ji ya matsu ayi bikin nasu. Baban sasa da yake shine waliyyunsu sai yace ya ba shi, suka kawo kudin gaisuwa, aka saka ranar biki idan ta kammala karatunta, amma ba'a tsayar da ranar ba sai ta kammala tukunna. Hajiya ita ce uwar biki, shi yasa duk wasu sayayya da uwa keyi idan zata aurar da diyarta ta dauki Aneesa sun shiga kasuwa sun sayi waasu abubuwan, da suka je Ummara ma ta siyo wasu. Ranar wata juma'a Aneesa ta shirya tsaf cikin atampa kalar atamafar ya amshi jikinta, to dora bakar riga ta yane kanta da gyalen ta sa pin ta matse. Basira ce ta aiketa wani gida a gwarbai, ta fito kofar gida rike da sakon a irin babbar ledar nan, a kofar gida taga wani mutum tsaye, ta tsaya ta dan risina ta gaisheshi, duk da bata san shi ba, yace dan Allah Alh Ali ya dawo kuwa? Tace bai dawo ba, amma nasan yana kan hanya. Yace ko ke diyarsa ce? Tace eh, yace yauwa dama wani muhimmin sako ne, tunda na ganki natsatsiya bari in baki, don Allah idan ya dawo ki bashi, zan kira shi a waya in yi masa karin bayani. Ya dauko wani file a bayan motarsa ya mika mata tare da cewa, don Allah ki adana sosai kafin ya dawo, nagode sai anjima. Ya shiga motarsa ya wuce. Har ta juya zata koma cikin gidan sai tayi tunanin bari kawai ta wuce da shi don bata sani ba ko abinda ke ciki sirri ne. Ko wasu muhimman takardu kada taje ta ajiye tsautsayi ya same su ta shiga uku, ko kuma basira tana iya bin sahu ta dauke ta boye don kawai Abbansu ya wulakantata. Idan ko ta boyen kanneta zata lakabawa ko ta yaga tace sune, tunda haka take musu binciki da ance sunyi kaza zai kama su da duka kamar Allah ya aiko shi, shi ya sa take taka tsantsan bata son laifin da za'a ce kanneta ne suka yi, tafi son ace idan ma dukan ne gara ya doketa, ko da yake yanzun ta girma da wuya ne zata yi laifi ya bugeta, sai dai idan Basira tace tayi mata abu kaza daga ranar ya daina amsa gaisuwarta. Idan tace abu kaza nasu ya kare ta aiko kanneta ba zai saya musu ba, sai ya ga dama... 69) Ita kuma Aneesa duk kudin idan Ishaw ya zo ya bata ko Hajiya ta bata boyewa take yi saboda Basira ta fara kulla mata sharrin wai yawonta take xuwa tana samo kudi gurin maza, ranar da ta kulla mata wannan sharrin tayi kuka tamkar ranta zai fita. Shi kuma Abbansu ya hau kai ya zauna tamkat bai san Ishaq ke musu hidimomi ba, alhalin wani tym din ma agaban shi yake bata kudin, ya ba Abban ita ma basira idan tana nan ya bata, idan kuma bata nan zai bayar yace a jiye mata, amma don sharri sai ta bage da yi maya sharri shi kuma Uban ya yarda har yana tirketa wai ta gaya masa gidan uban take xuwa idan baya nan ta samo kudi. Tai masa rantsuwa babu inda take zuwa duk bai yarda ba tana kuka taje ta dauko alkurani izifi sittin kuma cikakke ta zo gabansa ta dafa alquranin zata ranste ya kwace yana fada wai zata janyo masa masifa waya gaya mata ana rantsu da Alkurani, balle ita da baya da tabbacin tana da gaskiyya, akan abinda zata rantse din. Tace gara ya barta ta rantse ko da ajalinta ne zai sauka gara ya sauka ta huta akan kazafin da akayi mata. Da ya hanata haka tayi ta kuka, kusan sati tana kuka tare da ciwo mai tsanani da ya kamata, har sai da Hajiya ta zo gidan da kanta ta dauketa suka je asibiti, aka bata magunguna da allurai. Ta saka file din cikin ledat nan taga gara ta tafi da shi idan ta dawo ta san tym din ya dawo sai ta bashi bakinta kanin kafarta. Ta isa gidan da zata kai sako, ta tarar matar bata nan amma yanzun akace zata dawo ta jirata, gashi bata son tayi dare, saboda yamma ta gabato sosai, ta so ta bar sakon sai ta tuna Basira tace tabata ne hannu da hannu kada ta ba kowa. Kusan magriba sannan ta dawo ta bata sakon sannan ta riko file dina nan ta taho gida. 70) Mashin tayi tunanin hawa saboda shine zai kaita gida akan lokaci, don kuwa idan tace mota zata hau sai ta fito bakin titi ta shigo ta kuma kafin ta fita lungun nan sai ta dade. Tana dan tafiya tana waigen mashin. Kawai sai taji tafiyar mutum abayanta, ta soma taku da sauri saboda tsabar tsoro, can sai taji an ja gefen Hijab dinta, ta waigo da zafin tsiwarta zata yayyafawa ko waye masifa, kawai sai tayi ido hudu da sagir, ta sauke ajiyar hrt tace, Amma wlh ka bani tsoro daga sama ko kasa? Yace daga ina kike ke da magriban nan. Kin zo unguwarmu ko ki neme ni, dama ko sabon gidan mu baki taba zuwa ba. Tayi murmushi tace haka kurum sai in zo gidanku, da dai ina zuwa idan ana sha'ani da su haulat to amma yanzu ai da kunya ko? Yace meye abin kunya kefa 'yar gida ce a gidan mu tamkar su Haula, yanzu dai mu karasa ki gauda su Hajiya sai in kaiki a hala ta. Ta tsuntsire da dariya tace, au ashe kayi hala ban sani ba, daga mashin ashe mun koma hala. Yace lah? Baki san mashin din shine hala ta ba, ai wannan mashin dinmu shine halar samari. Ta sake dariya tace, kai sagir baka da dama. Gaskiyya ka rakani hanya kawai in hau mashin da ba son Aunty Basira ta aiko ni gurinta ba ta nan bane na tsaya jiranta da baka ganni ba. Yace, rabon zamu hadun ne ya sa hakan ta faru. Amma fa babu yadda za'ayi ina kallo ki hau bayan wani kato ya goya min ke alhalin gani kuma ina da mashin din nan. Don Allah zo muje da yanzun kin gaishesu ma munfito. Haka nan dai ya tilasta mata suka shiga gidansu. Da yake iyayensa masu mutnci ne suka dinga haba2 da ita. Ita kam, a darare ta dofana ta zauna, en matan gida ne suka gaisheta a wulankce, suna wani jin kai, ita dai duk ta kosa su bar gidan. Tana ji yana gaya musu, shima yanzun ya ganta an aikota gidan Alh. Isa tana tsaye tana jiran mashin shine ya cqQWe gara shi ya goyata a nashi mashin ya kaita gidan da wani kato ya dauketa, ko ba haka ba Hajiya? Yake tambyar mamansu Hanne, er tsohuwa tace, haka nan ne dana kana da gaskiyya. Suka yi ta dariya... 71) Sun fito daidai barandar gidan kenan. Sukaji hon din mita zata shigo, ya dubeta yace, ga alhajinmu nan ya dawo shima sai ku gaisa. Ta dafe kirji tace, gaskiyya ba zan iya ba kunyarsa nake ji sosai, don Allah ina zan boye idan ya shiga cikin gidan sai in wuce, ya janyo gefen hijb dinta yace, yace zo ki boye anan ai yanzun zai shige sai mu tafi. Da sauri ta bi bayansa ya tura kofar wani daki anan harabar gidan ta shiga, ta nemi gefen gado ta dan zauna a tsorace, sai ya da ya fita ne ta karewa dakin kallo ashe dakin sagir ne, sai ta tsorace, ita kam gara ma da ta tsaya ta gaida Alhajin ne da ya fiye mata, gashi sagir ya kutso ta dakinsa, kada kannensa suzo su ganta suce dama gurinsa ta zo ta fake da cewa an aiko ne gidan Alh. Isa. Alhajinsu na shigowa yayi fakin din motarsa. Sagir ya matsa ya gaishe shi ya amsa, yace sadiq ya dawo ne kuwa? Yace a'a bai dawo ba. Yace, ok to zo ka rakani nan gidan Mal. Ado ance bai jin dadi mu gaisheshi. Sagir ya dan kalli dakinsa yace to alh. Bari in dauko waya ta a daki. Ya shigo ya sami Aneesa a tsaye duk ta tsorace yace, bari in dan raka Alhaji dubiyar wani makocinmu ga gidan nan kusa yanzu zamu dawo. Tace sagir bari kawai in tafi kaga dare yayi Abbanmu ya dawo kada in jawa kaina laifi. Yace wlh ba dadewa zamuyi ba yi hkr. Ya fito ya ja kofar, Alh. yace ka rufe da key kaga ba kowa yau aharabar gidan, ko ka manta ranar da aka kwashe muku kaya ne. Ya kulle kofar da mukullin suka fita, su ka ci karo da kaninsa Sadiq shi dakinsu daya da hanne, ya mika masa key din tare da yi masa rada a kunne Akwai matata a dakin ka taya ta hira kafin mu dawo yanzu. Allah Allah sadiq yake ya bude yaga wacece, idan ta bashi fuska ma ya dan rage ahanya a gurinta, tunda dai yasan duk en matan da suke kawowa nan, en hutu ne. Basa kawo mai mutunci. Musamman shi sadiq da ya maida mace tamkar riga yau idan ya saka wannan gobe wata zai saka. Shi kam sagir da wuya kaga mace ya kawo sai dai irin marasa mutuncin nan sun su biyo shi en asha minti.....MIJIN ARO 1 **11 72) Yana bude kofa ya ci karo da Aneesa tayi tsuru2 a tsaye. Yayi murmushi yace, au dama kece, meye abin tsoro ki saki jikin mana ke da dakin mijinki. Tace haba dakin miji ai ba'a daura aure ba, tsautsayi ne ma yanzu ya shigo da ni dakinsa don wlh bansan dakinsa bane. Sadiq yayi wata munafukar dariya yace, Tsautsayi! To ai dama akan sami irin wannan tsautsauyin, balle irinku da kiris ya rage. Sai ya canza zancen nasa zuwa wata siga, hakan ya sa tayi shiru. Ya nuna mata gefen gado yace, ki zauna mana ai yanzu zai dawo. Ta ki zama, ya mika hannu yace muga file din hannunki na menene? Tace na Abbanmu ne aka bani inbashi. Ya matsa wai a dole sai ya amsa ya gani, da taga so yake ya hada jikinsa da na ta sai ta sakar masa. A gaugauce sagir ya shigo dakin yace, don Allah amarya yi hkr, ta so muje in kaiki gida, ai bamu dade b. Ita dai da sauri ta mike suka fito tana ta tsoron kada wani ganta bayan ganin da sadiq yayi mata gashi har ya neman yi musu wata fassara. Tun a bakin titi Aneesa tace sagir ya sauketa. Ta karasa, shi kuma ya koma, sai yace sam, ba zai yiwu ba ya ajeta a bakin titi, to meye anfanin kawo ta din da yayi, ita kuma tsoro take ji kada agansu tare a dauka wani gurin suka je tare, tunda yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba. Allah ya taimaketa babu kowa a kofar gidan shi yasa yana tsayar da mashin din ta shiga gida da saurinta. Abinda take tsoro shi ne dai ya faru, saboda Abbansu ta gani atsakar gida da Basira suna tsaye, ya sakar mata harara yace, daga gidan ubanwa kike? Ta dubi Basira wadda ta dauke kanta tace, Aunty Basira ce ta aikeni... Yace yanxun daga inda aka akeki kike ko ya? 73 MA IS BLANK PAGE 74) Yace maza taje ta nemo masa file din sa, yanzun zai fita da shi office. Gidan Hajiya ta shiga tana ganinta tace lfy? Ina zaki da sassafe? Ta gayawa Hajiya abinda ya faru amma bata gaya mata gaskiyyar inda ta bar file din ba, saboda bata son Hajiya taji ta shiga dakin sagir don ba mutuncinta bane. Hajiya tace, ki tashi tunda yana jiranki, kiyi maza ki dauko masa, Allah yasa sun gani sun boye tunda kawar Basira ce, balle taji furucin da Abbanku yayi.... Aneesa ta miki tace, Hajiya dan bani wayarki in kirata inki, hajiya tace tana daki je ki dauka, bata fito ba a dakin ta kira numbar sagir ta tambaye shi ko yaga wani file da ta bari a akan stool din dakinsa, yace ya gani Amma ya dauka na sadiq ne, shi yanzu ya fita ta bari zai kawo mata gida. Tace, ai gani nan a hanya zanzo in amsa na abbanmu ne, yace yanzun zai fita da shi office. Yace to ki karasa gidan sadiq na nan. Ko kuma ki bari in kira shi sai ya kawo miki gida. Tayi saurin cewa ka barrshi kawai zanje in amsa. Allah ya taimaka harabar gidan babu kowa, dama tana tsoron kada wani dan gidan ya ganta, ta shiga 3. Abude din yake, tayi sallama ta shiga sadiq na zaune yana shafa mai da alama wanka ya fito, yana sanye da singlet da dogon wando. Ya dubeta yayi murmushi yace, daga ina haka? Na ganki a tsorace? Ya sagir din yayi sammakon fita gurin aiki, tace dama ba gurinsa na zo ba, file din nan na jiya da ka gani shi na manta na zo dauka, sagir yace ka bani. Yace file? Na dauka da shi kika fita? Ai kuwa ban ganshi ba, ta gintse fuska saboda ta lura yana son maida abin wasan yara, tace wlh anan na barshi shi sagir ma yace ya ganshi. Yace ok to dan zauna bari in sa riga sai ki tayani mu duba. Ta daure fuska sosai tace, gaskiyya ba zama na zo yi ba, daukan file kawai na zoyi Abbanmu na can na jirana, don Allah idan ka gani ka bani. Yace maida wukar na tsinta, idan na baki wani tukwici zaki bani? Taji sanyi aranta da yace ya gani, tace au sai na baka tukwici? To fadi nawa kake so? Yayi murmushi, ni ba kudi zaki bani ba, bari kiga tukwicin.... 75) Kawai sai taga ya ja kofar dakin yana juyowa taja da baya tace, sadiq me kake nufi da nine? Ni fa ba irin en iskan en matan nan da ka sani bane, in ma banda rashin mutunci irin naka, ka rasa wadda zaka yiwa irin wannan cin zarafin sai ni da muke shirin aure da danuwanka. Ai ko wani ka ga zaiyi min irin haka, a tunani na sai inda karfinka ya kare dole zaka kare min mutuncina, albarkacin danuwanka. Kaga bani file dina in fita a dakin nan. Ya murmusa, haba Aneesa shi dan uwan nawa ince jiya nan kika wuni gurinshi ya gama kwasar gararsa, to meye nima don zaki sammin ragowarsa. Hawaye ya gangaro a fuskarta tace, haka dan uwan naka ya gaya maka? To ni sagir a gurina mai mutunci ne tunda ko hannuna bai taba rikewa ba, balle mugun alkabain da kake ikiraran mun aikata. Ni kam! Na bar ka da Allah shi zaiyi mana hisabi da kai ranar gobe kiyama, yanzun ka bani file dina in tafi ko in yi maka ihu... Dariya ya kyalkyale da ita yace, kiyi ihu azo a ganki kin kawo kanki gurin maza, kinga jiya an ganki a gidan nan da sagir yau kuma kin kanki gurina, kinga sai ta tabbata jarabarki ta isa. Oya! Yi ihun ina jiranki. Ta soma kuka saboda tausayin kanta yau Allah ya hadata da macuci mara tsoron Allah kuma masharranci. Addu'a ta soma karantowa a ranta saboda Allah ya kareta daga sharrin da yake shirin kulla mata, wanda idan ya kulla mata shi bata da mai shaidarta sai Allah, tunda gata adakinsu, balle kuma idan zance yaje kunnen abbansu ta shiga uku, dama ya furta kalmar zargin wani abu tsakaninta da sagir, idan yaji haka kuma shi kenan zaice zarginsa ya zamo gaskiyya. Ta durkusa tana kuka tana rokonsa ya bata file din don Allah. Da ta so ta kyale shi ta tafi tasan idan sagir ya dawo dole ya bashi, to amma tana tsoron me zai faru idan ta koma gida babu shi, dole idan abu yayi nisa a san a dakinsu sagir ta bar file din. Da kyar ya dauko ya bata da sassarfa ta fita a dakin tayi saurin ta bar harabar gurin... 76) Gidan Hajiya ta fara shiga saboda ta dan gyara fuskarta ko wanketa ne tayi, dalilin kukan da ta sha. Hajiya na ganin idanunta jajaye ta soma tambayar. Kin koma gida ne? Tace ban koma ba, yanzun na dawo, wani abu ya faru ne? Tace na dauka ko yayanki ya kira ta wayar Abbanku ne yayi magana da ke. Tace meye ya faru? Yanzun ne yayi min waya wai an kwantar da sultan a asibiti, ciwo sosai yakeyi Typhoid n Malaria, Tace subhanallahi! Ban shiga gidan kilan ya kira, Allah sarki sultan ikon Allah kenan gadonsu fah lullube yake da net, ruwa ma na gora suke sha, lallai na yarda duk kariyar mutum sai in Allah yin ikonsa, shiga cikin gidan sauro ko shan ruwan gora bai isa ya hana mutum kamuwa da ciwo ba, idan Allah ya nufa ciwon zai kama mutum kamuwa da ciwo ba idan Allah ya nufa ciwon zai kama mutum, in har kuwa mutum yayi taka tsan-tsan da lafiyarsa yaga cuta bata sameshi ba, ba to kada ya dauka daga gare shi ne, a'a daga Allah ne wannan. Kin amso file din? Ta nuna mata, gashi na ganshi Allah ya taimake ni. Tace, to maza ki kai masa kada kuma kiyi wani laifin. Tace Hajiya zaki duba jikin sultan din ne? Tace zanje gobe Insha Allahu, ina jin ma dake zamu tafi don sultan din ni dake yake ta kira, shi ya sa ma Ishaq yace zai kira Abbanku ya roke shi goben in tafi da ke. Tace, Allah ya sa ya barni, don nima naji ina son ganin Sultan din. Washe gari driver ya dauke Hajiya da Aneesa ya kaisu Abuja, kai tsaye asibitin suka wuce saboda Aneesa tasan asibitin sun taba zuwa da safeena. Yanayin yadda suka ga jikin sultan din abin ya basu tsoro don yana jin jiki sosai. Yana ganin shigowarsu ya miko wa Hajiya hannu ta matsa ta rike shi tace sannu Hassan, Allah ya baka lfy. Ashe haka ciwon ya kamaka sosai. Ya sake mika hannun gurin Aneesa ta matsa ta rike shi, tana masa sannu. Safeena ta matso suka gaisa, suka tambayi mai jiki. 77) Hajiya tace ina su Husaini, yace yanzun dukkansu dadynsu ya wuce da su gida yau duk rigima suke jin tunda muka zo da safe suke kuka, da yake dadynsu ne yake kwana da Sultan din ni sai in koma fida. Bari in sanar masa isowarku, ta dauko wayarta ta kira shi ta gaya masa zuwansu Hajiya yace gashi nan zuwa. Lokacin da ya shig Aneesa zaune take gefen gadon tana ba sultan tea, ya dube su yace, kai! Kai! Aneesa anyi sa'a yau sam yaki cin komai lallai zuwanki yayi kyau, dama tunda ya fara ciwon yake kiran Auntyn zariya da Hajiyan Zariya. Hajiya tace ai gamu munzo ashe haka jikin yayi? To Allah ya bashi lfy. Yace ameen... Sannan ya matsa gefen Hajiyar suka gaisa, yace ina ga tunda kunga jikin nasa sai muje in kaiku gida ku huta, ko da yamma ne sai in dawo da ku. Ya kwashe su ya kaisu gida, suka ci abinci sukayi sallah, sannan suka dankwanta, bayan la'asar sannan suka sake koma. Kwanansu daya a abuja a washe garin na biyunne zasu koma saboda jkin sultan din ya fara sauki, don daren da za su koma gida cewa yayi sai su Hajiyan su tafi dashi gida, ba zai zauna asibitin ba, tace to su tafi ita sai ta kwana da shi, ishaq yace ai ba zata iya rigimar sultan ba, don sam basa bacci ciwon yafi matsa masa cikin dare, da kyar aka lallashe shi suka tafi, sai kuka yake shi dai akai shi gida. Sun idar da sallah subahi kenan, hajiya taji an kirata a waya, Aneesa dake kusa da wayar tayi saurin miko mata tana cewa Ya Ishaq ne. Hajiya ta amsa tana cewa, kila har yanzun rigimar Hassan yakeyi, ina ganin yanzun zan shirya in iso asibitin jira har mafarkinsa nayi. Ta kara wayar a kunne suka gaisa da Ishaq ta tambaye shi mai jki, yace jiki kam Allah ya kawo iyakar ciwo, don gabanin kiran subahi ya amsa kiran Ubangiji, yanzun haka gamu nan tahowa gida. 78) Salati Hajiya ta sa, Aneesa ta matso tana tambayarta abinda ya faru duk da yake ta sha jinin jikinta, saboda yadda taji Hajiya ta saki salati. Hajiya tace Aneesa Hassan ya amsa kiran Ubangiji, Allah yayi masa rasuwa da subahin nan. Aneesa rudewa tayi, ta mike tsaye tana tafa hannuwa tana salati. Hajiya ta riketa tace, zauna ina zaki je? Inda ya tafi muma muna nan zuwa mu same shi, yanzu ko anjima, yau ne ko gobe ne ba sani ba. Tace mominsu ta sani? Tace ban sani ba ko ya kirata ya gaya mata, bari in sameta. Ke kika zauna nan dan ganinki da hawayen nan ita zata rude. Hajiya ta kwankwasa dakin safeena tare da yin sallama, daga ciki safeena ta zo ta bude kofar, tana ganin Hajiya jikinta yayi sanyi, ta bata hanya ta shiga dakin taga su Yautsa bisa kujera an har anyi musu wanka mai ake shafa musu. Duk suka haye jikin Hajiya. Safeena ta gaida Hajiya sannan hajiyan tace hassana har kunyi wanka ne? Yau dai ba sch. Tace, eh asibiti nake son mu tafi da wuri don kwana nayi ina mafarkin Sultan din yana ta bina yana kuka wai shi gida zai je akai shi gida, ni kuma tunda naga ya sami sauki, ko za'a salleme shi ne mu dawo gida tunda yafi son gidan. Tausayin ta ya kama Hajiya lallai safeena bata san danta ya rasu ba, mafarkin da tayi kuma dama tunda taji yana kuka zaije gida zuciyarta ta bata anya yarin nan ba gidansa na gaskiyya yake kuka zashi ba, ita dai tun jiya ta tsinke da al'amarin yaron shiru kawai tayi, ashe tunaninta zai zama gaskiyya. Hajiya tace yayi min waya yanzu an sallame su gasu nan ma tahiwa gida. Tace, an sallame su? Sallama da asussuba? Ko dai sultan din ya mutu ne ya boye miki yace, an sallamesu? Hajiya tace, haba mutuwa, in ma mutuwarce idan yagaya mana mai zamuyi inba hkr ba, tunda ba mu muka ba kanmu shi ba. Allah ne ya bamu aronsa, don ya amshi abinsa saimuyi masa butulci ko waye? Ai kuwa mutwa na sabon da akayi da mutum shi ake wa kuka ba mutuwar ba, da bata tsallake kan kowa, duk zaman ta mukeyi, kinga ki kwantar da hankalinki mu tsaimayi isoawarsu, ki sa aranki abinda ya faru daga Allane, ba wain don baya so Bawan sa bane jarabartasa mu da ta rashi, a'a jarabawace, bawa baya tawakkali to ya ci jarabarwar ubangiji, shi yasa muke addu'a Allah ya sa mu daga cikin musu juriya da dukkan da dukkan abinda Allah zai dora masa. 79) Kuka safeena ta somayi, ta zauna daf da hajiya tace dan Allah hajiya idan ya mutu ne ki gaya min wlh nayi miki alkwarin zanyi tawakkali kamar yadda kika tunasheni yanzun, tunda nasan duk son da nake masa bai kai wanda Allah ke masa ba, fata na Allah ya bamu hkrn jure rashinsa. Da taga Hajiya ta soma zubda kwalla sai ta shiga jero salati, Hajiya ta riko ta tace, kiyi hkr, kiyi juriya, ki yiwa Allah godiya shi ya baki Hassa yau ya amshi abinsa, kiyi masa addu'a rahamar Allah, bashi da hakkin kowa sai dai Allah ya sa mai cetonmu ne. Hajiya ce ta sa wa su Yusra kaya ita kuma safeena tana zaune tana sharar kwalla, har suka ji isowar su Ishaq fargaba ya dinga yi na yadda zai shigo yace ya tunkari Safeena da rasuwar sultan, saboda ya santa yanzun zata hargitsa kanta, bai san Allah ya taimakeshi Hajiyarsa ta sanar mata ba, ta hanyar nasiha da lumana, kuma har tayi tawakkali. Yana shiga dakinta yayi mamakin ganinta a nutse da Hajabi da Casbaha a hannunta tana ja, sai hawaye sa suka ki tsayawa sai sharewa take. Sanyi yaji a ransa lallai kasancewar Babba a guri ma rahma ne don zai aiwatar da abinda tunaninka da hikimarka ba za suyi ba, Hakika ya tabbatar duk iya lallashinsa da dabarunsa, zai yi wuya ya iya shawo kanta har tayi tawakkali haka, mutum daya ce zata ladaftar masa da ita farat daya, itace mahaifiyarta idan ta iso. Ya zauna wajen hajiya suka sake gaisawa, yace zamu shigo da shi a ina zaki yi masa wanka ga mamansu safeena nan isowa da en gidansu. Tace, ka kawo shi nan dakin mahaifiyarsa. Ba'a dade ba iyayen Safeena suka iso da yake tsakanin Unguwanninsu babu nisa, Mamansu safeena da hajiya ne suka yi masa wanka suka gyara shi, aka sallace shi akaje aka binne. Sai da akayi kwana 7 da rasuwar sannan Hajiya da Aneesa suka koma zaria cike da kewar rashin sultan, yaro ne hakurarre mai shiga rai ba shi da hayaniya irin dan uwansa. ****************************** **************80) A halin yanzun karatun Aneesa ya zo karshe, saboda har sun fara zana jarabawar su ta WAEC, hakan ne ya sa maganar auren Aneesan ta taso gadan2, shi kanshi sagir duk ya kagara ayi wannan auren ko don saboda en tsegumi irin su

Chapter 5 of 7