Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
Hanne da suke ta kai kawo da sukar wannan auren. Kamar yadda mahaifin Aneesa suka sa tym da zarar ta kammala jarabawa, shi yasa sagir yaje ya sami mahaifinsu don a sake komawa a tsayar da takamaimai rana tun da yanzu an riga an sa ranar da zata kammala duka jarabawarta. Sagir ya sami mahaifinsa da maganar, shi kuma sai ya kira iyayensu sagir din don ayi shawara, ashe Hanne na gidan dama tsegumi ya kawota, ita ma matsayinta na babbar yayarsu, sai duka aka kira har da ita, alhajinsu ya gaya musu dalilin kiran nasu suka nuna zahirin murnarsu, aka fara shawarwarin wace rana za'a fitar cikin watan biki, ana wannan shawara Hanne bata ce uffan ba, tayi shiru ne tana sakesaken ta hanyar da zata bullo da shirinta yadda zaiyi tasiri a zuciyar mahaifinsu ta gyara zama ta soma cewa, Alhaji ni dai ina da magana dangane da wnnan auren da ake son likawa kanina, yace ina jinki tace gaskiyya Alhaji wannan yarinyar tuntuni na gaya muku bata dace da sagir ba, ni dai a matsayina na er uwarsa na bashi shawara yaki dauka ni kuma ba zanso abinda zai cutar da shi ba. Mahaifiyarsu Hanne tayi caraf tace, kece dai kike ganin aibun yarinyar nan tunda ba kya kaunarta, amma mu ai banda abakinki babu wanda mukaji ya taba aibunta ta, in kuma da tana da wani mugun hali da anyo tattaki an gaya mana, wlh ki kiyayi kanki 'ya'ya mata ne kina da suMIJIN ARO 1**12 81) Hanne tace ni wlh gaskiyya ce nake fai in banda shi dan uwa nane, babu ruwa na da wanda zata aura ko cikin gidanmu waye bai san halin Aneesa ba, kwanakin baya fa zubarwar da yarinyar nan muna gani, a gidan nan. Babu irin sakarcin da yarinyar nan batayi, kwanaki fa sadiq yazo yake cemin har gidan nan take biyo sagir ko da yaushe, shine ma yace sai da ya fattataketa yace kada ya kara ganinta a dakinsu, tunda sagir din aurenta zaiyi ba shashanci ba ne a tsakaninsu, banda dakinsu sagir ma babu inda bata zuwa kuma ana zuwa ana gaya min. Haka kuruk kuma sai in kyale dan uwana ya auri shashar mace, ga shi tunda yana sonta bai zai taba ganin aibinta ba, gaskiyya alhaji wannan abin dubawane. Alhaji yayi alamar tunanin can sai yace, wannan maganar ba wai nayi na'am da ita bane. Amma zanyi bincike akai, kuma bai kamata koda za fasa auren ayi da irin wannan zance marar dadi ya fito daga garemu, ba musamman ma ke Hanne akwai zumunci tsakanin ku da su. Kada in kuma jin irin wannan zance daga gareki. Kema kina da 'ya'ya mata kuma ba zaki so ko da sunyi badaidai ba a zo ana yayatawa, balle idan basuyi ba, kinga ranki ba zaiyi dadi ba, kuma ki sani wlh duk abinda kayi wa dan wani za'ayiwa naki, walau khairan ko sharran, Ina gargadinki da kiyiwa bakinki linzami. Idan dan wani yayi abu mara kyau to kayi masa addu'a shiriya don baka san me gaba zata haifar ba, kai dinnan baka isa ka shiryar da naka ba sai in Allah ne ya shirye su, saboda haka duk mu taru mu nemawa 'ya'yanmu da na sauran musulmi shiriyar Allah. Allah ya shiryar damu dukkanmu, ameen. 82) Shiru Hanne tai maganar mahaifinsu ta ratsata, tabbas! Zancensa dutse, to amma ita fa auren Aneesa da sagir din ne bata so, ita kuma ta rasa hanayr da zata tarwatsa auren shi yasa ta bullo ta wannan sigar, idan tayi nasara hana auren sai ta nemin Allah gafara. ( Ji wani shirme Allah ai baya gafarta laifin dabkayi wa bawansa sai in bawansa ne ya yafe, to shima sai ya yafe maka). Duk wata hanya da Hanne zata bi sai da ta bi, tayi kutun2 ta hana auren sagir da aneesa! Balle tana ganin inda sagir ke aiki yana samu sosai har ya mallaki mitar kansa, shiyasa ta sha alwashin Aneesa ba zata aure shi ta huta ba, ita gata nan da na en matan turus! A cikin daki babu mijin aure, in bayan sagir kaninta ne da tuni ta hada aurensa da Haulat to babu hali, saboda sun haramta ga junansu. Ta so ta hada shi da yar kanwar hajiyarsu, mahaifinsu yace sam! Kada ma ta soma, ba zai yiwu ba tunda ta kushe wancan auren ba ta isa ta jona shi da wata ba, duk wadda ya akawo yanzun ita zai aura, babu kuma wanda ya isa ya hana shi auren duk yarinyar da ya kawo ko wacce iri ce. Abban aneesa yaji ciwo sosai da Alhajin su Sagir yayo tattaki da kansa ya bashi hkr, dangane da fasawar auren yaran nasu, magana ta fahimtar juna yayi tsakanin su inda ya haisda masa ce wa dan uwansa ne ya ba sahgir 'yar sa, ahaka dai zancen auren ya sha ruwa wanda shi Sagir har kuka yayi wa Aneesa akan shi dai ita yake so, ba zai yarda ya auri wata ba, bai nuna mata hanne ce sanadi ba. Bai san ta fara jin komai a bakin 'ya'yan hanne ba, ita kam ta rasa irin wannan kiyayya da hanne ke mata ita da mahaifyarta, da uwarta take nunawa daga baya sai abin ya koma kanta, duk wani sharri da mugun alkaba- sai ta dora mata shi, ita ko tunani batayi abinfa da kayi wa dan wani na sharri watarana za'ayi wayi gari ya iya komawa kan danka idan ba abin alheri kayi sai kaga ya sameka kaima da zuri'arka. Shi yasa kullum muyi nufin kulla hairan kada mu nufi kowa da sharri gara ayi ma sharri da kayi ma wani. 83) Wannan lamari ya tashi hankalin Aneesa da duk wani masoyinta musamman Hajiya. Ita kanta Aneesan har ta rame don a daddafe ta iya gama zana jarabawarta saboda zuciyarta na cikin halin bakin ciki da damuwa, ga babban zullumi da take fada da shi wani furuci da mahaifinta ya kira yayi mata na cewa ta fitar da wani mijin kafin su zana jarabawarsu na Neco don da zaran ta kammala ba zai jira komai ba zai daura aurenta ga duk wanda Allah ya nufa, saboda ta bangarensa akwai mutanen da suke zuwa neman aurenta dana ya dakatar da sune saboda akwai wanda take so, ciki ma harda abokansa, kuma idan tym yayi koda abokinsa ne zao daura mata aure. Damuwa tayi wa Aneesa yawa lokacin tana kwance a doguwar kujera a falon hajiya, hajiya ta fito daga daki ta zo ta zauna a gefen Aneesa itama tayi shiru, tausayin Aneesa take sosai saboda irin abubiwan da ke kunnowa rayuarta kai! Ta dubeta tace, Aneesa bana son inga kinzo kin takura kanki da tunani. Duk abinda kika ga ya sami bawa daga Allah ne, dama da kaddararsa ce hakan kuma bawa ba wuce kaddararsa, yanzu kina ganin kafin ku gama jaravawa akwai wadda zaki fitarwa da mahaifinki amatsayin miji? Aneesa ta numfasa tace, babu wani a yanzu don na riga na kori kowa, amma ina rokon Allah kafin wa'adin nan ya cika ya kawo min nagari zan gabatar masa idan ban samu ba. Na amince duk wanda yabani zanyi biyayya inshaAllahu, albarkacin biyayyan sai inga alheri. Hajiya tace ki kwantar da hankalinki, insha Allahu sai kin auri miji na gari fiye da sagir. Zasu ga sakayyar Alkhairin da Allah zai yi miki, sai sun sha mamaki indai ina raye ba za su ga naka sunki ba, da izinin Allah. Bayan tafiyar Aneesa wani tunani ne. Ya darsu a zuciyar Hajiya wanda itace zata iya sanadin faruwar haka, wanda daddaden buri ne aranta saboda irin kaunar da ke tsakaninta da Fatima wannan shine abu na karshe da zatayi don ganin zuri'ar Fatima bata tozarta a doron kasa ba. 84) Wayarta ta sauka ta kira Ishaq, Yana ganin sunan HAJIYATA a screen din wayarsa sai yayi murmushi saboda abin da ya jibanci Hajiya ko ita kanta jinsa yake har cikin ransa, sabida sanin duk duniya baya da kwatankwacin Hajiyarsa, don har tsiya yayin sa ke masa idan yace Hajiyata, sai su harare shi suce, dadin Abin dai ba kai kadai bane balle kace Hajiyarka. Ya kanyi murmushi ne yace, ni dai nasan tawa ce, in kuma karya nayi sai atambaye ta gata nan, dariya kawai suke yi don sun san da an tambayeta cewa take yi shi kadai ne nata su ba nata bane. Yayi sallama tana amsawa yace, Hajiyata ina kwana? Ya jama'ar zariya, ya su Aneesa. Tayi murmushi, tace duk lfy kowa yake. A ranta dadi take ji idan ya tambayi Aneesa saboda irin kaunar da yake wa yarinyar da wuya ne suyi waya bai tambayeta ba, idan ma tana gidan sai yayi magana da ita. Ita kam, addu'a takeyi Allah ya dorar da wannan kauna har karshe rayuwarsu, Allah sa nufin da ke zuciyarta ya kai ga nasara. Tace, wannan hutun karshe makon zaka sami zuwa zaria kuwa? Yace indai kina son gani nane ai sai in aje komai in zo, ko gobe ne ko yau ne zan aje in amsa kiranki. Tayi murmushi ita kam, bata da haufi akan Ishaq. Saboda ladabinsa a gareta, tace ba zan shiga rayuwarka aikinka ba, ka bari kanar jum'a ko asabar kana iya zuwa ne maganar bana gaggawa bane. Dan halas din kuwa ranar asabar ya iso zaria kafin sallar azhar . Aneesa na gidan Hajiya, ita hajiyan ta sa tai masa lafiyayyen dambun cous2 wanda yaji hanta da koda da kayan lambu, kamshin duk karade gidan. Shi kanshi daga isowarsa kicin din ya shiga ya iske Aneesa da ladidi a kicin din. Ya dubi Aneesa, yace wannan irin kamshi haka, me kuke hadawa ne mai lagawadar kamshi haka, tun daga bakin titi nake jiyo kamshi? 85) ladidi tayi dariya ta nuna Aneesa tace ka ganta nan tunda aka ce zaka zo tace ita zata yi maka girki, ni ban ma san sunan abinda ta girka ba, gashi nan ya cika gida da kamshi. Ya dubi Aneesa yana murmushi yace, ai ni yanzu na yarda dai kanwata kin zama gwanar girki, bansan yadda za'a yi ba, kuma ga aurenki ya matso, idan kika tafi gidan miji, kilan can zan dinga yin waya ana sam mini na angon. Rufe fuska tayi saboda kunya. Shi kam dariya ya dinga mata yace, bari in sassauta belt da neck tie dina yanzu zan fara dibar girkin nan dama da yunwa na shigo zaria, sukayi dariya. Aneesa sai da ya fita a kicin din ta ba shi da kallo yau shigar suit yayi nasu ruwan kasa, sunyi masa kyau tamkar wani bature ga hadadden kamshi da ya baza musu a kicin din ya fice abinsa, kai Allah yayi haddaden gaye anan wurin inji aneesa a zuciyarta. Sai da Ishaq yaci yayi hani'an yaje sallah daga can ya kuma gana da jama'arsa ya shigo gida, ya nutsu sannan Hajiya ta nemi ganawa dashi a dakin baccinta suka nutsu saboda zancen da zasuyi yana neman sirri da nutsuwa. Ta dube shi ya nutsu agefen gadonta akasa bisa wani tum tum mai taushi tace, ba wani abu yasa nace ka zo ba illa ina neman alfarma da nake son kayi mini, kuma ina ganin babu wanda zai yi mini wannan alfarma inji sanyi a raina inji bana kokwanto sai kai, ina fatan zaka share min hawayena. Baki ya bude yana mamaki, Hajiyata yanzun don kina neman alfarmar wani abu a gurina har sai kinyi kokwanto, ai ni kin fice neman alfarma a gurina sai dai ki bani umarni take in bi umarnin indai ba ya sabi Allah bane, kada kiyi kokwanto a kaina, fadi ko menene kike so in dai bai fi karfin arzikina ba zaanyi miki. Ta gyara zama tace, ba wata alfarma nake nema cikin arzikinka ba, saboda ni babu abinda baka yi mini ba, kai dan halas ne na gasken gaske, Allah yayi maka albarka ya albarkaci zuri'arka ya biyaka da aljanna. Ta danyi shiru tana jinjina lamarin, shi kuma yayi shiru cike da ladabi, umarninta kawai yake jira ya cika idan kuma bukata ce yayi gaggawa biya mata ita, don kuwa ji yake ko da fansar ransa ne ta umarta zai iya badawa. 86) Can tace, kasan nayi maka waya dangane da maganar auren Aneesa ka riga kasan komai. Yace kwarai kuma zancenta aurenta na raina don kuwa har na fara shirye2 na jira kawai nake inji ansa takamaimain tym sai in sanar da ke tsarin da nayi, don bana son kowa ya wahalar da kansa daga ke har abbanta da sauran en uwa, nine zan dauki ragamar yin komai, a yadda nake kaunar Mama da zuri'arta wlh babu abinda bazanyi musu ba. Hajiya ta numfasa saboda zancen da zata dauko ba wannan bane, ya sha bambam da duk wani shiri da yake yi a auren na Aneesa, tace ai maganar shirye2 ma ka aje ta agafe saboda a halin yanzun an fasa auran Aneesan, Ya juyo anfasa? Me ya faru? Tace mu dai takamaimai bamu san me ya faru ba daga can ba, amma mahaifin yaron ya zo ya bada hkr yayi kalamai na fahimta, cewa dan uwansa ne ya ba shi diyarsa shi kuma babu yadda zaiyi, shiyasa ya umarci sagir din ya amsa. Idanun Ishaq suka yi ja, ransa ya baci yace, amma wannan wulakanci ne, yarinyar nan bata kula kowa sai dansa nima har ina gargadinta tunda shi take so, kada ta kuskura ta kula wasu tarkacen samari, ashe zai yaudareta ne, ni ban yarda an bashi wata ba dama can mayaudari ne, Hajiya tace kada ka ji zafin yaron nan, shi sam bashi da laifi, tunda har nan ya zo yayi mini gamsashen bayani, kuma na yarda da bayaninsa, kawai mu dauka ba matarsa bace, shi yasa hakan ta kasance, ni dai yanzun burina, Allah ya bata miji na gari wanda ma ya fishi. Yace Insha Allahu Aneesa zata sami miji mafiyinsa, akwai wani abokina dan zariyan nan da muka taba zuwa gidan nan da shi ya ganta, yayi ta damuna da zancenta sai na gaya masa ta tsaida miji, tunda hakan ta kasance zance masa ya zo su daidaita. 87) Hajiya tace, kabar maganar wani abokinka, dama ni tun asali bana son Aneesa tayi aure inda dangin miji zasu dinga tsagwamarta, to gaskiyya dama en uwansa ba wani son auren suke ba, musamman Hanne da kannen ta, iyayensu ne ke so, shi ya sa da haka ta kasance ai banji ciwo sosai ba, shine yanzun nake son kayi mini alfarma a matsayina na mahaifiyaka wadda nasan na isa da kai, ka auri Aneesa don kai ne nake ganin zaka rike mani ita da zuciya daya. Ishaq ya dubi Hajiya duba na ya zanyi da wannan lamarin, yace ni in auri Aneesa Hajiy? Kina ganin ba zata shiga cikin matsala ba tsakaninta da Safeena, saboda safeena wayayya ce ta fita wayewa da wayau, sanna abin dubawa kuma safeena sam bata kaunar kishiya, ni kaina ina tunanin irin matsalar da zan fuskanta da ita duk ranar da nace zan kara aure, tunanai na ko da zan kara aure zan auro dai2 da ita ne wayayya ba wadda zata sha wahalarta ba, amma aneesa ba zata iya kishi da safeena ba. Hajiya ta girgiza kai tace, amma ka bani kunya tunda har kake tunanin ba zaka iya sarrafa matarka ba da gidanka, ina ce safeena karkashin ka take? Kaine zaka juyata ba ita bace zata juya ka ba, to ni mahaifiyarka nayi maka Umarnin auren Aneesa, wanda ina fatan alheri na kulla, don kuwa ina hangi wannan alherin tare da zamanku, idan kuma ba zaka iya ba saboda kada ran matarka ya baci tunda bata son kishiya sai in nema mata wani nagartaccen mijin cikin en uwana, wanda nasan ba za su watsa mini kasa a ido ba, za su share min hawayena. Ishaq yayi shiru yana jinjina irin wannan kauna da Hajiya ke wa Aneesa wanda har bata kaunar yarinayar ta shallake zuri'arta. Hakika yarinyar natsatsiya ce mai hkr da hankali ga shi son addinin ya ratsata kwarai mutum zai so ta zamo uwar 'ya'yansa don samun tarbiyya ta gari a gidansa. Shi kam! Yana kaunar yarinyar irin kaunar da zaiyiwa duk wanda jininsa ya gauraya da nasa, jin yarinyar yake tamkar Hajiyarsa ta haifeta, a matsayin autar Hajiya yake ganinta, sai dai bai taba jin ko so ko tunanin wai shi Ishaq zai auri Aneesa ba, illa dai wannan kaunar. 88) Ya dago idanunsa cike da danuwa ya dubi Hajiyarsa yace, Allah ya huci zuciyarki Hajiya, ni idan ban share miki hawayenki ba, waye zai share miki? Wlh ko da ba Aneesa da nake jinta araina ba, zan iya aurar duk yarinyar da kika yi mini umarnin in aura balle Aneesa da ta rayu tare da mu, tarbiyarmu ke gareta, komanta irin namu ne haihuwarta ne kawai bakiyi ba, amma kinfi kowa sannin cikinta da bayanta. Ki kwantar da hankalinki, na anshi auren er lelenki, ina fatan zaki taya mu da addu'a Allah ya tabbatar da alheri a tsakaninmu, ya bamu hkr zama da juna tunda kinsan babu wata soyayya a tsakaninmu. Murmushi Hajiya tayi irin murmushi nan mai bayyanar da farin ciki, ta dubi Ishaq tace, ni kam ka gama min komai a duniyar nan tunda ka amince zaka dasa daga inda na tsaya, wajen tallafawa rayuwar Aneesa, kwarai bana son rayuwarta tayi nisa da cikin zuri'ata. A kullum addu'a ta kenan, ashe Allah ya ga zuciyata da alherin da ke cikinta shi ya sa ya canza lamarin auren nan har gashi ya dawo cikin zuri'ata. Zanyi muku addu ba zan gushe ba har karshen rayuwata, tunda kun ginu akan kaunar juna to na tabbata kauanarku zata rikide ta zamo soyayya da izinin Allah, aneesa yarinya ce mai shekarun da ba su haura sha takwas ba, kai kuwa ka haura shekaru talatin, kai namiji ne mai ilimi mai wayau fiye da nata, kaine zaka koya mata yadda zata soka ba sai na gaya maka ba, kasan kuma a irin sigar ladabi da biyayyar da zata shiga gidanka da shi da kyakkyawar tarbiyar da take da shi, da su zata samo soyayyarka a gareka. Allah yayi muku albarka ya albarkaci wannan auren da za'ayi yasa alheri muka kulla. Dukkansu shiru sukayi na kusan mintuna 2, kowa da inda zuciyarsa ta nufa, ya dubi Hajiya yace, kin sanar da Aneesa wannan maganar? Tace ban sanar da ko ba daga ni sai kai sai Allah dake tare da mu kawai ne muka sani, yanzun nake son in kirata a gabanka in gaya mata. 89) Yayi saurin duban Hajiya yace, ki barta sai na tafi kinsan akwai nauyin juna a tsakaninmu. Tace ai na so ne tun yanzun ku fara fahimtar juna, amma tunda ka ce haka shikenan. Sai ka saya mata waya ku dinga yin magana. Yace zanyi ma Ali waya sai kawo mata su kyau ta zabi wadda take so. Tace, yauwa kafin ka wuce kaje ka sami babanka Alh. Sani da dan uwansa kayi musu bayani, sai su kai gaisuwa gidansu Aneesa. Ka turo da isassun kudin gaishuwar in ma sun bukaci sadaki, sai a bada tunda bai fi wata 2 ne zata kare karatun ba, da ta gama ne yace zai aurar da ita, kaga shikenan ayi a ahuta. Ishaq yace yanzun dai suje su yi maganar neman auren, komai zai iya biyo baya daga baya, ke naga duk kin matsu ayi abin da gaggawa ne. Tace eh dole in damu ayi saboda ubanta hutsumin mutum ne, yadda idan bata kawo masa miji ba, zai daura mata aure da wanda rabonsa ya rantse ai kaga ba zanyi yayi mata auren wulakanci ba, yarinyar da gatanta da komai a dauketa a aurar ga ko wane irin miji, in dai ina raye ba zan bari duk da ba iko na bace. A falo ya iske Aneesa zaune tana cin abinci, ladidi na kicin tana goge2. Aneesa na ganinsa tace Ya Ishaq ba dai har zaka tafi ba? Yace zanje uguwan juma ne yanzu zan dawo in wuce. Tace yaya ni yau banji kace girkin da nayi maka yayi dadi ba, kada ka sa Hajiya da Ladidi su yi mini dariya. Yace yanzun nan dama zance girkin ki yayi dadi, ya ma fi na kullum ga tukwicinki nan, Ina ladidi ta amshi na na taya ki da tayi. Ya kwalawa ladidi kira ta fito daga kicin din tana amsawa, ya mika mata en dubu guda 2 tayi ta godiya ta koma bakin aikinta. Aneesa kuma dubu biyar ya bata, ta amsa tayi godiya ya fice. Asalain Family house na su yaje a unguwan Juma, gidan mahaifin Alhajinsa wanda a yanzu kannen mahaifinsa ke zama da iyalensu. 90) A zauren gidan ya same su su duka biyun bisa manyan tabarme dake shimfide a zauren. Yayi sallama ya shiga Zauren Alh. Sani ya dube shi yana murmushi yace, a'a kaga direban jirgi ne da ranan nan, sannu da zuwa. Suka gaiggaisa suma dattijan kawari ne irin Alhajinsa shi ya sa ko da mahaifinsu ya rasu sune suka maye masa gurbinsa. Saboda dattakonsa da rikon zumuncinsu, ba irin zumuncin yanzu ba da ba'a abu domin Allah sai don ganin idon iyayenka idan suna raye, idan basa raye sai ayi wa dan danwa rikon sakainar kashi. Ishaq ya zayyane musu abinda ya kawo shi, suka taya shi murna. Ya kawo kudi dubu ashirin yace su kai na gaisuwar duk yadda akayi zai kira yaji, ya kawo dubu biyar2 ya ba su. Alh. Sani yace Madallah an gode Allah ya kara budi, munga kayan abinci direban ya kawo Allah shi albarka. A mota Ishaw tunani kawai yake yi, shi kam! Aransa bai jin son Aneesa ko kyas! Illa kaunarta da tausayi da suka gauraye da jininsa, shi dai umarnin duk abinda ya shafi Hajiya tace masa yake bi don ya faranta mata rai, tunda ya lura in har ya kuskurewa wani umarnin nata akan auren nan to zai daina ganin farin cikinta, shi kuma da ya daina ganin farin cikinta gara shi ya sallamar da nasa farin cikin tunda yasan yanzun rigima ce zata bullo a gidansa muddin ya gayawa Safeena zancen nan, don bai san ya zata dauki lamarin ba, tabbas! Ya san zayi ban kwana da zaman lfy a tsakanin, kaga kenan zaiyi bankwana da farin ciki, yana komawa ya gayawa Hajiya yadda sukayi, sannan yayi sallama da su ya wuce Abuja. Aneesa har zata tafi gida sai Hajiya ta kirata dakinta tace ta zauna zatayi magana da ita ne. Sun danyi shiru na en sakonni sanna Hajiya tace, Aneesa yanzu kina ganin akwai wani da zaki fitar nan da wata biyun da abbanki ya gindaya miki? Ta girgiza kai tace, Hajiya wa nake kulawa? Duk fah na gama korar samarin babu mai zuwa ko wa shakkata yakeyi, yanzu bani da zabi idan Allah kawo min wani to, idan bai kawo min ba haka zan hkr da duk wanda Abban ya zaba mini. 91) Hajiya tace kada ki damu ni nayi miki zabi, amma bansani ba, ko kice ba kya ra'ayin wanda na zabar miki. Tace Haba hajiya wlh ko kuturu ne kika zaba mini zan aura a yadda matsayinki yake a gurina, balle nasan duk wanda zaki zaba mini nagartacen ne wuya za'a same shi da wata mummunar illar duk yadda kika yi dani dayane. Hajiya ta numfasa tace, nayi miki miji kuma ba wani bane sai yayanki. Ta ware idanu tana al'ajabin sai tana jin tamkar kunnenta baiji sosai ba, ta tambayi Hajiya, Hajiya wane yayan nawa? Tace yayanki na nan gidan ina fatan ba zaki watsa min kasa a idanuna ba. Aneesa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace, Hajiya ban zan taba watsa miki kasa ba, amma ai yaya Ishaq ba tsaran aure na bane, ya fi karfin matsayi na, yayi min fintinkau, sannan matarsa tafi karfina, wayayyace ba irina ba ce, kuma da kunnena naji tana fadin yadda ta tsani kishiya, wai ko wani akace za'ayiwa haushi take ji, to balle ita, wlh ina tsoron wannan furucin nata. Hajiya tayi dan murmushi tace, kuruciya manya to Aneesa ai babu matar da zakiji ta furta tana son kishiya da bakinta, kuma ba wai kishiyar ita kanta ake tsoro ba, a'a makircin da zata shigo da shi gidan ake tsoro, wata bayannanen makirci wata boyayye na karkashin kasa, za'a yiwa wadda aka tarar har sai an fiddo ta gidan ta bar yaranta, wata kuma da alheri take shigowa, ta gidance zata ce sam bata yarda ki zauna ba zata shiga ta fita da makirci tabi karkashin kasa harda bin malamn tsibbu. Sai kin fita kin bar mata gidan, haka suke cewa wai gida nasu ne miji na su ne. To duk idan akayi hkr ke ta gidan kika tsare gaskiyya kikayi nufin idan ta zo zaki zauna lfy da ita, ki riketa da zuciyarki tsakani da Allah. To ko ta zo da mugun hali gidan da izinin Allah sai kyakkyawan kudurinki ya ruguza nata, idan kuma itace ta zo da nufin alheri ke ta gidan sharri a zuciyarki nan ma zaki ga Allah ya dorata bisa kanki, har ma ace daga zuwanta ta koreki. Alhalin zuciyarki ce babu kyau, amma duk idan zuciyar kowa ya tsarkake babu wani mai mugun kulli tsakaninsa da dan uwansa sai kiga zaman lfy ya wadata gidan. Gaskiya gidan nan akwai matsala tundana dawo na fuskance shi. Ya kamata mu gane mu magance matsalar da kanmu dan ci gaban gidan. Dan wannan maganar ma banso yiba. Dan Allah a kiyaye. MIJIN ARO **part 13 92) Ki kwantar da hankalinki da alheri a zuciyarki zaki shiga gidan. Ni ma da na hada auren ba da wata manufa na hada ba, fatana shine ya kasance alheri na kulla, in ma kinje gidan ki taddata da wani mugun kudiri a ranta, to ke kada ganin haka yasa ki canza alherin da ke xuciyarki, ya rikide mugun nufi, ki bar zuciyarki da alherinta Insha Allahu zaki ci ribar kyakkyawan kudurinki. Yanzu abu daya nake son inji daga gareki, kin amince ko baki amince ba? Kada kiyi shayin gaya minin gaskiyya kuma bana son ra'ayinmu ya sha banban a gaban mahaifinki don yau za'aje gidanku da maganar. Shiru kawai Aneesa tayi tana sauraron jawabin Hajiya. Ita kam! Gaskiya ta fada Ishaq yafi karfinta, don kuwa shi ajin farko ne a komai don hadadde ne na shiga gasa, ga kyau ga kudi ga tsabta da addini da taimakon addinin ga son 'yan uwa da taimaka musu, ita dai har yau ba taba ganin aibu ko wata illar tasa ba, komai yayi birgeta yakeyi sai take jin itama duk ranar da tayi arzikin kudi irinsa halayyarsa zata dinga kaman tawa, ita kam! Ba zata ce bata sonsa ba, saboda tun asali sun gidan tare ne kusan ma a inuwa daya suka rayu don tun tana tsumman goyo take karakaina a dakin mahaifiyarsa, shi yasa suka taso daga iyayensu har su kaunar junansu sukeyi, da abu ya sami daya nan da nan zaka ga sun taru sun kokawa juna idan na bakin ciki ne haka idan na farin ciki ne tare da yinsa, sau da yawa idan yayo waya zaizo zariya sai taji farin ciki, ya cika ta duk sai ta kosa ya zo ta ganshi, balle idan yace da 'ya'yansa zai zo, har mafarkin takeyi saboda yaransa kyawawa ne irinsu masu kwarjini kamarsa. Ita dai bata san dalilin da yasa take jinsa a ranta ba ashe akwai wani alheri da Allah zai kulla ne a tsakaninsu nan gaba, wai ita aneesa zata zamo matar captain Ishaq! 93) Shararren matukin jirgin saman da gwamnatin tarayya ke ji da shi saboda fasaharsa da baiwar da Allah yayi masa ta

Chapter 6 of 7