Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
ba dai naji dadi ne, tace me ke miki ciwo? Ni babu abinda ke min ciwo, haka nan dai naji jikina da garin ba sayi min dadi, Hajiya ta gyara zamanta tace, ruwa baya tsami banza amma ni nasan ba ya wuce matsalar gidanku wadda a kullum nuna miki nake yi hkr da addua zai iya yiwa mutum maganin duk wata matsala da ta sha karfinsa, bana so ki dinga sa damuwa da tunani a ranki sai ki ga kinga kankanuwarki ace jininki ya hau. Ko ita maman ku ba ki ga hkr take yi ba, duk da dai dama ita mai hkr ce, shi hkrn ai baya baci, kuma yana da ranarsa, ku cigaba da hkr wata rana sai labari Aneesa ta sauke ajiyar zuciya tace, shin wai hajiya idan akayi aure saurayi da budurwa, suna son juna dama kiyayya na biyo baya ne idan suka hayyafa? Hajiya tace, sam kiyayya bata biyi bayan zaman masoya, in dai sun gina soyayyatsu ne da tubali mai nagta, kuma suna son juna tsakani da Allah. Amma ko da tsakani da Allah ne suke son junan indai an samu wasu na shiga tsakani, in dai daya cikin masoyan ya bada kofar da za akawo cikas din abokin zamansa to tabbas zaki ga mummunar baraka, ta gifta tskaninsu ko da dayan shi bai bada kofa ta wajensa ba, sanna abu na 2 shine babbancin ra'ayi, in dai har za su dinga samun babbancin raayi na son zuciya bawai dalilin daya ya sabi Allah bane, to nan ma zasu dinga samun sabani wadda ba abinda zai biyo bayan sabanin sai kiyayya. Aneesa ta sake, Jefo mata wata tambayar, to Hajiya idan aka yiwa mutum kishiya dama dole sai daya ya cuci daya, shima mijin dole ya dinga babbanci yana wulakanta daya, ita wadda yake so sam ba zaiga nata laifin ba ko da tayi? Hajiya tace duk inda kika ga abokin zama 2 ko fiye sun hadu a inuwar mutum daya idan kika ga sun hada kai to daga namiji ne, idan ya kasance adali, in kuma kika ga ba hadin kai to ko dai baya adalci tsakaninsu ko kuma akwai matsala cikin matan. 51) Amma yawancin rashin zaman lfy kishiyoyi abu 2 ne rashin adakci daga wurin mijin ko kuma akwai masu shuga tsakani. Wadan da ba su da burin su ga ana zaman lfy. Akwai wasu kuma basu ma taka kara sun karya ba, zaki ga sun kawo matsalolon, kamar kowa ta dinga ganin auro ki akayi nima auro ni akayi. Babu ragayya tsakanin juna ko su singa wa juna gani2 da sauran su dai. Shi yasa duk rintsi ya kasance kai ka zauna da dan uwanka tsakani da Allah zuciya daya. To sai ki ga komai ya zo maka da sauki. Aneesa ta jinjina kai tace wadannan matsalokin kusan sune a gidanmu. Shi ya sa ni insha Allah ba zan auri saurayin da muke son juna ba, gara a aura mini wanda iyaye suka kawo sukace shi suke so, sannan bana son kishiya don ni dai gidan mu naga isharar zama da kishiyoyi matsala ce babba, wanda in bakayi sa'a ba ciwon xuciya sai ya kamaka ya kasheka abanza. Ni dai wlh ina tson kishiya, kada Allah ya hada ni da ita. Hajiya tayi dariya tace ki kwantar da hankalinki kishiya ba komai bace face alheri, duk sharrinta indai zuciyarki da tsarki sai kin gagareta, ke dai kiyi fatan ko da Allah zai hada ki da ita, to ya hada ki da tagari. Aneesa taxe ni dai nasan Maman kullum burinta alheri ne tunda Basira ta zo gidan nan bata taba fadar aibunta ba, ko mu muma bata barin mu fada. Ko da zatayi mana badaidai ba, mama ta dinga yi mana wa'azi da nasiha kenan akan hkr. Ta ya akayi basira ke cin Galaba akanta gurin Abbanmu, duk makircin da ta gaya masa yake dauka har ya dinga yiwa Maman cin mutunci ko da yaushe tace, idan kinga haka ta faru to jarabawa ce Allah keyi bawansa ya gani zai iya yin hkr, idan yayi hkrn sai ya ga sakyayyar alheri a tym din bai zata ba, idan kuma bawa ya kasa hkr to sai ya ciga ba da ganin ba badaidai ba arayuwarsa, ita mamanku hkrn da takeyi insha Allahi zai yi mata rana, ko mu dade ko mujima. 52) Aneesa sun gama xams din 2nd term kenan, Ishaq yayi waya safeena ta haihu twins again. A ranaar aneesa tayi tsallen murna ita da hajiya aka rasa gane wa ya fi wani farin ciki. Ta dubi Hajiya tace, amma dai don Allah zakije abujan kiga 'ya biyun ko? Hajiya tace, me zanje nayi? Duk jama'ar da za suje basu isa ba sai na je? Tace Haba hajiya shima fa yaya Ishaq yana son yaga kinje gidansa, shi ba wani dan fari ba amma kin dau kunyar Maman su sadiya kin dora masa shima matarsa ai saita ga kamar ba kya sonsa ne? Tace indai sai naje gidansa ne zata ce ina sonsa tace, to kada tace, tunda ita tana sonsa ai shikkenan. Ana gobe suna jama'ar zaria ta isa abuja ciki har da Hajiya, wadda da kyar da sudin goshi taje, don kuwa saida Ishaq ya zo zaria yayi lallashi sannan taje, a cewarta bata ga dalilin zauwan nata ba, yara dai idan akayi arbain ai za su zo ta gansu. Yaran kuwa kyawaawa tamkar su Sultan ga shi suma sai ka sha wuya zaka iya banbance tsakaninsu. Su ma canza suna akayi. Hassana Yasmin, Hussaina kuma Yusra. Taron sunan ya kayatar, safeena ta kece raini cikin tsaddadun kaya ita da yaranta, ji take tamkar ta fi kowace mace sa'ar miji, koko ita kadai Ishaq ya mallaka a duniya, domin kuwa ya kashe mata kudi ita da gidanta kamar ba gobe, dama burinta kenan, kawayenta na jami'a su zo ga yadda take bushasha agidanta. Duk wanda ya zo taron nan sai da ya tafi da katuwar jaka shake da abin arziki mai dauke da hoton twins da nasu Suhail a kasa. 53) Aneeesa tana ajin kusa da na karshe ne a halin yanzun, ta zama cikakkiyar budurwa farace ita tas, irin farin nan mai haske, tana da tsayi amma bata da jiki, sai dai fasalinta mai kyau ne saboda kirar kalangu da Allah yayi mata ga yalwar gashi, kirjinta cikakke ne ta yadda zai dauki hankalin duk mutumin da zai tsura mata idanu. Shi ya sa ko da agida take ta faya sanya gyale, idan zata fita kuwa babban hjibi take sakawa. Agidan Hajiya kuwa tunda gidan na jama'a ne ko da yaushe bata rabo da Hajibinta. In dai za a aiki Aneesa to ta dinga cin kar da gaisuwar samari kenan. Da suka bata kula su. Sai suka kawo kansu gida, da yake Abbanta yayi nata kashedin kada ya ganta ta tsaya da wani namiki. Shi ya sa ko sun aiko bata fita, idan mutum ya gaji da nacin zuwa sai samawa kansa lfya. Mutum daya ne har yanzun suke tare da shi, shine Sagir shima albarkacin yana kamar dan gidan ne. Ba a jamza birki ba. Kuma natsattsa ne shi, yana gayawa Aneesa da zarar ta gama secondary zai aurar da ita ne. To ita abinda ke bata mamaki yace aurar da ita zaiyi, amma ya hanata tsayaea da kowa, to ko shine zai zabo mata mijin. Ko yana nufin Sagir kawai zai bata tunda da shi kadai ya kyaleta suna tsyawa. In dai kuwa haka ne, to ta yarda da zabinsa kasancewar tana son sagir din, komai nasa mai kyau ne, daga siffa har zuri'a mai kyau sannan mai ilimi ne duka biyun, yanzun haka ya tafi bautar kasa Abia state, a yadda ya sha gayawa Aneesa da ya dawo za afara maganar aurensu, tunda yana da tabbacin aiki a hanni da zarar ya dawo. Zasu iya samun matsayar aurensu ta bangaren Yayarsa Hanne saboda tun asali tana dawa da wannan soyayyar tasu, kullum aikinta kenan sukar aneesa a gurin sagir, shi kuma yana nuna mata ko meye halin Aneesa zai iya zama da ita, tunda yana sonta, can gidan su ma haka take sukar lamarin sai ya kasance gaba daya kannen sagir din sun tsani Aneesa saboda irin tarin batancin da takewa mata, iyayensu mata ne kawai su ke son wannan alaka ta Aneesa da Sagir. 54) Basura amaryar Abbansu ta haihu kusan shekarar yarinyar daya kenan. Ita kuma maman su Aneesa tana dauke da tsohon ciki, wanda girman cikin tamkar na en biyu ne, gashi tunda ta sami cikin take fama da lararu har cikin ya tsufa gashi ta kumbura. Har anyi mata gwaje2 sun tabbatar da tana dauke da ciwon hawan jini, wanda ya soma taba lafiyarta. Wannan lamarin ya tashi hankalin jama'a musamman iyayenta da abokan arziki irin su Hajiya. Ishaq kam da yaji a washe garin ya iso Zaria. Ya sami maman ya tsa ta gaba da tambayoyin shin me ke damunta take tunani haka har hawan jini ya kamata, gashi zuciyarta na neman harbuwa da ciwo. Tayi dan murmushi tana latsa hannunta daya daya kumbura tace, babu abinda da ke damuna. Kawai Allah ne ya aiko min da wannan larurar. Ina nan ina addu'a kuma ku tayani. Ya tsurawa kafafunta idanu sun kumbura sintim sai sheki sukeyi. Ya numfasa yace, kafafun nan babu maganin da zasu sabesu? Haka ya zauna yana ta yiwa Mama magana ta kwantar da zuciya. Duk da ta boye masa damuwarta amma ai ya riga yasan komai, yasan irin zaman da sukeyi a gidan nan ita da yaranta, musamman Aneesa. Hajiya na gaya masa komai, kuma ya sha gayawa Maman duk wani abu idan ya taso na bukatarsu suje direct wurin Hajiya, kada su tambayi kowa, ita kuma Mama yau da gobe take dubwa shi ya sa wani tym din ko matsalar ta taso musu bata yarda Aneesa ta gayawa Hajiya, sai su hkr Allah ya kawo musu agaji. Da ishaq zai tafi ya bata dubu biyar, yace kuma idan wata bukata ta taso a gayawa Hajiya ko Aneesa ta gaya masa ta waya, ita ma Aneesa dubu 2 ya bata yace ta sayi kayan kwaliyya. A zuciyarta tayi dariya tace wai shi kullum ya bani kudi sai yace in sayi kayan kwaliyya, ko kuma so yake yaga tana kwaliyyar. Cikin Mama ya shiga watan haihuwa shiyasa, Aneesa ko makaranta ba kullum take zuwa ba, duk ranar da maman ta wayi gari ba karsashi. To bata zuwa, sai tayi zamanta tana lura da mamanta. 55) Ranar litinin Maman ta shirya ta tafi awo da yake asibitin kudi ne take xuwa, kuma babbar nurse din asibitin gidanta ba nisa tsakanin su da gidansu Mama, kuma tana da kirki har suna abin arziki da su Mama, yawanci ma idan Mama ta shirya da wuri tana aikowa mama ta zo tabi ta a motarta, su tafi asibitin. Yau ma mama na zuwa ta ganta waje jikin motarta tana jiran ta, suka yiwa juna murmushi. Ita ta soma gaida Mama. Maman jafar ina kwana? Ya jikin naki? Ta amsa da sauki, amman yau da ciwon mara na tashi kadan2, tace Allah ya sauwake bari mu karasa asibitin sai a duba ki, ina ganin ma haihuwa ce tunda EDD dinki har ya wuce, kila yau rike ki zamuyi. Tayi musrmushi tace, Allah yasa haihuwarce nima in huta, saboda yadda nake jin nauyin cikin nan kamar an dora min dutse, in bacin kunyi hoton kunce min daya ne, sai in ce ni nauyin mutum 2 nake ji. Allah dai ya raba ni da shi lfy, nurse din tace ameen maman jafar. A asibiti anyi wa mama awo suka ce insha Allahu zuwa gobe zata haihu. Amma idan ta kai gobe bata haihuwa ba, to da safe tayo shirin haihuwa ta zo asibitin. Su ka gaya mata adadin kudin da zata zo da shi. Da ta dawo gida, can sasan su Hanne ta shiga ta gaya ma Hanne yadda sukayi a asibitin. Amma ta iske Halima anyo mata waya kanwar babansu ba lfy ba lfy sosai acan kauyen sun tafi, kila gobe su dawo. Hanne tace idan Allah ya kaimu goben ba sai ku tafi da Aneesa ba, nu kuma ma biyo baya idan kin haihu. Dama maman ta gaya mata ne, ko zata ce zata rakata, tunda bata san ya haihuwar zata kasance ba, tabbas tasan da Halima na nan tare za su tafi ta rakata. Da abbansu aneesa ya dawo ta shiga dakinsa ta gaya masa, abinda akace a asibitin, sai ya kama fada, ni bani da kudi ahannuna yanzun da zan baki gobe kije asibiti, in banda janyowa mutum jidali, ya za'ayi haihiwa bata zo ba, suce aje asibiti. Ko ko su da kansu ne zasu janyo haihuwar da su sa mutum kashe kudi, to ni bani da su, sai na sama tym na amsa abank. 56) Mama ta sassauta murya tace ba wai kirkiro mini haihuwar za suyi ba, yau daman na gaya maka na tashi da ciwon mara shine, sukace haihuwa ce amma sai zuwa gobe, abinda yasa suka fi son in haihu a asibiti saboda sunce har yanzun kan yaron bai juyo kasa ba, akwai hadari. Ina fatan Allah ya kawo mini komai cikin sauki, ta mike da kyar ta bar masa dakin. Da daddare duk yaranta suna falonta. Suna kallo sun saka film din the message, ta tashi tsam daga cikin yaran ta shige dakinta ta kwanta. Ba barci zatayi ba, haka kurum ta ji tafi son zaman kadaici saboda hayaniyasu ta dameta. Aneesa da taji ta shiru a dakin sai ta biyo ta cikin dakin, ta zauna agefen gadon da Maman take, tace mama har kin kwanta ne? Tace Hayaniyar ce bana so shine, nazo na kwanta idona ma sam ba barci. Aneesa ta lura maman kamar tana cikin tsananin damuwa, saboda zahiririn abinda fuskarta ya bayyanar kenan. Tace mama hala zuwa asibitin goben ne ya dameki kike son saka zuciyarki cikin tunani. Tayi murmushinta da ta saba tace. Babu ko daya, saboda nasan duk abinda Allah ya hkunta shine zai faru akaina. Ni rayuwarku ke da en kannenki kawai nake dubawa nan gaba sai inga tamkar, abbanku watarana zai ce ya ga za daukar dawainyarku. Aneesa tace, idan zaice ya gaza mama ba gaki ba, mu ko da ke kadai zamu iya rayuwa, idan yace shi ya gaza damu, ba ga shi kina er sana'ar zannuwa ba, kuma ba laifi kina dan samu, a ciki Allah zai dunga taimakonki kina rufa mana asiri wata rana sai labari. Ta sake yi murmushin tace hmmm! Karama kenan, tunani na kada wata rana a wayi garo ni in riga Abbanku mutuwa, ina nan ma ya ki yi muku abinda ya wajaba akansa ina ga bana nan. Tace don Allah ki bar fadin haka, muna nan da ke sai kin aurar da mu har yaron dake cikinki. Sai kinga 'ya'yansa, tace Allah yasa inga yaran naku. 57) Kinga kece Babba ki hada kanku, duk da Aysha butsararra ce nasan nan gaba zata yi hankali tasan ina ke mata ciwo, yanzun yarinta ce kawai ke kwasarta. Tace, yanzun mama goben ya zakiyi da kudin zuwa asibitin? Tunda Abbanmu yace baya da shi, tace Allah zai rufa aisiri ina ganin kiyi sammakon zuwa wurin Malama Maimuna ki gaya mata uzurin da ke gabana, sai ta juya min kafin ta hada kudin zunnuwan wannan wata sai ta cire a ciki. Anees atace, yauwa hakan za'ayi da har na soma tunanin gaya wa Hajiya, tunda Ya Ishaq yace idan matsala ta taso agaya mata ko ayi masa waya$ tace gaskiyya ba za a gaya mata ba, dawainiyar da takeyi ita da danta tayi yawa, sai kace sune masu alhakin larurar mu, haba ido ba mudu ba ne, amma yasan kima. Aneesa da mamanta sun kai fiye da karfe daya na dare suna hira da tattauna al'amuran rayuwar yau da gobe. Maman na jefo mata en nasihohi cikin hirar. Da ta fahimci Aneesa barci yayi awon gaba da ita sai ta tashi tayi alwala ta soma sallar nafila, da ta idan ta cigaba da adduointa, har sai da tayi raka'atul fajr da sallar subahi sannan ta bar abin sallar. Tabi duka yaran ta tashe su dan suma suyi. Aneesa tana idarwa ta fita ta hura wutar itace tasa wa maman ruwan wanka kansancewar babu wutar nepa. Bayan tayi wanka ta shirya tsaf! Sannan ta taka a hankali tayi sallama dakin Abbansu Aneesa, ya amsa mata, sai da ta nemi izinin shiga sannan ta shiga, suna zaune shi da Basira ta hada musu tea mai kauri ga bread a gefe suna sha, ita kuwa can da yaranta ya barsu da koko, idan ma tea za su ha sai dai su sha ruwan bunu, saboda ba zai ba su madara ba ba kuma gata nan ta ruwa da ta gari a dakinsa. Kai duniya ina zaki da mu? Lahira akwai aiki a gaban marasa shuka gskiyya. Haka ta fada a zuciyarta. 58) Hannun kujerar da ke gefenta ta zauna, sanna ta gaisheshi, da taga Basira bata da niyyar tanka mata sai ta soma gaisheta, sannan ta tanka mata. Mama ta dubi maigidan tace, ni nayi shiri zan tafi asibitin, don kuwa har yanzu ina jin ciwon marar, da wa zamu tafi? Ya wani dubeta yace, da wa zaku tafi da ya wuce Aneesa tunda naga ita ta hannun damanki, jiya wajen sha dayan dare na leko dakin na jiku kuna, kulle a uwar daki kuna shawarwari ke baki da abokin shawara sai Aneesa, idan tayi aure sai ki koma kiyi da aysha. Tayi murmushi tace, ko aure bai raba mu ba, mutuwa ma zata iya raba mu. Ta mike tsam, dama ta dauka zai ce Basira ta rakata ne, amma tunda ya fad haka ko insha Allahu da Aneesan zata je, don ko menene ya sameta itace zata fi tausaya mata. Tana shiga daki ta tarar da aneesa har dama musu koko, ta zuba na Mana a babban kofi tana juyawa da ludayi don ya huce. Aneesa tace mama ke da wa zakuje asibitin? Tace da ke ya ce zamuje. Tace da ni kuma mama? Ni ce zan rakaki haihuwa? To haka yace na dauka zai ce muje da Basira, shine na tambya shi, amma tunda haka ne ra'aryinsa sai muje da ke din, babu komi Allah yana tare damu. Aneesa cike da damuwa ko tace. Sai mu tafi din amma ko in gayawa Hajiya ne, ko inyi waya tudun wada. Tace ki kyale kowa bana son gaya musu hankalinsu ya tashi, musamman Umma tunda ita ba zuwa zatayi ba, sai dai ta turo wani ya zo, kinga sai abarta cikin tunani, gara dai idan Allah ya saukeni lfy sai agaya musu hakan yafi dadi. Ta mikawa Mama kokon tace, ya soma hucewa gara kisha, ni bari inyi sauri in yi wanka mu tafi. Mama ta amshi kokon tana kurba a hankali sam bata jin dadin bakinta sha dai kawai takeyi don kada ta zauna cikin ba komai. Da za su tafi ta leka dakinsa shima yana kokarin fitowa ne zaije gurin aiki, tace masa zamu tafi Allah ya hada fuskokinmu da alheri, idan nayi maka wani ka yafe ni, kasan haihuwa siradin mutuwa ce ban sani ba ko zan tsallake. 60) Tace eh bata haihu ba, amma muna iyakn kokarinmu mu ga ta haihu da kanta. Amma idan haka bai yiwu ba dole aiki za'ayi mata, ki kira min babanku a wayar maman. Zan gaya masa halin da take ciki ne. Jikin Aneesa nan da nan ya shiga rawa, saboda jin irin halin da Mamanta tashiga. Ta kira lamabra Abban na su sai da ta kusa tsinkewa sannan taji ya dauka, sai ta mikawa Aunty nurse itace tayi masa bayanin komai, kuma tace ya kamata ya zo, ya kasance a gurin ko da za'a bukaci sa hannunsa idan ya kama ayi mata aiki. Yace yana nan zuwa idan ya gama da banki. Ciwo yayi wa Maman tsanani tace a kira mata Aneesa babu yadda za suyi, sai suka lullubeta sannan suka kira Aneesan, tana shigwa taga halin da Maman ke ciki sai ta soma kuka ta rike hannuwan Maman tamau. Mama tayi magana kyar, karama har yanzu Abbanku bai zo ba ko? Tace, na kira shi sun yi magana da Aunty nurse yace yana bank ne, amma zaizo, to yanzun na sake kira wai wayar akashe ta ke. Maman tayi murmushin nan nata wanda yawanci idan abu ya bata haushi a madadin ta nuna jin haushi, sai dai kaga tayi murmushi kawai, tace. Na so ya zo mu gana amma kila Allah ba zai ba shi iko ba, ni na san da wuya zan haifa abinda ke cikin nan nawa, kila Ajali na ne na kumsa, ko da bamu gana da Abbanku ba da sauran jama'ar gida duk ki gaya musu na yafe musu ni su yafeni. Allah ya sa na roki abbanku gafara yace ya gafarta mini, ki rokar min su Umma gafara, sannan ki cigaba da hkr da kannenki. Ku hada kanku.....(Cryi ng) Allah yayi muku albarka ya kare ku a duk inda zaku kasance. Hawaye ya gangaro ta gefen idanun Maman, Aneesa kuka sosai takeyi, ta sa hannu ta goge wa maman hawayenta tace, Insha Allahu kina tare da mu mama, ba zaki mutu ki barmu ba, idan kika mutu waye gatanmu, waye zai kula da mu kamar ke, ba zaki mutu ba mama. Ta sake kankame hannun Maman tana kuka. Maman tace, kuyi hkr Allah shine gatanku, zai share muku hawaye fiye dani, rashi na ba zai nakasa rayuwarku ba, Allah zai kasance tare da ku.... 61) Aunty Nurse ta budo kofar dakin ta dubi Aneesa tace, haba aneesa ya zaki shigo ki kara tayar mata da hankali kina koke2 muna kokarin ganin jininta ya daidaita, amma zaki sa ya kara hawa. Aneesa tace maganar mutuwa take mini shi yasa nake kuka. Aunty Nurse ko mutuwar zatayi, tace sanin gaibu ai sai Allah. Ki kwantar da hankalinki Insha Allah ba zata mutu ba zata haihu lfy. Yanzu ki koma can gida ku taho da wani babba tunda mun sake kiran wayar babanku akashe take, gara wani cikin yar uwanku ya zo kusa, ba ke ya kamata kina tare da ita ba. Gidan kanwar maman shine mafi kusa da asibitin, don mai mashin Naira ashirin zuwa talatin zai kaita, shi yasa tayi shawara zuwa ta kirata tunda neman na gaggawa ne. Tana yin sallama a tsakar gida ta ganta tana yanka alayyahu, sallamar Aneesa kawai ta amsa tace, hala yaya Fatima ta haihu ne? Don wlh cikin satin nan kusan kullum sai nayi mafarki da ita, yau da na tashi nake gayawa Babansu, khalifa yace idan na gama abin da nake inje in ganta ko hankalina ya kwanta, yanzun haka azhar nayi da zan tafi. Aneesa tayi murmushin yake tace, bata haihu ba, amma tana asibiti ne zata haihu, shine akace in in gaya miki mu tafi, kila ma aiki za'ayi mata. Salati ta saka, hakan ne. Ya fito da uwar gidanta tace, Maman Nana me ya faru naji kina salati. Ta gaya mata abinda ya faru, ita ma ta jajanta sannan tace, yi ki shirya ki tafi barin in karasa girkin, miko min wayata gata nan da na tashi na barta, in kira baban halifa inshaida masa. Kuyi ku tafi ko me kenan ki kirani a waya nima da na kammala girkin zan biyo ku asibitin. Suna isa asibitin Aneesa ta nufi dakin da Maman take sai taji kofar a kulle, kuma ba ta jiyo salatin da tafi ta bar maman nayi ba, a zuciyarta sai tayi tunanin ko har sun tafi da ita dakin yin aikine. Ta kwankwasa ofis din Aunty Nurse ta shiga ta zauna ta ganta ta tallabi kuncinta da hannu biy2 da ganinta tana cikin damuwa sosai. 62) Tana ganin Aneesa ta sauke hannuwanta daga tagumi tace, Aneesa kin dawo? Da wa kuka zo? Tace da kanwar mama ne. Abbanmu ya zo kuwa? Tace bai zo ba ina ta trying no amma har yanzu a kashe take. Muje inga ita kanwar Maman. Tace naji dakin da maman take a rufe, an tafi da ita dakin tiyatar ne? Tace eh an tafi da ita, muje takunnan inga ita kanwarta din. Kiran maman nana tayi office dinta, ban san me ta gaya mata ba, naga ta fito a rude tana kuka nayi saurin biyo bayanta nace, maman Nana me ya faru? Mama ta rasu ko? Ta ruko hannuna tace, Aneesa sai dai muyi hkr sunyi iya kokarinsu Allah bai ba su sa'a ba, don ba'a kai ga shiga da ita dakin tiyatar ba Allah yayi mata rasuwa, tunda sun jira Abbanku bai iso ba, yanzu kawai tafiya da ita zamuyi a motar aunty nurse. Aneesa jin numfashinta ta tayi yana neman daukewa, nan da nan jiri ya kwasheta ta tafi yuwww! Zata fadi maman Nana tayi yi saurin tallabota ta zaunar da ita bisa benci. Aneesa ta soma kuka tana surutai wadanda za su kaita ga sabon Allah. Maman Nana ta shiga yi mata fada, haba Aneesa kowa ma mutuwar nan ita yake jira ko kinfi Allah sonta ne da ya bamu aronta yau ya amshi abarsa. Ta zubo da hawaye tace, maman nana kin fi kowa sanin halin da muke ciki, mama na raye ma mun shiga halin garari balle ta kasa ta rufe idanunta. Tace mutum baya da wani gata sai Allah, shine gatanku babu mahalukin da zai zulunce ku sai Allah yayi maganinsa, ita dai tata ta kare. A bayan motar Aunty nurse aka saka gawar Mama tare da Maman nana da wata nurse, Aneesa da Aunty nurse suka zauna agaba. Sun baro asibitin da dan nisa ne Aneesa ta hango motar Abbansu ya taho asibitin, sai taji haushinsa ya kamata gani take ma rashin zuwansa akan lokaci shine yayi sanadin mutuwar mamansu, don da ya zo a tym da ake neme shi ya sa hannu, dan anyi mata aiki, amma don kada a dameshi da kira ma sai ya kashe wayarsa, ya kyaleta cikin azabar ciwo har tayi ajalinta.....MIJIN ARO part10 63). Maman Nana tace, Aneesa waccan ba motar kamar ta abbanaku? Ta dan dubi motar da jajayen idanunta tace, ba ita ba ce. Maman nana ta gano haushin Abban nasu takeji shiya sa tace haka, sai tace ki kira wayarsa idan shine kice mun dawo gida ya dawo can ya same mu, kada ki gaya masa abinda, tayi murmushi irin na mamansu, murmushin bakin ciki tace, idan yaji abinda ya faru zai damu ne? Wannan mutuwar fa mu ta shafa. Maman nana tace ya isa irin wannan shirmen naki, kina nufin kin fishi sonta ne? Aneesa tayi en danne danenta na karya tace wayar sa ta ki shiga, tana kallonsa ya mike hanyar asibitin. A kofar gida suka iske baban sasa, maman nana ce ta karasa suka gaisa tayi masa bayanin abinda ya faru, iya rudewa ya rude ya kama salati da surinsa ya shiga cikin gidan ya sanar musu, nan da nan mutuwar tayi tambari a unguwar, dama Aneesa tayi waya tudun wada ta gaya wa su Umma, su Aneesa na isowa en uwan maman suka iso a motoci maza da mata. Abbansu Aneesa ma sai gashi ya dawo jikinsa a mace saboda jin mutuwar nagartacciyar matarsa. Aneesa bata taba tunanin abbansu zaiyi kuka don mama ta rasu ba, amma sai ta ganshi yana kukan hawaye wasu na korar wasu. Ba a bata tym ba aka shirya maman aka sallaceta aka kaita gidanta na gaskiyya. Aneesa tana can dakin maman kwance cikin bargo saboda zazzabi ne ya rufeta. Ta nemo layin Hajiya ta gaya mata, kuka taji Hajiyan nayi hadi da salati, daga nan ta kira Ishaq shima ta gaya masa, shima ji tayi ya saka salati yace, what Aneesa! Mama ta rasu? Kada ki gaya min shirme, ko dai babyn da ta haifa ta rasu? Ta sauke ajiya zuciya irin na wanda ya sha kuka, tace wlh mama ce ta rasu har an tafi kaita ba'a dawo ba. Ta wayar taji faduwar tasa wayar, hakan ne ya nuna mata shiga halin rudani. 64) Ta koma ta kwanta hawaye na ci gaba da bin kuncinta, tabbas ba ita kadai tayi rashin Mama ba, Ishaw ma yayi babban rashi saboda yadda yake ji da mama, tamkar hajiyarsa, wajen shawarwarinsa kuma tamkar yayar sa ta jini yake daukar shawararta saboda yace duk shawarar da ta ba shi idan ya bi ko da zuciyarsa ba so, daga baya yana ganin anfanin abin. Ita kanta Hajiyarsa cewa take shi da mama ba'a sanin cikinsu, kuma hakan ne. Don ko matsala ce da shi direct yake xuwa ya gayawa mama ya nemi shawararta haka za su kasa su rufe Hajiya bata sani ba, har sai anyi maganin matsalat, wani tym din ba idan ba dalili ba Hajiyar ba ta ma sani, don ko lokacin aurensa da safeena da aka sami matsala, da shawarwarin mama yayi ta anfani har Allah ya ba shi sa'ar auren safeena sai ga shi ashe da rabon 'ya'ya har an fara da biyu2, ba'a ma san me gaba zata haifar ba, shi yasa lamarin aure ba'a son mutum ya ja tunga da yawa, ko ayi ranka babu dadi. Da Hajiya da Ishaq kusan a tym daya suka iso Zaria, shi jirgi ya biyo zuwa kaduna, daga kd direban abokinsa ya dauko shi daga airpoart zuwa zaria, ita kuma safeena gobe driver zai taho da ita da yaran. Hajiya kuka ta dinga yi da hawayenta saboda rashin Mama da sukayi, haka ta dinga fadan kyawawan halayyanta wanda kowa ya sani, wasu ma sai a tym dine ake tuna su, dama haka ake so ko bayan baka a fadi alherinka, mama kam ta sami yabo daga bakin jama'a na kuda ita da na nesa. Hajiya ta tambayi en uwan mama da suka cika dakin inda Aneesa take, suka ce tana cikin dakin baccin maman akwance. Ta mike ta shigo dakin ta zauna gefen Aneesa itama sai tashi daga kwance suna kallon juna suka soma kuka, dole Hajiya itace mai karfin halin da ta dinga lallashin Aneesa tare da gaya mata maganganu masu sanyaya rai da karfafa zuciya. Da kika rasa Fatima ba wai kin rasa jin dadi da gata gaba daya bane, ni din nan insha Allah zan maye miki gurbinta, zan zame miki uwa da uba, duk wata damuwarki ki gayan min, insha Allah zan share miki hawayenka. 65 IS A BLANK PAGE 66) A falon Mama ta same shi, shi kadai ne a falon yana sanye da wani yadi mai dan karen kyau, kalarsa dark blue, shi ya sa ya fito da zallar kyan Ishaq da yake fari ne har yafi Aneesa haske, ko da yake kalar jikinsa na en hutu ne, luf luf kamar jikin mace haka yake, ga gashi nan en kanana kwance a jikinsa, gaskiyya Ishaq mai kyau ne ga tsafta koda yaushe tas2 zaka ganshi, kamar farar takarda, lallai dole matarsa tayi kishin abinda don ta san mijinta mai kyau ne, kuma irin mazan nan ne a tsaye masu shegen kwarjini a duk inda suka shiga, ita kanta tasan yana da farin jini don a tarihin soyayyarsu tayi gwagwar maya da en matansa da suke rububin sonsa, balle shi dama tun asali rayuwarsa dan

Chapter 4 of 7