Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ganinta, "Nace maka bana gida naje unguwa.." "To ina nan ina jiranki, sai kin dawo.." Kasancewar duk abinda take fada mama tana jinta yasa mama fitowa daga cikin kitchen, "Nadiya keda waye ne?" "Mama wallahi wani nacaccen mutum ne.." "Haba nadiya, kefa yanzu ba karamar yarinya bace akan me zaki rinka yin abu irin na kananan yara, ko Amira ce tayi haka ai zakiyi mata fada bare ke da kanki, ina ga mai sonka wanda yatako yazo har inda kake? Ki tashi maza ki shirya kije" Jin abinda mama tafada yasata sakin kitson da take yiwa fadeela ta tashi tawuce daki, Kallon amir mama tayi tace masa, "Amir maza fita kofar gida kacewa bakon nadiya yayi hakuri tana zuwa, kabashi hakuri kaji, ai ba ayin haka.." Fita Amir yayi yana fita yaga wani handsome jingine jikin motarsa baka sai sheki take, gayen yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda kalar ruwan toka, da hula akansa itama ash colour amma ya zameta ya turata baya can keyarsa, hannunshi daure da agogon azurfa fari, Gaba daya kamshin turarensa na one man yagama cika ilahirin wurin, amir ji yayi gayen ya shiga ransa lokaci guda sannan gashi dan gayu dashi, Sallama amir yayi masa, dagowa amadi yayi ya amsa tareda mikawa amir hannu sukayi musabaha, "Mama ce ta aikoni tace kayi hakuri anty nadiyan zata fito yanzu" Murmushi amadi yayi har lokacin yana rikeda hannun amir, "Karka damu abokina, ai babu wani abu sai dai kawai yayarka bata sona ta tsaneni babu namijin da take jin haushi ahalin yanzu kamar ni" "Ba tsanarka tayiba, kawai dai halin rayuwa ne ya mayar da ita haka" amir yabashi amsa, "Amma dagaske wai ta taba aure?" "Ehh tayi aure harda yaranta twins, sun rabu da mijinne" Jijjiga kai amadi yayi, "nasan dai ba laifinta bane sai dai laifin mijin saboda nadiya tanada kalar mata nagari" "Hakane, gaskiya kam laifin ba a ita bane a mijinta ne kuma cousin dinmu ne ma amma yanzu babu aure a tsakaninsu saboda saki uku yayi mata, kaga kuwa duk macen da irin wannan kaddarar ta hau kanta dole ta nisanta kanta da maza musamman ma anty nadiya wacce ko kadan bata tsinci wani dadiba acikin rayuwar aure.." Amadi ya dago kenan da niyyar sake yin magana sai gata ta fito fuskarta adaure tasha kunu sai faman cika take yi tana batsewa saboda tilastata din da mama tayi ta fito ba ason ranta ba, Hannun amir amadi ya saki yana murmushi, "abokina sai mun sake haduwa, meye ma sunanka?" "Sunana amir" "To amir sai mun hadu next time, nagode" Wucewa cikin gida amir yayi ita kuma ta karasa fuskarta babu fara'a,juyawa yayi ya dora hannunshi asaman mota ya jingina yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi, Ba karamin kyau yaga ta kara yiba domin tayi kumatu ta yi haske, tana sanye da atamfa kalar ruwan toka da hoton dutsin guga ajiki, ta yafa mayafi ash colour tasaka flat din takalmi baki, Haushi taji saboda ganin sunyi anko da amadi, ji takeyi kamar ta koma gida ta sake wasu kayan, "Meye kuma harda sako kaya kalar nawa?" Yafada cikeda tsokana yana kallonta, sake daure fuska tayi, "Ni ban ma san kalar kayan da kasako kenan ba.." "Bawani nan kin sani kawai dai kidai nagane so kikeyi muyi anko" Sake k'uluwa tayi nan ta juya tana harare harare shikuma abin dariya yake bashi, sake niyyar tsokanarta yayi ya kalleta, "Har kin dawo daga unguwar? Ai da kin yi addressing dina naje na dauko ki" "Nagode.." Tafada batare data kalleshi ba saboda ta gane tambayar rainin hankali yayi mata tunda ai yana gani ta fito daga cikin gida, "Ina twins dina?" Ya tambayeta, "Dama kanada twins ne?" "Au da ke baki saniba?" Shiru tayi masa, dan haka ya kalleta yayi dan murmushi, "Kizo mu shiga mota karki gaji da tsaiwa ni kinga nasaba tsayawa a aji" "Basai na shiga ba, nifa aiki nakeyi ka fito dani.." "Daga dawowar taki daga unguwa kika hau aiki?" Sake yin shiru tayi dan haka ya kalleta yana duba agogon dake daure a hannunshi, "Nima ba zama nazo yiba dama ganinki kawai nazo nayi sannan naga gidanku, tunda nagani shikenan zanje natafi amma karki dauka natafi kenan, no i will be back soon, ko yanzu dai nasan kinyi believing cewar bazan taba barinki ba har sai kin zama mallakina koda kuwa bakya sona tunda ni ina sonki shikenan.." Juyawa tayi ta kalleshi fuskarta a tamke, "Nagode da sona da kakeyi amma kasani auren matar da bata sonka babban kuskure ne, sannan budurwa itace tafi dacewa dakai ba bazawara mai yara har biyu ba, Allah ya kiyaye hanya.." "A'a ni bazawara ce tafi dacewa dani ba budurwa ba saboda manzon Allah ma da bazawara yafara kinga kenan idan nayi haka na dabbaka sunna babba.." "Allah ya kiyaye hanya.." Tun kafin ya amsa tayi gaba abinta, binta da kallo yayi yana jujjuyawa kalmominta acikin ma'auni, Duk maganganun da take fada masa yana ji acikin ransa cewar akwai wani abune da yake damunta acikin zuciyarta wanda yakeda alaka da wannan sannan kuma ga maganar da amir ya fada masa dangane da ita cewar bataji dadin rayuwar aurenta nafarko ba, to indai hakane bawai sonshi dinne batayi ba kawai dai akwai wani abune wanda ta ajiyewa ranta, Waya yayi mata ta dauka dakyar murya a dakile, "Please turo min amir zamuyi sallama" Katse wayar tayi ta kalli amir, "kaje yana kiranka" "Wai waye wanda yazone?" Mama ta bukata, "Wallahi mama wani classic guy ne anty tasamu.." Daukar takalmi tayi ta jefeshi yayi saurin fita yana dariya, A tsaye jingine da mota yasamu amadi, "Abokina yi hakuri nasake fitowa dakai ko" "A'a wallahi babu komai" Kallonsa amadi yayi, "amir ni dagaske nake son yayarka amma kuma taki kwata kwata bani hadin kai mu fuskanci juna ban san dalili ba, shin mijinta nafarko ya cutar da itane?" "Gaskiya bakai kadai yaya nadiya ke yiwa hakaba, kaga bayan mutuwar aurenta manema da yawa sun fito suna sonta amma taki tace ita karatu zatayi saboda kamar yadda nafada maka abaya ko kadan bataji dadin aureba, Wannan dalilinne yasa yanzu bata sha'awar sake yi kwana kusa saboda kasan bahushe yace naji dadi shine gari ba na saba ba, abubuwan da anty nadiya tagani agidan aure suna da yawa, taga rayuwa kala kala daga karshe suka rabu da mijin babu arziki, to kaga wanda yaga haka ai fiyeda irin wannan ma zai iyayi" Jijjiga kai amadi yayi, "na fuskanceka amir, nagane dalilin nadiya na tsanata da kin amsar soyayyata, nikuma nayi maka alkawarin mutukar na auri yayarka bazata yi kuka daniba sai ko na farin ciki, bazan wulakantata ba, zan kula da ita sannan zan bata gatan da bata samu a aurenta na farko ba.." "Allah yasa, Allah ya tabbatar da alkhairi" "Amin" Hannu yasa a aljihu ya dauko kudi sabbi fil yan 500 na dubu biyar yabawa amir yace ya siyawa twins sweet daga nan ya shiga motarshi yatafi yana mai jin son nadiya yana sake ratsa duk kofofin jinin jikinsa,sannan yanajin wani tausayinta yana shigarshi, Tunda amir ya kawo sakon mama ke kallon nadiya tana son jin yanda zata karbi zancen amma ko uffan batace ba shikuwa amir sai yabon amadi yake tayi yana cewa mama wallahi guy din ya hadu sannan ga hankali ga class gashi dan gayu. Tunda yatafi nadiya bata kirashi ba ganin haka yasa shi ya kirata, kamar koda yaushe shiru tayi masa har fadeela ta shigo ta haye jikinta tafara yimata surutu jiyo surutun fadeela da yayi yace tabashi ita, mikawa fadeela wayar tayi ta kara mata ajikin kunnenta, "Momy waye?" "Dady ne" yabawa fadeela amsa ai kuwa nan ta hau tsalle saboda tazata dadyn tane duk da tafara mantawa dashi.... *_Ummi Shatu_*🏻 *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_BY_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of perfect & expert writers_ _Jinjina ga babbar yaya anty maijidda musa, nagode da kokarinki agareni, Allah yabarmu tare.._ *42* aishaummi.blogspot.com *T*salle fadeela tahau yi tana yiwa amadi surutu, nan yasamu abokiyar hira tanata yimasa labarin school dinsu harda su abcd da sauran karatun da ake koya musu a makaranta, Ita kanta nadiya sai da abin ya bata mamaki irin yanda amadi ya biye fadeela taketa yi masa surutu, shima fadeel ya shigo nan fadeela tabashi wayar tana cewa, "Ga daddy" Karba shima yayi nan hirar takoma amadi da fadeel, daga karshe ita nadiya ma baccine ya dauketa tabarsu sunata faman surutu bata san lokacin da suka gama ba, "Ina momyn take?" Amadi ya tambayi fadeel, "Gata nan tana bacci" "To kyaleta karka tasheta",nan yayi sallama da yaran ya kashe wayarsa. Tun daga nan kullum idan ya kira wayar dasu fadeel suke shan hirarsu suyi tayi masa surutu suna sashi dariya, Satinshi biyu da zuwa yasake shiryawa ya dawo acikin weekend ranar asabar, sai kawai waya yayi mata yace yana waje, amir ta kira tace yaje da bako awaje saboda ita tana kwance cikin bargo tana baccinta, Amir na ganin amadi ne yamaza ya koma cikin gida yafadawa mama, nan mama tace ashigo dashi falon baki, Amira mama tasa tayi masa girki nan Amira ta shiga cikin kitchen ta dora, Dakyar nadiya ta tashi tayi wanka ta shirya bayan mama ta leko tayi mata kaca kaca, shiryawa tayi cikin leshi dark brown da mayafinsa ta fita, Lokacin da zata shiga sai ga Amira itama rikeda faranti zata shiga, bata hanya tayi ta fara shiga sannan tabi bayan amiran, Sai da Amira ta gaisheshi sannan ta tashi ta fita kallon nadiya yayi yau dinma fuskarta adaure, "Wannan kanwar taki tanada hankali kamar amir.." Shiru tayi masa bata tanka ba, "Ina twins dina.." "Basa nan sunje islamiyya" Murmushi yayi bai kara cewa komai ba illah kawai kallonta da yake yi, Babu wanda ya kara magana haka suka cigaba da zaman kurame sai da suka dade ahaka sannan amadi yayi magana saboda yasan ita dai ba magana zatayi ba, "Nadiya....,ina so kiyi hakuri ki bani dama saboda komai arayuwa da kika ganshi kaddara ne sannan kuma bawai yana nufin cewa saboda mutum daya yayi maka butulci kowama butulu bane, a'a ita rayuwa ahaka take tafiya, yayinda wani ya bata maka sai wani ya dad'ad'a maka, nidai indai nine nayi miki alkawarin bazan taba cin amanarki ba.." Duk wannan maganganun da yayi bawai sunyi tasiri agareta bane kawai dai ta daukesu a matsayin zallar karya irinta yaya kabeer, "Dan Allah nadiya kibani dama domin na nuna miki irin son da nake yimiki" Har lokacin dai bata ce dashi ko ci kanka ba,shiru yayi yazuba mata ido kawai yana kallonta, "Bakaga an kawo maka abinci bane.." Tafada batare data kalli gefen da yakeba, "Kin damu da naci ne? Ai baki damu da koshina ko yunwata ba.." Bata sake tanka masa ba dan haka yajawo farantin abincin nan yabude yaga potatoes mix da wata hadaddiyar sos wadda tasha curry da hanta sai kamshi take, Kwallo biyu kacal ya dauka ya debi sos din yafara ci, "Kanwarki ta iya girki, ko kece kika yi?" "Bani bace.." Tafada tana sake hade rai, Shiru yayi yaci gaba da cin abincin yana binta da ido, Ihun sallamar su fadeel ce ta cika musu kunne sai gasu sun shigo cikin falon aguje suna ihu wai dadynsu yazo, Zuwa sukayi suka rungume amadi suna ihun murna, amir dake biye dasu yana cewa "karku bata masa kaya ku cire takalmin" Kasancewar milki colour din yadi ne ajikin amadi, Tunda su fadeel suka dawo amadi yasamu abokan hira bai sake bi ta kan nadiya ba, mama ma tashigo sun gaisa daga nan kuma amir ya rakashi wurin abba suka gaisa ai nadiya ji tayi kamar zatayi kuka da bakin ciki saboda ita bata da burin sake yin aure kwana kusa, Fita yayi zai tafi yana rikeda su fadeel amir yana binsu abaya, boot din motarshi ya bude yace amir ya kwashe kayan ciki yakai gida na twins ne yakawo musu, ita kam nadiya tana tsaye tana kallonsu kayane sosai yasiyo irinsu bobo, biscuit, chocolate, indomie da sauran kayan makulashe na yara, Bin amir sukayi zuwa cikin gida dan haka amadi ya matsa kusa da ita, "Baby zan tafi.." Wani haushi taji ya rufeta saboda ta tsani baby dinnan da yake kiranta dashi, "Allah ya kiyaye hanya" "Amin nagode da addu'a, sai yaushe?" Jin tayi masa shiru yasashi yimata sai anjima yatafi, Haka sukaita fama koda yaushe yana kiranta awaya sannan yana tura mata da kati, Har yanzu ita bata ji alamun zata soshi ba saboda zuciyarta ta dade da cire soyayya daga cikinta, Tana kwance taji yana kiranta awaya, dauka tayi bayan tayi tsaki, "Baby kina lafiya?" "Lafiya" "Dama fada miki zanyi zanzo ranar Thursday ko Friday" "Bana nan" "Ina kika tafi?" "Basai kajiba, sai anjima yanzu aiki nake" Kitt takashe wayar bata san mama na tsaye tana jinta ba, "Ke nadiya wai meyake damunki ne? Ashe dama bakida wayo? Allah ya dubi zuciyarki da irin halin da kika shiga yakawo miki wanda yake sonki tsakani da Allah shine kuma zaki butulce masa? To wallahi ki zauna kiyi karatun tanutsu saboda wannan yaron da gaske yake sonki idan har kika wulakantashi kika koreshi to bazaki samu wanda yakaishi ba agaba, Kuma wallahi idan har ke bazaki aureshi ba to ni ashirye nake da in bashi Amira ya aura, wallahi indai bazaki aureshi ba ki fada min sai ince masa yazo ya auri Amira, haba yaro mai mutunci mai son yayanki, ya dauki yaranki kamar nasa amma kekuma babu wanda kike ciwa mutunci sai shi, to yakamata ki yiwa kanki fada.." Juyawa mama tayi tafita tabar nadiya tana kuka, ita kwata kwata yanzu auren ne bata so,sannan maganar mama ta tsaya mata arai wai zata bawa amadi Amira idan ita bata sonshi, Koda yasake kiranta yace zai zo cewa tayi to, ranar kuwa na zuwa sai gashi yazo da misalin karfe 12 narana,shiryawa tayi cikin wani material ja mai kyau ta fita, Acikin mota ta sameshi dan haka ta tsaya daga waje tana faman ciccin magani, ta cikin mirror ya hangota yayi murmushi ya bude ya fito, tana ganinsa tajuya tafara tafiya batare da tayi magana ba, binta yayi abaya tiryan tiryan har zuwa cikin gidan falon baki, Zama tayi anesa dashi ranta ahade, suna zaune haka shiru husna tashigo dauke da faranti kato wanda aka doro kayan abinci aciki, Fried rice da hadadden salad wanda yaji kwai da sauran kayan hadi sai juice, "Zo muci abincin" yafada cikin tsokana, "Na koshi" tabashi amsa, murmushi yayi yafara cin abincin yana kallonta tareda nazarinta sam shi abinda take yimasa baya bata masa rai bare ya daga masa hankali asalima hakan sake burgeshi yake yana kara rura wutar sonta acikin ranshi, Suna nan zaune zaman kurame har yagama cin abincin ya kalleta, "Baby ko babu komai ai yakamata ace mun gaisa ko?" "Mantawa nayi" tafada tana dauke kanta, murmushin da yasaba yi kowanne lokaci yanzun ma shi yayi, "Na sameku lafiya?" "Lafiya" Shiru suka yi na dan wani lokaci, "Ina budurwata Amira yau ban ganta ba?" "Tana ciki" ta amsa masa fuskarta adaure, "Wannan ciccin maganin da kikeyi yakamata ki daina shi saboda nima yau ba wurinki nazo ba wurin Amira nazo domin na sauya shek'a....". *_Ummi Shatu_*🏻 🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ _*BY*_ _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_ _Special gaisuwa ga aminan kwarai abin alfaharina, Pherty Xarah, Fido sodangi, Kausar m Hassan, Khaleesat Haidar, Mom Shakur, Sadiya I Bala,Khadija Sidi, Teemah Cool, Hafsat Bunxa, Aisha Dansabo,Zee Ruma,da duk wadanda ban ambata ba, ina alfahari daku kawayena..._ *43* aishaummi.blogspot.com *J*i tayi gabanta yafadi bata san daliliba, saurin kallonsa tayi nan taga shi ba ita yake kallo ba ma sam, wayarshi yake kallo yana daddannawa, Maimaita maganar take yi acikin zuciyarta nan take kuma maganar da mama tafada ta sake dawo mata inda mama take cewa idan har bata sonshi bazata aureshi ba to zata bashi Amira, Faduwar gabanta ce ta tsananta nan tasake kallonsa still dai wayarshi yake kallo ba itaba, "Dama Amira ai itace tafi dacewa dakai baniba, Allah yabada sa'a.." Tafada cikin k'uluwa tareda tashi zata fita, "Amin, dan Allah ki turo min ita idan kin shiga ciki.." Ya fada da niyyar sake tunzurata, bata ko waiwayo ba tayi gaba abinta amma kuma haka kawai sai take jin wani irin haushi yana bakuntar zuciyarta, Cikin dakinta ta shiga nan taga Amira tana zaune tana gyara kayan sakawar su fadeel tana shirya musu shi acikin wardrobe, kamar bazata yi magana ba sai kuma tace da Amira, "Amira kije Ahmad yana kiranki.." "To anty.." Amira tafada gamida mikewa da sauri, "To Kodai dama yarinyar nan tasan da zuwanshi ne?" Ta tambayi zuciyarta, zama tayi taci gaba da aikin da amiran tatafi tabari. Amira nashiga falon baki ta iske amadi azaune, "Yaya Ahmad ina wuni?" Tafada cikin ladabi, "Lafiya Amira, yasu mama?" "Suna nan lafiya" "Yawwa dan Allah so nake ki shirya min su fadeela zamuje unguwa dasu.." "To yaya Ahmad" "Yawwa nagode" Fita tayi zuwa dakin mama inda Maman ke shiryasu bayan tayi musu wanka nan Amira tafadawa mama sakon amadi na ashiryasu zai kaisu unguwa, Kayansu Amira tasa musu tayiwa fadeela kwalliya sosai takama mata gashinta da ribom kalar kayanta pink din riga da bakin jeans skirt, shikuma fadeel pink din t shirt da bakin jeans ta fesa musu turare, Kama hannunsu tayi takaisu wurin amadi tace gasu nan sun fito, Kallon yaran kawai ya tsaya yana yi domin ba karamin burgeshi suka yiba ji yake aransa inama yaranshi ne,inama shine ya haifesu shida nadiya amma kowaye ya auri nadiya dafarko yayi masa overtaken ne kawai da tuni yanzu yaran nan nashine, Kama hannunsu yayi suka fita yayinda Amira ita kuma tafara tattare kwanukan abincin da yaci. Nadiya kam tana daki bata san abinda yake gudana ba amma jitake aranta amadi yama yi mugun raina mata hankali, daga ganin kanwarta sai yace ita yake so yanzu? Tsaki taja tayi juyi, "koma menene shi yajiyo dai dama ni ba sonshi nake yiba.." Shigowar Amira ne ya katse mata tunani, "su fadeel sunbi yaya Ahmad unguwa" "Kuma meye nawa ni aciki?" Nadiya ta bata amsa cikin fada, fita Amira tayi daga cikin dakin, jin karar shigowar massage awayarta yasata dubawa, _Wasafa nake yimiki babu wata shek'a da na sauya, so karki fara kishi da kanwarki dan naga har kishi ya bayyana acikin idonki karara,munje unguwa da twins dina nasan ke ko nace kizo ki rakamu ba zuwa zakiyi ba shiyasa banyi inviting dinki ba, sai mun dawo,1,4,3.._ Gyara kwanciyarta tayi tana hararar wayar kamar yana wurin, "ruwanka kuma" Amadi wurin wasan yara ya nufa dasu fadeel, kowa yagansu zaiyi tsammanin cewar yaranshi ne gashi suma sun fara shakuwa dashi sosai, Wasa suka rinka yi cikin farin ciki shikuma yana yimusu pics wani lokacin kuma ya shiga yayi musu tare, shi kansa bai san adadin yawan hotunan da yayi musu ba, Sai da sukayi wasa mai isarsu suka gaji tikis suka fara kiran yunwa sannan ya daukesu zuwa wani restaurant dake gaba kadan da wajen wasan yaran, Fito dasu yayi suka shiga ciki yayi musu order din abinci, amala da miyar ganye da kaza, shi yarinka basu abincin har suka koshi sannan yaci yabiya kudin abincin suka fito, Maimakon yakaisu gida sai ya nufi supermarket dasu nan suka shiga ya lodo musu kayan dadi kala kala yafito yana rikeda fadeela daya hannun kuma ledar da ya iyo shopping ce fadeel kuma yana biye dasu, Kamar a mafarki kabeer ya hango yaranshi wani rike dasu lokacin da yake packing acikin harabar supermarket din, duk da yadade rabonshi da yaran domin ba zuwa ganinsu yakeba amma ai bazai iya mantasu ba, cikin gaggawa ya fito daga cikin motarshi ya nufi wurinsu amadi, Amadi yana kokarin bude motarshi kabeer ya isa wurin, "Fadeel,fadeela...." Kabeer ya kira sunan yaranshi yana karewa amadi kallo, "Bawan Allah kai kuma waye da zaka dauko min yara ka kawosu nan wurin batare da izinina ba?" Kabeer yafada cikin gadara, Kallonsa amadi yayi "banfa ganeka ba, waye kai please" "Ohhh tambayata ma kake ko waye ni? Ok to nine mahaifin wadannan yaran kai kuma waye" "Allah sarki, ni nine wanda yake shirin zama babansu ta hanyar auren mahaifiyarsu" Ai take zuciyar kabeer ta tsananta bugu kishi ya bayyana a fuskarsa karara, haushin amadi ya kamashi musamman ma da yaganshi handsome babu alamun kauyanci ko shirme atare dashi, "To bani yaya na inyaso kaje ka auri uwar tasu ita kadai amma yaya tunda nawane babu wanda zaiyi min gadara dasu" Murmushi amadi yayi wanda ya bayyanar da beautiful point dinshi, "Amma dai kasan ai ba kai kadai ka haifi yaran ba ko? Dan haka tunda bakai kadai ka haifesu ba to baka da iko dasu kai kadai, idan yaranka kakeso ka karba kaje gidansu nadiya ka karbesu acan, amma nidai yanzu bazan baka yaraba yanda nafito dasu sai na mayar dasu wurinda na daukosu.." Kabeer najin haka yatada fada yana daga murya kamar wani zautacce, "Wallahi sai kabani yarana saboda bakai ka haifa min suba, kai fadeel kuzo mu tafi nine ubanku ba wannan ba" Zuwa yayi zai kama hannun yaran anan suka fashe da kuka suka kankame amadi suna makale kafada alamun bazasuje wurinsa ba abinda yayi mutukar sake daga hankalin kabeer, Nan mutane suka fara taruwa kabeer sai fada yake yana zagin amadi kamar wani marar hankali, ko takansa amadi baibi yasaka su fadeel a mota yashiga yatashi motarsa yabar kabeer yana cewa, "Wallahi yarana zan karbo, sai anbani yayana.." Wannan shine mafarin nadamar kabeer saboda yahadu da yayanshi na cikinsa amma sunki zuwa wurinsa daga yakai hannu zai tabasu sai su saka kuka. Nadiya na daki azaune bayan tayi wanka ta shirya tana kwalliya su fadeel suka shigo dagudu, fadeel ne mai kokarin dauko ledar siyayyar da amadi yayi musu, "Momy kinga uncle ya siya mana, kuma mun hadu da wani a supermarket sunyi fada da uncle yace wai shine babanmu.." Fadeela tafada tana zama akan cinyarta, sake tambayar fadeel tayi nan yafada mata kamar yadda fadeela ta fada, Tashi tayi tafita waje wurin amadi, yana saman motarshi azaune, Tsayawa tayi ajikin motar tana son ta tambayeshi abinda su fadeela suka fada mata amma takasa saboda basa doguwar magana dashi. Zuwa can tadaure ta kalleshi tace, "Naji su fadeel suna fada min wani zance" "Name?" Ya tambayeta, "Wai kun hadu da abbansu a supermarket" Shiru yayi mata baiyi magana ba, "Ya kayi shiru?" "Ehhh" Yace da ita yana kokarin dirowa daga saman motarsa, "Dagaske ne mun hadu dashi may be ma kiganshi yazo anjima.." Sai da taji kanta ya sara saboda ita yanzu bata son duk wani abu wanda zai hadata da yaya kabeer, "Zanje in tafi amma wannan shine tafiyata ta karshe bazan sake dawowa gidanku ba har sai naji matsayina awurinki, dan haka nabaki dama ki zauna kiyi shawara da zuciyarki sannan ki yanke hukunci akan maganarmu, idan har zaki aure ni kifada min idan bazaki aure niba karki boye min ki sanar dani gaskiya, nabarki lafiya" Bai jira amsar da zata bashi ba ya wuceta yaje ya bude motarsa ya zabureta yabar wurin..... *Fatan Alkhairi ga k'awar kirki maryama qaumi...* _Gaisuwa mai yawa ga masoyan littafin mijina sirrina, khairat dan dawaki,heedah, hajjaju chuchu, Nasma, kadija mai kano, Billy reality, mom amir,ummy aysha, meenah 4eva da duk wata masoyiyar MS..__* MIJINA SIRRINA.. 44-56 [8/13, 3:00 PM] Ummi Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ _*NA*_ *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_ Your birth day is the perfect day to say I care, because you will remeber me when u certainly make it a big affair, and when you do hold a party... I bet you will be the one who would care to make ur special day a costly affair!!!!HBD MARYAM QAUMI. _Fatan alkhairi ga masoyan Anty amadi, Hawwa mudi, baddo alka, salma luv and others.._ *44* aishaummi.blogspot.com *K*asa motsi nadiya tayi illah kawai kallo data rinka bin motar amadi dashi har ta daina hangoshi, gabanta ne taji ya tsinke yafara faduwa wanda bata san dalili ba, Dakyar tayi ta maza taja kafarta tabar wurin ta nufi cikin gida, da amira tafara cin karo tana kokarin hada kayan wanke wanke, daf da zata wuce ta shiga daki taji maganar mama daga kofar kitchen tana yimata magana, "Bakon naki yatafi?" "Ehh mama yatafi.." Tafada jikinta asanyaye, Kallonta mama tayi dakyau anan tagane cewar akwai abinda yake damunta dan haka tasake yimata magana, "Nadiya ya kamata dai ki zauna kiyiwa kanki karatun ta nutsu domin wallahi ina jiye miki yin nadama aduk ranar da kika bari wannan yaron ya subuce miki, kiduba kiga irin dawainiyar da yake yi da yaranki, ko haka ai yasa ki saurareshi.." Shiru tayi tana sauraren mama,itafa kowa yakasa gane matsalarta ne, ita gaba daya mazanne yanzu sun gama fita aranta, gani takeyi tunda yaya kabeer yayi mata wannan cin mutuncin to kowanne namiji ma hakan zaiyi mata, "Kinji abinda nafada miki ko..?" Muryar mama tadawo da ita cikin hayyacinta, "Ehhh naji mama.." Tabawa mama amsa, juyawa Maman tayi ta nufi cikin kitchen tana cewa, "Yawwa yadai fi miki" Daki ta shiga nan tasamu su fadeel duk sun wargaza kayan siyayyar da amadi ya iyo musu suda su waleeda da husna, Ko takansu bata biba ta nemi wuri ta zauna tana tunanin abinda zaije yazo nan gaba acikin rayuwarta, da ace su mama zasu barta to da ita da sake yin aure sai a lahira amma aduniya dai kam tagama, Tadade tana tunani acikin ranta har na tsawon wani lokaci,shigowar Amira ce ta katse mata tunanin da takeyi, "Anty nadiya wai ana sallama dake awaje.." "Amira dan Allah ku kyaleni kaina ciwo yakeyi.." Juyawa Amira tayi tafita,Amira bata jima da fitaba mama tashigo dakin, "Haba nadiya ki leka mana kiga ko wanene inyaso sai kibashi hakuri tunda bakya jin dadi.." Mikewa tayi ta fita batare da tayi magana ba, Kamar acikin mafarki ta hangoshi tsaye yasha wani black space (no respect) kamar kada ta karasa wurin sai kuma taga cewar gara taje inyaso sai ayi wacce za ayi, Yanda yasha kunu ya hade girar sama da kasa haka itama tasha kunun ta daure fuskarta tamau fiyeda yadda ya daure tasa, "Lallai yaya kabeer dinnanma dan rainin wayone.." Tafada acikin zuciyarta gamida karasawa wurinda yake zuciyarta cikeda tsanarsa tareda jin haushinsa, ita sai yanzuma take nadamar kasancewarta matarsa ada, Ko sallama bata yimasa ba ta tsaya tareda rike kugu, "Naji ance ana sallama dani dama kaine? Idan Kaine to gani kayi kafadi abinda ya kawoka domin sauri nake.." Mamakine ya kama kabeer ganin yanda nadiya ke faman kallonshi shekeke tana yimasa kallon hadirin kaji, "Waye wanda naga yakai su fadeela supermarket...?" Yafada cikin kunar rai tareda gadarar cewar yaranshi ne, Saida ta dan yimasa wani kallo mai taken ka rainawa kanka wayo sannan tace, "Saurayina ne wanda zan aura, da magana ne?" Wani takaici da haushine suka ziyarci kabeer lokaci guda,kallonta yayi ta cikin bakin glass dinshi, "Saurayinki?" "Kwarai kuwa domin ba bazawari bane saurayine sabo fil..." Saurin dakatar da ita yayi, "ya isa haka, kina jina, kibude kunnenki dakyau kiji daga yau sai yau, kar wani wanda ya sake gigin daukar min yarana domin ba wani dan iska bane ya haifar minsu, nine na haifi abina.." "Dakata yaya kabeer, kai har kana da bakin da zaka kira su fadeel da sunan yaranka? Yaran da kayi watsi da rayuwarsu ka banzantar dasu, yaran da harma sun manta da cewar kaine ubansu, tunda muka rabu dakai daidai da rana daya baka taba zuwa ka gansu ba bare ka dauki dawainiyarsu, kaga kuwa indai hakane to baka da bakin da zaka kirasu da 'yayanka..." Ta karashe maganar tana yin hucin bacin rai, "Haka kikace? Nadiya ni kike fadawa haka? To tunda abin babu mutunci aciki wallahi sai kin bani yarana, zanzo zan tafi da yayana inyaso kije ki auri duk uban wanda zaki aura.." "Wannan ne kuma baka isaba, sannan ni ba uban wani zan aura ba saurayi zan aura mai sona wanda babu abinda yasani na yaudara baima taba auren ba bare har ya zama uban wani.." Tana gama fadin haka ta juya tafara tafiya batare data sake sauraron kabeer ba, in banda daci babu abinda makogaron kabeer yakeyi saboda yasan nadiya magana ta fada masa,sannan gashi zatayi aure zata auri wani wanda bashiba, "To tunda kin zabi ayi rashin mutunci kisani wallahi sai na karbi yayana ko da karfin hukuma ne.." Tana jinsa amma bata waiwayo ba saboda ita yanzu bata kaunar koda ganin fuskarsa ne, kanta kuwa in banda ciwo babu abinda yakeyi saboda tashin hankalin yaya kabeer, "Ohh ni nadiya ko sai yaushe zan samu kwanciyar hankali?" Ta

Chapter 9 of 20