Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kyau tayiba sai dai babu annuri akan fuskarta sannan babu wanda zai kalleta yayi tunanin ta taba yin aure sai dai wanda yasani, "Baby muje ko?" Bude mata kofar mortar yayi ta shiga ta zauna ya rufe ya zagaya daya side din shima ya shiga, sai lokacin ta dan kalleshi har taga shigar da yayi, milk colour din wani hadadden yadine ajikinsa mai manyan zane marar kauri mai tsananin haske sannan yasa hula itama milk colour, sai zuba kamshi yake kana ganinsa babu tambaya kasan angone, "Baby bamu gaisa ba" Shiru tayi masa ta dauke kanta hakan da tayi yasashi matsawa kusa da ita, "Haba baby yanzu kuma ai ya kamata ace ana bani matsayina na miji, idan ina yimiki magana ya kamata ki rinka amsa min kidaina yimin wannan fushin..." Yakare maganar yana kai mata wani sanyayyen kiss awuyanta domin ba karamin kyau tayi masaba sannan yadade yana kwadayin yin hakan agareta, Jin bakinsa akan wuyanta yasata sake daure fuska amma bata yi magana ba, "Wannan yaron wai meyake nufi ne?" Tafada acikin zuciyarta saboda jin har lokacin bata kiss yake asassan wuyanta, "Baby..." Yakira sunata cikin tsokana, "Uhmmm" "Kinyi kyau wallahi sosai kamar kada nabarki ki koma gida, ko zaki zauna.." "A ina? Ai ba haka mukayi dakai ba" Murmushi yayi ya kamo hannunta, "to ai basai munyi haka dakeba, ra'ayinane.." Bata sake yimasa magana ba tayi shiru abinta saboda taga fitina yakeji da ita wayaga sabon shiga dama kuma tasan dole haka tafaru tunda shi ba taba yin auren yayiba, Har sukaje wurin dinner din yana rike da hannunta, dakanshi ya fita ya bude mata kofa ta fito suka shiga ciki wanda tun daga waje masu camera suka fara haskasu. Sai yau nadiya ta tabbatar da cewar amadi cikakken dan gatane agidansu, suma yayun nashi dukkaninsu sai da sukayi mamakin ganin nadiya domin basu zaci zasu ganta hakaba tunda sunji yace ta haihu har yara biyu duk azatonsu zasu ganta ta tsofe amma sai sukaga sabanin haka anan dukkkaninsu suka yaba da zabin nasa, "Lallai anty amadi dole arude ace aure akeso.." Inji anty hamida, "Kedai kibar yaron nan kina ganinshi silent.." Anty Dija ta fada tana dariya, "Gaskiya yayi zabe, matarshi kyakkyawa da ita wallahi amma kuma zanga yanda zasu kwashe da zee kanwar dad din su jawahir.." Anty siyama ta karbi zancen, "Bata san yayi aure bane?" Anty hamida ta tambaya, "Wallahi bata saniba, ai kin fada mata nayi saboda ba karamin aikinta bane kiganta ta hado kayanta ta taho domin tana sonshi wlhi kuma koni naso ace ya aureta.." "Ai autan hajiyanne kalar asararru da sakalai gareshi badan hakaba ai da zai iya yin mata biyu.." Inji anty Dija, "Wallahi fa, ai bazai iyaba.." Inji anty siyama, hirar tasuce ta katse sakamakon kiran dangin ango da akayi zuwa cikin filin, nan suka fiffita kowaccensu tana sanye da swiss lace maroon wanda sukayi iri daya sunsha head baki, Hannun nadiya amadi ya kama ya rike yana murzawa ahankali, "Wadancan duk yayuna ne baby uwar mu daya ubanmu daya, kinga waccen wadda ke rike da babyn itace babba sunanta anty Jidda ta kusa da ita kuma anty siyama ita ke binta dayar kuma ita nake bi sunanta anty hamida.." "Allah sarki.." Tafada ahankali saboda gaba daya jikinta yagama yin sanyi haka kawai, "Ko bakya jin dadi?" Ya tambayeta yana shafa hannunta, "Ikon Allah, wai meye haka?" Tafada tana kallonsa, "Allah yabaki hakuri, nadaina" tashi yayi yafita zuwa wurinsu anty Dija yahau yimusu ruwan nairori, Koda aka kira ango da amarya dakyar yasha kanta ta yarda suka fita tsakiyar filin, daga ita harshi babu Wanda ya taka tsayawa kawai sukayi, kallonta yake tayi k'asa k'asa yana jin sonta na karuwa acikin zuciyarshi. K'arfe 10 aka tashi daga dinner din, hannunta yakama suka fita bayan tagaisa da yan uwanshi, mota ya bude mata shima yazaga ya shiga ya zauna tareda matsawa kusa da ita, "Wai menene haka?" Tafada tana ciccin magani, "A ina? Kodan na matso kusa dake?" Ya tambayeta yana murmushi,shiru tayi masa ta dauke kanta ta rabu dashi, kamar dazu yanzu ma haka ya dameta da kiss, gaba daya ya takurawa wuyanta da hannunta, "Wayaga ba sabinba" tafada acikin zuciyarta, har sukaje round about din da aka sauketa dazu yana manne da ita, "Baby ai ba yau zaki tafiba ke" "Saboda me? Wallahi tafiya zanyi tunda bancewa mama zan kwana ba" "To shikenan zaki tafi, kin yarda gobe inzo?" "Um um" ta bashi amsa,kiss yakaiwa bakinta nan yagogi jan bakin dake kan lips dinta bai saniba, "Daga yanzu indai muna tare nayi miki magana kika ki amsawa haka zan rinka yimiki idan kuma awaya ne to zan barki da Allah.." "Nifa gida nake son tafiya.." Tun kafin ta rufe bakinta jeep din dazu tayi packing agaba dasu, "To ai gashi nan yazo, zaki tafi yanzu kiyi hakuri ba cinyeki zanyi ba.. Kinji..." Ganin yana shirin kaiwa bakinta kiss yasata fadin "naji" amma duk da haka bai fasaba sai da yayi kissing dinta abaki son ranshi, Har motar dasu Amira ke ciki ya rakata sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma motar da yake, gaba daya yanayin yau na musamman ne awurinsa lallai aure babbar ni'ima ce ba kadan ba, Yana shiga gida su anty siyama ma na shigowa kasancewar akwai haske sosai yasa suka ga jan bakin dake bakinshi wanda ya goga a lips din nadiya, "Anty amadi meye abakinka?" Anty siyama ta tambayeshi tana yimasa dariya, "Ni kuma?" Yafada yana kallonta, Dariya yaga sun saka gaba dayansu sunyi gaba hakan yasa ya tsargu, dakinsa ya shiga yaje gaban mirror ya kalli fuskarshi nan yaga bakinshi dama dama da jan bakin nadiya, Murmushi yayi ya zaro wayarshi daga cikin aljihunsa yafara kiranta......... *_Ummi Shatu_* [8/26, 3:14 PM] Ummi Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ _*NA*_ *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_ _Fatan alkhairi ga Maman Samha, zee gajouh, Maman humy, firdaus, pheey,Maman haneef, Maman Fati,da duk wani masoyin Amadi & Nadiya.._ _Gaisuwa ga aminiya maryam qaumi, u are always in my mind...._ *53* aishaummi.blogspot.com *L*okacin da ya kirata suna hanya dan haka taki dagawa, cigaba da kiranta yayi harta dauka amma fa ba don ta so ba, "Baby shine kika b'ata min bakina da jan bakinki ko?..". Abinda taji yafada kenan cikin muryarshi mai sanyi domin amadi ko kadan bashida zafi shiyasa muryarsa take sanyi kalau, "Uhmmm baby.." Taji yasake magana, "Ban gane abinda kake nufi ba.." Tabashi amsa, "Kin gane mana, kuma nasan kin gani kawai rabuwa kikayi dani nashiga cikin mutane ahaka.." "Wai me?" Ta tambayeshi, "Jan bakinki da kika goga min abakina.." Ajiyar zuciya ta sauke kafin tayi magana acikin zuciyarta, "nagoga maka kodai ka goga.." "Nidai nan gaba idan kin goga min dan Allah ki rinka goge min karki barni na fita ahaka ko kuma ma ki daina shafawa gaba daya..." "Saboda...?" Ta tambayeshi cike da gajiya da yin maganar, "Saboda indai muna kusa bakinki zai sha tsotsa.." "To sai da safe.." Tace dashi tana hararar shi ta cikin wayar kamar yana ganinta, "Ai ban sallameki ba, wallahi karki kashe idan kika kashe kuma.." "Kuma me?" "Nabarki da Allah tunda kinki jin maganata.." Fasa kashewa wayar tayi ta jingina kanta da jikin kujera tana sauraronsa bawai don tana son hirar ba sai dan babu yadda zatayi, "Baby kiyi min alfarma guda daya ki yarda gobe nazo naganki" "Yau ba gashi ka ganni ba..?" "Ai ganin da nayi miki yau bai isheni ba shiyasa nake son sake ganinki gobe.." "To gaskiya nidai ba sai kazo ba" Murmushi yayi ya zauna abakin gadonshi, "Yanzu baby ko nauyin fadar Kalmar bakiji ba? Cewa fa kikayi basai nazoba, nikuma ina son nazo saboda ina son ganin matata..." Shiru tayi hakan yasashi sake yin magana, "idan nasake yimiki magana kika rabu dani keda Allah.." "To wai dan Allah me kakeso ince maka ne? Ni agajiye nake ko gida fa bamu jeba muna hanya.." "To ai laifinki ne tunda sai da nace ki zauna ki kwana amma kika ki furr kikace ke tafiya zakiyi.." Shiru tayi batayi magana ba, jin taki yin magana yasashi fadin, "To yanzu so kike inbarki sai kinje gida?" "Uhmmm" "To shikenan zan barki amma da sharadi.." "Name?" Tafada agajiye domin tagaji da yin maganar ma, "Gobe zanzo naganki.." "Naji" tabashi amsa amma acikin zuciyarta cewa take "zaka zo ka dameni dai malam ina zaman zamana" "To shikenan sai goben, Allah yakaiku gida lafiya" "Amin.." Tafada tana mai alla alla da taji yakashe wayar amma bai kasheba kun san mutumin naku da d'an karen naci, "Sai anjima..?" Taji ya tambayeta, "Uhmmmm" "To sai anjima, i love you....!" "Uhmmmm" shine kawai abinda tafada, jinshi tayi yabata wani kiss na musamman ta cikin wayar sannan yakashe, "Ikon Allah.." Tafada ahankali bayan ta cire wayar daga kunnenta. Basu suka karasa gida ba sai 11:30 lokacin harsu mama sun kwanta, In banda yunwa babu abinda takeji nan taje tayi alwala tayi salla tana idarwa ta zubo abinci taci, ko kayan jikinta bata cireba ta kwanta saboda tsabar gajiyar da ta kwaso, Washe gari umman sumaila ta tafi haka suma su A'isha kannen kabeer sun tafi shiyasa yanzu gidan babu kowa sai su yasu, Fitowar nadiya kenan daga wanka tafara jiyo maganganu atsakar gida, hijabi tasa ta fita nan taga yaya kabeer zaune ra'as yanata faman gursheken kuka agaban mama, mama sai hakuri take bashi akan yadaina wannan kukan, "Mama dole inyi kuka tunda har narabu da nadiya, ashe nadiya zata iya auren wani mijin baniba? Ashe aure aka daura mata jiya? Ni najawowa kaina amma har yanzu ina son nadiya wallahi, ina kaunarta, dan Allah mama ki taimaka min nadiya tadawo gareni.." Yafada yana kuka kamar ba namiji ba, "Kayi hakuri kabeeru kadaina kuka, ka dauki kaddara, haka Allah ya zabar muku kasan kowa da iri tasa kaddarar, kayi hakuri kaci gaba da addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.." Mama tafada jikinta asanyaye, "Mama wallahi rabuwa da nadiya bashine alkhairi ba arayuwata.." "A'a kabeer ya isa karka yi sab'o kayi hakuri kayi shiru" Ita dai nadiya tsayawa tayi kawai tana ganin ikon Allah,ganin kabeer ya kura mata ido yana kallonta yasata saurin juyawa takoma daki saboda yanzu ita matar wanice gashi daga wanka tafito, bata san yanda suka kwashe ba tadai jiyo gidan yayi shiru alamun ya tafi, ko tausayinsa bataji ba domin tasan abin da zaisa taji tausayinshi yana gaba lokacin da duniya tayi masa atishawar k'uda. Shiryawa tayi cikin wata shadda ja mai mutukar tsada in banda maiko babu abinda takeyi, kwalliya ta danyi sama sama tasha turare ta fito tana kokarin daura dan kwali anan mama take sanar da ita wai kabeer ya dauki fadeel da fadeela yatafi dasu sai yamma zai kawosu, "Damuwarsa.." Tafada acikin ranta amma afili sai ta amsawa mama da to,dakin Abba ta shiga ta gaisheshi, bayan sun gaisa ya dauko mata kudin sadakinta yabata yace gashi nan hakkinta ne, rasa me zatace tayi saboda idan ta karba bata san abinda zatayi dashi ba daga karshe dai tacewa Abba ya ajiye mata awurinshi. Amadi bai samu zuwa da wuriba saboda yana can gida anata biki domin sai yau bikin yakare baki duk sun tattafi amma yayunshi duk suna nan babu wadda yatafi, Karfe 2 yasamu ya karasa gidansu nadiya koda ya kirata awaya ma sai da tagama jan ajinta sannan ta dauka duk da yanzu ma taji tarage jin haushinsa acikin zuciyarta, cewa tayi ya shigo lokacin da yace mata yakaraso, "Dakinki zan shigo?" Yafada cikin zolaya, "A'a kamanta kan gadona zaka zo.." Tana gama fadin haka ta kashe wayar, dariya yayi yafita daga cikin motarsa ya rufe ya shiga cikin gidan, yau tsakaninshi da mama 'yar surukunta sukayi dan dakyar ya iya gaisheta tareda yimata godiya daga nan yatashi ya shiga falon baki ya zauna, wayarshi ya zaro ya shiga Facebook yana duba sakonnin taya murnar da friends dinshi suka turo masa na auren da yayi, husna ce ta kawo masa ruwa da abinci da lemo, Yana nan zaune gimbiyar tasa ta shigo sai faman kamshi take budadawa gashi shaddar jikinta ba karamin kyau tayi mata sannan skirt din ta bayyanar da hips dinta sosai kasancewar dinkin riga da skirt ne, Fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna suka gaisa daga nan tayi shiru bata kara magana ba, "Baby zo muga kunshin naki..." Yafada yana kallonta, "Wanne kunshi kuma? Tun jiya bakaga kunshin nawaba sai yau" ta bashi amsa tana latsa wayarta, bai kuma yin magana ba ya rabuda ita yaci gaba da kallonta, ita kuma tanata faman latsa wayarta, Tashi tayi taje ta zuba masa abincin, faten doya sannan ta tsiyaya masa juice,juyawa tayi zataje ta zauna ya kirata, "Baby zo" Kasa yimasa musu tayi saboda ayanda yayi maganar babu alamun wasa, kamar kazar da kwai ya fashewa aciki haka ta karasa tana zuwa yasa kafarshi ya hardota jikinshi, Akanshi ta fada yasa kafa ya hardeta ta yadda bazata iya tashiba, "Shine nace kizo naga kunshin naki kika ki zuwa ko? Uhmmm?" Ita gaba dayama tarasa me zatayi kunya ko haushi? Shiru tayi taki amsa masa, hannayenta duka biyu yakamo yana jujjuyasu cikin nashi yana kallon kunshin, kamar zata saka kuka dan takaici, Bata gama wannan bacin ranba taji ya zame dan kwalin kanta, "Wowwww, baby kitsonki yayi kyau, waye yayi miki?" Yafada yana shafa kitson, hancinshi yakai bisa kitson yana shakar kanshin man kitson dake tashi akan nata, "Baby ashe dai kema kinada gashi, wowwww..!" Shiru tayi kawai tana jinsa sai tafiyar tsutsa yake yimata akanta wai shi ala dole shafawa yake, "Baby waye yayi miki kitson?" Shuru tasake yi, "Idan har baki amsa ba keda Allah.." Jin yahadata da Allah yasata amsawa, "Amira ce.." "Gaskiya dole nabawa Amira tukwici saboda ta fito min da ke sosai, ji kunshinki ma yanda yayi kyau..." Yakarasa maganar yana shafar hannayenta, Rungumeta yayi gaba daya acikin jikinshi nan kuma tace bata san zance ba tafara yimasa mutsu mutsu, "Allah idan kika tashi ban yafe ba.." Komawa tayi ta lafe ajikinsa tana turo baki, "Ai da sai kace min damuna zaka zo kayi, shiyasa dama ka matsa sai nabarka kazo.." Ko amsata baiyi ba saboda ya tafi wani uzurin daban a wuyanta, "Wallahi Ahmad dinnan bashida kunya ashe ana ganinsa haka.." Tafada acikin ranta saboda ita dai arayuwar aurenta na baya bata san wani abu waishi soyayya ba amma shi wannan gashi daga jiya da aka daura musu aure zuwa yau yana nuna mata kauna kamar zai hadiyeta. Babu yanda ta iya haka taci gaba da zama ajikinsa har yagama fitinarsa, juice ya tsiyaya yasha tareda jan jelar kitsonta, hade fuska tayi ta kalleshi nan suka hada ido fessss taji ya fesa mata juice din bakinshi afuskarta, "Kai, kai.." Tafada cikin masifa, "Allah yabaki hakuri.." Yace da ita sannan yafara goge mata da hannunshi....... _Jinjina ga babbar yaya mom minal..._ _*Ummi Shatu*_ [8/28, 10:48 AM] Ummi Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO.* _Gaisuwa mai tarin yawa ga sadeeya sunusi umar (antyn hafsat), this page is for you..._ *54* aishaummi.blogspot.com *H*ad'e fuska tayi taki koda sake kallonshi ne, ahankali yake share mata fuskarta da tafin hannunshi yana murmushi saboda ganin yanda ta daure fuska tasha kunu, "Irin wannan shan kunu haka baby, Allah yabaki hakuri bazan sake ba.." Bata bashi amsaba tayi shiru abinta amma fuskar nan murtuk take, koda ya kammala goge mata fuskar tata kin sakinta tatashi yayi nan ya sake hadata da jikinshi tsamtsam. Sun dade ahaka har sai da yaji an kira salla sannan ya dago kanta yana kallon fuskarta, "Baby kinji ana kiran salla.." Kamar dazu yanzun ma shiru tayi masa har saida yasake maimaitawa, "Naji" "To tashi nayi alwala muyi sallah ko..?" Dama kamar jira take dan haka cikin hanzari ta tashi daga jikinshi ta dauki mayafinta da dan kwalinta tana kokarin daurawa, "Ina zakije ne?" Ya tambayeta, "Ciki zan shiga inyi salla" tafada fuska abace, "Tsaya tare ai zamuyi.." Dayake akwai bathroom acikin falon nan ya shiga yayi alwala yafito, idonshi akanta fuskar nan tashi sai murmushi ketashi ajikinta, "Baby nafito shiga kiyi alwalar.." Tana jinshi amma tayi masa shiru nan yasake maimaitawa amma bata kulaba, Matsawa yayi gabanta yana balle maballin hannun rigarshi, "Baby..., baki jina ne? Nace kema kije kiyi alwalar sai muyi sallar tare, yau ina son inyi salla da iyalina ne.." "Banayi.." Tafada batare data kalleshi ba, murmushi yayi ya sunkuya asaitin fuskarta bayan ya dafa gwiwowinshi, "Baby kenan, wallahi lada zaki samu indai kikayi salla tareda mijinki, ni nasan abinda kika fada ba gaskiya bane dan haka ki tashi.." "Me zanyi idan natashi? Ba na rigada nafada maka ba, ko ahaka zanyi sallar.." "A'a....." Yafada tareda mikewa tsaye, "Idan har ba dagaske kike ba kije keda Allah.." Sororo tayi tana kallonshi saboda jin abinda yafada, "Wai komai sai kayi min Allah ya isa? Wannan wanne irin abune?" Ta fada cikin jin haushi, "Ehh nasan hakanne kadai zaisa ki rinka bin umarni na saboda kin rainani, bakya sona bakya kaunata, tunda bakya sona kuwa nasan bazaki rinka yimin abinda nake so ba.." Jin yace yabarta da Allah yasata tashi ta shiga toilet, nan ya zauna yana jiran fitowarta amma dama tun lokacin da tayi maganar yasan cewa badagaske takeba, Kamar zata fashe dan bacin rai haka tafito, shikam murmushi kawai yake, sallah yajasu ta la'asar raka'a hudu, yana yin sallama ta tashi ta koma can gefe taci gaba da addu'o'inta. Tashi yayi yana gyara agogon hannunshi yana kallonta yanda taci magani ta bata fuska, "Baby zanje na tafi.., wai ina twins ne banji motsinsu ba ko zunje school ne?" "Abbansu ne yazo ya daukesu sai anjima zai dawo dasu.." Kai yagirgiza "ina fata dai bai kalle min fuskar matata ba..?" Sanin bazata amsa ba yasashi saka takalminshi ya nufeta, mikewa tayi tana gyara mayafinta, Hannunta taji ya kama, "muje to ki rakani intafi.." Batace komai ba yajata suka fara tafiya, dakin mama taje ta sanar da ita zai tafi nan mama tafito suka yi sallama, su Amira kuma basa nan sun fita itada husna walimar wasu kawayensu da sukayi saukar alkur'ani mai girma, Yana ganin mama ta juya daki ya kama hannunta yana kallon fuskarta, "Muje ki kaini mota sai ki dawo..." Tafiya sukayi suna zuwa daf da soro sai ga fadeela da fadeel da abbansu yana rikeda hannuwansu, ganin kabeer baisa amadi yasaki nadiya ba dan haka kabeer ya harzuka ya cika dam, su fadeela na son zuwa wurin amadi amma haka ya hanasu furr ya kada kan yaranshi zuwa cikin gida, Ita kanta nadiya da ba wai son amadi takeba saida abin yayi mata ciwo saboda tasan ya shaku da yaran gashi ko yanzu ma kafin ya fito sai da ya tambayesu, Ji tayi ya matsa hannunta tareda tsayawa a cikin soron, "Nima idan kin tashi haifa min yara twins nake so kamar su fadeela.." Yace da ita bayan ya jinginata da jikin bango ya kama dukkan hannayenta ya rike, "Ai ba nice mai...." "Shhhhhhht..." Ya katseta bayan ya dora dan yatsanshi akan lips dinta, "Insha Allah nima twins zamu haifa.." Bata kai ga yin magana ba suka jiyo alamun takun tafiyar kabeer, dama amadi yana son ya rama abinda yayi masa yanzu dan haka yayi gaggawar zira hannunshi ta kugunta ya rungumeta, kokarin zamewa tafara yi, "Baby idan kika gudu wallahi bazan yafe miki ba..." Ya rada mata acikin kunne, daidai lokacin kabeer din ya fito, ganinsu haka suna bawa soyayya hakkinta yasa kishinsa motsawa, Ko kallonsa amadi baiyi ba, "Wai dan Allah meyasa kake yimin haka..?" Tace dashi ahankali kamar mai yin rada, "Saboda ina sonki baby..." Yabata amsa bayan ya kai bakinshi jikin kunnenta, Karshen bakin ciki kabeer yajishi saboda yasan da biyu suka yi masa haka, sunyi ne domin su kona masa rai kuma gashi sunyi nasara,ganin nadiya da amadi ahaka shine gani mafi muni agareshi, Cikin hanzari yawuce su ya fita daga soron zuciyarsa tana suya tareda tuno masa da wacece nadiya acikin jerin mata. Duk da kabeer ya fice baiza amadi ya saketa ba sun dade atsaye acikin soron domin sam baya son tafiya yabarta dan dai babu yanda zaiyi ne, Har bakin motarshi yajata yabude ya shiga sannan ya kalleta yana rikeda hannunta, "Baby sai nadawo ko?" "Uhm" ta amsa masa ciki ciki,murmushi yayi yasaki hannunta bayan ya sumbaceshi, "Agaida twins dina sai kinjini.." "Allah ya kiyaye hanya" tafada tareda juyawa ta nufi cikin gida, ta mirror ya kurawa hips dinta ido yana kallonta har ta shige ji yayi yana kishin wasu mazan su ganta shiyasa ya kuduri niyyar hanata saka mayafi. Cike da kaunarta yatafi, koda yaje gida ma kasa samun sukuni yayi har saida ya kirata yaji muryarta, tun daga ranar kullum idan ya kirata yace zai zo sai tace a'a, lokacin da ta gama shirin tafiya makaranta ma yace zai zo ya kaita shopping tace ita dai a'a, yace zaizo ya kaita makarantar nanma tace a'a, Hak'ura yayi ya tura mata 50 thousands ta account dinta yace gashi nan ta siyi duk abinda take bukata dama ya rigada yayi mata registration tun tuni, Ranar monday da safe ta shirya ta tafi, koda yaushe amadi cikin kiranta yake da yimata text, shi dinma yana can yanata shirye shiryen tafiyar da zaiyi. *** Cikeda damuwa kabeer yabar kofar gidansu nadiya ya tasamma gidansa, Lokacin da ya shiga gidan asabe mc na daki itada kawarta Lola suna tattaunawa akan kabeer, "Ni matsalata dashi yanzu tunda ya rabu da matar nan tasa abubuwansa suka dagule, yanzu maganar da nake yimiki hankalinsa yafara komawa kan yaransa domin dazu dazun nan sai gashi yazo min dasu..." "Wannan duk mai sauki ne mc, yanzu dai maganin dukan da yake yi miki nake so muyi sannan kuma malam mai dogon zamani yace inyi miki albishir da cewa da zarar ya ketara wannan abun da zaki ajiye akofar daki shikenan kin gama dashi sai yanda kika juyashi..." "Lola naji dadin wannan batu to amma duk ba wannan ba, kudinsa fa yanzu basa shiga hannuna.." "Mc kenan ai duk wannan mai saukine da zarar kin fara juyashi shikenan sai yanda kikayi da dukiyarsa.., amma ni menene kasona aciki?" "Babu bukatar kiyi gaggawa wajen jin kasonki lola domin kinada kaso mai tsoka.... Kinji ma kamar yadawo" Mikewa lola tayi ta leka window nan kuwa taga kabeer dinne, mayafinta ta saba da jakarta asabe ta rakata ta kofar baya ta fita bayan ta ajiye wani dan siririn bakin abu kamar gashi akofar dakinta...... *** Satin nadiya daya da komawa makaranta amadi yaje amma shi akwai abinda ya kaishi, tunda ya shiga makarantar yayi mata waya tace lecture zata shiga, sai 2 tagama lectures dinta sannan ta nufi office dinsa yana zaune ya dora kafafuwanshi bisa table dinshi, da sallama abakinta ta shiga, ansawa yayi ya dago yana kallonta, "Baby sai yanzu?" "Uhmmm" Murmushi yayi "nima har yanzu kinga ban samu na kammala ba kuma inajin gobe ne tafiyata fa.." "Allah sarki..." Tafada batare da ta kalleshi ba, "Meyasa kika yafa mayafi bayan riga da skirt ne ajikinki..?" Ya tambayeta bayan ya kura mata ido, shiru tayi bata amsa ba, "Ko kina so ne wasu mazan su rinka kalle min halittarki? Dan Allah kidaina saka mayafi.." "Naji..." Shine amsar da ta bashi, ta dan jima a office din amma kusan shi kadai yake zancenshi saboda sai yayi magana uku kafin tayi guda daya, daga karshe ta tashi ta tafi hostel, girki tayi masa farar taliya da miyar danyen kifi, sai da tayi wanka ta sake kwalliya ta saka wasu english wears riga da skirt bakake sannan ta dauki abincin ta fita bayan ta saka babban hijabi ash colour.... _*Ummi Shatu*_🏻 [8/29, 8:21 AM] Ummi Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* _Home of expert & perfect writers_ *55* aishaummi.blogspot.com *L*okacin da ta shiga office din nashi baya ciki da alama ya dan fita, Wuri ta samu ta zauna tana kallon yanayin office din nashi, Tashi tayi taje ta leka ta window nan dinma babu alamun tahowarshi hakan yasa tasake komawa ta zauna tana jiranshi, Jin zaman ya isheta ita kadai yasata daukar phone dinta ta kira mama suka gaisa ta hadata da fadeel suka fara hira, Tana cikin yin wayar amadi ya shigo shima wayar yake yi amma shi da hajiyarshi yake wayar saboda taji yana cewa, "Hajiya may be fa ni anan ma zan kwana saboda har yanzu ban gama dasu ba wallahi..." Bata san me hajiyan tace ba tadai ji yace, "Ehhh Gata yanzu ma muna tare bari na bata ku gaisa.." Kashe tata wayar tayi shi kuma ya matsa kan kujerar dake kusa da wacce nadiya ke zaune ya zauna tareda kai wayar jikin kunnenta, karba tayi ta makala a kunnenta, Sake matsawa yayi sosai da kujerar shi kusa da tata dama kuma kujerun suna facing juna, gaba daya kafafuwanshi da gwiwowinshi manne suke da nata, tsareta yayi da ido yana kallonta saboda yadda ta saki jiki sosai suna gaisawa da hajiyarshi, Mika mishi wayar tayi bayan sunyi sallama da hajiya nan ya hada da hannunta ya saka wayar a kunnenshi, basu wani jima suna magana ba ya cire wayar daga kunnenshi har lokacin yana rike da hannunta, "Me kika kawo min baby..?" Ya tambayeta yana kallonta, "Abinci ne.." Ta fada fuskarta babu yabo ba fallasa, "Me kika dafa min?" Sauke idonta tayi a kasa bata bashi amsaba haka kuma bata bari sun hada ido ba, "Ni ai baby nafi son..." Kiss ya kai mata akan lips dinta ya dago yana murmushi, "Kinci abincin ke?" Kai ta daga masa, "no ban yarda ba Allah sai dai muci tare.." Yayi magana cikin shagwaba irin tasu ta yan auta, Shiru kawai tayi tana jinshi irin yanda yake yi mata shagwaba da sauran abubuwa kamar wani karamin yaro, Sai da ya sake sumbatarta a kumatu sannan ya mike yaje wurinda ta ajiye masa abincin a saman fridge, "Baby ina zuwa.." Fita taga yayi, bai jimaba sai gashi ya shigo rikeda babbar dadduma, shimfidata yayi ya sauke abincin ya dora akai sannan yaje ya riko hannunta, "Tashi muje muci abincin.." "Nifa na koshi.." "Allah tare zamuci bazan ci ni daya ba.." Tashi tayi tabishi har zuwa kan carpet din, zama tayi shima ya zauna yana facing dinta, "Tun kafin naci abincin naji kamshinshi ya cika min ciki, baby kin iya girki sosai.." Ita dai bata yi magana ba ta bude abincin ta saka miya ta dauki spoon tafara juyashi, Kallonta yake yi ganin ta dan tsakuro zata kai bakinta yasashi saurin kamo hannunta tare da sauya akalar spoon din zuwa bakinshi, "Wai wai... Baby wannan abincin da kifin kan tudu kikayi amma ba da kifin ruwa ba saboda naji dadinsa yayi yawa.." Duk da bata son tayi dariya sai da yasata yau ta dan dara akaro nafarko da yaga tayi murmushi har hakoranta sun bayyana kuma wai shine silar sata dariyar, ba karamin dadi yaji ba ganin ta dan murmusa, "Dan kara bani inji.." Yafada yana langab'ar da kai, kamar bata jiba tayi, "Baby kibani nace... Ko sai nabarki da Allah zaki bani?" D'iba tayi ta kai bakinshi nan ya debi rabi ya sa mata rabi abaki, "Yawwa baby ai haka akeyi, kibani inbaki kinji... Uhm babyn amadi..." Babu yadda ta iya haka taci gaba da diban abincin tana bashi idan tasa mishi abaki sai ya ci rabi ya bata guntun, tasan idan bata bashi ba yanzun nan zai cemata yabarta da Allah ita kuma bata son Allah yayi fushi da ita akan ta sabawa mijinta, Taliyar bakinta ce ta nemi zubowa saboda yunkurin magana da tayi sakamakon babban dan yatsanta da taji yaja, ta bude baki kenan taliyar da ya sa mata ta taho,bakinshi yakai kan nata, "Baby rigimammiya idan kika b'ata min darduma ta sai kin wanke min.." "Ni tashi ma zanyi tunda dama na k'oshi.." "To ai ni ban koshi ba dan haka ba zaki tashi ba.." Haka ya hanata tashi taci gaba da bashi abincin yana ci, yaya kabeer ta tuno shi sam bai taba cin abinci tareda ita ba duk lokacin da ta jirashi ma inyazo masifa zai tisata agaba yanayi. Dan mugunta haka tayita tura mishi abincin yana ci har sai da ya cinyeshi tsaf ai kuwa ba karamin mugun koshi yayiba shi kansa jin cikinsa yake yayi masa nauyi, "Baby akwai juice a fridge idan zaki sha.." Tashi tayi ta dauko ta cika cup ta mika mishi, "Baby wallahi na koshi da yawa.." "Ai kuwa sai kasha.." Karba yayi ya dan kurba ya fara bata a baki tasha, "Washhhh, baby bazan iya tashi ba kamani in tashi.." Dakyar ta iya dagashi ya

Chapter 12 of 20