Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tabargaza, "Matsalar yan auta kenan wallahi basu da kunya ga shegiyar shagwaba" anty hameeda ta fada, "Ai wanda kikaji kadanne nifa daga cemasa baya yawo sai cemin yayi wai to zai fara zuwa hotel da clubs yana hutawa" anty siyama tafada tana dariya, "Zanyi maganinsa ai, wallahi karatu zai koma nanda wani month din.." "Yaya abinda nakeso dakai tunda yaron nan ya nuna auren yake so to muyi masa saboda mu kare masa mutunci sannan mu karewa kanmu, domin indai bamu yimasa aure ba kuma yana so to fa shaidan bazai barshi ba zai ta ingizashi daga karshe azo ashiga halin da ba aso,dan haka kayi hakuri muyi masa auren tunda yanuna yanada bukatarsa kuma karatu yace zai koma amma sai anyi masa aure" hajiya tace dasu tana rikeda kumatunta, "To hajiya shikenan za ayi kamar yadda kikace amma kifa tuna shekarun yaron nan kwata kwata 28 ne kacal fa ko 30 baiyi ba" inji yaseen, "Ehh babu komai mudai yimasa shikenan mun fita hakkinsa" hajiya tabashi amsa, "To shikenan hajiya" Akan haka suka tsaya na za ayiwa amadi aure amma har lokacin yaseen bai huceba haushin amadi yakeji saboda duk barazanar da ya dade yana yimasa akan cewar babu shi babu kula yanmata amma shine sai da ya kula su. Amadi kuwa duk da bai san abinda su hajiya suka tattauna ba bayan tafiyarsa hakan bai saka yaji son auren nadiya ya ragu acikin ranshi ba shi yanzu ne ma yake jin wani shaukin sonta acikin zuciyarshi,wayarshi ya dauka ya kirata, fitowarta kenan daga wanka kamar ba zata daga ba ta daure ta dauka, "Baby nah.., ya jikin?" "Da sauki" Shiru yayi yana sauraren muryarta har yaji tayi shiru, "Yanzu me kikeyi? Uhmmm?" Sai da yafi minti miyar da tambayarta sannan tabashi amsa, "Abu nake yi?" "Menene shi? Fada min sai inzo in tayaki" Shiru tayi masa har sai da yasake maimaitawa, "daga wanka na fito zan shirya, sai anjima" "Dan Allah tsaya kiji, karki kashe dan Allah, kinga da ina kusa nine zanyi miki wankan,nine zan shiryak..." K'ittt ta kashe wayar acikin zuciyarta tana mamakinsa dama haka yake shima, afuska kamar salihi ashe ashe, shika A ne, Murmushi yayi saboda shi kansa bai san lokacin da ya soma sakin layiba. Kwana uku da tsayar da maganar yiwa amadi aure yaseen yasake tarasu yafara tambayar amadi wacece yarinyar da yake so, "Sunanta nadiya" "A ina gidansu yake?" "A rano suke" Dukkaninsu mamaki ne ya kamasu saboda sun zaci zaice a abuja sai sukaji sabanin haka, "Good, wacece ita sannan waye mahaifinta?" "Mahaifinta babban dan kasuwa ne sannan yana aiki a state government, ita kuma dalibata ce a KUT amma bazawara ce ta tab'a aure kuma tanada yara biyu" Atsorace yaseen ya kalleshi yayinda yayunshi Mata suka hau salati da sallallami, "Auta bazawara?" Hajiya tace dashi cikin mamaki, "Anty amadi bazawara fa kace, kanada hankali kuwa?",anty Dija ta fada cikin zaro ido, "Da hankalina anty, ai ba haramun bane, ni wallahi ita nakeso kuma ita zan aura" "To kuwa bazaka aureta ba koda kuwa zaka mutu, kaji yaro da shashanci, sai kace marar mafadi? Karasa wacce zaka so sai bazawara?" Yaseen yafada cikeda mamaki, "Gaskiya auta nima anan ban goyi bayanka ba, kaje ka sauya shawara saboda nima bazan goyi bayan da ka auri bazawara ba, ai sai ta rinka yi maka wayo.." Hajiya ta dora nata jawabin, "Hajiya..." "Kai tashi ka fita daga nan, tashi ka fice ko inzo inyi ball dakai.." Yaseen yafada azuciye, tashi amadi yayi ya fita hankalinsa yakai kololuwar tashi, ransa kuwa idan yayi dubu to ya b'aci..... *_Ummi Shatu_* [19/08, 7:22 p.m.] Ummy Aysha: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO.* *49* aishaummi.blogspot.com *K*o gabansa dak'yar yake gani saboda tsananin damuwa da b'acin rai, dakinsa ya shiga ya zauna zuciyarsa tana faman yimasa zugi da zafi, gaba daya yama rasa abinda zaiyi kuka ko me? Tagumi yayi jikinsa sai tsuma yake, Gaba daya babu wanda ya goyi bayan amadi ya auri bazawara har hajiya wannan karon taki bin bayansa, anty siyama kuwa cewa tayi ai ga kanwar mijinta nan zee dake mutuwar sonshi a aura masa ita kawai anan ne kuma hajiya bata bada goyon baya ba tace adai kyaleshi yasake nemowa da kanshi. Tunda amadi ya shiga daki bai fitoba su hajiya sunyi tsammanin ko fushin ne har lokacin bai huce ba ashe ba haka bane zazzabi ne mai zafi ya rufeshi dan haka babu shiri ya kwanta ya lulluba da bargo, yana nan kwance har la'asar tayi ganin bai fitoba yasa hajiya lekawa dakin nasa nan ta hangoshi kwance cikin bargo, Hankali atashe hajiya taje gaban gadon tana kiransa, "auta..!!! Auta na, meya sameka?" Jin jikinsa tayi zafi zau lokacin data yaye bargon, "Baka da lafiya shine baka fada min ba auta? Meyasa?" Kamar hajiya zatayi kuka ta fita ta kira yayunsa nan ta taho masa da abinci da magani, kamar karamin yaro haka ta sakashi agaba ta bashi ya dan ci yasha magani, wani irin ciwo kansa yake yi masa kamar zai bar gangar jikinsa. Kasancewar autane shalele kowa sai da ya nuna damuwarsa akan rashin lafiyar amadi nan aka manta da batun maganar auren da yace zaiyi amma shi abin yana nan acikin ransa, har dare yayi dukkaninsu suna dakinsa ana hira shikam yana kwance kansa akan cinyar hajiya tana shafar kansa kamar wani jariri, Lokacin da yaga kowa yafice sai iya hajiya yasamu damar yimata magana, "Yanzu hajiya kun k'wammace inje inyi zina akan ku aura min wacce nake so? Hajiya idan fa bakuyi min auren nan ba tunda ina son yarinyar nan kuma ace itama tana sona to fa shaidan zai iya ribatarmu mu aikata abinda bashi kenan ba,saboda zamu rinka ganin ai tunda baza abarmu mu mallaki junanmu ba gara mu aikata komai, amma idan har kuka amince na aureta hajiya kun taimakawa rayuwata sannan kun tamaka mata itama, kuma ni banga abin gudu a auren bazawara ba tunda annabinmu ma da ita yafara alhalin shima bai taba yin aure ba, dan Allah hajiya kiyi min wannan alfarmar a matsayinki na mahaifiya ta, ku barni na auri nadiya.." Shiru hajiya tayi na wani dan lokaci sannan ta shafi sumar kansa, "To autana kabari zan duba Nagani kasan nafi kowa sonka shiyasa bazan taba bari wani abu ya cutar dakai ba, zanyi maka istihara nagani idan har aurenka da ita alkhairi ne Allah ya tabbatar idan kuma ba alkhairi bane Allah ya sauya maka da wacce tafita alkhairi" "Yawwa hajiyata, insha Allah ma alkhairi ne.." "Allah yasa haka" Sallama hajiya tayi masa ta tashi tafita ta ja masa kofar, shiru amadi yayi yana tunanin nadiya acikin ransa, shi ko zai koma karatu to yafi son sai andaura aurensa da ita saboda gani yake muddin ya tafi bai aureta ba to kafin yadawo wani ya aure masa ita. *** Kallon asabe kabeer yayi zuciyarsa cike da jin haushinta nan ya fincike hannunta daga jikin kwalar rigarsa amma bata hakura ba sai da ta sake cakumar wuyar rigar tasa, "Sakeni.., sakeni nace ko jikinki ya fada miki yanzun nan.." Yafada cikin karaji, maimakon ta sakeshi sai jan rigar tasa tayi ta ketata nan ya rufeta da duka itama tana ramawa amma da yake karfinsa da nata ba d'aya bane yasa yayi mata lilisss, zaginsa ta hau yi tana cewa dole dai sai ya zauna da ita ko yana so ko baya so, Cikeda bakin ciki yaje ya sauya kayan jikinsa yabar gidan, kusan koda yaushe hakace take faruwa, kullum acikin fada suke ta zageshi tass shikuma ya nada mata na jaki, shi kansa idan ya zauna sai ya rasa gane wacce irin musiba ce ta sauka akansa, nadiya ce ta fado masa nan kuma yaji hankalinsa ya sake karkata agareta take zuciyarsa tafara aiyana masa wani abu... *** A b'angaren nadiya kuwa tun tana fushi akan fadan da mama tayi mata har ta hakura ta ware amma bata taba sanin cewa Abba yayi magana da amadi akanta ba, Yau da safe misalin karfe 9 amira tazo ta kirata tace taje Abba na kiranta, fita tayi daga cikin bargonta ta dauki hijab dinta ta nufi falon Abba, Yana zaune shida mama ya kammala karyawa, Zama tayi ta gaidashi, cikin fara'a ya amsa sannan ya dubeta duba irin na maganar da za ayi mai muhimmanci ce, "Nadiya wannan yaron Ahmad tun yaushe yake zuwa wurinki?" Gabanta ne ya fadi ras rass domin jikinta yafara bata cewar Abba maganar aure zaiyi mata, "Abba bamu dade tareda shi ba kuma ni wallahi bani nafada masa gidanmu ba haka kawai naganshi yazo.." "To nadiya in banda abinki ai mai sonka shi yake zuwa Inda kake,sannan agaskiya ni na yaba da nutsuwar yaron wannan dalilinne ma yasa nabashi dama domin ya turo magabatansa ayi maganar aurenku tunda kedai yanzu ba karamar yarinya bace.." Hawaye ne suka fara bin kumatun nadiya wanda takasa magana, "Kiyi hakuri nadiya nasan ke mai biyayya ce sannan mai hakuri ce akan komai, to yanzun ma wannan biyayyar taki da nasanki da ita zaki yimin ki auri wannan yaron domin nagari ne, nasan abaya kinyi mana biyayya kin auri kabeeru wanda bakiji dadin zama dashi ba to yanzu kuma insha Allah zakiji dadi ko dan biyayyar da kike yimana.." "To Abba" shine kawai abinda nadiya ta iya cewa sai ko hawaye dake faman bulbula daga idanuwanta, "Allah yayi miki albarka nadiya, Allah yasa yaranki kema suyi miki irin biyayyar da kike yimana,kiyita hakuri kinji" "To Abba" "Allah yayi albarka,shikenan tashi kije.." Tashi tayi tafita tana faman hawaye, tana zuwa daki ta zauna ta shiga kuka, kuka take sosai kamar wacce aka rafkawa mutuwa, ita bakin cikinta ma amadi fa ko ta bakinta baiji ba amma shine zai tafi wurin Abba kai tsaye kenan auren dole yakeso ayi mata ko me?? Ta dade tana rusar kuka kafin ta dauki wayarta ta tura masa text massage, _Yaushe mukayi haka dakai, yaushe nace zan aureka da har zakaje wurin Abba kace zaka turo Manyanka,ka tab'a ganin inda aka yiwa bazawara auren dole? Ni nafada maka bana sonka ka rabu dani ko dole ne auren? Nidai kasani muddin na aureka to auren dole akayi min domin ban taba jin sonka acikin raina ba..._ Ganin massage dinta yasa amadi shiga cikin mamaki domin bata taba tura masa da text massage ba, yana karantawa yaji hankalinsa yatashi nan yayita kiran wayarta amma taki dauka daga karshe ma sai ta kashe wayar gaba daya, duk da cewa bashi da lafiya yana zazzabi haka ya figi mota ya tafi rano saboda fushin nadiya agareshi babban abune ko kadan baya son fushinta, Karfe 11 nasafe ya isa kofar gidansu sai dai yau baizo da niyyar shiga cikiba domin kananan kayane ma ajikinsa ga zazzabi dake damunsa, Wayarta ya kira taki dauka domin ta bude wayar lokacin, text ya tura mata cewar yana kofar gida tayi hakuri ta fito, dama kamar wadda take jira nan ta dauki hijabi ta fita afusace domin sai ta tsattsageshi sannan zataji dadi, kofar motar ta bude ta shiga yana zaune ya dora kansa ajikin sitiyarin motar saboda wahalar da yakeji,kansa ya daga ya kalleta yasake dorashi akan sitiyarin yana kallonta, "Baby meyake faruwa ne, laifin me kuma nayi?" "Au ba kasanma abinda kayiba kenan? Yanzu kayi min adalci da har zakaje wurin Abba ka kai kanka kace zaka turo ayi maganar aurenmu bayan bani nabaka wannan damar ba? Ka taba jin nace ina sonka bare har nace zan aureka? Ni ba sonka nakeba,wancan auren ma da nayi shima ba son mijin nakeba ko ahaka zan kare a auren mazajen da bana so basa sona? Ni shikenan bazanji dadin aure ba kowanne aure da akwai matsalar da zan fuskanta?" Kallonta kawai yake yi da jajayen idanuwansa wadanda suka yi ja saboda wahalar zazzabi har lokacin kansa yana bisa sitayarin motar akwance, sai da yaji ta tsagaita daga masifar da take balbala masa sannan yayi magana cikin muryarsa mai masifar sanyi, "Allah yabaki hakuri baby, wallahi bani nakai kaina wurin Abba ba, shine ya kirani yace inturo manyana amma kiyi hakuri, sannan idan kikace wai bana sonki bakiyi min adalci ba, da ace yanzu kin san halin da nake ciki saboda ke wallahi da sai kin tausaya min" "Wanne so kake min? So ko sha'awa? Babu wani sona da kake kawai kai dai kana sone kasamu wani abu daban atare dani daga nan kuma wulakanci ya biyo baya.." Murmushi yayi ya kalleta, "sha'awa fa kikace? Haba baby idan sha'awace ke damuna ba so ba ai da sai in nemi budurwa in magance sha'awata shikenan.." "To koma dai menene bari kaji koda ace zan aureka sai munyi yarjejeniya dakai sannan sai kayi min alk'awai guda daya.." Har lokacin fuskarsa dauke take da murmushi, jijjiga mata kai yayi, "yarjejeniyar me zamuyi sannan wanne alkawari kike so inyi miki? Zanyi miki shi ko na menene mutukar atare dani abun yake". *_Ummi Shatu_*🏻 [8/21, 3:30 PM] Ummi Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_ _Fatan alkhairi ga daukacin masoya masu bibiyar labarin.._ *50* aishaummi.blogspot.com *S*ai da ta hade rai sannan tace, "Koda na amince munyi aure to ba zaka kusanceni ta karfi ba har sai da yardata da amincewata.." Duk da cewar yaji maganar tata wata iri amma sai yaji tazo masa da sauki saboda bai zaci wannan maganar zata fada ba, Shiru yayi yana nazari amma kuma zuciyarshi tana ta tausarshi ta hanyar cemishi, "Tunda kana sonta kawai ka amince da kanta zata nemeka badai mace bace ai mata akwai rauni.." Ganin yaki yayi mata magana yanata murmushi shi kadai yasata yin magana, "Kai nake jira fa kayi magana" "Ni ai na amince karki samu damuwa..." Galala tayi tana kallonsa domin koda wasa bata dauka zai amince acikin sauki ba duba da cewar shi saurayine ba taba yin auren yayiba, "Shikenan tunda ka amince amma kasani alkawari fa ka dauka.." "Nasani.." Yabata amsa, "Shikenan yayi kyau" tafada tana kokarin bude kofar motar domin fita, "Baby zan samu maganin zazzabi agidanku? Wallahi zazzabi ke damuna yanzu ma ba kiji jikina ba" "Za a iya samu bari naje na duba.." Fita tayi yabita da kallo "baby riigima" yafada acikin zuciyarsa. Paracetamol ta dauko masa sachet daya sannan taje falon abba ta dauko bottle watar guda daya marar sanyi tafito, Yana nan kamar yadda ta tafi tabarshi haka ta dawo ta sameshi,mika mishi tayi yatashi ya karba ya balli maganin guda biyu yasha yana yamutsa fuska, Sake kwanciya yayi ajikin sitiyarin, dukkaninsu sunyi shiru babu wanda yake cewa komai da haka har bacci ya dan fara daukarshi sama sama, Juyawa tayi ta kalleshi da niyyar tayi masa sallama ta koma gida amma kamar da wasa sai taga wai yayi bacci, zuba masa ido tayi tana kallonsa, hakika duk inda ake neman cikakken namiji to amadi yakai matsalar kawai ita har yanzu bata sake dashi bane gudun kar akuma sake maimaita abinda yafaru abaya. Sai da yashaki baccinsa ya more sannan ya bude idonsa bai zaci zai ganta ba amma sai yaganta zaune, "Baby yi hakuri wallahi ban ma san time din da baccin ya daukeni ba" Shiru tayi bata tanka ba dama kuma yasan ba tankawar zatayi ba, "Bari naje na tafi.." "Allah ya kiyaye hanya" tafada tareda bude kofar motar ta fita, ko akwalar rigarsa abin da tayi, tashin motarsa yayi yakara mai ya nufi gida. Kwana biyu da faruwar haka hajiya tace masa ta amince ya auri bazawara mutukar hakan zai samar masa da kwanciyar hankali duk da bata so tayi nesa dashi, Tara yayunshi hajiya tayi tace musu subar amadi ya auri nadiya kamar yadda yake so kuma itama yanzu taji auren ya kwanta mata arai, babu wanda yayi magana acikinsu saboda dama sun san hakace zata faru tunda dan gaban goshi ne. Murnar da amadi yayi kamar zaiyi me, nan yaseen yace duk da haka dai zai koma karatu, amadi bai damuba saboda yasan idan har aka aura masa nadiya angama mai wahalar ko bata tare ba. Lokacin da yayi mata waya yace manyanshi zasu zo bata yi wani murna ba shi kadaine kawai ke murna, nan ta kashe wayar ta ajiye gefe tana dan karamin tsaki, "Anty nadiya nifa ina jiye miki wani abu guda daya, karfa yanzu yaya Ahmad kawai lallabaki yake sai kunyi aure yazo ya rama duk wadannan abubuwan da kike yimasa ko kuma yabari sai kin kamu da sonshi sannan ya rama koma har yayi doubling.." Amira dake gefe tana yin sak'a da kwarashi ta fada, "Amira kenan idan har yayi min haka ko fiye da haka zan barshi ne da Allah kawai kamar yadda nabar yaya kabeer da Allah, nasan haushina kukeji kuna ganin kamar bana kyautawa Ahmad saboda abubuwan da nake yi masa, Amira shi so yanada wahalar gaske sannan duk zuciyar da ta samu kanta acikin halin da na samu kaina dole ta tsani soyayya, Amira banida wani labari mai dadi da zan bayar Wanda na tsinta acikin auren da nayi abaya, kawai dai bautar Allah nayi amma bawai samun farin cikiba.." "To amma anty nadiya ai shi yaya Ahmad yanada banbanci da yaya kabeer, halayensu ma ba iri daya bane.." "Amira kenan ke yarinya ce, to bari kiji su maza gaba daya halayensu iri dayane sunane kawai ya banbanta su.." "A'a anty nadiya ni yanzu inada kwakkwaran dalilin da Zan iya fada wanda ya banbance yaya Ahmad da yaya kabeer" "Menene shi?" "Son yanmata, yaya Ahmad bashi da kule kulen yanmata, amma shi kuwa yaya kabeer kamar na mamajo" "Shi Ahmad din waye yafada miki baya kula yanmata? Ai ni yanzu banida yakini akan namiji domin bashida tabbas" "Da yana kulawa ai da zaki sani" "Tayaya Zan sani Amira? Gidanmu daya dashi?" Dariya Amira tayi "kai anty nadiya kina bani dariya.. Amma dai ya kamata ai ki sani" "Hakane" nadiya tafada,acikin ranta kuma wani tunani takeyi. Ranar asabar da safe yayan amadi yaseen da kanin mahaifinsu da yayan hajiya sukaje gidansu nadiya domin nemawa amadi aurenta, abba baiyi doguwar magana ba yace kawai yabashi sannan iya sadaki kawai zai kawo nan da karshen wata mai Kamawa sai adaura aure duk da sunyi yarjejeniyar cewar ba yanzu zata tareba har sai yadawo daga karatunshi wanda zai tafi zuwa London, Batare da matsalar komai ba baki sukayi sallama suka tafi, tunda su yaya yaseen sukace an bashi nadiya harma an tsayar da ranar aure ya rasa inda zai saka kanshi dan farin ciki. Ita kuwa nadiya tana gida babu yabo babu fallasa, tana kwance a tsakar gida da yamma tana karatun littafin Hausa kissa ko magani yaro yayi sallama yace wai ana kiranta awaje, hijabinta ta dauka ta fita duk da bata san waye yazo ba, Gabanta ne ya yanke yafadi saboda ganin yaya kabeer da tayi domin yau bata san da wacce yazo ba.... *_Ummi Shatu_* [8/23, 12:30 PM] Ummi Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ _*NA*_ *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_ _Gaisuwar yau takice ke kad'ai STYLISH BITCH, wanna shafin tukwicine agareki together with Baby Rashid_ *51* aishaummi.blogspot.com *T*unda nadiya tafito kabeer ya zuba mata ido yana jin wani irin sonta yana yawo acikin jinin jikinsa, fatan shi daya Allah dai yasa ta amincewa bukatarsa, Yau ganinshi tayi fuska asake ba kamar wancan lokacin da yazo ba dan haka ta dan saki fuskarta babu yabo babu fallasa, "Barka da fitowa.." Taji yace da ita wanda wannan ya haifar mata da tsananin mamaki domin bata zaci maganar kirki daga gareshi ba, "Kina mamakine nadiya? Bai kamata kiyi mamaki ba saboda duba da irin matsayinki da muhimmancinki acikin rayuwata da kuma rayuwar 'yayanmu.." "Hakane" tafada tana kallonsa har lokacin fuskarta tana dauke da mamaki, "Nadiya nasake shawara, naga kamar bai daceba in rabaki da yaranki adaidai lokacin da suke bukatar kulawarki shiyasa ma nafasa karbarsu zan bar miki su amma kuma ni ina ganin yanada kyau muyiwa kanmu adalci mu koma yadda muke ada" "Ban fahimceka ba yaya kabeer.." "Yawwa, nadiya abinda nakeso dake shine ni ina ganin mai zai hana mu rufawa kanmu da yaranmu asiri muce saki biyu nayi miki mukoma muci gaba da rayuwarmu da bawa yaranmu kulawa" Wani murmushin takaici nadiya tayi sannan ta kalleshi, "Lallai yaya kabeer, wato dai so kake mu jefa kanmu acikin halaka, mukoma muci gaba da zaman zina domin ba zaman aure zamuyi ba.." "Nadiya ba nufina kenan ba, dan Allah kiyi hakuri ki amince da wannan bukatar tawa,bafa wani abu bane sabo,da yawa daga cikin ma'aurata wadanda suka samu matsala irin tamu suna yin haka su rufawa junansu asiri su koma suci gaba da rayuwarsu..." "Yaya kabeer dan Allah mubar wannan maganar domin ba mai yiyuwa bace saboda ni ahalin yanzu ma da ranar auren wani akaina.." Ido kabeer ya kwalalo take fuskarshi ta sauya ya dubeta cikin tsantsar kishi, "Yanzu nadiya kinfi son ki auri wani daban baniba, nadiya kiyi hakuri ki yarda mu maida aurenmu" "Yaya kabeer idan mun ha'inci mutane da iyayenmu mun maida aurenmu ai bamu isa mu ha'inci Allah ba domin yasan komai, sannan kuma nifa yanzu bana yimaka tsananin son da har zan aikata babban sab'o.." "Nadiya...." Yakira sunanta cikin danuwa, "Sai anjima...." Bata sake sauraronsa ba tayi tafiyarta ta shige cikin gida tana mai jin tsanar kabeer tana sake shiga cikin zuciyarta domin inbanda ma ya rainawa kansa hankali yaushe zai tunkareta da wannan maganar,babu wanda ta fadawa ko mama bata fadawa ba tabar abin aranta ita kadai. Cikin satittikan da basu wuce 2 zuwa 3 ba Amadi ya kammala komai nashi na tafiya karatun da zai koma lokacin saura sati 2 daurin aurensa da nadiya wacce har yanzu tana nan akan dokin rigimarta bata sauko ba, Duk da mahaifinta yace sadaki kawai amadi zai bayar amma hakan bai hanashi niyyar yi mata lefe ba idan taje gidanshi. Ita kuwa nadiya tana can agida tafara shirye shiryen komawa makaranta domin hutunsu yakusa yakare saura kadan,ga damun da kabeer yaketa yimata akan dole sai sun hada baki sunce saki biyu yayi mata ba ukuba takoma gidansa, Ita sam bata shirin biki takeyi ba ta shirin komawa makarantarta take, Ana saura kwana biyar daurin auren amadi yaje gidan da yamma, babu yabo babu fallasa ta karbeshi, kaya yakai mata masu aji da matsayi swiss lace da material wai ta dinka tasa ranar biki, Adakile tayi godiya ta karbi kayan ta koma gida shikuma ya shiga ya debi su fadeel ya fita dasu, mama takaiwa kayan nan mama tahau cewa, "Ohh wannan yaro ai da kokari yake duk da abba yace sadaki kawai zai kawo amma bai hakura ba har saida ya kashe kudinsa ya siyo wadannan kayan, bai san mu ba taro zamuyi ba, aure kawai za adaura babu wanda zan gayyata, nida sake yin taro kuma sai Allah yakaimu bikin Amira.." Murmushi nadiya tayi "wallahi mama nima hakan yayi min daidai dama bana son ni aji ma zan sake auren..." "Allah dai yasa ayi cikin nasara" "Amin" nadiya ta amsa tareda daukar ledar kayan tashiga daki. Tunda kwanakin bikin suka karato nadiya take jin gabanta yana faduwa Wanda ko a lokacin aurenta nafarko bataji irin haka ba, har saida ta kasa daurewa ta fadawa mama irin faduwar gaban da take ji nan mama tace mata tayita addu'a insha Allah babu komai sai alkhairi. Ranar daurin auren kuwa nadiya tana kwance bata da niyyar tashi domin dama tace babu abinda zatayi ko kunshi baza tayiba bare wani kitso, dama kuma a masallacin kofar gidan abbansu kabeer za adaura auren domin shine waliyinta,amma tunda safe mamansu kabeer da kannenshi suka zo gidan sannan umman sumaila itama tazo da sauran dangi na kusa, shiyasa gidan ya danyi mutane sai shewarsu kakeji, Duk da bata so sai da Amira tayi mata kunshi domin dama ta iya babu kalar kunshin da bata iyaba daga kan baki har zuwa ja, Lallabata mama tayi tace ta daure tayi kitson ma tunda dai abune na lokaci guda sannan gashi gidan da mutane, haka ta zauna badan taso ba Amira tayi mata kitson, shuku biyu sannan anzubo wani tagaba wanda yabada style mai kyau,fati kanwar yaya kabeer sai tsokanarta take, Wanka tayi ta shirya tasaka wani leshi golden tasa sarka da dan kunne, karfe 2:30 amadi ya kirata dama kuma amir yashigo yana guda yana cewa "ina Anty amarya take? Mun dawo daga daurin aure har andauro,sadakinki dubu 50.." Gabanta ne yasake tsananta bugu nan ta tashi tayi salla raka'a biyu tazauna tana addu'a, shikuma amadi yasha kwalliya domin komai fari yasaka, farar shadda, farin takalmi, farar hula da Agogon azurfa, sai kiranta yake awaya saboda yana son yazo yaganta amma bata dauka ba gashi a can gidansu biki akeyi sosai, yayunshi sun hada mishi dinner ta musamman a ni'ima guest palace domin tayashi murna, duk danginshi na uwa da na uba sunzo dan haka gidan acike yake da baki, Bai hakura ba yaci gaba da kiranta saboda yana son taje dinner din amma yasan dakyar idan zata amince, jin ta daga wayar yasashi maida hankali kan wayar, "Baby ina kika shigane?" "Meya faru?" "Babu komai, kawai dai naga inata kiranki ne shiru bakiyi picking ba" "Bana kusa ne" "To shikenan, alhamdulillah yau dai gashi burina ya cika nazama mijin nadiya, yanzu alfarma daya zaki yimin ki shirya za azo adaukeki saboda da akwai dinner da..." "Wacce irin dinner? Ni ai kasan bazanje ba, kaine saurayi dan haka zuwa kai yakama" Murmushi yayi "yi hakuri dan Allah ki shirya.." "Nifa babu inda zanje.." Haka yayita rarrashinta amma taki furr tace ita bazata jeba, katse wayar yayi ya kira amir yace yaturo masa da number din mama, babu bata lokaci amir ya tura masa, kiran mama amadi yayi awaya suna gaisawa yafada mata yana son zai turo adauki nadiya saboda akwai dinner din da yan uwanashi suka shirya masa, sam bai fadawa mama cewar ya kirata taki amincewa ba, Kiranta mama tayi tace in anjima lallai lallai tazama cikin shiri itada Amira za azo adaukesu zasuje dinner,da to ta amsa takoma daki tana cije lebe gamida yin kwafa saboda jin amadi yakai kararta wurin mama. K'arfe 6:30 na yamma Amira tagama cancada mata kwalliya kamar a shago kasancewar duk irin kwalliye kwalliyen nan na zamani ta iya, acikin kayan da ya kawo mata tasaka wani pink din leshi ba karamin kyau tayi ba amma fuskar nan murtuk babu fara'a ko kadan.... *_Ummi Shatu_*🏻 [8/24, 9:50 AM] Ummi Liman: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_ *52* aishaummi.blogspot.com *K*owa agidan yiwa nadiya dariya yake yi k'asa k'asa saboda yanda ta cunbure fuska ita adole an takura mata amma kuma ba karamin kyau tayiba fa, Umman sumaila ce ta shiga dakin bayan tayi alwala, "Haba'yarnan ki saki fuskarki mana irin wannan shan mur haka, dan Allah ki saki fuskarki sai kifi kyau" Sai lokacin ta dan saki fuskarta, wayarta ce ta fara kara nan taduba taga shine, "Baby Ku fita anzo daukarku,yana jiranku awaje.." Ko amsawa bata yiba tayi yunkurin katse wayar, "Karfa ki kashe min waya, saboda ban gama ba" "Ina jinka.." "Ke haka akeyi ne, sai guduna kikeyi bakya son jin koda muryata meyasa? Yanzu fa mijinki ne ba saurayi ba.." "Naji" tafada tana yatsina fuska, "To shikenan sai kunzo" Katse wayar tayi ta tashi ta fita tana kiransu Amira wadanda ke can dakin mama sunata faman shiri itada aisha kanwar kabeer domin itama tace zataje, dukkaninsu suka fito har amir da husna walida dasu fadeela ne kawai ba aje dasu ba, wata hadaddiyar jeep ce aka zo daukarsu da ita wadda ta yaya yaseen ce drivernsa ne ma yazo daukarsu, Basu san irin gudun da drivern yayi ba saboda kafin 8 sukaji su acikin kano tsilin, Adaidai wani round about drivern yayi packing saboda dama akwai wata lafiyayyiyar croutoure black agefe tayi packing tana jiransu, "Yawwa amarya ga motar da zakije can Ahmad din yana ciki nikuma zan karasa da wadannan din can wurin dinner din.." "To, Amira zo ki rakani.." Tafada kamar wadda take jin tsoro, Tare da Amira suka fita zuwa wurin motar suna karasawa amadi ya fito daga bayan motar, "Amma kunyi sauri baby, Amira ashe kema zakizo?" "Yaya Ahmad ba dole ba" "To baby ku shiga mutafi" "Yaya Ahmad ni kaga motarmu can A'isha na cikima tana jirana" Bata jira komaiba ta juya ta koma motar da aka kawosu tabar amadi da nadiya tsaye awurin, Dan kallonta yayi, ba karamin

Chapter 11 of 20