Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
15 awurinsu nan ran nadiya yabaci, Dakyar suka rabu da yanmatan nan yadawo cikin motar yana shafa sumar kanshi, "Yanmata na kiyi hakuri nasan nayi laifi amma ki yafe min kannen wani abokina ne.." Ko ci kanka bata cemasa ba saboda shiru ma amsa ce da haka suka karasa gidansu, tun da mama taji sallamar nadiya tafara yimata lale sannu da zuwa, ba karamin dadi nadiyan tajiba domin mama tana mutukar kaunarta kamar zata goyata duk lokacin data ganta, Kafin wani lokaci ancikata da kayan cima kala kala, mama sai janta take da hira tana tambayarta mutanen gidansu su mama dasu Amira, Duk kannensa sai da sukazo suka gaggaisheta bayan duk sun girmeta babu sa'anta A'isha ce ma dai zasu danyi kusan sa'anni da ita amma daga Muhammad har fati sun girme mata sosai, Kasa kasa ta kalli kabeer nan taga yamaida hankalinsa kacokan akan wayarsa wanda ko ba afada mata ba tasan chaten yake yi.... *_Ummi Shatu_* [7/14, 9:19 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* *12* ~~~Wani b'acin raine ya sake rufe nadiya amma bata bari kowa ya fahimta ba, nan ta zauna agidan har sai da sukayi sallar mangariba sannan tayiwa mama sallama cewar zata tafi tareda fito da sabulun wanka wanda ta kawowa Maman ta bata, "Ah haba nadiya harda wahala? Ai nice zan baki bake zaki baniba, haba nadiya keda ba ma'aikaciya ba bamai Sana'a ba kuma shine harda dorawa kai wahala?" Maman tafada zuciyarta cikeda murna, cikin hanzari ta shiga daki ta dauko wata leda ta bawa husna tana fadin, "To ga wannan babu yawa, agaida mama dakyau dasu Amira nagode madalla Allah yabar zumunci, Allah ya nuna mana wannan lokaci yasa ayi damu, agaida Alhaji dakyau.." Godiya nadiya tayiwa mama sannan tafita, wani abin haushi kuma tana fita taga yaya kabeer tsaye ajikin motarsa shida wata budurwa wacce bata santa ba, Kamar tasaka ihu haka nadiya taji ita sai yanzu take gane yaya kabeer, yanzu take fahimtar koshi waye, mutumne shi mai yawan kule kulen yanmata shiyasa har tafara kokarin janye zuciyarta daga gareshi domin gaskiya bazata juri wannan halayyarba, Fuskarta babu yabo babu fallasa ta karasa wurin ta bude gaban motar ta shiga tana kallonsu ta cikin glass din motar, "Shikenan zee sai munyi magana kigaida gida" Yafada tareda bude kofar motar ya shiga, "Wannan wata yarinyace acan gaba damu kadan to kwana biyu bamu haduba sai yau shine muka tsaya muka gaisa" Yace da nadiya yana kokarin tada motar, Ko kala nadiya bata furta masa ba saboda abin yana cin zuciyarta sosai, duk tulin yanmatan nan na yaya kabeer ko mata goma aka bashi damar ya aura tasan sai wasu dole sunyi saura to bare mata hudu kacal aka halasta masa, Zuciyarta kamar zata fashe dan bacin rai sukaje gida, fitowa tayi zata shiga cikin gida yayi saurin shan gabanta, "Wai nadiya dan Allah meyasa kike son sauyawa ne daga yanda nasanki zuwa wata tadaban? Meyasa kike son yiwa soyayyarmu illah? Dan Allah nadiya kidaina bata ranki akan duk wata mace da zakiga na tsaya da ita, ki dauka afadin duniyar nan babu wata mace sai ke, kisawa ranki cewar kowacce mace abayanki take, ke kadai nake gani a matsayin matar aurena dan haka ki daina damuwa kina bata ranki" "Naji.." Shine kawai abinda nadiya tafada ta gegeshi zata wuce nan yayi saurin janyota wanda har sai da tafada jikinsa batare da ta shirya ba nan ya riketa yaki sakinta, Jinta tayi cikin wani irin sabon yanayi saboda tunda take da yaya kabeer haka bata taba faruwa a tsakaninsu ba tasan dai sau mafiyan lokuta yana rike mata hannu ko yaja hancinta ko kuma yaja mata kunne amma bai taba gwada rungumeta ajikinsa ba sai yau, Jin tana neman shagala yasata yin hanzarin zamewa, "Ai nace maka na hakura ko?" "To ai gani nayi kamar ba har zuciyarki ba shiyasa" Murmushi tayi masa irin wanda zai tabbatar masa da cewar da gaske ta hakuran, nan ya karasa sakinta ta shiga gida, tun daga lokacin maganar ta wuce awurinta domin adaren ranar ma raba dare suka yi suna hira awaya. Haka komai yaci gaba da gudana batare da nadiya ta sake nunawa kabeer damuwarta ba saboda bata son yasata acikin jerin mata masu korafi da rashin hakuri, koda yaushe tana lura dashi domin tana son ganewa ko ya sauya ko kuma yana nan kamar da, Kamar da din kuwa yake babu abinda ya sauya na daga kule kulen yanmatan da yake yi, wayo tayi masa ta karbi wayarsa aro tace zata kira kawarta nan ta shige dakin mama taje ta fara duban wayar ai kuwa sai da taji kamar zuciyarta zata buga domin bacin rai saboda massages ne na yanmata, da hotunansu kaca kaca, Shi kansa kabeer sai da jikinsa yabashi cewar nadiya bincike ta tafi yimasa awaya bawai kawarta zata kiraba kamar yadda tace nan ya tashi ya tsaya yana jiran fitowarta Amma shiru sai da ta shafe fiyeda mintuna talatin adakin mama tagama duba wayarsa ciki da waje sannan ta fito, da mamakinsa sai yaga fuskarta asake babu alamun damuwa anan ya danji dama dama saboda watakil zarginsa bai zama gaskiya ba kila ba bincike tayi masa a waya ba, Bashi wayar tayi suka dan taba hira ya tafi, yana tafiya nadiya taje tasamu mama wadda ke kitchen tana tuka tuwo, tsayawa nadiya tayi abayan mama, "Mama.." "Na'am.." "Mama nafasa auren yaya kabeer" "Saboda me?" Mama ta tambayeta cikeda razani bayan ta juyo tana kallonta, "Mama haka kawai" Rufe tukunyar mama tayi ta juyo tana kallon nadiya har na tsawon wani lokaci, "Nadiya lafiyarki kalau kuwa? Anya babu abinda yake damunki?" "Mama lafiyata lau, babu abinda yake damuna, nidai kawai yanzu bana son yaya kabeer abar maganar auren nan kawai ni yanzu karatu ma nake sonyi ina gama secondary zan tafi jami'a" Tsayawa kawai mama tayi tana kallonta cikeda mamaki domin sam nadiya bata taba nuna sha'awar ta na cigaba da karatu ba sannan tun farko ita ta nace ta nuna kabeer takeso shiyasa itama Maman har ta hakura ta amince ta mara mata baya ta yadda take tayata to amma abin tambayar shine yanzu wanne abu kabeer yayi mata har take neman canja ra'ayi akansa....? *_Ummi A'isha_* [7/14, 9:19 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO.* *13* ~~~Jan hannunta mama tayi zuwa cikin dakinta suka zauna agefen gado, "Nadiya idan da wani abu ki fada min saboda bazai yiyu haka kawai babu dalilin komai ki sauya ra'ayinki akan kabeer ba bayan kuma ada babu wanda kikeso kamarsa, Idan kawayene suke zugaki to ki sani zasu kaiki ne kawai su baroki, idan kuma kuruciyace ke daukarki to kisani zaki cuci kanki wanda bazaki gane hakan ba sai nan gaba zaki fahimci cewar kin yiwa kanki illah domin Allah ya baki dama ya zabar miki miji nagari wanda ya dace dake amma kinki amincewa, Idan kuma fada kukayi dashi to ki sanar min sai nakirashi naji menene ba'asi daga karshe na daidaitaku domin daga ke har kabeer ni dayane awurina babu banbanci.." Tunda mama tafara wannan maganar nadiya tafara zubar da hawaye wanda bata san dalili ba, jin mama tayi shiru yasata yin magana cikin kuka, "Mama nidai kawai yanzu bana sonsa ne wallahi nafasa aurensa.." "Nadiya kin taba ganin anfasa aure babu dalili? Karfa ki manta yau saura watanni biyu kacal ki kammala karatunki kuma kin sani kina gamawa ko wata daya bazaki kara agidan nan ba za a aurar dake saboda kece kika nuna haka tun farko, tun da fari ke kika nuna aure kikeso idan kin gama secondary har abbanki ya ji ya kuma yarda dan haka yanzu bakida bakin da zakice kin fasa" Kukan nadiya ne ya karu, "Mama wallahi nidai nafasa auren yaya kabeer, ni bana sonsa yanzu" "Ai nadiya ko bakya son kabeer yanzu tunda ada kin soshi dole ki aureshi, idan har abbanki ma yaji wannan maganar to kisani sai ranki ya baci dan haka ina mai shawartarki da kiyi gaggawar watsi da wannan hudubar ta shaidan.." Mama na kaiwa nan ta mike tayi ficewarta saboda ita atunaninta kawaye nadiya tasamu a makaranta suke hure mata kunne dan haka tayi komawarta kitchen taci gaba da aikinta tabar nadiya nata faman kuka, Har mama tagama tuwon abba yadawo nadiya na daki tanata faman kuka, sai da abba ya tambayi mama cewar ina nadiya sannan ta tuna ashe tabarta adaki nan ta tashi taje dakin nata tana shiga ta sameta tanata kuka bata daina ba, "Ke har yanzu kukan kike yi? To kici gaba dayi karki daina". Mama tafada tareda sake fita takoma wajen abba, Tun daga nan nadiya ta sauya kwata kwata, gaba daya haushin yaya kabeer takeji idanma yazo gidan bata saurararsa har sai idan mama na wurin, ko waya yanzu ta daina yi dashi idanma ya kira bata dauka dama kuma wayar mamace ita bata da waya har yanzu, Gaba daya abinda ke faruwa Mama tasani amma har yau shi abba bai saniba shima kuma kabeer gidansu basu saniba, yayinda ita kuma nadiya tafara rubuta jarabawar fita domin har sun fara practical, Lokacin da abba yaga sun fara practical tuni yabada order din gado tun daga kasar Italy, kaya aka kawo shiryayyu kama tun daga kan gado, kujeru, dining table da sauran kayan kawata gida hatta kayan kitchen an siyo, nan hankalin nadiya ya tashi saboda ganin wadannan kayan dan haka ta saka mama agaba tana yimata kuka akan ita wallahi yanzu bata son yaya kabeer karatu zatayi, da abin ya ishi mama sai taje ta fadawa abba tace ga nadiya can tasata agaba tana yimata kuka akan wai bata son aure karatu take so, Amir abba ya tura ya kirata ta shigo idanuwanta jajur alamun tasha kuka ta koshi, "Nadiya meyake faruwane? Naji mamanki tace kinzo da sabuwar magana" "Abba ni yanzu nafasa auren yaya kabeer karatu nakeso" "Ai nadiya ko agidan mijinki zaki iya yin karatu har kikai matsayin professor dan haka kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki kinji, shi aure baya hana karatu sannan karatu baya hana aure za a iya hada duka biyun, kabeer yayanki ne ba bare bane dan haka bazai cutar dakeba" "Abba ni kawai auren ne yanzu bana so" "Nadiya kefa da kanki kika kawo min kabeer kikace shi kikeso nikuma nabashi ke tareda yimasa alkawarin aure sai yanzu kuma yaji na canja magana? Ai aure tsakaninki da kabeer babu fashi, insha Allah kina gama makaranta da sati biyu zan daura miki aure akaiki dakin mijinki kamar yanda nayi alkawari ko bayan raina kar afasa" Hawayene suka cigaba da ambaliya akan kumatun nadiya nan Abba yace tatashi tatafi, tashi tayi tafita taje taci gaba da kukanta adakinta, Tsakanin d'a da uwa sai Allah nan itama mama taji hankalinta yatashi dan haka tabi bayan nadiya, adaki ta isketa tana kuka dan haka tazauna akusa da ita ta dafata, "Nadiya kiyi shiru kinji, ki saurareni kiji abinda zan fada miki, tun farko nadiya kece kikace kabeer kikeso wanda nikuma banso hakanba saboda wasu abubuwa da na hango amma ganin hankalinki ya karkata akansa yasa na amince saboda ki samu abinda kikeso, to yanzu idan muka Mara miki baya muka hanaki auren kabeer duniyace zata zagemu, shi kansa abbanki indan har na goya miki baya zaiga laifina, zaice saboda kabeer ba dangina bane shiyasa nake kin aurenku dashi, Dan haka ki nutsu kiyi hakuri kibarwa Allah ikonsa kedai kawai kici gaba da addu'a kinji" Tashi zaune nadiya tayi tafara share hawayen fuskarta tana kallon mama...... *_Ummi Shatu_* [7/16, 7:30 AM] Ummi A'isha🏻: [7/16, 7:29 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* _Gaisuwa da babbar murya ga masoyan mijina sirrina ina gaisheku aduk inda kuke, sannan ina taya kawata Batool Mamman marubuciyar littafin al'adun wasu murnar samun karuwa da mukayi, Allah ya raya mana boy cikin addinin islama yasa yayiwa addinin Allah hidima.._ *14* ~~~Kallon mama tayi bayan ta share hawayen dake gudana akan fuskarta, sannan ta bude baki dakyar tace, "Shikenan mama naji nayarda zan auri yaya kabeer kamar yadda kukeso.." "Ai bamu mukeso ba nadiya, kece kike so bawai auren dole zamuyi miki ba, yau da ace bakece kika fito kika nuna kabeer a matsayin wanda kikeso ki aura ba to da ko yace yana sonki bazan goyi bayan abashi aurenki ba mutukar bakya sonshi, to amma BAKIN ALKALAMI ya bushe dan haka kiyi hakuri ki rungumi kaddara saboda kabeer shine mijinki..." Jijjiga kai nadiya tayi, "to mama, amma gaskiya yaya kabeer yanada wata dabi'a wacce kowacce macen kirki bazata so mijinta ya kasance haka ba, yaya kabeer shegen son kula yan matanshi yayi masa yawa baya minti biyar sai kinji mace ta kirashi nikuma abin yana bani haushi" Dafa kafadarta mama tayi tana murmushi, "Haba nadiya, yanzu dama akan wannan zaki fasa auren kabeer? Ai wannan duk abune mai sauki da zarar kunyi aure duk zai manta da wadannan yan matan suma kuma zasu daina saurararsa su daina kulashi indai sukaji cewar yayi aure, wannan ba komai bane face halayya da dabi'un matasan zamani yawanci haka suke sai kiga wani ma yatara yan mata fiyeda goma kuma kowacce yana ikirarin cewar budurwarsa ce sonta yake.." Murmushi nadiya tayi na karfin hali, itama Maman murmushi tayi ta mike tsaye amma duk maganganun nan tayi sune kawai saboda ta kwantarwa da 'yarta hankali, "Ki saki ranki kinji karki sake nuna masa damuwarki ko bacin ranki akan haka, sannan tun daga yanzu ki zama mace mai daukar mijinta a matsayin sirrinta wacce bata fallasa asirin mijinta, ki koyi rufawa miji asiri kinji, bawai komai zaka rinka fada wanda ya shafi mijinka ba, shi aure da kike ganinsa nadiya zallar hakurine acikinsa dole sai ka koyi hakuri ka ji kaki ji kagani kaki gani sannan dole sai ka zama mai kawaici da mantuwa kar kayita tara laifukan da ake yi maka mutukar zakayi haka to bazaku taba zama lafiya da abokin zamanka ba domin koda yaushe mai laifine awurinka.." "To mama" Juyawa mama tayi ta fita, tabbas maganganun mama sun saukar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali nan da nan ta nemi damuwarta ta rasa nan tafara harkokinta kamar yadda ta saba ta dauko comprehensive book dinta ta bude domin karantawa bayan taje sunci abinci da mama da kannenta, Waleeda ce ta shigo da gudu tana rikeda wayar mama a kunnenta, "Yaya kabeer ga anty nadiyan.." Karbar wayar tayi tana murmushi, "Yaya KB" "Ranki ya dade, haka akeyi kuma gaba daya sai kibi ki manta da kabeer dinki? Anya kuwa kinyiwa yayanki halacci?" "Haba yaya kabeer ni na isa, waneni da mantawa da yayana, mijina sirrina..." Yanda tayi maganar ne yasashi yin dariya, "Kajita kamar gaske alhalin kin manta dani asalima fushi kikeyi dani bayan nikuma baki sanar dani laifina ba" "Yaya kabeer kenan wannan maganar ai tawuce so karma kace zaka tadata.." Ajiyar zuciya ya saki mai mutukar karfi, "Wato nadiya nikaina ban san irin son da nake yimiki ba shiyasa da kika juya min baya gaba daya hankalina ya kasa kwanciya.." "Ayya yaya kabeer ai nace maka yawuce ko" "Nagode matata, yanzu me kike shirya mana nadangane da hidimar bikinmu?" "Yaya kabeer ai shiri yana wurinka sai yadda kace.." "A'a yadda kikace dai gimbiya.." Murmushi tayi saboda yaushe rabonta da su zauna suyi waya ta minti biyu da yaya kabeer, "Yanzun me kakeyi ne?" Kin ganni adakina na tura A'isha taje ta kawo min abinci.." "Allah sarki gwauro.." Tafada cikin tsokana, "Gwauraye dai har dake ai ko ke ba gwauruwa bace?" "Gaskiya ba ita bace.." "Nima ai ba gwauron bane tunda inada matata nadiya saura lokaci kankani ta zama mallakina nakaita gidana, nakaita dakina...." Katseshi tayi ta hanyar cewa, "To ya isa yaya kabeer basai ka lissafa ba" Dariya yayi, "shikenan tunda kin hanani fadar sirrin zuciyata.." "Ba hanaka nayi ba amma basai ka fada ba dai, yanzu kabani labarin abinda kake shirya mana na biki" Sun dade tare awaya suna tattaunawa har zuwa wani lokaci, koda gari ya waye ma shine yazo ya kaita makaranta domin ranar tanada paper, Daga nan komai yaci gaba da tafiya yadda akeso domin sun shirya yanzu maganar bikinsu kawai suka saka agaba, Kamar da yanzun ma koda yaushe kabeer yana kan hanyar zuwa gidansu nadiya, Ita kuma nadiya yanzu gaba daya kanta ya dauki zafi saboda jarabawar da takeyi gashi gida sai shirye shiryen biki ake tayi mama kullum cikin fita take tana zuwa siyayyar abubuwan da ba asiya ba, Suma gidansu kabeer din ba abarsu a bayaba wurin shirye shiryen bikin domin har sun kammala hada lefe akwatuna bakwai masu tsananin kyau da tsada, Saura paper biyu nadiya ta gama jarabawarta aka kai lefenta, sai kawai dawowa tayi daga makaranta ta tarar da kaya makota sun shiga sunata gani, Mamakine ya kamata saboda yaya kabeer ne fa ya daukota daga makaranta ya kawota gida amma shine bai fada mata ba? Ai mutane naganinta suka hau guda suna cewa "ga amarya ga amarya.." Ko takan kayan bata bi ba tawuce daki tana kokarin cire takalminta, Dakin mama taje ta dauki wayarta ta kira kabeer, "Yaya kabeer shine ko ka fada min ankawo kayan nan ko? Sai kawai zuwa gida nayi natarar mutane na kallo" "Yi hakuri mantawa nayi, haba yanmata na ai kin san dai haka kawai bazan ki fada miki ba" "Shikenan dai nagode" Katse wayar tayi tatafi taje tayi wanka ta shirya, bata samu damar ganin kayanba sai da dare yayi bayan ankaiwa abba yagani, Komai da aka saka acikin akwatinan sunyi mata domin babu na banza gaba daya masu tsadane. Haka aci gaba da shirye shirye shiryen biki, musty abokin yaya kabeer shine babban abokin ango dan haka shine akan komai, Ayanda angwayen suka tsara za agudanar da kamu da walima sai dinner aranar da aka daura aure bayan ankai amarya dakin mijinta, ita dai nadiya duk abubuwan da suka shirya bata da matsala domin yanzu bikin saura sati biyu saboda yaune zata zana jarabawarta ta karshe, Kayan taya murna sosai yaya kabeer ya hado mata su greeting card, calendar, memo, key holder, handkerchiefs da sauran kayayyaki tududu wanda har mama sai da tayi masa fada tace shi da hidimar biki take gabansa meya aikeshi wannan aiki, Aranar da su nadiya suka gama jarabawar tun daga ranar kawayenta yan class dinsu suke zuwa su rakata rabon iv card domin har yaya kabeer ya buga ya basu, Shirye shiryen da ake gudanarwa agidansu nadiya sai wanda yagani domin gaba daya angyara gidan anyi sabon fenti abba ya zubawa mama sabbin furnitures nadiya nagani ta hau dariya tana cewa, "Mama Ashe kema kin zama amaryar tunda harda sabbin kaya" "Ahh nazama kam, gani uwar amarya sannan kuma amarya.." Kullum musty ne ke kaisu rabon iv card din itada kawayenta har suka kammala nan kuma tafara sintirin zuwa gyaran jiki wurin kawata KHADIJA SIDI domin kwararriyace wurin fito da amare, Cikin kwana biyu kacal da fara gyaran jikin nadiya tayi kyau tayi sumul fatarta ta sake gyaruwa ta dawo kamar bayan kwado dan tsananin laushi da taushi.... *_Ummi Shatu_*🏻 [7/16, 7:29 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* *UMMI A'ISHA* ® *HASKE WRITERS ASSO.* *15* ~~~A daren ranar kabeer yazo gidan, ganin nadiya yayi gaba daya ta sauya masa kamanni saboda tsananin kyawun da fatar jikinta tayi, gyaran jikin ba karamin karbarta yayiba ya fito da ita sosai sai kace balarabiya, "Yan matana.. Irin wannan kyau haka, ai da ahanya na hadu dake sai kiwuce nawuce domin bazan iya ganeki ba... Wow" Murmushi nadiya tayi, "kai yaya kabeer harda su tsokana haka" Sajen dake kewaye afuskarshi ya shafa yana cigaba da kallonta tacikin hasken kwan lantarkin da ya haskesu, "Allah ba wasa ba kin sauya min gaba daya, kinyi wani irin kyau Wanda ada banma san kina dashiba sai yanzu nagani" "Ohhh yau dai yaya kabeer tsokana yakeji dan haka bari nayi shiru nabarshi yayi tsokanarsa yagama" "A'a babu wani tsokana fa" Dariya tayi ta kalleshi, "yawwa namanta ban fada makaba su zarah maina suna nemanka saboda wai hall din da kukace za ayi dinner acan ba lallai ya isa ba.." "Jama'ar taku har nawace da bazai isaba? Zai isa harma yayi saura kudai kawai ku zama ready.." "Shikenan to zamu zama ready din kamar yadda kace" Murmushi yayi ya dan matsa kusa da ita, "har kin fara kamshin amarcin ne? Naji sai wani rikitaccen kamshine yake faman tashi.." Juyawa tayi tawuce tana dariya tana fadin "yaya kabeer kaganka ko... Hmmm" Tun daga wannan ranar basu sake haduwa sunyi mintuna biyar atare ba saboda gaba daya abubuwa sunyiwa kowannensu yawa musamman ma kabeer, Tun ana saura kwana biyu biki gidansu nadiya yafara cika da yan uwa musamman ma yan uwan mama wadanda suka zo daga kura domin mama haifaffiyar garin kura ce, Aranar musty yazo yakai su nadiya kunshi da saloon, basu suka dawo gidaba sai dare lokacin har yan jere sun dawo sunata faman koda gidan da irin daular da aka ajiye aciki,ita dai nadiya najinsu batayi koda tari ba saboda dama kabeer ya nuna mata gidan awaya lokacin da yayi yayi da ita suje tagani taki sai ya dauko mata hoton gidan awayarsa yakawo mata tagani, gida kam ya tsaru babu karya kamar a turai domin gidane irin tsarin na turawa. Saura kwana daya afara shagalin biki mahaifiyar kabeer ta aikowa da nadiya wani kayataccen leshi mai tsadar gaske a dinke tace tasa ranar kamu, ita kam nadiya koda yaushe aranta tana jin cewar tayi sa'ar uwar miji mai sonta da kaunarta, Ranar kamu ba karamin kyau nadiya tayiba tafito sosai domin wani leshi ne ajikinta golden da gwaggwaro shima golden sai takalmi da jaka, Nadiya tayi kyau iya kyau nan aka kwashesu zuwa wani hall wanda acan za ayi shagalin kamun, daf da za atashi angwaye suka zo nan kabeer yakasa rufe bakinsa sai fara'a yaketa faman zabgawa yasha wani yadin boyel brown da hula sai kamshine yake tashi ajikinsa, hotuna kam da video sun shasu babu adadi har su kabeer din suka tafi nan taron ya watse kowa ya koma gidansa yayinda su nadiya da sauran dangi sukuma suka koma gida. Washe gari da misalin karfe 2 aka daura auren kabeer da nadiya akan sadaki dubu 30 kamar yanda waliyyinsa ya bayar wato mahaifin nadiya, shikuma mahainsa yayiwa nadiya walinci, ana tashi daga wurin daurin aure suka wuce wurin walimar da abokanshi suka shirya masa nan akaje aka debo su nadiya ita da kawayenta, Yau dinma nadiya ba karamin kyau tayiba cikin wani jan leshi gashi an lullube jikinta gaba daya da lifayya wadda daga ganin adon dake jikinta kasan naira tayi kuka, Wa'azi aka gudanar awurin walimar sannan akaci aka sha, ango shima ba abarshi abaya ba wurin zuba kyau domin wata lafiyayyar farar shadda yasha wadda taji dinki mai tsada, Karfe hudu aka tashi daga walimar aka maida su nadiya gida, suna zuwa gida suka tarar da har anfara harhada kayan da za akai nadiya dasu domin abba yace ana yin sallar mangariba aje akaita, Ai kuwa nadiya najin haka sai kuka nan mama tazo ta kama hannunta suka nufi falon abba, Nan suka zauna tanata gursheken kuka, "Nadiya kiyi hakuri kidaina kuka kinji domin kowacce mace hakace take faruwa da ita arayuwarta mutukar wannan ranar tazo, nidai abinda zance miki shine kiyi hakuri kibi mijinki sau da kafa kiyi masa biyayya,ki zama mace tagari mai rufa asirin mijinta, ina miki addu'ar Allah yabaki rayuwa mai dadi agidan mijinki yasa ta silarshi ki shiga aljanna, Allah yayi miki albarka" "Amin amin, sannan kuma banda kazanta nadiya, banda rashin kunya, banda biye makota ana gulma, banda tona asirin miji, duk abinda yasaki kiyi abinda ya hanaki ki hanu, Allah yayi miki albarka yabaki yaya nagari" mama ta dora bayan abba yagama, nan mama ta kamata ta maidata inda ta daukota, da kuka da komai nadiya tasamu tayi wanka ta fito ta shirya lokacin har yan daukar amarya sunzo dan haka babu bata lokaci aka fita da ita aka saka a mota aka nufi gidan mijinta da ita lokacin ba afi karfe 7 nadare ba, Suna zuwa kuma aka fara shirye shiryen tafiya dinner, angama shiryata kenan ango ya shigo cikin wani sky blue din yadi marar kauri, itama kuma dama shigar blue tayi nan suka bada kala, Sai faman murmushi yake yimata amma ita duk idonta yayi ja saboda kukan da tasha gwanin ban tausayi, hannunta ya kama suka fita yana yimata magana ahankali, "Menene yasaki kuka yanmata na? Ko kukan rabuwa dasu mamane? Kiyi hakuri kinji ai baku rabuba zaki rinka zuwar musu.." Ita nadiya dai bata yi magana ba saboda tasan tana bude bakinta to fashewa da kuka zatayi dan haka taja bakinta tayi shiru, Iya kawatuwa wurin dinner din ya kawatu yasha decoration blue colour,nan aka fara gudanar da abinda za ayi gadan gadan, Daga nadiya har kabeer sunsha ruwan nairori wasu ma masu yimusu likin ita nadiya ba saninsu tayiba kawai dai tasan gayyar kabeer ce musamman ma wasu yanmata wadanda suka daddage sunata zubar musu da ruwan nairori, Karfe 12 aka tashi daga dinner din aka kwashi mutane zuwa gida, nadiya ita da kawayenta suna motar musty shine yakaisu gida yana zuwa yace kawayen su fito zai mayar dasu gidansu nan suka yi masa caaaah wai bazasu tafiba sai anbasu kudin siyan baki, cheque din 20,000 ya rubuta musu yabasu sannan suka yarda suka hakura suka fito bayan sun gama tsokanar nadiya wacce ke lullube ta tukunkune agefen gado tana risgar kuka... *_Ummi Shatu_*🏻 [7/16, 7:29 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO.* *16* ~~~Sai da akayi kamar mintuna ishirin da tafiyarsu zarah maina tafara jiyo karar mota alamun yaya kabeer ya karaso gidan, Sake gyara mayafinta tayi ta lulluba tana sauraren shigowarsa minti kadan kuwa sai gashi ya shigo hannuwansa dauke da ledoji manya guda biyu, Ajiye ledodin yayi ya karasa wurinda take ya zauna akusa da ita yana murmushi, "Yanmata nah.." Shiru nadiya tayi takasa ko motsi ganin haka yasashi dagota zuwa jikinsa, "Kidaina kukan haka kinji? Maza tashi kije kiyi alwala kizo muyi salla" Batayi musuba ta mike taje ta shiga toilet din dake cikin dakin tayi alwala tafito tazo ta iskeshi yana jiranta nan yajasu salla sukayi sallar nafila raka'a biyu kamar yadda sunnah ta koyar, Ledodin da ya shigo dasu yajawo ya bude ya fito da gasasshiyar kaza da snacks da drinks masu mutukar sanyi, "yan matana jeki kitchen ki dauko mana flate da wuka da cups.." "Yaya kabeer ban san inda kitchen din yakeba.." Jin abinda tace yasashi murmushi ya tashi dakansa yaje ya dauko yadawo ya zauna, "Ga kaza zoki ci kinji yanmata na" Duk da cewar nadiya najin yunwa sosai amma sai taji bazata iya cin kazar ba saboda kunyarshi dan haka ta jijjiga kai cikin dashewar murya tace, "Nakoshi.." Jan kazar yayi gabansa ya zage yafara cin abarsa batare da ya sake magana ba nan nadiya ta sake jin daci aranta saboda halin ko in kular da ya nuna mata, Tana kallonsa yagama cin kazar ya dauki juice yasha ya mike, "To tashi muje ki kwanta.." Tashi tayi yabi bayanta zuwa kan lafiyayyen Italian bed din da aka kafa mata acikin dakin. *** K'arfe 8 nasafe nadiya ta farka duk jikinta sai faman yimata ciwo yake saboda gajiyar biki wacce ta hadar mata da gajiyar da yaya kabeer ya tara mata adaren jiya, Dubashi tayi amma baya cikin dakin nan ta yunkura dakyar ta sauka daga kan gadon ta shiga toilet tasamu tayi wanka ta fito in banda yunwa babu abinda takeji nan tayi salla ta shirya ta zauna tayi tagumi tana jiran dawowarsa amma shiru babu alamunsa, Ganin har karfe goma da rabi tayi bai dawoba gashi tana jin rsananin yunwa yasata tashi taje ta dauko guntun snacks din da ya bari adaren jiya tafara ci tana ci tana hawaye saboda bakin cikin rashin ganin yaya kabeer, Ita abinda yasata kuka ma shine yasan irin yanayin da yatafi ya barta aciki maimakon ya tsaya ya tarairayeta yabata kulawa ya taimaka mata ya nuna mata soyayya kamar yadda kowacce amarya take samu daga angonta washe garin ranar da aka kaita amma ita yayi tafiyarsa yabarta bata samu wannan kulawar ba, Sannan ko acikin littattafan da take karantawa tana jin irin zumudin da angwaye keyi tareda nunawa amarensu soyayya amma ita sam bata samu haka ba, da kuka tagama cin

Chapter 3 of 20