Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya barta takoma saman gado ta kwanta tana haki, "Washh, yaya kabeer wlhi kabani wahala da yawa" "Waye yasa kici abinci yayi miki over?" "Kaine.." "A'a ni karki yimin sharri.." Murmushi tayi kafin tabashi amsa wayar tayi shutdown, komawa tayi ta kwanta tana cikeda farin ciki. Kamar yadda kabeer yafada kuwa da safe sai gashi yazo lokacin ko school su nadiya basu tafiba, asalima lokacin suke shiryawa, kanta babu ko dan kwali tana cikin kitchen tana cin soyayyen dankalin da mama ke soyawa sai gashi ya shigo, ba karamin mamaki nadiya tayiba domin ta zaci wasa yake yimata da yace zaizo da sassafe ya ganta, Dan tsananin kunya kasa gaisheshi tayi tana jinshi da mama suna gaisawa daga nan yawuce ciki falon abba, Bata bari yaji fitarta zuwa makaranta ba ta zare jiki tagudu. Abangaren Mustapha kuwa ba karamin dadin labarin da mahaifinsa yazo mishi dashi yajiba musamman ma da yaji cewar ba ayiwa nadiya mijiba asalima ko tsayawa da samari bata fara yiba,wanka ya dauka ya shirya ya fito ya nufi gidansu nadiyan, Tana falon abba tana yiwa su amir homework yaro yayi sallama yace wai nadiya taje inji Mustapha, kamar bazata yi motsiba har saida taji mama tayi magana sannan ta tashi tafita zuciyarta babu dadi, Tsaye ta sameshi ya saka hannuwanshi acikin aljihu yana yimata murmushi sai dai ita ko kadan bai burgeta ba, sallama tayi masa ya amsa cikeda kulawa nan suka gaisa yafara koro mata jawabi, "Nadiya wato tun ranar farko dana soma ganinki Allah ya jarrabi zuciyata da sonki da kaunarki saboda yabawa da nayi da hankalinki da nutsuwarki,ina fata zaki bani hadin kai har nakai ga cimma burina da muradina na mallakarki..." Saida taji yayi shiru sannan tayi magana, "Yaya Mustapha nagode da soyayyar ka agareni,hakika duk Wanda yace yana sonka to ya gama yimaka komai kuma bakada kamarshi,to amma nikuma inada wanda nakeso" Cikeda mamaki ya kalleta saboda shidai mahaifinsa yace mahaifinta ya sanar dashi babu wanda yake zuwa wurinta, "Kina da wanda kikeso? Waye?" "Yaya kabeer ne abokinka" Jin abinda tace yasashi yin shiru nawasu yan lokuta kafin daga bisani ya kalleta, "Shikenan nadiya nagode da kika fada min gaskiya baki rufeni ba, kuma nayi farin ciki da jin cewa kabeer ne wanda kike so domin mutumne shi mai kyakkyawan hali da dabi'a mai kyau, Allah ya tabbatar da alkhairi" Sallama yayi mata ya tafi nan itama ta juya ta shiga cikin gida tana dauke da farin cikin cewar tagama da babin Mustapha.. *_Ummi Shatu_* [7/13, 7:02 AM] Ummi A'isha *MIJINA SIRRINA..!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* *7* aishaummi.blogspot.com ~~~Hankali kwance nadiya ta koma gida taci gaba da gudanar da harkokinta, soyayyarsu itada yaya kabeer kuwa kullum sake yin gaba take tana kara kulluwa, koda yaushe suna makale awaya suna hira, sannan kusan koda wanne lokaci yana gidan mutukar nadiyan tana nan. Tunda nadiya ta sanarwa da mustapha cewar tanada wanda take so yaji hankalinsa ya dan tashi amma idan yatuno da cewar kabeer ne wanda take so din sai yaji ranshi ya danyi fari saboda yasan kabeer zai riketa riko na gaskiya wannan dalilin ne ma yasashi sanarwa da mahaifinsa yanda suka yi da ita, shima mahaifin nasa baiyi k'asa a gwiwa ba ya kira abban nadiya ya fada masa abinda yafaru gudun kar aga musty din yadaina zuwa bayan kuma manya sun shiga, shiru abban nadiya yayi saboda shidai a iya saninshi nadiya bata da wani saurayi amma tunda yaji haka to ya zama dole ya tuntubeta da zarar ya koma gida. Kamar yadda al'adar gidan take yauma zaune suke dukkaninsu a falon abba suna kallon tashar mbc drama, rage karar volume din tv din Abba yayi yace, "Yawwa nadiya kafin na manta zo ina son magana dake.." Kusa da mama ta dan matsa tana kallon abba, "Nadiya yaron nan mustapha da yazo wurinki yace kince masa kinada wanda kikeso hakane..?" Kai ta dagawa abba, "hakane Abba" "To waye?" Abba yasake tambayarta, kamar bazata yi magana ba dan kunya ta daure tace, "Abba yaya kabeer ne" Shiru abban ya danyi fuskarsa dauke da murmushi, "To kira min kabeer din, dama yau ai naga baizo gidanba" Tashi tayi ta fita tana cikeda murna, wayar mama ta dauka ta kirashi, "Yan mata.." "Yaya kabeer albishirinka?" "Goro" yafada yana murmushi, "To kazo abba yana kiranka" "To ai baki fada min albishir din da kika yimin ba" "Idan kazo zakaji" "To gani nan zuwa" Katse wayar tayi ta koma falon abba tana jin kamar ta daka tsalle dan tsananin murna, Tana shiga falon abba ta dan saci kallon mama nan taga fuskar Maman babu walwala sosai amma dai batayi magana ba, Nan kuma taji ranta ya dan sosu saboda tasan bacin ran mama yanada alaka da maganarsu itada kabeer tunda tun jimawa Maman ke yimata gargadin cewar karta bari soyayya ta shiga tsakaninta da kabeer, Tana ta tunanin abinda zaije yazo aranta taji sallamar yaya kabeer nan tayi hanzarin jan hijabinta ta rufe fuskarta saboda kunya sai dai amma tun kafin ya karaso kamshin turarensa ya rigashi karasowa, Cikin nutsuwa yayi sallama ya shiga bayan abba ya amsa masa, nan kuma su amir sukayi kansa suka cuccukumeshi domin yasaba basu sweet duk lokacin da yazo, Yau dinma saida yabisu ya basu daya bayan daya sannan suka kyaleshi ya nemi wuri ya zauna, cikeda girmamawa ya gaisheda abba da mama, "Kabeeru dalilin da yasa kaji nace kazo shine nadiya ce tazo min da wani zance cewar kai da ita kuna son junanku hakane?" Sunkuyar da kai kabeer yayi cikeda kunya yace "hakane abba" Dan fara'a abba ya fadada cikeda jin dadi yace, "To kabeeru babu shakka naji dadin wannan labari domin hakan zai kara dankon zumunci da aminci a tsakaninmu domin nadiya yar uwarkace, sannan ni mahaifinka ne ako ina zan iya tsayawa in nema maka aure bare agidana,dan haka ni a matsayina na mahaifin nadiya nabaka ita a matsayin matar aure ko bana raye ban yadda nadiya ta auri kowanne namiji ba face kai har sai dai idan kaine ka sauya akalarka, dan haka abinda nake so dakai shine da zarar ka koma gida ka sanarda yaya cewa ga abinda mukayi dakai saboda sonake yi nadiya na gama makaranta ayi bikinku da ita batare da andauki dogon lokaci ba" Ai kabeer najin abinda Abba yace yaji kamar an yimishi bushara da gidan aljanna, nan wani dadi ya rufeshi zuciyarsa ta samu wata nutsuwa mai kayatarwa tuni yafara yiwa abba godiya, "Abba nagode madalla, Allah yasaka da alkhairi, Allah yabar zumunci abba.." "Babu komai kabeer ai duk abinda nayi maka kaina nayiwa domin kai d'anane halak malak" Saida kabeer ya sake jaddada wata godiyar sannan ya tashi ya fita, cikeda jin kunya nadiya tabi bayanshi, tana zuwa tsakar gida kuwa ta iskeshi lafe ajikin bango dama ita yake jira ya harde hannuwansa ajikin kirjinshi, Kallonshi tayi yasha gaye cikin wata rantsattsiyar purple colour din shadda galila wacce tasha dinkin buba dan haka ba karamin kyau yayiba, "Yanzu kaji albishir din da nayi maka dazu?" Tafada cikeda murmushin kunya, "Naji wannan dalilinne ma yasani shirya baki tukwici, rufe idonki" Rufe idonta tayi tana murmushi, "yaya kabeer Allah dai yasa nima chocolate din zaka bani irin wacce kabawa su amir..." Bata iya karasawa ba saboda jin lebenshi akan nata, take jikinta yafara rawa tayi gaggawar bude idonta, nan ta juya zata gudu yayi saurin rikota, "Ai abba yace yabani ke ko baya raye nine mijinki, tsananin farin cikine yasa kikaga nayi miki haka so karki fassara ni da wata manufa, ko ba komai dai kin san ni yayanki ne dan haka bazan taba cutar dakeba" Har lokacin bata iya yin magana ba saboda tsantsar kunyar da ya haddasa mata, "Yaya kabeer nidai.." Hannunta ya rike ya matsa kusa da ita tareda leka fuskarta wadda ta kawar gefe guda, "Kedai me?" "Nidai kasani jin kunya" Murmushi yayi ya mike tsaye yana kallonta zuciyarsa cikeda farin ciki... *_Ummi Shatu_* [7/13, 6:59 AM] Ummi A'isha: ® _HASKE WRITERS ASSO._ *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ _*NA*_ *_UMMI A'ISHA_* *8* aishaummi.blogspot.com ~~~ "Wai kina nufin haka zamuje gidan kina yimin wannan kunyar?" Murmushi ta danyi "wai yaya kabeer ni duk ba wannan ba yaushe zaka zo muyi hira irin wacce muka dade ba muyiba?" Daga kai yayi yana kallon sararin samaniya alamun tunani fuskarsa kuma kunshe da murmushi, "Uhmmm, ina jin zanzo a weekend saboda ranar ne banida aiki da yawa sannan kema kina gida.." "To Allah ya kaimu, yanzu dai bari nakoma ciki saboda kai naga kana cikin farin ciki.." Dakatar da ita yayi ya hanata tafiya, "Ina kuma zakije bayan akwai labarai da yawa da nake burin ji daga gareki" "Labari kuma yaya kabeer? A wannan daren?" "To da sai awanne daren?" Ya tambayeta yana murmushi, "A'a yaya kabeer karfa ka sauya min maganata zuwa wata daban" Murmushinsa ne yasake karuwa, "kaji min yarinya da wayo, wai ke waye ya koya miki wayone? Ni ban taba ganin first born mai wayo irin nakiba" Dariya tayi ta rufe fuskarta, "har nakaika wayo? Kaima fa first born dinne amma kafini wayo ma" "A'a ban fiki wayoba zadai muzo daya, musamman ma tunda zuciyoyinmu sun kasance guda daya, sannan nan bada dadewa ba zamu zama abu daya..." Dariyace ta kwace mata nan tayi baya da sauri tana dariya, "Nidai yaya kabeer natafi da wannan sai anjima.." Shima dariyar yayi ya daga hannu alamun bye bye yana cewa, "Ok bye yanmatan yaya kabeer" Har taje daf da dakin mama dariyar take, a kofar daki taga mama tsaye fuskarta babu walwala sannan da alama ita take jira, "Mama..." "Zo nadiya" Maman ta fada idonta har ya danyi ja saboda bacin rai, jiki asanyaye nadiya tabi bayanta zuwa cikin bedroom dinta domin basu tsaya a falo ba, Zama mama tayi agefen gado itama nadiyan ta zauna, Kamo hannuwan nadiya mama tayi tana kallonta, "Nadiya nasan ke yarinyace karama wacce bata gama sanin rayuwa ba, wadda hankali bai gama ratsata ba, wacce bata san rayuwar aure ba, wacce bata san irin gwagwarmayar da kowacce mace keyi agidan aurenta ba, bawai ina son rabaki da kabeer bane nadiya a'a sai dai ina son kisani shi auren zumunci yafi komai gyara zumunci idan har yayi dadi amma yafi komai b'ata zumunci mutukar baiyi dadiba shiyasa zakiga tun farko ban so soyayyarku da kabeer ba saboda kabeer dan dakinane akwai zumunci mai karfi tsakanina dashi haka iyayensa, bana son azo ayi abu ba aji dadinsa ba zumunci ya baci.." Gaba daya jikin nadiya yagama yin sanyi saboda jin abubuwan da mama ta fada dan haka take taji jikinta ya fara yar rawa, "Mama kiyi mana addu'a kawai akan Allah yasanya albarka acikin al'amarin amma ni sam bazan iya rabuwa da ya kabeer ba saboda nafara sonsa tun ban san wacece niba.." Shiru mama tayi tana kallonta batare da tace komaiba, ita akwai abinda ta dade tana hangowa wanda ita nadiya ko kadan bazata iya hangoshi ba domin akwai kuruciya atattare da ita sosai saboda gaba daya yanzu bazata wuce shekaru 15 ba aduniya dan haka yanzune tafara saninma menene rayuwar, "Shikenan nadiya tunda kin kasa fahimtata shikenan bazan hanaki abinda kikeso ba Allah ya sanya alkhairi da albarka acikin tarayyarki da kabeer" Idanuwan nadiyane suka ciko da kwalla nan tayi saurin tashi ta fita saboda sai take jin kamar yanzu ne zata tafi tabar mamanta da yan uwanta, Duk da cewar mama sunyi haka da nadiya bata iya hakura ba tashi tayi taje ta iske abba a falonsa yana zaune shida su amir da waleeda nan ta tashesu tace sutafi dakinsu suje su kwanta,bayan fitarsu ta samu wuri ta zauna kusa da abba, "Abban nadiya wata magana nake son muyi dakai amma ta fahimta, dafarko ina son ka fahimceni ka gane cewar ni bawai bana son kabeer ne ko kuma yana da wani mummunan tabo awurina ba, kawai nidai bana son maganar aurensa da nadiya ne saboda auren zuminci bashida alfanu mutukar ba ayi daceba amma idan har aka dace yayi dadi to zumunci yana sake kulluwa, Ban so lokaci daya farat daya ka amince ka bawa kabeer nadiya ba saboda gaskiya nidai auren zumunci baya daya daga cikin abinda nake son yiwa 'yayana.." Abba bai tanka ba har saida yaji tayi shiru alamun ta gama sannan yafara magana da tausasashiyar murya, "Haba hajiya bilkisu, ai kabeeru dan dakinki ne, kin sanshi kin san halinsa sannan kin san ko wanene shi tun yana yaro dan haka bakida kokwanta acikin halayyarsa, kuma insha Allah wannan auren akwai alkhairi acikinsa ba kadanba da yardar Allah sai kowa yayi alfahari dashi kedai kawai kiyi musu addu'a kuma ni ina ganin da ace mu dauki nadiya mu baiwa wani wanda bamu saniba, bamu san asalinsa ba bamu san halinsa ba bamu san ko waye shiba gara mu baiwa na gida wanda muka san tushensa muka san komai nasa.." Jijjiga kai mama tayi alamar gamsuwa da bayanin da yayi mata sai yanzu ta danji ta samu nutsuwa akan zancen, "Shikenan to Allah ya tabbatar da alkhairi" "Yawwa hajiya bilkisu addu'ar da zamuyi kenan, kinga yanzu tana aji biyar next term zata shiga aji 6 nan da wata shekarar insha Allah zamu yi bikinta mu kaita gidan mijinta, amma kafin nan ina so nayi miki albishir da cewar keda ita yar taki na biya muku saudiyya zakuje ku sauke farali sannan ku iyo addu'a akan Allah ya basu zama lafiya da zuri'a dayyaba" Murna ce ta kama mama saboda jin albishir din da abba yayi mata nan ta hau fara'a tana mai yimasa addu'ar Allah ya kara masa budi acikin harkokinsa... *_Ummi Shatu_* [7/14, 9:20 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* _Anty maijidda musa (maman twins) shafi na 9 zuwa shafi na 13 nakine ke kadai domin jin dadinki, ina mutukar ji dake anty Jidda..._ *9* aishaummi.blogspot.com ~~~Nadiya na shiga d'aki ta kifa kanta jikin gado tafara rera kuka ahankali wanda ita kanta bata san dalili ba amma dai tafi zargin cewa na fargabar rabuwa dasu mama ne, shigowar su Amira da taji ne yasata yin shiru ta tashi ta shiga toilet, sai da ta gyara fuskarta sannan ta fito lokacin harsu waleeda sun kwanta, Itama kwanciyar tayi ta dauki wayar mama dake wurinta tafara yin game, kiran yaya kabeer ne ya shigo nan ta d'aga jikinta a sanyaye, "Yaya KB ya kaje gida?" "Ni ai nayi fushi dake, wato ko ki kirani kiji yaya naje gida ko?" "Ayya haba yaya KB ai kasan dai inada niyyar kiranka kawai dai Allah ne baiyi ba" Jin yanda ta marerece murya ya sashi yin yar dariya mai dan sauti, "Dadina dake ba a kada ke a magana mutukar a wayane amma idan a filine kuma kinfi kowa shiru" "Ai kai dinne yaya kabeer kwarjini gareka, kwarjini kake yimin" "Wanne irin kwarjini kuma?" Ya tambayeta ranshi cikeda farin ciki, "Yaya kabeer in tambayeka mana" "Allah yasa nasani yanmatan yaya kabeer" Murmushi tayi ta sake makale wayar a kunnenta, "Yaya kabeer kuma idan muka yi aure shikenan bazaka rinka kawoni gidan mama kullum ba ko?" Dariya ya fara yi mata saboda jin yarinta afili, "Haba nadiya kuma idan kikace kullum zan rinka kawoki ai sai su maman ma su gaji dake" "To yaya kabeer kazo mu zauna agidan su Maman mana gaba daya basai munje gidanmu ba" "Nadiya kenan, ke karamar yarinyace baki san menene aure ba, ko kin sani?" "Nasani mana yaya kabeer" "To fada min menene aure" Shiru ta danyi tafara tunani kafin tayi magana, "Yaya kabeer aure shine idan saurayi yaga budurwa yake sonta itama take sonshi sai ayi musu aure.." "Daga nanfa?" Ya sake tambayarta, "Sai akaita gidan da ya gina mata, iyayenta su siya mata kayan daki" "Uhum daga nan kuma fa?" Dan shiru ta sakeyi sannan taci gaba, "Sai ya siyo kayan abinci ta rinka yi masa girki tana share gida tana yin wanke wanke" "Shikenan?" "Ehh" tabashi amsa tana murmushi, shima murmushin yayi, "Shikenan kin gama?" "Nagama mana" Dariya yafara yi yana dad'awa har na tsawon wani lokaci domin sai yau yagama tabbatarwa da nadiya karamar yarinya ce wadda kuruciya ke dawainiya da ita, "Ba ayi muku biology ne nadiya?" "Ana koya mana.." Shiru yayi saboda baya son yasata taji kunya shiyasa bai son fada mata kai tsaye, "To tunda baki san menene aureba nabaki assignment ki zauna ki nutsu ki gano min menene aure" "To yaya kabeer zan yi" Murmushi ya dan yimata sannan yayi mata sallama,ajiye wayar tayi tanata tunanin maganganun da sukayi da yaya kabeer yanzu, To ita yanzu tayaya zata samo wannan assignment din da yaya kabeer yace ya bata? Ta raya hakan acikin ranta, gyara kwanciyarta tayi taci gaba da tunani can sai ta tuno cewar yan ajinsu dayawa tana ganinsu suna karanta littattafan hausa sannan kuma tana yawan jinsu suna labarin aure ko labarin soyayya amma ita bata taba tsoma bakinta aciki ba amma itama daga gobe zata fara aro littattafai tana karantawa domin ganin abinda ke tattare aciki, Sati biyu da kiran da abba yayiwa kabeer mahaifin kabeer suka zo domin su tattauna da abban nadiya. *** Alhaji Bashar Usman da Alhaji Mu'az usman yan uwan junane ciki daya uwa daya uba daya suna da kanne mata guda uku wadanda yanzu haka kowaccensu tana can agidan mijinta tareda yaranta, Alh Bashar shine babba sai mai bi masa alh mu'az daga nan sai Hajiya Kubra sai haj sa'ade sai yar autarsu hajiya Maimuna, Asalinsu yan jahar kano ne cikin wata karamar hukuma wacce ake kira da Rano, anan suka taso dukkaninsu sannan har yanzu anan kowannensu yake zaune tareda iyalinsa hajiya kubra ce kadai ke zaune a karamar hukumar sumaila, shi abbansu kabeer yana zaune a tsohuwar G. R. A, shi kuma abbansu nadiya yana zaune a unguwar Rano Quarters, Alh bashar yana da 'yaya guda hudu biyu maza biyu mata, kabeer shine babba sai Fati wacce ke binsa daga nan sai Muhammad sai autarsu A'isha, Tun lokacin da aka haifi nadiya yan uwa da dangi keta tsokanar kabeer suna cewa an haifa masa mata, haka itama nadiyan koda yaushe dangi da yan uwa cikin tsokanarta suke suna kiranta da matar kabeer, tun kabeer bai dauki abun da gaskeba har yazo ya fara yarda da abinda 'yan uwa ke fadi tsakaninsa da nadiya, Ita kuwa nadiya lokacin ma bawani kwakkwaran sani ta yiwa yaya kabeer dinba amma kowa yazo gidan sai taji yana cewa "matar kabeeru" duk sanda aka tsokaneta da wannan sunan kuka take yi domin bata sanshi ba..... *_Ummi Shatu_*🏻 [7/14, 9:19 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* *10* ~~~~Lokacin da nadiya ta dan fara hankali a lokacin ne ta gane yaya kabeer sai ta tsinci kanta cikin jin kunyarsa, haka kawai take jin kunyarsa sam bata yarda suna haduwa dashi, shikuma gidansu nadiya wurin zuwansa ne koda yaushe kusan kullum sai yaje gidan tun bai fara jin son nadiya ba har yaji yafara sonta lokacin yana makarantar gaba da secondary wato jami'a, da sonta yayi karatunsa yagama yafito yazo ya kama aiki a wani kamfanin turawa dake nan cikin garin rano, A boye suke gudanar da soyayyarsu ba tare da kowa ya furtawa dan uwansa ba amma su da kansu sun yarda cewa soyayya suke yi. *** Abban su kabeer da kanshi yaje yasamu abban nadiya domin kabeer ya sanar masa yanda suka yi da abbansu nadiya, gaba daya iyayen nasu abin ba karamin dadi yayi musuba musamman ma mahaifiyar kabeer domin tana mutukar kaunar nadiya tun lokacin da aka haifeta, kullum ita kenan aiken nadiya tazo tayi mata hutu amma ko sau daya nadiya bata taba zuwaba sai dai lokaci zuwa lokaci suna zuwa agaisa itada mama dasu Amira, Tunda mahaifiyar kabeer taji maganar auren nan tarasa inda zata tsoma ranta dan dadi, nan da nan tace sai afara tanadi. Batun soyayyar nadiya da kabeer kuwa abinsu gwanin sha'awa domin suna gudanar da soyayyarsu cikin burgewa da kulawa da juna, Koda yaushe yana gidan wai zai koya mata karatu amma kuma ba karatun suke yiba soyayyarsu kawai suke yi, yanzu itama nadiyan ta tsunduma harkar karance karancen littattafan hausa dan haka tana karuwa da abubuwa da dama wadanda ada bata sansu ba. Term din da suke ciki yana karewa ta shiga SS 3 a lokacin suka tafi aikin hajji ita da mama, ba karamar tsaraba ta jibgowa yaya kabeer ba tayi masa siyayya ta burgewa mai yawan gaske musamman ma turaruka da jallabiyoyi kala kala, Ranar da zasu dawo kabeer ne yaje airport domin daukosu, tun karfe 6 yake airport din amma jirginsu bai sauka ba sai misalin karfe 9 nadare, Kallon nadiya kawai ya tsaya yi domin hakorin da tasako ba karamin kyau yayi mata ba, ganin mama nema ya hanashi magana, Nan ya daukosu suka nufi gida, lokacin da sukaje mama fita tayi tana rike da jakarta nan itama nadiya ta yunkura zata fita kabeer yayi saurin riketa, "Hajiya nadiya ina kuma zakije bamu gaisa ba?" Murmushi tayi saboda jin ya kirata da hajiya, "Inye muga hakorin Allah yayi miki kyau" Hannu tasa ta rufe bakinta tana dariya, "haba yanmata na mugani mana" Dakyar ta iya bude bakinta yagani, hannunta ya saki yana murmushi, "Kinyi kyau sosai" "Nagode yaya kabeer" Tare dashi suka shiga cikin gidan yana rikeda kayansu da ya dauko musu daga nan yayiwa mama sallama ya tafi. Tunda su nadiya suka dawo kuma kabeer yaci gaba da zuwa gidan koda wanne lokaci,itama mama yanzu ta hakura tana son auren saboda ganin irin gata da soyayyar da Maman kabeer ke nunawa nadiyan sannan dama kabeer yarone mai biyayya Nadiya taci gaba da zuwa makaranta sannan soyayyarsu da yaya kabeer na tafiya yanda ya kamata sai dai kuma yanzu nadiya ta dan fara d'ar d'ar da auren yaya kabeer saboda wani dalili, Dalilin kuwa shine ayanda ta fuskanta yaya kabeer yanada yanmata masu yawan gaske, tun abin baya damunta har yafara damunta domin akwai lokacin da suka fita dashi ita da waleeda ta rakasu zai kaita shopping lokacin da sukaje shopping din suna gab da kammalawa wata budurwa tazo anan yatafi wurinta ya barsu nadiya, tun daga irin tsaiwar da sukayi da budurwar zaka fuskanci cewar saurayi da budurwa ne baya ga haka kuma sai kwantar da murya yake yi duk da dai nadiya bata jin abinda yake fada amna tagane cewar hakuri yake bawa yarinyar, anan ya kirgo kudi ya bata yadawo wurinsu nadiya wacce tagama shakar bacin rai, Ko takansa nadiya bata bi ba taja hannun waleeda suka fita sai shine ya dauko kayan da suka siya bayan yabiya kudin, Motarshi ya bude ya saka kayan sannan su nadiya suka shiga suka zauna, baiyi magana ba itama nadiyan haka nan yaja motar suka tafi, Tana kallonsa anata kiranshi awaya yana katsewa daga baya kuma ya dauka yace zai kira anjima, Wani haushine ya cika mata ciki domin koda yaushe ahaka yake ayita kiransa awaya yana rejecting ko kuma ya dauka yace zai kira ko ba afada mata ba tasan cewa yanmata ne ke kiransa domin yaya kabeer kyakkyawan namijine mai jida kyau da kuruciya sannan ga abin hannu domin aikin da yake yi da turawa yasamu nasibi sosai acikinsa sannan gashi da ilmi wannan dalilin ne yasa yasamu karbuwa sosai ake damawa dashi har kasashen waje suke fita aiki shiyasa kowacce mace zata yi burin mallakarsa, Babu wanda yayi magana acikinsu har sukaje gida amma kafin su karasa an kirashi awaya yafi sau 30 wanda kusan duk kiran na yanmata ne, Waleeda yabawa kayan ya rike hannun nadiya tamau tayadda bazata iya kwacewa ba, sai da yaga waleeda ta fita sannan ya sawa motar lock ya kalleta.... *_Ummi Shatu_*🏻 [7/14, 9:19 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(Labarin k'auna)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* *11* ~~~D'auke kai nadiya tayi ranta fal da takaici ita yanzu jin yaya kabeer take yafara fita aranta saboda kule kulen yanmatanshi, baya minti biyar sai mace ta kirashi sannan takasa gane alakarshi da wadannan tulin yanmatan, "Yan matanah.." Muryarshi ta katse mata tunanin da takeyi, Sam kin juyawa ta kalleshi tayi maimakon hakama sai kokarin kwace hannunta da ya rike tafara yi, "Juyo mana kiji abinda zan fada miki yanmata na" Nan dinma dai sake kawar da kanta tayi bata juya ta kalleshi ba ita bakin cikin da takeyi shine yanzu saura yan watanni kadan tayi candy kuma da zarar tagama school bikinsu za ayi ita dashi to haka zaije yana yimata wadannan kule kulen yan matan sai kace wani marar aji? "Haba nadiya ta, ya kamata ki kasance mai yimin uzuri da afuwa akoda wanne lokaci, dan Allah ki saurareni kiji.." Jin ya hadata da Allah yasata juyawa ta kalleshi, "Ina jinka" "Nadiya nifa wadda kika ganni da ita ba budurwata bace kanwar abokina ce, abokin nawa ma yanzu ba a kasar nan yakeba to shine tace wai in dan taimaka mata saboda sha'anin karatu dalilin dayasa kenan kika ga na dauki kudi nabata amma tunda bakiji dadiba kiyi hakuri.." Shiru ta danyi na dan wasu sakanni tana nazari, nadiya yarinyace mai wayo da basira da kaifin kwakwalwa shi kansa ya shaida haka sannan gata da saurin gano abu shiyasa wani lokacin har tsoron yimata karya yake yi domin atake zata gane kuma tafada masa sai dai kawai yaji tace "yaya KB nagane logic din.." Dagowa tayi ta kalleshi suka hada idanu abinda bai taba faruwa ba domin tsananin kunyarsa da takeji baya barinta ta iya hada idanu dashi, "Yaya KB idan har wannan budurwar kanwar abokinka ce baka da alaka da ita meyasa zaku ware ku koma wuri daya bazaku gaisa ku tattauna agabanmu ba? Meyasa zaku rinka maganganu kasa kasa alamun bakwa son kowa yaji abinda kuke cewa ciki har dani wacce kake shirin zama MIJINA SIRRINA, ni aganina ai duk wani abu wanda ya shafeka nima ya shafeni babu boye boye a tsakaninmu.." "Hakane nadiya, amma kisani komai yana son sirri, yanzu yarinyar nan da agabanku ne bazata iya rokona kudin ba saboda bani kadai bane.." "To amma da kuka gama yaya kabeer meyasa ko gaisawa baka kawota munyi ba a matsayina na kanwarka mai shirin zama matarka sirrinka?" "Ohhh nadiya kin fiya rigima, ki yarda dani wannan yarinyar banida alaka da ita" "To naji nayarda amma masu kiranka awaya tun dazu sukuma suwaye?" Sumar kanshi ya shafa kafin yabata amsa "yan companynmu ne" "Yan campanynku ne amma shine ka gagara daukar wayar saboda ina wurin?" "Amma dai ai kinga driving nake ko" Murmushin takaici ta danyi saboda har yanzu bata yarda da abinda yafada ba, "yaya kabeer gaskiya nidai bana jin dadin wannan abinda kakeyi, idan har zaka aureni to meye naka na kule kulen yanmata? Nasan dama tunda kana da kyau da kudi yanmata dole zasu soka to amma ai wannan ba yana nuna cewar ka sakar musu fuska kayita kulasu ba.." "Wai nadiya yaushe muka fara yar haka dakene? Kodai wasu kika samu suke zugaki awaje?" "Ko kadan ba maganar zuga bace yaya kabeer maganace ta gaskiya nidai bana son wannan kula yanmatan da kakeyi" "Shikenan naji kuma zan kiyaye, shikenan?" "Shikenan, bude min zan fita" Juyo da fuskarta yayi yana murmushi, "To ai baki tabbatar min da cewa mun shirya din ba" "Mun shirya karka damu" "To sai yaushe?" "Sai da daddare idan kadawo" "To kiyi min dan murmushi nagani mana" Yanda yayi maganar ne yasata yin murmushin ba tareda ta shirya ba, nan ya bude mata kofar ta fita ta shiga gida, ko mama bata fadawa abinda ya faru ba tabar maganar aranta shi dinma da yadawo da daddare bata nuna masa ba. Kwana biyu da faruwar haka yace ta shirya zai zo ya kaita wurin mama su gaisa, nan ta shirya taci ado cikin wani swiss material blue, tasa mayafi da takalmi blue da jaka, ba karamin kyau tayi ba nan yazo suka tafi tareda su husna wadanda zasu rakata dama ka'idar gidan duk inda zataje to dasu husna take tafiya ko walida idan kuma basa nan to Amira ko amir acikinsu wani zai rakata, Yana driving suna hira har suka hau titin da zai sadasu da unguwar, suna karya kwana sukaga wasu yan mata tsaye a bakin titi su biyu sunci uwar kwalliya, har ya dan gotasu sukaji maganar daya daga cikin yan matan tana tsayar dashi, "KB, kb, kb.." Packing yayi agefen titi ya dubi nadiya, "ina zuwa 2 minutes" Bata cemasa kala ba har yafice tana ganinsu ta cikin mirror shida yan matan sai dariya sukeyi, shida yace tabashi minti biyu saida ya shafe fiyeda minti

Chapter 2 of 20