Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abban nadiya tare suka zo ganin jariran anan suke tambayar kabeer sunan da zai sawa yaran yace sunan mahaifiyarsu abban zaisa da sunan mahaifinsu wato usman da Habiba nan su abba suka yita sawa yaran albarka dasu kabeer din, Adaki yasamu nadiya ya fada mata yanda sukayi dasu abba nan itama tabada goyon baya tace sai su rinka kiran yaran da nabeel macen kuma nabeela, Shagali iya shagali kabeer yayishi awannan haihuwar, komai da nadiya ke bukata itada yaranta ya tanadar musu, ranar suna aka nadawa yara sunan Habiba da usman, A washe garin suna kuma aka tafi da nadiya gida domin mamanta ta kula da ita tunda haihuwar farice sannan yara biyu, Tunda ta koma gida ta sake samun kwanciyar hankali, yaya kabeer yana zuwa kusan kullum yana ganinsu ita da yaranta dahaka har suka yi watanni biyu agida a lokacin ne abba yace zaman ya isa haka ya kamata su koma gida nan nadiya ta hada komai nata ta shirya kabeer yazo ya dauketa suka tafi. Komawarta gidanta nan ma babu wani bacin rai ko tashin hankali zamansu suke yi da kabeer lafiya babu wata matsala, dan uwanta kamal kuma kullum cikin kiranta awaya yake yana tambayarta yanayin zamansu da kabeer kullum hakuri da nasiha yake yimata yana nuna mata cewar shi zaman aure ibadane dan haka dole akwai jarrabawa acikinsa. Kwantar da hankalinta tayi taci gaba da kulawa da yaranta har suka yi watanni a lokacinne kuma kabeer ya bijiro mata da maganar kara aure..... *_Ummi Shatu_*🏻 [7/19, 7:50 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(True life story)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* *22* ~~~Tashin hankali sosai nadiya ta shiga lokacin da taji cewar yaya kabeer zai kara aure nan kuma tabi tafara ramewa amma mamanta da yaya kamal koda yaushe cikin kwantar mata da hankali suke suna cewa ai babu komai tadaina damuwa, Cikin dan takaitaccen lokaci ya hada kaya ya kai gidansu yarinyar nan manya suka shiga ciki yaci gaba da zuwa wurinta suna soyayya, sunan yarinyar munnira tana zaune acan wata unguwa wai ita hammaga, Daurewa nadiya tayi ta kwantar da hankalinta ta yakice tunanin abin aranta ta rungumi yaranta fadeel da fadeela wanda ahalin yanzu sun soma girma, Neman aurensa yaya kabeer yasa agaba amma kuma dayake munnira ba matarsa bace sai ta kwanta rashin lafiya mai tsawo har Allah ya karbi ranta nan yabarwa gidansu kayan da ya kai mata yace bazai karba, Daga nan kuma haka rayuwa taci gaba da juyawa har yasake haduwa da wata budurwa mai suna kareemat itama kuma da gaske yake sonta bada wasaba, Koda ya sanar da nadiya hankalinta ba karamin tashi yayiba domin bata san wacce irin mace zai auro ba saboda tana tsoron sake shiga damuwa kamar lokacin baya, Neman aure dagaske yaya kabeer yake yinsa domin baya son adauki dogon lokaci ba ayiba wannan dalilinne ma yasashi tura magabatansa da wuri, Nan da nan yafara gyaran gida sannan yafara kokarin hada kayan lefe ita dai nadiya tana zaune tana ganin ikon Allah amma tayi kokarin boye masa damuwarta, Lokacin da yagama gyara gidansa tsaf sai ya hadowa nadiya kayan fadar kishiya akwatuna uku ya iyo mata cikeda kaya ya kawo, Sai da yafara kaiwa mamansa tagani nan taketa fada saboda ita sam bata son yayiwa nadiya kishiya saboda bataga laifin yarinyar ba yarinya mai hakuri da biyayya da ganin girman nagaba, Haka ya debo kayan ya kawowa nadiya tana kitchen tana aiki, "Ga kaya can nakawo miki.." Jin abinda yafada yasata ajiye aikin da take tabi bayansa zuwa falonta nan taga akwatuna masu kyau sabbi dal guda uku, duk da cewar kayan ciki masu tsadane sannan sunada mutukar kyau hakan bai hana hankalinta tashiba, Zama tayi ta bude kayan tafara gani tana jin wani irin bacin rai acikin ranta tamkar zata fashe da kuka amma sai ta daure ta boye damuwarta tafara yaken dole, "Naga kaya kam kuma sunyi sosai ubangiji Allah yasaka da alkhairi yasa ayi a sa'a" Tace dashi tana kokarin hada kayan wuri guda, "amin" yabata amsa yana dauke dasu fadeel,tun da taga kayan kuma sai ta shiga damuwa hankalinta ya tashi nan takira yaya kamal ta fada masa yayita bata hakuri, maman kabeer dinma har gida tazo ta rarrasheta tabata hakuri tace ta kwantar da hankalinta koda ace kabeer ya kara aure to bazata wulakanta ba. Hakurin tayi ta dauki dangana ta zubawa sarautar Allah ido ta zauna tana jiran ranar da zataji yace ta shirya tazo aje akai kaya amma kuma shiru daga karshe ma sai yazo yace yafasa auren, Duk da cewar lokacin da yace zaiyi aure hankalinta ya tashi to yanzunma da yace ya fasa hankalin nata ba kwanciya yayiba saboda tasan bazata taba fita awurin mutane ba za aga kamar itace take hanashi auren. Amma koda ta zauna tayi tunani cewar Allah yasan gaskiya kuma yasan zuciyarta sai kawai ta share abin yadaina damunta nan ta kwantar da hankalinta babu daukar dogon lokaci tayi kiba ta murmure, haka taci gaba da zama tana mutukar kyautatawa yaya kabeer musamman ma yanzu data samu ta yaye su nabeel dan haka ta zage damtse tana kyautatawa mijinta. Shima yaya kabeer din yanzu babu laifi ya dan sauko yana dawowa gida akan lokaci sannan yana zuwa yaci abinci da rana kuma lokaci zuwa lokaci yana kiranta awaya yaji lafiyarta ita da yara kafin ya dawo gida, Harkokinsa kuwa koda yaushe sai samuwa suke suna sake budewa domin yanzu yatara kudi wanda shi kansa bai zaci zai mallaki irinsu ba dan haka ya fada harkar business nan yafara fita kasashen waje yana shigo da kaya ko wanne iri na amfanin yau da gobe kafin wani lokacin har yaya kabeer ya zama young millionaire, Nadiya kam koda yaushe cikin kyautata masa take musamman ma yanzu da taga ya nannemi aure amma Allah bai shirya za ayiba, ita dinma yanzu tayi fes da ita tayi kyau, duk lokacin da yafita saro kaya kasar waje yana kaiwa kamar wata daya acan koma fiyeda haka shiyasa take dauko su Amira su tayata zama kafin ya dawo. Haka rayuwar taci gaba da tafiya har tsawon wani lokaci, nadiya nazaune cikin kwanciyar hankali uwar mijinta da danginsa na mutukar sonta ko kadan basa son laifinta, yaranta har sun dan tasa domin yanzu shekararsu biyu da rabi. Acikin yawace yawacen da yaya kabeer keyi na fita kasashen waje kwatsam ya hadu da wata Mata ma'aikaciyar gidan wani radio,asalinta yar garin jos ce amma saboda tsabar bariki haka tafito daga gidan iyayenta ta gina gidanta ta tare tana duniyancinta sannan tana fita waje ta ziyarci duk kasar da takeso alokacin data gadama, Ganin yaya kabeer yasata rudewa nan ta nufeshi tana kwarkwasa tana faman jujjuya jikinta, kamshin turaren da ta saka kuwa kamar zaiyi magana, Farrr tayi masa da idonta ta kalleshi tana yauki, "Sunana asabe mc..." Dagowa yaya kabeer yayi ya kalleta..... _Gaisuwa da fatan alkhairi ga dunbin masoya wannan littafin ina gaisheku aduk inda kuke._ *_Ummi Shatu_*🏻 [7/20, 6:36 AM] Ummi A'isha: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(True life story)_ *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert writers)_ _Shafi na 23 tukwicine ga yan kungiyar haske writers association, Allah yakara hazak'a da basira hadida fasaha mai albarka.._ *23* ~~~Cikin yauki da kwarkwasa gamida jan hankali asabe mc tasake magana, "Haba handsome ya naji Kayi shiru bakace komai ba? Kodai banyi maka bane? Gaskiya amma idan har kaki kulani bazan ji dadiba.." Sake kallonta kabeer yayi yana mai kallon irin shigar dake jikinta, Wani material ne mai shegen kyau gashi daga gani mai tsadane kalar light blue yasha dinkin doguwar riga wadda ta tsaru tamkar yar kanti, ta yane kanta da dan siririn mayafi fari idonta sanye cikin farin face, "Har yanzu dai banji kace komai ba.." Dan yake kabeer yayi domin shi ko kadan bai taba ganinta ba sai yau, yau dinma yanzu, "Gaskiya ka hadu, duk macen data sameka tayi saaaa'a" Yanda taja maganar daga karshe yasa kabeer zuba mata idanuwanshi yana dan miskilin murmushi, "Kema kina da kyau ai..." Yafada yana fadada murmushinsa, "Well.. Tunda har ka yaba dani mai zai hana muyi exchanging contacts so kaga sai mu rinka gaisawa.." Kabeer baiyi musuba ya bata phone number dinshi ya karbi tata daga nan suka rabu kowa ya nufi wurinda zaije, Lokacin da yagama harkokinsa zai dawo gida tsaraba ya tulowa su fadeel da nadiya kamar gaske, Ya dawo ya iskesu lafiya nan kuma yaci gaba da kula dasu, satinshi biyu da dawowa Nigeria yana office a zaune yana aiki wayarshi tasoma ringing yana dubawa yaga asabe mc ce, "Ranka yadade..." Yaji muryarta bayan ya daga wayar, "Yakike..?" "Ranka yadade kuma haka akeyi daga ranar nan ban sake jinka ba nayi jiran nayi jiran har nagaji naji bazan jureba shine nace bari ni na kiraka na gaisheka" "To nagode asabe.." "No ka rinka kirana da mc shine daidai" "To mc shikenan sai kin jini" Katse wayar yayi yana murmushi wanda bai san dalilinsa ba, Haka da yakoma gida ma da daddare sai da asabe mc ta kirashi sannan kuma ta turo masa da wani cool massage, Tun daga wannan rana take kiransa akalla takan kirashi fiyeda sau biyar arana shiyasa tun baya kiranta har shima yafara kiranta yana mayar mata da reply din text massages din da take turo masa, Tsawon watanni biyu zuwa uku suka dauka suna waya amma nadiya ko kadan bata taba saniba, wata ranar juma'a kabeer ya kira asabe mc suka gaisa anan ta kashe murya ta marerece tace, "Gaskiya handsome ya kamata nazo har garinku naganka domin wallahi ina son sake ganin kyakkyawar fuskarka.." "A'a ai bakece zakizo ba asabe nine yakamata nazo kuma insha Allah zanzo.." "Yaushe? Karfa kahanani zuwa kai kuma kaki zuwar min.." "Zanzo, kibari zan sanar dake idan natashi zuwa" "To ina cikin garin kano dai duk lokacin da zakazo ka sanar dani.." Sallama sukayi tun daga wannan lokacin kusan koda yaushe asabe bata da magana sai ta tambayar kabeer yaushe zaije wurinta, ganin tanata damunshi akan yaje yasashi shiryawa yayiwa nadiya sallama cewar zaije cikin kano amma bai sanar da ita abinda zaije yiba, Sabuwar motarshi ya dauka wacce batafi 2 weeks da zuwa ba ya tafi bayan yasha kyau da kwalliya cikin wani sky blue din yadi mai tsada, sai da ya shiga cikin garin kano sannan ya kira asabe mc ya tambayeta unguwar da take nan ta sanar dashi tareda yimasa kwatancen gidan, Cikin dan takaitaccen lokaci ya samu gidan ya karasa, gidane safe contact mai parts dayawa kusan duk kawayen asaben ne agidan kowacce da part dinta sannan idan tayi bako sai ta saukeshi anan kawai dai gidan yan barikine, Lokacin da yashiga gidan da wata farar budurwa yafara cin karo tana brush abakin barandar part dinta daga ita sai gajeren wando da yar karamar vest, nan ya dauke idonsa yana jin kamar yakoma kada yashiga amma sai dai sam yakasa komawar haka ya kutsa kai yawuce domin dakin asabe mc shine na biyun karshe, Wata budurwa yasake gani sun fito itada wani saurayinta suna kokarin rufe kofa nan ya kawar dakai yawuce zuwa sashen asabe, Sai da yayi knocking sannan ya bude kofar ya shiga nan wani rantsatten kamshin turare wanda bai taba jin irinsa ba ya bugi kofofin hancinsa..... *_Ummi Shatu_*🏻 [7/20, 6:35 AM] Ummi A'isha: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(True life story)_ *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO.* *24* ~~~Bin tsarin yanda aka kawata falon ya rinka yi da idanuwansa, falone babba wanda aka kawatashi da jajayen kujeru, komai na falon ja ne in banda kamshi mai sanyaya zuciya babu abinda ke tashi daga cikin falon, Bai kai ga karasawa cikin falon ba yajiyo muryar asabe mc tana magana ahankali, "Barka da zuwa tauraro mai haskawa, farin wata sha kallo, yaro mai tashe dan kwalisa, kyakkyawa son kowacce kin wacce ta rasa ko tasan bazata samuba..." Juyawa yayi nan ya hangota tana takowa ahankali tamkar wata dawisu, wata classic atamfa ce ajikinta koriya sharr wacce ta dinku sosai dinkin riga da skirt wadanda suka kamata mutuka sannan suka fallasar da asirin surar da Allah yayi mata, Bakace doguwa mai faffadan hips da cikar kirji, tana da kyakkyawar fuska mai dauke da dogon hanci ga manyan idanuwa, iya kyau asabe mc tana dashi kusanma tana amfani da kyawun natane tana mallakar mazan da suka yi mata ko suka burgeta, Daurin dan kwalin da tayi tamkar gwaggoro yake ya nadu sannan ya tsaru, ko mayafi bata yafaba ta nufo inda yake tana murmushin da tasan zai sace zuciyar kabeer, "Ga wurin zama.." Ta yi masa nuni da hannunta, gaba daya kabeer ya yi la'asar kallonta kawai yake fuskarshi dauke da murmushi, "Da fatan ka iso lafiya?" "Lafiya lau.." "To yagida zance ko ya iyali?" "Iyali dai ranki ya dade.." Dan dammm tayi alamun bata ni dadiba ko kuma bata zaci zataji haka daga gareshi ba amma da yake gogaggiyar yar barikice sai tayi wani shu'umin murmushi tayi farr da idonta wanda yasha eye shadow kalar atamfar jikinta tace, "Masha Allah haka nake son ji, ashe dai kai dinma cikakken mutum ne kamar yanda na tsammata, gaskiya nayi mutukar farin ciki da jin haka.." Tana maganar ne tana kokarin zama akusa dashi nan fitinannen kamshinta yakai masa ziyara, "To yakike ya aiki ya fama da jama'a?" Yace da ita yana kallonta domin agaskiya ba karamin kyau tayi ba sosai, "To ya za ayi gashi nan munata fama.." Tafada cikin muryar jan hankali, Mikewa tayi tana taku ahankali ta nufi fridge taje ta bude ta dauko masa juice na kwali da battle water ta nufoshi, "Kar nabar bako babu ruwa babu lemo.." Shidai kabeer baya magana murmushi dai kawai yake danyi yana binta da idanuwa duk inda ta wulga, Ajiye ruwan da juice din tayi agabansa sannan ta juya ta nufi kitchen tana juyawa ahankali, Yanzu kam tasan kabeer ya shiga tarkonta kamar yanda tasaba danawa sauran maza sai dai kuma ita awannan karon bata danawa kabeer tarkon da zai shiga dan kawai suyi rayuwa awajeba a'a tarkon da ta dana masa so take ta mallakeshi ta aureshi sannan kuma ta rayu dashi, Glass cup ta dauka ta koma falon tana tafe tana yin wasa da cup din ta hanyar cillashi sama ahankali tana cafewa, Daukar juice din tayi ta tsiyayawa kabeer ta mika masa nan ya karba yafara kurba yana kallonta, "To ya aikin naku?" Ya tambayeta, "Aiki muna nan munata fafatawa amma fa abun ba sauki aikin namu akwai wahala sannan gashi da hatsari.." Ayanda take yin maganar tana yintane cikin nutsuwa da sigar dauke hankalinshi, Nan ya tattara hankalinsa ya mayar gareta tafara shirya masa labari wanda dama tadade da tanadarsa dominshi, Sun jima suna tattaunawa kafin ta mike tayi masa jagora zuwa dining table inda ta shirya masa hadadden faten doya da kifi wanda yasha manja da alayyahu, dama wannan shine favorite food dinshi nan ya zauna yafara kwasa batare da tunanin komai ba ita kuwa asabe mc dama ta dade dayin bincike akansa domin hatta gidansa sai da aka kaita aka nuna mata shi taganshi shiga cikine kawai batayi ba, bayada haka duk wani motsinsa saida ta bibiya dan haka tasan abubuwa masu yawan gaske atare dashi shiyasa bazai yimata wahalar samuba, Sai da ya cinye abincin nan cikin flate yasha lemon data hada masa sannan suka bar dining table din suka koma falo nan ta dan kalleshi tana yin fari da idonta, "Yakamata muje musha ice cream kafin ka tafi.." "A'a yanzu tafiya zanje nayi kin gane amma nayi miki alkawari next time idan nadawo zamuje.." "Ok to babu damuwa.." Tafada tana langabe kai tamkar wata karamar yarinya, tashi yayi tabi bayansa ayanda take babu gyale har zuwa waje wurinda motarsa take,ciki yashiga itama ta bude gefensa ta shiga ta zauna tareda shagwabe fuska, "Sam bana son tafiyarka kabeer saboda ina girmama lokacin da duk muka kasance tare, duk lokacin da zamu kasance tare to lokacine mai tsada da muhimmanci agareni, dan Allah kar kayi nesa dani, ka daure ka amsa gayyatar zuciyata nason yin kawance tareda kasancewa da taka zuciyar.." "Karki damu bazan ki amsa gayyatar zuciyarki ba domin tuni tawa zuciyar ta dade da aminta da taki.." Wani farin cikine ya mamaye zuciyarta wanda yakasa boyuwa akan fuskarta, "Yanzu to sai yaushe zaka dawo?" "Zan dawo bada dadewa ba" "Dan Allah kar kasa zuciyata adamuwa, wallahi idan har baka dawoba zan iya makancewa domin kaine hasken idaniyata..." Murmushi kabeer yayi tareda janyo cheque dinshi ya dauki biro ya rubuta mata kudi sannan yayi signing ya mika mata, Wal tayi da idonta tareda kallonsa, "50,000 baiyi yawa ba kuwa? Anya ayi haka?" "Babu komai is just the begining.." "Wato next time na tsammaci fiyeda haka kenan? Tafada acikin ranta afili kuwa sai ta murmusa tace, "To nagode Allah yabamu ikon rikewa junanmu amana, agaida iyali.." "Zasuji" Fita tayi ta tsaya tana daga masa hannu har ya bacewa ganinta.... *_Ummi Shatu_* [7/20, 6:35 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(True life story)_ *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO.* *25* ~~~Wani irin murmushi tayi wanda ita kadai tasan ma'anarshi tareda furta, "Yaro yarone, yaro bai san wutaba sai ya taka, kabeer kenan da sannu zaka gane wacece asabe mc.." Juyawa tayi ta nufi cikin gida cikeda takunta na k'asaita. Abangaren kabeer kuwa hankalinshi kwance yake driving yana sauraron music kusan kowanne bayan 15 minutes sai asabe ta kirashi taji ya hanya, nadiya kam tana gida bata san abinda ke gudana ba amma koda taga 3 na kokarin yi kabeer bai dawoba yasa ta kirashi awaya anan yake cemata yana hanya yakusa karasowa, Tunda ya dawo yana shiga falonta taji wani irin fitinannen kamshi wanda ita dai a iya saninta yaya kabeer bashida turare mai makamancin kamshin wannan amma sai bata zargi komai aranta ba nan ta gabatar masa da abincin da tayi tuwon shinkafa miyar agushi, Jan bakinshi yayi yai shiru bai sanar da ita komai ba agameda tafiyar da yayi haka itama bata tambayeshi ba domin tasan yana yin yawan tafiye tafiye musamman ma yanzu da yafara business. Tunda kabeer yaje gidan asabe sau daya yaji tayi masifar shiga ransa sam baya samun nutsuwa har sai ya kirata yaji muryarta, nan zatabi ta kalaminceshi da zancenta na yaudara mai cikeda makirci wanda tayi masa ado da birikanci, Dolensa babu shiri yasake shiryawa ya koma cikin kano yaje yaganta nan tabi ta cikashi da kayan motsa baki sannan ga shiryayyiyar fried rice wadda taketa faman kamshi, Sai da yagama cin abincin ya koshi sannan tayiwa kawayenta waya sukazo suka gaggaisa dashi domin dama tanata basu labarin cewa tayi babban kamu tasamu wani alhajin yaro wanda kuruciya ke daukarsa dan haka ita yanzu aure zatayi, Bayan sun gama gaisawa da kawayen asaben ne kabeer yabasu kyautar dubu hamsin,domin shi yanzu dan yayi kyautar dubu hamsin ba wani abu bane, Daukar asaben yayi suka fita bayan ta shiga daki ta sake sabuwar kwalliya tareda sabuwar shiga, cikin wata sabuwar shadda ta fito pink colour dinkin riga da skirt Wanda yayi mutukar kamata ta yafa wani dan yalolon gyale sai kamshi take zubawa nan suka fita, wani babban store yafara kaita taje ta lodi kayan da take bukata irinsu man shafawa, sabulun wanka, cosmetics da sauransu nan kabeer ya biya kudin daga nan kuma suka wuce wani hadadden park, Dakyar asabe tabarshi yatafi bayan ya mayar da ita gida, Haka yaci gaba da sintiri yana zuwa gidan asabe hira ita kuma dama ta dade dayin shiri akansa nan taci gaba da dorashi awata hanya wadda shi kansa bai saniba, lokaci kadan yaji bazai iya rayuwaba sai da ita, sonta yakeji acikin zuciyarsa kamar me, Babu bata lokaci yafara shirin neman aurenta, abbanshi ya sanarwa cewar suje jos wurin iyayenta su nemo masa aure nan abba yace sai sunyi bincike tukunna saboda sauran auren ma da ya nannema abaya duk sai da akayi bincike, Abba da kansa yasa aka bincika masa wacece asabe mc nan aka fede masa daga biri har wutsiya, cikeda takaici abbanshi ya shiga gida ya tarar da mamansu tana aikin girkin tuwon dare, Akofar kitchen din ya tsaya ya dafa bango, "Kinji kuma abinda yaron nan yake son jawo mana ko?" Cikin rashin fahimta mama tafito tana cewa "wanne yaron kuma?" "Kabeeru mana, wai aure yake nema auren kuma yarasa wacce zai zabo sai yar bariki, duk yan matan garin nan basuyi masaba sai yaje ya auro wadda bata da tarbiyya, wadda tabaro gidan iyayenta ta taho yawon tazubar.." Salati mama tafara yi tana tafa hannu, "Kabeerun ne zai janyo mana wannan abin kunyar agari?" "Shi dai.., amma yanzu zan kirashi zan gargadeshi da babbar murya, wallahi wannan auren ban yarda dashiba, mutukar nine ubansa ni na haifeshi kuma yana ganina da wannan darajar to kuwa bazai auri asabe mc ba.." "Yo Alhaji ai dama maganar auren wannan yarinyar ma babu ita, ga matarsa nan yar mutunci jininsa wacce tataso cikin tarbiyya, wallahi bazai yiyuba.." Zaro waya daga cikin aljihu abbanshi yayi ya kirashi yana dagawa yaji yace, "Kai kabeeru idan kagama abinda kake kazo gida ina son ganinka" Cikeda murna yabar abinda yake yi zai fita nadiya dake kitchen tana girki sai sallama kawai yayi mata yace zaije abbanshi na kiranshi, adawo lafiya tayi masa saboda bata san abinda ke faruwa ba, cikin kwarin gwiwa ya nufi gidan iyayensa saboda duk a zatonshi andace akan maganar aurensa da asabe mc........ _Sakon fatan alkhairi ga masoyan ummi shatu masu sonta masu kaunar rubutunta akoda yaushe suna bibiyarsa..._ *_Ummi Shatu_*🏻 [7/22, 8:23 AM] Ummi A'isha🏻: [7/22, 7:43 AM] Ummi A'isha *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(True life story)_ _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ ® *HASKE WRITERS ASSO* *26* ~~~Babu b'ata lokaci yaya kabeer ya shiga motarsa ya figeta bai zame ko inaba sai gidansu duk a tunaninsa abba da mama sun amince da maganar auren da zai kara amma koda yaje sai ya tarar da sabanin haka, Mama tana ganinsa ta zabga masa wata harara wacce rabon da yaganta tayi irinta tun yana yaro karami, Zama yayi yagaishesu nan kowannensu ya amsa fuskarsa adaure, "Kabeeru maganar auren wannan yarinyar da kayi ina mai baka umarni a matsayina na mahaifinka ka janyeshi sannan ka nisanceshi har abada, ko bayan raina ban yarda ban kuma laminta ba ka auri asabe mc.." Cikeda fargaba gamida mamaki mai hadeda tashin hankali kabeer ya dago ya kalli abba saboda abinda yaji abban ya fada ba karamin sakashi acikin rudu yayiba, "Abba saboda me?... " "Saboda mune muka haifeka ba kaine ka haifemu ba dan haka yazama dole kayi mana biyya, Kabeeru ai kabani mamaki ban taba sanin cewa haka kakeba sai yanzu, ashe dama baka da hankali baka da nutsuwa? Ai kabeeru ko mutuwa mukayi bai kamata kaje ka cusa kanka acikin abinda zai dameka ba, kana zaune da matarka lafiya babu tashin hankali babu komai shine zakaje ka auro gantalalliya marar mafadi,wadda bata samu yabo ba, yarinyar da bata gaban iyayenta zaman kanta take..." Mama ta karasa maganar tana faman numfarfashi,Kafin ta dora da cewa, "To wallahi baka isa ba, ba zaka shigo mana da ita cikin zuriyarmu ba muddin mune muka kawoka duniya.." Tana rufe bakinta abba ya dora daga inda ta tsaya nan suka hadu suketa yimasa fada ta inda suke shiga ba tanan suke fitaba, In banda gumi babu abinda yake hadawa domin babu abinda yake so yanzu kamar asabe, nan su abba suka yimasa kaca kaca ya tashi ya tafi, Hankalinsa ya tashi iya tashi, amma bai bari nadiya ta ganeba haka ya daure yabar abin acikin ransa shi kadai da niyyar idan su mama sun huce zaije ya shawo Kansu. Sati daya yabasu kullum yana zuwa gidan amma bai kara tada maganar ba har sai da sati daya yacika da fadan da suka yimasa aranar yaje gidan yafara lallashin mama, "Mama dan Allah kubarni nayi auren nan, kuyi min afuwa domin kamar jihadi zanyi..." "Kai kabeeru idan baka tashi kadaina yimin maganar nanba wallahi sai naci mutuncinka" Abba ne yafito daga cikin dakinsa yana kallon kabeer din ransa abace, "Kabeeru maganar nan bata wuceba? Ai mun gama magana aure nace bazaka yishiba mutukar nine na haifeka dan haka katashi kafice karka kuskusa ka sake zuwar min da magana makamanciyar wannan, kaje ka kula da matarka yar uwarka da yayanka idan kuma kaki zan sassaba maka.." "Kayi hakuri abba.." Kabeer yafada tareda tashi ya fita, Abubuwane suka hadu suka dagula masa lissafi domin kullum asabe damunshi take akan maganar aure sannan gashi iyayensa sunki amincewa alhalin shikuma yana mutuwar sonta, Shiryawa yayi yaje wurin asabe ya sanar mata da halin da ake ciki nan ta rinka famfashi tana zugashi tana nuna masa cewar ko babu yardar iyayensa zai iya aurenta dafarko bai yarda ba amma koda tafiya tayi tafiya sai ya amince, nan yabata makudan kudi yace ta hadawa kanta lefe, A Tsakaninsu suka saka date din daurin aurensu sati uku masu zuwa, Sati ukun na cika kuwa shida abokansa suka tafi jos aka dauro masa aure da asabe mc batareda iyayensa sun saniba ita kuwa nadiya dama ko zance makamancin wannan bata taba saniba, Aranar da aka dauro auren suka dawo shida abokansa, nadiya na cikin daki ta fito daga wanka tana shiryawa ya shigo cikin gidan nan ya iske su fadeel afalo da fadeela suna wasa akan motar wasansu, Wasa ya danyi musu sannan ya shiga wurin nadiya, tana kokarin daura dan kwali kenan ya shiga nan ya zauna agefen gadonta yana kallonta, "Nadiya magana nazo muyi.." Zama taje tayi akusa dashi, "to gani" "Nadiya dan Allah ki fahimceni, karki ga laifina, ba laifina bane haka Allah ya kadararta ki dauka cewar wannan abun kaddara ne.." Gaban nadiyane yafara faduwa saboda sai ta zargi cewar ko rasuwa akayi ko kuma wani abu makamancin haka, "Yaya kabeer wai menene? Dan Allah ka gaggauta fada min.." "Nadiya na kara aure yau, an daura min aure da asabe m..." Tsaye ta mike tana kallonsa afirgice nan hankalinta ya tashi, Bakinta yana rawa ta furta, "yaya kabeer aure ka kara? Shine baka sanar dani zaka kara aureba..?" Tashi yayi ya rikota zuwa jikinsa nan ta fincike tana zubarda hawaye, ko takansa bata biba ta fita tana kuka, hijab dinta ta dauka afalo ta saka su fadeel agaba suka fice nan yabiyota yana kokarin tsayar da ita amma taki, Kafafuwansu fadeel ko takalmi babu amma haka ta tisasu agaba suka hau titi.... *_Ummi Shatu_*🏻 [7/22, 7:49 AM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA SIRRINA...!*🌹 _(True life story)_ *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* ® *HASKE WRITERS ASSO.* *27* ~~~Ko sauraron kiran da yake yimata nadiya batayiba tayi tafiyarta tareda tare adaidaita sahu nan ta shige itada yaran, da hannu take yiwa mai adaidaita sahun kwatance saboda kuka take yi har sukaje kofar gidansu kabeer, Mama tana daki tana salla su aisha nafalo sai ga nadiya na kuka, dukkaninsu rudewa sukayi saboda basu san abinda ke faruwaba gashi kuma sun ganta sai kuka take, Kafin mama ta fito har abba yashigo yana cewa, "Wacece tazo tabar dan adaidaita sahu awaje bata bashi kudinsa ba..?" "Anty nadiya ce.." A'isha tafada tana kallon nadiya cikeda tausayawa, komawa abba yayi yaje yabiya dan adaidaita sahun sannan ya dawo cikin gida, Fitowa mama tayi tana yin sallama daga sallar da takeyi ko addu'a bata zauna yiba, "Nadiya menene? Meya faru? Keda kabeerun ne?" Mama tayi mata wadannan tambayoyin cikin rudewa, Kai nadiya ta daga alamun ehh, "To meya hadaku?" "Wai aure ya kara shine sai bayan andauro auren yazo yana fada min.." Salati mama ta rafka tareda rike habarta, nan abba ya shigo cikin falon cikeda mamaki, "Kikace aure yayi? A ina?" "Abba a jos, yanzu yazo yana fada min" Kafin wani yasake magana sai ga kabeer din ya shigo afirgice, Fada abba ya rufeshi dashi tun kafin ya zauna, "Auren da muka hanaka sai da kaje kayi ko saboda baka daukemu da muhimmanci ba baka ganin mutuncinmu, to tunda ka zabi haka kaje kayi duk abinda ka gadama amma kasani yazama dole ka saki nadiya, dole ka sakar musu yarsu domin bazaka hadata da cutar hawan jiniba" "Cutar hawan jini kuma ta nawa? Ai yadade da dora mata ciwon hawan jini sai dai aguji ciwon zuciya kuma.." Mama tafada cikin fada, Cikeda bacin rai abba yasake magana cikin tsawa, "Ka saketa nace, ka sakar musu yarinyarsu tun kafin bakin cikinka ya kasheta.." Zubewa kabeer yayi akasa ya fara rokon abba, "Dan Allah abba kayi hakuri wallahi ina son nadiya, dan Allah karku raba auren nan wallahi ina sonta.." "Tashi ka fice daga gidan nan, ko bakaji? Katashi ka fita tun kafin ranka ya baci" Abba ya nuna masa hanyar fita, nan kabeer yatashi yafita nadiya kuwa inbanda kuka babu abinda takeyi, fada mama da abba

Chapter 5 of 20