Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 8
Muka sakankace ga halaka, muka yi kalmar shahada, ni dai sai na runtse idona ina jiran in ji abin da zai faru. Ban san yadda aka fara ba, sai muka ji wata irin tsawa mai karar gaske, muka ji an dauki jirginmu an yi jifa da shi, ya fada bisa dutse, ya tarwatse, ashe ba dutse ba ne, bisa bayan kifi ya fada. Dukkanmu muka dulmiya cikin teku. Ni kuwa sai na cire rigata na fara ninkaya, Allah ya koro mini da wani allo na jirginmu da ya karairaye, na kama allon nan na hau na yi kwance bisa gare shi ina tura ruwa da kafafuna, iska da rakuman ruwa na ingiza ni gaba. Da na gaji da wutsil- wutsil da kafafu sai na yi kwance bisa allon nan kamar matacce, yunwa da kishirwa suka taso mini za su halaka ni. Na rika zargin kaina da kaina a kan barin gida da na yi. Wata zuciya ta rika yi mini fada tana cewa, "kai Sindibad! Kai Matafiyi! Ai duk abin da ya same ka ba ka da kaico! Sau nawa kana cewa idan ka kubuta daga hatsari ba za ka sake fita fatauci ba? Shin ka tsare wannan alkawari kuwa. Don haka kome ya same ka yanzu ba ka da kaico!" ya ce, ina bisa allon jirgi iska da rakuman ruwa na tura ni, wata zuciya ta rika yi mini fada da cewa, duk halin da na tsinci kaina ba ni da kaico, ni na jawo. A cikin wannan hali na yi da-na-sanin da ban taba yi ba, har na ce a raina idan Allah ya kaddara na kubuta daga wannan tafiya, to, ni da sake barin gida haihata- haihata. Haka iska ta yi ta tura ni ina cikin nadama mara iyaka, na sakankance ga halaka, duk da haka bakina bai daina addu'ar neman tsira daga Ubangijin talikai ba, mai tausayin bayinsa. Na kasance cikin wannan hali tsawon kwana biyu, har Allah ya yi ikonsa, iska ta tura ni bisa wani babban tsibiri wanda yake cike da itatuwa da koramu. Na rarrafa na shiga cikin wannan tsibiri, na tsinci 'ya'yan itacen da suka zubo kasa na ci, na sha ruwa daga wata korama, na jingina jikina ga bayan wata bishiya har hankalina ya dawo jikina. Da na ji na fara samun kaina sai na yi godiya ga Allah da ya kubutar da ni daga dulmiyewa cikin teku. Na ce a cikin raina, "yayin da bawa ya debe kauna daga rayuwa, sai ka ga taimakon Ubangiji ya zo masa ta inda ba ya tsammani. Wanda duk ya kai kukansa ga Allah ba ya tabewa. Hakika wanda ya jefa kansa cikin wahala da gangan, to ba shi da kaico." Na tashi ina zagayawa cikin tsibirin, ban gushe ba har na iso ga wata babbar korama wadda ruwanta ke gudu cikin sauri. Yayin da na ga wannan korama na gudu sai na tuna da kwale- kwalen da na taba yi na bi ruwan wata korama har ya kai ni ga tsibirin mutane. Na tsaya ina tunani, daga nan sai na yanke shawara a cikin raina, babu makawa in aikata kamar yadda na aikata a baya, watau in sana'anta dan kwale- kwalen da zan bi ruwan wannan korama, yalla in iske inda mutane suke, idan kuma na mutu, to, shi ke nan, haka Allah ya so. Na yi rantsuwa cikin raina, idan dai har na koma gidana lafiya daga wannan tafiya, to, ba zan sake fitowa zuwa ga fatauci ba. Na zabura, na himmatu ga tattara dogayen sandunan itace da kirare, na tara masu yawa. Na debi ciyawa na tufka iggwai. Na daura dan gado mai girma da tsayi kamar kwale-kwale, na yi guzurin 'ya'yan itace saboda abinci, na jefa dan gadon nan bisa ga korama, na shiga ina cewa, mai rabon ganin badi sai ya gani. Na yi ta tafiya cikin korama, ruwanta yana tura jirgina gaba, na tafi a cikin rana ta farko da ta biyu da ta uku har na fita daga cikin tsibirin, na rika cin 'ya'yan itacen da na yi guzuri ina sha daga ruwan koramar. A cikin kwana na hudu sai na ga koramar nan ta nufi karkashin wani dutse mai girma, da na ga haka sai hankalina ya tashi, na tuna irin wahalar da na sha a baya. Na ce a raina, idan na kubuta daga waccan tafiyar ta baya, to, yanzu fa? Ai ba kullum ake kwana a gado ba. Na yi nufin in sauka daga kan gadon nan kafin ya shiga karkashin dutse da ni, amma saboda karfin gudun ruwan koramar ban sami damar yin haka ba. Ruwa ya ja ni sai cikin karkashin dutse. Na buga sallallami, "babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki." Sai dai ba kamar yadda na zata ba, ban yi wata tafiya mai nisa ba cikin kogon dutsen sai na ga na fita a bayansa, haske sararin samaniya ya bayyana gare ni. Da na duba gabana inda ruwan nan ke tafiya sai na ga yana fadawa cikin wani katon rami ne, na ji karar saukar ruwa a kasan ramin kamar karar aradu. Na yi iyakar kokarina domin karkata jirgina daga fadawa wannan rami, amma ina. Da na ga dai babu makawa sai na shiga wannan rami, sai na rike jirgin nan gam da hannuwana don kada ya watsar da ni yayin da nake sullatawa cikin ramin. Ruwa ya tafi da ni na auka cikin ramin kwantsam! Allah ya kare ni ban fada bisa dutse ba. Ban gushe ba kwale- kwale yana tafiya da ni har guzurina ya kare, yunwa ta taso mini, ga gajiya da rashin barci. Na yi kwance bisa dan kwale-kwalen ina jiran mutuwata. Can sai ga ni a gefen wani babban birni. Gine-ginen birnin abin ban sha'awa, ga mutane da yawa ko'ina suna ta harkokin gabansu. Yayin da mutane suka gan ni cikin wannan hali sai suka yi tsammani koramar nan ciyo ni ta yi, suka jeho mini igiya domin in kama su fitar da ni, ni kuwa lokacin ba ni da sauran kuzari a jikina. Da suka ga haka sai suka jeho raga ta nannade ni duk da kwale-kwalena suka jawo ni waje bakin gaba. Na fadi gabansu sharaf kamar matacce, babu sauran karfi a jikina saboda yunwa da gajiya da rashin barci. Mutane suka zagaye ni suna kallo, daga nan sai wani dattijo mai kamala ya keto daga cikin taron mutane, ya saka mini riga, ya dauke ni ya tafi da ni gidan wanka, ya sa aka wanke ni fes, aka sanya mini tufafi masu kyau, aka feshe ni da turare mai kanshi. Dattijon nan ya ja ni zuwa gidansa. Mutanen gidan suka yi murna da zuwana kamar wani dansu ne ya dawo daga tafiya. Suka zaunar da ni bisa abin zama suka kawo mini abinci mai rai da lafiya, na zauna na ci na koshi, na sha abin sha, tatacce mai kyau. Kuyangi suka kawo mini ruwan dumi na wanke hannuwana, suka kawo mini adiko mai taushi na goge hannuwana da bakina. Na gode wa Allah madaukakin Sarki wanda ya kubutar da ni daga halaka. Dattijon nan ya kai ni ga wani daki inda zan rika kwana, ya sa bayi da kuyangi su rika yi mini hidima. Na kasance cikin kulawar dattijo tsawon kwana uku, in ci mai kyau, in sha mai kyau. A cikin kwana ukun nan karfina ya komo jikana, hankalina ya kwanta. A cikin kwana na hudu dattijo ya zo wurina ya zauna, bayan mun gaisa sai na ji ya ce mini, "hakika ka wadatar da mu da zuwanka, mun amfana daga arzikinka. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kubutar da kai daga halaka. Ya dana, shin yanzu hankalinka ya kwanta mu tafi kasuwa ka sayar da hajjarka? Yalla ka yi amfani da kudin domin yin guzuri idan za ka koma gida." Na yi shiru ina kallon dattijo. Na ce a cikin raina, "wace hajja ke gare ni wadda wannan dattijo ke magana? Ni ba ni da wata hajja a wannan birni." Dattijo ya ce, "kada ka damu, idan kana tunanin ba za a sayi kayanka da daraja ba, to ni zan ajiye maka su a cikin taskata har zuwa lokacin da aka sami mai sayen su da daraja." Da na ga dai kamar dattijo na yi mini wasa da hankali sai na ce a cikin raina, "bari in bi shi zuwa kasuwa in ga hajjar da yake cewa wai tawa ce." Na dube shi cikin ladabi na ce, "ya baffana, na yarda da abin da ka ce. Mu tafi wurin kayan nawa." Dattijo ya ja ni zuwa kasuwa, muna isa wajen dillalai sai na ga daya daga cikin su ya sa tarin sanduna da kiraren itacen kwale-kwalena a gaba, ga masu saye sun zagaye shi. Ashe sandunan nan duka na itacen sandal ne. Tajirai suka zagaye dillali suna sayen itatuwa, idan wannan ya saye sai wani ya yi kari, wani ma ya yi kari bisa ga na biyu. Haka suka yi ta kara kudi har aka sayi itatuwan dinari dubu. Daga nan sai dattijo ya ja ni gefe ya ce, "ya dana, wannan shi ne tamanin kayanka a cikin wannan lokaci na rashin kudi, idan ka sallama a karbi awalaja, idan kuma ba ka sallama ba in dauke su in ajiye maka a cikin taskata har zuwa gaba lokacin da suka kara kudi." Na kalli dattijo cikin girmamawa na ce, "ya baffana, na bar maka wuka da nama a cikin wannan sha'ani, duk abin da ka zartar daidai ne." Dattijo ya ce mini, "za ka sayar mini da su dinari dari, kari bisa ga abin da aka saya?" Na ce na sallama masa. Ya sa bayinsa suka kwashi itatuwa suka kai taskarsa suka kulle, ya ja ni muka koma gidansa. Ya jawo wani sunduki nasa da yake ajiyar kudi, ya kirgo dinari dubu da dari daya ya sa mini a cikin jaka, ya saka jakar a cikin wata 'yar karamar taska ya kulle da kwado, ya ba ni dan mabudin. Bayan kamar kwana biyu da haka, rannan muna hira da dattijo sai ya kada baki ya ce mini, "ni kuwa ina da wata bukata da nake so in nema gare ka, ban sani ba ko zan samu?" Na ce, "subhanalillihi, yanzu har akwai wata bukatar da za ka nema a wurina in ki yi maka ita. Me cece wannan bukata?" Dattijo ya ce, "ya dana, ka ga dai ni tsoho ne, ba ni da da namiji sai mace. Ina so idan ka yarda in hada ka aure da 'yar nan tawa, sai ka zauna tare da ni a matsayin dana, ka rika lura da dukkan harkokin kasuwancina da dukiyata duka." Na yi shiru cike da kunya, na kasa amsa wa dattijon nan magana tasa. Da ya ga ban ce komai ba, sai soshe-soshen kai nake yi kamar mara gaskiya, sai ya ce mini, "ba tilasta maka zan yi a kan wannan magana ba. Amma idan ka yarda yau din nan sai a daura aure, matarka ta tare. Kuma kada ka dauka yin auren zai hana ka komawa kasarku. Duk lokacin da ka ga damar komawa gida babu mai rike ka." "Na rantse da Allah ya kai baffana, " na fada kaina a sunkuye, "na dauke ka tamkar mahaifina a wannan gari. Kai ne uwata kai ne ubana, don haka duk abin da ka zartar a kaina na amince da shi." Nan take sai dattijo ya aika bayinsa aka kira alkalai da shaidu, ba tare da bata lokaci ba aka daura mini aure da 'yar dattijon nan, aka kwana uku ana biki. A kwana na hudu na shiga dakin amarya, na tarar da ita kyakkyawar gaske, ta sha tufafi na alfarma da aka layyace da zinariya da azurfa da sauran kayan jauhari iri-iri. Haka kuma dukkan sarkoki da awarwaro da 'yan kunnen da ta sanya na jauhari ne mai tamanin gaske, wanda sai manyan tajirai za su iya sayen su. Na zauna tare da matata, ina son ta tana so na. Ba mu gushe ba tare da 'yar dattijo har mutuwa ta zo wa dattijo. Aka yi masa wanka aka yi masa sutura aka kai shi gidansa na gaskiya. Daga nan sai duk dukiyarsa ta komo hannuna, na zama ni ne mai iko da bayi da kuyanginsa duka. Tajirai kuma suka hadu suka nada ni Sarkin kasuwa, da ma dattijon shi ne Sarkin kasuwarsu, na zauna a matsayinsa. Na yi sabo da mutanen wannan birni kwarai da gaske, na yi abokai attajirai masu yawa. A zamana cikin wannan birni, na lura da mutanen cikinsa na da wata tabi'a. Tabi'ar kuwa ita ce, farkon kowane wata sai fuskokin wasu daga cikin mazan garin duk su canza, su koma irin na tsuntsaye. Sai kuma su daura wasu irin manya- manyan fika-fikai su tashi sama, su haye bisa wani dogon tsauni da ke bayan gari. Ko me suke yi a saman tsaunin? Oho! Rannan da naga sabon wata ya kusa kamawa sai na ce a cikin raina, "bari in tambayi wani daga cikin mazan garin nan masu irin wannan al'ada ya tafi da ni inda suke zuwa." DAGA Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ20 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO Rannan da naga sabon wata ya kusa kamawa sai na ce a cikin raina, "bari in tambayi wani daga cikin mazan garin nan masu irin wannan al'ada ya tafi da ni inda suke zuwa." Yayin da farkon sabon wata ya kama, mazan nan suka canza kama, suka koma siffar tsuntsaye. Na tafi ga wani abokina na ce, "don Allah ka tafi da ni inda kuke zuwa ni ma na bude idona, idan kun tashi dawowa sai mu dawo tare." Ya ce mini abu ne da ba zai yiwu ba. Na yi ta rarrashin sa ina yi masa magiya har dai ya yarda da bukatata. Na tafi gidana na kimtsa na fito, ban fada wa kowa inda zan tafi ba. Na je wurin abokin nan nawa, ya ce in hau bayansa. Na hau bisa bayansa, ya fiffika da ni sama cikin sararin samaniya. Bai gushe ba yana tashi da ni har sai da na yi tsammani ko za mu keta rufin samaniya ne mu shiga ciki, domin sai da na rika jiyo wasu muryoyi suna tsarkake sunan Ubangiji. Lokacin da na jiyo muryoyin nan sai na amsa musu, "tsarki ya tabbata ga Allah, Ubangijin talikkai." Ai ina ambaton sunan 'Allah' sai aka jeho mu da wata irin wuta. Mutanen nan da suke cikin siffar tsuntsaye suka yi kasa da sauri, suka kauce wa wannan wuta, duk da haka sai da wasu daga cikin su suka kone suka zama toka. Wadanda suka tsira sai suka yi ta zagina suna la'anta ta. Suka jefar da ni bisa wani dutse mai girma suka tafi cike da fushin abin da na aikata, suka bar ni bisa wannan dutse da babu kowa. Na zargi kaina da kaina a kan fitowa tare da wadannan mutane. Na ce a cikin raina, "babu tsimi babu dabara face daga Allah madaukakin Sarki. Duk lokacin da na kubuta daga hatsari sai in auka cikin wani wanda ya fi shi." Na tashi ina tafiya bisa dutsen nan, ban san inda nake nufa ba. Kwaram, sai na hadu da wasu samari biyu, ka ce su watanni ne don kyau. Kowane daya daga cikin su yana tafe yana dogara sanda ta jar zinariya. Da muka hadu sai na yi musu sallama. Bayan sun mayar mini da sallama, sai na ce musu, "don Allah 'yan samari, su waye ku?" "Mu bayin Allah ne," suka amsa mini, "muna zaune ne a bisa wannan dutse." Sai suka miko mini sanda daya ta jar zinariya, suka tafi abin su. Da suka bace mini da gani, sai na ci gaba da tafiya ina dogara wannan sanda. Ina cikin tafiya sai na ji motsi wukur-wukur a bayan dutse, sai na ja na tsaya. Can sai ga wani babban maciji ya fito daga cikin wani kogon dutse. A cikin bakinsa ya hadiye wani namiji daga kafafunsa zuwa cibiyarsa, sauran jikinsa a waje yana kururuwa yana cewa, "wanda duk ya kubutar da ni daga wannan maciji Allah zai kubutar da shi daga dukkan wahala." Tausayin mutumin nan ya kama ni, ban yi wata- wata ba sai na daga sandar da ke hannuna ta jar zinariya na kwantara wa macijin bisa kai, nan take ya amayar da mutumin da ke bakinsa. sake bugun ta na biyu, ta juya da sauri ta shige cikin kogon nan da ta fito. Mutumin ya zo gare ni, jikinsa na bari ya ce,"ya shugabana, wallahi ba zan rabu da kai ba tsawon rayuwata. Kai ne mai gidana a bisa wannan dutse, ka aikata duk abin da ka so gare ni." Na ce masa babu laifi ga yin haka. Na shige gaba yana biye da ni a baya, muka ci gaba da tafiya bisa dutse har muka iso ga gungun wasu mutane. Da na dubi mutanen nan da kyau, sai na ga har da abokin nan nawa da ya dauke ni bisa bayansa, wanda kuma ya jefar da ni bisa wannan dutse. Na matsa kusa gare shi, na yi masa magana cikin harshe mai dadi na ce: "ya abokina, bai kamata aboki ya aikata abin da ka aikata gare ni ba." Ya amsa mini, "kai ne ka jawo wa kanka abin da ya same ka. Me ya sa ka ambaci sunan Allah lokacin da kake bisa bayana? Wannan abu ya yi kusa ya halaka mu duka." Na roki gafara wurinsa. Na kuma roke shi ya koma tare da ni zuwa cikin birni wurin iyalina. Ya yarda zai dauke ni bisa bayansa, amma ya gargade ni da kada in kuskura in kara ambaton sunan Allah yayin da nake bisa bayansa. Na kawo sandar zinariyar nan na ba mutumin da na kubutar daga bakin maciji. Muka yi ban kwana da shi yana kukan rabuwa da ni. Na dare bisa bayan abokina ya tashi sama da ni tare da sauran mutanen nan, kamar dai yadda muka yi da fari. Ba mu gushe ba muna keta iska cikin sararin samaniya har muka iso cikin gari. Ya sauke ni cikin gidana ya yi gaba abin sa. Matata ta taso ta tare ni da farin ciki, sa'annan ta gargade ni da cewa kada in sake fita tare da mutanen nan masu tashi domin su 'yan uwan shaidanu ne. Ba su sallah, ba su salati, ba su son mai sallah ko salati. Yayin da na ji zancen matata sai na cika da mamaki, na ce a cikin raina, "haba, ai biri ya yi kama da mutum. Ba don haka ba me zai sa mutanen nan su taso mini kamar za su cinye ni danye, lokacin da na ambaci sunan Allah." Sai na tambayi matata, "to, amma mahaifinki ba ya tashi tare da su?" Ta amsa mini, "mahaifina ba ya tashi tare da su, shi musulmi ne mai tsoron Allah." Daga nan sai ta canza zancen ta ce, "ka ga dai yanzu ba ni da uwa ba ni da uba a cikin wannan birni, duk sun mutu. Ina so ka tattara dukkan dukiyar nan tamu ka sayar da ita, ka dauke ni mu tafi kasarku, mu fita daga kasar wadannan shaidanun mutane." Na amince da maganar matata, na tattara dukkan dukiyar dattijon nan na sayar da ita, na sayi wasu kayan da zan yi fatauci da su a kan hanya. Na shiga cigiyar jirgin da zai nufi birnin Basara, na kuwa sami wasu fatake suka ce mini su ma can za su fatauci amma ba su sami jirgi ba. Na ce musu me zai hana mu sana'anta jirgin da kanmu. Suka yarda da shawarata, muka sami itatuwa masu yawa muka daura babban jrigi wanda zai ishe mu tafiya duk da kayanmu. Fatake duka suka sanya kayansu a cikin jirgi, na tafi tare da matata da wasu kayanta masu saukin dauka. Muka shiga jirgi muka tsunduma cikin teku, Allah ya tsare mu, muka tafi daga wannan tsibiri zuwa wancan, daga wannan birni zuwa wancan, muna saye muna sayarwa. Iska ta yi mana dadi, ba mu gushe ba muna tafiya har muka iso birnin Basara. Na yi sallama da abokan tafiyata, na dauki kayana tare da matata na nufi birnin Bagadaza, Gidan Aminci. Yayin da muka iso Bagadaza sai na nufi gidana, na kuwa same shi lafiya, babu abin da ya faru a cikinsa. 'Yan uwa suka yi ta zuwa suna yi mini barka da dawowa. Na sanya dukiyata a cikin taska na kulle. Yayin da abokaina suka ji labarin dawowa ta daga wannan tafiya ta bakwai wadda na share tsawon shekara ashirin da bakwai ba na gida, sai suka yi ta zuwa suna yi mini barka, da har sun debe tsammani da dawowa ta. Na ba su labarin abin da ya faru gare ni a cikin wannan tafiya tawa, suka yi mamaki, gayar mamaki. Tun daga wannan rana na yi rantsuwa ba zan sake fita gida ba da niyyar tafiya, a bayan kasa ne ko a cikin teku. Saboda wannan tafiya ta karshe ta ba ni tsoro matuka. Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki wanda ya maido da ni cikin kasata kuma cikin 'yan uwa da abokaina, lafiya. "Don haka ya kai abokina Sindibad dan dako," in ji Sindibad Matafiyi, "wannan ita ce irin gwagwarmayar rayuwar da na sha kafin in tara wannan dukiya da kake gani, ba don Allah ya hore mini tsawon rayuwa ba, da tuni an manta da ni a bayan kasa." Sindibad dan dako ya dukar da kai kasa ya ce, "ya shugabana, ina rokon ka don Allah ka yafe mini habaicin da na yi maka a baya cikin waka." Sindibad Matafiyi ya riki Sindibad dan dako babban amininsa, ya ba shi dukiya mai yawa da bayi, suka kasance cikin farin ciki da jin dadin rayuwa har mai yanke farin ciki, mai rusa gidaje da birane, mai raya kaburbura da makabartu, kaskon da kowane mai rai zai sha daga gare shi, ita ce mutuwa ta zo musu. Tsarki ya tabbata ga Sarkin nan da ba ya mutuwa har abada. Wannan shi ne abin da ya zo mini na daga labarin Sindibad Matafiya da Sindibad dan dako. wannan shine abunda yazo gareni na hikayar sindabad mai teku da kuma sindabad dan dako' wanda yadaukemu tsawon kwana ashiri muna kai'INSHA ALLAH Nan bada jimawa ba zan kawo wata sabuwan hikaya insha Allah, ANAN nake sallah na daku ni NAKU Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ. This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8