Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 8
su fadi kasa don tsoro, ina kallon abin da ke faruwa. Na ji kasusuwan abokina na karairayewa a cikin cikin maciji. Da ya gama hadiye shi sai ya juya ya tafi abinsa. Aka bar ni saura ni kadai a cikin wannan tsibiri. Bayan gari ya waye ina kan bishiya, na duba ko'ina amma ban ga alamun macijin nan ba. Da na tabbar ba ya kusa sai na sauko daga itaciya, jikina a sanyaye kamar mara laka saboda tsananin tsoro. Na tabbata babu abin da zai kubutar da ni daga wannan maciji. Kafin gobe war haka, ko shakka babu, na zama tarihi. Wata zuciya ta ce in fada cikin teku mana in mutu da maciji ya hadiye ni, amma sai na kasa aikata haka, kun san rayuwa da dadi. zanci gaba insha Allah daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ. whatsapp only pls 080327675479. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA Sabuwar Fassar Ibrahim Malumfashi, Danladi Haruna, Bukar Mada. Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce, bayan gari ya waye ina kan bishiya, na duba ko'ina amma ban ga alamun macijin nan ba. Da na tabbar ba ya kusa sai na sauko daga itaciya, jikina a sanyaye kamar mara laka saboda tsananin tsoro. Na tabbata babu abin da zai kubutar da ni daga wannan maciji. Kafin gobe war haka, ko shakka babu, na zama tarihi. Wata zuciya ta ce in fada cikin teku mana in mutu da maciji ya hadiye ni, amma sai na kasa aikata haka, kun san rayuwa da dadi. Daga nan sai wata dabara ta fado mini a cikin rai. Na je na karyo rassan itatuwa dogaye guda biyar, kowane daya ya fi ni tsayi sau uku, na ciri ciyawa na tufka igiyoyi, na ajiye su inda zan kwana karkashin wata bishiya. Da na ga marece ya fara shigowa sai na zauna karkashin itaciyar nan. Na dauko itatuwa guda hudu na daure su da kusurwowin juna, daya a kasa, daya a sama, daya a gefen dama, daya a gefen hagu, kamar dai an shata kofar wani babban daki. Icce na biyar kuma na daura shi a tsakiya daidai tsawona. Na shiga tsakiyar itacen na daure tafin kafafuna ga icce na kasa, na yi rawani da iccen tsakiya wanda ya taba kaina, na kwanta rigingine a tsakanin itatuwan nan, sun killace ni ta ko'ina. Can da dare ya yi, sai ga macijin nan sa-ka-ka-ka ya biyo warina, ya zo inda nake. Ya yi niyyar hadiye ni amma babu dama saboda itatuwa sun tsare ni ko'ina. Ya juya ko wane bangare yana neman makamata amma bai samu ba. Ni kuwa na yi zurui da ido ko kiftawa ba na yi saboda tsoro. Macijin nan sai ya tafi sai ya dawo har asuba ta matso, da dai ya ga babu yadda zai yi ya hadiye ni kuma ga gari na shirin wayewa, sai ya hadiyi miyau ya yi tafiyarsa. Da gari ya waye sai na kwance kaina, hannuwana na rawa kamar tsohuwar da sanyi zai halaka. Na nufi bakin gaba da sauri ko na sami hanyar fita daga cikin wannan tsibiri. Domin na san idan dare ya yi macijin nan zai dawo da tasa dabarar, don haka ba lalle ba ne dabarar da na yi jiya ta fisshe ni yau ba. Ina nan tsaye bakin gaba ina addu'a ga Allah da ya koro mini da mafita, sai na hangi wani abu can daga nesa cikin teku kamar jirgin ruwa. Na murje idanuna na kara hangawa, babu shakka jirgin ruwa ne, kuma babba irin na fatake. Sai dai jirgin ba tsibirin da nake ya nufo ba, yana shirin gilmawa ne ya wuce. Nan da nan na karyo ganye bishiya, na yi ta daga shi sama ina kadawa cikin iska, ina kira da karfi domin masu jirgin su ji. Allah da ikonsa kuwa sai suka hango ni, sai na ga jirgin ya karkato zuwa inda nake. Da suka zo sai na kwashe labarina duka na gaya musu, suka tausaya mini, suka saka ni cikin jirginsu muka tafi. Na gode wa Allah da ya kubutar da ni daga sharrin maciji na tausaya wa abokaina da suka halaka, na yi musu addu'a. Masu jirgi suka kawo mini abinci da ruwan sha mai sanyi, na ci na koshi, na gode wa Allah na gode musu bisa wannan karimci nasu. Hankalina ya kwanta, karfin jikina ya dawo, na kara yin godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya kubutar da ni daga halaka, sai na ga abubuwan da suka faru sun zama tamkar a mafarki. Ba mu gushe ba muna tafiya, iska kuwa ta yi wa jirginmu dadi, har muka iso ga wani tsibiri mai suna Assalahidati, wannan tsibiri kuwa cike yake da itatuwan sandal, Madugu ya ce a yada zango a cikinsa. Aka daure jirgi a bakin gaba, fatake suka fita da hajarsu domin yin ciniki. Sai Madugu ya juyo gare ni ya ce, "Bawan Allah, ga shi kai bako ne, ka gaya mana cewa kai falke ne wanda ya hadu da hadarurruka iri-iri har ka rasa hajarka. Ina so in taimake ka ka koma gida da dan abin hannunka, kada ka koma hannu rabbana. Kasan an ce alheri ba ya da kadan, masu hikimar magana ma suna cewa, ya da alheri a baya ka tsince shi a gaba." "Wane irin taimako kake so ka yi mini?" Na tambaye shi. Madugu ya ce, "Ka sani cewa mun fito gida da wani falke, tun da muka sauka a wani tsibiri muka huta ba mu kara ganin shi ba, ba mu sani ba ko yana raye ko ya mutu, har yanzu dai ba mu ji duriyarsa ba. Da na so sai mun koma gida in nemi iyalinsa in aika musu da hajar. Amma yanzu ina so in ba ka wannan haja ka yi kasuwanci da ita a cikin wannan tsibiri, ribar duk da aka samu, idan muka koma Bagadada, sai a raba ta biyu ka dauki rabi a ajiye wa mai kayan rabi. Ka yarda da haka in dauko maka hajar ka tafi tare da sauran fatake?" Yayin da na ji ya ambaci Bagadada sai na ji kamar ya tsire ni da allura, ashe ma wadannan fatake na wajenmu ne. Na amsa masa da sauri, "Na yarda da wannan sharadi." Na yi ta gode masa har babu adadi. Madugu ya ce a fito mini da hajar falken nan da ya bace. Mai kula da kayan jirgi ya tambayi Madugu, "Wane suna aka rubuta a jikin hajar?" Madugu ya ce, "Wadda aka rubuta wa sunan Sindibad mai teku. Wanda ya bata a tsibirin tsuntsayen Rukki. Wannan bako za mu ba kayan ya yi fatauci da su, ribar duk da aka samu sai a raba biyu ya dauki kashi daya." Mai kula da kaya ya ce, "Ai kuwa hakan da ka yi ya yi daidai ya Ra'isu." Yayin da na ji Madugu ya ambaci sunana, ban san lokacin da bakina ya subuce ba don murna na ce, "Wallahi ni ne Sindibad mai teku." Suka kalle ni haka galalala kamar masu kallon motsattse. Da na ga dai alamun ba su yarda da zancena ba sai na tambayi Madugu, "Yalla ka san Sindibad din ne?" "Ni ban san shi ba," in ji Madugu, "amma shi mutumin Bagadada ne, ana yi masa lakabi da Sindibad mai teku. Da shi muka baro kasar Iraki har muka iso wani tsibiri na manyan tsuntsaye, tun daga nan sai ya yi mana batan dabo. Muna kyautaata zaton wata dabba ta cinye shi a cikin tsibirin." Daga nan sai na fashe da kuka, kuka mai tsanani, na ce, "Ya kai wannan Madugu amintacce! Wallahi ni ne Sindibad mai teku. Bari ka ji yadda abin ya kasance haka. Yayin da muka sauka a cikin wancan tsibiri da kake magana, mun tafi tare da wasu fatake domin mu zagaya cikinsa. Sai na zauna a gindin wata bishiya mai sanyin inuwa, na ci abinci na sha ruwa, daga nan sai na kishingida domin in huta sai barci ya kwashe ni. Yayin da na farka sai na ga kun tafi kun bar ni. Wallahi wannan hajar tawa ce, da a ce za mu hadu da tajirai masu dibar lu'ulu'u a kwarin macizai da sun shaida ni, domin na shaida musu labarin yadda aka yi jirgi ya bar ni a tsibirin Rukki, da yadda aka yi na baro tsibirin na fada cikin kwarin macizai inda tajirai ke dibar lu'ulu'u ta dabarar jefa danyen nama." Lokacin da fatake suka ji jawabina sai suka kewaye ni suna kallo, wasu suka yarda da maganata wasu kuwa suka ce karya nake yi. Amma yayin da wani daga cikin fataken nan ya ji na ambaci kwarin macizai mai lu'ulu'u sai ya kara dubana tun daga kasa har sama, ya juya ga fatake ya ce musu, "Ku saurari zancena ya ku 'yan uwana. Idan ba ku manta ba lokacin da ina ba ku labarin tafiye-tafiyen da na yi da abubuwan ban mamaki da na gano, na gaya muku cewa akwai wani kwarin macizai wanda yake cike da lu'ulu'u, babu mai iya shigarsa balla ya kwaso wannan dukiya. Na gaya muku cewa sai dai mu rika yanka dabba muna fede ta, sai mu jefa naman a cikin kwarin, lu'ulu'u mai yawa zai lillike a jikin naman. Idan tsuntsaye masu farauta sun shiga kwarin za su dauko naman su fito da shi, sai mu kore su mu cire lu'ulu'un. Kamar yadda na gaya muku wata rana na jefa dabbata a cikin kwarin, yayin da tsuntsu ya fito da ita sai na ga mutum a tsaye kusa gare ta. To, kun dai san sauran labarin da na fada muku, daga karshe dai kuka ce labarina zuki-ta-malli ne, wai babu wani kwarin lu'ulu'u a duniya." Fatake suka amsa gaba daya, "An yi haka kuwa, ka gaya mana wannan labari amma daga karshe muka karyata ka." Falke ya nuna Sindibad ya ce, "To, wannan shi ne mutumin da ya fito tare da dabbar da na jefa, kuma ya ba ni dukiya mai yawa wadda tamaninta ba ya misaltuwa, ya gaya mini sunansa Sindibad mai teku. Daga nan muka tafi tare da shi har birnin Basara, a can muka rabu ya ce zai nufi Bagadada, mu kuma muka nufi tamu kasa. Na gode wa Allah da ya turo shi nan, domin ya gasgata labarin da na ba ku kuka karyata ni. Kuna nan zaune kifin rijiya kawai, ba ku san kome ba sai mutum ya kawo muku labari ku karyata shi. Ni na yarda da shi, babu shakka wannan hajarsa ce." Yayin da Madugun jirgi ya ji zancen tajiri, sai ya matso kusa gare ni, ya dube ni da kyau ya ce, "Yaya yanayin hajarka take, idan har gaskiya kake fada?" "Abu kaza da abu kaza ne a ciki," na amsa masa. Na kuma kara tuna masa wasu abubuwa da suka faru yayin tafiyarmu a cikin jirgi daga Basara zuwa tsibirin da suka bar ni. Daga nan sai ya yarda lalle dai ni ne Sindibad. Ya rungume ni cikin kirjinsa yana cewa, "Wallahi ya shugabana, labarinka abin mamaki ne da ban tausayi. Godiya ta tabbata ga Allah da ya kubutar da kai daga halaka ya kuma sake sada ka da hajarka.". kuna tare neda Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ10. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA Sabuwar Fassarar: Ibrahim Malumfashi, Danladi Haruna, Bukar Mada. Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce, Madugun jirgi ya yi godiya ga Allah da ya kubutar da ni daga halaka ya kuma sake sada ni da kayana. Na karbi hajata na shiga ciniki, in sayar in saya, na sami riba mai tsananin yawa. Muka ci gaba da zagaya tsibirai muna saye muna sayarwa har Allah ya kawo mu kasar Hindu. Muka sayi kayan yaji masu yawa irinsu citta da tafarnuwa, saboda suna da riba sosai a Birnin Bagadada. Daga Hindu kuma sai muka ci gaba da tafiya har muka dangana da kasar Sin, muna saye muna sayarwa. A cikin tekun Hindu na ga abubuwan mamaki wadanda ba su ko kidayuwa. Kadan daga cikinsu su ne, na ga wani irin katon kifi kamar saniya, sai ya fito da 'ya'yansa bisa ruwa yana ba su nono suna sha, kamar yadda 'yan Adam ke shayar da 'ya'yansu. Saboda tauri da karfin fatar wannan kifi, da ita ake yin sulke ko garkuwa wadanda ake amfani da su wurin yaki. Haka kuma na ga wasu kifayen, wasu siffar jakai wasu siffar dawaki. Na ga kuma kunkuru wanda girmansa ya kai kafa ashirin, wannan kunkuru zai iya daukar kato kome girmansa, ya yi tafiya da shi bisa bayansa. Na kuma ga wani tsuntsu wanda idan ya yi kwai ba ya kyankyashe shi sai bisa ruwa. Ba mu gushe ba muna tafiya cikin teku, cikin kyakkyawan yanayin iska da tsarewar Ubangiji har Allah ya nufe mu da dawowa Birnin Basara. Na huta kwana biyu a Basara, daga nan sai na dunkule kayana na nufi Birnin Bagadada, birnin aminci. Na isa gidana lafiya, na tarar da 'yan uwa da abokan arziki lafiya. A wannan tafiya na sami riba bisa riba har abin ba ya kidayuwa. Na bayar da sadaka ga mabukata, na ciyar da marayu, na rarraba wa abokaina kyaututtuka iri daban-daban. Na ci gaba da rayuwata kamar da, in ci mai kyau in sha mai kyau. In sanya sutura ta alfarma in harde bisa karaga ina hura hanci kamar wani sarki. Wannan shi ne labarin tafiyata ta uku a cikin teku. Idan Allah ya kai mu gobe lafiya, zan gaya muku labarin tafiyata ta hudu a cikin teku wadda ta fi sauran tafiye-tafiyen da na ba ku labari ban mamaki. Bayan Sindibad mai teku ya gama wannan labari sai ya ba Sindibad dan dako dinari dari ya kuma ce a kawo musu abinci da abin sha. Aka jera akussan abinci da nama, Sindibad mai teku ya ci tare da Sindibad dan dako a akushi daya, sauran tajirar duka suka ci daga nasu akussan. Bayan sun gama cin abinci, sun sallaci sallar isha'i sai suka yi sallama da mai gida suka watse, kowa ya nufi gidansa yana mamakin labarin mai gida. Dan dako ya nufi gida zuciyarsa cike da mamakin labarin da takwaransa mai teku ya bayar. Ya kwanta barci yana alla-alla gari ya waye ya koma gidan mai gida domin ya ji labarin tafiyarsa ta hudu a cikin teku. Tun da assalatu dan dako ya farka, bayan ya yi sallar asuba sai ya zauna yana wuridi har gari ya yi sha. Da ya ga rana ta kunno kai haskenta ya sauka bisa jigayi da rufin gidaje, sai ya kimtsa ya nufi gidan Sindibad mai teku. Ya isa gidan, bayi suka shigar da shi dakin mai gida, ya zauna yana jiran fitowarsa. Bai dade da zama ba sai ga sauran tajirai suna shigowa daya bayan daya. Bayan sun hadu gaba daya, can sai ga mai gida ya fito cikin sutura ta alfarma, yana takawa dai- dai kamar dawisu. Suka gaisa da sauran abokansa tajirai, ya harde bisa karagarsa kusa ga Sindibad dan dako. Aka kawo musu abinci suka ci suka koshi, suka yi barkwanci a tsakaninsu cikin annushuwa da farin ciki. Daga nan sai Sindibad mai teku ya fara bayar da labarin tafiyarsa ta hudu: TAFIYAR SINDIBAD TA HUDU A CIKIN TEKU. Ku sani ya ku abokaina, bayan na dawo gida daga tafiyata ta uku da dimbin dukiya wadda ba ta misaltuwa. Na zauna cikin farin ciki, ba ni da wani aiki sai dai kullum in gayyato abokaina mu wanke goma mu tsoma biyar. Ina nan kan haka sai ran nan wasu attajiran fatake, abokaina daga Basara, suka kawo mini ziyara. Bayan mun gama kwasar gara sai muka shiga hirar duniya da labarin tafiye-tafiye. Nan fa zuciyata ta motsa, suka takalo mini sha'awar sake fita cikin duniya, na manta kwata-kwata da wahalhalun da na sha a baya. Na yi sha'awar ganin al'ummomin wasu kasashe da al'adunsu. Nan take na yanke shawarar sake fita cikin duniya domin yin fatauci. Tun daga wannan rana na fara shirye-shiryen tafiya, na sayi kayayyakin zuwa fatauci masu yawa da tsada fiye da wadanda na taba tafiya da su a baya. Da lokacin tafiya ya yi sai na yi sallama da 'yan uwa da abokai, na kwashi kayana sai Birnin Basara, inda zan hadu da abokan tafiyata, wadanda suke su ne manya-manyan attajiran birnin. Muka shiga jirgi muka fada teku. Iska ta yi wa jirginmu dadi, muka yi ta tafiya daga wannan tsibiri zuwa wancan, muna saye muna sayarwa. Ran nan muna tafiya cikin dadin rai, kwatsam sai teku ta canja mana hali. Guguwar ruwa ta taso, rakuman ruwa kuwa suka yi ta kwallo da jirginmu kamar zai kife. Da Madugu ya ga haka sai ya ce a dakatar da tukin jirgi. Jirginmu ya tsaya cak a tsakiyar teku, yana tangal-tangal kamar zai kife saboda rakuman ruwa da ke juya shi, mu kuwa babu abin da muke yi sai addu'a. Muna cikin wannan hali sai wata guguwa mai karfi ta keto daga cikin teku ta bugi jirginmu bugu mai karfi. Nan take jirgi ya kakkarye, dukanmu muka dulmiye cikin teku duk da kayanmu, babu wanda ya koma ta kan dan uwansa, kowa sai ya yi ta kansa. Na yi ta iyo cikin ruwa ina sallallami har hannuwana suka gaji, na sakankance da halaka. Ina cikin wannan hali sai Allah ya koro mini da wani yankin itace babba na jirginmu da ya karye, na kama shi da kyar na haye. Ashe akwai sauran fataken da ba su nutse ba, su ma sai Allah ya yi musu katari da hawa bisa wannan icen jirgi tare da ni. Muka rika tura ruwa da kafafunmu allon nan yana tafiya da mu da taimakon iska. Muka kasance cikin wannan hali kwana daya da yini daya, iska da rakuman ruwa suka yi ta tura allon nan da sauri. A cikin kwana na biyu sai teku ta lafa, iska mai dadi ta rika kadawa, rakuman ruwa suka kwanta. Ba mu gushe ba muna tafiya bisa allon jirgi har muka dangana ga wani tsibiri a tsakiyar teku. Muka ja jiki muka sauka cikin tsibirin, muka yi kwance kamar matattu saboda tsananin gajiya, ga yunwa ga kishirwa, ga kuma uwa uba sanyi mai tsanani da ke ratsa mana jiki. Bayan mun dan sarara sai muka tashi muka rika zagaya tsibirin. Wannan tsibiri cike yake da ciyawa, babu wasu itatuwan kirki balle mu sami 'ya'yan itacen da za mu ci. Da muka ga dai yunwa na shirin halaka mu, tilas muka rika dibar ciyawa muna ci kamar dabbobi. Da muka cika cikannanmu da ciyawa, sai muka sami wuri muka kwanta, barci kuwa ya yi awon gaba da mu, ba mu farka ba sai da gari ya waye. Bayan gari ya waye sai muka tashi muka ci gaba da zagayawa cikin tsibiri, hagu da dama. Can sai muka hangi wani gini kamar gida. Muka nufi wannan gida wai ko za mu sami abinci da ruwa. Yayin da muka isa bakin kofar gidan sai muka ga wasu mutane suna fitowa daga cikinsa. Mutanen nan tumbur suke haihuwar uwarsu, babu mai ko bante balle riga, su ake kira zindirawa. Suna ganinmu sai suka kama mu, suka ja mu suka nufi cikin gidan nan, ba su zame ko'ina da mu ba sai gaban wani tsoho, yana zaune bisa abin zama. Ashe sarkinsu ke nan. Tsoho ya yi mana ishara da mu zauna. Muka zauna, amma jikinmu bai ba mu ba. Mutanen nan suka kawo mana wani irin abinci wanda ba mu san shi ba, ba mu kuma taba ganin irinsa ba duk tsawon rayuwarmu. Abokan tafiyata ba su yi wata-wata ba sai suka far ma abincin nan da ci, saboda tsananin yunwa, kamar wadanda suka shekara ba su ci kome ba, da ma an ce wanda ruwa ya ciwo idan aka mika masa takobi sai ya kama. Ni kuwa raina bai ba ni ba akan in ci abincin nan, duk da matsananciyar yunwar da nake ji, ko kyamar abincin ne ko kuwa wani abu ne na daban ya hana ni cin sa, Allah kadai ya sani. Ashe rashin cin abincin nan alheri ne gare ni, shi ne sanadin kawowata har zuwa wannan lokaci da nake ba ku wannan labari, ban mutu ba. Domin kuwa abokan nan nawa na gama cin abincin sai duk suka fita daga cikin hayyacinsu, suka rika yin wasu halaye kamar mahaukata, ko kuma kamar wadanda aljanu suka shafa. Daga nan sai zindirawan nan suka kawo musu ruwan wata irin kwakwa suka kwankwada, suka kuma shafe jikinsu da ruwan kwakwar. Zindirawa na gama aikata wannan abu ga abokaina, sai abokan nan nawa suka rude, idanunsu suka rufe, suka fada wa sauran abinci da ci, ba ji ba ga ni, sai ka ce guzumar da ta ketare rani da kyar aka kai ta cikin danyar ciyawa. Tausayinsu ya kama ni saboda yanayin da na ga sun shiga. Ni kuwa babu wanda ya kula ni daga cikin zindirawan nan, kuma ba su tilastani in ci abincin nan ba, don haka ba su shafa mini kome ga jikina ba. Duk da haka zuciyata cike take da tsoron abin da zai faru gare ni. Ina ta kallon wadannan zindirawa a sace, can sai na tuna wani labari da na taba ji game da su. Su dai wata kabila ce ta matsafa, sarkinsu kuwa dodo ne mai cin mutane. Duk mutanen da kaddara ta koro cikin tsibirinsu sukan kama su, su ba su wannan abinci na tsafi wanda zai juyar musu da hankali, daga nan sai su ba su ruwan kwakwan nan su sha, bayan sun sha su shafe musu jiki da shi. Shi ke nan sai hankulan wadannan mutane ya gushe, cikannansu su bude kamar randa, ta yadda za su yi ta cin abinci ba su koshi. Cikin 'yan kwanaki kadan sai su yi bul- bul kamar turkakkun shanu. Su za a rika yanka wa Sarki kamar raguna, ana gasa masa yana ci. Su kuwa talakawan Sarki danyu suke cin nasu mutanen, ba ma sai an gasa ba. Yayin da na tuna wannan labari game da wadannan zindirawa sai hankalina ya tashi, na tausaya wa abokaina, ni kuma na shiga tunanin abin da zai faru gare ni. Aka damka abokan nan nawa ga wani mutum wanda zai rika kula da su. Kullum sai ya rika fita da su kiwo cikin tsibirin nan, suna cin ciyawa ba su kula ba, kamar dabbobi. Nan take kuwa cikin 'yan kwanaki suka yi kiba. Ni kuwa duk na rame na yankwane, saboda ban yarda na ci abincinsu ba, duk kuwa da cewa kullum sai sun kawo mini abincin wai in ci. Da suka ga dai na ki kula abincinsu, kuma ga shi duk na rame, daga fata sai kashi, sai suka yi watsi da ni suka ma daina kula ni. Ni kuwa da na ga haka sai na saci jiki wata rana na sulale daga gidan nan na gudu. Bayan na yi nisa da gidan zindirawa sai na tasar wa bakin gabar teku, wadda take da nisa kwarai daga gidan zindirawa. Na kusa isa bakin gaba ke nan, sai na hangi wani tsoho daga cikin zindirawan nan. Ina ganinsa na shaida shi, shi ne wanda ke kiwon mutanen da suka kama. daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ 11. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA Sabuwar Fassarar: Ibrahim Malumfashi, Danladi Z. Haruna, Bukar Mada. Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce, bayan na yi nisa da gidan zindirawa sai na tasar wa bakin gabar teku, wadda take da nisa kwarai daga gidan zindirawa. Na kusa isa bakin gaba ke nan, sai na hangi wani tsoho daga cikin zindirawan nan. Ina ganinsa na shaida shi, shi ne wanda ke kiwon mutanen da suka kama. Yayin da tsohon nan ya gan ni sai ya shaida ni, ya san cewa kuma ina cikin hankalina ba kamar sauran da yake kiwo ba, don haka sai ya tabbatar da cewa ina shirin tserewa ne. Ga mamakina sai na ga yana daga mini hannu yana yi mini ishara da in koma da baya in bi ta hanyar da ta yi hannun dama. Na ga yana nuna mini cewa wannan hanyar da na biyo mai hatsari ce. Don haka ban yi gardama ba, sai na juya da baya na nufi hanyar da ta yi hannun dama. Na rika gudu don tsoron kada a kama ni, idan kuma na gaji da gudu sai in yi tafiya, har na bace wa tsohon nan. Yayin da rana ta fadi duhun dare ya fara mamaye tsibirin nan, sai na sami wuri na zauna. Na yi niyyar in kwanta in yi barci saboda gajiya, sai wata zuciya ta ce ahir! Don haka na yi zaune ina ta karanto duk wata addu'a da ta fado mini cikin zuciya. Can da dare ya raba sai na tashi na ci gaba da tafiya. Ban gushe ba ina tafiya har hasken safiya ya keto sararin samaniya, wuri ya yi sha da hasken safiya gwanin ban kaye. Rana ta dago sama, haskenta ya haske duwatsu da ciyawa da jigayi. Daga nan fa sai cikina ya fara kiran ciroma, na duka na ci ciyawa da hakukuwa gudun kada in halaka da yunwa. Na lasa dan danshi-danshin raba da ke jikin ciyayi a matsayin ruwa, daga nan sai na ji karfin jikina ya dan dawo. Na ci gaba da tafiya tsawon wannan rana, ban gushe ba har sai da dare ya yi. Na zauna na huta, bayan dare ya raba na ci gaba da tafiya har zuwa wayewar gari. Na ci ciyawa, na sha ruwan rabar da ke jikin ciyawa. Ban gushe ba cikin wannan hali har tsawon kwana bakwai. A cikin kwana na takwas ne na hangi wani abu can daga nesa kwarai, ban gane ko menene ba. Na nufi wannan abu ina cewa a cikin raina ko ma menene ya kashe ni in huta da wannnan bakar wahala. Yayin da na yi kusa da abun sai na ga ashe gungun mutane ne suna dibar goran yaji. Da suka hango ni sai suka taso mini, suka zagaye ni suna kallo, kamar masu kallon wata bakuwar dabbar da ba su taba gani ba. Suka tambaye ni, "Mutum ko aljani? Daga ina ka fito cikin wannan tsibiri." Na amsa musu, "Ni mutum ne dan uwanku." Na ba su labarin abin da ya faru gare ni duka, da wahalhalun da na sha. Na kwashe labarina duka na gaya musu, na kuma fada musu irin bakar wahalar da na sha a cikin wannan tsibiri. Suka yi mamaki matukar mamaki, suka ce, "Wallahi labarika abin mamaki ne da tausayi matuka. To, amma yaya aka yi har ka gudo daga al'ummar zindirawa, wadanda babu wani mutum da zai shiga hannunsu ya kuma tsere daga gare su?" Na gaya musu ni ma ban sani ba. Allah dai ne ya kubutar da ni daga hannunsu. Na gaya musu abin da ya faru ga abokan tafiyata. Mutanen nan suka zaunar da ni karkashin wata bishiya mai sanyin inuwa, suka kawo mini abinci mai rai da lafiya suka girke a gabana. Suka ce in ci abinci kafin su gama dibar goran yaji. Na nade hannun rigata na sa abincin nan gaba. Na yi ta wulka loma har ina sarkewa, kamar wanda za a kwace wa abincin. Ban cire hannuna daga cikin akushin abinci ba har

Chapter 4 of 8