Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 8
Da yawa mutane a wurina suke kamun kafa idan suna neman wata bukata ga Sarki. Na zauna a wannan birni cikin dadin rai da kwanciyar hankali. Sai dai abu daya kawai ke tayar mini da hankali. Wannan abu kuwa shi ne, na sha tambayar mutanen wannan birni labarin Bagadada har na gaji, amma ban samu wanda ko ya ce ya taba jin sunan birnin ba. Wannan shi ne kawai damuwata. Domin duk wannan daula da nake ciki ina matukar son in koma kasarmu, cikin 'yan uwana da abokai. Wata rana na shiga wurin Sarki Mihirjanu sai na same shi tare da wasu baki 'yan kasar Hindu. Na yi musu sallama, suka mayar mini da sallamata. Bayan mun gaisa sai suka tambayi labarina da kuma kasar da na fito. Ni kuwa na ce musu ku fara gaya mini labarinku. Suka ce mini su 'yan asalin kasar Hindu ne, amma ba kabilarsu daya ba. Akwai 'yan kabilar Shakiriya daga cikinsu, wadda kabila ce mai son zama lafiya, ba ta takalar kowa kuma ba ta yaki da kowace kabila. Akwai kuma 'yan kabilar Burahamiya, wadanda babu ruwan su da shan giya, sai dai masu arziki ne sosai a kasar Hindu, sun mallaki shanu da rakuma da tumaki da awaki. Haka kuma suka ce mini akwai kananan kabilu a kasar Hindu har guda saba'in da biyu. Na yi mamaki da jin wannan labari nasu. Ni kuma na duka na kwashe nawa labari na gaya musu, na kuma gaya musu na fito ne daga kasar Bagadada. A cikin abubuwan mamaki da na gani, wadanda ba zan manta da su ba, a dan zaman da na yi a tsibirin Sarki Mihirjanu, akwai wani dan karamin tsibiri mai suna Kasilu, wanda ke makwabtaka da na Sarki Mihirjanu. Kullum sai dare ya yi tsaka sai a yi ta jiyo ganguna da algaitu na tashi kamar ana biki, duk da cewa babu dan Adam ko daya a cikin wannan tsibiri. Sai dai ana jita-jitar wai mutanen boye ne ke wannan shagali da dare. Haka kuma na taba ganin wani kifi mai tsawon zira'i metan a cikin teku, inda masunta ke su. Girman wannan kifi sai da ya tsorata kowa. Masunta suka hadu suka dauko itace suka kore shi ya gudu cikin ruwa. Na taba ganin kuma wani kifi mai kai irin na mujiya a cikin wannan tsibiri. Kai, abubuwan mamaki da na gani suna da yawa a wannan tsibiri. Na ci gaba da zama tare da Sarki Mihirjanu, kullum ina zuwa bakin teku domin daukar rahoton jiragen da ke shigowa da kuma masu fita. Wata rana ina bakin teku kamar yadda na saba ina jiran isowar jigi. Na yi tsaye na dogara ga wata sanda ina kallon ruwa. Can sai na hangi wani babban jirgi yana nufo gabar ruwa inda nake tsaye. Da jirgi ya iso bakin gaba sai ya tsaya. Aka daure shi da igiya, aka aza itatuwa masu fadi daga cikin jirgin zuwa ga saman kasa, inda mutane za su taka su fito. Fataken dake cikin jirgin suka yi ta fito da hajojinsu daga cikin jirgi. Ni kuwa ina tsaye ina daukar lissafin kayansu. Bayan sun fito da kayansu duka sai na tambayi madugun jirgin, "Iyakacin kayan da kuka zo da su ke nan?" Ya amsa mini, "Ya shugabana, akwai 'yan uwanmu da suka halaka a cikin wannan tafiya, mun sayar da kayansu duka, saura na mutum daya daga cikinsu muka zo da shi wannan birni. Idan mun sayar da kayan za mu kai wa iyalansu kudin a Birnin Bagadada, Gidan Aminci." Yayin da na ji ya ambaci Bagadada sai gabana ya fadi, na tambaye shi, "Menene sunan falken da kuka zo da kayansa?" Ya amsa mini, "Sunansa Sindibad." Da na ji haka sai na kalli madugun nan da kyau sai na gane ashe dai madugun jirginmu ne da muka fito gida tare. Saboda saje da gemun da suka fito masa ne buzu-buzu a fuska ya hana in shaida shi da farko. Na yi wata irin kara don murna, har sai da ya tsorata. Na dube shi na ce, "Ya madugu, shin ba ka shaida ni ba? Ai ni ne Sindibad da muka fito tare da kai da sauran fatake daga Bagadada. Lokacin da ka yi kiran mu da mu koma cikin jirgi kafin katon kifin nan ya nutse da mu, muna nesa da jirgi. Kafin mu yi taku daya har ya nutse da mu cikin ruwa, sauran wadanda muka nutse tare duk sun halaka. Amma ni sai Allah mai girma da daukaka ya jeho mini wani gungumen itace na haye bisa gare shi. Iska ta yi ta tura ni har ta kawo ni cikin wannan tsibiri. Ina yawo cikin tsibirin na hadu da 'yan bargar Sarki Mihirjanu, suka kawo ni gaban Sarki. Na gaya masa labarina, ya tausaya mini har ma ya nada ni mai kula da gabar teku inda jiragen ruwa ke sauka. Don haka wadannan kaya da ke cikin jirgi nawa ne da na fito da su daga gida domin yin fatauci." Da madugu ya gama jin zancena sai na ga ya rike baki cikin mamaki yana yi mini wani irin kallo na rashin yarda. Ya rika tafa hannu yana sallallami, "Babu Sarki sai Allah. Mhm! Lallai zamani ya lalace, mutane ba su tsoron Allah! Sun mayar da yin karya kamar a sha ruwa a tafi." . Za mu ci gaba ==>Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ4. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA Sabuwar Fassarar: Ibrahim Malumfashi, Danladi Haruna, Bukar Mada. ... Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce, na ce wa madugu hajar da ke cikin jirgi tawa ce wadda na zo da ita daga gida domin yin fatauci. Da madugu ya gama jin zancena sai na ga ya rike baki cikin mamaki yana yi mini wani irin kallo na rashin yarda. Ya rika tafa hannu yana sallallami, "Babu Sarki sai Allah. Mhm! Lallai zamani ya lalace, mutane ba su tsoron Allah! Sun mayar da yin karya kamar a sha ruwa a tafi." Da na ga dai madugu bai yarda da zancena ba sai na ce masa, "Ya Ra'isu, Wallahi gaskiya nake gaya maka. Shin ba ka gane ni ba ne?" sai na rika duba kaina wai ko wani abu ya canja ne a jikina. Madugu ya amsa mini, "Watau don ka ji na ambaci haja wadda mai ita ya mutu a cikin ruwa, kake so ka yi mini karya don kawai in ba ka hajar. Hala kurege ya cije ni da zan yarda da maganarka? Muna kallo da idanunmu duk mutanen da suka nutse cikin teku suka mutu. Babu daya daga cikinsu da ya tsira." Na kara maraairaice masa, "Haba Ra'isu! Don me zan yi maka karya gemai-gemai da ni. Ai karya na daya daga cikin alamomin munafuki. Saurari labarina da kunnen basira." Na kara gaya masa labarina, tun fitowar mu daga Birnin Bagadada da biranen da muka ya da zango muka taba ciniki. Da yadda muka sauka bisa bayan kifi muna tsammanin tsibiri ne, da yadda kifin ya nutse da mu cikin ruwa. Na gaya masa yadda aka yi na tsira har na zo wannan tsibiri. Na dai gaya masa kome tun daga farko har karshe. Yayin da sauran fatake suka ji labarina sai suka ce lallai wannan Sindibad ne, babu shakka. Madugu ya yarda da labarin da na gaya masa. Suka yi mini barka da arziki da na kubuta daga halaka. Suka ce, "Wallahi mun dauka dukanku kun mutu." Madugu ya ba ni hajata, na kuwa gan ta yadda take, ko allura ba a taba ba. Lalle wannan madugu da amana yake. Na debi kayayyaki masu daraja da ke cikin hajar na kai wa Sarki Mihirjanu kyauta. Na gaya masa abin da ya faru, na ce masa masu wannan jirgi abokan tafiyata ne da muka fito gida tare. Ya yi mamaki matukar mamaki, ga shi kuma gaskiyata ta fito ta labarin da na gaya wa Sarki tun farkon zuwana gare shi. Sarki ya kara girmama ni. Ya kara mini kyaututtukan kaya ninkin wadanda na ba shi sau goma. Na sayar da hajata a wannan tsibiri, na sami riba mai yawa. Na sayi wasu kayayyakin da na san za su yi tsada a Birnin Bagadada. Bayan 'yan kwanaki kadan duka sauran fatake suka sayar da hajarsu suka sayi wasu kayan da za su koma da su. Da suka gama shirin tafiya na sa kayana a cikin jirgi. Na tafi wurin Sarki na yi ban kwana da shi. Ya kara mini wata kyautar fiye da wadda ya ba ni a baya. Na bar wurinsa yana kuka ina yi don sabo. Muka shiga jirgi muka fada teku. Iska kuwa ta yi mana dadin sha'ani. Muka yi ta tafiya kwana da kwanaki ba tare da wani hatsari ba. Allah da ikonsa ya kaddare mu da isowa birnin Basara lami lafiya. Bayan mun huta a birnin Basara mun kuma taba ciniki, sai muka yi gaba zuwa gida Bagadada, gidan aminci. Kwanci tashi muka iso bakin gabar tekun birnin Bagadada. Kowane falke ya rungumi kayansa ya nufi gida. Ni kuwa sai da na bidi masu rakuma suka yi mini labtun kayana zuwa gida. 'Yan uwa da abokan arziki suka yi ta zuwa suna yi mini barka da dawowa. Bayan kwana biyu na sake sayen kayayyakin da na sayar a gidana, na kawata shi fiye da yadda yake da farko. Na sayi bayi da kuyangi masu yi mini hidima. Na sayi gonaki da gidaje da filaye. Na bude rumfuna a cikin babbar kasuwar Bagadada ina ciniki a cikin su. Na zama dai hamshakin mai arziki fiye da da. Da yake an ce mai hali ba ya barin halinsa, sai na koma wa halina na da, na rika tara abokai ina kashe musu gara suna kwasa. Na manta da wahalar da na sha a baya. Amma da yake ina saye da sayarwa ina samun riba, dukiyata ba ta ja baya ba. Wannan shi ne labarin tafiyata ta farko. Idan Allah ya kai mu gobe zan gaya muku labarin tafiyata ta biyu, wadda ta fi wannan hatsari da ban mamaki. Yayin da Sindibad mai teku ya gama ba da wannan labari, sai ya sa aka sake fito da akussan abinci da abin sha. Aka aza wa kowane tajiri akushin abinci da abin sha a gabansa. Shi kuma ya ci tare da Sindibad dan dako. Bayan sun gama cin abinci ya kawo dinari dari ya ba dan dako, ya ce, "Karbi wannan kudi ladar tsayawa da ka yi tare da mu. Mun hana ka zuwa neman kudi." Dan dako ya karbi kudi ya yi godiya, ya tafi yana mamakin irin wahalhalun da mutane ke fadawa garin neman kudi. Ya kwana yana tunanin wannan labari. Da gari ya waye, tun da safe ya shirya ya nufi gidan Sindibad bahariyi. Yana zuwa aka karbe shi hannu bibbiyu, mai gida ya zaunar da shi kusa gare shi. Jimawa kadan sauran abokan Sindibad mai teku suka iso gidan. Kuyangi suka yi ta fitowa da akussan abinci da nama da gorunan ababen sha. Bayan sun ci sun koshi, sai mai gida ya fara ba da labarin tafiyarsa ta biyu a cikin teku: TAFIYAR SINDIBAD TA BIYU A CIKIN TEKU Ku sani ya ku abokaina, bayan na dawo daga tafiyata ta farko na samo dukiya mai dimbin yawa. Na zauna cikin jin dadi da kece raini, kamar yadda na gaya muku jiya. Ran nan sai zuciyata ta karkata ga son shiga duniya domin ganin kasashe da tsibirai. Na yi sha'awar kara fita zuwa fatauci. Na kwashi kudi masu yawa na sayi hajar da zan tafi da ita. Na yi sa'a kuwa wani sabon jirgi mai kyau, wanda aka kawata da kyallaye masu ban sha'awa zai fita da fatake. Na biya kudi na shiga tare da kayana da sauran fatake. Jirgi ya motsa, muka nausa cikin teku. Muka dace da yanayin teku mai dadi, muka yi ta tafiya daga wannan tsibiri zuwa wancan tsibiri, daga wannan gari zuwa wancan gari. Duk garin da muka je mukan tsaya mu yi ciniki, mu sayar da kayan da muka zo da su mu kuma sayi wadanda za mu ci riba a gaba. Haka muka ci gaba da zagaya garuruwa da tsibirai har wata rana Allah Madaukakin Sarki ya kawo mu ga wani babban tsibiri a tsakiyar teku. Tsibiri ne mai cike da bishiyoyi da nunannun 'ya'yan itace. Ga furanni launi daban-daban kowace tana fitar da irin kamshin da Allah ya hore mata. Tsuntsaye na ta rera wakoki iri-iri, suna tashi daga wannan bishiya zuwa waccan. Ga koramu ko'ina na gudana, ruwansu garai-garai kamar mudubi. Amma duk kyawun tsibirin nan ba mu ga alamun dan Adam ba a cikinsa. Madugu ya ce mu sauka nan mu huta. Aka daure jirgi a bakin gaba, dukkan fatake muka sauka daga cikin jirgi, muka fantsama cikin wannan tsibiri domin kashe kwarkwatar ido, muna tu'ajjibin ikon Ubangiji, Buwayi gagara misali. Na zo ga wata korama mai ruwa gawanin dadi, na zauna karkashin wata babbar itaciya da ta saki inuwarta ko'ina. Na zaro 'yar gurasa daga cikin jakata na ci, na sha ruwan koramar nan na zauna ina hutawa ni kadai. Wanna wuri da dadin zama yake, ga sassanyar iska na kadawa gami da kamshin furanni, kukan tsuntsaye ya hadu ya kara wa wurin armashi. Nan da nan sai na ji wata kasala ta rufe ni, na dan kishingida wai in huta. Barci mai nauyi ya dauke ni. Bayan na shafe lokaci mai tsawo ina barci sai na farka. Na nufi inda jirginmu yake da sauri, amma ina, ashe na makara. Jirgi ya tafi ya bar ni a cikin wannan tsibiri da ke tsakiyar teku, fatake na tsammani ina cikinsu. Na yi yawo cikin tsibirin nan amma ban ga mutum ko aljani ba. Hankalina ya tashi, zuciyata kuma kamar za ta fashe saboda fargaba. Ga shi dai an bar ni ni kadai babu abinci babu kuma wani dan Adam da zan gani. Na sakankance da halaka, na ce a cikin raina, "Lalle ba kullum safiya take Jumu'a ba. Idan da farko na tsira daga halaka a tafiyata ta farko, yanzu ba lalle ba ne in tsira." Hawaye suka yi ta zuba daga idanuna, na yi da- na-sanin sake fitowa daga gida domin kwadayin fatauci. Na tuna irin jin dadin da nake yi a gida, ga nama ga abinci iri-iri sai wanda raina ke so nake ci, ga sutura. In kwanta wuri mai kyau, duk wani aiki kuma sai dai in sa bayi su yi mini. To, amma yanzu fa? Kwayar abincin ma da zan ci sai na nema. Da ma an ce garin tone-tone zakara ke tono wukar yanka shi. Na yi nadamar fitowa daga Bagadada, bayan duk wahalar da na sha a tafiyata ta farko. Na yi ta tafiya cikin wannan tsibiri ina cewa,"Daga Allah muke, gare shi muke komawa." Ina tafiya ina tangadi ina surutai ni kadai kamar sabon mahaukaci ko wanda aljani ya shafa. Bayan na yi tafiya mai nisa, babu alamun gari ko kauye ko gida sai na yanke shawarar hawa wata doguwar bishiya domin hango abin da ke nesa. Na hau bishiyar na duba ko'ina, Gabas da Yamma, Kudu da Arewa, ban ga kome ba sai itatuwa, can gaba kuma ruwan teku ne iyakar ganin ido. Har zan sauko daga kan bishiyar nan sai na hangi wani abu fari tas can da nisa daga shiyar Kudu. Na sauko na nufi inda wannan abu yake. Da na zo kusa gare shi sai na gan shi kamar dutse, ga shi dai fari tas, girmansa kamar daki, amma kuma siffar kwai. Na zagaya wannan dutse amma ban ga kofar shiga ba ko wata matakala da zan hau samansa. Wannan irin dutse ya ba ni mamaki, sai na yi wata 'yar alama daidai inda nake tsaye a gindin dutsen. Na rika tsagaya shi ina kidaya takun kafar da na yi, da na zagayo inda na yi alamar nan sai na ga na kidaya takun kafa hamsin daidai. Na tsaya ina tunanin yadda zan hau wannan dutse mai santsi, lokacin kuwa rana ta yi tsakiya. Kwatsam sai na ga hasken rana ya gushe wuri ya yi duhu. Sai na yi tsammani ko gajimare ne ya rufe rana, amma da na tuna ai wanna lokacin rani ne, sai tunanina ya canja. Na daga kaina sama da sauri domin ganin abin da ya rufe hasken rana, sai na hangi wani irin tsuntsu mai girman gaske a cikin sararin samaniya, ashe fika-fikansa ne suka rufe hasken rana. Na yi mamaki da girman wannan tsuntsu, gayar mamaki, sai na tuna da wani labari da na taba ji fatake da alhazai na bayarwa. Wai a wani tsibiri da ke tsakiyar teku ana samun wasu irin manya- manyan tsuntsaye wadanda ake kira Rukki. Wai wadannan tsuntsaye sukan fyauce giwa idan tana kiwo, kamar yadda shaho ke fyauce dan tsako, su kawo wa dan jinjirinsu wannan giwa ya cinye ta shi kadai. Nan da nan na gane ashe dutsen nan fari mai santsi dake gabana shirim kamar daki, ba dutse ba ne face kwan wannan tsuntsu, Rukki... zanci gaba Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ links5. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO Daga Littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA Sabuwar Fassarar: Ibrahim Malumfashi, Danladi Haruna, Bukar Mada. ... Sindibad mai tekui ya ci gaba da labarinsa ya ce, yayin da na daga kaina sama domin in ga abin da ya rufe hasken rana sai na ga wani katon tsuntsu, wanda girmansa ba ya misaltuwa, ashe fika-fikansa ne suka rufe hasken ranar. Na yi mamaki gayar mamaki, sai na tuna da wani labari da na taba ji fatake da alhazai na bayarwa. Wai a wani tsibiri da ke tsakiyar teku ana samun wasu irin manya-manyan tsuntsaye wadanda ake kira Rukki. Wai wadannan tsuntsaye sukan fyauce giwa idan tana kiwo, kamar yadda shaho ke fyauce dan tsako, su kawo wa dan jinjirinsu wannan giwa ya cinye ta shi kadai. Nan da nan na gane ashe dutsen nan fari mai santsi dake gabana shirim kamar daki, ba dutse ba ne face kwan wannan tsuntsu, Rukki. Ina nan tsaye kusa da kwan nan ina mamakin sarautar Ubangiji har tsuntsun nan ya sauko kasa. Ya lullube ni tare da kwansa, ya yi kwance, nan take barci ya dauke shi. Tsarki ya tabbata ga Ubangiji wanda ba ya gyangyadi balle barci. Yayin da na ga tsuntsun nan ya yi barci, sai wata dabara ta zo mini. Na tube rawanina na yaga shi, na murda shi ya zama kamar igiya. Na yi damara da shi sa'annan na daure kaina ga kafar Rukki mai kama da jikin bishiya don girma. Nufina idan ya farka daga barci zai tafi neman abinci ya tafi da ni. Ta haka zan sami damar fita daga wannan tsibiri ke nan, watakila ya kai ni kusa ga wani birni ko kauye. Haka na kasance daure ga kafar wannan tsuntsu tun da rana har gari ya kusa wayewa ban runtsa ba, gudun kada ina cikin barci ya tashi da ni ban shirya ba. Da gari ya waye sai Rukki ya farka daga barci, ya yi kuka da karfi ya kada fika-fikansa ya tashi sama da ni daure a jikin kafarsa. Ya yi ta yin sama har sai da na zaci ya kai kololuwar sama ta farko sa'annan sai ya yiwo kasa-kasa a hankali ya sauka cikin wani kwari. Lokacin da na ga tsuntsu ya sauka cikin kwari sai na yi sauri na kwance kaina daga kafarsa. Na fita daga karkashinsa ina neman inda zan boye don kada ya gan ni, watakila ya hadiye ni. Amma sai na ga bai ma lura da akwai wata halitta kusa gare shi ba, saboda kankantata gare shi. Daga nan sai na ga ya tura kafarsa cikin wani katon kogo ya kamo wani abu ya tashi sama da shi. Da na lura da kyau sai na ga wani irin maciji ne mai girman gaske ya kama, yana ta wutsilniya. Ya tafi da shi tun ina kallonsa har ya bace mini. Na yi mamaki matukar mamaki. Ashe ni ban sani ba, a cikin wani irin kwari nake mai fadi da zurfin gaske. Ban gane haka ba sai da na daga kai na sama, sai na gan ni kamar ina cikin rijiya. Yayin da na ga haka sai hankalina ya tashi, na zargi kaina bisa wannan halin da nake ciki. Da ban baro gida ba da duk wannan wahala ba ta same ni ba. Tsibirin da na baro ma ya fi wannan rami kwanciyar hankali. A can ina samun 'ya'yan itace da ruwa, amma nan ban da duwatsu da rairayi babu kome. Babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki! Duk lokacin da na kubuta daga wata halaka sai kuma in kara fadawa cikin wata halakar. Na ci gaba da tafiya a cikin wannan kwari ina tunanin yadda zan fita daga cikinsa. Da na lura da kyau sai na ga ashe rairayin wannan kwari duk lu'ulu'u ne. Da na isa ga bangon da dutse ya yi wa kwarin sai na ga dutsen na jauhari ne mai daraja. Na daga kaina sama amma ban ga wata matakala da zan hau ba da za ta fitar da ni daga cikin wanna kwari. Wannan shi ake kira ga koshi ga kwanan yunwa! Ga dukiya nan ko'ina a cikin kwarin, amma ni da nake neman hanyar fita daga cikinsa ba ta dukiya nake yi ba. Ban da wannan kuma kwarin cike yake da wasu irin macizai masu girman gaske. Kowane maciji girmansa kamar iccen dabino, idan ya bude baki kuwa sai ya hadiye doki. Wadannan macizai sukan boye da rana saboda tsoron tsuntsayen da ke farautarsu irinsu Rukki da mikiya. Sai cikin dare macizan suke fitowa su nemi na su abinci. Yayin da rana ta fara yin ja za ta fadi, sai na fara neman inda zan boye wa wadannan macizai kafin rana ta sake fitowa. Yunwa da kishirwa duk sai suka bace saboda tsananin tsoro. Ina nan ina dube-dube sai na hango wani kogo mai kofa matsattsiya. Na yi sauri na shige cikin wannan kogo, na jawo wani dutse mai fadi na rufe kofar, na ce a cikin raina, "Zan kwana a nan, idan rana ta fito sai in fita in ci gaba da neman hanyar da zan fita cikin wannan rami." Na jujjuya idanuna ko'ina a cikin kogon domin ganin abin da ke ciki. Numfashina ya dauke lokacin da na ga wata macijiya daga can saman wani dutse a cikin kogon da nake, tana kwance bisa kwayayenta tana barci. Nan take jikina ya dauki rawa, gashin jikina ya mimmike, na daga hannuwana sama na fara addu'a ga Ubangijin talikkai. A wannan dare dai ban runtsa ba har gari ya waye. Da na ga hasken rana ya ratso ta cikin kwarin sai na janye dutsen da na rufe bakin kogon na fito waje. Na ci gaba da tafiya ina tangadi kamar mai maye, yunwa kuwa sai dafa ni take yi, ga tsoro cike fal a cikin raina. Ina cikin tafiya ina jan kafafu sai na ga an jeho wani abu daga sama ya fado kusa gare ni, tim. Na yi tsalle gefe guda don tsoro. Da na duba abin da aka jeho sai na ga kamar alfadari ne aka yanka, aka fede fatar, aka cire kai da kafafu aka jeho naman. Na daga kaina sama, amma saboda zurfin kwarin ba zan iya ganin wanda ke bisansa ba. Na yi mamakin abin da ya sa aka jeho wannan nama. Daga nan sai wani labari ya fado mini a rai. Na taba jin fatake na cewa, a wata kasa akwai wani kwari wanda rairayinsa na lu'ulu'u ne, duwatsunsa na zinariya. Wai mutanen kasar kan yanka wata dabba sai su jefa namanta a cikin kwarin. Lu'ulu'un zai lillike naman da aka jefa. Shi kuwa wanda ya jefa dabbar sai ya koma wani wuri ya make yana kallo. Akwai wasu tsuntsaye dake shiga cikin kwarin neman abinci, idan suka ga naman sai su dauko shi su fito cikin kwarin da shi, su sauka bisa wani dutse suna ci. Idan mai dabbar ya ga haka sai ya fito ya kori tsuntsun, ya cire lu'ulu'un da ke jikin naman ya koma gida. Ta haka suke tara dukiya mai yawa. Idan ba ta wannan hanyar ba babu mai iya shiga cikin kwarin balle har ya kwaso abin da ke cikinsa na dukiya. Yayin da na ga an jeho wannan dabba cikin kwari ta fado kusa gare ni, sai labarin fatake ya fado mini ga rai. Nan take sai wata dabara ta zo mini. Ban yi wata-wata ba sai na cika aljihuna da lu'ulu'u na kuma kumsa wani mai yawa a cikin rawanina. Ina cikin dibar lu'ulu'u sai na ga an sake jeho wata dabbar jif, kusa gare ni. Da na gama kwasar abin da nake iya dauka na lu'ulu'u sai na kwanta kasa rigingine. Na dauki dabbabr nan na aza bisa kirjina, ta rufe ni ruf, ba a iya gani na. Na kama wani wuri a jikin dabbar na rike gam. Ina nan kwance karkashin dabbar nan, kamar yadda na zata, sai ga wani katon tsuntsu, mikiya, ta diro bisa naman nan. Ta dauke shi da kafafunta ta tashi sama, ina rike da dabbar, ta fito daga cikin kwarin ta sauka bisa wani dutse mai fadi domin yin kalaci da abin da ta farauto. Tun kafin ta fara cin naman nan sai na ji ana tsawa da kururuwa ana buga itace ga kasa domin dai a tsoratar da ita. Tsuntsuwa ta firgita ta tashi sama ta bar dabbar a nan. Ni kuma sai na ture dabbar daga kaina na mike tsaye. Tufafina duk sun rine da jinin dabbar. Attajirin da ya kori tsuntsuwar nan bai ko kula da ni ba, hankalinsa na ga lu'ulu'un da zai cire daga jikin dabbar. Sai da ya zo kusa ga dabbar sai ya gan ni tsaye kamar gawar da ta tashi. Saboda tsananin tsoro sai ya yi mutuwar tsaye, ya kasa yin gaba balle baya. Ko bakinsa ma ya kasa motsawa balle ya yi mini magana.. zanci gaba insha Allah. 6. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO Sindibad ya ci gaba da labari ya ce, tun kafin tsuntsuwa ta fara cin naman nan sai na ji ana tsawa da kururuwa ana buga itace ga kasa domin dai a tsoratar da ita. Tsuntsuwa ta firgita ta tashi sama ta bar dabbar a nan. Ni kuma sai na ture dabbar daga kaina na mike tsaye. Tufafina duk sun rine da jinin dabbar. Attajirin da ya kori tsuntsuwar nan bai ko kula da ni ba, hankalinsa na ga lu'ulu'un da zai cire daga jikin dabbar. Sai da ya zo kusa ga dabbar sai ya gan ni tsaye kamar gawar da ta tashi. Saboda tsananin tsoro sai ya yi mutuwar tsaye, ya kasa yin gaba balle baya. Ko bakinsa ma ya kasa motsawa balle ya yi mini magana. Amma saboda son dukiya irin ta dan Adam, da ya farfado daga mutuwar tsayen da ya yi, sai na ga ya duka wurin dabbar nan yana duba karkashinta. Ya juya ta gaba daya bai sami lu'ulu'u ko daya ba. Sai ya buga sallallami yana cewa, "Babu sarki sai Allah mai girma da daukaka, wanda muke neman kariyarsa daga sharrin Shaidan jefaffe!" Ya yi ta tafa hannuwa yana salati cike da jimami yana cewa, "Ya aka yi wannan abu ya faru? Shike nan na yi asarar dabbata?" Na matsa kusa gare shi. Yana ganina sai hankalinsa ya komo gare ni. Ya tambaye ni, "Wanene

Chapter 2 of 8