Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
sai da na ji na kai masabar gatari. Na yi hamdala ga Ubangiji da ya kubutar da ni daga kabilar zindirawa. Bayan mutanen nan sun cika kwandunansu da goran yaji, sai suka sanya ni a cikin jirginsu suka tafi da ni zuwa ga nasu tsibiri. Muna zuwa sai suka kai ni ga sarkinsu. Sarkin nan kuwa mutumin kirki ne, ya karbe ni da hannu biyu-biyu cikin fara'a. Bayan mun gaisa sai ya tambayi labarina. Na duka na kwance masa bakin jaka. Sarki da fadawansa suka yi mamaki mai yawa da jin wannan labari nawa, ya umurce ni da ina zauna kusa gare shi. Ya sa aka kawo abinci da nama, muka ci tare da shi. Bayan mun gama muka wanke hannuwanmu da ruwan wardi muka goge da adikon da aka yayyafa wa miski. Na yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Na kuma gode wa wannan Sarki kwarai da gaske bisa ga wannan irin karimci nasa. Bayan an watse daga fada sai na shiga cikin gari ina zagayawa domin ganin yanayin garin da al'ummarsa. Garin cike yake da jama'a, kowa yana harakar gabansa, babu ruwan wani da wani. An bubbude rumfuna ana ta ciniki, kowace rumfa cike da kayan masarufi. Na lura da cewa mutanen garin mutane ne masu hannu da shuni, kuma 'yan kasuwa ne sosai. Hankalina ya kwanta da mutanen wannan gari. Kwanci tashi har na yi abota da 'yan kasuwa masu yawa. Na kasance abin girmamawa a cikin wannan gari kamar wanda ya yi shekara da shekaru. Wani abu da ya ba ni mamaki da mutanen wannan gari shi ne, ban taba ganin sun hau doki da sirdi ba. Kome tsadar doki haka za a hau shi babu sirdi babu wata kwalliya. Hatta Sarki da fadawansa duk haka suke hawan nasu dawakin. daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ12. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA Sabuwar Fassarar: Ibrahim Malumfashi, Danladi Z. Haruna, Bukar Mada. Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce, bayan an watse daga fada sai na shiga cikin gari ina zagayawa domin ganin yanayin garin da al'ummarsa. Garin cike yake da jama'a, kowa yana harakar gabansa, babu ruwan wani da wani. An bubbude rumfuna ana ta ciniki, kowace rumfa cike da kayan masarufi. Na lura da cewa mutanen garin mutane ne masu hannu da shuni, kuma 'yan kasuwa ne sosai. Hankalina ya kwanta da mutanen wannan gari. Kwanci tashi har na yi abota da 'yan kasuwa masu yawa. Na kasance abin girmamawa a cikin wannan gari kamar wanda ya yi shekara da shekaru. Wani abu da ya ba ni mamaki da mutanen wannan gari shi ne, ban taba ganin sun hau doki da sirdi ba. Kome tsadar doki haka za a hau shi babu sirdi babu wata kwalliya. Hatta Sarki da fadawansa duk haka suke hawan nasu dawakin. Ran nan dai sai na kasa hakuri, da aka tashi daga fadanci sai na tambayi Sarki, "Allah ya ba ka nasara, me ya sa ba ku hawan doki da sirdi? Na ga cewa sirdi yana sa mahayi ya ji dadin zama bisa doki, kuma yakan kara wa doki karfi da kuzari." Sarki ya dube ni cike da mamaki, "Menene kuma sirdi? Ban taba jin wannan abu ba tun da nake." "Allah ya ba ka nasara, idan ka yarda zan yi wa dokinka sirdi, ka hau shi ka ji yadda ake ji." Cikin doki, Sarki ya ce ya amince. Na ce a sassako mini itace. Nan take Sarki ya sa aka sassako mini itace irin wanda nake so. Na nemo wani kwararren masassaki, na kwatanta masa yadda zai sassaka sirdi da wannan itace. Na sami tawada na zana masa, a kan itacen, siffar yadda nake so sirdin ya kasance. Masassakin nan gwani ne, nan da nan ya yi kamar yadda nake so. Na samo fata na lullbe sirdin da ita na dinke. Na sami wani masaki ya saka mini rigar sirdin da gashi mai taushi da laushi, kamar yadda na kwatanta masa, na shimfida rigar gashin bisa ga sirdi na dinke ta tare da fatar. Bayan sirdi ya hadu yadda nake sonsa, sai na je ga wani makeri na kwatanta masa yadda zai kera mini likkafu da ragama. Ya aikata yadda na umurce shi. Ya goge su suka yi fari tas, ya shafa musu bulari, suka yi ta daukar ido kamar azurfa. Na sami wani mai tufkar igiya ya tufka mini linzami na alharini. Na hada kayan nan wuri guda. Na tafi bargar Sarki na zabo wani ingarma cikin wadanda Sarki ke hawa. Na daura masa sirdi da likkafu da ragama, na jawo linzami na aza bisa ga sirdi, na ja ragamar doki na nufi wurin Sarki da shi. Sarki ya dubi doki ya cika da mamaki, ko ba kome dokin ya kara kyau. Na nuna masa yadda zai taka likkafa ya hau. Ya taka ya haye bisa doki, na mika masa linzami na fada masa amfaninsa. Ya yi tafiya da doki kamar taki hamsin, ya juyo ya dawo. Nan fa ya shiga gode mini kamar ya dauke ni ya goya. Ya kawo dukiya mai tarin yawa ya ba ni ladar wannan aiki da na yi. Yayin da Wazirin Sarki ya ga sirdi ga dokin Sarki sai ya ce lalle in yi masa irinsa. Nan da nan na hado masa nasa sirdin, shi ma ya yi mini kyautar dukiya mai yawa. Daga nan fa sai fadawa da attajiran gari kowa ya taso yana so a yi masa sirdi. Na hada abokan aikina muka yi ta sassaka siradda muna sayarwa, kasuwa ta bude gare mu. Muka sami dukiya mai yawa wadda ba ta kidayuwa. Na zama hamshakin attajiri cikin kankanen lokaci. Sai ya kasance har daga makwabtan wannan birni ana zuwa sayen sirdin doki gare ni. Na kara samun daukaka ga Sarki, ya rike ni tamkar dansa, barci kadai ke raba ni da shi. Ina nan cikin wannan birni cikin kwanciyar hankali da jin dadi, ran nan ina tare da Sarki muna hirar duniya sai ya takale ni da wata magana, ya ce, "Ka sani ya kai Sindibad, yanzu ka zama daya daga cikinmu, kuma na dauke ka a matsayin dana, har ba na so in rabu da kai. Ina so ka bi umurnina a cikin wannan magana da zan gaya maka yanzu?" Na dukar da kaina kasa cikin ladabi na ce, "Allah ya ba ka nasara, ai yadda ka dauke ni a matsayin danka haka na dauke ka a matsayin ubana. Babu wani abu da za ka umurce ni da shi, face na aikata shi. Menene wannan abu da kake so ka umurce ni da shi?" "Ina so in aura maka kyakkyawar budurwa daga cikin 'ya'yan manyan mutane, mai ladabi da ilmi da biyayya. Ka sani mutum duka bai cika mutum sai fa in yana da mata. Ina so ka yi mini biyayya a kan wannan bukata tawa." Na sunkuyar da kaina kasa cikin tsananin jin kunya, na yi shiru ban ce kome ba. "Ya na ji ka yi shiru ba ka amsa mini ba?" Sarki ya tambaya. Na amsa masa, "Allah ya ba ka nasara, ai don wannan ba sai ka tambaye ni ba. Na amince ka aura mini duk wadda ka ga dama." Sarki ya ce, "To, madalla." Ya sa aka tara alkalai da malamai da shaidu. Aka daura mini aure da wata kyakkyawar budurwa 'yar manyan mutane, wadda mahaifinta ya mutu ya bar mata dukiya mai yawa ta kudi da dabbobi da gidaje da gonaki. Bayan ubanta ya mutu sai Sarki ya dauki nauyin kula da ita. Yarinya ce kyakkyawa tamkar wata dan daren goma sha hudu. Sarki ya aurar da ni ga wata budurwa kykkyawa wacce ta gaji dukiya mai yawa daga mahaifinta. Sarki kuma ya ba ni kerarren gida, na-gani-na- fada, kusa da fadarsa, na tare da amaryata a ciki. Ban da wannan gida kuma Sarki ya ba ni bayi da kuyangi farare da bakake, ya kuma nada ni daya daga cikin waziransa, ya yanka mini albashi da ake biyana kullum. Na zauna cikin dadin rai, na manta da duk wata wahala da na sha tun daga kifewar jirginmu a cikin teku da kuma wahalar da na sha a cikin tsibirin zindirawa. Na zauna tare da matata wadda nake matukar kauna, ita ma tana matukar sona kamar ta hadiye ni. Har na rika cewa a cikin raina, "Babu makawa idan zan koma gida Bagadaza in tafi tare da ita." Sai dai kamar yadda masu iya magana ne ke cewa, kana taka Allah na tasa. Bari ku ji abin mamakin da zai faru. Ina nan zaune da matata cikin tsananin soyayya, sai ran nan matar makwabcina ta mutu. Na zagaya domin in yi masa ta'aziyya sai na same shi cikin tashin hankali da tsananin tsoro. Na yi masa gaisuwar rashin matarsa ina rarrashinsa, "Ka yi hakuri haka Allah ya kaddara. Allan da ya dauke matarka shi za ya kara ba ka wata wadda ta fi ta, ku ci gaba da rayuwarku cikin dankon soyayya." Yayin da makwabcina ya ji zancena sai na ga ya kara fashewa da kuka, ya ce, "Ya kai abokina, ta yaya zan sake auren wata mace bayan saura kwana daya ya rage mini a cikin duniya." Na dafa kafadarsa na ce, "Subhanalillahi! Don me kake yi wa kanka fatar mutuwa ga ka da lafiyarka?" Ya ce mini, "Ai iyakacinka da ni yau, gobe war haka ni ma na kwana kiyama." "Saboda me?" Na tambaye shi cikin mamaki. Ya gaya mini cewa, al'adar wannan birni ce idan daya daga cikin ma'aurata ya mutu, mata ko miji, tare za a rufe su duka biyun da mataccen da mai rai a kabari daya. Wai don kada daya ya ci gaba da rayuwa ba tare da dan uwansa ba, wai soyayyar da aka yi a nan duniya ta dore har can. Ko ya gaya musu ana soyayya a barzahu. Wannan kuwa ko Sarki ne haka za a yi masa. Da na ji haka sai na yi sallallami na ce, "Wannan abu ai bai dace ba, don me za a rufe mutum da ransa tare da gawa? Ya kamata a watsar da wannan mummunar al'ada." Ina nan zaune gidan wannan makwabci nawa ina taya shi jaje, sai mutanen gari ke zuwa kungiya- kungiya suna yi masa ta'aziyyar rasuwar matarsa suna kuma yi masa ban kwana. Daga nan sai ga masu binne gawa sun shigo da sunduki. Suka saka gawar matar a cikin sunduki suka tafi da ita tare da mijinta zuwa bayan gari. Suka isa ga wani tsauni kusa ga gabar teku. Suka share kasar wurin sai ga wani katon dutse mai fadi kamar marufi ya bayyana, suka ciccibi dutsen nan suka dauke shi da kyar suka ajiye gefe daya, ashe rijiya ce aka rufe da dutsen. Da na leka rijiyar nan ban ga iyakar zurfinta ba. Suka dauki sundukin nan wanda gawar matar take ciki suka ingiza cikin wannan rijiya. Daga nan sai suka kama mijin suka daura masa doguwar igiyar kaba mai kwari ga hakarkari. Suka rataya masa gora cike da ruwa, da gurasa kwara bakwai a cikin jaka. Suka rika zura shi cikin rijiyar nan a hankali har ya kai kasan rijiyar, ya kwance igiya daga jikinsa. Mutanen nan suka fitar da igiyar, suka mayar da katon dutsen nan suka toshe bakin rijiyar kamar yadda muka same ta da farko, suka mayar da kasa saman dutsen. Muka tafi muka bar abokina da gawar matarsa a cikin rijiyar. Yayin da na ga abin da ya faru ga makwabcina sai na ce a cikin raina, "Wallahi wannan mutuwa har ta fi ta farko zafi. Gwamma mutum ya mutu bisa gadonsa da a kashe shi da yunwa da kishirwa." Na nufi wurin Sarki na ce masa, "Allah ya ba ka nasara, me ya sa ake rufe mai rai tare da matacce a cikin rami guda?" Sarki ya ce mini ai al'adarsu ke nan kaka da kakanni. Muddin miji ya mutu to za a rufe shi tare da matarsa, haka kuma idan matar ce ta mutu za a rufe ta tare da mijinta. Na tambaye shi, to na ji ku al'adarku ce. Idan irina wanda yake bako matarsa ta mutu, ko ni na mutu fa? Sarki ya ce ai babu banbanci ga kowa. Da na ji haka sai na ji hantata ta dauki rawa, tsoro ya kama ni. Na ji kamar an sanya ni cikin wani irin kurkuku mai kunci, nan take duk sai na tsani wannan birni da al'ummarsa. Na ce a cikin raina, yanzu idan matata ta riga ni mutuwa shi ke nan ni ma na mutu, lalle da sake wai an ba mai kaza kai. Daga nan sai na fara shawarar in rabu da matata ko kuma in tsere daga wannan birni, duk da dai Allah kadai ya san gawar fari tsakanin ni da ita. Na yi iyakar kokarina in kawar da wannan tunani a cikin raina amma na kasa. Inan nan zaune da matata lafiya, sai ran nan ta ce mini kanta na ciwo. Wasa-wasa dai har rashin lafiya ya kai ta kwance. Bayan 'yan kwanaki kadan sai ta ce ga garinku nan. Mutane suka yi ta zuwa suna yi mini ta'aziyya, suna kuma yi mini ban kwana, kamar dai yadda suka yi wa makwabcina. Aka yi wa matata sutura, aka sanya mata tufafi masu tsadar gaske. Aka sanya mata sarka da awarwaro na zinariya. Sai ka rantse da Allah idan ka ce mata sannu za ta ce maka, "mhm!" Aka dauke ta tare da ni aka nufi bayan gari wurin rijiyar nan da aka rufe makwabcina tare da matarsa. Da zuwa sai aka bude bakin rijiyar nan aka jefa matata a ciki. Abokaina kuma suka zagaye ni suna yi mini ban kwana, wasu daga cikinsu har suna zubar da hawaye. Ni kuwa sai na rika kururuwa ina cewa, "Wallahi Allah ya haramta wannan danyen aiki da kuke shirin aikatawa. Ba ku ganin ni bako ne, ba al'adarmu daya da ku ba. Don me za ku rufe ni da raina? Wallahi da na san haka al'adarku take da ban yarda na yi aure ba." Af, babu wanda ya kula da hargowata, suka kama ni da karfi suka daure da igiya, suka zuba mini ruwa a cikin gora da 'yar gurasa guda bakwai, suka zura ni cikin rami kamar dai yadda al'adarsu ta tanada. Da suka ji na sauka kasan ramin sai suka yi mini magana da karfi, wai in kwance igiyar da aka zuro ni da ita cikin ramin daga jikina, ni kuwa sai na ki. Da suka ga ba ni da niyyar kwance igiyar sai suka jeho mini ita cikin ramin suna cewa, tafi da ita idan igiya na amfani a lahira. Suka ja dutse suka rufe bakin rami gam, suka tafi abinsu. Na sami kaina a cikin wani irin rami mai duhu, sai kasusuwan mutane ko'ina bargaja kamar an watse kara. Ga wani irin doyi da hamami na tashi, cikin dan kankanin lokaci sai na ji iska na gagara ta shaka. Na zargi kaina da kaina, na ce a cikin raina, "Wace wauta ta sa na yi aure a cikin wannan birni? Babu shakka duk abin da ya same ni ba ni da kaico." Na ci gaba da cewa, babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki. Duk lokacin da na kubuta daga halaka sai in kara fadawa cikin wadda ta fi ta. Wallahi mutuwa a cikin ruwa ta fi wannan mummunar mutuwa da zan yi. Ina ma a ce na mutu a cikin teku lokacin da jirginmu ya kife, ko kuma yunwa ta kashe ni a cikin tsibirin zindirawa. Na ci gaba da zama cikin wannan rami, ba na iya banbance dare balle rana, bakina kuwa ba ya rufuwa, kodayaushe ina karanta duk addu'ar da ta fado mini cikin rai. Na jefa kaina bisa kasusuwan matattu na yi kwance, hawaye na zuba daga idanuna. Na ci gaba da rokon Allah ya kubutar da ni daga wannan hali da nake ciki. Na yi ta jiran mutuwa ta zo ta dauke ni, amma ba ta zo ba... Whatsapp only pls 08032767547 kuna tare neda Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ13 HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO Na jefa kaina bisa kasusuwan matattu na yi kwance, hawaye na zuba daga idanuna. Na ci gaba da rokon Allah ya kubutar da ni daga wannan hali da nake ciki. Na yi ta jiran mutuwa ta zo ta dauke ni, amma ba ta zo ba. Bayan wani lokaci sai yunwa ta fara dafa ni, makoshina kuma ya bushe don kishirwa. Sai na jawo 'yar gurasar nan da aka turo da ita na ci daya, na sha makwalwa guda ta ruwa. Daga nan sai na tashi na fara dube-dube cikin ramin ina nazarinsa, da yake yanzu idona ya saba da duhun ramin. Na ga cewa rami ne mai fadin gaske, daga kowane bangare na bangayen ramin akwai hanyoyi da suka huda bangayen suka yi rariya. A barbaje ko'ina a cikin ramin kasusuwan mutane ne wasu har sun yi fari saboda dadewa. Na matsa nesa daga tsakiyar ramin na sami wata rariya wadda babu kasusuwan mutane a wurin na zauna. Na kasance cikin wannan rami har 'yar gurasa da ruwana suka kusa karewa. Da ma kuwa kullum sau daya nake ci na sha makwalwar ruwa guda. Tuni wata zuciya ta ce mini, "ka ci kadan daga gurasar, ka sha ruwa kadan, wa ya sani ko kafin ka cinye ta Allah ya koro maka da wani taimako." Rannan dai na kusa cinye 'yar gurasata, ina zaune ina tunanin abin da zan yi idan gurasar nan ta kare, sai na ji an bude bakin ramin nan, wani irin haske mai karfi ya kwararo cikin ramin. Watakila wani ne za a jeho cikin ramin, na ce a cikin raina. Na hangi kawunan mutane suna lekowa cikin ramin, daga nan sai aka jeho sunduki cikin ramin ya fado tim. Sai kuma na ga an zuro wata mace da igiya, tana ta sheka kuka, an ratayo mata goran ruwa da jakar gurasa kamar yadda sukan yi bisa al'ada. Bayan ta sauko kasan ramin nan sai na kura mata ido daga inda nake make, na gan ta kyakkyawar mace ce, amma ita ba ta gan ni ba saboda idonta bai saba da duhun ramin ba. Da suka zuro ta sai suka janye igiyar suka mayar da dutse suka toshe bakin ramin. Na dauki kashin kwaurin wata gawa, na lallaba ta bayan matar nan, na yi mata kum daya bisa madigar kai, ta kwallara ihu ta fadi kasa sumammiya. Na kara kwantara mata kashin nan bisa kai karo na biyu da na uku har sai da na tabbatar da ta mutu. Na lalube gurasa da ruwan da aka zuro ta da su, na kuma ciccire kayan zinariyar da aka yi mata kwalliya da su, da ma ga al'adarsu duk mata da kayan kwalliya masu tsada ake zuro su. Da na cire dukan kayan zinariyar da ke jikin wannan mace sai na koma lungun da nake na make. Na rika cin gurasar nan kadan-kadan ina shan ruwa kadan. Haka na kasance cikin wannan hali tsawon lokaci, duk lokacin da aka turo wasu sai in kashe mai ran in dauke gurasarsa da ruwa, in cire zinariyar matar, da haka na tara zinariya mai yawan gaske. Ni kuwa idan aka gan ni babu abin da zai raba ni da gawa, ga shi dai na rame na bushe kamar kwarangwal, 'yar gurasa da ruwan da nake sha don dai na rayu ne ba wai don ina koshi ba. Rannan ina kwance cikin ramin nan ina tunani, sai na ji wani abu yana motsi cikin ramin nan kamar ana jujjuya gawarwakin. Na ce a cikin raina, "mene ne wannan? Kar dai a ce kura ce ta shigo cin gawarwakin mutane. Wannan dabba akwai shegen kwadayi." Na yi zumbur na mike tsaye, na lalubo katon kashin nan da nake kashe mutane da shi na rike shi gam, na lallaba na nufi inda motsin ke fitowa. Ko da dabbar nan mai tonon gawarwaki ta gan ni sai ta ruga a guje ta bi ta wata rariya da ke jikin bangon ramin ta bace. Na bi cikin wannan rariya da rarrafe, bayan na yi nisa sai na fara hango wani haske daga can nesa, sai ya fito sai ya bace, kamar hasken tauraruwa idan tana nisawa. Na nufi wannan haske da sauri, ina matsawa kusa hasken na kara karfi, daga nan sai na tabbatar da cewa kofa ce mai fita waje zuwa ga bayan kasa. Na ce a cikin raina, "lalle ruwa ba ya tsami banza! Ko dai wannan kofa an yi ta ne domin wani dalili na daban ko kuwa haka ta tsiru bisa kudirar Ubangiji. Na tsaya ina tunani shin in ci gaba da tafiya ne ko in koma da baya, domin ina jin tsoron in kara fadawa cikin wani hatsarin wanda ya fi na baya. Wata zuciyar ta ce in ci gaba da tafiya, kome ta fanjama, fanjam. Na tafi har na iso ga kofar nan, sai na ga ashe dai kofa ce mai fita waje daga bayan tsaunin nan wanda kusa gare shi ne aka gina rijiyar da ake jefe mutane. Sai dai ga alamu, da, kofar karama ce, dabbobi ne suka kara mata girma domin shiga cikin rijiyar wajen cin gawarwakin mutane. Yayin da na ga haka sai zuciyata ta yi fari, hanyar tsira ta samu bayan da har na debe tsammani daga kubuta. Na bi ta kofar na fita sai na gan ni a bayan dogon tsauni wanda daga bayansa birnin da na baro ne, a gabana kuwa ruwan teku ne. Saboda tsawon wannan tsauni ba zai yiwu mutum ya hau shi ya gangara bayansa ba, don haka sai ya zama tamkar ganuwa tsakanina da birnin nan. Na gode wa Allah da ya tsirar da ni daga halaka. Bayan na gama nazarin sabon wurin da na tsinci kaina, sai na bi ta cikin rariyar nan na koma cikin rijiya, na tattaro duka kayan zinariya da tufafin mata masu tsada na fito da su gefen tsaunin nan. Na sami wuri na kafa 'yar bukka, ina jiran taimakon da Allah zai turo mini wanda zai yi sanadin fitata daga wannan tsibiri. Na rika komawa cikin rijiyar kullum idan an jeho mutane sai in kashe mai ran, in dauke abincinsa da dukiyar da aka turo, hatta tufafinsu ba na bari. Na dawwama bisa ga wannan hali, ta haka na jibge dukiya mai tarin yawa a cikin wannan bukka tawa. cikin tsibiri bayan tsauni, na rika komawa cikin rijiyar nan ina kashe duk wanda aka turo ina dauke abincinsa da ruwa. Na debe tarin dukiyar da ake turo gawarwakin nan da su na dangin zinariya da azurfa da tagulla da lu'ulu'u da sauran duwatsu masu daraja, hatta tufafin mamatan ban bari ba. Na jibge dukiya mai yawa a cikin bukkata, na zauna zaman jiran tsammanin warabbuka, wai malam ya ki noma don zakka. Wata rana ina zaune bakin bukkata sai na hangi wani babban jirgi a tsakiyar teku zai wuce, tozayen ruwa na yin sama da kasa da shi. Nan da nan sai na dauki yankin adiko na daura shi ga wata doguwar sanda, na nufi bakin gabar teku ina daga wannan sanda sama ina karkada adikon nan cikin iska. Allah kuwa ya nufi masu jirgi suka hango ni, suka karkato da jirginsu zuwa gare ni. Da suka iso kusa gare ni sai Madugunsu ya ce, "kai, mutum ko aljani? Me kake yi cikin wannan tsibiri kai kadai kusa ga wannan tsauni da ba mu taba ganin wani mutum ba?" Wallahi ni mutum ne dan uwanku," na amsa musu. Na ci gaba da cewa, "ni falke ne jirgi ya yi hatsari da mu, duka 'yan uwana suka halaka, ni kuwa Allah ya kubutar da ni da dukiyata zuwa ga wannan wuri bayan na kama wani allon jirgin na hawo, iska ta turo ni nan. Na yi bukka na ajiye kayana ina jiran Allah ya koro mini da wani jirgi da zai wuce ta nan." Da fatake suka ji labarina sai suka tausaya mini, suka dauke ni cikin jirginsu duk da dukiyata, bayan na daure ta wuri guda cikin zannuwa. Na kawo lu'ulu'u mai yawa na ba Madugun jirgi na ce masa, karbi wannan ladar kubutar da ni da kuka yi daga cikin wannan tsibiri. Amma sai Madugu ya ki karbar dukiyar da na ba shi, ya ce, "ai mu ne ya kamata mu taimake ka, domin ka fi kowa bukatar taimako a halin yanzu. Idan muka tsinci falken da jirgi ya yi hatsari da shi, mukan taimaka masa, mu tarairaye shi, mu kawo masa abinci da nama. Idan muka same shi tsirara, mu ba shi tufafi ya sanya. Haka za mu yi ta kulawa da shi har mu iso wani birni inda za mu hada shi da mutanen kasarsa, daga nan kuma mu ba shi guzuri daga cikin dukiyarmu. Hala ba ka ji masu iya magana na cewa, Allah na taimakon wanda ya taimaki dan uwansa ba." Na duka na yi ta gode musu. Na gode wa Allah Ubangijin talikai da ya kubutar da ni daga halaka, na manta dukkan wahalar da na sha. Abu daya ne ba zan manta da shi ba har in koma ga Allah. Duk lokacin da na tuna lokacin da aka rufe ni cikin rami da gawar matata sai hantata ta motsa don tsoro. Muka ci gaba da tafiya cikin jirgi a yanayin teku mai dadi, daga wannan tsibiri zuwa wancan har muka iso ga wani babban tsibiri wai shi Tsibirin Beli. A cikin wannan tsibiri akwai wani babban birni wanda tsayinsa da fadinsa tafiyar kwana biyu ne. Bayan mun bar wannan tsibiri da kwana shida sai muka isa wani tsibirin mai suna Tsibirin Kala, shi kuwa tsibiri ne daga cikin kasashen Hindu. Wannan tsibiri na karkashin mulkin wani babban Sarki ne mai girman runduna. Mutanen tsibirin gwanaye ne wajen samar da kafur da rama. Kwanci tashi muka ci gaba da tafiya har Allah mai girma da daukaka ya nufe mu da isowa birnin Basara cikin kwanciyar hankali da dadin rai. Na kwana biyu a Basara, daga nan na nufi gidana a Bagadaza, Gidan Aminci. Na sami gidana lafiya, babu abin da ya canza a cikinsa. 'Yan uwa da abokan arziki suka rika zuwa suna yi mini barka da dawowa. Na yi ta rarraba musu dukiya. Na kwashi tarin dukiyar da na dawo da ita na jibge a cikin taska. Na ciyar da marayu da miskinai da zawarawa. Na koma ga tsohon halina na bushasha, na shiga cikin dukiya ina bundum-bundum. Wannan shi ne labarin tafiyata ta hudu a cikin teku. Idan Allah ya kai mu gobe zan gaya muku labarin tafiyata ta biyar wadda ta fi wannan ban mamaki. DAGA Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ14 HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO Wannan shi ne labarin tafiyata ta hudu a cikin teku. Idan Allah ya kai mu gobe zan gaya muku labarin tafiyata ta biyar wadda ta fi wannan ban mamaki. Da Sindibad Matafiyi ya gama bayar da wannan labari sai Sindibad dan dako ya rike baki cike da mamakin wannan labari da ya ji. Aka hallaro musu da abinci da abin sha. Sindibad dan dako da Sindibad Matafiyi suka ci tare a cikin akushi daya. Sauran tajirai kuma suka ci daga nasu akussan. Bayan sun gama cin abinci

Chapter 5 of 8