Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 8
tausayin mu ba, ya koro mana da hanyar kubuta, babu shakka dukkanmu halakakku ne. Don Allah ku yi ta addu'a, yalla a sami daya daga cikinku wanda Allah zai karbi addu'arsa ya kubutar da mu." Yayin da muka ji bayanin Madugu sai muka dukufa ga rokon Allah, amma ba a jima da wannan magana ba sai wata kakkarfar iska ta taso ta yi ta juya jirginmu kamar ana juya waina. Lokacin da muka ga haka sai duk muka fara sallallami muna rokon juna gafara, don mun tabbatar da halakarmu ta zo. Iska ta kwashi jirginmu ta buga shi ga wani babban dutse a tsakiyar teku, nan take ya karairaye, allo-allo, muna gani dukiyoyinmu suka dulmiye cikin ruwa. Wa ma yake ta dukiya ana maganar ceton rai. Da yawa daga cikin fatake suka halaka a cikin ruwa sai 'yan kadan da Allah ya tarfa wa garinsu nono, suka kama dutsen nan suka hau. Ina daga cikin wadanda suka hau dutse. Dutsen nan kuwa dogon dutsen ne, saboda tsawonsa har ba a iya ganin karshensa, ya tafi har cikin giza-gizai. Dutsen kuma daga kasa ya rufe ko'ina kamar an gina katanga. Ashe dutsen nan bisa wani dan karamin tsibiri yake. Da muka gangara cikin tsibirin sai muka ga babu kome a cikinsa na daga itatuwa ko ciyawa, daga yashi sai yashi, sai kuma allunan jiragen ruwa masu yawa wadanda suka kakkarye, ga kuma dukiya nan babu adadi wadda ruwan teku ya turo bisa tsibirin daga duk wani jirgi da ya yi hatsari kusa ga dutsen nan. Muka sami korama wadda ruwanta yake gangarowa daga saman dutse, ruwan mai dadi ne. Ruwan koramar nan ya yi wutsiya biyu, daya wutsiyar na gangarawa cikin teku, daya kuma sai ta bi tsawon dutsen daga kasa ta koma karkashinsa. Fatake kuwa da suka ga dukiya tsibi-tsibi a cikin wannan tsibiri, sai suka zama tamkar mahaukata, suka rika diba suna ta watsawa sama suna kururuwa. Na nufi wurin koramar nan domin in sha ruwa, sai na ga tsakuwar da ke cikinta duk lu'ulu'u ne mai darajar gaske, rairayin wurin kuwa duka dussar zinariya ce da sauran jauhari iri-iri, sai daukar ido suke yi wal, wal, wal, kamar mudubi. Haka kuma a cikin wannan tsibiri akwai sandunan Siniya da sandunan Kumriya, ga kuma ambar mai yawa wanda zafin rana ke narkawa yana gudana gefen koramar nan yana shiga cikin teku. An ce irin wannan ambar din ne mai gangarawa cikin teku wasu dabbobi da ke cikin ruwa kan hadiye saboda kanshinsa, amma da zarar sun hadiye shi za su ji cikinsu yana zafi, kamar ana hura musu wuta, dole sai sun amayar da shi. Ambar din da suka amayar zai daskare bisa ruwa ya canja launi, daga karshe teku ta tura shi gefenta, idan fatake da matafiya suka gan shi, wadanda suka san shi sai su diba su yi ta cika goruna, su narka, suna sayarwa, shi ne turaren ambar. Yanzu kuwa ga ambar a cikin wannan tsibiri, gangariyarsa. Ba a samun irin wannan ambar a cikin birane, saboda babu wani dan Adam da ke iya zuwa wannan tsibiri har ya same shi, wanda ake samu shi ne wanda dabbobin ruwan nan kan amayar. Muka ci gaba da zagayawa cikin tsibiri muna kallon ikon Allah, muna cike da mamakin irin tarin dukiyar da ke cikinsa, zukatanmu kuma cike da zullumin abin da zai faru gare mu. Bayan wani lokaci sai yunwa ta far mana, muka yi ta bincike cikin tarkacen dukiyoyin nan har muka sami wata jaka da gurasa a cikinta, duk ta bushe. Wannan gurasa muka rika ci kadan- kadan, muna jin tsoron ta kare babu wani abinci. Karfinmu ya fara karewa, ciwo ya kama wasu daga cikin fatake, suka rika mutuwa daya bayan daya, ba mu gushe ba cikin wannan hali muka rage saura 'yan kadan, da yawa daga cikin mu sun mutu. Duk wanda ya mutu sai mu yi masa wanka mu yi masa sutura, daga cikin wata hajar suturu da muka samu, mu haka kabari mu rufe shi. Ba mu gushe ba cikin wannan hali har sai da dukkan fataken nan suka mutu, na rage saura ni kadai ina gararamba a cikin tsibirin da saurar 'yar gurasar da ba ta wuce guda biyar ba. Duk lokacin da na tuna abokan tafiyata sai in buga salati ina cewa, "babu tsimi babu dabara face daga Allah madaukakin Sarki, da ma ni na fara mutuwa kafin saura. Yanzu idan na mutu shi ke nan babu mai rufe ni."17 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO Sindibad Matafiyi ya ci gaba da labarinsa yana cewa, kuna ji na ya ku abokaina, yayin da dukkan abokan tafiyata suka mutu a cikin tsibiri, na kasance saura ni kadai a cikin sa da 'yar gurasar da ba ta wuce guda biyar ba. Sai na tona wani rami mai zurfi da fadi ina cewa a cikin raina, "wannan shi ne kabarina. Idan abincina ya kare, na fara sansanar kanshin mutuwa, in kwanta a ciki in mutu, iska ta tura rairayi ya rufe ni." Na yi ta zargin kaina da kaina bisa ga barin gida da na yi, idan dai don dukiya ne, ai ina da ita a gida wadda tsawon rayuwata ba zan iya cinye ko da rabin ta ba. To me ya sa na baro gida? Wata zuciya ta amsa mini da, "kaddara!" Na tuna irin wahalhalun da na shiga a tafiye-tafiyen da na yi a baya, da yadda Allah ke kubutar da ni bayan na debe tsammani daga kubuta. Na tambayi kaina, anya zan kubuta daga wannan tafiya kuwa? Ban gushe ba ina nadama sai wani tunani ya zo mini game da wutsiyar koramar nan mai shiga karkashin dutse. Na ce babu shakka in ga inda ruwan wannan korama ke zuwa, wa ya sani ma ko ruwan ya bulla har bayan dutsen, watakila ma in sami 'yan Adam a wurin? Sai na debo sandunan Siniya da na Kumriya, na samo alluna masu fadi daga fasassun jiragen ruwan nan, na adanta dan karamin kwale-kwale wanda zai iya daukata da wasu kayayyaki. Bayan na gama shirya wannan jirgi yadda nake son shi, sai na jefa shi cikin koramar, kun san mutum game da son dukiya, sai na debi lu'ulu'u da sandunan Siniya da na Kumriya, na kwashi rairayin zinariya, na debi turaren ambar daskararre, gangariya, mai yawan gaske na cika goruna da shi. Na sanya duk wadannan kaya a cikin kwale-kwale na shiga, na tuka, na rika bin wutsiyar korama mai shigewa cikin dutse. Na ce a cikin raina, "idan Allah ya nufa in tsira, sai in tsira, idan kuwa Allah bai nufa in tsira ba gwamma in mutu cikin koramar nan da in mutu cikin rairayin tsibiri. Na tafi cikin jirgi kamar yadda aka fada cikin wannan waka: Tashi ka motsa ka bar nan wurin, Gida ne na tsoro da halin tsiya. Ka nemi wadata cikin duniya, Akan kama zomo da son juriya. Kasan duk wahala takan zan gudu, Sauki yakan zo bayan shan wuya. Wurin duk da an kaddara mutuwar, Mutum za ya komo ba ya tirjiya. Ina gargadin ka a kan sirrukanka, Ka boye su gam-gam cikin zuciya. Ban gushe ba ina tuka jirgi ina bin tsawon korama har na kawo inda take shiga karkashin dutse. Wurin kuwa wani irin kogo ne mai girman gaske. Kwale-kwale ya shiga cikin kogon da ni, na ci gaba da tuka shi ruwa na ja na. Yayin da na shiga cikin kogon nan sai wani irin duhu ya mamaye ni har ba na iya ganin abin da ke gabana. Bayan haka kuma sai na ji kamar ina gangarawa kasa ne a cikin wani kwari mai zurfi. Duk da haka dai ban karaya ba, na ci gaba da bin ruwan koramar nan. Ina cikin tafiya sai na kawo wani wuri inda fadin koramar ya ragu har kwale-kwalena na taba gabar koramar, kuma na ji kaina na tabo rufin wannan kogo, babu damar juyawa da baya, a haka dole na ci gaba da tafiya ina tunanin idan fadin koramar nan ya ci gaba da raguwa ai kuwa jirgina ba zai iya ci gaba da tafiya ba, watakila ya makale a nan, shi ke nan na kawo kaina mahalaka. Na ci gaba da tafiya cikin kwale-kwalena, kaina na ta buguwa da bangon dutsen da ke samansa, da na ga haka sai na yi kwance rub- da-ciki cikin jirgi, na bar wa Allah ikonsa. Jirgina sai tafiya yake yi kwana da kwanaki, ni dai ba na iya bambance dare balle rana. Rannan dai ko barci ne ya kwashe ni, ko kuwa suma na yi, ban sani ba. Sai dai na farka na ji wata sassanyar iska na bugu na, da na bude idona sai na ga haske fayau. Na dubi inda nake na ga har yanzu dai ina kwance ne a cikin jirgin nan a gefen wata babbar korama. Na yi karfin hali na mike zaune, in duba haka sai na ga ashe mutane ne suka zagaye ni suna kallo, kamar masu kallon wata bakuwar halitta. Na dube su da kyau sai na ga ashe mutanen Hindu ne da mutanen Abasiniya. Yayin da suka ga na mike zaune ina kallon su sai wani daga cikin su ya yi mini magana, amma ban ji abin da yake fada ba, saboda ba na fahimtar wannan harshe. Duk abin nan da ke faruwa sai na ga kamar mafarki ne nake yi. Yayin da mutanen nan suka gane ba na fahimtar zancensu, sai wani daga cikin su ya canja harshe ya yi mini magana da Larabci, "aminci ya tabbata a gare ka, ya kai dan uwana. Wanene kai? Daga ina ka zo wannan wuri? Don Allah menene bayan dogon dutsen nan wanda babu wani mutum da ya taba zuwa wurin?" Na mayar masa da sallamar da ya yi mini da farko, "aminci ya tabbata a gare ka, ya dan uwana." Maimakon in ba shi amsar tambayoyinsa sai ni kuma na kora masa tawa tambayar, "don Allah wannan wane wuri ne? Ku kuma wadanne irin mutane ne?" Ya amsa mini, "mu manoma ne. Mun fito ne domin mu yi ban ruwa ga kayan lambunmu sai muka same ka cikin wannan kwale-kwale kana barci. Muka kyale ka har sai da ka farka da kanka. Gaya mana yadda aka yi ka zo nan." Na ce musu su kawo mini abinci idan suna so su ji labari, na fada musu yunwa nake ji kamar za ta halaka ni. Nan da nan suka kawo mini akushi cike da abinci, na ci mai isa ta na koshi, na ture akushi gefe na yi hamdala ga Sarki Allah. Bayan hankalina ya kwanta, karfin jikina ya dawo, sai na kwashe dukkan labarina na fada musu, na kuma fada musu abin da ya faru gare ni lokacin da na shiga karkashin dutsen nan. Da suka ji labarina sai suka rika tafa hannuwa don mamaki, suka ce da junansu, "babu makawa mu kai shi ga Sarki ya gaya masa wannan labari mai ban mamaki." Suka kwashe ni duk da kwale-kwalena da kayan da na labto masa na lu'ulu'u, da jauhari, da zinariya, da turaren ambar, da sauran dukiya mai yawa, suka kai gaban Sarkinsu wanda ake kira Sarkin Sarandib. Suka fada masa labarina duka, Sarki ya yi mamaki, ya yi mini barka da arziki, ya marabce ni da girmamawa. Ya sake tamabaya ta labarina, na duka na fede masa biri har wutsiya, ya yi mamaki, matukar mamaki. Na tafi ga kayana na debo lu'ulu'u da sandunan Siniya da sandunan Kumriyya da turaren ambar mai yawa na kawo wa Sarki. Ya karba ya yi godiya mai yawa, ya sa mini albarka. Sarki ya sa aka ba ni wani gida nasa nan kusa ga fada, na zauna tare da shi cikin dadin rai da girmamawa. Tsibirin Sarandib yana bisa wani yanki ne na duniya wanda lokutan dare da yini duka sa'o'i goma sha biyu ne maimakon ashirin da hudu, don haka dare da yininsu takaitacce ne ainun ba kamar na sauran wasu yankuna na duniya ba. Tsawon tsibirin awo tamanin ne, fadinsa awo talatin. Tsibirin na kewaye da wani babban dutse mai tsawo, wanda ya yi wa tsibirin kamar baka, fadin dutsen daga farkonsa zuwa karshensa tafiyar kwana uku ce ba tsayawa. Sa'annan daga can karshen dutsen akwai wani kwari mai zurfi da fadi. Daga gefen dutsen akwai itatuwa da tsire-tsire na kayan yaji masu yawa, daga cikin dutsen kuma ana samun nau'o'in jauhari iri-iri, kamar su zinariya da dangoginta. A cikin kwarin kuma akwai irin su lu'ulu'u da sauran wasu ma'adinai masu daraja. Nakan tafi wurin wannan dutse ina kallon sa, ina mamakin irin ajiyar da Allah ya yi a cikinsa, idan na gama kallon sa sai in koma fada wurin Sarki. Sau da yawa fadawa kan tambaye ni game da mulkin Halifa Haruna Rashid. Nakan gaya musu irin yadda yake tafiyar da mulkinsa cikin adalci da yadda yake kaunar talakawansa. Idan suka ji haka sai su yi ta mamaki suna sa masa albarka. Haka ma idan na hadu da fatake sai mu zauna mu yi ta hirar kasashensu da irin yadda sarakunansu ke tafiyar da mulkinsu, ta haka na sami labrin kasashe masu yawa. Akwai ma lokacin da Sarki da kansa ya tambaye ni labarin Halifa Haruna Rashid da yadda yake gudanar da mulkinsa, na gaya masa kome na daga mulkin Halifa a Bagadaza. Sarki ya yi mamaki ya ce, "wallahi Halifa kuwa ya cika Sarki mai adalci. Babu makawa idan ka tashi komawa kasarku zan ba kyauta ka kai masa." Na ce ma Sarki, "na ji, na karba. Zan kuwa shaida masa cewa kana matukar kaunarsa saboda adalcinsa." Na ci gaba da zama tare da Sarki cikin girmamawa da kwanciyar hankali. Muna nan kan haka, wata rana ta daga ranaku sai na ji labarin cewa akwai fataken da za su tashi zuwa Birnin Basara, na ce a cikin raina, "ai kuwa bai kamata fataken nan su bar ni ba." Na tafi wurin Sarki na fadi kasa na sumbaci kafafunsa, na fada masa labarin fatake, na ce ina so in bi su zuwa gida. Sarki ya dube ni ya ce, "duk abin da ka yi daidai ne. Idan ka ga dama kana iya ci gaba da zama da mu har bayan ranka, idan kuma ka ga dama ka koma kasarku, babu mai hana ka." Na kara sunkuyar da kai kasa na ce, "wallahi ina jin dadin zama da kai, Allah ya ba ka nasara. Ba domin zuciyata na shaukin ganin 'yan uwana da abokaina ba, da na zauna tare da kai har abada." Sarki ya sa aka kira masa Madugun fatake, ya damka ni a kan kulawarsa. Ya biya mini kudin jirgi da kudin kayana. Ya sa Ma'aji ya kwaso mini dukiya mai yawa daga taskarsa, ya ba ni kyauta. Ya kuma kawo wata gagarumar kyautar ya ba ni, ya ce idan na isa gida lafiya in kai wa Halifa. Ya kuma kawo wasika ya ba ni, ya ce, "ka kai wa Halifa wannan wasika, hannunka da nasa. Ka ce muna gaishe shi sosai." Ita wasikar an rubuta ta ne bisa fatar wata dabba wadda ta fi fatar tinkiya kyau, nesa ba kusa ba, launin fatar kuwa rawaya ne. An yi rubutun da launin shudi, irin na ruwan teku ko sararin samaniya. Abin da wasikar ta kunsa shi ne: Aminci ya tabbata a gare ka. Daga Sarkin Hindu mai rundunar giwaye dubu, mai fadar lu'ulu'u da zinariya dubu. Bayan godiya ga Allah Madaukakin Sarki, da salati ga shugabanmu Annabi Muhammadu da Alayensa, ga wata 'yar kyauta nan da muka bayar a kawo maka, muna fatar za ka yi murna da ita. Mun dauke ka dan uwa kuma masoyinmu saboda irin labarin alherinka da muka ji, muna fatar za mu sami bayanin wannan wasika daga gare ka. Sai dai kyautar ba wata kyautar a-zo-a-gani ba ce idan muka yi la'akari da irin karfin arzikinka. Amma ai an ce, dirhamin masoyi ya fi zinari dubu na makiyi. Wassalam, mun bar ka lafiya. Sai mun ji daga gare ka. Kyautar da Sarki ya bayar a kai wa Halifa kuwa ita ce ta wani babban gora cike da zababben lu'ulu'u mai darajar gaske. An yi wa goran nan ado da zane-zane iri-iri, masu ban sha'awa, da ruwan zinariya da azurfa, an shafe shi da bulari, yana ta kyalli. Akwai kuma karaga wadda aka shimfida fatar maciji bisanta, irin fatar macizan nan masu hadiye giwa. A jikin fatar akwai wasu dabbare-dabbare ko digo-digo, girmansu kamar dirhami, an ce duk mai kallon fatar macijin nan, to, ba ya rashin lafiya har abada. Akwai kuma miskali dubu na sandunan Hindiya, da kuma wata kuyanga kyakkyawa tamkar rana. Yayin da lokacin tashin mu ya kusa, sai na yi sallama da Sarki da dukkan abokaina. Da ranar tafiya ta zo na shiga jirgi tare da sauran fatake, muka mika cikin bahar. Iska ta yi mana dadi, muka tafi muna addu'ar neman kariya daga Allah Ubangijin talikkai. Cikin kudurarsa da ikonsa kuwa muka isa birnin Basara lafiya, bayan na huta kwana biyu, sai na shirya kayana duka na nufi Bagadaza, Gidan Aminci. Da isa ta Bagadaza ko gidana ban leka ba, sai na nufi fada wurin Halifa. daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ18 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO Bayan godiya ga Allah Madaukakin Sarki, da salati ga shugabanmu Annabi Muhammadu da Alayensa, ga wata 'yar kyauta nan da muka bayar a kawo maka, muna fatar za ka yi murna da ita. Mun dauke ka dan uwa kuma masoyinmu saboda irin labarin alherinka da muka ji, muna fatar za mu sami bayanin wannan wasika daga gare ka. Sai dai kyautar ba wata kyautar a-zo-a-gani ba ce idan muka yi la'akari da irin karfin arzikinka. Amma ai an ce, dirhamin masoyi ya fi zinari dubu na makiyi. Wassalam, mun bar ka lafiya. Sai mun ji daga gare ka. Kyautar da Sarki ya bayar a kai wa Halifa kuwa ita ce ta wani babban gora cike da zababben lu'ulu'u mai darajar gaske. An yi wa goran nan ado da zane-zane iri-iri, masu ban sha'awa, da ruwan zinariya da azurfa, an shafe shi da bulari, yana ta kyalli. Akwai kuma karaga wadda aka shimfida fatar maciji bisanta, irin fatar macizan nan masu hadiye giwa. A jikin fatar akwai wasu dabbare-dabbare ko digo-digo, girmansu kamar dirhami, an ce duk mai kallon fatar macijin nan, to, ba ya rashin lafiya har abada. Akwai kuma miskali dubu na sandunan Hindiya, da kuma wata kuyanga kyakkyawa tamkar rana. Yayin da lokacin tashin mu ya kusa, sai na yi sallama da Sarki da dukkan abokaina. Da ranar tafiya ta zo na shiga jirgi tare da sauran fatake, muka mika cikin bahar. Iska ta yi mana dadi, muka tafi muna addu'ar neman kariya daga Allah Ubangijin talikkai. Cikin kudurarsa da ikonsa kuwa muka isa birnin Basara lafiya, bayan na huta kwana biyu, sai na shirya kayana duka na nufi Bagadaza, Gidan Aminci. Da isa ta Bagadaza ko gidana ban leka ba, sai na nufi fada wurin Halifa. Aka yi mini iso na shiga wurinsa, na kawo kyautar Sarkin Hindu na ba shi. Ya tambaye ni labarin Sarkin, na gaya masa. Yayin da Halifa ya karanta wasika sai ya tambaye ni, "ya kai Sindibad, shin abin da Sarkin nan ya rubuta kuwa gaskiya ne." Na amsa masa, "ya shugabana, Wallahi duk abin da ya rubuta gaskiya ne. Ni na gani da idona fiye da abubuwan da ya rubuta a cikin wannan wasika. Duk lokacin da zai yi wa talakawa jawabi ana daura masa karagarsa bisa bayan toron giwa, tsayin wannan giwa ya kai zira'i goma sha daya. Daga gefensa kuma sai fadawansa su yi sahu biyu, kowane sahu a gefen hannunsa daya. A gabansa wani sadauki zai tsaya rike da mashi na zinariya, a bayansa da wani sadaukin rike da takobi ta zinariya. Idan kuma zai yi kilisa zai hau doki tare da mahaya dubu, kowane mahayi cikin sutura ta alfarma wadda aka yi wa kwalliya da jauhari iri daban- daban. Idan za a fita kilisar sai wani mai shela ya rika shela yana cewa, 'wannan shi ne Sarkin da babu kamarsa a duk cikin Sarkuna.' Haka mai shelar nan zai ci gaba da yi wa Sarki kirari, wanda ban rike kirarin ba duka, amma daga karshe yakan ce, 'wannan shi ne Sarkin da ke da kambin da duk wani Sarki bai da irin sa.' Idan wannan mai shelar ya kare, daga can kuma sai wani ya dauka yana cewa, 'duk da wannan Sarki zai mutu, babu makawa wata rana zai mutu.' Sai shi kuma wancan na farko ya ce, 'tsarki ya tabbata ga Sarkin da bai mutuwa har abada.' Saboda adalcin wannan Sarki, ya Halifa, ko alkali babu a birninsa, dukkan mutane suna tsare dokoki sau-da-kafa, babu mai yin laifi a cikin su." Halifa ya yi shiru yana mamaki, daga nan sai ya ce, "yadda karfinsa yake wasikarsa ta rigaya ta bayyana mini. Babu makawa shi Sarki ne mai karfin mulki da karfin arziki." Daga nan sai na kwashe labarun sauran tafiye- tafiyen da na yi da hatsarin da na shiga a cikin kowace tafiya da abubuwan mamakin da na gano, na fada wa Halifa Haruna Rashid. Yayi mamaki matukar mamaki, ya sa aka rubuta wadannan labaru cikin takardu aka adana su a dakin karatu domin na baya su karanta su karu da abubuwan da ke cikin su. Halifa ya yi mini godiya mai yawa, ya kawo kyautar dukiya wadda har ta fi wadda na fita da ita zuwa fatauci yawa, ya sallame ni. Na tashi na nufi gidana cike da farin ciki, na iske gidana lafiya. 'Yan uwa da abokai suka yi ta zuwa suna yi mini maraba, na rarraba musu kyaututtuka. Na bayar da sadaka ga mabukata, na ciyar da marayu. Na ci gaba da rayuwata kamar yadda na saba cikin dadi da shagali, na manta dukkan wahalhalun da na sha a baya. Wannan shi ne labarin tafiyata ta shida a cikin teku, idan Allah ya kai mu gobe zan gaya muku labarin tafiyata ta bakwai kuma ta karshe wadda ta fi wannan ban mamaki. Da Maigida ya kare wannan labari sai ya sa aka kawo abinci da abin sha, suka ci tare da dan dako, da suka gama cin abinci ya kawo dinari dari ya ba shi, suka yi sallama. Sauran tajirai suka tafi suna mamakin wannan labari da suka ji. Sindibad dan dako ya tafi gidansa cike da mamakin wannan labari. Ya kwanta yana dokin gari ya waye domin ya ji labarin tafiya ta bakwai da mai gida ya yi a cikin teku. Gari na wayewa dan dako ya yi salla, ya kimtsa ya nufi gidan takwaransa. Bayan duka sauran tajirai sun hallara sai Maigida ya fara labarin tafiyarsa ta bakwai kuma ta karshe. TAFIYAR SINDIBAD TA BAKWAI A CIKIN TEKU. Sindibad Matafiyi ya ce, "ku sani ya ku abokaina, lokacin da na dawo daga tafiyata ta shida sai na ci gaba da harkokina kamar yadda na saba, na manta kome na daga wahalhalun da na sha a baya. Ina nan haka sai sha'awar tafiye-tafiye ta motsa mini a cikin rai, na ji babu abin da nake so kamar in shiga duniya, in ga mutane da al'adunsu. Daga nan sai na shiga shiye-shiryen zuwa fatauci. Na hada haja mai yawa wadda zan fita da ita, da lokaci ya yi, sai na yi sallama da 'yan uwana da abokai, na nufi Birnin Basara. Ina zuwa kuwa na sami wani babban jirgi zai tashi da fatake masu yawa, na biya kudi na saka hajata a cikin jirgi. Na yi abota da fataken nan, da lokacin tafiya ya yi sai jirginmu ya motsa, muka tsunduma cikin teku, muka bar birnin Basara cikin aminci. Muka yi ta tafiya cikin yanayi mai dadi har muka iso ga wani babban birni mai suna birnin Sindu, muka yada zango cikin wannan birni muka dan taba ciniki. Daga nan sai muka ci gaba da tafiya cikin aminci, muna hira da juna. Muna cikin wannan hali sai wata iska mai karfi ta fara kadawa, ba a jima ba sai hadarin ruwa ya hadu baki kirin. Aka kuwa goce da ruwa kamar da bakin kwarya, muka lullube hajojinmu da barguna gudun kada ruwa ya bata mana kaya. Muka yi ta addu'ar Allah ya fisshe mu cikin wannan hatsari. Muna cikin wannan hali sai muka ga Madugu ya tattare rigarsa ya cusa cikin wando, ya haye saman jirgi yana waige-waige cikin teku. Daga nan sai muka ga ya cire rawaninsa ya jefar cikin jirgi, ya rika kuka yana marin fuskarsa kamar dan yaro, ya tuge gemunsa ya watsar. Da ganin haka sai hankulanmu suka tashi, muka tambaye shi, "ya Ra'isu, me yake faruwa ne?" Sai ya amsa mana da cewa, "ku yi ta kank ya ku fatake. Ku sani cewa iska ta karkatar da jirginmu daga tafarki, mun shiga mahaukaciyar teku daga cikin tekunan duniya masu hadari." Yana gama fadin haka sai ya sauko da sauri, ya shiga wani dan sako inda ya ajiye kayansa. Ya dauko wata 'yar karamar jaka mai launin shudi wadda aka yi da audugar rimi. Ya debo wani garin magani kamar toka ya zuba shi bisa wani dan faifai, karami. Ya cudanya garin maganin da ruwan teku, ya jira zuwa wani dan lokaci, ya lakaci garin maganin ya sansana ga hancinsa, ya kuma lasa ga harshensa. Sa'annan ya bude sundukinsa ya jawo wani littafi ya bude shi ya fara karantawa da karfi yadda kowa zai ji a cikin jirgin, "ku sani ya ku fatake, a cikin wannan littafi akwai abin al'ajabi, daga ciki shi ne duk mutumin da ya sami kansa cikin wannan teku, har abada ba ya tsira daga cikinsa domin ana kiran wannan teku da suna Mazaunin Sarki. A cikin wannan teku ne sundukin da aka rufe shugaba Sulaimanu dan Dawuda. A cikin wannan teku akwai macizai manya-manya masu munin siffa tare da wasu irin kifaye wadanda duk jirgin da ya ratso ta cikin tekun za su hadiye shi duk da kayan da ke cikin sa." Yayin da muka ji haka sai tsoro ya kama mu, ba mu ankara ba sai muka ji an dauke jirginmu cak daga saman ruwa aka kuma sako shi ya fado cikin ruwan. Daga nan fa sai muka rude muka shiga addu'a babu ji, babu gani, muna neman Allah ya kubutar da mu daga wannan hali da muke ciki. Can sai muka ji wata irin kara mai kama da aradu, muka firgita, don tsoro nan take wasu daga cikinmu suka some, masu karfin hali su ne wadanda suka saki fitsari cikin wando. kuna tare ne da Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ19 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO Can sai muka ji wata irin kara mai kama da aradu, muka firgita, don tsoro nan take wasu daga cikinmu suka some, masu karfin hali su ne wadanda suka saki fitsari cikin wando. Kwaram sai ga wani katon kifi ya bayyana a gaban jirginmu, girman wannan kifi kamar tsauni yake. Sai kuma muka ga wani kifin ya bayyana wanda ya fi na farkon girma. Kafin ayi haka sai kifi na uku ya taso saman teku, wannan kifi duk ya fi sauran biyun girma da muni. Ba zai yiwu in bayyana muku irin halin da muka shiga na tsoro ba. Kifayen nan uku suka rika zagaya jirginmu, kamar kudan zuma na zagaya hure kafin ya sauka kansa ya tsotsi zaki. Daga nan sai babban ya bude bakinsa zai hadiye jirginmu, girman bakin nan nasa tamkar kofar gari.

Chapter 7 of 8