Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
sai Sindibad Matafiyi ya kirgo dinari dari ya ba dan dako, suka yi ban kwana ya tafi. Sauran tajirai ma suka fita suna mamkin wadannan labaru da Sindibad mai teku ke bayarwa, domin kullum suka zo sai su ji labarin yau ya fi na jiya dadi da ban mamaki. Suka yi ta alla-alla gobe ta yi domin su ji labarin tafiyarsa ta biyar wadda ya ce ta fi sauran da ya yi a baya ban mamaki. Haka Sindibad dan dako ya koma gida yana mamaki, bayan ya yi salla sai ya kwanta barci zuciyarsa cike da tunanin labarin da ya ji. Da gari ya waye ya tashi ya yi salla ya yi wuridi, sai ya kimtsa ya nufi gidan Sindibad Matafiyi. Yayin da sauran tajirai suka hallara sai mai gida ya fito ya harde bisa abin zamansa. Aka gaggaisa da juna, aka kawo musu abinci suka cika tumbinsu, suka dauraye makogwaronsu da abin sha mai sanyi. Daga nan sai mai gida ya fara bayar da labarin tafiyarsa ta biyar a cikin teku. TAFIYAR SINDIBAD TA BIYAR A CIKIN TEKU Kuna ji abokaina, bayan na dawo daga tafiyata ta hudu na ci gaba da sha'anina kamar yadda na saba, na manta da duk wasu wahalhalu da na sha a baya. Bayan wani lokaci mai tsawo, rannan ina zaune gaban gidana ina shan iska, ina tunanin duniya, sai bakin halin nan nawa na son tafiye-tafiye ya motsa. Na ji babu abin da nake so kamar in sake shiga cikin duniya, in ga duniya, duniya ma ta gan ni, don an ce na zaune bai ga gari ba. Nan take sai na shirya kayan haja masu yawa na yi niyyar fita zuwa fatauci. Na yi ban kwana da abokaina da 'yan uwa, na nufi birnin Basara. Da zuwana sai na nufin bakin teku inda jiragen ruwa ke tashi zuwa sauran sassa na duniya. Na tarar da wani jirgi sabo fil a bakin teku. Jirgin ya ba ni sha'awa, na yi cinikinsa gaba daya aka sallama mini. Na sa kayana a ciki, na dauko hayar matuka, na sayi bayi wadanda za su rika yi mini hidima. Wasu daga cikin fatake suka biya ni kudi suka saka kayansu a cikin jirgin. Kafin mu fara tafiya sai da aka yi addu'a aka shafa Fatiha don neman tsari daga hatsarin teku da kuma neman sa'a bisa ga fataucin da za mu tafi. Yayin nan jirgi ya motsa, ya nausa da mu cikin teku. Muka yi ta tafiya daga wannan birni zuwa wancan, daga wannan tsibiri zuwa wancan, daga wannan teku zuwa waccan, muna saye muna sayarwa, muna kuma kashe kwarkwatar idonmu a duk birni ko tsibirin da muka yada zango. Har wata rana muka iso ga wani babban tsibiri wanda babu kome a cikinsa sai rairayin hamada. A cikin tsibirin muka hangi wani farin abu kamar dutse mulmulalle mai siffar kubba, rabinsa a kafe cikin yashi, girman wannan dutse kamar rumbun ajiye hatsi. Sauran fatake suka nufi wurin farin dutsen nan, ni kuwa na yi zaune cikin jirgi ina kallon su. Ashe abin nan da suka gani ba dutse ba ne face kwan tsuntsuwar nan da na taba ba ku labari mai suna Rukki. Fatake suka sami duwatsu suka fara bugun kwan nan. Wani daga cikinsu ya rugo wurina ya ce mini, "fito ka ga wani irin daki na farin dutse mai ban mamaki da muka gani a cikin wannan tsibiri." Ko da na je kusa da dutsen nan sai na gane ko menene. Na yi musu tsawa ina cewa, "kar ku fasa wannan dutse, ba dutse ba ne face kwan wata tsuntsuwa mai suna Rukki. Idan kuka fasa shi tsuntsuwar nan za ta zo ta kakkarya jirginmu ta halaka mu gaba daya." Af, kafin in rufe bakina har sun fashe wannan kwai, wani irin ruwa mai yawa mai yauki ya fito daga cikin kwan, daga nan sai dan tsuntsun ya biyo wannan ruwa ya fito. Kafin mu san abin da ake ciki sai muka ga wuri ya yi duhu, hasken rana ya bace. Wata iska mai karfin gaske ta taso har muna faduwa kasa. Muka daga kawunanmu sama mu ga ko hadari ne ke tasowa, sai muka ga ashe tsuntsun nan ne Rukki da muka fasa wa kwai ya taso. Da ya ga mun fasa masa kwai sai ya rika yin wani irin kuka mai karfi kamar aradu, nan take sai ga wasu tsuntsayen biyu irin sa suna shawagi bisa ga kawunanmu. Da na ga haka sai na kira matukan jirgi da sauran fatake na ce musu, mu yi gaggawar komawa cikin jirgi mu bar wannan tsibiri kafin tsuntsayen nan su halaka mu. Muka fada cikin jirgi da gudu, matuka suka tuka da sauri muka juya wa tsibirin nan baya. Da tsuntsayen nan suka ga haka sai suka dauko duwatsu manya-manya da kafafunsu, girman kowane dutse kamar daki, suka biyo mu. Tsuntsu na farko ya sako dutsensa daidai kan jirginmu, cikin zafin nama matukan jirgi suka kauce wa wannan dutse, ya fado dab da jirginmu. Karfin fadowar dutsen ya sa jirginmu ya tangada kamar zai kife, Allah ya kiyaye dai bai kife ba. Matukan jirgi na kokarin shawo kan jirgi sai tsuntsu na biyu ya sako nasa dutse, wannan karon sai dutse ya sauka a tsakiyar jirginmu, nan take jirgi ya tarwatse, ya yi dai-dai. Dukkan fatake da hajarmu suka nutse cikin ruwa, ni kuwa Allah ya taimake ni na kama wani allon jirgi na hau, na yi ta iyo da kafafuna iska na tura ni har na isa bakin wani tsibiri. Na isa shajaran majaran, na gaji likis ga kuma yunwa da kishirwa na koda ni. Na ja jiki na shiga cikin tsibiri, na yi kwance kamar matacce saboda gajiya da yunwa. Bayan na huta, sai na tashi na fara tafiya cikin wannan tsibiri. Tsibiri ne mai yalwar itatuwa da furanni, da koramu suna gudana. Ga 'ya'yan itatuwa nunannu, da tsuntsaye masu launi daban- daban suna shawagi tare da rera wakoki masu kwantar da hankali. Kasan tsibirin kuma ciyawa ce ta fito kore shar ta lullube wurin lif kamar an shimfida darduma. Wannan tsibiri da kyawo yake kamar wani yanki ne na aljanna. Na tsinki 'ya'yan itace na ci na koshi, na sha ruwan korama na kore kishirwa. Hankalina ya dawo, na yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki.Na sami inuwa mai sanyi na zauna har sai da rana ta fadi, duhun dare ya fara shigowa, ban ga kowa ba, ban ji muryar kowa ba sai kukan tsuntsaye. Daga nan sai na kwanta a wannan wuri na mimmike, barci kuwa ya yi awon gaba da ni. Ban farka ba sai da gari ya waye. Bayan gari ya waye sai na tashi na ci gaba da tafiya a cikin tsibirin, ban gushe ba ina tafiya har na iso ga wani dan tabki wanda ruwan koramu ke taruwa a cikinsa. Na iske wani dan tsoho tukuf zaune a gindin wannan tabki, jikinsa duk tsumma, ya daura igiyar rama ga kwankwasonsa. Na ce a cikin raina, "watakila wannan dan tsoho shi ma jirginsu ne ya karye Allah ya kubutar da shi zuwa wannan tsibiri." Na matsa kusa gare shi na yi masa sallama, sai ya amsa mini da hannu, amma bai yi magana ba. Na tambaye shi, "Baffa, me ya zaunar da kai wannan wuri?" Ya yi doguwar ajiyar zuciya, ya yi mini alama da hannu kamar yana cewa, "samari, ka taimake ni ka dauke ni bisa kafadarka, ka kai ni karshen waccan korama." Ya nuna wajen da hannunsa. Na dubi inda ya nuna da hannunsa. Na ce a cikin raina, "bari in taimaki wannan dattijo, watakila ba shi da lafiya ne. Wa ya sani ko sanadin taimakonsa Allah ya yi mini rahama." Na duka na dauke shi bisa wuyana, na kai shi wurin da ya nuna mini. Na ce masa sauko na kawo ka inda ka ce. Amma sai tsohon nan ya ki sauka, maimakon ya sauka ma sai ya kara makalkale mini wuya da kafafunsa. Na ga kafafun baki kirin, sirara lullube da gashi, kamar kafafun dawaki har da kofato. Da na ga wadannan irin kafafu nasa sai na tsorata, na yi niyyar in jefar da shi in gudu, amma sai na kasa cire shi daga jikina, domin ya makalkale wuyana gam, numfashi ma da kyar nake yi. Ya kara makalkale mini wuya har na kasa sheda, na fadi kasa don wuya. Maimakon mugun tsohon nan ya kyale ni yayin da ya ga na fadi kasa, sai ya sake gyara zama bisa wuyana yana jira in tsahi. Da ya ga ba ni da alamun tashi sai ya sa duga- dugan kafarsa ya fara buguna ga hakarkari. Wayyo Allah! Zafin wannan bugu ba ya misaltuwa, kamar ana sa guduma ana buguna ga awazzai. Ban san lokacin da na mike tsaye ba da sauri, na ci gaba da tafiya kamar dokin da ake yi wa kaimi. Ya yi ta nuna mini wurare da hannunsa inda yake so in kai shi, daga wannan bishiya zuwa waccan, daga wannan tabki zuwa wancan. Idan ya ga na rage sauri sai ya buga mini busassun kafafun nan nasa ga hakarkari, sai in zabura in kara mai. Haka tsohon nan ya yi ta wahalar da ni dare da rana, ya yi fitsari bisa wuyana, ya yi kashi bisa wuyana. Na zama dokinsa tsakanin karya da gaskiya, dare da rana yana bisa wuyana, ko barci zai yi sai dai ya yi bisa wuyana. Idan zai yi barcin sai ya nannade wuyana da kafafunsa, ya kwanta bisa gadon bayana, idan ya farka sai ya yi mini ishara da mu tafi. Na zargi kaina da kaina bisa taimakon wannan mugun tsoho, na gwammace mutuwa da wannan bakar wahala. Na rika cewa a cikin raina, "faufau ba zan kara taimakon kowa ba tsawon rayuwata." Haka na kasance cikin tsananin azaba da wahala, tsawon zamani. Ban gushe ba cikin wannan hali, wata rana ina yawo da tsohon nan bisa wuyana har na zo wani wuri inda gorunan duma suka fito, sun zuba 'ya'ya manya-manya a kasa. Na ciri gora daya na fafe shi daga sama na yi masa 'yar kofa karama, na katse tuwon da ke cikinsa na zubar, na shanya shi ga rana har ya bushe. Na samo 'ya'yan inabi na yi ta matse ruwansu a cikin goran nan har na cika shi fal da ruwan 'ya'yan inabi. Na ajiye goran nan a rana tsawon kwanaki har sai da na tabbatar cewa ruwan inabin nan ya zama giya. Na dauki goran nan na rika sha daga giyar nan ina samun kuzarin da nake daukar wannan tsoho, kuma tana taimaka mini wajen mance damuwar da nake ciki. Na ci gaba da shan giyar inabi har wata rana tsohon nan ya yi mini ishara da hannu yana tambaya ta, "menene wannan abu da kake sha?" Na ce masa, "wannan shi ne ruwan farin ciki, mai kore dukkan damuwa, mai sa nishadi a cikin zuciya." Na kurbi giya na yi sassarfa da shi cikin itace. Daga nan kuma sai na yi ta tikar rawa ina waka cikin farin ciki. Yayin da tsohon nan ya ga haka sai ya miko hannunsa alamun in ba shi wai shi ma ya sha. Saboda tsoronsa da nake ji ban ko yi musu ba, sai na mika masa goran giya. Ya karba ya daga gora sama, makwal, makwal, makwal, sai da ya shanye duka giyar da ke ciki. Yana gama shanyewa sai shegiyar ta fara aiki, abinka da bakon giya, sai ya jefar da goran nan kasa ya mace. Ya rika wata irin jijjiga bisa wuyana kamar wanda doki ke sukuwa da shi. Daga nan sai na ji shar ya sako mini fitsari ga jiki, ya jika mini tufafina duka da fitsari. Giya fa ta hau kan tsohon nan, sai na ji dukkan gabobinsa sun saki, kafafunsa da ya nannade wuyana da su sun warware, nan take ya fita daga cikin hankalinsa. Ina ganin haka ban yi wata-wata ba sai na riki kafafunsa da hannuwana biyu, na cire shi daga kan wuyana, na yi hajijiya da shi na kwantara kafuri ga kasa... DAGA Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ15 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO ga giya ta buge tsoho, duka gabobin jikinsa sun saki, sai na riki kafafunsa na cire shi daga kan wuyana, na yi hajijiya da shi na kwantara ga kasa. Gudun kada ya farka daga maye ya kara cutar da ni, sai na dauko wani katon dutse na kwantsama masa bisa kai. Kansa ya fashe, kwanya ta tarwatse ko'ina, bai ko shura ba ya mutu cikin maye. Na tafi na bar mushen banza a nan, ina mai rokon Allah ya kona shi da wuta mafi radadin azaba. Na yi wa Allah godiya da ya raba ni da shaidanin tsohon nan. Na ci gaba da kasancewa cikin tsibiri ni kadai, ina ci daga 'ya'yan itace ina shan ruwan koramu. Na kasance ina zama kusa ga gabar teku ko Allah zai koro da wani jirgi da zai wuce ta kusa ga wannan tsibiri. Wata rana kuwa ina zaune bakin gaba ina kallon ruwan teku ina tunanin abin da ya faru a baya, na tambayi kaina da kaina, "anya kuwa zan koma gida daga wannan tafiya tawa?" Kamar an ba ni amsa, sai na hangi wani jirgi daga nesa yana keta ruwan teku, ya tinkaro wannan tsibiri da nake ciki. Jirgi ya iso bakin gaba ya tsaya, daga dama gare ni, nesa da inda nake tsaye ina kallon sa. Mutanen da ke cikin jirgin suka yi ta fitowa suna shiga cikin wannan tsibiri. Yayin da na ga haka sai na nufi wurin su. Suna ganina sai suka zagaye ni suna kallo. Suka tambayi labarina da dalilin zuwana wannan tsibiri. Na kwashe labarina duka na gaya musu. Suka cika da mamaki suka ce, "ka sani cewa tsohon nan da ya hau bisa wuyanka ana ce masa Shaihul Baharu, ba mutum ba ne, tsohon dan ruwa ne. Bai taba hawa wani mutum ya sauka daga gare shi ba har sai mutumin ya mutu, idan kuma ya mutu sai ya cinye gawar. Kai ne mutum na farko da ya hau har ya sauka daga gare ka ba tare da ka mutu ba." Daga nan sai suka kawo mini abinci iri-iri suka girke a gabana, na zauna na ci na koshi. Suka ba ni sabbin tufafi na saka, na watsar da na jikina domin tuni sun zama tsummokara. Bayan sun huta a cikin wannan tsibiri, sai suka saka ni cikin jirgi na tafi tare da su. Muka yi ta keta ruwan teku har Allah ya kawo mu wani birin a bakin teku, wannan birni ana kiransa Birnin Birai. Gidajen wannan birni duka masu tsawo ne kamar benaye. Birnin zagaye yake da ganuwa, yana da babbar kofa daya ta shiga mai wani irin kyaure na marke mai karfi, wanda aka adanta da karafuna domin kara masa karfi. Wannan kofa tana kallon teku, wanda duk zai shiga birnin, to, sai in ya fito ne daga bangaren teku. Bayan birnin kuwa tsaunuka ne masu tsawo, babu kome a saman su sai birai. Kodayake sunan wannan birni Birnin Birai, amma ba biran ne a ciki ba mutane ne. Dalilin da ya sa ake kiransa Birnin Birai saboda biran da ke zagaye da birnin ne wadanda suke yi wa mutanen cikinsa ta'adi daga lokaci zuwa lokaci. Har ta kai ma kullum da dare sai mutanen birnin su shiga cikin 'yan kananan jiragen ruwa su shige cikin teku su kwana saboda tsoron barnar wadannan birai. Yayin da na ji wannan labari sai na ji gabana ya fadi, domin na san arangamar da na taba yi da wasu birai. Muka shiga cikin wannan birni domin kashe kwarkwatar ido, ni kuwa da karambani sai na ratse ta wani lungu na rabu da abokan tafiyata. Lokacin da na gama duba wannan birini sai na nufi bakin teku inda jirginmu yake, lokacin kuwa marece ya yi, duhu ya fara sauka. Ina zuwa sai na tarar da babu jirgi, babu dalilinsa, abokan tafiyata sun tafi sun bar ni. Na yi zaune cike da bakin ciki mara misaltuwa, na yi ta zubar da hawaye kamar ruwa. Ina nan zaune cikin wannan hali sai ga wani mutum daga cikin mutanen birnin ya zo wurina. Yayin da ya lura da halin da nake ciki sai ya ce mini, "amma kai bako ne ko?" "I, ni bako ne matafiyi," na amsa masa, "mun zo wannan birini tare da abokan tafiyata, bayan mun gama yawo cikin birnin da na dawo sai na tarar da sun tafi sun bar ni." Mutumin ya ce, "Allah Sarki. Tashi mu tafi, kada ka kwana cikin wannan birni birai su halaka ka." Na ce, "To." Na tashi na bi shi zuwa ga wani kwale-kwale nasa, na shiga tare da shi. Na ga sauran mutanen birnin duk sun shiga cikin nasu jiragen ruwa, muka shiga cikin teku muka kwana. Bayan gari ya waye sai duk mutane suka koma cikin birni suka ci gaba da kasuwancinsu. Haka na ga mutanen wannan birni sun kasanace, duk wanda ya kuskura ya kwana cikinsa sai dai da safe a isko gawarsa, biran nan sun kashe shi. Da zarar asuba ta yi sai biran su fice daga cikin birnin su koma bisa tsaunuka suna cin 'ya'yan itace, haka ake kullum, ga mutum da kerarren gida amma ba shi da ikon kwana ciki. Birnin nan yana nesa kwarai da kasashen bakar fata. Na ga abubuwan mamaki da yawa a cikin wannan birni, amma babban abin da ya fi ba ni mamaki shi ne, wata rana muna cikin kwale- kwale inda muka saba kwana ni da abokina, sai ya tambaye ni, "abokina, shin ba ka da wata sana'a ce ta hannu da za ka rika yi a cikin wannan birni namu kana samun kudi? Ka ga kafin ka tashi tafiya ka sami guzuri." Na amsa masa, "ni falke ne mai arziki kwarai da gaske, domin har jirgin ruwa na mallaka, sai dai jirgin ya yi hatsari cikin teku ya nutse da dukiyata mai tarin yawa." Na ba shi labarin abin da ya faru gare ni, na kara da cewa, "ban da fatauci ban iya wata sana'a ta hannu ba." Lokacin da ya ji haka sai ya yi shiru yana tunani. Daga nan sai ya kawo wata jaka da aka yi da auduga ya ba ni, ya ce, "amshi wannan jakar ka cika ta da 'yan kananan duwatsun da ke bakin teku. Ka tafi tare da mutanen da zan hada ka da su, ka aikata abin da ka ga sun aikata. Da yardar Allah madaukakin Sarki za ka sami dukiya fiye da wadda ka rasa a hatsarin jirgi." Muka tafi bakin teku tare da shi, na tsinci tsakuwa manya da kanana na cika jakar nan da su. Muna nan sai muka ga wasu mutane suna fitowa daga cikin birni kowane yana dauke da jaka irin tawa. Abokina ya je kusa gare su ya ce musu, "ku taimaki wannan mutum, bako ne. Ku tafi tare da shi ku koya masa abin da kuke yi, ko ya sami sana'ar kore wa bakinsa kuda. Ku kuma Allah zai biya ku a kan taimakon bako." Suka ce mun ji mun yarda. Muka gaisa da su, na yi sallama da abokina na bi wadannan mutane. Muka yi ta tafiya cikin daji har muka iso ga wani kwari mai fadin gaske. Babu abin da ke cikin wannan kwari sai wasu irin dogayen bishiyoyi masu tsayin gaske, jikin bishiyoyin kuma sumul yake babu ta yadda za a yi a hau saman su. Muna shiga cikin wannan kwari sai muka tarar da birai masu yawa suna barci karkashin wadannan bishiyoyi, suna jin motsinmu sai suka farka, suka bazama cikin daji da gudu, wasu kuma suka haye saman itatuwan nan suna kallon mu, suna yi mana gwalo. Sai abokan tafiyata suka tsaya, suka bude jakarsu suka rika dauko tsakuwa guda-guda suna jifan biran da suka haye saman dogayen bishiyoyin nan. Su ma birai sai suka rika tsinko 'ya'yan itacen suna jifar mu da su, wai su rama. Da na dubi 'ya'yan itacen da suke jifar mu da su sai na ga ashe kwakwa ce irin ta kasar Hindu. Sai ni ma na je ga wata bishiya wanda na ga birai da yawa sun taru samanta, na yi ta jifarsu da tsakuwa suna jeho ni da 'ya'yan kwakwa. Na yi ta tsince 'ya'yan kwakwar ina zubawa cikin jakata, ko kafin tsakuwata ta kare har jakata ta cika da 'ya'yan kwakwa. Sauran abokaina kowa ya cika jakarsa da 'ya'yan kwakwa, daga nan sai muka juya zuwa gida. Ko da muka isa har marece ya yi. Na nufi wurin abokin nan nawa dan kirki, wanda ya hada ni da wadannan mutane, na ba shi abin da na samo, na kuma yi masa godiya mai yawa. Amma sai ya ki karbar 'ya'yan kwakwan nan, ya ce mini, "ka tafi da su cikin birni ka sayar ka amfana da kudin. Ka ci gaba da yin haka kullum." Ya kawo mabudin gidansa ya ba ni, ya ce, "idan ka samo 'ya'yan kwakwar, ka zabe masu kyau ka adana a cikin gidana, ka sayar da wadanda ba su da kyau. Idan ka bar wannan birni namu za ka sami dukiya mai yawa daga 'ya'yan kwakwar da ka tara. Domin da yawa fatake kan zo takanas domin sayen wadannan 'ya'yan kwakwa su kai kasashensu su sayar." "Allah ya yi maka albarka," na ce masa. Na rika fita kullum tare da mutanen nan masu dibar 'ya'yan kwakwa, suka rika nuna mini itatuwa wadanda ke yin 'ya'ya masu kyau. Cikin 'yan kwanaki kadan na tara 'ya'yan kwakwa zababbu masu yawan gaske, na kuma sami kudi daga wadanda nake sayarwa kullum. Na rika sayen kayan haja ina ajiyewa. Da kadan-kadan na tara dukiya mai yawa a cikin wannan birni. Ina nan kan haka, wata rana sai ga wani babban jirgin fatake ya zo wannan birni. Suka saya, suka sayar, da yawan su sai na ga sun sayi 'ya'yan kwakwa domin komwa da su kasashensu. Na je ga abokina na gaya masa labarin zuwan jirgi, na ce masa ina so in koma kasarmu, cikin 'yan uwana. Ya ce mini, wannan daidai ne. Na yi masa godiya mai yawa, muka rabu muna kuka don sabo. Na tafi ga Madugun jirgi na nemi izinin tafiya tare da su. Ya amsa mini babu gardama. Na dauko hajata da na tara a wannan birni, da 'ya'yan kwakwa na sanya cikin jirgi. Da lokacin tafiya ya yi, aka kwance jirgi muka tafi cikin teku, muka bai wa birnin Birai baya. Muka yi ta bin garuruwa da birane, mu saya, mu sayar, na rika sayar da 'ya'yan kwakwar nan da kudi masu yawan gaske, cikin dan kankanin lokaci sai na mayar da dukiyata da na yi asara har na ninka ta ninkin-ba-ninki. Daga cikin biranen da muka shiga har da wani birni wanda mutanen cikinsa ba su da wata sana'a sai noman citta da tafarnuwa da kayan yaji, na sayi masu yawa domin za a sami riba gare su a Bagadaza. Daga wannan birni sai muka wuce zuwa wani tsibiri mai suna Tsibirin Usirata, a nan na sayi sandunan Indiya bayan na sayar da wasu daga cikin 'ya'yan kwakwa. Daga nan kuma sai muka ci gaba da tafiya bayan kwana biyar muka iso ga wani tsibirin, a nan kuma na sayi sandunan Siniya masu daraja fiye da sandunan Indiya. Sai dai su mutanen wannan tsibiri maguzawa ne, babu ruwansu da wani addini, sun mai da shan giya kamar shan ruwa, zina kuwa a wajen su ba su dauke ta a bakin kome ba. Haka suke kara zube kamar dabbobi. Daga wannan tsibiri kuma sai wani tsibirin, shi kuma mutanen cikinsa ba su da wata sana'a sai a ba su kudi su yi nitso cikin teku su lalabo wa mutum lu'ulu'u. Na ba da 'ya'yan kwakwa aka lalubo mini lu'ulu'u mai yawan gaske. Haka dai muka ci gaba da tafiya daga wannan tsibiri zuwa wancan, daga wannan birni zuwa wancan. Har Allah mai girma da daukaka ya nufe mu da isowa birnin Basara lami lafiya. Bayan na huta kwana biyu, sai na kwashi kayana sai Bagadaza, Gidan Aminci. Na ishe gidana lafiya. 'Yan uwa da abokai suka yi ta zuwa suna yi mini barka, a wannan tafiya ma na dawo da dukiya mai yawan gaske. Na bayar da kyaututtuka ga abokaina, na rarraba sadaka ga mabukata, na ciyar da miskinai da marayu. Na ci gaba da sha'anina na bushasha na manta da duk wahalhalun da na sha a baya. Wannan shi ne labarin tafiyata ta biyar, idan Allah ya kai mu gobe zan fada muku labarin tafiyata ta shida, wadda ta fi wannan ban mamaki. Aka kawo musu abinci da abin sha, suka ci suka koshi. Sindibad Matafiyi ya ba Sindibad dan dako dinari dari, ya sallame shi. Sauran tajirai suka yi sallama da mai gida suka tafi suna mamakin wannan labari da suka ji. Haka shi ma Sindibad dan dako ya tafi yana mamaki, ya kwanta barci yana alla-alla gari ya waye domin ya koma gidan Sindibad Matafiyi ya ji labarin tafiyarsa ta shida. Gari na wayewa dan dako ya kimtsa ya nufi gidan Sindibad Matafiyi. Bayan sauran tajirai sun hadu an kawo musu abinci sun ci, sai mai teku ya fara labarin tafiyarsa ta shida. daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ 16 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO TAFIYAR SINDIBAD TA SHIDA A CIKIN TEKU. Bayan na dawo gida daga tafiyata ta biyar, sai na ci gaba da sheke ayata, ina more rayuwata daga dukiyar da na tara wadda ba ta da alamun karewa. Ana nan rannan sai wasu abokaina fatake suka kawo mini ziyara, muka zauna muka yi ta hirar duniya, da labarin tafiye-tafiye. Daga nan sai bakin halina na son shiga duniya ya motsa, na ji babu abin da nake so kamar in shiga duniya, in gano kasashe da mutane da tadojinsu. Daga nan sai na yanke shawarar zuwa fatauci. Na tafi kasuwa na saisayi kayayyakin da nake bukata, na hada haja na kulle ta wuri daya. Na yi ban kwana da mutanena na nufi birnin Basara tare da hajata. Na iske jirgi zai tashi da fatake, na biya kudi na sanya kayana tare da fatake. Da aka gama shiri tsaf, sai jirgi ya motsa cikin teku. Muka bar birnin Basara cikin aminci, muka tsunduma cikin teku bisa ga kudirar Ubangiji madaukakin Sarki. Muka yi ta tafiya mu shiga wannan gari, mu bulla wancan, mu shiga wannan tsibiri mu shiga wancan, muna saye muna sayarwa muna kuma ganin al'umma daban-daban, kowace da irin al'adunta. Ba mu gushe ba cikin wannan hali, wata rana ta daga cikin ranaku muna cikin tafiya cikin teku, gaba ruwa, baya ruwa, dama ruwa hagu ruwa. Kwatsam sai muka ga fuskar Madugu ta canza, ya yi wata irin kururuwa mai firgitarwa, ya cire rawaninsa ya yi jifa da shi cikin jirgi. Ya yi tsalle ya yi faduwar 'yan bori, ya rika marin fuskarsa yana tuge gemunsa, muka ji yana cewa, "kaicona! kaiconku 'ya'yana! Shi ke nan kun zama marayu!" Muka zagaye shi duk hankulanmu a tashe, muka tambaye shi, "ya Ra'isu, menene ke damunka?" Ya ci gaba da kuka bai kula mu ba, muka yi ta rarrashin sa, daga nan sai ya ce mana, "ku sani ya ku jama'ar fatake, jirginmu ya bar hanyar da muka sani, mun shiga wani tafarki wanda ban san shi ba. Idan ba Allah ya ji

Chapter 6 of 8